mata, kai ina wannan ai sai dai aikin shed'anun wallahi,
Dan haka sai kawai ta maida hankali wajen karanto addu'o'in neman tsari daga shaid'anu kafin ta tub'e ta shiga makewayin ta yi kunna shower ta tsaya a k'arkashin ruwan sanyi tana ta k'ok'arin ganin ta ture tunanin nukan dake neman rikita mata kwalwa,
Ta dad'e a cikin bayin kafin tayi wanka ta fito,
Sai da ta fara tsane gashin kanta da ruwa yama jagab da towel duk da bawai ruwan jikin gashin nata ya tsane duka bane bata damuba tana fitowa gaban Mirror ta k'arasa tayi zaman shafan mai saida ta gama shafa man kafin ta taje gashin kan nata sama sama ta d'aure shi da jan ribom k'arami sannan ta mik'e ta k'arasa inda akwatin ta yake ta ciro wasu riga da wando masu fad'i sosai na bacci ta zura a jikinta kafinta fesa turare k'aramin hula ta d'aura akan nata,
Wayarta da tun shigowar ta cikin d'akin ta ajiye akan gadon ta d'auka dan yunwa takeji unin yau d'in bata wani saki jiki taci abinci a gidan rasuwa ba, tana ta tsumin sai sun fita sannan taci ma ranta abunda take so gashi shi wannan d'an iyan ya wani zo ya kejesu a cikin gida yasa an rufe mishi gate ta yanda bazasu samu damar fitan ba.
tunda dai yau Sarkin isa iko da mallaka mulkin nashi ya motsa yace bazasu fita ba to gara ta gama komai da wuri ta kwanta ta hutama ranta shi kuma idan yaso sai yaci kanshi,
Inyagan ta a arha yau ai gobe dai ba ganin ta zaiyi ba kuma daga ita har wancan mai shafar aljannun gidan zasu bari kowa yayi ta kanshi.
Koda ta fita wannan karan ba iya Hajiya da Sultana kad'ai bane a falon ah ah harda ma shi kanshi gogan shima ko kunya baiji ba ya wani dawo falon ya zauna cikin k'annin shi mata,
Tana fitowa falon bata kalli inda su Hajiya ke zaune ba kawai sai ta wani wuce su ta k'arasa inda shi gogan ke hakimce,
Tana zuwa bata jira komai ba ta mik'a hannun ta kamo nashi hannun ta kama janshi,
Ita nan a dole wai so take ta d'ago shi daga zaunen da yake ita nan ga yar mai k'arfi itama sai dai kuma duk yanda tasa k'arfin dan ta tadashi hakan ya gagara dan shima gogan zama yayi gingirim kamar wani gunki yana binta da kallo kuma baice mata komai ba,
"Kai Ya'ya wai dan Allah bazaka tashi ba kana ganin k'arfina sai k'arewa yakeyi๐ฃ" ta fad'a tana b'ata fuska kamar mai shirin fashewa da kuka.
"Me zan miki ne wai kike son damuna?"
"Kai yaya ka taso ka gani mana, ai kasan dai haka kawai bazan zo ince ka taso ba"
Mikewa yayi ita kuma taci gaba da jan hannun shi kamar wasu rak'umi da akala sai da suka gitta su Hajiya Sultana da magantu da cewa,
"Sister ina zaki kaishi kuma? yanzun nan fa na kirashi ya fito saboda muci abinci ke kad'aifa muke jira dama yanzun kuma kin fita kin janye shi kuna shirin komawa"
Sultana na saukewa Hajiya itama ta d'aura da cewa,
"Ah lallai kam, to da kika fito kike neman k'ara mai dashi cikin d'akin mai zai miki a ciki ne wai?"
"Uhmm nidai Hajiya ba ruwan ku ai takardun motana zamuje ya bani tunda gobe idan Allah ya kaimu idan muka fita da safe ba k'ara dawowa zamuyi ba,
To idan na manta ban k'arbi takardun ba kuma fa?
In ma abincin ne ku faraci kafin mu fito suma su Meelat ai naga basu gama ba balle su fito in kuma kunajin yunwa ne ai sai ku faraci ku biyun,"
Kamar da gayya haka tajashi fuuuu suka wuce ita ta bud'e kofar d'akin shi ta fara turashi ciki kafin tabi shi a baya,
Suna shiga ta nemi gefen gadon shi ta zauna tana wani irin cika tana batsewa,
Sai faman girgiza kafarta data d'aura d'aya kan d'aya takeyi, shiko tsayuwa yaci gaba dayi a gaban ta, shi bai zauna ba kuma bai tanka mata ba, dan bai sani ba ko laifin hanasu fitan ne yasa ta kawo shi d'aki take neman tsare shi saiya fad'a mata dalilin shi na hanasu fitan,
"Kambala'i wallahi da gaske yarinyar nan bata da hankali lallai nema, wannan ma ai rashin sanin darajar kaine kawai daga ganin mutum.... "
Kyacci tayi tama kasa k'arasa fad'ar me tayi niyyar cewa,
"Wai me ya sameki ne kuma?"
Ak ya tambaya ganin yanda take ta wani girgiza uwa wata mai shirin tada aljannu.
"Eh aima dole ka tambayeni mai yake faruwa,
Allah kuwa Taubashi ina fad'a maka inma asiri kake ma yan mata shi yasa da zarar sunyi ido biyu dakai suke kware maka gara ka ceci kanka ka karya asirin nan inba haka ba wallahi wata rana yan matan aljannu ne zasu fara bibiyar ka, haba dan Allah shikenan rayuwa kai da zarar kayi ido biyu da mace tun tafiya batayi nisa ba sai kaji zance yana neman canzawa"
"Mai yake faruwa ne nace?" Ya k'ara tambaya a karo na biyu,
"Ba kana kallo ba ita wancan bak'uwar dake kama da shafar aljannu to wallahi d'azun nan taje wajen Hajiya tana kuka take had'a Hajiyar da Allah da annabi akan tasa baki wai ita Sultanan ke son kafa,
Kuma harda cewa ma tayi wai inba kai ta aura ba bazata iya rayuwa dako wani mijin ba,
kaji fa, to tunda yanzun aka fara samun wacce ta iya tunkarar Hajiya gaba da gaba ba kunya bare tsoron Allah tace mata sonka take to tabbas zuwa gaba ma sai an samu wacce zatace kunyi auren sirri"
Da kallo yake ta binta jama'a ga abun dariya amma kuma ba halin darawan, juyawa yayi ya maida kanshi gefe a yayinda dariyar ta nemi kubuce mishi karamin dariya mara sauti yayi yana rufe bakin shi da hannu kafin ya juyo inda take ya k'arasa ya zauna,
"Wai ita wacece Sultanar?"
"Yarinyar Yayan Baba Auta cefa, a abuja suke zaune nima ba wani sanin ta nayi ba sai wannan zuwan da sukayi, waya sani ma ko lafiyar kwalwa ne bai isheta ba"
Ta fad'a tana tsatsare shi da ido tana jin me zaice kuma,
Ga mamaki ta wai sai gani tayi fuskar nan tashi dake kwana ta uni a d'aure tamau amma sai ya wani saki fuskar yana murmushin shi mai narkar da zuciyar mai kallo,
Giraren shi ya d'age kamar yanda ya saba indan zaiyi magana da ita yace,
"Ashe ma yar uwarki ce, shi yasa tun jiya dana ganta nima na kasa nutsuwar kamar yanda naga itama ta rikice taga yaro d'an sawalwalin yan mata,
To ashema abun zaizo da sauki tunda harta gani kuma ta yaba aini kuma babu wani zancen jan aji kawai kice mata na bada gari, ta turo manya kawai ayi batun sa rana dama nima na gaji da zaman tuzurancin nan haka, dama jira nike inji wata ta taya, bari ki gani inje in same su muyi magana baki da baki in a shirye take aini sharr wallahi kinga ko anan gidan saita fara zama kafin in kammala wancan koya kikace?"
Ya k'arasa fad'a yana kureta da kallo ganin yanda tayi tsaye kawai tana bin bakin shi dake motsi da kallo kamar wacce bata gane me yake cewa ba,
"Kaiii Wai kaima nan son nata kakeyi?๐"
Ta tambaya a shekek'e tana jiran ya bata amsa,
"To me zai hana bazan sota bayan ita dake mace ta kasa boye nata son da take min duk da irin kunyar da aka san mata dasu,
gata da kyanta masha Allah aini ban san duk wancan zazzafan gayun data d'auka dan ni tayi ba da tuni na yaba,
Amma kinga d'an bawan allah sai komawa gefe mayi Ina Satan kallon ta"
Fuuuu ta mik'e bayan ta cika bakinta da iska tana shirin ficewa daga cikin d'akin ya rik'o kafadunta ya dawo da ita cikin d'akin,
Baya ta juya mishi tana kunkuni take cewa,
"Ni ka kyaleni inyi tafiya ta, badai Sultana kake soba kaje ai sai kuyi ta soyayyar ku can in kunga dama ma kuna iya konewa ni ba ruwa na"
Juyo da ita yayi ita kuma sai kokarin kwacewa take ya hanata damar hakan,
"Kishi Taubashiya?
Fad'amin kishina kikeyi ne?"
"Allah ya kyauta to akan me zanyi wani kishin ka, bayan kai ba mijina ba komai ba"
"Kishina kikeyi Meenal ko ki yarda ko karki yarda"
"Ni bana wani kishin ka kawai dai ina fad'a maka gaskiya ne"
Ta fad'a tana murgud'a baki batareda ta dena jijjige jijjigen jikin da takeyi daga tsayen ba,
"Kina son kiji gaskiyar abunda yake cikin zuciyata Meenal?"
"Akwai wani gaskiyar ne bayan wanda ka furta yanzun cewar kana son Sultana?"
Itama ta maida mishi da tambaya tana kauda kai gefe,
"Akwai Meenal!
Akwai gaskiyar dana dad'e ina shakkar fad'a miki ita,
Gaskiyar da aduk sanda mayi yunk'urin furta miki sai zuciyata tayi nauyi sai kuma inga kin min kwarjini ta yanda nake rasa kwarin gwuiwata a gaban ki,"
Zagayawa yayi zuwa gefen data juya fuskarta yakai kafafuwar shi k'asa yana mai kamo tafukan hannayen ta cikin nashi,
"Meenal ina son ki yarda da duk wata kalmar da zakiji ta fito daga bakina a yanzun zuwa cikin kunnen ki,
Domin sakon dake d'auke cikin zuciyata ne nike son isar ma taki zuciyar,
Ke ba k'aramar yarinyar da nayi ta ririta soyayyar ta a shekarun baya bane balle ince zaki kasa gane kalamai na,"
"Kara riko hannun ta yayi da kyau jin tana mutsu mutsu tana son zare hannun daga rikon daya mata,
"Ina sonki Meenal,
Ina matuk'ar kaunar, ina so ki sani cewa da kaunarki nike kwana a cikin k'irjina haka kuma da ita nike tashi,
Ita wancan yarinyar cewa tayi bazata iya rayuwa da wani namijin ba sai nikoh?
To ki sani cewa ni kuma bazan iya kasancewa a raye da cikakkiyar lafiya aduk sanda na k'ara rasaki a karo na biyu a cikin wannan duniyar ba,"
Sakin hannunta guda d'aya yayi sai ya d'aura duka hannayen nashi biyu akan hannun ta na dama,
Sai da yakai hannun nata kan lab'b'anshi ya sakar mata wani kalar kiss mai tsotse jinin jiki ba tareda ya saki hannun ba duk da yanda yake ganin jikin ta na d'aukar karkarwa, yaci gaba da cewa,
"Ina son ki Meenal wallahi ina son ki sona gaskiya da gaskiya bawai so na wasa ba, ki taimaka ki amshi tayin soyayya ta ki kuma bani dama ni kuma in gabatar da kaina a wajen iyayen mu su aura minke in tashi daga matakin tuzurun da kika dad'e kina kirana zuwa mijin auren ki.
Misalin k'arfe 8 da mintoci Salman ya iso kofar gidan AK domin yau bai samu damar zama a can gidan rasuwar ba gashi kuma yana ta cema Meenal d'in zai zo Allah baiyi ba kuma yasan gobe idan har suka koma Zaria to wuyan gani zata mishi,
Bai manta kwatancen da Meelat ta mishi ba dan haka koda zai taso bai kirata a waya ba har saida ya iso kofar gidan ya nemi waje yayi parking.
Kiran wayanta da yayi,
Hakan yayi dai dai da lokacin da AK yake durk'ushe a gaban ta yana koro mata kalaman da suke tsotse mata ruwan jiki,
Da kyar ta samu ta sanya hannun ta guda da yake free ya zaro wayar daga aljuhun wandon jikin ta jikinta na karkarwa.
No editing ๐ฅณ
*Ummiee ce*โ๐ผ
[9/8, 2:20 PM] Ummiee Zaria: โ๏ธ๐ฑ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA*๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ๐ฑโ๏ธ
*BOOK 2*
*PAGE 22*
Batareda hannun ta ya dena rawa ba ta samu ta d'auki wayar ta dannata a speaker, shi kuma jin ta d'auka bayan yayi sallam dabai jira jin amsarta ba ya d'aura da cewa,
"Ranki ya dade gani a kofar gidan fa, Allah yamin isowa, hello! Hello!! Hello Meenal kina jina kuwa?"
Yayi ta maimaitawa jin tayi shiru bata amsa ba,
Hannu AK ya mik'a ya zare wayar dake cikin hannun nata ya yanke kiran kafin ya kashe wayar gaba d'aya,
Mikewa daga tsugunen da yake yayi sai ya kamo kafad'un ta da takufan hannayen shi ya k'arasa da ita gefen gadon shi ya zaunar, ita dai da ido kawai take bin shi kurrr ko kyaftawa bata son idon sunayi dan so take ta tantance shi d'in ne dai a gaban ta ko kuma wani shed'anin aljanine yayi suffa irin nashi dan taga alama yau gidan ruwan aljannu akeyi,
A k'asa inda kafafuwan ta suke ya nemi waje shima ya zauna bai yarda kuma ya saki sannayen ta ba yanzun d'in ma tafin hannun ta yana cikin nashi yana mamma tsa matasu yaci gaba da cewa,
"Karkiyi mamaki kokonto ko jin shakka akan dukan kalaman da zakiji daga gareni, I know that I am not perfect, niba kowa bane face d'an Adam wanda Allah kan iya jarabta a ko wani irin lokaci,
Ni ba d'an soyayya bane dan haka ban kasance cikin sahun mazaje masu wasa da zuciyar mata ba,
Na sani abu d'aya ke miki yawo akai shine yanda yan mata ke yawan bibiyata,
Sai dai ina so ki sani yakice su da nikeyi daga jikina hakan bawai yana nufin ina wulakanta su bane kawai saboda sun nuna suna sona,
Ah ah ita d'iya mace kaddara ce mai daraja, kasancewa ta namiji kuma bashine zai bani damar yin amfani da son da suke nuna min dan in wulakanta suba,
Domin ko da nike namiji ai ina da yayye da kuma k'anni mata kuma bazanji dad'i idan naga wani yana wulakanta min suba,
Wannan dalilin ne yasa duk mace da ta nuna min tana buk'atar kusanta kanta gareni ni kuma sai in nesanta kaina da ita,
Tarayya na tsakanin namiji da mace sun kasune kamar haka,
Kodai tarayya ta soyayya, ko kuma Abota na had'uwar jini ko kuma mummunar alaqar da addini ya haramta mana,
Idan naso zanyi amfani da damar makin da nike dashi akan su wajen bin son zuciya in shiga cikin rayuwar su in kuma yi amfani da son da suke min in cimma manufata ko wacce irice akan su batareda nasha wahala ba,
Amma kuma miye amfanin hakan wacce riba zanci idan na aikata hakan bayan a rubuce take cewa abunda kayi ma wani kaima shi za'a maka, ya zanji idan wani abu mara kyau ya faru da nawa ahalin?
Wannan dalilin shine yasa a kullum nike k'ara rik'e kaina nike kuma k'ara nesanta kaina dako wacce mace sai dai kuma ku dama sauran jama'a gurguwar fahimta kukamin a ganin ku kawai Ina amfani da damar da nike dashi ne wajen wulakanta mata,
Kun kasa hasaso cewa sufa matan ba nine nike gayyatar su zuwa duk inda nike ba, Kaini inda so samuna nane ace in rayu can wani wajen daban inda bazan dunga had'a ido da matan ba da hakan zaifi min saboda tsoron fad'awa halaka da nikeyi akoda yaushe,
Kin san meya canza ra'ayina akan mata?"
Ya tambaya a yayinda ya mik'a hannun shi ya gyara mata zaman gashinta daya zame daga cikin ribom d'in data d'aure shi ya maida mata shi ta gefen kunnenta,
Kafin ya d'anja hannun rigar shi ya fara tsane mata sauran ruwan da yake gangarowa daga cikin gashin ta yana Saukowa kan wuyanta,
Hannun ta ta mik'a ta rigo nashi saboda yanda takejin gab'obin jikin ta suna k'ara sanyayewa,
Saida ya shafa gefen fuskanta da tafin hannun shi kafin ya k'ara komawa gaban ta d'in yayi zaman d'alibi a gaban malamin shi kana ya d'aura da cewa,
"Kece macen da sonta ya fara narkamin dakakkiyar zuciyar da nike tak'amar cewa bata isa ta kamu da son kowata mace ba har sai wanda nid'in na duba naga ta cancanta,
Yes nasan na raina ajin mata saboda yanda suke bibiyata kullum kamar naman da aka kasa a mayanka,
Sai gashi kwatsam sonki yayi min shigar saurin ta yanda banyi zato ko tsammani ba,
Nayi zaton soyayya kamar karatu ne mataki mataki wanda za'a farashi daga k'aramin mataki zuwa matakin sakandire wanda in ka kaican kaike da damar zab'arma kanka hanyar da kake ganin zata bulle da kai,
Kodai ka d'auki fannin science ko kuma art,
Kin san me? "
Ya k'ara tambaya yana cigaba da binta da kallo ita d'ai ko motsin kwarai bata iyawa balle kuma ta samu kwarin gwuiwar amsa mishi,
Shima dai ganin bazata amsa d'inba sai kawai yaci gaba da cewa,
"Na dade ina hasaso kalar macen da zan nema aduk sanda na shirya fara gudanar da soyayya, ko sau daya ban tab'a hango kaina cewa wai ni ABDUL KHAREEM AHMAD MAI JAMA'A, zan k'are akan son k'aramar yarinya ba sai da zuciyata ta butulce min wajen nuna min isarta a kaina ta fad'a sonki da karfin tuwo,
Na d'auka cewa soyayyar kamar wasan kwaikwayo ne yanda kaso haka zaka tsara ka shiryata kuma ka gabatar,
Sai da na fara sonki na gane cewa ita soyyaya afkuwa kawai takeyi kai tsaye bawai mu ke k'irk'irarta ba, sai da nayi nisa a cikin soyayyar ki kafin na tabbatar da cewa zuciya tana da matsanan cin son kanta ita kawai ta samu wanda take so shi tafiso amma shi lokaci yafi adalci wanda ya cancanta shi yake bawa, kamar yanda abunda yake faruwa tsakanina dake,
Kinga a shekarun baya inda na furta miki kalmar so bana da tabbacin cewa ko zaki aminta sai dai kuma koda baki amince ba nasan zan samu goyon bayan mutane da dama wanda kuma hakan yana iya tab'a zumunci dan duka gefen biyu kowa zaiso ya gwada ikon da yake dashi ne a kanki,
Amma da yike shi lokaci yafi yima kowa adalci sai gashi lokacin yazo kuma komai ya warware batareda wani abu ya shiga tsakanin zumunci ba.
Meenal ki sani ko ina numfashi ko banayi bazan tab'acin amanar soyyaya ta dake ba.
Shin kinsan cewa duk yawan jama'ar mutanen danake mu'amalanta kad'an daga cikin sune suka samu kusanci da zuciyata?
Misali iyayena saboda ina samun kariya daga garesu, kema haka naji akanki tun daga sanda na gano kishin ki a kaina, tundaga sannan kuma ban k'ara tunanin kowacce mace ba saike,
Kawai a kullum burina shine na k'are rayuwata tareda ke a cikin shi,
Ki sani ko ki soni ko kada ki soni har abada bazan tab'a dena sonki zan k'ara mai maita miki a karo mara adadi cewa, ni AKA Mai Jama'a *INA SONKI*ยณ.
Meenal bana so na sakeyin saken da zaki kufcemin ki amince dani na miki alkawarin cewa bazakiyi dana sanin bani amanar kankiba,
Nayarda ko bakya sona wallahi zan zauna dake dan kaunar da nike miki kad'ai ta isa ta riqe auren mu,
Nidai kawai ki amince min akan kaunar da nike miki dan yardar ki kad'ai nike nema.
Ban tab'a sarewa ba dai dai dana sa'a guda tun ranar dana rasaki a kullum cikin addu'a nike idan har son da zuciyata ke miki alhairine a tsakanin mu allah ya tabbatar min dashi,
Sai gashi yanzun bayan shekararun da har na sare nafara cire raina akanki Allah ya k'arbi addu'ata ya dawo min dake cikin rayuwata,
Dan Allah karki sake jefa zuciyata a cikin quncin data rayu a ciki tsayin shekarun da kikayi nesa dani,
Ban sani ba ko k'ila a cikin zuciyar ki akwai wanda kikejin soyayyar shi, amma ni a wajena hakan bai isa yasamin linzami ba domin ko son wani bashi ne ba a soka shine muradin ko wani mai so, bazanyi gaggawa wajen sonjin ra'ayin ki a kaina ba,
Dole zan baki dama kije kiyi tunani akan hakan."
"Mik'ewa yayi tsaye sannan ya wuce gaba zuwa wajen k'aramin pridge din dake cikin d'akin ya ciro mata ruwan gora mara sanyi sosai kamar yasan tana buk'atar jik'a makoshin ta da takejin ya bushe mata qamas,
Sai da ya bud'e murfin goran sannan yakai hannushi guda daya ya tallafe kanta yakai mata ruwan a baki,
Sai da tasha kusan rabin goran sannan ya cire goran daga bakin ta ya maida kan nashi bakin ya shanye sauran, jefar da goran yayi anan tsakiyar d'akin ya kamo hannun ta,
"Muje kici abinci nasan mu suke jira tun d'azun"
Ya fad'a a yayinda yake cigaba da mata jagora da niyyar barin d'akin,
Abin takaici abin dariya da gudu yan gulman da suka lab'e daga bakin kofar d'akin suka bar wajen suka koma cikin falon ko wacce na neman wajen zama suka wani fuska suna kama wata hirar,
*Abinda ya faru bayan Meenak taja Ak zuwa d'akin kuwa shine*.......
Suna shigewa kusan a tare Maryam da Meelat suka fito Maryam daga kitchen ta kwaso sauran kayan abincin da bata gama kawowa kan dinning ba ita kuma Meelat sai yanzun ta gama shiri shi yasa ta fito,
Suna ganin sun shige duk sai suka dawo tsakar falon sukayi tsai-tsaye gulma na cin su sai dai kuma ganin Hajiya sai suka so su fuske,
"Ku kuma wannan tsayuwar zakarun damben da kukazo kuka min a tsakar kai na menene?"
Hajiya ta tambaya a yayinda take bin fuskokin su da kallo,
Dariya Sultana ta fashe dashi mara k'ara sosai tana nuna kofar d'akin na AK take cewa,
"Kunga abunda na fad'a muku koh? Wallahi da gaske itama tana son shi, ai naso ace kuna kusa d'azun kuga a yanda ta iya kai kanta d'aki da kyar"
"Ya akayi ne mutuniyar?"
Meelat ta tambayi sultanan tana dafa kafad'arta,
"Ke Beb dan Allah bamu musha wai ya akayi ne anci ancinye bamu da labari tun d'azun da naga kin d'au wanka naso inyi magana sai kuma dai na share"
Waje dukan su suka nema suka zauna akan 3sitter din da Hajiya ke zaune duk da kujerar ta musu kad'an basu damuba,
Tsaf Sultana ta shaida musu abunda ta fad'ama Hajiyan a gaban Meenal d'in tun kafin takai k'arshe suke dariya,
Hajiya ko da mamaki take kallon su sai can ta bud'e baki tace,
"Oh wai kuma kenan kun gane cewa shi Yayan naku son Meenal d'in yake?"
"Haba Hajiya waye ma zai zauna dasu yace bai fahimci komai dake gudana a cikin zukatan su ba!"inji Meelat,
Sultana kuma ta d'aura da cewa
" Wallahi itama son shi take Hajiya ba gashi ba dai yanzun kinga komai daya faru a gaban idon ki,
"To kenan ke da kikazo kina min kukan cewa kina son shi wannan d'in ma duk shirin kune a kansu ko ya abun yake?๐ค"
Hajiya ta tambaya cike da mamakin su ta yanda suka gudanar da komai gashi tun ba'aje ko ina ba su wad'anda aka ma gadar zaren sun fad'a,
"To wai yayan nan kenan kuna nufin wayau kuka fini shi yasa tuntuni ni na kasa zarge su waje d'aya ko yayane?"
"Ah Hajiya wane mu mu miki yawau kawai gani mukayi dukan su inba hakan aka musu ba bazasu fito fili su amayar da abunda ke cikin zukatan suba musamman ma dai shi da yakeyi kamar yana shakkarta wallahi,
Sad'af sad'af Sultana ta cire takalmin kafarta ta k'arasa bakin kofar d'akin AK d'in da turawa kawai Meenal tayi kuma bai wani rufu da kyau ba ta kafa kunne tana jiyo hirar dake gudana tsakanin AK da Meenal d'in ganin hakan ne kuma suma Maryam da Meelat suka rufa mata baya,
Basai ga Hajiya itama ta rashi tinkis tinkis tabi sahun suba,
Kaf hirar daya gudana tsakanin su a cikin kunnuwan su babu abunda basuji ba,
Hajiya ce ta fara komawa kan kujerar data dawo cike da Mamakin AK sai faman gyacci da gyad'a kai take saboda tsabar mamakin kalaman da kunnuwan ta sukajiyo mata sun fito daga bakin AK din,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 60 Chapter of 92