Share this page
ya tuna da tonunan da Meenal din tace ta tura mishi a cikin wayar, Dan haka sai ya d'auko wayar ya gyara zama bayan ya shiga cikin ma'ajiyar hotuna ya fara bincike, Hotunan daya gani kusan kala 10 ne kuma dukan su na mutum d'aya ne sai guda biyun da sukayi ita da Meenal din ne hakan ya tabbatar mishi da cewa sune wanda meenal din ta tura mishi dan haka sai ya fara bin su d'aya bayan d'aya yana karema hotunan kallo, Ya dad'e yana kallon hotunan bai iya furta komai ba sai kuma zuwa can yace, "Meenal kenan wato saboda taga Teemah tana da d'an jiki kad'an shine yasa take son had'ani da wannan kenan?" Eh kam gaskiya yarinyar cikin hoton tadan d'auki hankalin shi duk da a iya hoto ya ganta amma yana jin cewa zatayi dai dai da tsarin shi dan ya lurada cewa ta mallaki dukkan abunda yake buk'ata a wajen macen da zai zauna da ita a matsayin matar shi na aure, wato wayewa kyan fuska cikakken diri da wasu abubuwan wadanda shi ya barma kanshi sani, A bayyane kuma ya k'ara furta cewa, "Koma batayi ba ai dole in amsa haka da hannu bibbiyu ma kuwa tunda ta fito daga wajen abunda nike matuk'ar girmamawa a yanzun, Inma batayin ba duk ni zan saita ta zuwa tsarin da nike muradin ta kasance min. *UMMIEE ZARIA*โœ๐Ÿผ [8/23, 9:51 PM] Ummiee Zaria: ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA!*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆโšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ *BOOK 2* *PAGE 10* Shi kam a Yanzun gani yake bashi da kalmar da zaiyi amfani wajen nuna godiyar shi ga Meenal, Domin dai duk da kasancewar ta yarinya k'arama da ya tabbatar da cewa a haife zai iya haifan ta sai gashi ta sanadin ta ne yau ya kasance cikin nutsuwar daya rasa tsayin wasu shekaru a yanzun Allah da ikon sa zai kwanta yayi bacci lafiyar Allah kuma ya tashi ba tareda yayi wani mugun mafarki ba sab'anin lokutan baya da baya samun isshen bacci, rashin baccin nashi kuma bazai sa yace ya tashi ya gabatar da nafila koda raka'a biyu bane, domin a lokacin nema yake jin wata irin muguwar kasala haka zai b'ata dare a banza shi baiyi bacci mai dad'i ba shi kuma bai raya daren ba, sai gashi yanzun Allah da ikon sa a cikin k'asa da wata d'aya komai ya canza ciki kuwa harda ibadan shi dan ya k'ara kusanta kanshi ga mahaliccin shi sosai ga kuma azkar da yakeyi akoda yaushe, yasan kuma yawan farin cikin da yakeji a zuciyar shi duk suna da na saba ne da hakan, Yasan ya aikata kura kurai da dama a baya, domin dai adah can baya tunawa da damuwar kowa sai na matar shi kad'ai baik'i yab'ata da kowa ba indai har ita zatayi farin ciki to bazai tab'a damuwa ba wanda dalilin hakan ya b'ata mu'amalan shi da mutane da yawa bayaga abokan shi da sukayi kokarin ganin sun dawo dashi kan hanya ciki harda wasu daga cikin yan uwan shi wad'anda ya shatawa layi duk akan matar shi sai yanzun ne kuma yake jin bak'in cikin hakan ya kuma d'aura aniyar gyara kuskuren shi da yardar Allah, Adah can baya yakan manta cewa akwai hak'k'in uwa da uba ya'ya da kuma k'anne ciki harda hak'kin ita kanta matar da iyaye suka aura mishi da take zaune cikin gidan shi a matsayin matar shi, ya nisan ta da kowa babu mu'amala mai kyau balle akai batun shak'uwa dan harta yaran daya haifa duk da a Yanzun sunyi girman da zuwa gaba kad'an yasan maganar auren su za'a fara amma suma bai samu damar da zai zauna ya jasu a jikin shiba balle har yasan damuwar su da kuma abunda suke buk'ata na yau da kullum dan a lokacin uwar yaran ita kad'ai ce a gaban shi ta yanda baya iya tuna kowa sai ita, ita kad'ai dai itace a lokacin yake gani kamar duk wani farin cikin shi yana tare ne da ita, Sai gashi Yanzun Alhamdulillah dan ba iya nutsuwar zuciya yake jin cewa yasamu ba harma da nutsuwa ta cikin gangar jiki domin a Yanzun mazan takar shi ta dawo ta yanda akoda yaushe yake jin kanshi a matsayin cikakken namiji kamar wani saurayin da yake cikin lokacin kuruciyar shi sab'anin shekarun baya da inba yana tare da Teemah bane bayama tuna cewa shi din namiji ne, Abun mamaki ashe abundai daya raina itace warakar shi zai fito a sanadin ta, dan hakan yasa yake ganin me nene ma wanda Meenal zata nema a wajen shi har ya kasa cika mata shi? Dan a Yanzun ta wuce neman abu a gunshi shi dai da yake matsayin Babban yayan ta shine zaiyi tsayin daka wajen ganin cewa bata rasa komai na buk'atar rayuwa ba, Duk da ko a Yanzun bawai matsayin daya bata ya canza bane, Ah ah sai dai yana d'aukar al'amarin ta da girma ne sosai ya kumayi imanin cewa ita d'in tun farko dama ba matar tashi bace shi yasa yake mata fatan Allah ya had'ata da wanda zai kaunaceta kamar fitar numfashin shi, Ya d'ade zaune yana cigaba da kallon hotunan Moon tunawa da paper din da Meenal ta rubuta mishi sunan yarinyar ne yasa shi mik'ewa dan tun a ranar yana dawowa ya cire shi a cikin aljihu ya saka shi a cikin wallet din shi gudun kar ya salwanta, Inda wallet din yake ajiye akan side drawer ya nufa yana budewa ko ya zaro shi a inda ya soke shi, Babu b'ata lokaci ya bud'e ya karanto, a bayyane ya furta, "Maimoon, Lagos, ah lallai zuwa Lagos ya kamani," Address dinta da Meenal din ta tura mishi ya k'ara dubawa, kafin ya d'auko wayar shi yayi saving number din dake rubuce a jikin takardar da sunan "Moon" Sai da yayi kamar ya danna ma number d'in kira sai kuma ya fasa, domin kafin komai ya fara shiga tsakanin su zai so ya Santa da kyau ta yanda zai san ta inda zai fara dan ganin ya kamo zuciyar ta cikin kwanciyar hankali, kuma ma gani yake ai yanzun yayi wuri ace ya kirata. Komawa kan kujerar daya taso yayi ya zauna yana k'are mata kallo, "Wannan yarinyar da wuya itama inba irin halin kawarta take da ba, daga ganin bakin nan nata sai tayi yawan surutu, wai zata ma so tsoho kamata kuwa?, Allah ka dafamin in samu shawo kanta cikin sauki" Ya fad'a a bayyane, can kuma kamar wanda aka tsungula sai ya fita daga wajen hotunan ya koma wajen ajiyar lambobi, Number din da yayi saving da suna Joseph ya aikama kira, Number din bata dade da shiga ba aka d'auki wayar da harshen turanci suka gaisa, Da harshen kuma sukaci gaba da magana inda shi Sarki yake tambayar Joseph din cewa yana gari kuwa? Shi kuma Joseph din ya amsa da cewa eh yana nan, "Zan turo maka pic din wata yarinya da address a kanta ina son sanin komai a kanta, idan nace komai ina nufin komai", ya jaddada mishi, "Babu damuwa sir duk abunda kake buk'ata zaka sani akanta cikin kwana biyu" "Ok zan tura maka pic da address din yanzun" Bayan Joseph ya amsa ne kuma Sarki ya yanke wayar sannan ya tura mishi, "Ina ganin lokaci yayi da zan waiwayi Lagos" Ya furta a bayyane domin tun kafin faruwar komai dama ya dad'e baije garin ba, ga shi kuma yanzun Zaria bata zuwuwa gaskiya dan ido da kunya wallahi, Bai san da wani idon zai kalli baban shi da Malam ba idan yaje dan ta uwar gida mai sauki ne domin tuni suka dai daita tsakanin su, ba iya ita kad'aiba ma harda yan uwan shi yanzun shida kanshi yake kok'arin kiran su, Shima kuma baban nashi suna waya dan shine ma ya shaida mishi komai daya wakana bayan ya gama mishi wankan tass a randa shi Sarkin ya kira shi, ya kuma ce mishi ya kira Malam ya bashi hak'uri, Ranar daya kira Malam d'in sai Allah ya rufa mishi asiri wayar bataje ba dan wayar Malam din yana rufe, Ranar daya k'ara kira kuma ya samu malam d'in yayi zaton zaiyi mishi fad'a ne ko ya nuna b'acin ranshi kamar yanda Baban shi yayi, Sai malam ya bashi mamaki dan nasiha Kawai yayi mishi sosai mai shiga jiki ya kuma tunasar dashi akan rik'e ibada daga k'arshe kuma ya kora mishi warning akan ko kusa ko alama koda wasa shi Malam din yaji cewa Sarki ya saki Teemah tofa babu shi bashi, Dan bayan mutuwar auren da maganar ta fita su dangi duka kowa tsinuwar shi akan Teemah ya k'are a zaton su ko itace silar da auren ya mutu shi yasa duk suke ganin laifin ta, yasan kuma tunda uwar gida tasa ya saki Meenal tana iya cewa ita ma Teemah sai ya saketa, dan haka Malam ya fad'a mishi cewa yayi na farko yayi na k'arshe idan ya samu matsala da matar shi inyaga cewa abin yafi k'arfin shi to yakai maganar gaban mahaifin ta tunda Allah yasa har yanzun yana raye, Sannan ko dan darajar ubanta yaci a d'aga mata k'afa ga kuma yara har 4 Allah ya basu a matsayin zuri'a dan haka shi Sarki yayi hakuri daduk abunda ya faru a baya sai kuma a kori gaba, Wannan abu sosai ya k'arama Malam kima a idon Sarki, domin dai a wannan lokacin da muke ciki bako wani uba bane za'a cutar da yarshi ya kauda kai balle kuma har ya rok'ama wacce ta cutar da yar nashi arzikin cigaba da zama da mijin data raba da yarshi alhalin yasa yana da ikon rabata da nata mijin itama, To dai shima Sarki har yanzun fa bawai ya dena son matar nashi bane, domin dai ita d'in ita ce mace ta farko da zuciyar shi ta fara mata wankakkiyar kaunar da babu algus a cikin ta har yanzun kuma baya dena son nata bane, Sai dai muce kaunar ta sauka daga kaso d'ari zuwa kashi 45, Ya yanke hukuncin hukunta ta shi yasa ma har yanzun bai gwada neman ta ko a waya ba, tunda ya binciki mai gadin gidanta ya shaida mishi cewa bata gidan yasan tana gidan su dan haka bai damuba dan shima yana buk'atar suba juna space kowa ya sarara, dan yasan idan ya tunkareta a yanzun ana iya haihuwar uwar da bata da ido, To gashi kuma yanzun uzurin zuwa Lagos ya kamashi dan yau d'ai daga ganin hoton yarinyar nan yaji ya zak'u yakai gareta dan ya ganta a fili dan yasan zatafi kyan kallo a zahiri, kwana biyun da Joseph yace mishi zaiyi dai dai da sanda shima zai koma KD dan haka yana komawa Lagos zai wuce, Bai tashi daga wannan sak'ar zucin ba har sai da kirar Sa'eed ya riske shi inda yake ce mishi ya dawo mishi da zab'in gidan da yake ganin yafi dacewa, Babu b'ata lokaci ko ya k'ara jawo laptop d'in ya kunna, a wannan daren dai bai kwanta ba sai da ya kira wanda batun gidan ke hannun shi ya kuma tura mishi Number din Sa'eed akan ya kirashi a gobe suje dashi yaga gidan sai suyi ciniki duk yanda akayi sai su fad'a mishi, ya kuma turama Sa'eed din number din mutumin shima. Bayan kwana biyu, Ya samu damar kammala aikin daya kaishi Calaba lafiya lau cikida tarin nasarori, dan haka ya tattara zuwa Kaduna, baiyi yunkurin zuwa Zaria ba yadai kira Sa'eed din shida Salman akan suzo su same shi, Dan haka a randa ya iso suma suka isa kadunar sun samu wancan mutumin ma da za'a siya gidan a hannun shi har ya rigasu zuwa ma, koda suka isa su d'in ya aika bank suka ciro kud'in gidan millions of Naira, abunda ya Sa'eed matuk'ar mamaki shine ganin takardun gidan d'auke da sunan Aminatu b'aro b'aro, hakan yasa bayan wucewar wanda aka siya gidan a hannun shi Sa'eed ya kasa shiru sai da yayi magana da cewa. "Sarki kunyi mantuwa fa wajen suna a takardun" "Bamuyi mantuwa ba Sa'eed sunan da ka gani akan takardar na mamallakiyar gidan ne a yanzun" "Meenal?" Sa'eed ya anbata da alamar tambaya. "Kwarai ita d'in dai domin ta cancan ta shi yasa na siya mata, itama kuma kyauta zatayi dashi ko zaka cemin baka san buri kanta bane?" Cike da mamakin dabai saki Sa'eed din ba ya amsa da cewa, "Burin ta uku, Zama likita Hawa babbar motar da zata kasance mallakinta Na ukun kuma shine idan tayi kud'i ta ginama Baba Malam k'aton gida ya koma can shi kad'ai yabar family house" "Madallah ashe baka manta burukan kanwar taka ba, to cikon na ukun ne na cika mata, sai dai ina rokon alfarmar maganar ta tsaya a tsakanin ni da kai sai ita Meenal din shi yasa kaga na aiki Salman ban bashi daman dazai san komai akan maganar ba dan bana son matsala dan ina gudun kar hassada ya shiga tsakanin ta da yan uwana na yarda da kai shi yasa na damk'a komai a hannun ka, idan ka kai mata ita zata gabatar ma Baba Malam dashi a matsayin daga wajen ta ya fito, Ban san yaushe zatayi hakan ba amma ina fatan zaka tayani rufe maganar nan?" "Insha Allah Ya'ya kamar yanda ka yarda dani bazakaga sab'anin abunda kake zato daga wajena ba, mungode ubangiji Allah ya k'ara arziki dan ba Meenal ce kad'ai zatayi godiya ba harda ni nima dan ba ita kad'ai ce take da burin canza ma Malam muhallin zama ba harda mu muna sai dai duk bamuyi yunkurin yin hakan bane saboda munsan bazai amince ba amma idan abun ya fito daga wajen ta tabbas bazai k'i amsa ba dan shima yasan ta rayu da burin gina mishi gidan dama tun tana k'aramar ta, Mungode kwarai ubangiji Allah ya cigaba da bud'e maka kofofi na alkhairi yasa ka gama da iyaye lafiya, Allah ya raya iyali ya kuma kareka daga sharrin Makiya" Ya k'arasa fad'a yana dukewa zuwa kasa, "Kai miye haka tashi mana so kake Salman ya shigo ya fara tambayar ba'asi, dan Allah tashi ko ka manta nima yaron Malam ne tun kafin a haifo ku?" Bayan dawowar Salman daya aika kasuwa yin siyayyar abubuwan da yasan za'a buk'ata a gidan ne kuma ya had'a musu da tsarabar daya taho dashi daga Calaba, sai da ya ware na gidan su dana gidan Malam sannan suma d'in ya jik'asu da nera sukayi Sallama da juna suka kamo hanya dan jirgin yamma zaibi zuwa Lagos dan haka yana buk'atar hutu sosai kafin yamma. *UMMIEE ZARIA*โœ๐Ÿผ[8/27, 5:20 PM] Ummiee Zaria: ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆโšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ *BOOK 2* *PAGE 11* Tun safe Sarki ya k'ira d'aya daga cikin yaran shi dake can Lagos d'in ya bashi umarni akan su gyara mishi gidan kafin ya iso, Domin dai dama koda ma ace matar gidan tana gidan idan yayi tafiyan daya dad'e baije Lagos din ba to kafin ya dawo su yake turawa su kintsa mishi gidan dan ita dai Teemah haka Allah yayi ta da rashin iya gyaran waje baya tunanin kuma zata iya canzawa, ita dai barta a tsaftar jikin ta tsaftar muhalli ne dai bata da katabus, dan zata iya wanka sau goma a rana amma ba tareda damu da sharan d'aki ko sau d'aya a rana ba, dan dama tun bayan barin shi Lagos da aka maida shi KD aiki ya zamana ta samu freedom dan haka tuni ta d'auki yar aikin dake mata komai daya shafi aikin gida sai in Sarki yazo garine shine mai aikin ke dena zuwa idan ya koma kuma saita dawo da ita, duk da yanda zuciyar shi ke azalzalan shi akan ya kirata domin ya shaida mata zuwan nashi k'iyawa yayi, dan tun bayan barin ta zaria dama yayi alwashin cewa bazai kirata ba har sai in itace ta kirashi da kanta tunda har ta iya tsallakewa tabar garin bada izinin shiba, yasan fushin rashin gaskiyar data sabayi a duk sanda suka samu sab'ani koda ko ace shine mai gaskiya ba itaba shi takeyi a yanzun d'in ma, jira take ya kirata ya kaskantar dakai yana bata hak'uri kamar yanda ta saba ita kuma sai taji dad'in kafa mishi tarin sharud'an da baya iya tsallakewa a wancan lokacin yanzun kam ko kusa bayajin zai iya zubar da kanshi akan abunda yasan cewa koda ya aikata aiba haramun ya aikata ba, tunda ita yarinyar da take tunanin ya kwanta da ita d'in ai matar shice ta aure wanda ya biya sadaki kamar yanda ya biya nata sadakin itama, Ana cewa mata na kishi amma gaskiya wani kishin yana zarce ka'ida dan kishin teemah akan shi in batayi wasa ba sai ta d'aura ma kanta lalurar da babu mai mata maganin shi, Duk da yasan cewa a ayyukan da take aikatawa shima yana da nashi kason laifin domin shine tun farko ya sake mata, ta yanda ta samu damar aikata duk abunda take so batare daya takura taba, Ya sani cewa yana son matar shi sosai domin shi din irin mutanen nan ne da basa iya cusa ma kansu son abunda baiyi dai dai da ra'ayin suba, Teemar shi itace mace ta farko daya fara so, Yaso ta da dukkan zuciyar shi sai dai baiyi zaton cewa zatayi amfani da soyayyan da yake mata wajen juya akalar rayuwar shiba,bai sani ba ko soyayyar da yake nuna mata ne yayi yawan da take ganin kamar bazai tab'a iya rayuwa da ko wacce mace ba sai ita, ta manta cewar shi d'in namiji ne musulmi kuma wanda Allah ya halatta ma yin mace sama da biyu ma tunda yana da halin da zai auro su, duk da cewa yana da tabbacin cewa ita ma d'in tana matuk'ar kaunar shi, koba komai ai duk inda kaga kishi tofa yana tafe ne a cike da soyayya, matsalarta d'aya da bata iya sarrafa kishinta a duk sanda ya motsa mata sai kuma daraja da matsayin da miji yake dashi a wajen matar shi wanda ita bata duba wannan darajar in ta tashi magana dashi kai tsaye takeyi babu wani girmamawa ko ladabi, bata san inta aikata ba dai daiba ta duk'ar da kai ta nemi afuwa, ah ah a kullum ita gani take cewa ita dai itace akan dai dai. Zaije Lagos da kuduri ne guda biyu, na farko dan ya samu dai daito tsakanin shi da matar shi, dan a yanzun bayajin zai iya d'aukar wani sabon kalubalen da zata iya kawo mishi, dan haka zaiyi bakin kokarin shi wajen saita ta ta dawo kamar ko wacce macen kwaran da miji zaiyi alfahari da ita, Miye matsalar ta? Kud'i sune abunda tafi bawa mahimmanci fiye da auren ta, shima kuma Allah ya wadata shi yana da kud'in dan haka zai sakar mata su inhar zata dawo mishi kalar matar da yake fata, maganar aikin ta a can kuma duk yanda take son shi dole zata hak'ura ne ta dawo KD taci gaba da aikin zai nemar mata transfer in kuma tace a'ah tofa zai bata zab'ine yasan a yanda take son shi bazata yarda ta zab'i aikin ta akan shi ba, idan sun dawo nan Kaduna kuma zasuje suba uwar gida hak'uri ta dawo musu da yaran su a hannun su dan yana buk'atar had'e kan ahalin shi waje d'aya yana son yaran shi su taso da so da kaunar junar da yataso a cikin shi tsakanin shi da nashi k'annen, Sai kudurin shi na biyu, dan zuwa yaga Moon yarinyar da tunda yayi tozali da hotunan ta suka kafe mishi a kahon zuciya, Joseph ya Kira shi akan ya kammala duk wani binciken daya sashi yayi a kanta, yanzun sauran aikin nashi ne, shi dai a gefen shi ta mishi % percent bai san koshi d'in zai samu karb'uwa a wajen taba, sai dai kuma zaiyi iya bakin kokarin shi wajen shawo kanta harta amince dashi ba tareda ya nemi taimako daga wajen Meenal ba shi kadai zaiyi ma kanshi yak'i saboda ba iya farin cikin shi yason ya inganta ba harda na Mahaifiyar shi yasan cewa zataji dad'i kwarai inta samu labarin yana neman aure balle kuma idan taji cewa yarinyar tana da alaqa da Meenal, ร—ร—ร—ร—ร—ร— Alhamdulillah ya samu isa garin na Lagos lafiya, Joseph daya Kira tun kafin ya taso ya shaida mishi lokacin isowar shi, Shi d'in ne ya d'auko shi daga Airport sai da suka tsaya a wani restaurant sukayi takeaway kafin suka k'arasa gidan shi, Envelope d'in da yake kunshe da bayanan binciken da Joseph yayi mishi akan Moon ya gabatar mishi sama sama ya mishi bayani akan ta domin suna cikin tattaunawar ne shi Joseph din ya samu Kira na gaggawa akan an wuce da matar shi asibiti zata haihu, wannan kiran shiya katse komai duk da Joseph d'in yaso Sarki ya zauna dan ya huta shi yaje asibitin amma Sarki ya nuna mishi cewa babu komai su tafi taren kawai, Dan haka suka rankaya zuwa asibitin, motar Joseph a gaba motar Sarki da d'aya daga cikin sojojin dake gadin gidan yake ja kuma suna binshi a baya a haka har suka isa asibitin, koda suka je sun samu an shiga da Matar Joseph din d'akin haihuwa sai iyayen matar dana Joseph din ne a wajen suna zaman jiran tsammani, Basu yi tsayuwa na mintuna 20 a wajen ba ya farajin muryar d'an shi Abubakar da suke Kira da Boy yana kwala kiran sunan shi, "Daddy! Daddy!! Daddy oyoyo ga dady" Yaron yake fad'a da harshen turanci a yayin da ya k'araso da gudu cike da murna ya rungume uban nashi, Wanda shima Sarki mamaki yake akan su kuma me sukazo yi a asibitin da daren nan, duk da mamakin da yake ciki hakan bai sa ya kasa nuna farin cikin shi na ganin sanyin idaniyar shi a dai dai wannan lokacin ba koba komai shima yayi kewar yaron nashi, dan haka sai yasa hannu ya d'ago shi yana jefa shi sama yana cafewa, "Oh my Boy kaida waye kuka fito da daren nan daya kamata ace kana kan gado kaima kana bacci?" Sarki ya tambaya, sai dai mai makon Boy ya bashi amsa sai shima ya jefo mishi tambaya kamar haka, "Daddy kaima kazo duba Baby da Smole Mom tace Momy zata haifa ne koh" Ya tambaya yana shafa fuskar baban cike da farin cikin ganin baban nashi da yayi a lokacin, "Sabon Baby na Momyn ka kuma? Ita kuma Momyn naka tana ina?" Ba tareda yaron ya damu ba ya amsa mishi da cewa, "Ai tana ciki kuma kullum ma anan take kwana ko nace ta tashi mu koma gida bata zuwa" Sosai kan sarki ya d'aure dan bai fahimci surutan da Boy ke mishi ba inya fahimta dai dai fa yaron yana nufin Teemah tana nan asibitin kuma wai anan take kwana bata komawa gida, ga sabon Baby da yaji Boy d'in ya ambata, to kenan Teemah nada ciki kenan? "Kai da waye kukazo nan?" "Smole Momy" ya amsa yana nuna mishi inda Aziza ke can gefe tana amsa waya da alama bata san cewa Boy ya sulale a wajen ba, shi kuma sarki dama tunda yaji yaron ya ambaci smole Momy yasan ita yake nufi dan duka yaran haka suke kiranta, Excusing kanshi yayi daga nan inda su Joseph suke ya kama hannun yaron suka k'arasa inda Aziza take, Da gudu Boy ya k'arasa wajen yana fad'a mata cewa ga dadin shi yazo ganin Momy da baby, Gaisuwa sukayi tsakanin ta da Sarki cike da girmamawa tana mishi barka da zuwa, bai iyace mata komai ba harta mishi jagora zuwa d'akin da Teemah take, wanda isar su yayi dai dai da fitowar Brigadier general Abubakar da matar shi Aunty Rahma daga d'akin na Teemah, Dan haka babu b'ata lokaci Sarki ya zube zuwa k'asa domin nuna girmamawa ga sirikan nashi da suka rik'eshi tamkar d'ansu,

Chapter 51 of 92