Share this page
namu a sanda kukaje nema ma d'anku auren ta koba haka ba? Dan da ace baku rike Jidda da mutunci ba bazamu baku auren Bilkisu ba" "Wannan haka yake" suka k'ara maimaita wa, a cikin masu amsawar kuma harda Malam wanda yake amsawa cike da alfaharin an yabe su, Cigaba yayi da cewa, "baku tsaya anan ba bayan Bilkisu kuka k'ara d'aukar yarmu kuka ba naku yaron, eh saboda ai itama Meenal din da kuke tak'amar takuce muma tamu ce kamar yanda kai Malam Adamu ka fad'a a d'azun" Yar k'aramar dariyar raha akayi, Baba Adamu kuma ya amsa da cewa "kwarai Meenal taku ce Alhaji" "To kaji gaskiya dai gashi kuma bayan ita yanzun kuma kun k'ara biyomu kun nemawa d'an gatan d'anku auren Yar mu Maimunatu wanda muna sa ran insha Allah nan da yan watanni ne za'a gabatar da nasu bikin koba haka ba kunga ko ai alaqa tsakanin mu daku takai kololuwar da ko yaro ya d'aga kai bai iya hango wa, dan haka ne yanzun bamuyi shayin zuwa nan d'in tafe da kayan mu ba dan mun san wuyarta dai mu nema ne a wajen ku mun san bazaku hana ba" "Wannan haka yake" Baba Adamu ya amsa dashi shida Alhaji Kamal shiko Malam kauda kanshi yayi gefe, "To yau dai zuwa mukayi dan mu nemarwa takwarar marigayi Abdul Khareem auren Yarku mai Babban suna munzo gareku da yak'ini muna kuma fatan Allah yasa wani bayyi mana shigar sauri ba?" Tsit falon yayi shi Baba Adamu yayi shiru ne dan a ganin shi an kai gab'ar daya kamata ace Malam yayi magana yanzun kam, Su kuma sauran yan falon sunyi shirune suna jiran jin amsa daga bakin mutum biyu ko dai Malam ya amsa musu ko kuma Baba Adamu, Kafe Malam Baba Adamu yayi da ido dan haka dole badan Malam yaso ba ya fara magana kamar haka bayan yayi gyarar muryar daya saba, "Alhamdulillah muna yi muku Barka da zuwa kuma duk munji bayanan da aka gabatar, Kafin ku shigo mun zauna mun d'an tattauna da shi Adamu domin shi da kuka ba Sallahu shine ya d'anyi nauyin baki wajen isar min da sak'on ni kuma rashin sanin abinda yake faruwa yasa a jiya bayan mun gama karatun da muke gabatar wa a masallaci na gabatar da sanarwar bada auren ita Mamana ga Sheikh Naseer malamin dake mana karatu wanda ya kasance d'ane a wajen k'anwata Zahra wacce uwa d'aya uba d'aya suka haifemu kamar dai yanda kuka san bamu da yan uba," K'ananun maganganu ne suka fara tashi daga can bakin k'ofa inda su Sa'eed ke zaune, inda suke tabbatar ma juna da zargin su dan su dama tun jiya sun zargi cewa Meenal ce Malam yaba Shehi ba kowa ba, lallai ko akwai gwarama yau, Gyaran murya Malam ya k'arayi, kafin ya d'aura da cewa, "Sannan kuma bayan sanar war da nayi daren jiya safen yau ma na samu bakuntar mutum uku wadanda dukan su sunzo min har nan cikin falon nawa sun kuma gabatar da kansu a matsayin masu son neman auren Meenal din wadanda dukan su dangin tane na kusa, mutum na farko da yaxo akan maganar Yayan tane domin dai k'anin mijin da muka aura mata da farko ne shima yaxo yana rokon mu aura mishi ita yana son ta ya kuma yi alkawarin riketa da amana, Mutum na biyu kuma shima yaro yayan tane domin da uban shi damu yaran wa da Kane muke, Na ukun su kuma shima d'ana ne domin yaron k'anwar muce wacce ita kebin Adamu wato kunga ko dukan su ukun makusanta ne na kusa wanda in akace abi cancan ta dukan su sun cancanci a aura musu Meenal" Dan shiru yayi sai dai kuma babu wanda ya amsa harya gama sauke ajiyar zuciyar shi yaci gaba da cewa, "Bayan su ukun can kuma d'azun nan da azahar kafin isowar ku na k'ara samun bukuncin wasu manema auren nata inda suke shaida min cewa d'ansu yaso ita Meenal din tun kafin wancan auren nata amma itace a lokacin batayi saurin bashi dama ba acewar ta sai ta gama makaranta zatayi aure, suma dai fitaccin ahaline wadanda koba niba kowa zaiso had'a zuria dasu, To gaku kuma kunzo kuma duka dai buk'atar d'aya ce daku da sauran duka dai auren uwata kuke nema...." Katse shi Hajiya tayi saurin yi tun kafin ya gama feso maganar dake cikin bakin shi, "Duk wannan lissafe lissafen da kayo ni basu ne damuwata ba domin duk cikin su ban cire mijin da zan iya sadaukar wa ita ba, Shi Salman d'in in yana da kunya ai ko hanyar falon nan bazai biyo ka da zancen son auren matar da d'an uwan shi uwa d'aya uba d'aya ya saka ba, ko ya manta irin rikon sakainar kashin da d'an uwan shi yayi mata ne? Da badun jajircewa naba da kila har yanzun tana gidan shi a girke tana cigaba dayi mishi shara da wanke wanke, Anji ba haramun bane amma dai ko babu komai ana barin halas dan kunya dan haka cire shi a lissafi wannan ba mijin Aminatu bane, Mu gangara kan shi Hashimu yake kowa? Oho koma da miye sunan shi shima bai cancanci auren Meenal ba dan bazan yarda daga hannun mai mata d'aya ta fad'a hannun mai mata biyu da tarin yara ba sannan kuma ba wani darajar ta yake gani ba barin in baka labarin yanda hirar su ta kasance a gidana kafin yazo maka da zancen" A gurguje ta labarta musu hirar Hashim da Meenal na ranar da yaje tudun wada kafin ta gangaro kan Aliyu, "Shi kuma Aliyun in ba neman fitina da shegen kwad'ayi irin na maza ba ina shi ina batun k'ara aure? Auren ma ya rasa wacce zaice yana so sai Meenal dan Allah kun tab'a ganin inda aka had'a gudun jirgin sama dana mota? Ina ai bama zai yuwuba dan haka shima na cire shi a lissafi, Allah sarki bawan Allah Sheikh shikam wannan dai da ace bada jikana ya had'a nema ba wallah dako ni ina iya yi mishi tsaye wajen ganin an bashi mata! Kuma ko yanzun ma karkuyi zaton cewa son kaine zai sa in zabi nawa jikan in barshi, ah ah wallahi ita dai Yarinyar ne na tabbatar da cewa jikana take so bashi wanda babanta ya k'ara zab'ar mata a karo na biyu matsayin mijin da zata aura ba, amma idan ana musu ana iya kiran ta dan aji nata ra'ayin aka su biyu, Yauwa batun shi wancan yaron Bashar ne ko Bashir shi dai d'an gidan Master Wanda ake cewa suma sunzo d'azun to ku nasan kune baku san shiba tun a wancan lokacin amma ni nasan shi dan har suma yayi a falona ranar da aka d'aura mata aure shakarun baya, Shima na cire shi a jerin masu neman aure dan koba komai wannan sha'anin na cikin gida ne bazamu kawo bare ba, Yauwa ina magana akan Shehi da kuma Jikana Abdul, Wannan dai ni kaf banga abunda za'a tsaya ba kai wahala ba, shi dai jikana shi yaga yar uwar shi saboda ra'ayin kanshi bawai dan wani ya tallata ko kuma a cusa mishi ita bisa dole ba, ah ah shi yaji ya gani cewa kaf fad'in garin nan k'asa dama duniyar gaba d'aya ita dai yaji ya gani yake so, Duk kunyar dana san yaron nan dashi haka ya murtsiketa tass ya tareni za zancen cewa yana son yar uwar shi, wanda ni kuma dama tun kafin ma ya furta alamomin da yake nunawa sun tona mishi asiri a wajena kafin kuma ya furta mata abokan shi ya fara fesama su kuma suka sameni har cikin d'akina aminin shi ya shaida min halin da shi Abdul din yake ciki, Inda ace naso to da tun lokacin zansa a shige gaba a nemar mishi auren ta a lokacin tunda bayan mutuwar auren ta ni daku duk munsan cewa bata tareda idda a kanta amma banyi Hakan ba, Kunsan me yasa?" "Ah ah Hajiya" da yawa daga cikin su da suka natsu suna sauraron ta suka amsa, Ita kuma sai taci gaba da cewa, "Saboda so nike ya tantance abinda yake ji akan ta, ni kuma so nike in gane zurfin da Soyayyar ta yayi a cikin nashi zuciyar, Bana son inyi saurin shigewa gaba akan maganar ne saboda koda yake jikana bazan so ya sameta salin alin ba dan so nike yasan zafin ta yanda ko bayan auren zai riketa da kyau ba rikon sakainar kashin da wasu mazan sukeyi ma mata ba" Dan dago kanshi malam yayi yana kallon hajiyar dan yasan dai maganar ta na k'arshe da biyu tayi shi, Ita ko bata damu ba taci gaba da cewa, "Dan haka sai nakau dakai ban nuna na gane komai ba har zuwa sanda ya gaji da nuk'u nuk'u dan yakeyi ya furta mata, Tun lokacin daya furta kullum bashi da magana saina shidai in tura a nemo mishi auren ta surutun shi kuma bai sa nayi hakan ba duk da cewa duk da iyayen shi basa gari ina da damar dazan wakilta wasu su nemo mishi auren kuma a bashi amma banyi hakan ba, saboda so nike ya d'and'ana zafin da akeji a yayinda zakaga wasu mazan suna kaima abinda kai kake farauta cafka, hakan zai sa kaima ka jajirce, to Alhamdulillah duk wasu abubuwan da nike buk'atar tantancewa a tsakanin su na kammala ina kuma da tabbacin cewa ko yanzun aka d'aura auren su zasu rike junan su su kuma rayu cike da soyyaya shi yasa na had'o kan duk wad'anda suka dace a gabatar da komai a gaban su muka taho, Mun taho da komai daya kamata tun daga kan kud'in gaisuwar uwa da uba har zuwa komai da ake buk'ata wajen gabatar da neman aure, domin a sanya mana rana, to amma yanzun zuwa na da kuma jawaban da naji daga bakin ku hakan yasa na canza ra'ayi bayan gabatar wa Ina so Uban shi ya biya kud'in sadaki kawai a wannan taron a d'aura aure gaba d'aya domin hakan ne kad'ai zai sa hankalina ya kwanta, jikana dai ba d'an iska bane baya shaye shaye baya sata, haka kuma baya caca balle yabi Matan banza duk inda aka shiga ko ina nasan jam'a zasu shede shi dan ba abanza yaci sunan da kakan shi yasa miba Mai Jama'a, Kai Usmanu kun fito da kud'i a jikin ku ko nice zan biya mishi sadakin?" Daga can bakin k'ofa kusan mutum hudu suka had'a baki wajen cewa "nine zan biya mishi" Musty Farouq da abokin Musty da kuma Ya Sarki wanda basu ma san da tsayuwar shi a wajen tun d'azun ba sune suka fad'i haka, "Kai masha Allah kunji yan albarka to kai Adamu ai sai ka yanke mana sadakin auren yarka kaga masu jiran a fad'a su biya ma suna da yawa ashe, kaga dai alamun kowa nason wannan had'in kenan, oho wanda baiso bama dai In allah yaso sai anyi balle kuma rabon ciki da haihuwa basu bar kowa ba. *Ummiee ce*✍🏼 [10/7, 10:40 PM] Ummiee Zaria: βšœοΈπŸ”±πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *DANGINA*πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ”±βšœ *BOOK 2* *Page 45* Bud'ama Sarki hanya sukayi ya shigo cikin falon shima tareda Ya Sheikh wanda shima dawowar shi gidan kenan dan tun safe ya fita a gidan zuwa gwargwaje inda yakai ma wani abokin shi ziyara dawowar shi gidan yayi dai dai da shima Sarki zai shigo dan haka sai kawai suka shigo gidan a tare, koda suka iso kofar falon Sarki yaso ya juya ya koma shi Sheikh ne ya hanashi akan gara su isa suji me yake faruwa dan daga ganin taron ga kuma motocin da suka gani a farfajiyar gidan sun kasan abune mai mahimmanci ake tattaunawa a falon wanda ya had'a kan ahalin gidan, suma kuma ai ahalin gidan ne dan haka su k'arasa kawai ayi dasu suma. basu san abubuwan da aka tattauna akai daga farko ba jawaban da Hajiya ta gabatar daga k'arshe kawai sukaji dan haka sai shi Sarkin baiyi k'asa a gwuiwa ba dan dama yayi niyyar cewa in batun auren ya tashi shine zai shige ma AK gaba duk da cewa yar gida za'ayi , yanzun kuma da yaji bayanan Hajiya dole ya bata goyon baya kodan a kawo k'arshen rarrabuwa da kawunan ahalin yake son yi akan zancen auren Meenal d'in daya tashi a yau kamar tashin Bomb yake shirin tarwatsa kan ahali wanda babu wani yayi zaton haka, Shifa bawai yana ma Salman bakin ciki bane danshi Salman d'in yana son matar dashi ya saka ba, ah ah shi dai kawai cancanta yake dubawa kuma koba komai ita Meenal AK take so bai kamata a k'ara tauyeta akaro na biyu ba dan in akayi hakan itace zata cutu tunda su mazan dukan su koda ace sun aureta hakan bazai hana su k'ara wani auren baya itaba kenan dai duk wanda aka aurawa a tsakanin su Salman din ba'a mata adalci ba, yama gode Allah da Allah yasa ya shigo gidan a dai dai dan shigowar shi dama yazo ne dan yaba Malam hak'uri akan abinda Salman yayi shi kuma yayi amfani da damar ya kawo zancen AK ga Malam to ashe ma Mai gayya mai aiki ta gaji da jiran gawon shanu ko kuma dai itama labarin jerin gwanon neman auren ne yaje kunnen ta shi yasa ta kwaso nata iyalan ta taho? Komai dai ya akayi shi hakan ya mishi dai dai yau yana bayan Hajiya tuk'uicin kyautar datayi mishi ne shima zai maida mata. Shifa Sarki dalilin aikaΒ²r da Salman ya aikata da safen na zuwa wajen Malam kai tsaye bayan tun farko saida iyayen shi suka tsawatar mishi amma yayi kunnin uwar shegu dasu yayi gaban kanshine yasa shi barin komai dake gaban shi a yau d'in ya taho Zarian bayan Uwar gida ta kirashi ta labarta mishi abinda ake ciki, Domin bayan da Salman ya bar wajen Malam gida ya koma dan ya riga ya k'una baya tsoron wuta dan haka yana zuwa kafin ma labarin ya koma kunnin su Uwar gida shi da kanshi yakai musu labarin ya kuma kafa musu hujja da cewa inhar mutanen tudun wada da suma suke matsayin iyayen Meenal ta gefen Mahaifiyar ta zasu iya ture komai daya faru a baya suba Sarki auren yarsu a karo na biyu, to shima baiga dalilin da zai sa anan suce zasu hana shi auren Meenal ba tunda dai shi yace yaji ya gani yana sonta, dan haka tunda su sun kasa tambayo mishi shi yakai kanshi kuma su sani babu abinda zai hana shi auren Meenal inhar ta amsa tana son shi yasan Malam zai aura mata shine dan koba komai yafi su Aliyu da Hashim kwarin gwuiwa koba komai a cikin su shine Saurayi yasan Malam bazai bata mai mata ba, Fad'a sosai Malam Sulaiman da Uwar gida suka rufe shi dashi akan me zai aikata haka amma bai saurare suba sai ma ficewa da yayi yabar gidan kuma a yau basai gobe ba zai k'ara komawa wajen Meenal su daddale kafin Malam ya nemeta domin jin ta bakin ta, K'ananan surutan da gidan Malam Sulaiman din ya d'auka ne yasa ita Uwar gida ta kira Sarki a waya dan gara yazo ya tsawata ma Salman d'in dan ita dai bata san da wanne zataji ba da surutun kishiyoyi da facalolin ta keyi akan maganar ko kuma da iskancin da Salman din ya tsiro musu dashi na k'in jin maganar su, Itama fa bawai tana k'in auren bane, ah ah tadai san cewa ko kowa zaiso auren tofa bai zama lallai malam yayi murna da had'in auren ba kilama laifinta zai k'ara gani ko kuma yace itace ma ta tura mishi Salman d'in, tunda itace dai tayi tsaye aka ba Sarki Meenal ga kuma abinda ya biyo baya yanzun kuma ace Salman wannan ai laifinta kawai Salman din yake son Malam ya cigaba da gani wallahi. Sarki bai zauna ba sai da ya k'arasa har gaban kujerar da Hajiya take bayan sun mik'a gaisuwar su ga mutanen da suka tarar a cikin falon shi Sheikh a bakin k'ofa su Sa'eed suka gyara mishi ya zauna anan ne kuma yake tambayar su "me yake faruwa ne? " su kuma suka d'an labarta mishi komai a gajarce, Sarki ko hannu yasa a cikin aljihu duk wata takardar Naira dake jikin shi sai da ya zubeta a gaban Hajiya tundaga kan yan dubu zuwa k'ananan canjin dako shi bai san nawa ne a dadin kud'in ba, Yana gama zube mata su ya koma da baya shima can dai gefen da su yaran gida suke Abdul ne ya tashi a inda yake yaba Sarki wajen ya zauna, Tun sarki bai kai ga zama ba Musty da Kamal suma suka mik'e yanda Sarki yayi ma aljihunan shi kwal haka suma sukaje suka zazzage nasu nauyin aljihun a gaban Hajiya wacce take ta faman washe baki ranta fess sai albarkha take sanya musu, Malam ko a lokacin idan ka mishi kallo d'aya bazakayi marmarin k'arawa ba saboda ya d'aure fuska sam babu alamun fara'a ido kawai yasa yana kallon ikon Allah, Dan wallahi yasani sarai cewa da biyu Hajiya tayo mishi gangami saboda yace wani abunda bai dace ba a gaban sirikai girman shi ya zube, wai shi za'a biyo har cikin d'akin shi a nuna mishi isa akan Yar da ubanta ma a k'ark'ashin ikon shi yake, wallahi da yasan haka ne zai faru a yau da ba sanarwar bada auren Meenal d'in ga Sheikh zaiyi a daren jiya ba auren kawai zai d'aura in yaso sai yaga uban da zai kashe auren. Abun mamaki sai gashi harda ya Sheikh shima yabi ayari cikin masu juye tattalin arzikin aljihun su a gaban Hajiya kafin ka an kara kud'i sun taru domin kaf d'in yara mazan dake falon sai da suka juye aljifan su bayan sun gama kuma haka suma iyayen Maza sukabi ayari, shi dai Malam kallon ikon Allah kawai yakeyi, Alhaji hamza ne ya fara fidda nashi kudad'en sai Alhaji Musa, Shidai Baba Adamu cewa yayi yaga alamun yaron nasu d'an gatane dan haka bazai sa musu ko sisi ba dan kud'in shi tattalawa zaiyi ya Siyama Meenal din gadon bacci, Farantin da aka d'aura ruwan da Abdul ya kawo musu Hajiya ta juye kayan cikin farantin a k'asa, Sai da tasa gyalen ta ta goge farantin kafin ta kwashe kud'ad'en nan kaf ta zuba a farantin ta k'arasa gaban Malam ta ajiye, "To Malam Almu ga sadakin takwarata nan yan uwan ta sun biya, Nasan dai ko kud'in zaku yanke bazaku yanke wanda zaikai adadin wannan ba dan haka gashi nan shima in bai wadatar ba zamu k'aro ninkin adadin su saboda ta cancanta" Mai da kallon ta ga sauran jama'ar falon tayi saida ta k'arewa kowa kallon tsaf kafin ta tsaida duban ta akan Sheikh, "Malam Naseer" Ta kira sunan shi a sanyaye, "Na'am Hajiya" shi kuma ya amsa mata fuskar shi a sake, "Kai kuma bawan Allah daga zuwa kaima sai kabi ayarin masu tarbace? Tun baka san ko sadakin wa ake had'awa ba, to da fari dai hakuri zan baka kayi hak'uri nazo nayi maka shigar sauri ina fatan bazaka kullace ni a cikin ranka ba?" "Ah ah Hajiya me yayi zafi da harni zan k'ullace ki kuma?" "To dai batun in tsaya yi maka kwanaΒ² ma duk bata taso ba, Zanyi magana ne akan sanarwar da Malam ya bada jiya cewa ya baka mata shin kai kasan wacece aka baka ne?" Sai da yakai duban shi kan Malam kafin ya amsa mata da cewa "ah ah Hajiya ban sani ba sai dai koma wacece ina farin ciki zan kumayi maraba da shigowar ta cikin ruyuwata tunda har kyautar ta hannun Baba Malam ya fito yasan na cancanta shi yasa ya bani na kuma gode ubangiji Allah ya k'ara girma yasa a gama lafiya" "Ameen..... " D'aukakin jam'ar dake cikin falon suka amsa gaba d'aya, Ita kuma Hajiya sai taci gaba da magana bayan ta amsa da Ameen din itama, "Masha Allah lallai ka cancanci a baka mata ako ina ne kuwa Naseer, To a jiya dai shi Baban naku ya sanarda cewa ya baka Meenal sai dai sunan tane bai k'ira acan d'in ba dalilin rashin kiran sunan nata a jiyan kuma wannan shiya barma kanshi sani, Amma mu dai ya fad'a mana cewa itace ya baka a wannan zaman da mukeyi, Ba bayarda ita din da yayi gareka ne damuwar ba, ah ah damuwar shine daya k'ara d'aukar ta ya bayar a karo na biyu ba tareda yayi shawara da kowa ba bayan ita din ai kowa yasan cewa tana da uwa a raye koba komai in ba'aji ra'ayin ita Yarinyar ba tunda ana ganin cewa an isa da ita to ita kuma uwarta fa?, ko har yanzun dai ita uwa nata alaqar kawai na haihuwa ne amma in anzo batun hukunci akan abinda ta haifan shikenan sai kuma a nuna mata cewa bata da ikon ko isar da za'a iya jin ta bakin ta?, Humm koda yike ba wannan maganar nike son fad'a maka ba kana jina koh?" Ta tambaya tana kallon Sheikh d'in, Baba Usman ne yayi saurin tarar numfashin Hajiyar jin da yayi ta fara sauka akan layi dan shidai bazai so ta raba halin ta a falon kafin subar gidan ba dan haka sai yayi saurin d'aurama Sheikh da cewa, "Kayi Hakuri Naseer shi Baban ku bai san da batun neman da d'an uwan ku yakema ita Meenal din ba nasan shi yasa yayi kwad'ayin baka ita saboda cancantar ka, sai dai mu kuma tun kwanaki muka gabatar ma Baban ku Adamu da batun neman shi kuma sai Allah bai bashi ikon kawo ma Malam zancen ba sai yau. zuwar mune kuma Malam yake sheda mana cewa kai yaba Meenal duk da cewa daga safen yau zuwa yanzun bayan kai daya ba a jiya mu mune mutane na biyar da mukazo neman auren ta a yau, Bamu san abinda ke cikin zuciyar ka akan ita Yarinyar ba barin ma kuma daya zamana Malam bai kira suna ba tun jiyan sai dai mu muna da tabbacin cewa ita da d'an uwan ta suna son junan su shi yasa suka had'a kansu k'arewa ma itace ta buk'aci shi d'an uwan nata ya kawo zancen nan gaban iyayen ta shi kuma ya wakilta mu a matsayin mu na iyayen shi maza, muna fatan koda ma ace kana son ta to zaka iya sadaukar da son da kake mata dan ganin ta samu abinda take so a wannan karon?" Tunda Baba Usman ya fara magana kan Sheikh yake k'asa domin idanuwar kowa a kanshi yake kowa so yake yaji mai zaice kuma, Shiko a zuciyar shi mamaki kawai yakeyi, shifa wallahi koda Malam ya bada sanarwar tun jiya bai kawo kowa a cikin zuciyar shiba sai Fauxieyerh saboda kaf gidan kowa yasan da cewa yafi shakuwa da kuma sakewa da ita, dan haka shi yasa koda suka dawo gida a jiyan bai nemi jin ta bakin Malam din ba dan shi bai tab'a kawo zancen Meenal a cikin kanshi ba, Jama'a shi wani tsautsayi ne zai sa shi auren wancan Yarinyar data iya cinye maza da kalaman bakin ta? Yarinyar dazai ce ta koma tasa hijab ita kuma tabi ta wani k'ofar ta fice daga gidan ba tareda ta sanya hijab din ba, Ah ah wallahi shikam Meenal tafi k'arfin shi garama da akayi walkiya inba haka ba da haka zai saki baki shi a ranshi yana tsammanin Fauxieyerh a gefe kuma ana shirin aura mishi Meenal, Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke kafin ya d'ago kanshi yana kallon Malam yace "Baba dama ba Fauxieyerh bace Yarinyar daka bada sanarwar zaka bani auren ta a jiya?" Dagowa shima Malam yayi fuska d'aure yace " Meenal ce Yarinyar dana sanar da cewa na baka a jiya kuma har

Chapter 81 of 92