Share this page
ya dace, Idan nayi nan sai tayi nan na rasa me take nufi dani, wai har cemin fa tayi wai ita ba aure ne a gabanta ba yanzun, to wai so take ta maida ni d'an iska in zuba ido ina kallon maza na mata layi daga nan har zuwa sanda taga dama kafin muyi auren? Kana kallon dai yanda nike ta k'okarin canza kaina duka a kokarina na ganin na shawo kanta amma kasan me? Har yanzun banga wani canji mai girma a tareda ita ba har yanzun kallon taubashi abokin wasan ta take min" Ya k'arasa fad'a a dame sosai, "Bana so in tauye tane shi yasa nike tabi a sannu ba tareda na gabatar da kaina a gaban manya ba, amma tunda hakan ta zab'a ni kuma bani da wani zab'i sai na aikata hakan, idan Allah yasa su Baba Usman su iso lafiya zanyi magana dashi kawai suje su nemar min auren ta idan yaso daga baya ma daidaita tunda haka ta zab'a" "Hakan ma tunani ne mai kyau, nima naso inyi maka wannan maganar gara batun yaje gaban manya saboda idan hakan ya faru shine zata k'ara tabbatar da cewa da gaske kakeyi, Yanzun dai kar kayi fushi tashi kaje ka sameta a sashen Hajiyan kuma idan kaje koda wasa karka nuna mata b'acin ranka" "Musty yarinyar nan fa ta riga ta gama raina ni wallahi," "Ah ah ba raini bane su mata haka suke, hakan kuma da takeyi shike kara tabbatar da cewa tana da class dan haka karka damu kanka, Kasan yan magana sukace Mai ganin abu daga nesa da tantama yake sai mutum ya matso kusa zai gano abunda ya dace, Muje in taka maka" Jawo hannun AK din yayi ya mik'ar dashi tsaye, haka suka jera suna tafe suna k'ara tattauna wa sai da yakai shi har bakin k'ofar falon kafin ya juya ya koma da baya zuwa side d'in Hajiya Jummai shi kuma AK ya shiga falon da Sallama. Zaune a falon ya sameta wayarta ne rik'e a hannun ta wanda ta maida gaba d'aya hankalin ta akan wayar tana faman latsewa, da alama chatting takeyi kuma yasan baya wuce ace dasu Meelat take chat d'in, Kwarai kamar yanda ya hasaso dasu take chatting domin tun bayan tashin Hajiya ta maida hankalin ta akan wayan saboda yau su dukan su suna online suna magana ne akan isowar da Moon zatayi Zaria jibi, hankalin ta ya d'auku akan hirar nasu dan haka gaba d'aya sai bata k'ara tunawa da batun AK daya aiko yaro kiranta ba, Har ya isa inda take sam bataji motsin shigowar nashi ba gane hakan da yayi shi kuma sai ya koma ta bayan ta gefen kunnen ta yakai hannun shi ya tafa su da k'arfi "Faff" karar Sautin tafin hannun nashi suka shiga cikin kunnuwanta a bazata, sosai ta firgita wanda har hakan saida yayi sanadin data jefar da wayar dake hannun ta, tana shirin zurawa da gudu a cikin halin firgicin da take shi kuma ya rik'o kafad'un ta da hannun wanshi ya maida ta zaune, "Ke dallah can matsoraciya kawai, wai me yasa kin cika tsoro ne? daga d'an tafa hannuwa shi kenan duk kin wani bi kin firgice kamar wacce tayi karo da kura ko wani abun da zai iya cutar da ita! Nine fa ba kowa ba" Tureshi ta farayi tana kai mishi duka tako ina, Tsalle d'aya yayi ya tsallako daga bayan kujerar da take ya dawo ta gabanta yana dariya, "Nidai wallahi ka dauki alhakina, babu damar mutum ya zauna shiru indai kana gida sai ka sashi yayi surutu, waima Ina ruwan ka dani to?" "Niko keda ruwa dake Darling da fari dai wana kama?"ya tambaya yana tsats tsareta da ido, "To ni wani abu na maka da zaka kamani?" "Oh da gaske baki san abinda yasa zan kamaki ba? To waye na turo yaro ya kiramin tace ma yaron ya koma yace min tayi bacci? Shi baccin ai naga shi nazo na sameki kinayi, ba d'azun dama nace miki zanzo hira ba, mai yasa baki fitoba kika shanya ni a waje? wulakanci ne hakan da kikayi fa, amma dai ba komai na yafe miki karki k'arayin haka next time dan naji haushi sosai da kika shanya ni baki fito ba" Ya fad'a a fizge bayan ya d'an kame fuskar shi kad'an, Shiru tayi ba amsa, Shima kuma sai yayi shiru da bakin shi daga karshe ma sai ya jinginar da kanshi a jikin kujerar kawai yaci gaba da binta da kallo kamar ya samu tv shi dai wallahi Allah ya sani baya jin zai tab'a iya gajiya da kallon ta, dan shi kad'ai yasan yanda yake ji aduk yanda ta kasance kusa dashi irin haka Allah dai yakai damo ga harawa, ko baici ba ai zaiyi burgima son rai wallahi, Shifa bai iya kallo yana d'auke kaiba ah ah inzai kalleta kallon ga daga yake mata ita kuma sam ta kasa sabawa da hakan, da zarar ya fara kallon ta duk sai taji ta tsagu bazata samu kwanciyar hankali ba har sai ta dena jin nauyin idanun shi a jikin ta, dan haka ko yanzun bayan data d'auki wayarta kasa cigaba da chatting din tayi ko nasu chat din dake shigowa cikin wayarta kasa karanta su tayi a tsanake dan bata gane komai kuma, sunyi zaman a haka na tsayin lokaci baice mata komai ba sai kallo itama kuma ta kasa tanka mishi, gajiya tayi da zaman ta mik'e tana mikewa kuma shima ya mik'e tunda ta fara taka matakalan benen bata yarda ta juyoba domin tunda taji takun tafiyar shi a tare suke haurawa tasan bazai wuce yace zashi d'akin Hajiya ba, Sai dai abunda bata sani ba shine ita dashi a tare suka kai cikin d'akin da yake matsayin nata yanzun a gidan, bata lura dashi ba kwata kwata dan haka koda ta shiga sai tayi tsaye a tsakar d'akin dafe da k'irjin ta tana sauke a jiyar zuciya a jejjere dan tun dazun bata samu damar shaqa ko sauke numfashi da kyau ba har saida ta shigo cikin d'akin, Tunawa da tayi cewar bata kulle k'ofar d'akin bane hakan yasa ta juyawa da niyyar ta kulle k'ofar gudun karma idan ya fito daga d'akin Hajiyar yace zai lek'o nata, sai dai kuma tana juyawa taci karo dashi tsaye kik'am a gabanta hannayen shi goye ta baya yana binta da kallon nashi da yake mugun takurata, Bud'e baki tayi da niyyar kwarara ihu sai shi kuma yayi azamar daura hannun shi manuniya a saman lab'b'anta, "Shishshsh" yayi mata alamun tayi shiru da bakinta, Ganin hakan ita kuma sai ta fara matsawa baya saboda kusancin dake tsakanin su yayi yawa sosai ta yanda har tana iya ganin yanda numfashin shi yake sauka a k'irjin shi dan rigar dake jikin shi duk da cewar bata kama shiba sam amma wuyar rigar yana da fad'i sosai kuma yadin rigar irin mai kwanciya ne a jiki, ga kuma gashin dake kwance lufluf akan k'irjin nashi da suka nuna kansu ta inda wuyan rigar ya sauka, Kallo d'aya tama wajen a cikin kuskure tayi saurin d'auke kanta bata k'ara gigin kai idonta wajen ba ta ci gaba da matsawa baya, Ganin tana yin baya shi kuma sai yaci gaba da binta tana matsawa yana binta har takai jikin wardrobe din d'akin ta jingine dashi, K'ara matsowa yayi sai dai bai yarda ya matse mata waje da yawa ba sai yayi amfani da hannuwan shi ya dafe jikin wardrobe din ya zamana ya sanya ta a tsakiyar hannayen nashi, Kankame jikin ta dake rawa sosai tayi bayan ta runtse idonta da kyar ta samu ta iya fusgo magana da karyayyar murya tace, "Me.. Me... Me kakeyi, meee kakeyi haka dan Allah? Mai maa kazooyi anan too?" Murmushin mugunta yayi yana cigaba da kallon ta yace, "Oh baki ma san abinda nazo yiba bayan nazo tad'i kin shanya ni a waje saboda rashin tsoron Allah kika k'i fitowa, na shigo har ciki kuma haka bakiji tausayina ba kika k'ara shareni daga k'arshe ma sai guduwa kikayi, na biyoki kuma kina tambayar mai nazo yi, to hira nazo muyi a cikin d'akin tunda anan kike so muyi hirar koh?" Ya tambaya yana d'age mata girar shi, "To aini dama nace maka bazan zo ba" "To da bakizo ba bagashi ni dana matsu dason ganin naki nazo ba, ko bakiyi murna da zuwar nawa ba?" Tura baki tayi kafin ta bashi amsa da cewa, "To ai hira a k'ofar gida akeyi shine kai kuma ka Kama ka biyoni har cikin d'akin bacci na, anan ne zamuyi hirar ko koh so dai kakeyi Hajiya tazo ta ganka in shiga uku, Mai zance mata idan ta sameka anan? Nidai dan Allah ka rufamin asiri ka tafi ba dan halina ba" "Oh kunyan Hajiya kikeji bayan a gabanta na maimaita kalaman soyayya ta a gareki, Idan ta tambaya zance mata nazo hira ne mana tunda a gabanta na aiko yaro kika ce acemin kinyi bacci, Ni kuma bazan iya bacci ba tareda na ganki ba shi yasa na biyoki har nan" Ya furta hakan babu alamun damuwa ko d'ar a tareda shi, "To ai ka ganni tun a falo mai yasa baka tafi ba?" "Ok saboda ba iya ganin naki ne ya kawoni ba zuwa nayi ki bani amsar da nike jiran ji daga gareki, Shin kin amsa soyayyar tawa in aika nawa iyayen can gidan ku ko koh har yanzun baki gama nazarin da kikeyi a kaina ba?" "To aini na fad'a maka ba yanzun zanyi aure ba" "Ni kuma Ina mai tabbatar miki da cewa yanzun shine lokacin da nike buk'atar ki a cikin rayuwana dan haka rashin shirin ki bazai dakatar dani ba" "Nidai dan Allah ka tafi to naji na yarda gobe zan baka amsar eh ko ah ah din da kake son ji," "Gobeee" ya furta yana hura mata iskan bakin shi akan fuskarta, "Lallai bakya son in tafi indai har sai gobe ne bazan iya jira ba, kodai ki amsa ki furta min da bakin ki cewa kina sona ko kuma yau in kwana a cikin d'akin nan.... " Tun bai gama furta kalmar kwana a d'akin ba ta katse shi da cewa, "Meee 😳 "idanuwa a waje tana binshi da kallon tarin mamakin shi daya ke neman sa zuciyarta tsayawa daga aikin, "Wai anan d'akin zaka kwanan?" Ta tambaya saboda ta k'arajin tabbaci daga bakin shi, "Oh kina wasa dani koh kina ganin kamar bazan iya ba, Ok to bari ki gani" Kamo hannun ta yayi suka k'arasa k'ofar dakin dake bud'e har yanzun, da kafar shi yayi amfani wajen tura k'ofar ya rufe kafin ya murza key a jikin k'ofar, Kuka take shirin fashe mishi dashi ganin da tayi da gaske ya kulle k'ofar d'akin, K'arfi yasa ya juya ta kafin ya matsa gab da ita ya had'a bayan ta da k'irjin shi sai dai sam bai yarda ya matse taba, Duk'o da kanshi yayi saboda tazarar tsayin dake tsakanin su, ya cusa kanshi a gefen wuyanta ba tareda ya kwantar ba, rawa jikin ta ya d'auka dan take taji wani zazzabin tsoro yana neman kamata kankame jikinta tayi sosai, Bakin shi ya maida kusa da kunnen ta kafin murya can k'asa ya furta mata cewa, "To yane Dr kin shirya amsar Soyayyar nawa kuwa? Ko har yanzun kina da ja" Shiru tayi jikinta naci gaba da rawa, "Kinsan dai in baki amsa ba ana zan kwana koh?" Ya kara fad'a bayan yayi k'asa da muryar nashi sosai fiye da yanda yayi magana da ita a d'azun, "Eh na shirya yanzun indai na baka amsa ai zaka tafi koh?" Ta tambaya da muryar kuka dan Wallahi ita dai a tsorace take,kawai ya fice mata a cikin d'akin shi tafi muradi, "To kice kina sona sai in tafi, kuma da shauk'i nike so kalaman su fito daga cikin bakin ki" "To shikenan naji Ina sonka amma da sharad'in ba yanzun zamuyi aure ba" Ta fad'a da shakakkiyar murya, "Ban yarda dako wani sharad'i ba An mata, kuma ni ba haka nike son kalmomin su fito daga bakin kiba, haba ai ko kema kin san cewa sam baki furta kalaman naki da shauki yanda ya daceba, haka nike so inji kince, Abdul Khareem Ina sonka na kuma amince zan aureka mu rayu har k'arshen numfashi" Ya jero kalaman a natse kuma a tsare yana kwaikwayon muryar ta, "In kuma hakan bai miki ba bari in maimai ta miki nawa kalaman sai ke kuma ki bani amsa," A yanzun kam jingina ta yayi da jikin shi ya kuma ziro hannayen shi ya d'aura akan nata wanda suke cikin juna a dai dai cikin ta, "Ameenat Ina sonki irin son da zuciya da gangar jikine kawai suka san adadin shi, dan Allah ki tausaya ki amshi soyayya ta, ki bani dama in gabatar da kaina a gidan ku matsayin mai neman auren ki, ni kuma nayi miki alkawarin cewa zan kula dake fiye da yanda zan kula da kaina zanci gaba da sonki har zuwa gushewata" Yana maganan ne yana k'ara kan kameta a cikin jikin shi cike da shauk'i, hucin numfashin shi da kuma gashin gemun shi da yake gogar mata wuya sune abinda suka kassara ta ita kuma, sai dai duk yanda taso ta kwaci kanta hakan ya gagara saboda k'arfin su ba d'aya ba kuma ba rik'on wasa ya mata ba, "Ki dena wahal da kanki bazan sakeki ba har sai kin bani amsa, kinyi shiru ke nike saurare fa ko baki so in tafi in barki kiyi bacci ne?" "Ina so" ta fad'a da shakakkiyar muryar ta wacce tayi sanyi kalau, "Uhumm to ki fad'amin mana" "Ina, Iii... Inaa sonnn.. kaaaa" "Banji abinda kikace da kyau ba" "Ai nace Ina son ka nidai ka sakeni haka ka matseni fa kuma ai d'azun nan nace maka bana son kana tab'ani.... " Bata kai karshen zancen ba yasa karfi ya matse ta ya d'aga ta sama ya fara juyi da ita a cikin d'akin, Shi yana ihun murna ita kuma tana ihun kiran dan Allah ya sauketa tana ganin jiri, dan da gaske jirin take gani "Dukan k'ofar d'akin hajiya keyi ta waje tana faman kiran sunan Meenal, "Ke Meenal wani sabon shegen taka ne kuma zaki shiga d'aki ki rufe kina yima mutane iface iface, bazaki zo ki bud'e k'ofar nan ki gaya min ihun ubanme kikeyi ba" Jiyo bugun k'ofar da Hajiya keyi ba kakkautawa ne yasa shi sauke ta bai tsaya bi ta kanta ba duk da cewa yana kallon sanda jiri ya kwashe ta ya watsar a kan gadon ta dake gefe, Da sauri ya bud'e k'ofar d'akin yana budewa kuma ya janyo hannun Hajiya ya fara jujjuyata irin rawar nan da turawa keyi, ya farayi da ita sam bakin shi yak'i rufuwa tsabar farin cikin daya ke ciki, Bige hannun shi hajiya tayi da karfi ta kumayi amfani da k'afarta ta take nashi kafar da karfin da allah ya bata, Ta kuwa yi nasara dan Zafin bugun dana taka war su suka sanya shi cin burki na dole, a shagwabe ya kalleta, "Hajiya bakiga Ina cikin farin ciki bane shine kike so ki b'ata min mood din da nike ciki mai dad'i," Jawo Hajiyar yayi ya rungume tsan tsan cike da murna yake cewa, "Hajiya takwarar ki ta amsa tayin Soyayya na a yau, ta kuma yarda ta bani dama in tura iyayena a nemo min auren ta, shi yasa kikaga Ina ta murna Hajiya burin ki zai cika kwanan nan na ganin aure na" Daure fuska sosai Hajiya tayi tana binshi da kallo sheqeqe ta bud'e baki tace, "Shi soyayyar duk yafi k'arfin a bada amsar shi a ko Ina duk fad'in gidan nan har sai an shigo har cikin kuryar d'aki?, Kenan da tace ace maka tayi bacci wanko naka kafafuwan kayi ka biyota har cikin d'aki saboda gaka rasa kunya, to fita maza fita mata daga d'aki kuma kar in k'ara ganin ka a cikin d'akin nan koda wasa," "Hajiya bafa abunda kike tunani bane, kema ai kin san bazanyi haka ba, kawai dai na kasa hakuri akan jan ajin da take min ne shi yasa na biyota har nan d'in kiyi hakuri," Hannun ta yaja sai da suka kai bakin kofa yaci burki, kafin ya juya yana kallon Meenal data cukuikuye kanta a k'asa ta had'a kai da gwuiwa a gefen gadon tun bayan shigowar hajiya d'akin, "Dr good night " Ya fad'a yana aika mata da kiss din da yayi ma yatsun shi guda biyu ya nuna ta dashi, janye shi Hajiya tayi tana kai mishi bugu da mitan cewa bamashi da kunya a gaban idonta yake aikama jikarta kiss wato shi ga fitsararre sirikin zamani tana cigaba da mitan suka k'arasa fita daga d'akin tana cema Meenal , "Ki taso ki kulle k'ofar ki kuma dunga kulleta da key kina ji na fad'a miki karki yarda ki dunga kwanciya baki kulle kofa da makulli ba " Bata iya mik'ewa daga inda take ba har sai da ta tabbatar da cewa sun sauka k'asa kafin taje ta tura k'ofar d'akin ta rufe da key ta koma kan gado ta kwanta a rigingine tana kallon silin din dakin, murmushi ne ya kwace mata sai tayi saurin kai hannu ta rufe fuskarta tana mai jin kunyar kanta da kanta, Wai yau ita Meenal itace ta furta cewa tana son wani, harma ta bashi daman zuwa ya nemi a auren ta a wajen iyayen ta, Sam batayi zaton cewa hakan zaizo mata da wurwuri ba, lallai AK ya shammace ta da yawa, ita da taci buri mai girma nayin rayuwar da take so ta yanda zata biya bashin Yarintan ta da aka dakushe mata, sai gashi tun ba'aje ko Ina ba da alamu burin nata dai bamai cika bane. *UMMIEE CE*✍🏼 [9/20, 10:20 PM] Ummiee Zaria: βšœοΈπŸ”±πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *DANGINA*πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ”±βšœοΈ *BOOK 2* *PAGE 32* No editing πŸ˜’ Daga ABU kai tsaye Unguwar Malamai Bash ya wuce dan dole yana buk'atar yin bincike akan Meenal daya gani yau, da gaske auren nata ya mutune har take shirin yi wani auren ko ya abun yake? Idan yayi nazari akan maganar da yarinyar can mai kama da yar tsana ta fad'a mishi kenan hakan yana nufin auren Meenal ya mutu zawarci takeyi a yanzun haka! To amma in haka ne mai yasa bata neme shiba, Yayi zaton cewa a yanda komai ya kasance a tsakanin su suka rabu suna masu kewar juna ba tareda sun shirya rabuwa a lokacin ba ai bai dace ace yanzun auren ta ya mutu kuma harta kasa neman shi dan ta shaida mishi ba, yanzun ashe da ace baiyi katarin ganin ta a yau dinba da shikenan har saita k'arayin wani auren kafin in yana da rabon jin zance yaji daga baya? Anya Meenal tasan cewa rashinta ne ya hana shi yin wani auren har yanzun kuwa? Yaso Meenal irin son da bai tab'a tsammanin cewa zai iya hak'urin rashin ta ba, sai gashi a daidai lokacin daya gama tsara yanda zasu gudanar da rayuwar su a karkashin inuwar aure bak'in labari ya iske shi a ranar d'aurin auren ta, Sumewa yayi fa tsaf a sanda iyayen ta suke fad'a mishi cewa yau din shine za'a d'auren ta, *BARI MU D'AN KOMA BAYA KAD'AN* Idan baku manta ba a ranar d'aurin auren Meenal da Sarki wancan lokacin Aunty Hassana ta amshi Number din Bash a wajen Meenal da sunan cewa ita zata kira shi ta shaida mishi halin da ake ciki, In baku manta ba kuma a wannan lokacin shi Bash din yana ta fama da Meenal din ne akan ta amince mishi ya turo magabatan shi dan shima ya gabatar da kanshi a gaban Malam amma sam tak'i a cewar ta karatu zatayi. Abinda bata sani ba ita kuma shine tunda yabitaΒ² akan ta bashi dama tak'i shine kawai ya yanke hukuncin cewa a ranar d'aurin auren nasu Raheenat shima zai tura nashi iyayen, Dan haka koda kiran Aunty Hassana ya riske shi akan idan yana da hali yazo gidan Hajiya tana neman shi baiji wani d'arba dan koda ta kira dama shima yana tare da nashi iyayen ne da zasu tafi wajen d'aurin auren tare dan so suke idan an gama daura auren su kuma sai su nemi ganin malam dan su gabatar mishi da abinda ya kawosu wato neman auren Meenal, Ba karamin dadi yaji ba a sanda yaji cewa kiran daga yayan Maman Meenal ne, kawai sai tunanin shi yake bashi cewa k'ila Meenal din ce ta gabatar dashi a wajen su tunda inba haka ba ta ina Yayar mamanta zata san da zaman shi balle kuma harta samu number din shi ta kira shi kai tsaye haka, Dan haka daya tashi tafiya gidan sai bai tafi shi d'aya ba suka wuce tare da Kanin Maman shi d'aya da kuma wani Yayan Baban su wanda idan yaran mazan gidan su zasuyi aure shine yake shigewa gaba. Tarba na girma da mutunci akai musu duk da cewa ita Aunty Hassana batayi zaton cewa tare zaizo da iyayen shiba, sai bayan data fito ne taga bashi kad'ai bane dan dole suka koma sashen Hajiya domin dai bazai yuwu abar iyayen nashi a mota suna jira ba, Kuma koba komai tunda abun ba wanda za'a tsaya ana boyewa bane tasan dole zasuji dan haka sai tayi musu iso suka d'unguma zuwa Falon Hajiya gaba d'ayan su, Bayan sun gama gaishe gaishe ne Yayan Baban Bash din ya gabatar da kanshi a matsayin waliyin Bash da cewar dama a yau din sun shirya da sunan idan an gama d'aurin aure ne suma zasu gabatar da nasu neman auren sai kuma ga kira shi Bash din ya samu shine yasa suka d'unguma sukazo gaba d'aya tunda dai suma nan d'in ai iyayen Meenal ne tunda sun san da ace har wannan lokacin Prof Abdul Khareem yana raye dashi da kanshi yana iya bashi auren Meenal din, Jikin kowa yayi sanyi a wajen saboda jin abinda yake tafe dasu, Hajiya ko harda yar kwallanta dan ita wallahi da ace tasan da batun bash d'in nan da wuri da tabbas zatayi tsaye wajen ganin auren nan bai tabbata ba amma ina sai gashi ya bayyana mata a cikin kuraren lokacin da babu abunda zata iyayi dole saidai tayi hakuri, dukan su a wajen rasa kwarin gwuiwar shaida musu zancen auren Meenal din da za'ayi a ranar sukayi, Ita Anty Hassana dama tunda ta musu iso ta lallab'a tabar falon Abba Ahmad daya kasance shine Babba a yaran Hajiya shi Hajiya ta wakilta akan ya shaida musu halin da ake ciki, Saida yayi ma Bash doguwar nasihar data jefa Bash d'in cikin kokonto kafin ya shaida musu halin da ake ciki na auren ita Meenal din da Bash din keso, ya kuma fad'a musu gaskiyar cewa itama kanta yarinyar bata samu labarin d'aurin auren ba sai a jiya sannan aka shaida mata, tun jiyan kuma har yau bata cikin yanayi mai dad'i faruwan hakan ne kuma yasa ta shaida musu cewa bash d'in ne yake neman ta da kuma cewar ya dade yana son ta bashi damar gabatar da kanshi a wajen iyayen ta amma sai batayi hakan ba, Sun san cewa a yanda yake sonta dole zaiso ace ya kasance a wajen d'aurin auren kannin ta yau d'in sai dai kuma su bazasu so ace ya riski labarin a wajen daurin auren ba shi yasa suka kira shi dan su shaida mishi abunda yake faruwa, Tashin hankali irin wanda yake zuwa babu zato bare tsammani shine ya faru a wannan rana domin dai tuni fa Bash ya d'auke wuta, abu kamar wasa sai gashi ya zama gagarumi domin dai tunda suka fahimci ya suma suke faman sheqa mishi ruwa a k'okarin su na ganin ya farfad'o sai dai shiru, ya sheme kawai abinshi babu rai ba alamar shi, dan haka hankali

Chapter 68 of 92