Share this page
ya k'ara jan hankalin su akan rike zumuncin dake tsakanin junan su, Domin yana fatan zaman lafiya da fahimtar juna ya tabbata a cikin ahalin shi ko bayan kasa ya rufe mishi ido, Haka dai a ka tashi wannan taro jiki a sanyaye kowa na mamakin ya akayi auren Sarki da Meenal ya mutu, A wannan rana dai mutuwar auren shine ya zama labari mafi zafin daya dunga watsuwa a tsakanin ahalin. #No aditing ๐Ÿ˜’ #Team AK #Team Sheikh Naseer #Team Hajiya #Team Malam *Ummiee Zaria*โœ๐Ÿผ [8/20, 8:48 PM] Ummiee Zaria: โšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA!*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ *~{{ MY FAMILY}}~ BOOK 2* ยฉยฎ *UZ-2023.* *RUBUTAWA* *ZAINAB USMAN* *~{{UMMIEE ZARIA}}~*โœ๐Ÿผ *Page 3.* *AK d'an mai karfi, da Yusuf wase* kuwa kasancewar basu bar garin Kaduna da wuri ba hakan yasa basu samu damar shigowa cikin garin na Zaria ba sai gaban nin magariba, Hakan nema kuma yasa koda suka iso basu samu damar shiga gidan na Hajiya ba sakamakon tsayawa gaisawa da matasan majalisar nasu da sukayi, wanda gaisuwan nasu shiya kai su har zuwa lokacin sallan Magriba to bayan an idar da Sallah din ma da kyar Mai Jama'a ya samu ya zare jikin shi a cikin jama'ar shi domin Yusuf dama suna fitowa daga masallaci ya wuce cikin gidan bai tsaya a wajen ba. Kamar wanda magnet ke janshi haka ya samu kanshi da d'aukin zuwa sashen na Hajiya fatan shi dai kawai shine Allah yasa yarinyar nan itace abu na farko da zai fara yin tozali da ita a sashen, Dan haka gudu gudu sauri sauri haka ya fad'a sashen shi turaren shi ya dauka ya k'ara feffesawa had'ida gyara zaman hulan shi kafin ya fito kai tsaye zuwa sashen na Hajiya cike da takun shi na mazajen dake ji da kansu, Sai dai tun kafin ya k'arasa ya farajin hayaniyar Hajiya inda take cewa... "Shike nan duniya ace mutum bazaici abincin kwarai ba rayuwa sai mace tasha tea da safe tea da rana tea da dare uwa dai wata jinin larabawa ko buzaye? Takwara indai baso kike ki k'arasa karmashewa ta yanda ubanki Almu zaiji dad'in fadamin maganar banza ba ai kamata yayi ki ceci kanki ki bani had'in kai ki dunga cin abunci masu gina jiki ta yarda ko mak'iyi yaganki yasan cewa zawarci ya amshe ki, ke bakiga mazan yanzun sun fison mace mai d'an mulmulallan jiki ba, ina amfanin mace ta zauna a rame uwa wata mai cutar yunwa, to nidai Allah ya sani gidan nan babu kishirwa bare ayi batun yunwa, so kike dai sai ubanki ya samu hanyar fad'amin maganar banza in ya ganki a bushe" Murmushi ne ya subuce mishi a zuciyar shi yake cewa, kuji min tsohuwar nan fa, towa yace mata ni yar lukata nike so matata ta zama me?" Mai makon yabi ta kofar falon sai ya juya akalar shi zuwa tacan baya yabi ta kofar kitchen, kamar yanda ko yayi tsammani a bud'e kofar take ba'a kulle ta da makulli kamar ko yaushe ba, dan haka ya bud'eta kai tsaye ya shige ciki. Koda ya bullo cikin falon ta wajen dinning duk Sallamar da yake Hajiya da idon ta ya fure take tama meenal mita wacce ke zaune a kan kafet din dake tsakiyar falon manyan littafan tane na karatu kewaye da ita sai wani littafin dake yin jotting abubuwan da take tsinta a cikin littafan gefe d'aya kuma kofin shayi ne sai wani k'aramin bowl dake d'auke da dambun nama a cikin shi, Lallai hausa sunyi gaskiya a yayin da sukace kubar rai da abunda yake so, Domin ko hakance ta faru da Mai Jama'a tun bayan wanzuwar shi a cikin falon idanun shi basu sauka a ko inaba kai tsaye sai akan abar kaunar shi wacce daman ita din itace abunda yake da buri da fatan yin tozali da ita a daidai wannan lokacin, Bai san yayi kewarta da yawa ba sai lokacin domin kuwa mai makon ya k'arasa inda suke duk da alamu sun nuna cewa sud'in basuji shigowar shi ba, Ah ah kawai sai ya samu kanshi da gyara tsayuwar shi bayan daya jingina jikin shi da dinning din dake wajen kawai yaci gaba da bin fuskarta da kallo, bakin ta kawai yake kallo a yayinda take amsa ma Hajiya da cewa, "Wai ke Hajiya waye ma yace miki yawan cin abunci shike sa mutum yin kiba ne? Kuma ni Allah ma ya sani cewa ko kadan bana son k'ibar da kike ambata min shi yasa ma yayo ni haka" Daga kan bakin ta ya maida kallon shi zuwa kan dogon hancin ta dake nan d'an zuwat abunshi sai kuma kyawawan idanuwan ta dake kyalli akoda yaushe sakama kon ruwan dake cikin su hakan nema yasa abu kadan kesata kuka, Kanta da babu d'an kwali sai wani d'an karamin hankaci da tayi amfani dashi ta dan daure kan dashi, saboda kasancewar hankacin karami ne kuma hakan yasa sai bai rufe mata gashin kan nata dake tsefe da kyau ba, sakamakon tea din da take Shane kuma zafin da tea din yake dashi hakan yasa zufa tsatsafowa a goshinta har ya zama silar da gashin dake kwance goshin ta kwanciya lambam a gaban goshin nata, Mik'a tayi na alamar gajiya da zaman da tayi a wajen, mik'ar data nemi tarwatse mishi dan nutsuwar daya samu a yan kwanakin sakamakon bankaro k'irjinta da tayi zuwa gaba, gashi kuma dama ba wata rigar arziki bace a jikin nata half best ce a ciki sai kuma ta d'auko wata fibgilar shimi dake nan shara shara ta d'aura akan half best din wanda hakan bai wani rufe komai na daga ainihin surar jikin taba sai ma k'ara fitowa da surar nata yayi a zahiri, tasan cewa ba kasafai a yanzun hajiya ke samun bak'i mazaba tunda Mai Jama'a ya dena zama a garin sai bakin gidan suka ragu dan haka koda ta dawo gidan take zama a sashen na hajiya bata da shamaki shigar data keso shi takeyi sai dai yawancin lokuta in zata zauna a falon sai ta kullo kofar falon saboda gudun fad'owar wani cikin falon ba tareda ta kimtsa ba, yau kuma ganin dare ya fara kuma kofar falon yana rufe dan haka ta fito a bunta dan akwai abu mai mahimmanci da take son yin nazari akan shi, tun kafin magrib take zaune sakamakon fashin sallan da takeyi shi yasa koda lokacin sallan yayi bata tashi ba dan hatta da tea din da take sha Larai ta rok'a ta had'o ta kawo mata dan bata son abunda zai katse mata abunda takeyi din tafison sai ta kammala sai ta tashi gaba d'aya. Runtse kwayar idanuwan shi yayi gam yana karanto kalmar innalillahi wa innah ilaihir raju'un, yasin inda ace yarinyar nan tasan da tsayuwar shi a wajen to da sai yace da gayya tayi mik'ar dan taga yana kallon ta, to amma ai koba kowa bai dace mace ta saki jiki tana wani gantsaro kirji da sunan mik'a ba๐Ÿ˜’ dan hakan d'aukar alhaki ne, kawai daga zuwan shi tana neman had'o mishi tarzoma, *Ita ko Meenal* da fari kamshin turaren shi data dad'e da haddacewa ne ya fara sumame zuwa hancin ta, taso ta share dan a zaton ta kamshin ne kawai irin yanda wani lokacin idan mutum na zaune sai ya dunga jin kamshin abubuwa, sai dai kuma daga baya tsigar jikin tane taji yana tashi gaba d'aya sai takejin ta tsargi kanta kamar dai akwai idon dake yawo a jikin ta, Dan haka sai ta d'ago kanta zuwa ga wajen Hajiya dan taga ko itace ke kallon ta, sai dai kuma sai ta iske gaba d'aya hankalin Hajiyar nakan shirin da ake gabatarwa ne a tv hannun ta kuma rik'e da carbin ta da take ja sakamakon azkar din da takeyi duk bayan idar da sallar magrib, Da kad'an da kadan ta fara yawo da kwayar idonta a cikin falon har zuwa lokacin kuma tsigar jikinta bai bar tashi ba, kurrr idanuwan ta suka shige cikin nashi ga mamakin ta sai taga yana mata murmushi, A zaton ta gizo ne yake mata dan haka sai tayi kokari wajen fusgar nata idanuwan daga cikin nashi ta runtse su da karfi sai dai kuma ilai dai koda ta bud'e shi din dai taci gaba da gani tsaye ya rungume hannayen shi a kirji yana sakar mata murmushin shi kai kayatarwa, Baya baya tayi kafin ta bud'e bakin ta ta kwad'a ihu tana mai nuna inda yake da hannu, "fatalwa Hajiya! Fatalwa!! Wallahi fatalwa ne a falon nan" Ta fad'a a yayin da ta isa wajen Hajiya da rarrafe ta wani irin cumuimuye kanta a cikin jikin Hajiyar, "Fatalwar lafiya! Ke kin taba ganin fatalwa ne a gaske dan ubanki, kuma shi fatalwar duk ta rasa wajen zuwa sai falona da kullum yake cike da tsarki, dallah can ni cikani" "Wallahi Allah da gaske nikeyi Hajiya ba gashi can a tsaye wajen dinning table dinki ba" Kai duban ta zuwa wajen Hajiya tayi, "Wannan ne fatalwar? Ikon Allah aiko da sai ince lalacewar zamani takai inda takai tafale da ado da kwalliya, kiga mutum a tsaye da kafafu biyu kice wani fatalwa, to waini uban wa ma na kashe da zaimin fatalwa? Yo ni ko shedanun aljannu ai sai sun shirya kafin su nufo inda nike balle wata tsiya can wai fatalwa," "Hajiya kalli fuskar shifa murmushi yakeyi wallahi" "Ikon Allah, kai kuma dan mak'iyin uban mutum wani salon iya shegen ne wannan zaka fad'omin daki daga sama kamar wani dan aljannu? Kai tsaya ma ina fatan dai ba zuwa Kayi kaima ka amso shegiyar layan nan ta k'arya da ake cewa ana b'ata in an latsata ba?" Dariya dukan su suka bashi, Dan haka ya shiga kyakyatawa ba kakkautawa a yayinda yake karasowa wajen su, Da kallo Meenal ta bishi domin dai wallahi tsayin rayuwarta ita bata tab'a ganin shi yana dariya harda kyakyatawa irin hakan ba, dan haka sai ta kure shi da kallo tana ganin yanda dariyar ya mishi kyau matuk'a sakamakon fararen hakoran shi da suke jere reras ga wushirya a tsakanin su sama da k'asa, "Wai kema tsoron kikaji kamar wannan zabuwar jikar taki Hajjaju ta?" "Allah ya sawake in tsaya jin tsoron wani abun halitta can da yawar ka" Ta k'arasa fad'a tana aika mishi da harara. "Ke kuma mai kikeyi a gidan nan?" Ya tambaya a yayinda yakai zaune a kasan shima kamar yanda suma suke zaune, "Oh wai meenal kake magana? Ai Allah yayi dai bana na kwato ta daga hannun wancan uban nata dake musu mulkin mallaka dan haka ta dawo hannuna, fata nike Allah ya fiddo mata da d'an dashe shen miji na nuna ma sa'a kwanan nan in wanke ta in kai mishi ita" "Allah ya sawak'e ni bazan k'ara yin wani aure yanzun ba" Meenal ta amsa dashi tana murgud'a baki. "Ah ah wallahi karma Kiyi ka kanki mugun baki, aure ai ya zama dole, to so kike in saki a gaba inyi ta kallo bayan tako ina kinkai minzalin auren? Ina ce suma kawayen naki batun aurar dasu iyayen su sukeyi to so kike su suyi auren ke kuma kici gaba da zama a gaban mu salon Almu yasamu dalilin da zai kullaceni da kyau kinga kin bashi damar fad'amin magana kenan, zaice na baro ki daga gida na kawo nan kuma na d'aure miki gindi kinki aure, Ah ah wallahi aure kam bari dai ki gani mijin dai ya fito" "Hajiya tunda tace bata son auren ki barta mana har sanda ta shirya!" "Kai matsa can bani waje, kai in ana maganar aure har ma kana da bakin tsomawa? Ka daiyi ta zama har mutuwa tazo tayi wuf da kai baka ajiye mana wanda zamu gani mu dunga fad'in cewa oh ga d'an Abdul Khareemu ba, kana nan kana sha shanci mtws duk dai ka gama tara kudin kana mutuwa kasafin su za'a mana muci kaji kaiko kana can an turbud'e a karkashin kasa" "To wai dama ni Hajiya na taba zama dake ne nace miki bazanyi aure ba?" "Oh to ka samu lafiyan kenan kwanan baya ai cemin kayi baka da lafiya yin aure saboda nika d'auka shashasha" Shiru yayi wannan karan ba amsa, Kuji hajiya fa tana neman tona mishi asiri a gaban yarinyar nan, Sad'af sad'af Meenal ta mike a yayinda ta tuna cewa bafa kayan kwarai bane a jikin ta dan siket din dake jikin tama ko gwuiwar ta bai k'arasa ba dan haka ta bayan kujerun falon ta dunga bi harta fada cikin daya daga cikin dakunan dake nan k'asa dan bazai yuwu ta wuce zuwa sama da kayan dake jikinta ba alhalin shi din yana zaune a falon dan ba kadan ba duk take jin ta tsargu, haka kawai ya wani shigo ma mutane babu sallama. Sabon gaisuwa sukayi shida Hajiyar bayan ta bace ma ganin shi, kafin suka d'aura da hira anan kuma Hajiya ta bud'e babin bashi labarin abubuwan da suka faru a cikin kwanakin da suka wuce da bashi a cikin gidan. Suna kuma cikin hirar ne Yusuf ya shigo shida Musty wanda shima bai dad'e da isowa daga Abuja ba, dan haka suma suka zauna akaci gaba da hirar dasu har zuwa lokacin da akayi kiran sallan ishsha'i, hakan ne kuma yasa dole suka tsagaita da hirar da suke suka tashi da nufin zuwa su gabatar da nasu sallan, har sun kai bakin kofa Yusuf ya dawo baya, "Hajiya yau fa ina da labari mai tsada da zan baki amma sai kin bani goron albishir kafin nan kuma yunwa nikeji๐Ÿ˜ž" Ya k'arasa fada yana narke fuska, [8/20, 8:48 PM] Ummiee Zaria: ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA!*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆโšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ *~{{MY FAMILY}}~BOOK 2* ยฉยฎ *UZ-2023.* *RUBUTAWA* *ZAINAB USMAN* *~{Ummiee Zaria}~*โœ๐Ÿผ ~~~*Page 4* Allah yasa albishir da haihuwan Saniyata zakamin, dan satin daya wuce danaje gidan gonar na samu guda a cikin su da ciki tsoho kuma Zakariya yace min suna saran haihuwar ta cikin satin nan" Hajiya ta fad'a tana washe baki, "Ah ah kam wannan albishir din nawa wanda kika dade kina jira ne kedai kawai ki tanadi goron ki na albishir ni kuma idan na dawo in baki shi da zafin shi," Yana gama fad'in hakan ya take ma su Musty baya wadanda suka fice tuni, Da gudu gudu ya samu ya cimmusu, kamar dama AK jiran isarshi ya ke ya wani bishi da kallo yana cin magani, "Yusufยณ" Ya kira sunan Yusuf din har sau uku shima kuma Yusuf din yaci gaba da amsawa ba tareda ya gajiya ba. "Wallahi in ka fada Allah ya isa na" "Kai dallah can ware, ai wallahi kaji dai nama Kara rantsewa yasin sai na fad'a" 'Oh amanata zakaci bayan na yarda da kai?" AK ya tambaya yana marairaice wa, "Amana ta nawa kuma? Amana ta wuce wacce ka cinye tsakanin ka da zuciyar ka, malam ni mafita kawai nike nemo maka saboda ina kaunar ka da yawa bazan so inga kana wahala ba" "Kai wai ku tsaya kunfa sani a duhu ban gane ba, meke faruwa ne anan?" Musty ya tambaya yana shiga tsakaiyar su, "Ni dai Allah ya isa na wallahi, kuma ma laifina ne dana fada maka damuwa ta" Cewar AK a yayin da yayi gaba ya fice daga gidan ya barsu a baya Yusuf na mishi dariya. "Wai Baban Affan bazaka fadamin abunda yake faruwa ba?" "Me zai hana in shafa maka, amma dai gaskiya labarin mai tsada ne wallahi bazan fada muku ba sai naji saukar alert mai nauyi cikin asusuna," "Ah haba Baaba kar muyi haka mana nine fa Mustyn ka" "Koma dai miye na dai fada maka amma ga Satan amsa zan baka, *abokin ka ya fad'a soyyaya*" Wata irin fashewa da dariya Musty yayi kafin ya tsagaita da dariyar anan inda suke tsayen yayi ruku'u na nuna godiyar shi a wajen Allah subhanahu wata'alah, "Ai dole kayi ruku'u wallahi" Rungume Yusuf yayi tsamtsam bayan ya dago cike da tarin murna da farin cikin da suka sauka mishi ya sanya duka karfin shi ya d'aga Yusuf din sama yana juyawa dashi irin yanda akewa yara, Dan koba komai dama shi Musty din yafi Yusuf din jiki kasancewar Yusuf din bafulatani sai ya zamana hatta da jikin shi irin na fulanin ne, "Kai miye haka dallah ni saukeni ya zaka wani dunga juyi dani kamar ka dauki karamin yaro, dan allah saukeni juwa nike gani" Ya fada yana dukan kirjin Mustyn a kokarin shi na ganin ya sauke shi, Ajiye shin yayi yana dariya shi kuma saiya rike Mustyn sakamakon jirin da yakejin yana neman kadashi, "Kai dan iskane wallahi musty taya zaka wani dunga juyi dani a filin Allah dan kawai kana takamar ka fini girman jiki to yasin kayi ma kanka bazan baka labarin ba" "Kama isa ka shafa min mai abaki sannan kace bazaka fadamin ba, wacece dan Allah?, kai amma wallahi AK dan rainin wayau ne wai dama soyayyar ce duk tasa ya firgice uwa wanda ya shekara rashin lafiya? Oh Allah na gode maka ashe zanga wannan ranar da AK zaiso wata macen sab'anin matan da kullum sune suke binshi" Dafa kafadar shi Yusuf, "Kaga Malam muje kafin mu rasa jam'i kardai ka manta kanun labarin kawai na fad'a maka cikakken labarin sai naji alert tukun a hakan ma kuma har sai Sadeeq ya dawo zuwa gobe tukun dan yace min zai shigo gobe" "Fad'i ko nawa kake buk'ata wallahi zan tura maka a yau din nan in dai zaka bani labarin nan, Allah Yusuf in kaki fadamin jinina yana iya hawa kafin safe" "Oho in ka kashe kanka ai Jameela ce zatayi a Asara kaga kana mutuwa ni kuma zuwa zanyi in roki alfarma a matsayina na abokin ka a bani ita in aura basai an canza ranar auren da aka sanya ba, dan haka kama kanka Malam" Duk yanda musty yaso Yusuf ya bashi labarin wacece yaushe kuma abokin nasu ya fara soyayyar k'iyawa yayi har sukaje sallan suka fito, Wannan karan AK bai jira sun jera ba yayi gaba abunshi dan da gaske haushin wase yakeji, Ya daga fada mishi sirrin shi dan wulakanci zai wani zo ya nemi baza labarin shi a faranti yana tallah dashi. Sai da ya sake sabon wanka kafin kiran Musty ya same shi akan shifa suke jira ya shigo suci abunci suna sashen Hajiya, "Oh dama acan sashen Hajiyar kuka saba cin abunci ba anan ba? Ko koh tsabar son ayi munafunci na a bayan idona shi yasa kuka wuce can? Wallahi nidai ban yafe ba duk wanda yayi gulma na" "Ai sai kayi shegen mita kamar goyon mace kuma anyi gulmar naka kayi abunda zakayi, malam in zakazo muci abinci bismillah in kuma baka zuwa ma duk cikin ka tayi atoh" Ya k'arasa fad'a tareda tsinke wayar nashi, Hajiya, Meenal, Musty, Yusuf dukan su su hud'un zaune suke a kan dinning table din falon na Hajiya ko wanne da plate din abunci a gaban shi, sab'anin Meenal da nata plate din ke dauke da meat pie guda biyu sai lemun kunun aya mai sanyi data tsiyaya a cikin kofin tambulan tana cin meat pie din tare dashi, Doguwar riga ce a jikinta shigar datafi ta'amali dashi a koda yaushe sai dan kwalin rigar data daura shi akan nata ba tare da ta d'aure ba, Hira suke gudanarwa wanda kuma rabin hirar akan tsare tsaren bikin Musty ne wanda a yanzun bikin nashi ko wata biyu bai kaiba, Da sallama ya shigo d'akin kuma yanzun din ma dai kamar d'azun ta kofar bayan ya Kara biyowa ya shigo, Hajiya ce ta dago kai bayan sun amsa sallamar, "Wai kai Abdul wannan kofar ta kitchen itace kake so ka mayarmin da ita kofar shiga da fitar ka ko ya yah? Karfa kaga dan d'azun ka shigo tanan bance komai ba kayi zaton kyaleka nayi, Wannan ai salon ka nuna ma barayi hanya ne, ke tashi kije kisama kofar key ki kuma ciro key din ki kawo min nan sai inga ta inda zaibi kuma idan ya tashi fita" Shidai bai tankata ba har sai da ya samu kujera wacce take kallon kujerar da Meenal ke zauna yaja shima ya zauna, zaman nashi kuma yayi dai dai da mikewar Meenal taje ta kulle kofar ta kuma ciro key din kamar yanda hajiya ta buk'ata, Sai dai kuma tashin ta na zuwa da dawowa duk tayi sune idanuwan AK yana kanta dan itama dai sabon wanka tayi tadan feffesa turare kawai kuma sai zuciyar shi ke raya mishi cewa wai tayine saboda shi, kujimin wani kwala kai a faranti fa irin na jikan innan๐Ÿคจ. "Hajiya k'ofa dukan su sunan su kofa, dan na biyo ta nan kuma ai ba laifi bane tunda naga dai ni din ba bako bane" "Kace haka mana dama, amma ai a gaban idon ka d'azun ka firgita takwara kasa ta fara kiramin fatalwa ana zaune kalau" "To Kiyi hak'uri zan kiyaye" "Da dai yafi maka kam, ke kuma sai an rok'a ne kafin ki zuba mishi abuncin?" "Toni nasan wanda yake son cine hajiya? Kuma ai baice azuba mishi bama!" "Amma dai kin iya jin baki da neman magana inba haka ba har zaki kwana ki hantse a gidan nan sannan kice min wai baki san me zaici ba bayan kinga dukan mu anan tuwon muke ci in bake da shegen tsurfa ba da kika maida kanki wata iri bazaki zage kici abunci mai nauyi ba" Hannun shi ya mik'a ya dauki plate, "Kyaleta Hajiya zan zuba da kaina" Shiru sukayi kowa yaci gaba dacin abunda ke gaban shi har suka kammala, kafin suka dunguma suka koma falon na Hajiya yayinda Hajiya taci gaba daba Wase labarin gidan gonar su Yusuf din dake samaru wanda suke tayata kiwon nata dabobin. Musty ne ya jefo ma meenal tambaya da cewa, "Bestyn ki fa tace min ke suke jira batun cire anko wai tunda kika zo gidan nan baki zuwa ko ina daga makaranta sai gida shi yasa baku samu damar zuwa kasuwa ba" Mai makon Meenal ta bashi amsa sai Hajiya ne ta amsa mishi da cewa, To kai Musty ta ina macen dake iddah zan saketa sakaka ta kama yawo salon ubanta ya sani a bakin duniya, A'ah wallahi koma miye zasuyi su jin kirta har zuwa gaba kadan in kuma ya zama dole ita Jamilan basai suje ita da Maryam su fito da ankon ba, cire anko dai ba wata tsiya ba," "Hajiya kasuwa kawai fa zamu awa nawa ne mun siyo mun dawo?" Cewar Meenal. "Eh fa kasuwar koma minti daya ne nidai nace a'a dan dole inyi kaffa kaffa dan kar kiyi mamaki ace ubanki yana nan yasa masu kula mishi da shiga da fitan ki dan kinsan dole na mishi kike zaune a gidan nan badan yana so ba kamar wani shine yama yata nakudar ki" Cike da haushi ta tashi fuuuu kamar wata kububuwa ta haye sama tana turo baki, "Ai sai dai Kiyi ta fushin ki amma babu abunda zai canza in fad'a miki, aini kuma shi kenan na d'auko ma kaina jangwam magana daya biyu ki wani dunga turomin baki dan kaniyar ki, da dai ina zamana abuna baki na Alaikum yanzun banda halin in zauna shiru a cikin gidan nan sai dai in kina makaranta, ai dole ma Kiyi aure da wuri wallahi tun kafin a ganmu a rana a mana gwai Allah" Ita fa Meenal bawai saboda abunda Hajiya tace bane yasa ta wuce sama ah ah tadai tuna cewa bata da pad din da zata canza cikin dare ne dan a kayan data kwaso a gidan Sarki pad guda daya kawai ta gani, Dan haka koda ta shiga cikin dakin kudi taso d'aukowa domin ta fita shagon dake waje ta siyo saboda

Chapter 46 of 92