Share this page
aika, shi babban damuwar shi ma yanda duk suka wani kira abokan aikin shi dana kasuwancin shi suka fad'a musu maganar bikin yanzun haka zasu zo suga amarya wata yar ficika a wajen bayan kowa yasan tsarin shi. (Jama'ah Sarkin nan mafa dan rainin wayau ne ku fad'a mishi da babbar murya cewar muma auren dole za'a mana ba son shi mukeyi ba🙄). isowar su Moon sosai ya kara sa Meenal ta sake jikin ta suke abubuwan su ita da kawayen ta kullum kuma tana lissafin kwanakin da suka rage mata ta koma gida aci gaba da hidima da ita da yike ma ba wani shagalin biki za'ayi ba walima ce kawai aka shirya za'ayi su kuma sun shirya yin zaman yinin su a gidan su Meelat yanda zasu fi sakewa, Tun ranar da shedan ya nemi sa AK yayi abun kunya ya kama kanshi ya kiyaye duk abunda zai had'a shi da Meenal a cewar shi amarya tsautsayi gareta dan a yanda ya tara ta da yawa din nan yasan inya riketa tofa bazata sha ta dad'i ba a hannun shi, Sai dai a yan kwanakin sosai su Moon suka matsa mishi akan alkawarin wayar daya musu da dad'ewa akan in sun gama secondary zai siya musu manyan wayoyi dan so suke suci biki da wayoyin su a hannu yanda zasu samu daukar hotunan biki. Share Please #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦*DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ """""Page 30 Meenal kuzo muje Ya Ak yana kiran mu, d'ago kanta data d'aura akan pillow tana waya da D'an gidan Master tayi tana maida duban ta zuwa ga Moon dake maganar, "In kunje kuce mishi nayi bacci" ta fad'i hakan k'ara maida hankalin ta kan wayar da takeyi dan sosai takejin dad'in waya da Bash dan tsaf yake maida kanshi karamin yaro yayi ta biyema shirmen ta. " kutmelesi lallai nema Babin nan Kin ma isa kisa inyi k'arya! Wallahi inya tambaya cewa zanyi kince baki zuwa, Moon taso muje waya sani ma ko alkhairi ke kiran mu" Banza Meenal tayi da ita su kuma ganin hakan suka sa kai suka fice basu k'ara bi ta kanta ba. Tana nan a kwance tana ci gaba da wayar har suka dawo, da gudun besfa suka shigo d'akin suna ihun murna suka wani kankame ta suna cigaba da ihu, "Ke dallah ki yanke wayar nan haka, alkhairin Allah ya same mu da rana tsakar nan" Aisha ta fad'i hakan tana karb'e wayar Meenal d'in ta kashe ta gaba d'aya, "Ke miye haka bamu gama maganar da mukeyi ba fa kike kashe min waya dan Allah, Ni bani wayata kina ganin ina zaman zamana Bash yana neman ya kwanto min kurar da zata cinye ni har kasusuwa na" Babu wacce tabi takan abinda take cewa a cikin su sai ma kwalayen dake hannuwan su da suka mik'a mata a tare. Surprise suka had'a baki wajen fad'a cikin ihu. "Ke Beb please bar wannan zancen a gefe duba kiga abunda muka samo" cewar Aisha, bin kwalin wayar Meenal tayi da kallo a yayin da ta wuntsulo babu shiri zuwa inda suke " ke Sister kamar fa kwalin waya nike gani,ko idanuwa na ne basa gani da kyau?" Hannuwan ta bibbiyun ta mik'a ta karb'i kwalayen a hannun su, Aisha ce mai taya ta bud'ewa dan Moon gaba d'aya tsabar zumud'i yasa ko zama ta kasa murna kawai takeyi ji take tamkar ta lashi tafin kafarta tsabar dad'i, Bayan sun fidda wayar daga cikin kwalayen su kuwa haka suka dunga kallon wayoyin kamar wasu sabbin shiga, "Ke Moon wallahi wannan irin wayar dake hannun Aunty Sas ce, wooo mu yan mata muma mun faso gari, Allah dai ya k'ara arziki Mai Jama'a wallahi Ya'ya ya dad'e bai burgeni irin yau ba, ashe da rabon muma zamu rike babbar waya yar shafa" kashewa sukayi ita da Moon cike da farin ciki gefen Aisha Moon ta zauna, "ke Sister ai wallahi Ya AK dan aljannah ne kin san Allah dayace muzo cikina harya d'ura ruwa all my thought nayi zaton ko waccen mai zubin yan ruwan ta fad'a mishi tsokanarta da Meenal tayi d'azun ne shi yasa nike ta rara gefe, Allah dai yabar mana Yayan mu ya nuna mana ranar auren shi ku kwakw kwaso Alanta da shoki wallahi" "Kaiii.. wai ban fa gane ba ,ku tsaya mu nawa ne a wajen nan? " Meenal ta tambaya. "Uku" suka had'a baki wajen bata amsa. "To mu uku amma kuma naga wayoyin kwaya biyu kacal tawa wayar fa? " ta tambaya tana daure fuska, "nifa ban son halin wariya da nuna yan ubanci ya zai baku waya bai bada nawa ku kawomin ba?" "Dallah rufema mutane baki Malama ba saida mukace miki yana kiran muba? Fad'amin wani amsa kika bani ? cewa fa kikayi muce kinyi bacci, to badan halin kiba dai yace in kin tashi kije yana neman ki" "To aini da nace kuce ina baccin nayi zaton an kai mishi gulma nane, kunga karku kunna wayoyin bari inje in amso nawa in dawo, kuma Malamai bari inje in dawo in baku labari D'an gidan master zai ballo min ruwa wai zai tura iyayen shi wajen Malam a mishi tambayar aurena " "Tambaya? " suka had'a baki wajen furtawa suna masu zaro idanuwa waje, Moon ne ta kalli Aisha sannan ta d'aura da cewa "neman aure cikin neman aure kenan fa? Tab" Meenal batabi takan abunda Moon tace ba ta fice daga d'akin tana mai cewa bari taje ta dawo, har ta fita kuma ta dawo ta d'auko wani zumbulelen Hijjabin Aisha ta zumbula ta fice daga d'akin, Bayan fitar ta Aisha ne ta kalli Moon, "Waike mai yasa bakin ki bashi da kintsi ne? Yanzun da kikace neman aure cikin neman aure data fahimci wani abun kuma mai zakice mata? " Shiru Moon tayi ba tareda taba Aisha amsa ba sai can ta nisa kafin tace, "Aisha wallahi ina matuk'ar jin tausayin Meenal ban san ya zataji a yayinda batun auren ta kai tsaye zai isa zuwa gareta ba? karfin hali kawai nikeyi wajen danne harshe na amma ni banji dad'in da aka boye mata ba, auren mutum yau sauran kwanaki amma ace mutum bai sani ba! Kalli yanda take ta shirye shiryen ta hankali kwance, kina jin fa saurayin ma da take ikirarin tana so d'in ma ta kasa bashi daman zuwa gaban iyayen ta saboda ya nuna auren yake so da wuri" ta karasa fad'a hawaye na taruwa a idon ta, Matsowa kusa da ita Aisha tayi, "Moon duk yanda kikeji nima inajin kwatan kwacin hakan to amma ya zamuyi tunda iyayen mune suka zab'i su boye mata nasan suna da nasu dalilin nayin hakan, nidai Addu'a na Allah yasa mijin yana son ta nasan in shi yana son ta komai zaizo da sauk'i domin shi zaiyi k'ok'arin cusa mata soyayyar shi a hankali², kuma ai su dama gidan su kinsan da wuri ake musu aure sai dai gaskiya nima inajin tausayin Bash dan na lura kaf cikin samarin ta yafi sauran sonta itama kuma naga alamar kamar tana d'an son shi duk da dai kullum tana cewa bata wani son shi nasan karya takeyi. Amma dai kiyi hakuri ki rufa ma kanki asiri karkiyi katobaran da maganar auren nan Meenal zataji shi a bakin ki tunda har su Meelat suka kasa fad'a mata to kema kisa ido" Bayan fitowarta kai tsaye d'akin shi ta wuce dan tasan ba lallai ace harya koma majalisar shi ba dan tana lura bai fiye zama a wajen da rana fatse fatse ba, Jiyo karar TV yana aiki a falon hakan yasa dole sai da ta bud'e murya ta kwad'a sallama yanda zai jiyota, Daga ciki shi kuma bayan ya amsa Sallamar kana ya bata umarni akan ta shigo, Su uku ne a falon, Musty, Yusuf Wase, sai kuma shi Dan mai k'arfin, kamar wata ta Allah haka ta durkusa har kasa tana gaishe su kamar malamar islamiya, su dai sauran amsawa kawai sukayi ba tareda sun raya komai a cikin ran suba, shiko gogan k'are mata kallo kawai yakeyi da mamaki yau kuma bayan dogon hijjabin data aro harda wani gaisuwar munafunci kuma har k'asa. kai shifa yaga alamar shi kad'ai yarinyar nan ta raina ma wayau wato saboda tasan abun da ta aikata d'azun shine yanzun ta wani zo kamar wata ta Allah, to shidai bazai biye mata su zama d'aya ba. "Zauna mana kin ma mutane tsaye a Saman kai" ya fad'a yana mata nuni da kujerar dake gefen shi,waje ta nema ta zauna d'in kamar yanda ya buk'ata, "Ya Musty an gama mana d'inkin mu kuwa? Kasan gobe zan koma gida! " "Haba Bestyn mu kayan Amarya guda ai dole a had'a shi da wuri, Mai kyau bata fad'a miki nakai mata su wajen ta jiya bane? " "No bamuyi waya ba yau dan dama tace min yau bazata shigo nan ba sai da yamma" Katse su AK yayi da cewa. "Malam idan kana son magana da itane ka bari in sallameta tukun na, amma yanzun nina kirata! " Ba tareda Musty ya tanka abunda AK d'in yace ba, ya mik'e ya shige ciki yana cema Wase "Yusuf in zaka fita ka tasheni please". "Gani Ya'yan mu" tace jin shiru bai kara cewa komai ba. "Miye ma sunan ki? " Dagowa tayi ta kalle shi, Dan Allah jama'a inba neman magana ba kuji min wani tambaya fa, "Wai yauma ka k'ara manta sunan nawa? " Shiru yayi bai bata amsa ba, ita kuma dan a zauna lafiya burinta dai ya bata wayarta ta samu damar fecewa a d'akin in yaso sai ya ciji kanshi ma in yaso, hakan yasa ta bashi Amsa da cewa "Meenat, Meenal, Ameenatu yar Baba Malam" "Shekarun ki nawa? " "Saura kad'an in cika 17" Sai da ya d'ago idanuwan shi yayi mata kallon mintoci sannan yana ci gaba da kallon nata yace "mai ya had'aki da wacce tazo nema na d'azun har kika mata rashin kunya? " Saida ta wani d'auke kai tana hararar gefe sannan tace "to ba ita bace kawai zata wani shigoma mutane gida kai tsaye kamar gidan, su kuma kawai daga gani na kamar wata nid'in yar aiken ta ce zata wani cemin (Kee shiga ki kiramin Abdul) ta fad'i hakan tana kwaikwayon muryar Hafsan, To shine ni kuma nace mata ba ke ba sai dai Keke, to kawai daga nace haka shine zata wani tasomin tana min masifa harfa kamar zata rufeni da duka ta ringayi wai na mata rashin kunya ni kuma nace mata ai da bata baro gidan su tazo gidan su saurayi ba da nima ban ganta ba balle in mata rashin kunyan" Shiru tayi bayan takai nan a labarin da take bashi, jin ta tona ma kanta asiri, itafa matsalarta d'aya shine bata iya shirga karya ba, atoh gaskiyarta take fadi sai dai uban kowa ya mutu. "Uhummn ina jinki cigaba ai ba iya nan aka tsaya ba sai kuma kikace mata me inajin ki? " Shiru tayi tana rarraba idanu, "Kimin magana" ya fad'i hakan a yayin da ya d'auko kwalin wayar dake gefen shi wanda tunda ta shigo falon idon ta ke kan kwalin kuma tsaf yake ankare da ita, "Kinyi shiru ko iya abunda ya faru kenan? " "To ba ita bane tazo gidan mutane kuma ta kama musu masifa, in ma aikena zatayi ai sai tace min kanwata shiga ki kiramin Yayan ki Abdul in yana ciki,cikin lalama koba komai ai tunda ta haifeni ai bazan k'i zuwa ba, to ni kuma da naji haushi ne nace mata ai itama gashi nan ta zama tuzuruwa kullum tana yawon zuwa wajen saurayi bayan tasan ba auren ta zaiyi ba" Zumbur ta mik'e ta koma can bakin kofa, "Wallahi kika sake kika bar d'akin nan kin ma kanki" ya fad'i hakan a yayin da yake nunata da kwalin wayar hannun shi, bubbuga kafafuwan ta ta farayi a k'asa cike da shagwaba irin na sakakkun yara sannan tace "ai wannan d'aukar alhaki da jan raine in dai dan Allah zakama mutum abu ai basai ka tsaya ka fara tono tsofaffin laifukan da yayi maka ba, kuma dai ai koba komai Allah yana son mutum mai yafiya mai maida komai ba komai ba, kuma ni ai taimakon ta nayi dan Manson Allah S, A, W cewa yayi in kaga mutum yana aikata ba dai² ba ka fad'a mishi gaskiya in yaso ko baiyi amfani da abunda ka fad'a ba kai dai ka fita hakkin shi, kuma ai kowa yasan cewa ciwon y'a mace na y'a mace ne, itama inaga ta rasa mafad'a ne shi yasa basu fad'a mata cewar ta hakura dakai haka nan ba tunda dai kai ba auren ta zakayi ba. "Keee ni nace miki budurwa tace ita dama harda zakice min ba auren ta zanyi ba?" "Allah kuwa budurwar kane tunda itace kullum take zuwa wajen ka harma fad'a takeyi da sauran yan matan ka, nidai in saboda itane dan na fad'a mata gaskiya kake fushi to kayi hakuri " Yusuf wase dake zaune a falon tuntuni duk da hankalin shi yana kan film din da yake kallo a Tv amma tsaf kunnuwan shi yake Jiyo mishi tattaunawar da akeyi tsakanin AK da yarinyar data lissafo sunayen ta har guda hud'u kuma wai duka ita ke amsa sunayen ne yayi dariyar da har saida sautin dariyar tashi ta fito fili, lallai Allah da iko yake ashe yana raye zaiga ranar da wata d'iya zata iya fuskantar abokin shi irin haka gaba da gaba yana fadar magana tana maida mishi da amsa ba tareda tsoro ko fargaba a cikin muryar taba? Wacece wannan yarinyar da har AK ya zauna yake mata magana a hankali haka bada taratsi ko hargagin daya saba ba, Dan haka ya dago kanshi dan ya kare mata kallo, ga mamakin shi sai ya hango wata yar karamar yarinya wacce in ba karya idanuwan shi suke mishi ba kai tsaye zai iya cewa shi kamannin ta ma tsaf yake mishi kama dana abokin shi sai dai kawai dan ita mace ce, cire duban shi yayi daga kanta ya mayar kan fuskar AK dan ya kara tantancewa sai akayi sa'a suka had'a ido shima AK din kallon shi yakeyi, Gira d'aya Wase ya d'age ma AK alamun lafiya? "Dariyar me kakayi? " AK ya tambaya. "An hana dariya ne? " Shima ya maida mishi da tambaya maimakon ya bashi amsa, "Malam tashi kabar min falo ka wuce ciki! " "Kai harka ma isa kace in tashi, dan uban ka bakaga ina kallo bane? " "Kaje ciki kayi kallon" "Kai banfa zuwa ko ina wallahi anan nayi niyyar zama garama kayi ta kanka" Muryarta ne ya katse su yayin da, Ta kira sunan AK da wata irin shagwababbiyar murya "Ya Abdul" "Ai nace miki ki dawo ki zauna koh? " "Bazaka duke niba? " "Dama na tab'a dukan ki? " "Ah ah" "To zoki zauna" Sai da ta maida duban ta wajen Wase sannan tace "Abokin Yaya kana sheda yace bazai duke Niba koh?" Shima da yike miskilin ne bai iya amsa mata da baki ba illah kai daya gyad'a mata kawai yaci gaba da kallon shi ita kuma ta dawo ta zauna a kujerar dake kusa da AK sabanin d'azun data zauna nesa dashi sosai. "Yayan mu dan Allah kayi hakuri kaga ni gobe ma zan koma gidan mu in bar muku gidan ku" "Eh ki bar nan kuma kije gidan mijin shima kici gaba dayi mishi rashin kunyan da kika saba koh? Allah dai yasa baya duka dan zama dake in mutum nada saurin hannu wata rana saiya karya ki" Ba tareda ta bama abunda ya fad'a mahimmanci ba tace "kai Yayan mu Kannina su Raheenat nefa za'ama aure ni sai na gama makaranta" Maganar da tayi ne yasa ya tuna cewa ashefa duk wainar da toyawa a b'oye akeyi ita shashashar batama san wainar da ake toyawa ba, Allah sarki haka nan kuma sai yaji ya tausaya mata,yanzun ace shine za'ama irin auren nan yanaga ai sai yayi kanin mutuwa wallahi amma sai ya kauda maganar da cewa, "ki tabbatar kuma baki shigo kin d'auke min turare ba kafin kibar gidan nan" Dariya ta kyalkyale dashi irin dariyar dabai tab'a ganin tayi ba "Eh kin d'auka cewa ban san kece me d'auke min turare da shower gel d'ina ba? Kallon ki kawai nikeyi" "To kayi hakuri ni ai kamshin ne yake min dad'i ina son kamshin sosai" "Eh kina son kamshin amma bakya son mai turaren! " "Na'am" ta amsa dashi domin kasa² kwarai yayi maganar ta yanda ba kowa ne zai iya jiba. Paper bag d'in dake gefen shi ya d'auko sannan ya saka kwalin wayar dake hannun shi a ciki, "ga nawa gudun mawar bikin nan Allah ya bada zaman lafiya" ya fadi hakan yana mik'a mata, "In bud'e inga miye a ciki? " "Ah ah ki bari sai kinje ciki sai ki bude kinji" Harta yunkura zata fice daga falon ya kira sunan ta. " *AMMINA* " Juyowa tayi tana kallon shi har yanzun murmushinta mai kyau take aika mishi. "Kiyi hakuri da duk yanda rayuwa ta juya miki, karkice zakiyi fushi kik'i yin biyayya ma iyayen ki kinji? Allah ya baku zaman lafiya ki kula da kanki" Oho ita fa wallahi bata wani fahimci abunda ya fad'aba dan haka da ameen kawai ta amsa tana ficewa daga falon da sauri shima dai dan karta ruga da gudu ne yayi mata fad'a. Shiko da kallo ya bita jikin shi duk yayi sanyi, Dan yan kwanakin nan da yayi tareda ita a gida d'aya sosai yarinyar ta tsaya mishi a zuciya sosai yakejin tausayin ta, karamar yarinya da ita za'a tauye mata rayuwa, Mai da bayan shi yayi ya kwantar cikin kujeran yana mai sauke ajiyar zuciya, "ya dai? " wase ya tambaya "dai dai" shi kuma ya maida mishi da amsa. Sosai sukayi celebrating din samun sabbin waya k'arin dadi kuma gashi harda kyautar turare da wani set din d'an kunne da sarka mai kyau da Ak ya mata. Washe gari ranar da zata koma gida, bayan sun gama karyawa Rukayya ce ta shigo tace mata taje Baba Usman yana kiranta a falon shi, Ba tareda tunanin komai ba ta bi bayan Rukayyar dan zuwa amsa kiran, Duka Yayyan maman ta mazan su da matan duka ta samu a falon suna zazzaune kafin su iso falon tabbas hira taji suna tayi sai dai kuma tana shiga kowa sai yayi shiru aka rasa mai magana har saida ta fara gaishe su tukun na, bayan gaisuwa, Aunty Hassana ce ta kirata da cewa "Meenat My daughter zoki zauna anan kusa dani" dan haka can kusa da ita din Meenal ta zauna, Baba Usman ne ya fara magana kamar haka. "Mai sunan Hajiya kuma ya naga yau kin fi kullum fara'a ne kodan yau zaki gudu gidan ku kibar Takwarar taki? " Murmushi tayi "Baba ai na dade a gidan nan fa kuma ana ta shirin biki ni ina nan kuma jibi ne Daurin aurefa shi yasa zan tafi da wuri inje mu karasa shiri," "Ah lallai kam gara kiyi harama, Sai da yayi gyaran murya sannan ya d'aura da cewa "Meenal " "Na"am"ta amsa dashi. Shi kuma yace idan na tambayeki zaki bani amsa, " Sai da ta gyad'a kai sannan ta bud'e baki tace "eh Baba" "Yauwa d'iyar kirki, so nike ki fad'amin kaf fad'in duniyar nan wanene kike ganin yafi kowa sonki? " Ba tareda wani fargaba ba ta bashi amsa da cewa "Babana Malam sai Mommy da Baba Auta" "Masha Allah to kenan ashe wanda yake matukar kaunar ki kamar yanda Malam ke son ki zai iya yanke ko wani irin hukunci a rayuwar ki? " Wannan karan ma bata b'ata lokaci ba ta amsa da cewa " eh " "Yayi kyau amsar da nike son inji kenan dama a bakin ki, amma ina so in miki nasiha da cewa shi bawa bashi ke tsara rayuwar shi sannan ta tafi mashi a yanda yake soba, ina fatan duk abinda kikaji kuma gani a gidan ku idan kin koma bazaki bari yayi tasiri a cikin zuciyar ki ta yanda zaisa ki manta cewa su wadanda suka yanke wannan hukuncin akan ki sunfi kowa sonki ba, ina fatan ki d'auki abin a sannu kuma kiyima iyayen ki damu ma biyayya kinji, Allah ya miki albarkha" Duk da kasancewar ba komai take sawa a zuciyarta ba balle ya dameta ba amma dai wad'an nan kalaman na Baba Usman masu kama da gugar zana sun sa ta farajin wani iri a cikin jikin ta, shin kodai wani abu na faruwa ne wanda ita bata da masaniya? "Baba akwai wani abun da yake faruwa ne wanda ya kamata ace na sani kuma ban sani ba? " Ta tambaye shi da sanyin jiki, Bai iya bata amsa ba sai Dady Ahmad ne ya amsa mata da cewa ba komai mai sunan Hajiya tashi kije ki k'arasa shirin ki gaba d'aya zaku wuce dasu Momin ki can gidan naku, Bayan fitan ta haka sukaci gaba da tattaunawar su duk dai akan batun auren na Meenal. "Zuwa k'arfe nawa ne shi Mijin nata zaizo? " Dady Ahmad ya tambaya, "To jiya dai Mukhtar cemin yayi da safe zaizo" To Allah ya kawo shi lafiya bari in koma ciki akwai abinda nikeyi in sun k'araso sai amin magana. *** Koda 11 na safe ta buga su Meenal sun dad'e da isa Unguwan Malamai sai dai kuma saida ta sauke tarkacen ta a gidan su Meelat a cewarta ta dawo gidan su Meelat din kenan har sai an watse biki, Wani ikon Allah kuma sai gashi wannan karon sai ganin al'adarta tayi kawai babu ciwon marar kwata² hakan kuma ba karamin dad'i ya mata ba, a cewar ta zata sakata ta wala a bikin nan babu ciwon mara babu fargaban wanke make-up in zatayi sallah dan haka gayu Salamu Alaikum. Bayan ta huta a gidan su Meelat suna cikin shan hirar su misalin karfe 1 Maman Kano da wata mata d'aya daga cikin kannin Malam suka shigo gidan nasu Meelat a cewar su wai tunda aka fara biki basuga Meenal d'in ba shine sukazo tafiya da ita dan ga Amare can ana musu kunshi itama taje a mata, Babu yanda Meenal batayi dasu Moon akan suzo suje can gidan tare ba amma sukak'i acewar su taje kawai zasu zo daga baya dan Maryam ta kira musu wata Sadiya ita zata zo ta musu, Haka suka tasa keyarta har gida, tun a hanya duk wad'anda suka had'u dasu sai taji suna fad'in Amarya amarya ita dai bata damu ba in an kirata da sunan sai dai ta washe baki a zaton ta kila basu san cewa banda ita a cikin wad'anda za'a aurar bane. Sai dai kuma harta a cikin gidan nasu ma dake cike dam da baki na nesa dana kusa wadanda suka fara hallara nan dinma duk inda suka wuce suma dai amaryar kawai suke ta fad'i, sashen su taso ta fara wucewa bayan sun shigo domin su Maman kano sashen matan Malam suka wuce bayan sun ce mata in sun gaisa da Mamanta tazo ta same su a wajen innar su a mata kunshi, Da murnar ta ta shiga sassan nasu dan gidan fa ko ina masha Allah dan hatta da yaran gidan mata dake aure nesa duk sun iso mazan dake kasar waje ma duk sun dawo dan haka mai makon ta wuce wajen Mommy Hauwa sai ta juya akalarta zuwa inda Yayyenta sai da ta bisu duk sukayi gaisuwar yaushe gamo sannan ta karasa sashen su, tunda ta shigo take kwala kiran sunan Mommy Hauwa "Mommy! Mommy!! Mommy!!! Mommy na dawo" daga saman bene Mommy Hauwa ta amsa da cewa "eh aifa kin dawo kam dan inba keba babu mai kwalamin kira irin haka sai ke uwata" Ta fad'a tana murmushi domin dai ko ita tsayin kwanakin nan tayi kewar Meenal din ga kuma aure yanzun dazai d'auke mata ita saukin tama kusa da ita zata zauna, Da gudu Meenal ta haura sama tana jero ma Mommyn sunayen Yayyen ta wadanda suka gaisa yanzun

Chapter 26 of 92