Share this page
baci, "Karya kakeyi wallahi baka isa ba, Sarki harni ce zaka cema yarinyar can matar kace har kana min kurari, to ka sani bazan bari ka k'ara kusan tarta ba domin bazan tab'a yarda in wulakanta a cikin kawaye na ba, kamar yanda ba kowa yasan cewa mijina yayi aure ba haka auren zai dauwama har sai ka gaji da ganin ta ka saketa, sannan kuma kamar yanda ka canza shawara nima na canza nawa shawaran na barin ta zauna da kai a matsayin yar aikin gida, yanzun kam tabbas dole ta koma gidan ubanta. Wannan safiya dai abubuwa ne marasa dad'in fad'uwa ko a baki suka afku a gidan Sarki, Teemah tayi alwashin raba auren Meenal da mijinta yayinda shi kuma yaci alwashin cigaba da zama da matar shi harma da kudurin maida ita cikakkiyar macen aure, Rai babu dad'i Teemah tabar gidan a kuma ranar ta tattara ta koma Lagos ba tareda tayi sallama da kowa ba. 🀣🀣🀣Nace mu fad'ama teemah gaskiya ne ko kuma mu barta da halin ta? πŸ€”. Please I really need to see your comment akan abunda ya faru #team SarkiπŸ₯° #team AK #Aminatu & Teemah *UMMIEE ZARIA*✍🏼 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: βšœοΈπŸ”±πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *DANGINA!*πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ”±βšœοΈ ~{{MY FAMILY}}~ *FREE BOOK* *RUBUTAWA* *UMMIEE ZARIA*✍🏼 """"Page 39.... Gaba d'aya tunani sun cin kushe mata kwalwa, domin dai duk yanda taso ture kalaman na Teemah abun ya gagara, harta da baccin da takeji kafin shigowar su yanzun kam tsaf shima baccin guduwa yayi ya kama gaban shi, "To kodai da gaske ne kenan da mutane ke cewa kishiya nama kishiya asiri? Ko kuma ta raba ta da mijin ma gaba d'aya, dan kwana kin baya bata mantaba haka wata kawarta a makaranta ta dunga ciwon da aka rasa gane kanshi, sai da tayi kamar zata shek'e dan maganin asibity ake tayi ya zamana ana magani daban cuta daban, da allah dai ya nufa cewar kwanan ta na gaba tana warkewa ita kuma kishiyar ta kwanta wani irin kazantaccen jinya, jinyar nata ne kuma ya zama sanadin tonuwar komai. kuma wallahi kishiyar nata malama ce sosai kowa yake ganin girman ta. To itafa allah ya sani ba komai take tsoro ba, illah dai kar azo a turo mata wani mugun abun duk da komai ya samu bawa nufin Allah ne kuma hakan yana daga cikin kaddarar shi, dan haka wannan karan kam dole ta magantu ko ba tama kanta yak'iba dole zatama d'an uwanta ko badan alak'ar aure ba shi d'in jinin tane. ya kamata ta samu wanda zata tattauna maganar nan dashi ko dan ta samu mafita tasan ta yanda zata bullo ma al'amarin, domin dai shi wancan Sojan tun zuwan ta gidan nan tana lura ana idar da sallah yake tahowa gida abunshi, bata tunanin yana tsayawa domin yin azkar bata sani ba ko inya dawo gida dai yana yin shi a d'akin shi, to dan Allah mutum ya tsare azkar d'in ma basai Allah ya kareba, balle kuma ace bakayi gaba d'aya, Ita dai yanzun damuwarta shine to wa zata tunkara kai tsaye? Malam shine mafi kusanci da ita a koda yaushe in tana da wani damuwa koda ko a fannin karatun tane har gobe shine kan gaba a al'amuranta, to amma yanzun kam batajin zata iya tunkarar shi da maganar nan, to jama'a in taje me zata ce mai?, cewa zatayi tun auren su har yau mijinta bai tab'a kwanciyar aure da ita ba ko me zata ce? Su Meelat kuma tasan ko ta fad'a musu babu wani mafitan da zasu samar mata,dan su kullum laifinta suke gani, a cewar su wai inshi bai neme taba ita taja hankalin shi mana tunda Allah dai ya albarkaceta da kayan alatu, kuji wani rashin mutunci wai itace suke nufin takai mishi kanta kut, jama'a wannan abun kunyan ma in duniya taji ai bata ba k'ara fita gida wallahi to Ina zata kai abun kunya fisabilillahi shi da yake namiji ya iya rik'e kanshi sai ita kamar wata yar wiwi, to ai ko bushe bushe ta fara batajin zata iya aikata wannan aiki irin na tsofaffin dilolin kayan marisa. "Mommy " Zuciyar ta ta ambata mata, "Eh Mommy ya kamata ta tunkara to amma ta Ina zata fara mata bayani bayan basu saba hira da ita akan komai daya shafeta ba, "Hajiya Innah" Yes Hajiya inna zata dosa kai tsaye koba komai dama ita tasan abinda ake ciki tun tuni in yaso shi kuma Malam zatace mishi dai yasa Sarki a addu'a, tasan in ta fad'a mishi hakan ba lallai ya tsanan ta bincike ba, Komawa tayi ta kwanta tana ta faman sak'a da warwara, Kai jama'a Ina ma amfanin auren mijin wata!, Yanzun nan fisabilillah inda saurayi aka aura mata ina zata fuskanci wadan nan abubuwan, aure shekara da shekaru babu wani cigaban da aka samu, wai dan mafa ba gari d'aya suke da wancan mahaukaciyar matar ba dan tasan da gari d'aya suke tofa da tuni anyi wacce za'ayi kowa yasan matsayin shi, dubi fa yanda da sanyin safiyar nan tazo ta hautsina mata kwalwa da hayaniyarta na banza, ko ita ce mata akayi shi mijin nata yana gaban tane ko koh? Ai wallahi Allah yasa ta k'ara gigin maimaita zuwa mata gida da asuban fari yasin sai ta d'auki mataki da kanta tunda shi mijin tsoron ta yakeji, Gaba daya ma sai taji zaman gidan ya sire mata arai dan wallahi dama tun tuni tana tausar kanta ne dan dai ta samu taga ta kammala karatun ta dan tasan koba komai igiyar aure darajar shi katangace ga d'iya mace indai zata rik'e darajar da kyau, tasan inda bata da aure tofa ko hidimar samari na iya sawa hankalin ta ya rabu gida biyu, amma yanzun hankali kwance take karatun ta dan ta kama kanta sosai babu wanda zaiga fuskar ma da zai tareta da batun wani shashanci, Amma kam tabbas tana gama karatun ta maganar rabuwa ne! , tunda ba sonta yake ba falillahil hamdu gara su sallami juna atoh batayi lalacewar da zata rasa mijin aure ba, a baya can ma daba cikakken hankali da nutsuwa take daba anyi rububin ta balle kuma yanzun ai tasan sai ta h'ada go slow, Sauka daga kan gadon tayi ta isa gaban pic dinta da suke mak'ale jikin bango, sai da ta gama k'are musu kallo tsaf sannan ta juya zuwa gaban mirror nan ma taci gaba da kallon kanta da irin suffar da Allah ya mata, Fari da idanuwan tayi yayin da ta k'awata fuskarta cike da murmushi, A bayyane ta furta. "Oh Allah na gode maka da kayoni kyakyawa son kowa k'in masu hassada," Hannun ta ta maida kan gashinta dake tufke a tsakiyar kanta ta d'aure shi da ribom, kamo ribom din tayi ta janye shi kamar jira gashin keyi domin tana cirewa kuwa gashin ya watsu a bayan ta wasu kuma suka dawo ta gefen fuskan ta. Duk'ar da wuyan ta zuwa baya kad'an tayi sai ta girgiza kan nata wanda hakan yaba sauran gashin da suka zubo a fuskan ta damar komawa baya suka had'e da sauran suma. Lallai zanyi wulakanci zan kuma gwara kan yan maza a duk ranar da allah yayi na samu yancin da wannan auren jeka nayin kan ya guntule, Domin kam babu ni babu kuma auren mai mata rashin auren mai matan kuma bayana nufin k'in kulasu bane, No zan dai rike musu zuciya da aljuhu ne ta yanda zanyi ta walagigi dasu har sai na gaji dan radin kaina kafin in sallama su! K'alu bale gareku matan dake ikirarin cewar basu ba zama da kishiya, domin alqawari nane sai na firgita muku rayuwa, abun nan da kuke ikirarin cewa da kishiyar gida gara ta waje dashi zanyi amfani wajen tabbatar muku cewar da kishiyar waje gara ta cikin gida. Dan haka ga shawara kyauta zan baku ko wacce mace ta rike wuyan mijinta dam, dan yana kuccewa ya shigo hannu na ya kad'e, domin ni din nan.. Zan zoma duniya da sabon salon zawarci, domin dole in gigita yan maza da salona, tsoho ko magidanci basu a layina, bazan k'ara mai maita kuskuren da nayi na farko wajen auren mijin wata ba, wannan karan nida kaina zanyi yak'in ganin na tsamo wanda ya cancanta, bana son ragon namiji ba kuma nason wanda ya cika fara'a ko kuma mai yawan wasa, Cikakken namiji nike so mai cikakkiyar izza da aji, in son samu ne zanfi son wanda mata ke shakkar tun karar shi ta yanda ko bayan aure zan samu salama nasan zuciyata bazatayi ta bugawa saboda tsoron halin da zai kasance a duk sanda ya fito waje ni ina gida ba. Komawa tayi ta zauna a gefen gadon tana murmushi. "To yaushe auren zai mutu da har zaki samu cikar burin ki?" wata zuciya ta tambaye ta. Sai da ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi tana tallabe fuskanta cike da rud'ani ta amsa da cewa. "Duk ma yanda zanyi auren ya mutu sai nayi, auren biyayya ne dama kuma nayi biyayyar tuni, a yanzun kam bamai mani dole akan in zauna a wajen da ba'a tab'a kallo na da daraja ba" Sallamar Sarki tareda shigowar shi cikin d'akin kai tsaye ne yayi silar katsewar hirar dake gudana tsakanin ta da zuciyarta. Gefen gadon shima ya nema ya zauna inda take zaune yana mai kare mata kallo, Kamar yanda itama take binshi da kallo tun shigowar shi har zuwa zaman da yayi a gefen ta dan abune wanda bai tab'a faruwa ba wai Sarki ya shigo d'akin ta harma ya nemi waje ya zauna, domin dai sau tari dama in kunga ya shigo d'akin to sallahun wani aikin zai bata a tsaye kuma yake tsaya mata har ya fad'i sakon, baya kara b'ata lokaci kuma Bayan hakan yake komawa inda ya fito, tun daga shekarar auren su har zuwa yau din nan kuwa. Shine ya yanke shirun nasu da cewa. "Abinda ya faru a gidan nan yau, Ina son ya tsaya a cikin gidan nan, ma'ana bana son kowa ya samu labarin komai daya farun, Ina fatan kin gane bayani na?" Galala tabi shi da ido tana kallo. Lallai nema mutumin nan kujimin wani k'arfin hali fa, wato so yake tayi shiru da bakin ta karta fad'ama kowa har sai matar shi taje ta had'o wani mugun abunta akan su, ita in abun a iya kanshi zai tsaya mai zai dame ta? To amma wannan batun fa akanta akeyin shi dan haka wallahi bazatayi shiru ba ita kam. "Waike mai yasa kika raina mutane ne? Sai mutum ya dunga magana dake kina mishi banza!" Tsam ta tashi daga inda yake ta koma can karshen gadon, "To aini ba nice na b'ata maka raiba balle kazo ka sauke a kaina, kuma ai ita matar taka ba yau ta fara zuwa gidan nan ta fad'amin magana ba, kaji na tab'a kai karar ta a wani waje ne? Kuma nidai kaja mata kunne ta dena zuwa min gida in ma neman ka take ai akwai waya basai ta kiraka ba, shine zata zo ta hana mutane baccin safe, kuma miji indai nata ne nima bana so atoh gara ma mutum ya sani tunda shima baya so to a sallami juna kawai kowa yaje yayi rayuwar shi," Ta k'arasa fad'a da kunkuni, Sai dai kunkunin nata bai hanashi jin abinda take cewa ba, duk wata kalma data furta tsaf ta shiga kunnen shi. "Dawo nan inda kika tashi ki zauna!" "Nidai ka tashi ka tafi nifa ko lafiya ma bana da ita bacci zanyi kafin anjima" "Likitoci na ciwo ne dama?" Ya tambaye ta "To ai likita ba mala'ika bane da zaik'i yin ciwo" "To in kin kwanta wazai had'a kayan karin?" Babu b'ata lokaci ta bashi amsa da "matar ka mana" "Oh ke kenan?" "Aini yar gadin gida ce, ita dai Gimbiyar nike nufi" Bai k'ara tofa komai a maganar taba ya mike da niyyar yabar d'akin dan yaga alamar itama wannan hautsina mishi kai zatayi inya biye mata. "Kisha magani to kafin ki kwantan, Allah ya k'ara lafiya" Bayan fitar shi mai makon ta kwanta din kawai sai taci gaba da aikin gyaran d'akin data fara a haka har ta gyara duk inda yake buk'atar gyara a gidan Bayan ta gama kitchen ta fad'a ta dafa ruwan tea ta soya kwai ta dawo falon ta karya sannan ta koma d'akin ta ta shirya ta fice a gidan domin shima gogan ya fice a gidan tuni tasan kila yana can wajen lallashin Gimbiyar dan kartayi bindiga, Sau uku ta gwada kiran number din Hajiya amma babu Kira d'aya wanda yaje, a gurguje ta shiga gidan su ta gaisa da mutanen gidan bata shiga sashen suba dan tasan bazata iske Mommy ba taso ganin Malam sai dai shima yayi fitar safe zuwa wajen wani sa suna kuma bai dawo ba, tasan kuma inta zauna jiran shi zata iya yin latti dan karfe 10 ake nema yanzun, ga kiran dasu Meelat ke mata tun d'azun. Bawai dan ta gama abinda zatayi bane a cikin makarantan ba, sai dai uzurin da take dashi nason zuwa wajen Hajiya kuma so samu dai tayi zuwan ita d'aya dan su samu damar tattaunawar su da kyau, bawai kuma dan bata son su Maryam su san maike faruwa bane, ah ah tasan in sun sani a yanzun tabbas hanata zuwa zasuyi, dan haka sai ce musu tayi bata jin dad'i tana son zataje ta amshi wani magani a hannun Hajiya daga can kuma akwai inda zasuje da Mommy Hauwa, sunyi mata fatan samuwar lafiya yayin da suka rakora har bakin motar ta sai da ta bace ma ganin su sannan suka koma cikin makaranta. A hanya ma tayi ta kiran number din sai da kyar ta sameta, "Hajiya kina gida kuwa?" Ta tambaya Bayan sun gaisa, "Ina nan me zaki kawo mun?" "Ni babu abunda zan kawo miki ganin nan dai a hanya" "To Allah ya kawo ki lafiya," Koda ta isa sashen Hajiya Jummai ta fara wuce wa acan tayi sallah taci abinci sannan ta k'arasa sashen Hajiya, Yau dai da alama Hajiya zaman d'akin ne ya motsa domin dai bata falon ta inda ta saba zama, can kuwa ta isketa a d'akin ta ta baje wad'an su takardu kona miye oho, Waje ta nema ta zauna, "Hajiya ya d'akin naki yau naji ya d'ume da gumi ne? Bakya jin zafi kike zaune baki kunna ko fanka ba," "Ai dole kice zafi tunda kin fito falon Jummai dake bulbula ac da fanka duka suyi ta aiki ita ko tsoron kar sanyi ya kamata batayi, Niko da tsufana bazan yarda in k'ara gayyato ma kaina wani ciwon da yarana zasuyi ta faman jinya ba, insha Allah da kwari na zan mutu, Ya akayi ne nasan tunda kika kirani kafin kizo nasan akwai wani abun, meya faru?" "Akwai Hajiya kuma abubuwa sun faru yau, sai dai kuma kafin in fito shi Ya Sarki yazo har d'aki ya sameni aka cewa abunda ya faru in barshi a cikin gidan ma'ana kar in fad'ama kowa" "Yace miki karki fad'ama kowa kuma shine ni kika d'auko kafa kikazo dan ki fad'amin? To amma tunda kinzo ai bazan kore kiba miya faru ne haka?" Gyara zama Meenal tayi ta koro ma Hajiya tsaf abinda ya faru harda ma maganganun da Teemah take fad'a mata aduk sanda suka had'u, dama ikirarin da tayi yau cewa zasuga abunda zai biyo baya. Salati da sallallami Hajiya ta d'auka tana kankance ido cike da masifa take cewa. "Amma dai ke koh Aminatu kinji haushi, wallahi kin dai ji haushi albasa batayi halin ruwa ba, Ina ce komai nawa kikayi gado kamar yanda kikaci gadon sunan, Innah ashe da saura, yanzun nan ki zauna har wata kishiya tayi asubancin shigo miki gida ta fetsa kalar nata rashin mutuncin kina cikin gidan a raye kina kallon ta baki shek'a da gudu zuwa cikin kitchen din ki kika d'auko tabarya kikayi ma kanta fashin kwakwa inya so duk abunda zai faru ya faru ba, Ah gaskiya baki kyauta min ba, ni da wannan zancen da kika kawo min ai zanfi farin ciki in kirana zaman sulhu akayi police station Bayan kin rotse mata kai wallahi, Ke wai ma tsaya, Ina magungunan da kwanakin baya nace ki dunga zubawa a binci in zakiyi girki? Kar dai kice min duk uban wahalar da nasha wajen ganin an kammala had'a muku maganin nan a banza ya tashi bakiyi amfani dashi ko sau daya ba?" Ta tambaya tana tsare Meenal din da kallo, Ita ko sosheΒ² ta kamayi alamun rashin gaskiya, hakan ne kuma yaba Hajiya amsar tambayar ta cewa Meenal din batayi amfani da maganin ba. "Wai a Ina kikayo gadon sakarcine Meenal? Kin san maganin miye na baki kuwa? Maganin karin ko wani irin asirine fa, da zarar Allah yasa aka dace sai kiga da mutum yayi amfani dashi duk wani mugun abun dake jikin shi sai ya warware cikin kankanin lokaci kuma insha Allah wani bazai k'ara cin galaba akan ka ba, Tun wancan lokacin da kika bani tabbacin babu abinda ya shiga tsakanin ku nike tsaye kanki dan ubanki wajen amsar miki taimako ashe ni kikema kallon shaΒ² Ina ta gantalin ganin Allah ya tsareki daga sharrin kishiya, Ka tseta Meenal tayi da cewa, "Allah Hajiya duk wanda kika bani dan ni inyi amfani dashi nayi, na wajen nashi ne kawai tsoro yasa ban zuba mishi ba gudun kar wata rana ya gani yayi zaton ko Ina da nufin cutar dashi ne" "Eh ke baki da nufin cutar shi amma ai shi gashi ya cusa ki a cikin gida ya kafe kamar hoton enlargement, baki mishi amfanin komai saina gyaran gida da girki, Ita kuma dan ubanta ki barni da ita badai takamar ta matsafa ba, to mu bama tsafi amma mun yarda da kudurar ubangiji, dan haka lokaci yayi da nata wasan zanje karshe, su magungunan da nike bakin ya kikeyi dasu? " Suna nan a cikin magunguna na, To abunda za'ayi yanzun tashi kije maza ki had'amin kansu, zan aiko a amsa min anjima ko kuma kilama in shigo unguwar naku da kaina dan na dad'e banje ba, kuma bance ki fad'ama kowa abinda yake faruwa ba" "Hajiya" Ta kira sunan sai kuma tayi shiru, "Ya akayi akwai wani abun ne kuma?" Hajiya ta tambayeta. "Hajiya ni so nike ya sakeni, kinga baya sona nima kuma ba son shi nikeyi ba, nidai gara ya sakeni kawai zaman da nayi da Allah ya bada lada," A dar dar tayi maganan dan bata san yanda Hajiya zata fassara maganar nata ba. "Baki fara son shi ba kike nufi duk wannan shekarun da kukayi da aure? " "Hajiya ni ban tab'a jin son shi a zuciyata ko sau d'aya ba" "To Ina amfanin ka zauna da wanda baka so har karshen rayuwa, ai tunda har kin tabbata bakya son shi kwantar da hankali yar nan indai Ina raye an gama miki dole, wannan aure kam sunan shi matacce insha Allah dama kaddara ce tasa aka d'aura zaren to yanzun kam nice zanyi tsayin daka wajen tsinke shi, amma dai karki tada hankalin ki a yanzun dan dole mubi komai a sannu, dan in muka matsa ita waccan matar tashi gani zatayi kamar ta samu nasara akanki kenan, Yanzun abunda zaifi shine mu maida hankali wajen karya kadarin ta, kinji ko yar albarkha, ni dan dai ma kince baki sone da sai ince kiyi hak'uri kiyi zaman ki a gidan ki, dan yanzun dai ko kin fito ya riga ya b'ata miki suna kowa kallon bazawara zai dunga miki" "Nidai Hajiya koma me za'a kirani na yarda amma na gaji da auren nan haka" "Yo yar nan tunda kikace kin ganji yanzun kam ai babu dole, Allah dai yayi maki zab'i mafi alkhairi. Bayan baro warta gidan Hajiya koda ta dawo gidan su Sarkin ta shiga suka gaisa da jama'ar gidan kafin ta fito ta shiga gidan Malam, Tun tana gidan su take ganin kiran Sarki a wayar ta amma tayi kememe tak'i d'auka dan tasan bazai wuce yace abinci yake nema ko wani abun yake buk'ata ba, Sun dan taba hira da Malam a cikin hirar ne kuma ta sako mishi zancen addu'ar da take so ayi ma Sarki, Shiru yayi yana nazarin ta, amma ganin bata mishi wani k'arin bayani ba yasa shi amsa mata da cewa za'ayi insha Allah, Bayan ta shigo gidan ta dakin ta ta wuce kai tsaye taje ta ajiye tarkacen data shigo dasu sannan ta kama hanyar zuwa wajen Sarki, Da sallama ta shiga sai dai kuma bashi a falo, tayi kamar zata juya sai kuma zuciyar ta ta mata ishara da cewar ta duba dakin baccin shi, Tun daga cikin corridor d'in da zai sadaka da d'akin nashi ta fara jin wani irin nishi nishi wanda ta rasa gane kanshi, A haka dai tayi karfin halin k'arasawa ta bud'e kofar d'akin ta shiga bakin ta dauke da sallama, Abunda idanuwan ta yayi tozali dashi ne yasa zuciyar yayi kwance kwance ya yanke ya fad'i har wayar hannun ta da Hajiya ke kira ita kuma take kokarin Amsawa ya kucce daga hannun ta zuwa kass........... Babu editing duk inda kukayi karo da mistake please ignore it 🀨. Huhuhuhh, bafa ayi komai ba tukun yanzun ne wasan zai soma. Toya kukaji page din yau, Jiya banga comment da yawa bafaπŸ™„ *Ummiee Zaria*✍🏼 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: πŸ”±βšœοΈπŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *DANGINA!* πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦βšœοΈπŸ”± ~{{MY FAMILY }}~ *RUBUTAWA* *UMMIEE ZARIA*✍🏼 `````` *Page 40*.... Da gudu ta k'arasa shiga cikin d'akin bakin ta na faurta kalmar Innalillahi wa'innah ilairir raju'un.... Haka taci gaba da maimaita wa, a rud'e ta doshi inda yake kwance yana ta faman mulmule akan tile's d'in d'akin domin alamu sun nuna cewar tsabar azabar ciwone yasa shi fad'owa daga kan gadon badan ya shirya ma hakan ba. "Ya'ya! Ya'ya!! Ya'ya mai ya same ka? waiyo Allah na dan Allah ka tashi meke maka ciwo?, innalillahi dan Allah ya'ya ka tashi dan Allah muje asibiti, yama zaka zauna a gida Bayan kasan baka da lafiya! Ni ai ban san cewa ciwo kakeyi shi yasa kake ta kirana ba da nazo tun d'azun, kasha magani kuwa? Ina kake ajiye maganin ka in d'auko maka? meke maka ciwo ka fad'amin sai in d'auko maka maganin a d'akina in baka dashi anan" Take tambayan shi cikin kuka domin duk ta rud'e wannan shine karo na farko da take ganin zafin ciwo yasa Babban Namiji mulmula a kasa, Shiko tsabar azabar ciwo ne yasa gaba d'aya ma baya gane mai take cewa, dan sosai yake jin ciwon bada wasa ba, Shi bai san me yasa a cikin kwanakin nan yake yawan fama da sha'awa ba,domin dai a iya sanin shi har yazo garin nan ya gama kwanakin da zaiyi lafiya lau yake komawa ba tareda ko sau daya yaji cewar yana buk'atar keb'ewa da ita ba, dan sau tari sai ma inya koma Kadunan ne abun ke damun shi har sai yaje Lagos ya sauke damuwar shi sannan yake jin daiΒ², To amma yanzun kam abubuwa sun canza mishi domin wata rana sai yaji kamar yaje ya nemi yarinyar nan sai kuma ya rasa kwarin gwuiwar shi, yayi zaton in Teemah tazo zai sauke a kanta sai dai hakan bai samu ba, wannan dalilin nema yasa ranar ya nemi Teemah sai kuma akayi rashin sa'a bata cikin tsarki, yasan za'a iya samun matsala inya kwana a wajen ta shi yasama ya gwammace ya dawo gida ya kwana a ranar, Ita kuma tayi zaton daya kwana a gida ya nemi Meenal ne shi yasa tazo tayi nata kalar haukan daga karshe kuma gashi ta tattara ta tafi ta barshi da bala'in da bai san inda zai samo mafita ba. Shi dai ba dan iska bane domin dai a can baya da yayi rashin ji ma ba'a hayyacin shi yayi ba kuma a iya shayeΒ² ya tsaya baiyi neman mata ba har zuwa sanda yayi aure, balle kuma yanzun da har yake da yara sun zama yan mata, to shida keda yan mata Ina zai yarda ya tab'a yar

Chapter 35 of 92