Share this page
bazai canza komai ba" "Mommy aure fa kuma ni ai banyi kwantai ba ina da samari na da kulumm suke cewa suna sona fa! ai dan karkiyi fad'a shi yasa na hanasu zuwa gidan nan kuma kullum sai Bashar yamin magana akan ya turo a tambaya mishi na hana shi" sai kuma ta k'arama kukun nata volume tana kallon Mommy taci gaba da cewa "yanzun shike nan Mommy an rabani da Bash kenan? Yanzun shikenan nima na zama mayau dariyar da ake cewa?, Mommy Bash fa kullum yana cemin yana sona sosai duk ranar daya rasani bai san ya zaiyi rayuwa ba, gashi zakumin aure bada sanin shiba, Allah sarki Bash kila dai haukacewa zaiyi shima ya fara tsince² a bola irin na mahaukata" cike da ihu sosai ta kwara da cewa "shi kenan ni Meenal za'a sani d'aukar alhalin daba nawa Bash zai haukace idan ya rasani, shi kenan kowa zai koma yimin kallon mayaudariya" "Ke Meenal" Mommy ta kira sunan ta a tsawace, "Idan baki rabani da wad'an nan surutan iya shegen naki da basu da amfani ba sai na sab'a miki kamanni , zaki bani hankalin ki nan muyi magana na fahimtar juna ko a'ah? waima da izinin wa kike kula samarin a waje da har kike ikirarin wani can zai haukace dan ya rasaki? Fad'amin shid'in matsayin shi har yafi na mu iyayenki ne da zaki kasa bin umarnin mu dan kina gudun karya haukace? To ba hauka ba yama rataye kanshi ya mutu inya so, sakarcin banza da wofi kawai kuma wallahi ki yimin shiru da kukan nan naki kafin in tattaka ki" Jin yanda Mommy ta fututtuke take ta fad'a yasa ta yin shirun na dole dan tasan yanda ba kowa daga ita sai Mommyn a d'akin tofa yasin tana iya zagewa ta nad'a mata na jaki kafin wani yazo kwatar ta ta tabbatar taji jiki, Kasa kasa tayi da murya kafin tace "Mommy to in auren zaku min basai kuce in fito da miji ba shine kawai za'a had'ani da Ya Sufyan" Ta fad'i hakan da sheshshekar kuka tana turo baki. "Oh baki gode Allah bama ashe da kika samu Sufyan d'in su kuma kannen ki da aka had'asu da wadancan iyayen nasu kinji wacce ta kalubalanci batun auren a cikin su? Sai ke shafaffiya da mai da kike shirin nuna mana cewar bamu isa ba, Wato saboda Malam yana d'aure miki gindi Meenal shine yasa kike ganin kamar babu wanda ya isa dake koh Meenal? To ki sani mune iyayen ki dan haka aure kuma kamar an d'aura nagode Allah ma daya sa shine mijin kin kuma san ba wasa yakeyi daku ba, dan haka kije kiyi mishi shirme ya banka miki kashin bala'i wallahi kin kuma san kina da kishiya dan haka gara ki kama kanki tun wuri" Shigowar Aunty Hassana d'akin ne yasanya Mommy Hauwa yin shiru daga karshe ma ta fice a d'akin. Tasowa tayi ta rungume Aunty Hassana kukan ta yana dawowa,dan sosai abun ke k'ara tukota a kirji "Mommy kinji wai auren dole zasu min kuma ni ina da wanda yake sona, kuma ko jiya sai da ya rokeni yana son ya turo iyayen shi na hana shi shine kawai yau za'ace aurena za'a d'aura da wani bayan shi kuma na riga na gayyace shi, dan Allah Mommy mai zan fad'a mishi yanzun ya yarda cewar ba yaudarar shi nayi ba? Bash yana sona Ban san wani hali zai shiga ba kinga fa koda na tashi d'azun tarin miss call din shi na samu a wayata, ni wallahi ban san ya zanyi ba" Haka Aunty Hassana ta zaunar da Meenal tana ta bata baki daga karshe kuma ta amshi Number Bash din a wajen Meenal d'in akan cewar ita da kanta zata kira shi yazo su iyayen ta su fad'a mishi abunda yake faruwa dan yasan cewa ita d'in bata da laifi kuma bata yaudare shiba. *Bari mubar amaryar Sarki haka mu lek'a halin da uwar gida sarautar mata Teemah take ciki* Tun bayan barin Sarki Lagos take ta faman fad'i tashi na ganin yanda zata bullowa al'amarin domin dai wannan yak'in nata ne dan haka bazata sanya kowa a ciki ba dan kamar yanda ta k'udiri aniyar babu wanda zai san da batun auren cikin kawayen ta, tofa hakan take so ya kasance sai dai kuma tasan hakan bazai samu ba dole sai tayi kamar tanayi, ta dai tattaro bala'in gabas da yamma kudu da arewa wanda take da tabbacin kamar yanda bokayen ta suka tabbatar mata da cewar auren bamai dorewa bane tofa hakan ne zata kasance domin dai basu tab'ayi mata alkawari suka sab'a ba, taso a daukar mata mataki mafi tsauri akan yarinyar data yarda zata aurar mata miji sai dai hakan ta bai cimma ruwa ba domin dai an fad'a mata komai zatayi bazata samu sa'a akan yarinyar ba, sannan shima Sarki barin gefenta da yayi hakan ya jawo nakasu sosai akan abubuwan dake jikin shi ga kuma alamu sun nuna cewar akwai wanda yake b'ata musu aiki dan haka suka had'a mata abubuwan da zatayi mishi amfani dashi in ta isa gareshi wanda dole itace zatayi su da kanta, sannan kuma sun kara da jan kunnen ta akan cewar koda wasa in taje karta yarda tayi wani abun da zai iya kawo wani sab'ani tsakanin ta da Sarki dan hakan na iya b'ata musu aiki. To dai ta shirya tsaf akan da zarar biki ya rage kwana biyu zata musu dirar mikiya, hakan ne kuma ya faru dan ko shi Sarki bata fad'a mishi cewar ta taso ba har sai sanda ta iso kaduna sannan ta kira shi cewar gata fa a kaduna amma inta huta ko zuwa yamma ne zata wuto Zaria, ko kusa ko alama tsayin kwanakin nan bata tab'a nuna mishi cewar ta san abunda ke faruwa na batun auren da yake shirin yiba, Shi kuma harga Allah abubuwa ne suka sha mishi kai da kuma cewar da tayi zata zo yasa ya yanke hukuncin in ta iso sai suyi ga da ga. Yaji wani iri sosai bayan ya gama amsa kiran nata ta yanda har yakejin cewa bai kyauta mata ba, gashi yanzun ta baro aikin ta da duk abubuwan dake gaban ta masu mahimmanci a wajen ta tazo dan ta duba jikin mahaifiyar shi amma su kullum yan uwan shi bak'inta kawai suke gani komai tayi bata burgesu, yana dai Addu'ar Allah yasa ya shawo kanta cikin sauk'i domin dai yasan ba'a kyauta mata ba. Shi yanzun babban damuwar shima inda zai sauke ta dan yasan bata son sauka a gidan su gidan shi kuma daya gina domin ta gashi yanzun wata harta maye gurbin ta ga kuma yanda sukayi da Hajiyar can dake amsa sunan kakar yarinyar, dan haka yana ga hotel kawai zai sauke ta yasan itama zata fi son hakan tunda bata iya sakewa a cikin yan uwan shi. ****** Duk yanda Aunty Hassana taso Meenal ta fito daga d'akin nan ta koma wajen su Raheenat k'i tayi, a cewar ta tunda kowa baya son ta babu inda zata taka k'afarta domin dai harta kayan data sanya d'azun tub'e su tayi sannan ta koma toilet ta sake sabon wanka duk ta wanke kwalliyar da tayi a d'azun ta dawo kan gadon taci gaba da kwanciya daga ita sai wata tsohuwar doguwar riga kamar wata mai jinya. A haka su Moon suka shigo suka sameta, "Kunga ku kwashi sheggun kafafuwan ku d'aya bayan d'aya ku ficemin a d'akin nan dan banga uwar da kukazo yimin ba jajayen munafukai kawai, badai har daku za'a had'a kai aci amana taba, kuje ku da Allah alhakina kuma yana kanku, dan haka sai ku koma gefe ku zuba ruwa a kasa kusha, ace wai duk yanda na d'auke ku ku rasa abunda zaku sakamin dashi sai wannan, daku fa muka dunga gantalin rabon ankon biki da raba cingum, ina ta yawo a gari ina fad'in k'anne na zasuyi aure kullum jimami nike saboda nasan yanda auren nan yazo ma yaran nan, ashe basu bane abun tausayi nid'in dai da nike tausar su nike basu baki akan suyi biyayya nice abar tausayin da aka tsaida ranar aurena ba tareda sani naba, ashe su gata aka musu tunda koba komai an sanar musu sannan aka had'asu da mazajen nasu da suke ta rawar jiki a kansu nifa? A rasa da wanda za'a had'ani aure sai Sarki ko waccen su mazajen su sunzo sun gana dasu amma ni har yanzun da ya rage awanni kad'an in tabbata a matsayin matar aure bamuyi ido biyu da mijin ba, kenan dai shima dole aka mishi badan yana soba tunda ko nema na ya kasayi, Ku kuma wallahi duk nasan matsayin dazan ajiye ko waccen ku munafukai kawai kuma insha Allah dukan ku kuma auren dolen za'a muku kuji inda dad'i" Allah sarki Meenal wallahi basu ba hatta ni kaina na tausaya mata, Amma kuma ya bawa ya iya? Kaddara fa ba'a iya guje mata sai hakuri, Masu karatu ina mai k'ara baku hak'uri nasan bakwa son auren, kuyi hakuri please 🙏. Karasawa inda take sukayi ko waccen su jikin ta a sanyaye Meelat da Maryam kan kasa rike kukan su sukayi wanda kukan nasu shi ya kara tada kukun Meenal din sai gashi duk sun taru suna kukan babu mai ba wani hakuri, Kiyi hakuri Meenal to mema zamuce miki bayan mai afkuwa ya riga ya afku, mun san ko mun fad'a miki hankalin ki kawai zaki tada wanda hakan bashi zaisa a fasa auren ba, sannan kuma an gargad'e mu da karmu fad'a miki dan Allah kiyi hakuri muma munajin babu dad'i kamar yanda kikeji" "Karya ne baku san ya nikeji ba, tunda baku za'a dauka akai gidan mijiba, koba komai har yanzun a gaban iyayen ku kuke kuma a gaban su zakuci gaba da zama har zuwa sanda lokacin naku auren zai zo, na tabbata kuma su bazasu rufe muku komai ba hasalima sai wanda kuka fidda cewa kuna so zasu baku ku aura, Nifa? Ku kirgamin a wanni nawa suka ragemin inyi a cikin gidan nan domin dai nasan ko suma nike ana shafamin ruwa tofa babu mai bari in k'ara kwana a cikin gidan nan domin yanzun kaf gidan babu mai kaunata babu wanda ya damu da damuwa ta, Tun safe nike d'akin nan amma kamar wata agola a wajen rabon gado haka na kasance babu wanda ya shigo ya dubani ko a wayata babu wanda ya kirani hatta Malam da kullum nake ganin yafi kowa sona yau bai tuna da wani hali nike cikiba, shin kun ma san da kiran wa na fara cin karo a wayata bayan na tashi daga dogon baccin dana tabbatar bana lafiya bane? " Bata sarara domin jin amsar suba ta d'aura da cewa, " Bashar ya kirani sau adadin da bazan iya tunawa ba tsoro nike shin ko har maganar yaje kunnen shine? Fisabilillahi wani amsa zan bashi da wani kalami zanyi amfani wajen fad'a mishi cewar komai daya faru bani da masaniya ta yanda zai yarda dani?" Kuka ta fashe dashi sosai su kuma suna ci gaba da bata hakuri. Duk halin da Meenal ta tsinci kanta a ciki hakan bai hana jama'ar gidan cigaba da gudanar da harkokin su cikin farin ciki ba, hasalima duk wanda ya tambayi ina take cewa akeyi bata gidan. *An daura aure lafiya* aure kuma ya dauru😟 masu fatan alkhairi sunyi akasin hakan kuma dai sun barma zuciyoyin su, Tunda Magrib ya gabato Mommy Hauwa da kanta ta shigo d'akin ta tasa Meenal a gaba har zuwa ban d'aki tayi sabon wanka bayan sun fito kuma tayi tsaye a kanta har sai da ta shirya sannan ta fice daga d'akin ita ko Meenal har zuwa wannan lokacin babu abunda takeyi sai aikin kuka idanuwan ta ko kallo guda zaka musu kaji baka sha'awar k'ara kallon su, Daga ita har kawayen ta dukan su babu mai walwala bikin aure da akeyi cikin nishad'i to nata dai komawa yayi kamar wani bikin mutuwa, barin ma da yamman nan da taga ana ta kara haramar mik'a su Raheenat d'akunan su dan ita Raheenat Kaduna za'a kaita dan haka da wuri suka wuce da ita ko sallama Malam bai bari tayi da Meenal ba, ita ko Sa'adatu da yike cikin garin Zaria ne anan cikin GRA yasa sai gab Magrib d'in suka wuce ya rage saura Meenal kad'ai da za'a mik'a gidan Malam Ladan dake makotaka da gidan Malam d'in kafin a wuce da ita d'akin ta, kasan cewar ita kusa ne hakan yasa sauran jama'ar sukayi ma sauran amaren rakiya, anayin sallar ishsha'i babu jimawa itama Billyn ya Sa'eed aka kawo ta a kuma lokacin ne Malam ya bada izinin a fito da Meenal din itama a mik'ata nata d'akin amma kafin a fita da ita sai da aka sadata da falon malam inda iyayen ta suke suka k'ara yin mata nasiha da kuma ban hakuri, Amma Mommy Hauwa kam b'oye kanta tayi itama tana nata kukan dan bata da k'arfin zuciyar da zatayi sallama da Meenal d'in tadai riga tayi mata nasiha a matsayin ta na uwa dan haka sai dai ta bita da addu'a kuma. Meenal tasha kuka, kukan nata koh ba karamin tab'a jama'ar gidan yayi ba sai dai ya zasuyi tunda dai ai dama ko ba dade koba jima ita ya mace dole aure za'a mata ta tafi nata gidan, Malam ko bai iya cewa komai ba illah hakuri daya ringa bata da kuma sa albarkha har aka fita da ita daga gidan a cikin motar dasu Kwaro suka kawo duk da kasancewar tsakanin gidan Malam da gidan su Sarki babu wani tazara amma haka suka laya manya manyan motocin su kamar wasu masu shirin barin gari sojojin nan duk sun sako kakin su na aiki dan su tabbatar ma da jama'a cewar bikin fa nasu ne, Tarba ta girma da arziki suka samu a wajen Uwar gida da nata ahalin wanda anan din ma dai nasiha suka yima Ameenatun da alkhawarin zasu riketa amana domin ko babu aure ita d'in dolen suce, daga nan kuma ka sada Amaryar Sarki da gidan auren ta. To a can din ma dai komai da zasu bukata na daga abinci da ruwan sha da sauran su duk an tanadar musu, tunda ake bikin aure a gidan Malam ba'a tab'a kai amarya yan kaita su kwana a gidan ba sai akan Meenal domin da ankai ta ake juyawa amma sai ga shi ita uwar Malam tsabar gata duk da kasancewar ta cikin unguwa Malam bai hana kowa kwana ba saima umarni daya bayar akan a samu wadanda zasu zauna tare da ita su d'ebe mata kewa kar tunani ya mata yawa, a gidajen amare da yawa in kawaye sun kwana zaka samu cewa sun raya daren ne cike da farin ciki dan wasu ma kusan kwanar zaune sukeyi suna hira, sab'anin gidan Meenal daya kasance shiru babu wani kara kaina dan ita dama ganin kukanta yayi yawa yasa tun kafin su fito da Aunty Hassana ta tsareta taci abinci ta hada mata da maganin bacci dan haka koda suka iso gidan da aka mik'ata d'akin ta umarni Aunty Hassana ta bayar akan su koma falo domin zuwa lokacin bacci ya fara cin karfin Meenal din, Su kuma kawayen waje can suka koma wajen abokanan ango suna daddalewa domin dai tunda aka fara hidimar bikin babu wanda ya nemi wani a cikin su gashi har amarya ta tare a d'akin ta koda suka nemi ganin ango uzuri abokan suka basu akan cewa shima bayajin dad'i shi yasa bai zo tare dasu ba, sai dai abokan sunyi musu sallama ta girma a matsayin su na kawayen amarya kafin suka juya suka koma masaukin su bayan kawayen sun tabbatar musu da cewa basa bukatar komai aka bar wasu daga cikin yaran Sarkin domin su kula da gidan. *Jama'a wai ina Angon ya shige ne?* Kwaro Sarki yaba mota ya je ya d'auko Teemah a Kaduna a wannan ranar basu shigo Zaria ba sai gabanin Magriba, kai tsaye kuma Hotel din daya kama domin ta yayi ma Kwaro umarnin wucewa da ita domin yafi son ya fara ganawa da ita kafin ta isa gidan su, Dan haka koda Kwaro ya kaita d'akin da Sarki ya kama ya rakata da akwatin ta, bai kuma tsaya ba yayi sallama da Sarki ya koma domin shi ke kula da bak'in su dake zuwa dama duk wani zirga² na bikin. Kasan cewar bata da wani gajiya a tareda ita hakan yasa Sarki ya fara gabatar mata da abinci, sai da taci tayi nak sannan ta fara tambayan shi "ya mai jikin ta k'araji suna gida ne ko asibitin? " "Jiki da sauki tana gida domin a gida likitan ke zuwa yana dubata" "Allah ya k'ara lafiya sai mu tafi yanzun ai ko inje in duba jikin nata dan shine mak'asudin zuwa na garin!" "Yaran kifa? Bakya d'aukin son zuwa kigan su? Kin san dai sunyi kewar ki suma!" "Hhhh ko sunyi kewata ya zasuyi tunda haka uban su ya zab'ar musu, an nuna min kaka tafi uwa mahimmanci na gode Allah dabai yoni a matsayin juyaba tunda gashi harna haifo wani d'an, kasan ko ai dama koba komai shi d'a namiji kason mata biyu yake ci dan haka ban yi fad'uwar bak'ar tasa ba" Shareta yayi jin tana son tsokalo wani maganar daban kuma. "Zamu tafi can d'in amma dai kafin nan ina bukatar matata, koba komai ai an san nayi kewa" ya k'arasa fad'a yana d'age mata giraren shi, Ji tayi kamar ta waftoshi ta kikkifa mishi mari, wato ga dokin shi ta iso saura sukuwa koh? Shida ake batun aura mishi sabuwar budurwa ne dan bashi da kunya zai wani ce yayi kewarta bayan abunda yake shirin aikata mata? Wallahi da badan akwai aikin da aka bata wanda sharad'in shi shine dole sai yayi amfani da ita da abun a jikin taba da bazata bari ya kusanci jikin ta a yanzun ba da saita hora shi har ya koma yana rokon ta allah annabi tukun na dan ta nuna mishi cewa ita ba Teemar banza da hofi bane, amma ba komai a jure zuwa rafi koba komai ai durkusa ma wada ba gajiyawa bane, hakan nema yasa ta murmusa cike da kissa ita ma tace, "Nima nayi kewar kakkarfan jarumi kuma Sarki a fadar zuciyata, amma kafin a shiga filin wasa a dan barni in d'an gyagygyara domin bawa wasan damar samun armashi, Shi kuma sokon gado ya koma a dole yana jiran ta shiryo a shiga filin wasa aci gaba da fafatawa, Sai da ta d'auki kayan aikin da take bukata ta shige cikin makewayi tayi amfani dana matsawa daga gogawa harma dana feffesawa sannan ta fito, Allah da ikon sa yau dai sab'anin sauran kwanakin da take jan ra'ayin shi harma ta mantar dashi Addu'ar da aka koyar damu na ma'aurata yayin saduwa da iyali yau dai Allah ya bashi ikon karantowa kafin su fara fafatawa. Sunfa dambatu iya dambatuwa domin dai dama dukan su jarumai ne a wannan fagen, Bayan komai ya kammala kamar wani soko haka Sarki ya saki baki ya dunga ratata ma Teemah zancen abun dake faruwa na batun auren da uwar shi ta bashi umarni akan dole, ya kumayi mata alkawarin Karin auren shi bazai taba sawa ya canza mata ba domin dai shi din nata ne har gaban abada, ya daiyi b'ab'atun shi duk a son shi na fahimtar da ita cewar babu laifin shi kuma bama son yarinyar yake ba, ita kuma gudun karya yi tunanin wani abun daban hakan yasa tadan nuna bacin ranta akan yanda kai tsaye zaiyi mata kishiya ba tareda sanarwa ba. Kai jama'a yasin na gaji😰😰 Mu had'e gobe idan Allah ya kaimu da rayuwa, Ummiee Zaria ce✍🏼 💗💗💗 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!* 👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 *Free Book ga masu buk'ata daga farko zasu iya tuntub'ana kai tsaye 08061358462* """"Page 33 *Masoya masu juriyar bibiyar labarina Ina mai baku hakurin rashin ganin posting kullum,I am very sorry for that abubuwan ne da yawa,masu kira da masu ajiyemin sak'o na fatan alkhairi Ina godiya matuk'a da kaunar ku a gareni,domin ku ke k'aramin kwarin gwuiwa nagode kwarai* *AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _infection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_ _Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ *08089965176* *07084653262* ****** Sosai ya zauna yayi ta aikin lallashin ta kafin ma ta nuna ta sauko daga fushinta, ta kuma nuna mishi cewar komai ya wuce koba komai ai tunda umarnin uwar shine ita ma zata tayashi ganin yayi ma uwar na shi biyayya, hakan da tayi ba kad'an ba ya k'ara kankaro mata mutunci a idanun shi. Shi yayi mata jagora har zuwa gidan su domin dai tace bata kwana sai taje ta duba yanda mai jiki ta k'araji, Hak'ik'a ta shayar da mutanen gidan matuk'ar mamakin ganin ta a wannan daren, domin dai koda wasa babu wanda yayi tsammanin zuwan nata a wannan lokacin duba da dad'ewar da tayi bata zo d'in ba , ga kuma wani sabon salon sauyi da suka gani k'arara a wajen ta domin dai tunda ta iso ta aro wata sabuwar d'abi'a na ladabi ga kula nan² da takeyi akan uwar gida dama sauran jama'ar gidan abinda ya zame ma yan gidan bak'o dan ba halin ta bane damin sun sani cewar sau tari intaga dama ko zuwan tayi har tayi zaman ta ta koma ba lallai wani ya ganta ba amma yau duka sassan gidan saida ta shiga ta gaishe su har da tsaraba abunda bata tab'ayiba tsayin shekarun aurenta da Sarki kuwa! , Sai dai kuma duk wannan rawar jikin nata ko kusa ko alama y'a ranta dake gidan kaf d'insu babu wacce ta kusanci inda uwar tasu take, domin dai ko d'aukin da yaro kan nuna na ganin uwar daya dad'e bai ganta ba kwata² yaran nan basu nuna hakan ba domin koda uwar gida tace suje su gaida maman su daga bakin kofa sukayi tsaye babu

Chapter 29 of 92