Share this page
wajen shiba, ni kuma sai aka k'ak'aba min shi duk da nasan kawata na son shi amma babu yanda na iya, kasan har hakuri saida ta bani akan cewa da tasan cewa shine zai zama mijina da bazata tab'a yarda ta furta tana son shiba, kuma lokacin da nike gidan shi bata tab'a zuwa gidan sai baya nan saboda bata son su had'u shi yasa ni kuma da muka rabu ya rok'eni in fad'a mishi abunda nike so sai na bashi hoton ta da address dinta harma da number ta akan cewa idan yaji yana sonta ya neme ta to kaga ashe ya nemeta har sun sasanta kansu shine zai kawo ta in warware mata dan nasan dole ko ba komai zataji wani iri kar ace tana soyayya da mijin daya rabu da kawarta" "Amma dake da ita duk yarinta ke damun ku" AK ya fad'a yana tab'e baki, "Kai ya'ya yarinta kuma? Halacci dai nayi mata dan bashi da mugun halin da za'akishi" "Wacece ita hala?" Kauda kanta gefe tayi, "ai idan na fad'a maka fad'a zakayi tunda gashi yanzun ma kace wai yarinta ke damun mu" "Waye yace miki zanyi fad'a nid'in? Ai nima nasan zafin soyayya yanzun dan haka bazanga laifin kuba dukan ku, ke abunda kikayi kin kyauta shi kuma Allah yasa yasota da gaskiya har cikin zuciyar shi kar yayi mata kallon macen da aka cusa mishi kamar dai yanda ya miki" "Ah ah bazaiyi haka ba insha Allah," "Wacece nace ko bazaki fad'amin nima in goya muku baya ba?" "Moon" "Kina nufin Maimoon dai na Baba Usman?" "Eh" girgiza kai yayi kafin yace "allah ya shirye ku yaran nan ashe kun dad'e da k'onewa an kara ne kawai babu wanda yayi a cikin mu" "Kai dan Allah waima konewa, nidai dan Allah kasa baki a maganar nan nasan idan Hajiya ta amince dole kowa ya yarda kaji?" "Ke wai mutumin da ba'a tabbatar da lafiyan shi bane zaki had'ashi aure da yar uwar ki?" "Lafiyan shi kalau mana waye yace maka bashi da lafiya ne?" "Oh lafiyar ce kenen yasa yayi ta kallon ki uwa hoto..... "Katse maganar yayi bai k'arasa ba itama kuma sai kawai ta basar, Sukaci gaba da hira tana mishi magiya akan dan Allah yasa baki Hajiya ta amince, *** A unguwar malamai ko Sarki yana isowa Zaria ya kira Moon a waya cewa ya shigo tana ina ne? Yanke wayar tayi sai ta tura mishi text cewa tana gidan su Meelat amma yanzun zata ajiye Maryam a gida dan motar meenal wanda shi Sarkin ya bata tana hannun Moon d'in da ita suketa zirga zirga ita da Sultana, idan ta ajiye Maryam zata kira shi sai ya fad'a mata inda zata same shi dan gaskiya a tsorace take bata son wani ya gansu a tare, Bayan ta sauke maryam a gida ta juyo a k'ofar gidan shi ta sameshi shima a cikin nashi motar kamar yanda yace mata zai jirata a wajen, bata fito daga motar ba ya kunna nashi motar yayi gaba ita kuma ta dunga binshi a baya har suka fita daga cikin unguwar suka kama hanyar tudun wada, horn ta dunga danna mishi tana son ya tsaya dan tana son taji ina zai kaita badai gidan Hajiya ba amma ya shareta ta kira shi a waya yana d'auka sai cewa yayi ta kwantar da hankalin ta tabiyo shi suje kawai, Ita dai a babu yanda zatayi ne ta dunga binshi kila ya lura da tana cikin furgici shi yasa ya canza hanya ba wanda ita ta sani yabi ba kafin ta ankara dai kawai tagan su a bakin gate d'in gidan Hajiya ne bai tsaya a waje ba horn yayi aka bude mishi gate ganin motar Meenal a bayan nashi ne kuma yasa su Isah basu tambaye shi wajen wa yazo ba tunda tare yake da yar gida, A harabar gidan dukan su suka nemi waje suka faka shine ya fara kashe tashi motar ya fito ya koma motar da Moon ke ciki dan ta kasa kashe motar balle ta fito, Sak'e² kawai takeyi, me Sarki yakeyi haka da zai jawota suzo gidan nan bayan yasan Meenal tana nan, gefen mai zaman banza ya bud'e ya shiga ya zauna, "Hajiyata idonki kenan, to barka da dare ya gajiyar hidin dimu ai da nace to Sarki kuma laifin me yayi tunda gimbiyar shi ta baro kudu zuwa arewa babu kira ba sak'o? Ashe dai ina da sauran gata ba'a manta dani ba, Karki damu kanki cewa zakiyi wani dogon tunani akan dalilin zuwan mu nan, dafarko dai nazo gaisheda Hajiya ne ina kuma son gabatar da kaina a gaban ta kafin Allah yayi ma su Baba Usman isowa gobe, na biyu kuma nazo ganin kanwata ce ina son kuma tasa baki ko zaki yarda da batun neman aurena a wajen ki ki yarda cewa ba yaudaran ki zanyi ba nasan duk wannan nuku²n da kikeyi saboda Meenal kikeyi abunda baki sani ba shine da yardar Meenal na kawo kaina gaban ki, sai da na fara rokon alfarma a wajen ta akan tamin hanyar yanda zan sameki tunda nidai ina sonki kuma addini bai haramta aure a tsakanin muba ita tabani number address dama sauran bayanai a kanki dan haka kima dena damun kanki da zaton ko kinci amana ko wani abun makamancin haka nine nan na ganki ina so ba cusa min ke akayi ba" (Ku gane Sarki ya boye mata gaskiya ne saboda kartaji ba dad'i, bawai da wani nufin daban ya juya labarin ba) "Ina fatan cewa yanzun da kikaji gaskiyar komai bazaki k'ara hanani gabatar da kaina ko kuma kici gaba da boye soyayyar muba?" D'ago kanta tayi ta kalle shi, "dama Meenal tasan komai?" "Eh ta sani" "To amma bata nuna min tasani ba" "Saboda bata son kiji babu dad'i shi yasa" "To ya akayi kasan su Baba zasu iso gobe?" "Saboda na riga na gabatar da kaina tun a Lagos yanzun haka Abban ku na Saudia ake jira yana isowa komai zai kammala ina fatan kinyi farin ciki dajin hakan?" Kafafuwan ta ta cusa a tsakanin cinyoyin ta tana boyewa murmushi kwance a fuskarta, "Oh kunyana kike ji yanzun kuma, to bari kiji nidai gaskiya bazan yarda aja lokaci mai tsayi ba dan ina bukatar matata, sannan kuma zakiyi hak'uri dan idan Allah ya nufa an d'aura auren bazaki zauna a Lagos ba Kaduna zaki zauna tare da uwar gidan ki da yaranta bazan hanaki aiki ba sai dai ina fatan aikin ki bazai sa ki gaza samun lokacin da zaki bani kulawar daya dace ba?" Shiru tayi bata amsa mishi ba, Wayar shi ya ciro ya kara kiran Meenal ya shaida mata cewa suna harabar gidan, "Ya'ya sun iso" take fad'ama AK, "Ai naji isowar su tun d'azun kuma nace miki ki dena kirana ya'ya koh" "To da wani sunan zan kiraka?" "Jeki shigo dashi zamu zab'i sunan daga baya" "To muje tare" Tare suka fita tunda suka fito kuma AK ya kama hannun Meenal din ya runtse cikin nashi tayi tayi ya sake mata hannu yak'i, "Oh ke bakya son shima ya gane cewa kema kin samu mijin aure ne?" Koda suka isa hannu AK da Sarki suka ba juna sukayi musabaha ko wannen su fuska kadaran kadahan babu fushi kuma babu sakewa, a can gefe Moon ta lab'e dan daga AK har Meenal din kunyar su takeji wallahi, AK ne ya musu jagora har falon na Hajiya suna shiga kuma Moon ta gudu sama Meenal kuma ta take mata baya tana tsokanarta da cewa ai dama ta fad'a mata cewa koma miye take boyewa idan tayi wari zasuji, "Da gaske dai ashe kaine sirikin nawa?" AK ya fad'a bayan sun zauna, Karamin dariya shima Sarki yayi kafin ya maida mishi martani da cewa, "Kamar yanda kaima gashi da gaske naga alaman kana shirin zama sirikina, ko ka manta ita Meenal din kanwata ce, kaga kenan komai yazo da sauk'i sai muyi bani mandaqo in baka Manda kai anan kaine zaka jagoranci zamowana siriki a gidan ni kuma sai in maka jagoranci nima a gidan mu kaga komai ya tafi dai dai kenan" Dariya AK yayi kafin yace "ina fatan dai ka shirya fuskantar Hajiya gaba da gaba koh? Dan kasan itace boss gaka kuma jami'in tsaro balle ince ka bata cin hanci dan ina fad'a maka matar nan yar rashawa ce" Dariya Sarki "karkaji komai na riga na shirya fuskantar kowa dama qalubalen daga kanwar kace itama nasan yanzun kam na gama da gefen ta," "To ai ba laifi indai ka shirya to nidai na baka dan koni ina iya aurar maka da ita"'cewar AK, "Allah ko mutumina? To in haka ne nima na baka uwar Malam a matsayina na Babban yayan ta ka fito kawai idan ka shirya" Sarki ya fad'a yana bashi hannu suka kashe, Sultana ce ta sauko kasan ita nan a dole wai kitchen zataje alhalin kuma tsabar gulma ne ya fiddo ta Sarki take son gani dan labarin shi kawai takeji yau kuma gashi yazo har gida ina zata yarda wannan damar ta wuce ta bata sauko sun gaisa ba, "Yauwa Sultana koma saman nan dan Allah kice ma Hajiya tayi bak'o" "To" ta amsa dashi kafin ta mik'ama Sarki gaisuwa bayan ta k'are mishi kallo, juyawa tayi zuwa d'akin na Hajiya da Sallama ta bud'e k'ofar ta shiga, "Me kuma ya faru na dawo d'akin ma bazaku barni in huta ba sai kun biyoni" "Allah dai ya baki hakuri Hajiya dama Mai Jama'a ne yace in kiraki kinyi bak'o yana falo yana jiran ki, kamar dai saurayin Moon ne yazo gaishe ki dan tare da ita suke" tana gama fad'a mata ta fice daga d'akin, Ita kuma Hajiya jin cewa saurayin Moon shi yasa bata b'ata lokaci ba ta ziro hijabi ta fito ita dai Allah ya sani tana matukar so taga ta aurar da jikokin nan nata, shi wannan din da yazo in dagaske ne ai dama kawai zata bashi ya turo iyayen shi ayi a wuce wajen dan dama ita Batama Moon din sha'awar auren Lagos, Batayi saurin gane ko waye a falon ba har saida ta sauko ta nemi wajen zama ta zauna shi kuma sarki tana zama sai ya zamo daga kan kujerar shi ya fara gaishe ta, Lafiya lau suka gaisa sai da ya koma ya zauna ta kare mishi kallo da kyau kafin ta maida kallonta kan AK " kai Abdul nace wannan kamar d'an gidan uwar gida ko? Ina nufin tsohon mijin Meenal koba shi bane? To me kuma ya kawo shi nan? Nidai Sultana cemin tayi Saurayin Maimunatu ne yazo gaishe ni koshi wancan d'in ya wuce ne?. *Ummiee ce* [9/30, 10:51 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 39* D'aure fuska AK yayi dan karma Hajiya taga fuskar shi sakwa² ta d'auki maganar su shiririta dan yasan halinta tsaf tana iya daga shi har Sarkin ta musu fatattakar kare, amsa mata yayi da cewa, "Eh shi d'in ne dai wanda kika hasaso kuma babu wani wanda ya wuce shine dai, tareda Moon d'in suka zo nan koma menene tsakanin su ai zakiji daga bakin shi tunda dai gashi yazo," "Kai d'an nan kar kayi fushi kaji, karkaji nace mai ya kawo ka nan kayi zaton ko da wani nufi na fad'i hakan, ah ah wallahi kai kam ai ka zama d'an gida zuwan daren nedai ya bani mamaki, dan nasan ba sabon ka bane, to Barka da zuwa fa ya wajen iyalin naka da ita uwar gidan kuna dai lafiya koh? ance ma kayi sabon gida dan haka, ka dawo nan Kaduna gaba d'aya kaida iyalin taka to Allah ya sanya alkhairi yasa anyiwa wayan raine, allah kuma ya k'ara arziki a kuma cigaba da kiyaye addu'a sai kaga kofofin arziki suna ta budewa wallahi" "Ameen ya rabbi Nagode kwarai Hajiya kowa lafiya lafiya Allah kuma ya k'ara miki lafiya kema" Sarki ya amsa dashi kanshi a k'asa, "To ameen dai madallah ina fatan dai lafiya dan nayi mamakin ganin ka?" Hannun shi yakai bayan k'eya yana gyara zaman hular dake kanshi kafin ya d'an k'ara sassauta murya duk da muryar tashi bata rik'uwa yace, "dama Hajiya nazo gaisheki ne" "Kai madallah aiko ka kyauta nagode da gaisuwa Allah dai yayi albarka kaji, Gashi kuma kayi min zuwan dare amma dai nagode wanda ya biyoka har gida ya gaisheka ko bai kawo maka komai ba ai ya kula da kai, toni zan shige daga ciki ka gaisheda gida" Ta yunk'ura da niyyar tashi AK ya tsaida ita inda yake cewa, "Hajiya zuwan nan da yayi fa wajen ki yazo dan iri ya gani a gidan ki ya biyo, kuma ni a matsayina na yaron gidan babba munyi magana dashi harma na bashi sa Albarkan ki dai muke nema yanzun Hajjaju" Komawa tayi ta zauna tana maida kallonta kan AK dake magana, "Kasan nifa idan mutum zaiyi magana dani nafi gane ya fito kai tsaye ya fayyace min komai bana gane nuku² da kananun munafunci, yo fadama gareni a cikin gidan balle ace ina noman rani da za'azo neman iri a wajena?... " Katseta ya k'arayi da cewa "amma Hajiya aikema kince Sultana ta fad'a miki cewa saurayin Moon ne yazo koh" "Kai dakata min dan Allah,ina ce koda na fito ku biyu na cimma zaune anan d'in shifa wannan d'in da kakeji da gani shine dai tsohon mijin Aminatu ko baka ganeshi da kyau bane ko kuma dai kallon tsoro ka mishi? Ina had'in tsohon mijin Aminatu kuma da Moon wacce ke can kudu?ina ga dai a hanya suka had'u shi kuma ya rage mata hanya zuwa nan gidan kasan kuma ita Sultanan ba sanin shi tayi ba shi yasa tace haka inba hakaba Wannan ma ai ba zancen da kai zai d'auka bane abu dai kamar muna garin da ba'a sallah" K'ara d'aure fuska AK yayi jin Hajiya tana neman jagwalgwala maganar, da hausa fa yayi magana da ita bada wani yaren ba balle tace bata gane me yake cewa ba, shi kuma Sarki sai wani k'ara nok'e kai yake, "Hajiya koma dai garin suwa muke shi dai d'in da kike gani yau yazo gidan nan ne dan ya gaishe da kakar budurwar da yake nema ya kuma gabatar miki da kanshi a matsayin mai neman auren jikar ki, Kai kuma ka wani zauna kayi shiru ni kad'ai zan maka yak'in neman auren ne?" Dif ruwan kan Hajiya ya d'auke dan Wallahi ita dai a cikin kalaman da AK yayi babu guda d'aya wanda zata iya cewa ta fahimci abunda yake nufi, Kuji wani hauka fa wai cewa yake shi Sarkin ne wai saurayin moon to wannan batu ai sai dai a garin mahaukata wallahi, "Tuf tuf tuf" ta tofar da miyau daga bakin ta, "Kai dai kana da bak'ar d'abia wallahi Abdul, wacce magana ce kake fad'a haka irin ta masu shaye shaye?, Shi Sarkin shine yace maka son Moon yake ko koh ah ah kaine da iya tsara zance ka tsara jawaban ka dan kawai ka mai dani wata abokiyar wasar ka, to wallahi ka fita idona tun wuri in rufe, ya mutum zaizo har gida dan ya gaishe ni da girman ka da komai sai kawai ka wani tak'ark'are ka dunga sheqa mishi k'arya, Kai kuma wallahi ka daiji kunya dirkeken soja dakai ka zauna kana jin yana sheko k'arya akan ka baka zage kwanji ka wauwanke mishi fuska da mari ba aikin banza kawai" Gyara zama Sarki yayi duk da yanda yaga Hajiya tana kumfar baki hakan bai sare mishi gwuiwa ba, domin dai tunda har ya iya kawo kanshi ba wani can da ban bane ya kawo mata zancen to gara ayi wacce za'ayi kawai, dan haka sai ya zamo daga kan kujerar da yake zaune bayan ya zame hular kanshi ya ajiyeta a gefe, bai yarda ya kalli fuskar hajiya ba ya fara magana, "Hajiya kiyi hakuri ban sani ba ko har yanzun a mai laifin daya aurar miki jika ya saka kike kallona, bazanga laifin kiba in kin kalleni a matsayin mai lefin sai dai ina mai k'ara baki hakuri abunda ya faru tsakanina da Meenal ya riga ya faru ya wuce, aure ne Allah ya kaddara a tsakanin mu a cikin zaman mu kuma sai Allah yasanya hijabi a tsakanin mu, tun kafin in san zan auri Meenal nakejin soyayyar yar uwarta a cikin zuciya ta, ban bayyana bane a wancan lokacin saboda nayi duba da k'aracin shekarun su ko secondary school basu gama ba, Allah ya sani ban tab'a kallon Meenal da fuskar soyayya ba a tsayin zamana da ita, rashin sonta kuma bai sa na cutar da ita ba, nasan zaki fassara abin ta fuskar cewa kusancin yayi yawa na auri Meenal yanzun kuma ince ina son Moon saboda dangar takar iyayen su da suke uwa d'aya uba d'aya amma Hajiya a addinan ce hakan ba haramun bane....." Hannu Hajiya ta d'aga mishi alamun dakatar wa, "Eh kawai haka mutane ke cewa ba haramun bane amma mu hausawa cewa mukayi ana barin halas kodan kunya kuma wata kusar tafi wata, dab haka in ma dai wannan shirmen ne yasa ka kwaso jiki da tsakar daren nan uwa mafatauci ka duro min gida tattara maza maza ka koma inda ka fito, idan a dangin ku kun saba kwamacala ni anan gidan baza'ayi min ba, yo ita Moon din hauka takeyi ma da zata yarda harta kulaka kana matsayin tsohon mijin yar uwarta sune fa sukayi ma Meenal din yan matanci a matsayin kawayen amarya, yo wannan abi idan ya tabbata kuma ai sai a buga mu a jarida wallahi ace ka auri yar mace ka saki ka koma kan yar namiji," K'ara gyara zama yayi ko gezau bai nuna alamun mikewa ba balle tasa ran zai bar mata falon, Sultana wacce tun d'azun take zaune akan dinning domin bayan ta kira Hajiyar data sauko kitchen ta shiga ta zubo abinci ta zauna tanaci, biyu ta raba hankalinta d'aya akan abincin da take ci d'aya kuma tana k'arewa Sarki kallo tana kuma sauraren hirar dake gudana a falon, Ko ita fa maganar yayi mata wani iri, taya ma zaka auri k'awa ka saki sannan kuma kace zaka auri aminiyar ta wannan abun baiyi ba sam koda ko ace babu dangan taka na jini a tsakanin su balle kuma tsakanin Moon da Meenal kai gaskiya kusancin yayi yawa ko ita bazata goyi baya ba dan hakan yana iya shafar zumunci, tututura abincin tayi ta maida plate din kitchen ta wuto da niyyar haurawa sama ne Hajiya ta tsaida ta, "Ke Sultana haura maza kiyi min kiran Moon ta sauko yanzun ina son magana da ita dan bazasu mai dani wata sakarya ba ita Moon din har idonta yayi budewar da zata zagaye taje tana soyayya da tsohon mijin yar uwarta" "Hajiya me yasa kike so dole dai sai kin tadama kanki hankali ne wai? Miye na damuwa a cikin maganar nan naga dai AUREN nan ba wai ya haramta bane, amma sai tada jijiyoyin wuya kikeyi idan ita yarinyar tana son shi zaki hanata abunda take so ne?" "Kwarai zan hanata dan ko ban isa da itaba na isa da ubanta" ta amsa dashi tana huci, "Hajiya dan Allah kiyi hakuri wallahi ba yanda kike tsammani bane, da zuciya d'aya nike son Maimoon kuma nayi alkawarin zan kula da ita zan riketa amana idan kuka bani auren ta dan ina sonta" "Ita waccan da aka aura maka da farko meya hanaka kulawa da ita ka riketa amanan? Ita data kasance maka zab'in uwama kayi fatali da ita ka kai gida ka jirgeta uwa majigi shine zaka k'ara sad'ad'owa ido babu kunya kace wata jikar nawa kake so, wato ni gani Hajiyar mahaukata ni kuma sai in goya maka baya to baka isa ba har yanzun rass nike lissafina bai goceba," Su ukun suka sauko Maimoon Meenal sai Sultana a bayan su, kuka mara sauti moon takeyi Meenal ke bata hakuri da cewa tabar kukan tana kuma share mata hawaye har suka sauko k'asan, Tun kafin su nemi waje zama hajiya ta kaida tambayoyin ta kan Moon d'in, "Ke bar kukan munafuncin naki dan bazai fishsheki ba kizo ki fad'amin uban meye tsakanin ki da tsohon mijin yar uwar ki, Maimoon ashe har zaki iya zagayewa dan cin amana kije kina soyayya da mijin daya maida miki yar uwa k'aramar bazawara sai yau da tsakar daren nan saboda tsabar kun shahara wato kun riga kun gama kulla tuggun ku shine ya wani kwaso min ke kukazo min gida zai wani ce wai yazo gaisheni da kuma rok'on iri, to ba iri ba yabanya ma taci buhun ubanta, ido ba kunya kika kwaso shi kuka yimin saukar dare alhalin ko sanda yana auren yar uwarki gata nan nidai ba zuwa min gida yakeyi ba, Ke kuma da kika wani kwakumeta a jikin ki wani irin rashin sanin ciwon kaine wannan amanar ki taci fa ta koma tana tarayya da tsohon mijin ki duk bamu da labari... " "Hajiya dan Allah kiyi hakuri ki dena fad'ar nan haka dare nefa, amma sai faman fad'a kikeyi kuma ai ban ce miki bani da masaniya akan abunda yake faruwa ba, nasan kuma kuma nice ma na bashi number waya da adireshin gidan su moon d'in acan Lagos yaje ya sameta" "La'ilaha illallahu muhammadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam³" hajiya ta dunga maimaita tana tafa hannuwa cike da jimami da mamaki duka a lokaci d'aya, "Yanzun nan ke yar gidan Jidda Ashe rashin sanin ciwon kan naki har yakai can, ace miji ya sake ki wai kuma harya dawo ya miki dadin bakin cewa yar uwarki yake so ke kuma saboda rashin sanin ciwon kai kika d'auki number da adireshin ta kika bashi, To ke Moon dama can son nashi kema kikeyi koh shi yasa koda yaje kika amshe shi hannu bibbiyu?" "Ah ah Hajiya wallahi gashi nan koshi zai fad'a miki gaskiya tun sanda yazo wajena ni ban bashi fuska ba shine dai ya nace kuma koda na fad'ama Umma itama cewa tayi in rabu dashi bata bani goyon baya ba, shi yasama koda yace zai tura ni kuma na hanashi turawa saboda ban san da wani idon zan kalli mutane ba wallahi Allah Hajiya ko yanzun ban san cewa nan gidan zai kawo muba da bazan biye mishi muzo tare ba dan Allah kiyi hakuri Hajiya"ta k'arasa fad'a a yayinda ta durkushe a wajen tana kuka, "Maimoon" AK ya kira sunan ta a dake, Bata iya amsawa ba saboda tsoron daya rufeta dan tasan kila shima kallon yar cin amana zaiyi mata, "Waiba sunan ki na kira bane da bazaki iya amsawa ba, taso ki dawo nan kusa dani tambayar ki zanyi" ya fad'a a tsawace, Da rarrafe ta k'ara inda yake hawaye dama² a fuskarta, "Kina son Sarki?" Dan dago kanta tayi kad'an ta saci kallon hajiya wacce ba ita kad'ai ba dukan su Moon d'in suke kallo sai dai ita kuma mai makon ta bashi amsa ah ah sai kawai ta maida kanta k'asa ta fashe da kuka mai k'aramin sauti irin mai fitowa daga cikin zuciyar nan, Ita taya zata iya amsa cewa eh tana son shi bayan ga Hajiya nan ta kafa ta tsare akan bata yarda da zancen auren ba, Batajin ta Meenal domin a zaman da sukayi ita da Meenal a cikin d'akin zancen da suka tattauna kenan dan Meenal din ta fito ta fad'a mata gaskiyar cewa itace taba Sarki number da Address din ta kuma inhar Moon din tana son Sarki har yanzun ita zata tsaya ta jajirce wajen fahimtar da iyayen su bayan ita kuma suna da goyon bayan AK dan haka shawo kan Hajiya bazai zama aiki ba, amma yanda taga Hajiya na tada jijiyoyin wuya ne ya karya mata kwarin gwuiwa dan Wallahi idan har Hajiya tace ah ah to ah ah din ne zai tabbata ita da Sarki sai gani sai hange. "Moon karkiji tsoron kowa anan ki fad'amin in har kina son Sarki ni kuma na miki alkawari wallahi zan tsaya miki har sai na tabbatar da d'aurin auren ki, kin san dai koni ina da ikon aurar dake koh amma bazan

Chapter 75 of 92