Share this page
ba'a dauketa da daraja ba a matsayin ta na uwar Meenal sai yau da biki ya rage ko sati uku bai kaiba ne za'a fada mata, sannan saboda tsabar son kai shine Mukhtar zai wani zo yana mata dadin baki, to harma akwai wani wanda zaiso Meenal sama da ita uwarta ne? Itafa ta kawo Meenal din duniya da bata haifota ba har shi Malam din zai sota ne, kai soyayyar ma taci uwarta wani irin sone wannan za'a tauyema yarinya hakkin ta sannan ace wai soyayya. Murje murje ta farayi a kokarin ta nason ta kwace daga rikon daya mata, "Ka cikani nace, ka cikani yau sai Malam ya fad'amin in shi yayimin nakudar Meenal, kullum yana min abubuwa ina shanyewa saboda kai kanin shi da kuma darajar jinin dana had'a dakai shine yau kuma Meenal wai ita zai aurar saboda tsabar kiyayyar shi gareni hakan yasa tun tasowar yarinyar nan sai da yasan yanda ya juya mata kai ya cire zuciyarta kwata² akan yan uwana, Nina haifeta amma yafini sanin damuwar ta, ce muku akayi hakan bayamin zafine ko a tunanin ku bana son tane dana kauda kai akanta na bar mishi yana yanda yake so da rayuwarta nayi hakan ne saboda in daraja shi a matsayin shi na yayan mijina, wai aure! Aure fa amma sai yau ake fadamin ni uwar ta ashe ni bani da wata daraja kenan sai na haihuwarta da nayi, naga su sauran yaran tuni aka sanar da iyayen su batun auren su." Mikewa tayi daga kasan da take zaune tana ta murje² tana zuba rikici ta koma inda yake zaune ya zabga tagumi yana binta da kallo, "Wa zaku aurama yarinya ta? waye mijin? Badai tsohon itama za'a aura mata kamar sauran ba? Abban su ka bani amsa waye mijin Meenal d'ina? " Shidai yau ya shiga ukun shi, shi bai kar zomoba amma rataya ya zame mishi dole, gashi komai akan shi yake karewa, ya dad'e baiga Jidda ta fice a saiti ba wannan dalilin yasa ya kasa tun karanta da batun auren. "Sufyan ne zai aureta! " "Wanene kuma wani Sufyan? Kayimin gwari² yanda zan gane Abban su dan wallahi bazan zuba ido a nakasamin rayuwar yarinya a aura mata tsoho ba!" "Sufyan din mu Sarki dai da kika sani yaron Uwar gida da Y'aya Sulaiman" Ai kamar wacce ya caka da allura haka ta wani irin zabura ta fara kai kawo a cikin d'akin sai faman mai maita sunan takeyi da alama ta manta waye ma ake kira da Sarki sai zuwa can kuma sai gashi tayi tsaye cak kamar wacce aka danna ma Pause ⏸ "Sufyan Sarki" ta maimaita sunan tana zaro idanuwa, "Wai Sarki dai naku Sojan ruwa kake magana akan shi ko wani daban? Bai iya amsa mata da fatar bakiba illah gyada mata kai da yayi alamun eh shifa. "Sarki dai dakoh iyayen shi yanzun baya tunawa da sha'anin su balle kuma yaran daya haifa Wanda suke hannun uwar shi shid'in kuke shirin aurama yata taje tayi Kishi da mushrika Wanda kowa yasan da karfin asiri ta dauke hankalin shi akan kowa? To indai shine ko bazan taba yarda Meenal taje gidan da sunan zaman aure ba balle har tayi Kishi da matar shi, akan hakan kuma na shirya batawa da kowa ciki kuma harda kai daka Haifeta, in auren ya zama dole ku bata wani in ma baku dashi niko a cikin yaran yan uwana zan had'a ta da wani amma bazan yarda Meenal ta auri Sarki ba" Tana gama fadin hakan ta fice daga dakin nata zuwa nasu Meenal........ Share Please #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen. ```Page 28 Bata tsaya jiran komai ba ta bankad'a kofar d'akin ta shiga sai dai kuma tayi rashin sa'a domin ko babu kowa a cikin d'akin, Shiko Baba Auta data fito ta bari a zaune yana sakar zuci, domin tunda ta rikice din nan salati kawai yake yana sanar ma ubangiji akan Allah ya sanyaya mata zuciyarta yasan duk abunda ta fada akan gaskiyarta ta fad'e shi amma a yanzun kam baya tunanin akwai wani abun dazai hana faruwar auren nan anan kusa hakuri kawai zasuyi subi yarsu da Addu'a Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, tunanin cewa karfa Jidda taje ta samu Malam garan gatsau d'in nan tace bata amince da batun auren ba yasa shi mikewa ba shiri ya fita daga d'akin sai dai yana fitowan itama ta fito daga d'akin su Meenal, bata kulashi ba ta dawo fuuu ta kara komawa cikin d'akin ta da niyyar d'aukar waya ta kira Meenal din, ganin ta koma cikin dakin sai shima ya bita dan gara komai za'ayi ayishi cikin d'aki koba komai d'aki yafi waje sirri ai, "karki kira Meenal domin bata san da maganar ba, bama ita kadai ba kaf gidan ba kowa ya sani ba illah mu, kimin wannan alfarmar karki fada mata yanzun in lokacin yayi nida kaina zan fada mata" Durkushewa tayi a wajen tana cigaba da fidda hawaye take cewa, "Ba'a kyauta min ba wallahi wannan ba adalci bane Abban su, ni bazan yarda da wannan tsarin naku ba domin kaf a tsarin auren nan kowa yasan yata ce zata cutu, Meenal dina zakuma auren cushe zaku kaita inda kuka san kishiyarta bazata bari tayi daraja a idon mijin ta ba, sannan ace wai soyayya shi Malam in son gaskiya yakema Meenal aishi ya kamata ya dakatar da zancen auren bawai ya hada auren ba, nidai ban yarda ba bazan bada Meenal anakasa min ita a banza ba" Dagota yayi daga kasa zuwa cikin jikin shi yanaci gaba da rarrashi, "Kiyi hakuri Jidda nasan dole ranki zai baci hakan yasa saida na nemi afuwar ki kafin in fad'a miki abunda ke faruwa, na b'ata darare masu yawa ina kasa bacci saboda tunanin mako mar Meenal da kuma yanda zan tunkare ki da batun, sai dai ki sani ina da yakini akan Malam bazai tab'a yanke hukuncin da zai cutar da Meenal ba, sannan ina mai k'ara baki hakuri kamar yanda kika saba yimin biyayya wannan karon ma ki k'ara akan nada domin bana son ganin ki cikin tashin hankali, ki dauka wannan auren kaddarar Meenal ne sai kibita da Addu'ar Allah ya bata ikon jure ma zafin kaddarar Allah kuma ya tabbatar da alkhairi a cikin auren ya kauda fitina" "Abban su so kakeyi kace inyi shiru insa ido akaimin yarinya gidan kishiya mai asiri?" "Komai asirin ta Jidda bata isa tayi abunda Allah bai kaddara faruwar shiba, duk abunda Allah ya tsara zai faru a cikin rayuwar Meenal ko tana gaban mu wannan abun saiya sameta, ki duba irin wahalar da yarinyar nan take sha na ciwon mara duk wata yayin al'adarta kodan shi ya kamata ki mata fatan alkhairi kinji Jiddatulkhair" Kunsan ance tsakanin mata da miji sai Allah domin ko haka Baba Auta yasa Mommy Hauwa a gaba sai da ya rarrashi matar shi tsaf ya kwantar mata da hankalin cewa babu abunda zai faru domin ko a nan gidan Sarki na cikin unguwan Meenal din zata zauna, dan yaga alamar zaman Meenal din da kishiyarta ne ke tada mata hankali, "Amma dai Abban su kai zakaje ka gayama hajiya batun auren koh? Dan wallahi nidai bazan je insha fada akan laifin dabani ce na aikata ba! " Ta fad'i hakan tana mai kureshi da ido, murmishi yayi a cikin zuciyar shiko cewa yayi uwar Meenal ma ta amince balle kuma kakarta, amma a sarari sai ya bata amsa da cewa "Koni bani da kwarin gwuiwar tun karar Hajiya a yanzun abu daya dai zanyi shine zan kira Usman in fad'a mishi halin da ake ciki shi kuma sai ya isar da sak'on kunnen ta dan hakan zaifi sauk'i, ke kuma sai ki kira sauran yan uwanki ki shaida musu halin da ake ciki" "Abban su sati uku fa biki kuma ban shirya komai ba! " "Shirin auren diya mace ai dama na ubane kin san kuma koda ace ba Meenal bace Malam zai aurar shi mai d'aukar dawainiyar komai daya danganci bikin auren ne balle kuma auren Yar gaban goshin shi dan haka kisa ranki a inuwa ki koma gefe ki zama yar kallo" "Wani irin in koma gefe in zama yar kallo kuma ai kasan dai ba'a biki ace uwa bata fitar da nata kayan ba" "Baida komai tunda kin dage zan tura miki kud'i sai kiyi naki siyayyar, ina fatan hakan yayi miki? " "Eh hakan yayi nagode Allah ya kara arziki bari in kira su Ya'ya in fada musu, to amma ita Meenal din fa? " Ta tambaya a marairaice dan Allah ya sani gaskiya tana fa tausayama Meenal wallahi. "Wannan kuma kece zakiyi duk yanda zakiyi dan karta gane komai har zuwa lokacin bikin dan ban son tashin hankali " A wannan ranar ba'a kwana ba sai da Jidda ta kira kaf yan uwanta ta shaida musu batun auren Meenal din sai dai bata shaida musu kalubalen dake gaban Meenal d'inba ta bari sai sun iso sai su tattauna, a kuma ranar Baba Usman shima yayi kiran Hajiya Innah ya shaida mata abunda ake ciki, Wuhuhu ina wuta ta saka Malam kuma Kunsan wacece Hajiya dan haka tayi fada tayi fada kamar ta cinna ma kanta wuta, bata iya hakuri ba saida ta dauko mota da kanta ta tuko kanta zuwa gidan Malam dan taji dalilin wannan dibar albarkha daya shirya mata, a cewar ta so yake yaga iyakarta inba haka ba har itace zaisa ranar auren jikanta bata da labari sai dai kwatsam taji wai biki saura sati uku kamar wani a wasan kwaikwayo, So yake wato yaga karshen arzikinta ta kasa fitar da jikarta kunya to wallahi ahirrr din shi dan su kudi suke binsu suna guje musu insha Allah bazata ji kunya ba komai da akema yar gata shi za'ama jikarta wato shi mai Dangi shine ya dauki jikarta yaba dan kannin shi bayan itama gata nan da zabga zabgan jikoki wanke hannu ka tab'a. Koda ta isa gidan tun daga fitowarta daga mota ta fara abunda tafi kwarewa akai wato jidalin fadanta na kullum sosai fa ta burkice ta zuba tijara son ranta ta kira sunan Malam ta kira shi da Babban kwabo wato tunda yasan uban Meenal bazaija da hukuncin shiba shine yasa zai aurar mata da jikarta babu notice tafa tata nata iya iyawarta sai dai kash bata taki sa'ar samun Malam din a gida ba sai Baba Adamu ta samu ta kuma kafe kaida fata cewar bata zuwa ko ina sai taga Malam ido da ido taji dalilin daya yanke hukuncin aurar mata da jikarta bada yawunta ba, komai isar shi dai ai ita itace ta haifi uwar Meenal kuma da Jidda bata haifi Meenal din ba ai isar shi a iya kan nashi yaran zai tsaya, Da kyat dai Baba Adamu ya samu ya bata hakuri sannan yasa cikin yaran gidan suka maidata gida, bata tafi ba saida tabar ma Baba Adamun kashedin cewa gobe²n nan take bukatar a kawo mata Jikarta gidan ta tazo ta zauna da ita na tsayin kwanakin daya rage kafin auren dan itama tana da hakki akan jikan ta, to dai Baba Adamun ya mata alkawarin goben za'a kawo mata Meenal din sannan kuma ya fada mata cewa Meenal din ma bata san da batun auren ba, Wannan jidalin na Hajiya shiya tona halin da ake ciki na auren Meenal a gidan har jama'ar gidan dama makota sukaji labarin cewa Sarki ne zai auri Meenal, Yan bakin ciki dai sunyi haka ma yan farin ciki sun yi, bayan dawowar Malam sai da ya tara kaf ahalin gidan yaja musu kunne akan cewa koda wasa baya son suyi kuskuren har da zaisa Meenal tasan da batun auren Wannan kenan. To gadai Meenal zata koma gidan Hajiya da zama na tsayin satikai, shin koya zaman nasu zai kasance ita da abokin fadan ta AK mai jama'a ga kuma hajiya a gefe, Ina labarin mutanen Lagos Sarki da matar shi, ana dai ta Shirin biki angon ma bai san meke faruwa ba, Ga kuma Teemah uwar Kishi a gefe itada ta lashi takobin cewa bata ba zama da kishiya, Moon budurwar mai gidan yan gayu, koya zataji in akace gidan nan Meenal ne zata zauna a cikin shi matsayin matar gidan? Huhuhuhh ga kuma uwar gayya Meenal ta dage sai shirye shiryen bikin kanne takeyi bata san cewa itama amaryar bace ko ya zatayi in ta samu labari ohooooo, Kowa ya hasaso amsar 🤣🤣🤣🤣 Babu editing 😰 Share Please #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen. ```Page 29 *A gurguje* Washe gari kamar yanda Hajiya ta bukata haka Mommy Hauwa ta had'a Meenal da kayan ta zuwa gidan Hajiya, hakika hakan baima Meenal din dad'iba domin a cewar ta zirga zirgan zai mata yawa a matsayin ta na Babbar ya'yar amare, dan ma Allah ya taimake ta sun riga sun kamala exam's din su gaba daya, Koda bukatar Hajiya na komawarta can Tudun wada yaje kunnen Malam baiyi musu akan hakan ba domin koba komai yasan zamanta acan din shima zaifi mishi kwanciyar hankali domin tabbas intana nan sai an samu mai dogon bakin dazai furta batun auren nata a gaban ta. Ita ko Hajiya kaf yayan ta saida ta kira takai musu karar cewa Malam ya nuna mata mulki da isa akan jikarta ya nuna mata bata da wani matsayi dan haka tana bukatar ganin su in ma bazasu samu damar zuwa ba tofa kowa ya turo da nashi gudun mawar dan tama fi bukatar kudaden da zasu turo akan zuwan nasu domin kayan yar gata takeso ta hadama jikarta dan Malam yasan cewa kullum cikin shiri take ita batayi gadon tsiya ba, to dai suma tunda Allah yasa sun san ko sunzo a lokacin ba wani tsiyar zasuyi ba domin infa Hajiya ta kafe ta kafe kenan yasa sai kudaden data bukata suka tura mata, ita kuma taci gaba da shirye shiryen ta na auren jika, Tsaf ta shiga ta fita tabi kwakwafin wanda za'a aurama jikar tata acan ne kuma tajiyo abinda batayi tsammani ba, wato ashe kiyayyar da Malam kema Jiddan ta har ya kai ya dauki yar Jidda yaba yaron dan uwan shi da matar shi ta gagari kowa! Yanzun da ace bata raye kenan haka za'ayi auren ba tareda an shirya Meenal din ba gayarta za'a dauka akaima kishiya wato taji dadin nakasa ta da kyau, to ai in sun san wata basu san wata ba ita kam da ranta da lafiyarta bazata sadaukar da rayuwar Takwarar ta, dan haka tuni itama ta zage damtse wajen neman ma Meenal din duk wani maganin da tasan na tsarin jiki ne sai da ta tanade shi, Satin farko na komawar Meenal gidan bata fuskanci ko wani damuwa ba, domin dai Hajiya bata takura mata kuma duk inda suke bukatar zuwa yawon rabon anko da katin biki Dan gidan Master ne ke zuwa yana kaisu dan sosai yakeji da Meenal din a kokarin shi nason ta bashi dama ya gabatar da kanshi a gidan su tunda gashi allah yasa har za'a aurar da kannin ta yasan koya nema baza'a hanashi ba domin shi baiki ba wallahi a hada bikin ma dana kannin nata, amma yasan Hajiyar tashi ba yarda zatayi da hakan ba sosai fa ta samu yanda take so a wajen Dan gidan Master dan sosai ya bud'e mata bakin aljihu take ta dandake kan nerori domin dai duk abunda take so jiki na rawa yake mata shi, Gashi kuma kwanan nan ta lura ba Malam kadai ba yanzun harta da Mommy Hauwa sosai take sake mata fiyeda lokutan baya domin abun mamaki kulum cikin tambayan ta abunda take so take ga yawan daukarta da sukeyi zuwa kasuwa ita dasu Meelat zuwa siyayyar kayan da take zaton nasu Raheenat ce domin dai dama ko yayyin su maza in zasuyi auren Mommy ne ke hada musu kayan auren, dan haka sai bata damu ba a zaton tasan kila dan Mommy tasan in tace su Raheenat din suzo suje kasuwar tasan ba lallai su sake jiki su zab'i abubuwan da suke bukataba shi yasa, dan haka ta zage damtse da zuciya d'aya ta maida hankali ta dunga d'aukar duk abunda taga ya mata kyau dan tasan dai auren dole ne za'ama kannen ta to amma inta bada nata gudun mawar wajen ganin an shirya musu dakunan su da kyau tasan hakan zai rage musu damuwa, Bawai kananan siyayya kadaiba hatta da kayan gado dasu kurjeru komai ita ta zaba musu sai dai abunda bata sani ba harda nata kayan ta zaba'a domin komai itama sai an tambayeta choice din ta, cikin sauk'i dai abubuwa sukaci gaba da tafiya, Biki ya rage saura sati biyu Mai Jama'a ya duro Zaria domin duk wainar da ake toyawa baya gari yaje Lagos akan wasu harkokin su, ita kuma Hajiya hidindumun data sa a gaban ta sun sha mata kai dan haka ko a waya bata tuna ta bashi labarin abunda ke faruwa ba, a kuma sati biyu da bikin ne Hajiya tasama Aminatu takun kumin fita domin zuwa lokacin ta gama hada duk wani tanadi da tayi domin gyarar jikar nata, ta kuma fad'ama harta da masu gadin gidan cewa koda wasa suka kara barin Meenal din ta fita saita b'ata musu rai wallahi. Ganin cewar Meenal ba had'in kai zata bata ba yasa ta fada mata cewar maganin ciwon marar tane ta amso mata kuma ka'idar maganin sati biyu ake shanshi kuma in an fara amfani dashi ba'a zuwa ko ina gida ake zama dalilin ma da yasa tace Jidda ta maido mata da ita nan kenan, in kuma bata bukatar ta warke ga kofa nan tana iya komawa gidan su, Saida Meenal ta kirga kwanakin daya rage mata kafin zuwan al'adarta sai taga kwanakin duka basufi goma ba, to kenan in har tabi umarnin Hajiya ta zauna tayi amfani da maganin tana sa ran kenan wannan watan lafiya lau zatayi al'adarta kamar na sauran mata, gashi kuma dama tsoron da take ji kenan domin lokacin zuwan nashi a lissafin ta zaizo a cikin bikin ne dan Haka ba komai zata jure zama dai na kwana kin a gidan Hajiya ai mai sauki ne in aka hada da wahalar da take sha duk wata, sai dai gaskiya za'a takura mata dan bata gama rabon katin biki ba amma ba damuwa tunda gasu Moon zasu iso ga kuma su Meelat a gefe, sai dai kuma ya zatayi da yan anacen samarin ta da bata amshi kudaden data yanka musu na anko ba? Wannan ma ba damuwa tunda dai ga waya shi dai Dan Master tasan shegen kwakwa gareshi dole sai yazo inda take dan ma ta gode Allah iliya dan mai karfi bayanan balle yasa mata ido, Ita fa gaba daya bata damu ba domin dad'inta kawai takeji cewa zatayi bikin kannen ta cikin koshin lafiya batareda mutane sun taru akanta suna faman yi mata sannu kamar mai ciwon mutuwa ba. Bayan dawowar AK yayi mamakin ganin Meenal kwana 1&2 a gidan batareda ta koma gidan suba dan iya sanin shi yasa inba dai Moon sunzo ba tofa bata yarda ta kwana a gidan ranar dai ya gaji da ganin nata dan Allah ya sani yarinyar nan fa ba karamin takura mishi takeyi in yana waje ba, dan yanzun ma wani sabon iskanci ta tsira da zarar ta hango shi saita fara mishi wakar da in tanayi yake jin kamar ya shako wuyarta har saita daina numfashi kafin ya saketa, wai shi yarinyar nan take ma wakar.. .. .. Turun turun tuzuru wai yaushe zaka auree. Tuzuru wai yaushe zaka aure.... Wai shi shi din nan da girman shi da mutunci da komai amma tsabar rainin da yarinyar nan ta mishine yasa har take mishi wakar tuzuru wai yaushe zaiyi aure, insha Allah duk ranar daya riketa sai ya fada mata taje gida ta tambaya shekarar Baban ta Adamu nawa yayi a duniya ba tareda mata ba in yaso sai tazo ta hada shekarun da nashi aga wayafi wani zama tuzuru a lokacin! Suna zaune a falon Hajiya tuwo yake ci kamar yanda kowa yasan yafi son cin abinci mai nauyi, "kinyi wanka da ruwan maganin dana hada miki? " Hajiya ta tambaya Meenal wacce fitowarta kenan daga dakin da Hajiya ta sauke ta, "eh nayi"ta bata amsa tana wucewa cikin kitchen da plate din dataci abinci a hannun ta, Saida yaga kulewar ta sannan ya waigo gefen Hajiya, "Me yarinyar nan takeyi a gidan nan wai?" "Ban gane me takeyi a gidan ba!" "Eh na tambaya ne saboda nasan ba zuwa takeyi haka nan ba balle kuma harta kwana gashi kuma tunda na dawo nike ganin ta a gidan kuma na tambayi bala yace min tayi kusan sati a gidan ko laifi tayi a gidan su ta gudo nan? " "Kai dai ka sani da neman ba'asin ka, yarinya ita da gidan kakan nin ta ka kama tambayar me takeyi gaskiya dai ka canza hali wallahi" Ta fada tana karkata dan kwalin kanta zuwa gefe a dai dai lokacin ne kuma Meenal din ta fito daga kitchen waya kare a kunnen ta amma cikin su babu mai iya jin abinda take cewa a wayar harta wuce su ta koma d'aki, Sai da Hajiya ta tabbatar ta shige sannan ta baro kujerar da take zaune ta koma wacce mai jama'an yake kai, duk wannan kusancin da suka samu bai wadace taba sai da tayi kasa da muryar ta sosai tana kara kallon kofar dakin da Meenal ta shiga kai da ganin yanda takeyi ko ba'a fada maka ba kasan cewar irin gulmar nan dako kuda ba'a son yaji shi take Shirin yi. "Aure fa uban ta zai mata karshen watan nan.... " Wani irin mummunar shaka romon daya surb'a a lokacin ya mishi domin har cikin kwakwalwar shi romon ya wuce, aiko sai tari ya biyo baya domin a lokaci guda yaji kurjin shi ta dauka da wani irin radadi

Chapter 23 of 92