shekarun baya,
Firrr yanzun kam ta hanashi zuwa zaria komai akeyi bai zuwa sai dai aike hatta da yaran shi dake hannun uwar gida yanzun bai wani damuwa da al'amarin su ta uwar su kadai yakeyi.
Ita ko Teemah duniya tayi mata dad'i domin dama tuni abunda take so kenan taga Sarki yazama mata mijin kan tace, gashi kam ta samu dan yanzun dai sunan kawai yana aiki a KD ne amma duk sati yana Lagos bayan haihuwar ta kuwa hutu tasa shi d'auka na musamman dole ya koma Lagos sukayi jegon tare, ganin cewa yanzun shi kanshi da komai daya shafeshi yana karkashin ikon tane yasa gaba daya harta da yaran ta dake Zaria bata tunawa dasu balle kuma acewar ta yanzun ta haihu tunda ta haifo Namiji.
Al'amarin Sarki wannan karan ba uwar gida kad'ai ya dama ba hatta da ubanshi mahaifi dama sauran yan uwan shi kwarai abun ya damesu, domin dai suma sunata nasu kokarin bakin gwargwadon nason ganin ya dawo hayyacin shi sai dai ina, domin sosai Teemah ta rike wuta wannan karan.
Daga karshe dai sun tsaya akan matsaya d'aya cewa dole dai su k'arayi mai aure a wannan lokacin domin indai yana da wata matar anan Zaria dole ko baizo garin dan iyayen shi da yaran ba ya zo kodan matar shi.
Hhhhhh naku wasa ne, wanda bai tuna da uwar shi bane zai tuna da wata mata.
A hakan dai sosai uwar gida ta matsama Malam Sulaiman akan maganar cewa yaje ma Malam dan Susan wani mataki suke kai yanzun duba da cewa su Meenal din na gab da kammala makaranta,
Gaskiya Malam yana cikin halin k'ak'ani kayi, domin dai sosai abubuwa suka rikice mishi domin dai tsayin lokaci daya d'auka yana Addu'a akan nemawa Aminatu zab'i mafi alkhairi bai tab'ajin kin had'in aure tsakanin ta da Sarki ba, sai dai shi abunda yake hangowa idan yabada ta aure ma Sarki meye zai iya biyowa baya? Domin dai tsaf yana sane da chakwakiyar da ake ciki hatta shi da kanshi sosai yake tsaye wajen yin ma Sufyan d'in Addu'a dan ganin ya dawo hayyacin shi domin a bayyane take cewar a yanzun kam Fateemah tasha kan Sufyan, to amma in yak'i auren yaba ma wani Aminatun ba lallai Malam Sulaiman da Uwar gida su mishi uzuri ba, dan haka yana ganin gara ayi auren in yaso sai su bisu da Addu'a kawai,
To amma Aminatu fa?
Hakuri zatayi koba komai ai Sufyan d'an uwanta ne koba komai yasan bazata k'ishi ba tunda ba wasu samarin take kulawa ba dama balle har tasan abinda take so.......
Hhhhhhhhh akwai gwarama fa. Domin ko dai Malam ya amsa cewa yabama Sarki Aminatu su iyayen Sarki suje su shirya sai dai ya kwab'e su akan Sam koda wasa baya son maganar neman auren ya fita waje dan haka dole komai na neman haka suka gudanar dashi a sirance domin Malam ya tabbatar ma kanshi da cewa bayan shedaniyar mata da Allah ya had'a sarki da ita tofa ba tantama akwai na kusa dashi da suke mishi bita da kulli, lokaci yana ta tafiya har ya rage baifi wata d'aya dasu Aminatu zasu fara jarabawar su ta fita ba,
Kai jama'a Malam bazai tab'a iya dena halin shiba, domin dai wannan karan ma a kokarin shi na ganin cewa bai kuntata ma Meenal ba yasa ya yanke hukuncin aurar da Raheenat da y'ar wajen shi Sa'adatu wadanda suke gudanar da rayuwar su cikin kwanciyar hankali ba tareda tsammanin zancen auren su zai taso nan kusa ba domin dai dama duk cikin su Meenal ta girme su sun san ko auren za'ayi sai dai ita amma me?
Kwatsam ranar wata Juma'a kamar yanda suka saba zuwa islamiyar safe kafin a dawo ayi shirin tafiya makarantar boko, suna isowa kofar gidan suka fara ganin cincirin don mutane, iya hasashen su sun gaza gane ko taron jama'ar na menene domin dai ba'aiyi haihuwa a kusan nan ba balle suce taron suna! Basu ga kuma alamun bak'in ciki ko alhini a fuskar mutanen ba balle suce taron mutuwa ake, to me ya faru? Sai dai kuma babu mai basu amsa hakan yasa dole sukaja kafafuwar su suka shige cikin gida.
A farfajiyar ko ba taron komai akeyi ba saina baikon auren Raheenat da Sa'adat wad'anda Malam ya duba a cikin wad'anda suka fito neman auren Aminatu ya musu madadi da kannen ta.
Soyayyar da Malam yakema Aminatu soyayya ce mafi kololuwar girma wanda hakan yasa koshi baya son yazama sanadiyyar k'uncin ta balle kuma wani, sai dai soyayyar ta rufe mishi ido sosai ta yanda baik'i wasu su shiga wani yanayi ba indai ita zata samu sassaucin damuwa a zuciyarta,
Hakan nema yasa shi yanke hukuncin ya hadesu ukun ya aurar sannan a maimakon ita kad'ai a cikin su ta auri mai mata da yara hudu ya yanke hukuncin suma sauran duk masu mata da yaran zasu aura, sai dai a maimakon ita mai yara 4 su nasu mazajen yaran su sun zarta hakan, dalilin shi na kara rufe zancen auren ta tuntuni kuma shine dan kartaji ba dad'i amma yanzun inta samu labarin auren sauran ko nata yazo bazataji damuwa mai yawa a zuciyarta ba, dan zataga cewar ai an aurar da kannen tama balle kuma ita,
Duk yanda suka so suji taron me ake gudanarwa hakan bai samu ba daga karshe ma Ya Sa'eed ne ya kwashe su zuwa Kano a wannan ranar suka kaima Maman Kano ziyara da sunan washe gari zasu dawo, babu wacce tayi tunanin wani abu daban domin dama sun dad'e basu je kanon ziyara ba dan haka tuni suka sake jikin su suka dunga yawace yawace.
''''''''''*******'''''''''''''
Uwar gidan Malam Innan yara ce zaune a falon na Malam sai dai lokaci lokaci takan d'aga kai ta duba agogon dake manne jikin bango domin tasan dai zuwa yanzun tuni su Malam suka tashi a wajen karatun da sukeyi na dare shida magidan tan dake zuwa d'aukar karatun, sai dai kuma gashi shiru har yanzun bai shigo ba har ana neman karfe 10 na dare yanzun.
Jin motsin shi da kuma gyarar muryar shin nan daya zamar mishi (Bakandamiya) littafin Surayyahms🥰.
hakan yasa ta kara gyara zama, domin tabbas yau bata iya bacci saita tattauna da Malam akan batun baikon yaran nan da aka gudanar dashi da safe Wanda su iyayen gidan ko alama basuji kamshin maganar ba sai baiko dasa rana kawai ne ya musu dirar mikiya, domin dai aiko ada can baya kafin baiko sai Malam d'in ya turo mane man sun gana da yaran kafin asa ranar aure,
Da sallama ya shigo.
"Innar yara kece zaune? ashe na barki da jira mun d'an tsaya tat tauna wani batu ne da Sa'eed akan batun nashi auren dan so nike a had'e shi gaba d'aya dana yaran nan ayishi a huta koya kikace? "
Ya Kara she tambayar nashi a yayin da yakai zaune.
"Nima abinda ya kawoni kenan Malam"
"Ah to madallah amma yanzun dai fara zuba min abinci tukun ni kuma bari in d'an shiga daga ciki in canza kayan nan kin san an fara zafi a gari."
"To Malam a fito lafiya"
Har ya kai bakin kofar d'akin shi kana ya waigo gyarar muryar shi yayi wanda hakan ya maida hankalin ta kanshi.
"Nace ina fatan kin tahomin da nawa kason kunnun tamban dan d'azun naji yara na cewa kin dama kunun tamba?
Murnushi tayi tana cigaba da shirya mishi abincin,
shi kuma ya shige ciki yana ayyana cewa mata kenan, wato daga jin batun baikon yayan su shine ta kwaso jiki tazo dan ta tutsiye shi ya fad'a mata dalilin yin hakan, alhalin kosu Adamu da Auta babu wanda ya bude baki cikin su yace mishi mai yasa yayi haka? Mata hooo komin tsufan su dai basa tab'a ganin sun girma, girgixa kanshi kawai yayi ya shige makewayi dan ya watsa ruwa.
Bayan fitowar shi bata tada maganar ba har sai sanda ya kammala cin abincin shi ta gyara wajen sannan ta dawo ta zauna,
"Malam mike faruwa a gidan nan bamu da masaniya haka? "
"Wani abune ya faru a gidan hala? "
Shima ya maida mata da tambaya maimakon ya bata amsa,
"Ah ah ina magana akan baikon da akayi da safe ne nasu Raheena da Sa'adatu, kawai kuma sai mukaga ana taro bamu da masaniyar komai akan hakan! "
"Allah sarki eh wallahi baiko ne akayi harma da sa ranar auren da zarar an samu hutu domin so nike kowa ya samu damar halattar bikin auren koba komai ai mun dad'e bamu aurar da yan mata ba a gidan koh?"
Katseshi tayi da cewa,
"Amma Malam yaran fa"
Hannu ya daga mata yana mai daure fuska shima yace
"dakata Ameenah indai akan batun nan ne zan fad'a miki gaskiya inhar ba Addu'a zakiyi Allah yasa albarkha ya kuma tabbatar da alkhairi ba to ina ganin zaifiye miki alkhairi kiyi shiru da bakin ki, in kuma ban baki zakiyi to zaifi kyau kije kiyi ma iyayen yaran bawai niba domin na riga na yanke hukunci"
"Allah ya baka hakuri Malam amma ni dama gani nayi su yaran suna da mazajen da suka nuna suna bukatar auren su anan cikin gida, kuma koba komai yan magana na cewa gida bai koshi ba aiba'aba dawa nama ba!
Kaga ita Raheena ai Abubakar ke neman ta tun zuwan shi garin nan domin a sashena ma sukeyin zance, ita kuma Sa'adatu Farouq ke neman ta ban fad'a maka bane saboda nasan ba yanzun zaka aurar dasu ba, "
(Abubakar yaron Maman Kano ne aikine ya dawo dashi Zaria yana aikin Banki, shi kuma Farouq yayan Meenal ne)
"To ai gashi nan nauyin bakin naki yaja musu kinga kenan koba komai ni bani da laifi, domin dama ai wani baya auren matar wani sud'in ba matan su bane dan haka sai suyi hakuri su nema a wani wajen domin dai kin san bazai yuwu ince an fasaba tunda na riga na basu, kuma abunda baki saniba shine duk su ukun zan aurar harda uwata suma mazan zan tuntub'esu in akwai wanda ya shirya auren a cikin su duk a had'a ayishi lokaci daya a huta"
"Meenal d'in itama auren zaka mata? "
"Oh bakiji abinda nace da kyau bane hala? To bari in maimaita auren itama zan mata ina kuma fatan cewa baki manta da neman auren nata da uwar gida da Sulaiman suke tamin jele akan shi tsayin shekarun nan ba? To Alhamdulillah yanzun kam lokacin auren yazo dan dazarar sun kammala jarabawa bikin zai gudana, ina fatan kuma yanzun bazaki ce nayi son kai ba? "
Galala Innan yara ta saki baki tana kallon Malam cike da mamaki, lallai hakika yan magana sunyi gaskiya da suke cewa hali zanen dutse to ita kam yanzun me zatace tunda harta da yar gaban goshin shi a wannan karon bata tsira ba,
"Innalillahi Wa'innah Ilaihir Raju'un"
Sai da ta maimata sau uku a cikin zuciyarta tamkar wacce aka aikoma da sakon mutuwa sannan tace,
"Malam Sarki zaka aurama Meenal? Malam Sufyan fa! Wanda kowa yasan yanda matar shi take,
ta gagare shi amma dan bala'i kalli yanda ta zame mishi matar jaraba ta yanda har yanzun ya kasa rabuwa da ita, gashi yanzun har an kai matakin data rabashi da iyayen shi ciki kuwa harda yaranta wanda itace uwar su ba yayan riko ba! Malam Meenal din zaka aurar gidan kishiya mai tsafi?
Dan babu tantama tsafi yarinyar nan keyi shi yasa ta gagari kowa,Malam Meenal din kafa kake neman ka sadaukar a inda baka san kalar rayuwar kuncin da zata gudanar in anyi auren ba domin ko Wanda bai damu da yayan cikin shi dama iyayen shiba ina tabbatar maka itama ba zatayi daraja a idon shiba, Malam na rokeka ka soke batun had'in aure tsakanin ta da Sarki in ma auren nata a yanzun ya zama dole saboda lalurar ciwon ta Malam ka duba koda cikin yaran d'akina ne kona Dije ka hadata da wani, inba haka ba Malam zaka cutar da ita"
Bai bari ya barta ta karasa ba ya katseta a tsawace da kiran sunan ta
"Ameenahhh wai ba nace in bazaki fad'i Alkhairi akan auren nan kimin shiru ba? Ko ke kin san gaibu ne? fad'amin kinsan abunda ka iya faruwa anjima ko gobe? Ah ah koko dan Allah ya had'a shi aure da shaid'aniyar mace shike nan sai mu yanke tsammanin mu akan shi mu sakar mata shi kamar yanda takeso taci gaba da mulkarshi kamar Sarki da Bafade iye? Ko koh dan bakece kika haifeshi ba shi yasa kike kalubalantar auren? Fadamin idan a cikin yaran ki Allah ya jarabta da samun mace irin haka shin komawa gefe zakiyi ki rungume hannu ki zuba ido kina jiran ikon Allah ko koh zaki tashi tsaye ne da Addu'a domin neman ma kanki mafita? Aminatu ban sanki da son kai ba, koba komai uwar yaron nan kawarki ce ta kusa kinga ko inda kara dan kawarki ai nakine! Sannan uban yaron nan fa dan uwan kine tako ina dai Sarki dolen kine dan haka ban son in karajin wata magana a bakin ki sab'anin addu'ar sanya alkhairi domin mu bazamu gaji da fad'ama Allah ya kawo mana d'auki a wannan al'amarin ba"
"Kayi hakuri Malam nima insha Allah bazan k'ara kalu balantar zancen auren ba, ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya kuma kad'e fitina,"
"Ameen" Malam ya amsa dashi kana yaci gaba da cewa "munyi magana da yaron ki gobe su Auta zasuje gidan iyayen yarinyar dan haka sai ku fara shiri"
"Malam aini keda shiri nida keda auren yan mata uku ai ba zama kuma Allah dai ya bamu aron rai in mik'asu d'akunan su cikin aminci kamar yanda na mik'a sauran yan uwan su. "
*Bayan wasu kwanaki *
Maryam, Jameela, Aminatu duk sun fara zana jarabawar fita yayin da a gefen su Aisha da Moon suma hakan take duk sai d'auki suke akan su gama su taho Zaria domin yanzun kam ba fashi duk hutu a zaria sukeyin shi, dan yanzun an samu cigaba suma Meenal duk ta jajje gidajen su, dan an samu cigaba sosai ta fannin Meenal din dan yanzun ta sake sosai da yan uwan ta *Danginta* na wajen uwa sosai take jin dad'in yanda suke mu'amalan tarta suke nuna kulawar su akanta,
Sunyi jimami matuka a sanda zancen auren su Raheenat ya fito domin abun ya dake su matuk'a, wai su da koh sakandire basu gama bane za'a aurar, amma ya suka iya biyayya ga Baba Malam wannan kam tilass ne, ba amaren kadai bane sukaji rashin dad'i harda Meenal sai dai koda tajema Malam da maganar amsar daya bata shi yasata dole tasha jinin jikin ta ta koma ba amaren hakuri barin ma Raheenat da suke kwana d'aki daya, sosai tasan yanda Raheena da ya Abubakar suke kaunar junan su Wanda kusan duk jama'ar dake gidan sun san da hakan. Dan sosai ya shiga ciki tashin hankali a yayinda labarin ya iskeshi dan babu wanda koda wasa yayi zaton Malam zai aurar dasu Raheenat din a yanzun, da yasan abinda zai faru kenan da tuni ya gabatar da kanshi a wajen Malam sai dai kuma yanzun kam bakin alkalami ya riga ya bushe sai dai hakuri kawai da zaiyi shi akan dole,
Shirye ² aure fa yana ta kankama su Meenal sune amarori kirjin biki dan itace gaba² akan komai daya shafi amaren.
Duk abunda ke gudana fa nasa rana ku sani hatta da uwar Meenal bata sani ba domin dai Baba Auta gaba d'aya kwarin gwuiwar dazai tun kareta da batun nema ya nema ya rasa, to me zaice mata, ta shirya Malam zai aurar da Meenal nan da yan satikai ko ya zaice mata,
Yaje har wajen Innar yara akan ta taimake shi tazo ta fad'ama Jiddah din abinda ake ciki amma matar nan firrr tak'i a cewarta bata kar zomo ba wallahi baza'a bata rata ya ba, ya koma dai yasan ta yanda zai fad'a mata ai matar shine domin dai yasan aure ba fashi garama ya fad'a matan dan kullum kwanakin kara kusantowa sukeyi...........
Kun daiga yanda na daure na zuba muku tarin Read more saboda ina son yayi sauri koh?
To yasin in banga comment ba shiru zakuji gobe🤨🤨
Aci gaba sa Sharing dinshi please 🙏 .
#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*
*👨👩👧👦DANGINA!👨👩👧👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_
ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._
*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}
*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen.
```Page 27
Tunda ya baro wajen Innan yara yake ta famar sak'a da warwara,
Allah ya sani ba karamin kunyar Jidda yakeji ba dan hakika yasan ba'a kyauta mata ba sai dai koshi da yake matsayin uban Meenal babu wani abunda zai iyayi dan dakatar da batun auren.
Ganin cewa shirun bazai kawo maslaha ba yasa koda ya shigo kai tsaye d'akin Jiddah ya wuce domin gara ayi ta a kare yau kawai.
Waya ya sameta tanayi dan haka ya nemi gefen gadon da take zaune shima ya zauna, sallama tayi ma wanda suke wayar sannan ta juya gareshi,
"Barka da shigowa! yanzun ka shigo ko tun d'azun? na dan tsaya gyara kayane shi yasa banji shigowar naka ba"
Bai iya bata amsa ba illah kamo hannu wanta da yayi duka bibbiyun ya zare wayar dake rike a hannun nata sannan ya runtse hannun a cikin nashi hannuwan yana d'an mur murzasu ta yanda bazata ji zafi ba.
Daga kanta tayi gamida maida kallonta zuwa fuskar shi tana karantar yanayin da yake ciki domin karara ta karanto tarin damuwa kwance a fuskar nashi,
"Abban su me yake faruwa ne? Kasani koda baka fito fili ka fad'amin ba ina lura da yanayin da kake ciki tunda da aka fara maganar auren yaran nan domin nasan damuwar taka tana da alak'a da batun auren! "
Ajiyar numfashi ta sauke tana shafa tafin hannun shi ta d'aura da cewa, "Meye abun damuwa akan abunda ba yau aka fara ba! Naga dai tun tale tale dama haka kuke aurar da yaran ku da kananun shekarun su balle kuma yanzun da su d'in zamu iya kiransu kai tsaye da suna yan mata, gashi Alhamdulillah duka mazajen nasu ai babu yaro balle suyima yaran garaje, ina ganin gara kabar duk wata damuwa kabisu da Addu'ar fatan alkhairi sai kaga nan da wani d'an lokaci mun samu k'arin jikoki a gidan"
ta karasa fad'in hakan tana mai sanya murmushi a fuskarta duk dai dan taga ta rage mishi damuwar dake kwance a fuskar shi.
Duk abinda take cewa kallonta kawai yakeyi batareda yayi yunkurin katseta ba harta kai aya, sannan ya d'an k'ara janyota zuwa kusa dashi sosai yana mai kwantar da kanta akan kafadun shi,
"Hauwa'u Jiddah"ya kira sunan ta yana mai kallon cikin idon ta,
Dago kanta tayi ta kalle shi dan an dad'e rabon da taji ya kira cikakken sunan ta haka, dan ko sunan nata zai kira sai dai yace maman wane ko kuma ya kira ta da Jidda amma yau ya kira ta da Hauwa'u Jidda,
Sai da ya k'ara kwantar da kanta da kyau yana d'an bubbuga gefen kafadarta a hankali sannan yaci gaba da cewa. " da fari ina mai neman afuwar ki akan abunda zai fito daga cikin bakina zuwa cikin kunnuwan ki, Jidda ki sani a kullum ina alfahari da kasancewar ki matar aurena kuma uwar yarana, tsayin shekarun auren mu bazan iya tuna rana guda da kika tab'a b'ata min rai ba, duk da nasan cewa ni d'in lokuta da dama nakan b'ata miki amma baki tab'a fushi kika juyamin baya ba, dan haka yauma ina fatan zakimin uzuri akan abinda zakiji daga gareni"
Waiyo Allah wallahi da yasan yanda kalaman nan nashi ke rugurguza mata zuciya da yayi gaggawar fadin mata abunda zai fada.
"Abban su ka taimakeni ka fad'amin abunda ke faruwa, ko dai wani laifin ne mai girma na maka ban sani ba? "
"Bakimin laifin komai ba Jidda nine dai da Ahalina muka aikata miki laifi mai girma, hakan nema yasa nike kara neman afuwar ki, kiyi hakuri ki kuma kara hakuri,"
"Dan Allah Abban su ka fito ka fad'amin abunda ke faruwa, ko dai rasuwa akayi ne? Fadamin waye ya rasu kake boyemin? "
"Ah ah ba rasuwa bane, Akan lalurar da Meenal take fama dashi ne na ciwon mara"
Saida ta sauke nannauyan ajiyar zuciya saboda jin cewa ba wani mugun abun bane ya faru.
"Nasan baki manta kwanciyar da tayi a asibitin Dr Mubarak ba? "
Bai jira ta bashi amsa ba ya d'aura da cewa, "a lokacin Dr yama Malam bayani akan cewa Meenal bazata rabu da ciwon ba har sai sanda tayi aure in Allah yasa an dace zata rabu da ciwon gaba daya in ma bai wuce lokaci daya ba dai zai ragu har ta dena ciwon ma gaba daya wata rana, Wanda kuma ina da tabbacin kema kin san da hakan a matsayin ki na likitan mata sai dai nasan dalilin ki na boyewar bai wuce duba da karancin shekarunta da kuma burinta data taso dashi na zama likita kamar kiba,
Jidda kece kika d'auki cikin Meenal har zuwa haihuwarta dan haka nasan kinfi kowa sanin zafinta, amma zan miki tuni da Abu guda Malam Uba yake a wajena domin ya zarce matakin da zan kira shi da sunan wana ko in kira shi da Ya'yana, domin tun tasowa ta nike samun kulawa ta musamman a wajen shi na sani Malam ya nuna rashin amincewar shi a lokacin auren mu, wannan kuma na dauke shi a matsayin halin dan adam dan tuni na goge hakan daga cikin zuciyata abunda nike son ki gane anan shine Malam yana da iko dani balle kuma yaran dana haifa cikin su kuwa harda Meenal da kowa yasan cewa koni da nike matsayin mahaifinta banfi Malam kaunarta ba, domin a bayyane yake ta yadda ko makaho yasan Meenal takai kololuwar matsayin da Malam bai had'ata da kowa ba a wajen shi kema kuma kin sheda hakan, kamar yanda Malam ya amsa sunan uba a wajen Ameenatu tun daga haihuwarta har zuwa yanzun ki sani yanzun din ma ya kara tabbatar da matsayin shi wajen sauke hakkin dake rataye a wuyar shi matsayin uba domin ko *Malam ya fidda ma Ameenatu miji harma ansa ranar auren atakaice dai dukan su ukun zamu aurar rana daya*"
"Innalillahi wa'innah Ilaihir Raju'un"shi tayi ta mai maitawa ba adadi domin kalmar shi ta karshen daya fada shi yayi tayi mata amsa kuwwa a cikin kunnen ta,
Sosai ya kara kankameta a jikin shi dan tabbas yasan dama maganar dole zata daketa.
"Kiyi hakuri"kawai yayi ta maimaita mata, kuka sosai ta fashe mishi dashi dan gaskiya Allah ya gani bazata iya daurewa ba, dan sosai takejin wani irin kuna da bacin rai yana taso mata.
"Aure! Aure!! Aure!!! Meenal din ta ne za'ayima aure shine saboda tsabar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 92