Share this page
kaf abubuwan ta na amfani motar da Sarki ya bata wacce take amfani da ita in tazo garin da ita tayi amfani tabar garin sai da ta tsaya a kaduna nan ma ta kwashe komai nata tsaf sannan ta nufi Lagos garage ta nemi driver din dazai tuk'ata suka tsadance yaja ta tun daga kaduna zuwa Lagos a mota abinda bata taba kwatan tawa ba, tsayin rayuwar ta amma tashin hankalin da take ciki yasa gaba d'aya bata iya tunawa da batun hawa jirgi ba, teemah bata tab'a tabbar da zancen yan magana dake cewa tafiya yankin azaba ce ba har sai a wannan ranar domin dai tayi wuji wuji ta kuma galabaita sosai haka ta dunga kwarara amai kafin su isa duk ta gama firgicewa, address din gidan Brigadier general taba driver din motan dan haka can suka nufa, Shidai driver dama Allah Allah yake yaga sun isa lafiya batareda ta mace mishi a cikin mota ba dan haka suna isa bayan ya tabbatar gidan su ya kaita shima ya kama gaban shi domin dama ta riga ta tura mishi kud'in shi a cikin account tun ma kafin su taso, Ganin halin da take ciki na ciwo yasa babu b'ata lokaci Aunty da autan su suka kwashe ta sai asibiti dan kamar jira jikin nata yake su isa gida jini ya tsinke mata, To ta dai sha dakyar kafin likitoci su gano cewar cikin dake jikinta ne ke neman hanyar fita wanda ko ita uwar cikin bata san da zaman shiba, dan ita bayan data dawo hayyacin ta Aunty ke mata batun cikin ma musawa tayi da cewa al'ada takeyi har sai da likitan ya zauna ya mata bayanin cewa ba al'adah bane cikin ne dai dama tun farko bai zauna a cikin mahaifan taba amma dai yanzun sunyi kokari sun mai dashi dan haka zasuci gaba da rikon ta a asibitin har zuwa lokacin da cikin zaiyi kwari sosai domin basa bukatar tayi ko wani aiki hutu kawai take buk'ata kuma hakan bazai samu ba sai tana cikin asibitin, Badan taso ba haka nan dai a babu yanda zatayi ta amince da zaman asibitin saboda soyayyar ta nason haihuwar d'a namiji, duk da babban kudurin ta na dawowan shine zuwa takaima OBA ziyara dan ya D'aukar mata matakin gaggawa akan Sarki da Meenal, Tunawa da batun Sarki da Aminatu cewa suna can fa suna cin amarcin su da tsinke a yayin da ita kuma ta kasance kwance a gadon asibiti har tana shirin rasa cikin da take fatan ya zame mata sanyin idaniya inya kasance d'a namiji, wannan tunani da damuwar data d'aurawa kanta shiya k'ara sawa jikin nata ya rikice. *Ummiee Zaria*โœ๐Ÿผ [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA!*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆโšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ ~{{MY FAMILY}}~ *RUBUTAWA* *UMMIEE ZARIA*โœ๐Ÿผ ```` *Page 47* A yawancin lokata da dama mukan tsinci kan mu da son ganin mun nesanta zukatan mu akan yawan tunanin wasu tunanun nukan da dama wadanda muke ganin sun addabe zuciyar mu, Sai dai kuma sau tari duk yanda zamuyi kokari wajen nuna juriyar mu dan ganin mun danne tunanin ko muyi kokarin gogeshi dan kar ya zamana abinda zamu ringa tunawa akoda yaushe hakan sai ya faskara a garemu, domin kuwa wani yankin tunanin yakan zama dauwa mam mene tun daga cikin kwalwa harma a cikin zuciyar mu, Hakan ne kuma ya faru da AK a kokarin shi na son ganin ya ture duk wani tunanin Meenal bayan komawar shi Kaduna kan har kokin shi, sai dai ina abun fa sam ya gagara, domin sau tari yakan so ya maida kanshi irin so busy d'in da bazai iya tunanin komai ba sai abinda yakeyin amma sai kaga tun kafin aje da nisa ya gaza tab'uka komai, tun yana iya kokarin shi wajen ganin ya boye komai a cikin zuciyar shi kamar yanda ya saba sai gashi kafin ya ankara hakan ya tab'a tunani dama kuzarin shi, Sadeeq, Musty, Yusuf sun sha zaunar dashi dan son suji takai maiman abinda ke damun shi amma sam ya kasa fad'a musu, kullum in sun matsa mishi da tambaya sai dai yace musu gajiyar aiki ne kawai, gashi kuma sunyi sunyi dashi akan ya koma gida ya huta su zasu ci gaba da kula da komai yak'i, To kwana biyun nan dai haka nan yake jin jikin shi kamar wanda ciwo keson kamawa dan haka yau ya yanke hukuncin zama a gida ya huta, Sai dai koda ya kwanta da sunan hutun zuciya da kwalwa basu bashi had'in kai ba domin ko tsaf ya nemi bacci daga cikin idanun shi ya rasa, haka nan yake jin zuciyar shi sam babu dad'i duniyar gaba d'aya ta mishi k'unci, inda wani zai tambaye shi mai yake da bukata a yanzun? Shi kanshi yasan bashi da wannan amsar sai dai kuma acan k'asar zuciyar shi yake jin sautin sunan Yarinyar nan na mishi amsa kuwa, sosai kunnuwan shi suke buk'ace da son jin muryar ta, muryar da aduk sanda ta shiga kunnen shi sai tsigogin jikin shi sun mik'e, haka ma sosai idanuwan shi ke cike da maraicin son ganin kyakyawan fuskarta, fuskar da komai kuncin da yake ciki idan ya kalleta sai yaji ya samu sassauci, Ga dai number din wayarta daya lalubo a cikin group dinsu na *Dangi* da suka bud'e domin tattaunawa wanda shima yana ciki, Sai dai kuma gaba d'aya ya rasa kuzari da gwarin gwuiwar kiranta kai tsaye domin hakan bai tab'a faruwa ba a tsakanin su, kamar yanda bata tab'a kiran shiba haka shima bai tab'a kiranta ba koda wasa, Sai dai lokaci lokaci yakan zauna ya bud'o hoton ta data d'aura a dp dinta na WhatsApp da takan canza lokaci lokaci yayi ta kallo har sai yaji ya gamsu sai ya rufe wayar, to yanzun kam an kai matakin da ba hoton yake buk'atar cigaba da kallo ba ah ah ita d'in dai kaco kam yake son gani koda koh ace bazasuyi ma juna magana ba, sai dai kuma a yanzun sosai yake tsoron abinda kusancin nasu zai iya haifar mashi, Ganin cewa bashi da wata mafita hakan yasa shi yanke hukuncin d'aukar wayar shi dan ya kira Hajiya, ya tabbatar da cewa indai yarinyar nan tana gida tofa babu shakka za'a sameta ne tare da Hajiyar a yanzun dan kwana biyun nan ya gane cewa sam hajiya tabar yayin kowa sai Yarinyar, Kira ya danna ma number din Hajiya, kiran farko haka wayar taci gaba da ringing had'e da bugawar zuciyar shi, amma abun haushi har wayar ta gama k'ara ba'a d'aga kiran ba, K'ara maida wani kiran yayi shima d'in dai ba'a d'auka ba, kamar dai ya hak'ura sai kuma ya kasa, dan haka sai ma ya k'ara kiran wayar a karo na uku, kiran na gab da yankewa aka d'aga daga can gefen, "Assalamu Alaikum Hajiya bata kusa inta dawo za'a fad'a mata an kira!" Tana gama fad'in hakan k'it ta yanke kiran ba tareda ta saurari abinda wanda ya kira d'in zai ceba, "Hummm " yaja wata irin dogowar ajiyar zuciya mai cike da tarin sinadaran dake ba mutum nutsuwar daya rasa tsayin lokaci, Murmushi mai kama da dariya yayi kafin ya furta a bayyane cewa, "Marajin magana, wato tunda ta isar da sak'on shi kenan sai kawai ta wani yanke wayar ta, to dama wa yace mata muryar Hajiya nike son jine?" Kara kiran wayar yayi a karo na hud'u, kuma wannan karon ma bata d'auka ba sai da wayar take gab da katsewar, "Ke yarinya waye yace miki ki yanke min waya tun banyi magana bane? in Hajiya bata nan ke bazaki iya amsar sakon ba, kawai kin d'auki waya ko gaisuwa ma babu kuma kika yanke min waya hala baki iya karatu bane da baki karanta sunan wanda ya kira wayar ba?" "Wake magana?" Ta tambaya kai tsaye babu ko d'ar a cikin muryar ta, "Kaiii" ya fad'a yana zaro idon shi waje dan baiyi tsammanin amsar da zata bashi ba kenan, kai yarinyar nan wai mai take nema dashi ne? Har shine ma wai zatace ma wake magana, "Wanene ke magana nace?" Ta kara tambaya, "Baki iya karatu bane?ko kuma muryar tawa ce ta zamar miki bak'uwa ayau" Ya maida mata da amsa, "Baka amsa min tambayar da nayi ba, kaga malam in bazaka fad'amin ko waye ba zan yanke kiran ne aina fad'a maka cewar Hajiya bata nan, kuma nufin ka dan naga suna shi kenan bazan tambayi ko waye ba!" Ta fad'a cikin kunkunin data saba, "Ni kuma na rantse miki da Allah in kika yanke min waya sai nazo har inda kike na zane ki, inga k'aryar rashin kunya" "Eh ai dama kai kullum maganar ka kenan zaka zane mutum, in karfin gaske kake tak'ama dashi ka kama hanya zuwa sabon gari mana aiga gidan yan danbe can sai kaje ka dambace son ranka, badai dan kaji Hajiya nace maka d'an mai karfi shi yasa kake k'ara bubud'ewa kana ma mutane barazana ba, ni kuma insha Allah duk sanda ka tab'ani yayan mage zan hayo su taremin kai a hanya su min maganin ka" Lallai ma yarinyar nan wato kenan dai tsabar neman magana ne yasa take tambayan shi cewa wake magana tsaf ta gane shi ashe, a bayyane ko amsa ya bata da cewa.. "Oh ashe ke d'in yar sara suka ce bani da labari?" "Ban fara ba amma a kanka zan gwada" "Ai ban san yar ta'addace ke zaune tareda Hajiya ta ba da tuni na miki cinne, amma yanzun tunda kin tona kanki to tun wuri ki tattara naki ya naki kodai ki koma gidan ku ko kuma daga nan ki wuce d'akin mijin ki da kika gudo kai tsaye," "Haba taubashin tuzuru ai sai ka fito kawai kanka tsaye kace bak'in ciki kakeji saboda na dawo gidan Hajiya zan hanaka rawan gaban Hantsi kaida ala koron yan matan ka, ba shakka Ashe shi yasa ka tattara ka fece ko sallama babu tun ranar da mukayi ido biyu da kai, to bari in baka albishir, nan dai gidan da kaima kake tak'ama dashi ka sani cewa irin wannan tak'amar naka nikeji akan shi, dan haka yanzun da nike cikin shi kai kuma kakajin haushi koh? to sai ka share waje kayi zaman ka acan inda kake dan gidan nan zama na a cikin babu fashi," "Ke wai nine dai kike cema tuzuru koh?" ya tambaya "To naga dai ai ba karya nayi ba, koba tuzurun bane? " "To tuzuruwa nasan naki tuzurancin nema yasa har kike jin haushi na, dan haka kema ga gidan nan ki share domin zaman zawarci!" Ya karasa fad'a da dariya a muryar shi, Kuka ta fashe mishi dashi sosai ta wayar. "Ni wallahi ba bazawara bace allah ya kiyaye min in zama bazawara," take fad'a da muryar kuka, "Oh inba zawara ba me cece? fad'amin yarinya ce ke ko budurwa ko kuma matar aure?" "Ni ka kyaleni ina ma ruwan ka dani inma mecece aini ya shafa," "Ah ah wallah nima ya shafeni, bakiga shi yasa na kasa sukuni ba........" Shiru yayi yana rufe bakin shi da hannun shi jin yana shirin yin katob'ara, "Miye ya shafeka?" "Ke kin isheni da surutu idan Hajiya ta shigo ki fad'a mata na kira, ko kuma kima barshi kawai zan kirata anjima" Kit ya tsinke kiran bai k'ara sauraren jin ta bakin taba, mirginawa yayi sannan ya janyo filo ya rungume a k'irjin shi tsam tsam, cike da shaukin soyayyar daya dade baiji shi a tare dashi ba, A wannan lokacin ita kuma haka taci gaba da danna mishi kira da number din Hajiya babu k'akk'autawa amma harta k'ari kiran ta gama bai d'auki wayar ba, dan yasan koya d'auka fadar dai zasuci gaba dayi, shi kuma yanzun nutsuwa yake buk'atar samar ma zuciyar shi ba hargitsi ba, Yana a cikin wannan yanayin har Yusuf daya shigo gidan ya iso har cikin d'akin bai sani ba, Shima Yusuf din ganin halin da AK din yake ciki hakan yasa kawai sai ya nemi kujera ya zauna yaci gaba da kallon shi yana kuma nazartar shi, dan shi tuni ya fara harbo jirgin abokin nashi duk da kuwa yanda yake b'oye musu hakan bai hanashi gano cewar ya fad'a soyayya ba, Cigaba da mulmule mulmule AK yayi akan gadon domin Shifa tuni ya fita daga cikin duniyar mutane ya haura can sama kololuwa cikin furannin soyayya, Shiko wase yana dai zaune yana ci gaba da kallon ikon Allah dan dama tunda ya shigo ya kunna record a wayar shi ya ajiye saboda maganin musu, Juyowar da AK yayi ne idon shi ya sauka akan Yusuf din dake zaune akan kujera abunshi ya zuba mishi, ido, "Mtws" yaja tsaki a bayyane, kafin yace "Wase wani kalar iskancine wannan zaka fad'omin cikin d'aki babu notice? Kasan dai hakan haramun ne ko a musulunce ko?" "Eh ai dan uban mutum tunda nasan ba mata gareka ba me zai hana ni shigowa kuwa bayan nayi sallama baka amsa ba? Ko ka fara danne yan mata ne a cikin gidan bani da labari? Aikin banza ka wani kama pillow ka kankame a kirji kamar ka samu mace, mtsw" Ya karashe fada da jan tsaki, "Kai banza ne wallahi kawai ina cikin yanayi mai dad'i kazo ka katse min, mema ya kawo ka gidan nan? Ai nace muku yau hutawa zanyi babu inda zanje" "Wannan kuma kai ka jiyo amma kam tunda har na iya baro nawa iyalin na taho kasan dolen ka fita wallahi, dan kira nasamu daga wajen mutanen can na Barnawa," "Oh my God to shine bazakuje kuji dasu ba dole ne sai kun takura min," "Hakuri zakayi ka shirya muje inka dawo sai ka huta dan na musu alkawarin cewar zamu zo" Badan yaso ba haka dai ya shirya din suka tafi, ba su suka dawo gidan ba sai yamma liss, koda suka shigo abincin da suka siyo a hanya suka bud'e, Hankalin Yusuf kacokam ya mai da kan AK dake cin abincin shi hankali kwance, "Wai kasan me yasa some time bana son zuwa garin nan?" ya tambayi AK "Ina ko zan sani tunda ba tsibbu na fara ba," Shima ya bashi amsa. "Ai kai banza ne wallahi dan Allah dan annabi ka taimakeni ko dan ni kayi aure, wallahi ka sani Allah ne shaida na cewa da ciwon yunwa nike komawa gida duk sanda nazo garin nan, saboda bana samun cin abunci da kyau, haba dan Allah ina ma amfani k'aton namiji kullum sai yaje siyan abinci, amma fisabilillahi in kana da mata ni har zanji wani d'ar nema tunda koba komai nasan zanci mai d'adi koda bai kai na matana ba, ni wallahi ina mamakin inda ka kai kyankyamin ka bayan nasan ba a ko ina kake iyacin abinci ba ada amma yanzun a garin nan da alama kaf gidan abincin su ka sanshi," Ajiye cokalin shi yayi yana bin Yusuf da kallo, "Kai amma wallahi Wase kama raina min wayau, banyi aure dan buk'atar kaina ba sai dan saboda in kazo gidan nan kaci abinci zanyi? To kenan kuku zan auro a matsayin matana in ajiye maka ko ya kake so inyi ne iyeh Abba Ahmadu?" "Ai kai kaji tsiyar ka, sam ba zaka tsaya ayi maganar arziki da kai ba" "Eh na tsiya na iya can nafi kwarewa, aure kuma layine idan nima yazo kaina zanyi shine koda kuwa ban shirya ba, ba kuma wani ne ke cidani ba balle yace ya gaji" "Ai kai a duniya indai musu ne babu wanda ya kaika, ga bak'ar zurfin cikin da in bakayi wasa ba sai ya zama ajalin ka, badai ka iya tara damuwa a cikin kirjin kaba ka zauna a wajen harka rasa abinda zuciyar naka ke muradi kaga ka huta ai" "Ohhh ashe ka fara maita ban sani ba tunda har ka iya gane cewa ina da wata damuwa, to malamin duba fad'amin ya gobe na zata kasance?" Wayar da yayi record din d'azun ya d'auko kunno record din yayi ya ajiye a gaban Ak "Can you explain this to me?" Hannu ya mik'a ya d'auko wayar yana kallo, "Miye wannan d'in?" Ak ya tambaya. "Kai dai zaka bani amsar akan abinda ya jefa ka cikin shauk'i haka da har na shigo cikin d'akin tsayin lokaci baka sani ba!" Hummmm" ya sauke doguwar ajiyar zuciya kafin ya d'aura da cewa, "Wase yaushe ka koma dan sa ido ne bani da labari, ko kuma dai ka fara aikin binciken sirri akaina ne?" Serious sosai Yusuf yaci kafin ya kira sunan Ak "Abdul Khareem Ahmad, yaushe muka fara b'oye ma juna damuwar mu?, bani kad'ai ba dukan mu munsan kana da damuwa duk da kana ta kokarin boye mana, wanda kuma hakan ba sabon mu bane boye damuwar juna, a ganin ka mu bazamu iya tallafa maka bane idan har ka shaida mana halin da kake ciki? Su sauran sun sa maka idone dan suga iya gudun ruwan ka amma ni yau na gaza bazan iya barin garin nan ba har sai nasan abinda yake damun ka, in kuma ban kai matsayin da zan sani ba to, duk da jikina yana bani cewa damuwar naka tana da alak'a da mace, na kuma k'ara samun tabbacin hakan ne saboda yanda na sameka a d'azun, Fad'amin wata mai sa'ar ce tayi nasarar samun ka, ka sani ko yar waye mu din masu tsaya maka ne har sai mun d'auko ta mun kaimaka ita cikin d'akin ka zama na din din din a matsayin mata, ina rokon ka karka b'oyemin komai" Shiru falon ya d'auka kamar babu wani abu mai rai a cikin shi kafin zuwa can AK ya yanke shirun da cewa " wata karamar yarinya ce take shirin sa kaina ya tarwatse da tunanin ta Yusuf!" Sai kuma yayi shiru tsayin lokaci bai kara cewa komai ba, shi ma kuma Yusuf din bai tofa ba dan so yake ya amayar da duk abinda ke cikin shi, ba tareda shi ya takura mishi da yawan tambaya ba. "Yusuf karamar yarinya cefa ni banma san ta yanda zan iya tunkarar taba balle har kuma in gabatar mata da kaina a matsayin masoyi, kaima kasan hakan bai tab'a faruwa dani ba, ban saba tarar mace dan ingabatar mata da kaina ba a kullum matan ne ke tarana suna gabatar da kansu da bukatar su gareni dan haka ban san ta ina zan fara ba, kawai dai ina tsintar kaina a ciki farin ciki sosai a duk sanda na ganta ko naji muryar ta, haka kuma nike kasancewa cikin kewa da kad'aici a duk sanda na nesan ta kaina da ita, ban san dalili ba amma ji nikeyi a cikin zuciya ta cewa ita kad'ai nike muradi ita din zata wadatar dani in zauna da ita kad'ai a matsayin mata a yanzun shine kadai muradi na, sai dai kuma ban san ta ya'ya hakan zai faru ba" "Kenan dai kana so kace min har yanzun bata san cewa kana sonta ba?" "Bata sani ba dan ban tab'a nuna mata koda alama ba, hasalima auren ta bai dade da mutuwa ba amma wallahi kullum da tsoron kar in k'ara rasata a karo na biyu nike kwana nike tashi" "Bazawara" Wase ya ambata cike da mamaki, "Eh bazawara amma kuma wacce a zahiri ne ta amsa sunan a bad'ini kuwa budurwa za'a kirata" "Kai malam karka wani yi mata kwaskwarima duk macen da akama aure indai an d'aura tofa sunan ta bazawara ne" Katse shi AK yayi da cewa,,, "ban damu ba Yusuf koda wani suna za'a kirata, tunda har zuciyata tana sonta ko a ya na sameta hakan zanci gaba da zama da ita balle kuma abinda na shaida maka Ina da tabbaci akan shi" "Wacece ita? ma'ana ina nufin yar inace miye sunan ta ina ne garin su su waye iyayen ta? Duk ina son in sani!" "Karka damu kanka ita din ai ba bak'uwar ka bace," "Eh amma ai in baka fad'amin ba bazan san ko wacece ba!" "Sunan ta Amina amma Meenal suke ce mata yarinyar Aunty Jidda dake Unguwar Malamai zaria" "Kaiii" Yusuf ya ambata, "Kai mai jama'a badai yarinyar nan da akayi ma auren dole kwanan baya? Koba mai kiranka tuzuru ba?" "Ita fa" "Kai amma kun dace fa yasin kuwa ina fad'ama dan ni dama tun lokacin can naso inyi maka tsegumi amma sanin halin ka yasa na basar, to ya akayi auren nata ya mace ne?" "Sakaran miji ta samu mana, ya kaita gida ya kafe kamar wanda yakai ajiyar kud'i a banki" "Ahaf to ai mu Alhamdulillah indai haka ne gaba ta kaimu mai ya rage yanzun ai fad'awa kawai zakayi ayi faka faka a wuce wajen, dan wallahi yarinyar nan mai zafice da zarar kayi wasa sai dai ka fara ganin daka dakan motoci na layi alhaji," "Kai ban son wulakanci ya muna maganar arziki kai kuma kana sako wasa ne," "Ba zancen wasa ba Allah koni da ace baka ciki tofa tuni zanje inyi kamun k'afa a wajen Hajiya a bani ita in adana kogi ai baya k'in k'ari" Mtws Mai Jama'a yaja tsaki yana yunk'urawa da shirin barin mishi wajen, "Sorry sorry am just kidding, ni mai zanyi da k'arin wata mace kuma Allah na tuba, amma dai seriously zama bai ganka anan ba, can din dai daka guda zaka koma domin kasan yan magana sunce kula da kaya yafi ban cigiya, kar ka zauna anan ka saki baki acan kuma sai ka koma kaji ana wani zancen daban" "To idan na koma taya zan tun kareta, sanin kanka ne cewa soyayyar nan ni bak'onta ne, ban tab'a yin so ba balle in san yanda zan sarrafa ta wajen aika sakon inda ya kamata," "Karkaji komai indai soyayya ne matakan ta ai ba tsaurara kamar yanda kake zato bane, mataki na farko da zaka fara takawa shine jawota a jiki, Kaga duk wannan muzuran naka da kiran zan zane miki jiki da kakeyi, tofa duk ajiye su zakayi a gefe ka koyo tausasan kalamai wajen yin magana da ita," "Kai ban gane tausasan kalamai ba? D'an daudu kake son in zama a gabanta ne ko me? Kana ganin ta fa itama a taitsaye take kamar shinkafar da aka jik'a da ruwan zafi aka tsame, ita ba tafashe ba ita kuma ba dahuwa ba, yarinyar nan da zafina ma ba tsorona take ba in kuma naje mata a sanyi sanyi aishi kenan sai ta karasa maida ni mahaukaci," "Oh to a tsai-tsaye zaka tafiyar na naka salon soyayyar kenan, to ai yayi dama irin salon ai yafi bada citta, nidai ai mafita nike baka, indai kana son ta tofa dole ka ajiye duk wani girman kanka a gefe ka jawota a jikin ka har ta shak'u dakai, idan hakan ya kasance tofa bazaka sha wahala wajen yad'a manufofin kaba, jawo ta jikin naka kuma ya had'a harda d'aukarta kana d'an fita da ita yin siyayya haka ko kuma shan ice cream in ban manta ba tun a shekarun baya na Santa da son cin kaza, nasan ka gane mai nike nufi ta wannan gefen, amma tsakani da Allah karma kace ban fad'a maka ba zaka sha fama, dan kalarta ne kalar macen da suka kasance burin kowane cikakken namiji, Dan haka sai ka shirya ma yak'i da wadanda zasu fito rububin neman auren ta suma, yanzun dai inaga tunda kwana biyu kai ma baka lek'a ba ai ka tashi mu wuce Zarian kawai tunda mun gama uzurin da yake nan d'in dan dama nima gobe nike son in wuce Wase amma ba kwana zanyi ba. *Ummiee Zaria*โœ๐Ÿผ [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: โšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA!*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ ~{{MY FAMILY}}~ *RUBUTAWA* *UMMIEE ZARIA*โœ๐Ÿผ ```` *Page 48*..... *Masu ajiyemin sak'o a WhatsApp da masu kiran waya dan suji ya jikin mama ta k'araji, ina mai farin cikin sanar daku cewa Alhamdulillah jiki yayi sauki sosai wallahi nagode kwarai da gaske da kulawar ku gareni ubangiji Allah ya saka da alkhairi Allah yabar zumunci* ********* Ba tareda wani b'ata lokaci ba Mai Jama'a ya shige ciki, cike da zumud'i domin ji yake kamar wanda yayi shekaru bai sanyata a cikin idanuwan shiba,wani bak'on al'amari yakeji a tare dashi, ada shike nesanta kanshi da kusantar duk wani abu daya shafeta, amma yanzun zuciyar shi cike take da kwad'ayin son kasancewa tare da ita aduk wani saukar numfashi nashi, a cikin zuciyar shi yake fatan Allah yasa yana zuwa ita ce zata

Chapter 41 of 92