Share this page
ya maida min yarinya bazawara Hajiya shi kenan ita bazata mori kuruciyar ta taji dad'in rayuwa kamar sauran yara ba Hajiya?" "Mmmttttwwwsssss" Hajiya taja wani uban dogon tsaki tana me kallon Jidda shekek'e cike da takaici, "Kai amma dai wallahi Jidda kinci amana ta, abinci fa kika shigo kika iske inaci, saboda tsabar rashin mutunci kika d'aga min hankali kika sa na tsamo hannuna na iso gunki a firgice duk a zatona ko wani mugun abun be ya k'ara faruwa, Ke yanzun nan saboda rashin sanin ciwon kai shine har dan wannan auren na da babu gwara ba dad'i ya mutu kikazo kika tasamu kina kuka? Nida nike zaton in kinji labari zaki yo hayan DJ suzo da manyan sifiku su kunna muyi celebration yarki ta samu freedom, To wallahi kama kanki tun kamin kisa in kullace ki, ina abun bak'in ciki anan fisabilillahi," "Hajiya auren Meenal nefa nace miki ya mutu" "Eh auren Meenal d'infa, yo shi dama auren nata irin kowani aurene da kuke tunanin zai dauwama, to ki godewa Allah domin da auren ya dauwama ina mai tabbatar miki cewa itama yar naki zata dauwama ne cikin kunci da bakin ciki domin dai tsayin zaman ta a gidan nan har zuwa ranar da na d'auko ta na kawo nan sunan ta na budurwa bai canza ba dan dai shi Mijin zuwa yayi ya jingine, ban san uwar da yake jira da ita daya ajiyeta yana kallo babu sauke hakkin aure ba, su iyayen nasu basu fad'a miki dalilin mutuwar auren bane?" Kasak'e Jidda tayi tana sauraron jawabin hajiya batareda tayi yunkurin katseta ba har sai da Hajiyar ta bukaci jin ta bakin ta, "Hajiya ni ban san komai ba d'azun ne Abban su daya shigo yake cemin Ya'ya Adamu yana son ganina, to dana jene shine ya nuna min takardar yace min takardar sakin Meenal ne kuma ita Meenal din tana nan tare dake tun tuni shine nazo" "Ikon Allah to kenan kice sai yau sukaga daman gabatar da takardar sakin, to barka da zuwa! Wato dai kinzo jin k'arin tabbaci akan batun sakin ne koh? To ina zuwa" Hajiya bata jira komai ba ta wuce zuwa d'akin ta, cikin kankanin lokaci ta dawo da takardar sakin a hannun ta, "Ina ga waccan ai iya takardar kika gani koh? To ga wata sai ki bud'e ki karanta abunda ta kunsa" Ta k'arasa fada tana mik'a mata ita kuma Hajiyar ta juya ta koma kan dinning table tana mitar ita dai an d'auki alhakin ta an yanke mata cin abinci har shayinta yayi sanyi. Mikewa Meenal tayi ta fice daga falon a sanyaye dan sosai taji babu dadi ganin Mommy na kuka a dalilin mutuwar auren ta, Dole muji babu d'adi idan wanda muke so ya rabu damu amma ba akan wanda ya auremu ya jingine a gida ba, Tasan bata son Sarki sai dai kuma hakan bashi ke nufin ta tsane shiba, saboda a iya zaman da sukayi bazata ce ga wani abu gagarumi daya aikata mata ba, sai dai kuma kowa yasan ba rabuwa ake ma kuka ba sabo ne abun kokawa, To itama dai wannan sabon na tsakanin su shi takeji a yanzun ba kuma iya kewar shi takeyi ba tana kewar abubuwa da yawa data samu ta dalilin shi, domin a sanadin shi ta samu gida, gidan da ake kira da suna *Gidan Meenal* gidan da yake nan ne take zama ta sakata ta wala tayi duk abunda take so ba tareda wani ya takura ta ko yasa mata ido ba, falon ta, kitchen d'inta, d'akin data ware danyin karatun ta, daku nan baccin ta, kayan kallon ta, da kayan jin kid'anta a lokacin da take cikin nishad'i, garden din da takanje ita da kawayen ta su zauna dan hutawa, swimming pool din gidan wanda dashi ta koyi yanda ake yin Iyo a cikin ruwa, Duka wadannan abubuwan da suke a matsayin nata, a kwanakin baya shi kenan yanzun ta rasa su saka makon mutuwar auren ta, Ita dai a wajen ta wadan nan abubuwan sune inta tuna suke mata tsaye a rai, bawai kuma dan gidan su babu ba sai dan banbancin dake tsakanin kalmomin nan guda biyu, Wato *GIDANA* da kuma *GIDAN MU* da can a gidan su ta rayu, kafin a samu ci gaba ta koma zama a gidan da ake kira nata yanzun kuma mai makon wad'ancan gidajen sai gashi ta dawo zama a gidan Hajiya, bata rasa komai na buk'ata anan d'in ba ba kuma ta fuskantar ko wani irin takura, sai ma nan nan da Hajiya keyi da ita, amma ku sani akwai banbanci mai nisa tsakanin gidan auren ki da kuma gidan ku, to itama irin wannan banbancin takeji a yanzun. *Bayan Meenal ta fice* Hajiya na daga kan kujerar da take cin abincin ta ta d'ago kai tana kallon Mommy Hauwa data kafe takardar nan da kallo hawaye naci gaba da zarya a idon ta, "To idan kin gama kukan ki k'araso nan in baki amso shin tambayoyin ki" Goge hawayen tayi sannan ta tashi itama taja kujerar da Meenal ta tashi wanda yake daura dana Hajiya ta zauna, "Ga tea nan na had'a miki zauna kisha dan nasan yanzun haka baki karya ba kika fito" "Bana jin yunwa Hajiya, nidai dan Allah ki fad'amin mai ya faru?" Daga hannunta hajiya tayi tama Jidda nuni da kofar falon, "Wancan kofar itace inda kika biyo kika shigo koh?" Bata jira amsa ba ta d'ora da cewa, "Dama kinzo jin tabbacin batun sakin ne ai dama koh? To ga dai takardar nan kin ma karanta dan haka kwashi kafafuwan ki ki koma can inda takardar ta fito sai suyi miki bayanin dalilin sakin wanda suka manta basu rubuta a jikin takardar ba, dan bazaki zo har gidana ki nemi mai dani wata shashasha ba kamar akan yarki aka fara sakin aure" Tea din ta d'auka da zafin shi da komai amma hakan nan ta kafa shi a baki bata sauke kofin ba har saida ta shanye shi tass, Hakan kuma bai sa hajiya ta k'ara bi takan taba illah ma abincin ta data maida kai taci gaba daci, sai da taci ta koshi sannan tayi hamdala, kana taja kujerar ta baya ta fita daga wajen dinning din ta koma falo ta kunna TV tayi zaman ta tana mai maida hankalin ta kacho kam akan kallon da takeyi, kamar bata san da zaman Jidda a falon ba. Bayan tashin Hajiya ita kuma Jidda kayan wajen ta tattara takai kitchen daga can ta tsaya ta wanko fuskarta kafin ta dawo falon ita ma ta nemi wajen zama, Sunyi zama na kusan minti 15 kafin hajiya ta mulla dan kanta ta d'ago kai, "Taso ki dawo nan muyi magana" Tashi Jidda tayi zuwa inda ta nuna mata domin ai dama ita abunda take buk'ata kenan, Sai da Hajiya ta sauke ajiyar zuciya kafin ta fara magana a tsanake kamar haka. "Hauwa'u kinji babu d'adi a sanda wan Mijin ki ya gabatar miki da takardar shedar mutuwar auren yar da kika haifa koh?" Shiru Jidda tayi bata amsa ba sai ma idanuwanta da suka cika da hawaye, "Nifa bance kimin kuka ba, in kin san kukan kuma zakiyi kije gida duk randa kika natsa sai kizo in fad'a miki abinda kike son ji," "Kiyi hakuri Hajiya na shirya, na daiji babu dadi ne kasancewar Meenal karamar yarinya kuma mace ta farko da kaddarar zawarci ya fadawa a kaf cikin Danginta," "Nasan kina jin babu dadi Jidda amma ba meenal ba kowama bai wuce kaddarar shi, mu gode Allah da nata kaddarar bai kasance mummunar kaddara ba domin a zaman da tayi na tsayin shekaru a gidan ta ba tareda kuma data samu kulawar kusanci da Mijin auren taba da Allah yaso sai ya ratso wani mummunar abunda zai zama abu mafi muni a garemu, sai gashi Allah ya kare mana ita ta iya ci gaba da rike kanta har zuwa wannan lokacin da komai yazo karshe, dan haka godiyar mu ya kamata mu gabatar wajen ubangiji ba kuka ba," Shiru Jidda tayi tana sauraron Hajiya. "Jidda nice na haifeki amma ni kaina ina mamakin wasu daga cikin halayenki na halin ko in kula da kike nuna ma yarinyar nan Meenal, Badan komai ba sai dan yanda kike wofantar da duk wani abunda ya shafeta, yarinyar nan fa ba d'iyarki ta farko bace amma sai gashi kusancin da d'anki na fari yake samu dake ita ko rabin shi bata samu a wajen ki ba, lokuta da dama sai inga kamar kikan manta da cewa kece uwarta, domin baki damu ba sam da son sanin, Wani hali take ciki? , Miye damuwar ta? , tun tana yarinya kika saki ragamar ki a matsayin uwa zuwa ga wasu daban, sam baki nuna mata cewa ke d'in bango ne majin gina a gareta ba balle ta samu damar jinginar ki a yayinda take buk'atar mai lallashin ta, komai kin sake ma mutanen gidan ku da kuma yayan ubanta, Ni ko a nawa ganin ai duk son da wani zai nuna ma d'a baiyi kamar uwa ba domin dai uwa ita tafi kowa sanin ciwon abinda ta haifa, Yarinyar nan bakijata a jikin ki tana k'arama ba, Baki jata a jikin ki tana matsayin budurwa ba, Haka kuma da kuka aurar da ita sai kika k'ara nesan ta kanki da ita, Fad'amin tunda kike da ita ta tab'a tun karar ki da wani damuwar da take buk'atar kece zaki mata maganin ta?" Shiru Jidda tayi. "Kinyi shiru saboda hakan bai tab'a faruwa ba, ku dai kun aurar da ita kun mik'a babu wanda yake bin sahun ta balle wani ya hango nakasun dake cikin rayuwar auren dake gudana tsakanin ta da Mijin da kuka aura mata, shekara 1,2,3 har zuwa tsayin shekaru 6 babu b'atan wata babu bari balle akai ga batun haihuwa alhalin ga kannen Bayan ta nan duk sun haihu, Fada min kin tab'a zaunar da ita a matsayin ki na likita ki bincike ta? A cire matsayin uwa a gefe" "Kiyi hakuri Hajiya nayi kuskure" "Kin san me Hauwa'u? Ni ana ganin yawan fad'ana ne kawai amma duk da hakan komai akeyi baya wuce gani da jin kunnuwa na, bazan b'oye miki ba kinyi sake sosai domin dai gaki a raye amma hakan bai sa yar da kika haifa tasan dadin ki a matsayin ki na uwa mace ba, Karki manta in ma kinayin hakan dan Kiyi ma sauran mutanen gidan ku dashi malam kara ne, shi din fa namiji ne, akwai abubuwa masu yawa wanda komai kusancin dake tsakanin Meenal da malam bazata iya fad'a mishi suba, Su kuma sauran matan gidan ku Karki manta ba sune iyayen ta ba dan haka babu wannan shakuwar da zata tunkare su da damuwar ta a koda yaushe, ni kuma ba unguwa daya muke daku ba dan haka inba zuwa tayi ba ba komai nike iya fahimta akan zaman ta da Mijin ta ba," Sosai hajiya ta tsage Jidda akan yanda take mu'amalantar Meenal kafin daga karshe ta d'aura da bata labarin irin zaman da Meenal tayi a gidan ta harma da dalilin da yasa Hajiyar wutowa da ita gidan ta daga asibiti kafin batun saki ya biyo baya, "Nasan komai zai faru babu uwar da zata so ace yau yarta ta k'ara dawowa gabanta da sunan zaman zawarci, wata kilama zuciyar ki tana nan tana raya miki cewa tunda saki d'aya ne a dai'daita ta koma d'akin ta, To wallahi wannan karan na shirya muku tass tundaga kanki ke uwarta har zuwa shi wancan mai nuna yafi kowa iko da ita d'in duk dai dai nake daku, dan tunda har yarinyar nan ta nuna ta gama auren tofa ta gama shi kenan koda ko ace shi Mijin naso balle kuma shima baya muradi, yarinyar nan dai ba yara ta to tara a gidan ba balle ace ta koma tayi hakurin zama saboda su, ba kuma tsohuwa bace balle ace tayi zaman tsufa inta fito babu mai auren ta, Kin daiji na fada miki in zaki farka daga baccin asarar da kikeyi gara ki farka, kina iya tafiya na gama dake saura kuma shi d'ayan uban nata nashi sammacin Nike jira dan nayi mamakin da naji shiru banga ya biyoni gidan nan ba ashe sak'on ne bai kai hannun ku ba sai yau" "Malam baya nan amma yau zai dawo" cewar Jidda, "Kai masha Allah to allah ya kawo shi lafiya" ****** Bayan Jidda ta isa gida, Baba Auta ta samu zaune a falo, Bata kulashi ba duk da tambayan da yake mata cewar yayi kiran wayarta bata d'auka ba, Ganin ta wuce shi zuwa ciki hakan yasa shima ya yunk'ura yabi Bayan ta zuwa d'akin nata, Ita ko da shigan ta d'akin mayafinta kawai ta cire ta haye gado ta runtse ido tana fatan Allah yasa idan tayi bacci ta farka taga komai ya zama mafarki, wani yace mata mafarki takeyi ba Meenal dinta bane aka saka ba. Shigowa yayi ya zauna a gefen ta, ita kuma duk da taji motsin shi bata nuna tasan da zaman shi a wajen ba. "Kiyi hakuri Hauwa'u kinji bana son kisa maganar nan a ranki balle wani abu ya sameki, Kiyi fatan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, ki tashi ki shirya mu wuce na riga na had'a kayan tafiyar" "Eh ai dama kullum aka cuceni abunda kake cemin kenan inyi hakuri, tunda na haifi yarinyar nan nake fuskantar abubuwa Kala Kala akan ta, a tunanin ku bana son tane? Nice fa uwarta nina haifeta nafi kowa sanin zafin ta amma a hakan kullum nike kauda kai kar aga zak'ewata, Ko ka manta cewa auren dole kuka mata, haka kuma nayi shiru na hak'ura badan naso ba, amma kawai sai ya sako min ita, fisabilillahi da yasan baya sonta mai yasa ya aureta, Suma kuma iyayen shi sun san baya son aure suka matsa mishi ya aureta wannan ai son kaine tunda gashi nan komai a kanta ya k'are" To dai Bayan dogon lallashi baba Auta ya lallab'a matar shi sun wuce zuwa Abuja, Yayin da shi kuma Malam yayi ma garin na zaria shigowar la'asar sakaliya, *Tofa ya abubuwan zasu kasance kenan?* Bari in muku wani tuni, in baku manta ba kunji cewar Malam mutum ne mafad'aci, a wancan lokacin harda kajin gidan shi in suka matsa mishi umarni yake ba yarwa duk a kame su a yanke, Sai gashi yau zai dawo ya iske takardar mutuwar auren Meenal din shi yarinyar da yake ma kololuwar soyayyar da allah ne kad'ai yasan adadin ta, In baku manta ba saboda gudun abunda ka iya tab'a zumuncin shi da yan uwan shi hakan yasa ya d'auki lokaci Mai tsayi bai amince cewa zaiba Sarki auren Meenal din ba, Sai gashi daga yin aure Bayan shekara 6 aure ya mutu an b'ata ma maman shi suna daga budurwa zuwa bazawara, Koya ya zaiji in wannan bakin labari ya iske shi? Wani mataki zai d'auka gudun kar hakan ya k'ara faruwa akan wata daga cikin ahalin Bayan Meenal. Haha haha, wai ina labarin gwarzon mu Abdul Khareem Ahmad Mai Jama'a ne? Shiru dai har yanzun bai iso zaria ba. Shin AK zai samu cikar burin shi na auren Meenal cikin sauk'i kamar yanda yake hangowa kuwa? Yaya soyayyar su zata kasance ne, zatayi saurin amsa mishi intama ta fada soyayyar shi ko wani ne zai zo yayi ma nata zuciyar kutse? Yaya teemah zataji a sanda labarin mutuwar auren mijinta zai isketa? Wani mataki zata d'auka dan hana shigowar wata gidan ta Bayan Meenal? Shin Sarki zaije ya nemi yarinyar da Meenal ta bashi number da adireshin? Ko kuma hakura zaiyi yaci gaba da zama da Gimbiyar shi? Wadan nan tambayoyi dama wadansu masu tarin yawa duka zaku samu amso shin sune a cikin littafin *DANGINA* kashi na biyu, Wanda zaici gaba da zuwa muku nan bada jimawa ba insha Allah. Ina mika godiya zuwa gareku yan uwa makaranta da kuka b'ata lokacin ku wajen karatun littafi na, Nagode kwarai da yanda kuka dunga k'arfafa min gwuiwa da fari nayi zaton cewa bazan iya ba amma kuka tsaya a kaina wajen ganin ban dakata ba, Nagode da soyayyar ku a gareni, Kuna da yawan da bazai yuwu ince zan tsaya lissafo sunayen kuba, Sai dai ako ina nike zan kasance mai alfahari daku akoda yaushe, Son so fisabilillahi ina fatan Allah ya had'amu a littafi na biyu cikin aminci da sallama, *Domin yin gyara shawara ko matashiya akan wani abunda na manta zaku iya magana dani kai tsaye a wannan number din 08061358462 Nagode* *Alhamdulillahi* *Ummiee Zaria*โœ๐Ÿผ [8/20, 8:48 PM] Ummiee Zaria: โšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA!*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ ~{{MY FAMILY }}~ ยฉยฎ *UZ-2023.* *BOOK 2* *RUBUTAWA* *ZAINAB USMAN* *~{Ummiee Zaria}~*โœ๐Ÿผ *Bismillahir Rahmanir Rajeem* *Ina mai mik'a yabo da godiya na ga Allah mad'aukakin Sarki wanda bai hafa ba kuma ba'a haifeshi ba Ubangijin sammai da kassai, Sannan ina k'ara salati zuwaga shugaban mu d'an gatan Allah, Annabin mu Muhammad (S.A.W), tareda iyalansa da sahabban sa baki d'aya. *SADAUKAR WA* A wannan tafiyar gaba d'aya littafin tun daga farkon shi har zuwa karshen shi zai zamo sadaukarwa ne ga d'aukakin masoya da suka jure wajen bibiyar labarin in daga farko har zuwa yanzun, Ku d'in kun kasance abun alfaharina, na fara rubutu banyi zaton labarin zai zaga har zuwa inda banyi zato ba, sai gashi a sanadin littafin *DANGINA* na had'u da mutane kalaยฒ wasu iyayena wasu yayye wasu kanni, Lallai na yaba da kaunar ku gareni, tun daga kan Marubuta dama makaranta da a kullum kune ke bani gwarin gwuiwar ci gaba da rubutu, Kuna da yawan da bazai yuwu ince zan zano sunayen ku ba, ina dai so ku sani cewa na yaba matuk'a๐Ÿ’˜. *Ga masu buk'atar littafin daga farko zaku iya tuntub'ana kai tsaye da wannan number d'in* 08061358462. Karku manta littafina kyauta ne banyi shi dan in siyar ma makaranta ba, dan haka karkuji d'ar kuba duk wanda kuke so. *Page 1* ``````` Tunda Allah yama Malam isowa da maraicen nan gaba d'aya bai samu zama ba, domin bayan tafiyar shi anyi wani rashi na d'aya daga cikin d'aluban shi da sukayi karatu a k'ark'ashin shi, dan haka koda ya iso babu jimawa ya shirya ya wuce can wajen iyalan mamacin domin yi musu ta'aziyya bashi ya samu sukuni ba dai har sai zuwa dare. A gefen Baba Adamu kuwa tun a sanda Baba Auta yama shi sallama akan zai wuce Abuja a ranshi yaji cewar gudun hijira ne kawai Adamun zaiyi dan baya son gamon su da Malam, domin dama tun zamanin k'uruciya ma in sukayi ma Malam d'in laifi shi Auta Hijira yake yabar gidan har sai Malam yayo bikon shi kafin ya dawo. Bai matsa mishi ko tambayan dalilin da yasa zai wuce d'in ba dan yasan Auta dannewa ne kawai yakeyi amma shi a matsayin shi na wanda yake gaba dashi yasan dole abunda ya faru ya dake shi, domin dai babu uban da zaiyi alfahari da kasancewar d'iyar shi bazawara, Malam bai shigo cikin gida ba har sai misalin karfe 9 da wasu mintuna na dare, a yayin da shi kuma Baba Adamu ya kasa ya tsare a farfajiyar gidan yana jiran isowar shi dan gara ya gabatar mishi da komai a daren nan dan Malam mai iya mishi sai Allah yana iya idan shi yace ya bari sai gobe ya tunkare shi da batun, shi kuma Malam d'in yahau shi da fad'a akan wani dalilin ne ya hana shi gabatar mishi da takardar a yau? "Ah ah Adamu kai kad'ai zaune a waje lafiya kuwa? Ko kodai jiran shigowa na kakeyi ne?" Malam ya tambaya a yayin da hankalin shi yakai kan Adamun dake zaune a kan d'aya daga cikin kujerun da aka ajiye dan zama a kofar falon Malam, "Eh Malam barka da dawowa an dawo lafiya ya hanya da gajiyar tafiya?" "Alhamdulillah lafiya lau muka iso, kai kuma kazo kayi zaune a nan kai kad'ai ai ko sauro bazasu barka ka sarara ba, da kasan kana jirana ai da ko a waya ka kirani, tunda dai ba komai nikeyi a wajen ba na dai tsaya ne muna gaisawa da makota tunda kwana biyu bana nan abubuwa sun d'an faffaru, kuma ai da ka bud'e falon ma ka shiga" "Ba komai Ya'ya na daiji zaman a nan d'in ne dama shi yasa ban shiga cikin ba" "To madallah bismillah mu shiga daga ciki koh!" Malam ya ambata a yayin da ya tura kofar falon da sallama suka shiga, Bayan sabuwar gaisuwar da suka sake da tambayar bayan saduwa ne malam ya d'aura da cewa, "D'azun auta ya kirani cewa sun wuce abuja shida mai d'akin shi zasu d'an kwana biyu kafin su dawo, wato dai Auta take taken shi so yake dai yabar gidan nan dama garin baki d'aya, ni ban san me mutane suke so su zama ba gaba d'aya dai da zarar mutum yaga ya d'an tara yan kud'ad'e sai kaga ya manta da gidan su sai ya ware kanshi can a gefe shi d'aya, niko gani nike mai yakai zama cikin ahalin ka dad'i fisabilillahi fa, amma yanzun da zarar nayi magana sai ayi min wata fassara ta d'aban, tunda aikin shi ya koma Kaduna ya fara wannan galantoyin tsakanin kaduna da zaria nasan cewa gaba kad'an zaice ya gaji da yawon zai kwashe iyalanshi ne su koma can, yanzun nan fisabilillahi in banda abun Muntari a kadunar har za'a samu wata makaranta data d'ara ita wannan ABU d'in daya bari ne? Ni dai bazan k'ara magana ba ma balle aci gaba da cewa na fiye takura" Duk surutun da Malam keyi Adamu baice komai ba sai dai d'an murmushi da yakeyi, "To ina ce dai lafiya? dafatan dai babu abunda ya faru a gidan bayan tafiya na? Koda yake ko wani abun ya faru nasan zaku magance shi basai kun jira dawowa na ba" Daga kanshi yayi ya kalli agogon dake mak'ale a jikin bangon falon nashi, "Ashsha ashe dare ya fara haka gashi gaba d'aya na manta dana ware tsarabar uwata ban ce yaran nan su mik'a mata ba harna fita, Baiwar Allah nasan babu mamaki ta shigo bata iskoni gida ba" Wayar shi dake gefe ya d'auka kafin ya lalubo Number din Innar yara kira d'aya biyu ta d'auka, "Na shigo fa tun d'azun amma babu wacce tazo dubani a cikin ku" Daga can gefen Ita kuma ta amsa mishi da cewa, "Ayi mana afuwa Malam ita Dije nan wajena ta amshi maganin ciwon kai tasha to nasan babu shakka bacci ne ya d'auketa ni kuma ban san ka shigo ba shi yasa amma zan iso yanzun" Sai da ya yanke wayar sannan yace da Adamu, "Kaga halin matan nan koh? Mata biyu amma na shigo tun d'azun an rasa wacce zata shigo ta bani abunci a cikin su" "Ayi musu uzuri ya'ya indai abinci ne ai koni sai in had'a maka tunda gashi can ai naga an ajiye" "Allah mai iko, aiko kaga ni sam ban kula da cewa an ajiye abincin ba, to d'auko sai ka zuba mana muci ai mun kwana biyu dama bamu samu damar cin tuwon dare tare ba" Duk da cewa Baba Adamu yaci nashi abincin hakan bai hana shi zuba musu wannan d'in ba suna ci suna hira a haka har Ameena ta shigo ta same su, Koda ta iskosu itama zama tayi sukaci gaba da hiran Malam na basu labarin yanda tafiyar shi zuwa Mai duguri ta kasance, [8/20, 8:48 PM] Ummiee Zaria: โšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ *~{{MY FAMILY}}~BOOK 2* ยฉยฎ *UZ-2023.* *RUBUTAWA* *ZAINAB USMAN* *~{Ummiee Zaria}~*โœ๐Ÿผ *Page 2* A wannan dare sam Malam bai samu sukunin yin bacci cikin salama ba, domin kam sosai fa abun ya

Chapter 44 of 92