kafin ta shigo, "Mommy wallahi maganin Hajiya ya karbe ni kin gani wannan karan ina period d'ina lafiya lau babu ciwon mara ko d'aya kuma tun jiya yazo min" ta karasa fad'a tana tsalle² cike da nishad'i dan abun ba karamin farin ciki ya k'ara mata ba wai yau ita ke period lafiya lau babu matsalar komai,
Sai da ta gama tsalle²n ta sannan ta kwantar da kanta a kafadar Mommy "Mommy wai fa su yan bikin nan sun d'auka ko harda ni za'ayin ma aure tun da muka fito gidan su Besty dasu Maman Kano ake ta wani cemin amarya, ni dariya ma suke bani ko basu gane ni bane? "
Sai da ta daga fuskanta sama tana kallon Mommy sannan ta kara jefa mata tambaya da cewa "mommy na canza ne wai? Kema kinga na k'ara kyau koh? " bata tsaya jiran amsa ba tace "wallahi dai Hajiya wannan karan inaga taji wa'azin malamai ne Kinga fa ko masifarta fa yanzun ta daina! Allah ko zatayi fad'arta nidai wannan karan bata min sai dai tana ma su Moon"
"Matsa ki bani waje! Wato bazaki dena cema uwata masifaffiya bako Meenal? "
"Yi hakuri mommy na dena ai bazan kara ce mata haka ba tunda tamin magani ciwon marana gashi na warke in an gama biki ma zan amsa kud'i a hannun Baba Malam in kai mata ta k'ara amso min wani maganin kafin wannan yayi expired"
"Kinje kin gaishe da Baban naki? "
"Banje ba naga d'akin shi a kulle bayan kuma jiya nace mishi yau da wuri zan dawo shine bai jirani ba! "
Ta karasa fada tana tura baki,
"To yanzun dai sauka kije ki samu su Raheenat din a wajen innar ku kema a miki kunshin in Baban naki ya dawo sai kiji dad'in nuna mishi,
Tunda Meenal ta shiga sashen Innar su inda aka keb'e domin gyaran amare bata kara taka kafarta a kofar gida ba, har akayi kunshi aka gama aka d'aura da dan gyaran jikin da ba'a rasa ba domin dai Hajiya ta riga ta gyara jikarta tsaf.
Misalin karfe 10 saura Malam ya bada izinin a kawo mishi Amaren domin daman in zai aurar da yara tun kafin d'aurin auren yake zaunar dasu ya musu Nasiha,
Dashi da Baba Adamu
sai Yara Maza na gidan Manya sune suka musu nasiha, nasiha mai shiga jiki kuwa domin dai hatta da Meenal da bata san tana cikin sahun amare ba wannan nasiha ya ratsata domin nasiha ne suka musu akan biyayya ma'ana biyayya ma iyaye kafin ma akai ga biyayyar miji, wannan nasiha shi ya goge rashin adalcin da Meenal take ganin kamar anyi ma kannen ta su Raheenat na auren wuri harma a cikin zuciyar ta take musu fatan Allah ya basu ikon cin ribar biyayyar da sukayi ma iyayen su.
Sai da Malam ya sallami kowa, kowa ya kama gaban shi zuwa makwanci amma banda Meenal data gyara zama domin a satikan da tayi bata a gidan ba sosai ta tara labaran da take son bama Malam, shiko bayan fitan su cikin d'akin shi ya shiga ya fito da wasu kana nun gora masu d'auke da ruwan rubutu a cikin su, bayau ya fara bata ruwan rubutu tana shaba dan haka nayau ma batayi musu ba ta amsa ta shanye dan dama tunda aka kaita sashen Innar su take ta bata magunguna tana sha duk a zaton ta dai maganin ciwon marar tane dan dama hakane tun kafin yazo ake fara bata maguguna.
Sai bayan da Malam ya bari ta gama bashi labaran dake bakin ta tsaf harda na kyautar da Abdul ya mata sannan ya kira sunan ta.
"Aminatu "
Wallahi sai da gabanta yayi kwance kwance ya fad'i dan Wallahi ita dai tsayin rayuwar ta bata tab'ajin Malam ya kira sunan taba sai yau hakan nema yasa ta kasa amsawa sai tana ganin kamar ba ita yake kira ba, har sai da ya k'ara mai maita kiran sunan nata,
"Na'am "ta amsa dashi bayan ta tabbatar da cewa da ita dai yakeyi.
"Aminatu nayi miki laifi dan haka nema nike neman afuwar ki ki yafemin nasan na aikata miki ba dai dai ba,"
Wallahi wani irin dumm haka taji a cikin kunnuwan ta kamar wacce ta gwauru da bango,
Ta bud'e baki da niyyar yin magana ya tari numfashin ta da cewa
"karkice komai tukun ki bari in gama magana tukun, Uwata tundaga ranar dana yanke hukuncin nan nike jin kunyar had'a ido dake, na tabbata da wani daga cikin iyayen ki ne suka yanke hukuncin dana yanke akan ki hakika dasai na sab'a musu sai gashi ni dakai na ne nake shirin b'ata miki rai, ina so ki yafe min laifin dana aikata ko zan samu in denaji a raina cewa ban kyauta miki ba"
Da rarrafe ta karasa inda yake fuskarta na zubda hawaye, "Babana me yasa zaka aikata min haka? Wacece ni da har zan zauna a gaban ka ka dunga neman afuwa na bayan kai din kai kafi kowa iko dani, hatta dani kaina bani da iko da kaina kaine ke iko dani, Baba babu wani abunda zaka aikata min wanda har zai sa inyi fushi ko wata banzar tsoka a cikin kirji ma'ana zuciyata ta rayamin cewa baka kyauta min ba, wallahi duk hukuncin daka d'auka akan rayuwata ka isa dani ne shi yasa ka zaratar dashi, wacece ni da bazan maka biyayya ba? Kaine Baban Meenal wa nake dashi sama dakai da har zan juya maka baya ko in k'aluba lanceka Babana, ai ka wuce ka nemi yafiya a wajena sai dai ni in durk'usa maka, kamin aikin gafara in na aikata wani laifin ne Babana"
Ta karasa fad'ar hakan cikin kuka dan Wallahi sosai kam hankalin ta ya tashi,
Kamota Malam yayi ya jingina da jikin shi, ruwan dake gefen shi na gora ya bud'e yakai Mata baki, kadan ta iya sha,
"Meenal gobe idan Allah ya kaimu za'a d'aura auren ki tareda na K'annin ki su Raheenat! Ina fatan zaki min biyayya kamar yanda kikace kuma bazaki bani kunya ba? "
Wani irin shuuuuuu ta ringaji a cikin kunnen ta kamar kana sauraron Radio network ya d'auke musu,
"Kiyi hakuri nasan burin ki shine karatu, ki sani cewa bazan tab'a aura miki mijin da nasan bazai tayani wajen ganin cikar burin kiba, bazan tab'a rusa miki burin ki na zama likita ba insha Allah wata rana ko bana raye sai an kiraki da suna Dr Aminatu dan jarabawar ku na fitowa nida kaina zan kaiki makaranta kamar yanda na saba,"
Da kyar ta iya bud'e baki tace "Baba aure zakamin nima? Ashe shi yasa mutane suke ta cemin amarya! Wa zan aura to? Ni ai duk samari na ban turo ko d'aya cikin su wajen ba ka kullum ce musu nakeyi karatu zanyi, harshi ma Bash din gidan master da kullum yake matsamun na fad'a mishi ni karatu zanyi"
"Ba d'aya daga cikin samarin ki bane uwata, Yayan ku Sufyan Sarki shine mijin dana zab'a miki ina fatan kuma zaki karb'eshi hannu bibbiyu? "
"Baba Sarki mai karnuka ne zan aura?"
Kwarai taso ta danne duk wani tashin hankalin da take ciki sai dai kuma ina shekarun ta basu kai ta yanda zata iya sarrafa abinda takeji a cikin jikin ta da kuma zuciyarta ba,
Wani irin jiri jiri haxo hazo haka ta dunga gani sai ganin ta ya koma kamar irin nefa Suna wasa da wuta tsakar dare a inda babu haske ko kad'an din nan,
domin dai wal wal ta dunga ganin haske da duhu na zuwa mata a tare ga kuma mararta datayi wani irin kullewa lokaci daya,
Da lalube ta samu ta riko hannun Malam "Babana Suma zanyi, Suma wallahi suman yana kusa, bana gani Baba ka kunna haske duhu nike gani tun tana sambatu dai har tayi dif............
❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
Naso ace anyi Daurin auren nan yau wallahi wayata babu caji, shi yasa, sai yanzun suka kawo mana wuta.
Kuyi hakuri nasan da yawan ku bakwason auren Sarki da yar gidan Malam sai dai ina mai baku hakuri kar kuce saboda haka zaku ajiye karatun littafin Dangina domin dai ba'ayi komai ba tukun,
Kusha ruwan sanyi ku sarara.
Team Sarki😟
Team Mai Jama'a 😰
Ummiee Zaria ✍🏼[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨👩👧👦 *DANGINA! * 🔱⚜️👨👩👧👦
''''''Page 31
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_nfection_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*08089965176*
*07084653262*
**************31
Farouq Malam ya kira ya d'auke ta zuwa wajen Mommy Hauwa, yasani daman cewar bazasu kwasa ta dad'iba hakan nema yasa yayi ma Dr Mubarak magana, shi ya bashi maganin baccin daya zuba mata a cikin ruwa tasha domin in har ba hakan yayi ba yasan ba lallai bane ta iya kwantar da hankalin ta balle harta samu yin bacci yau, yasan koda Allah yakai rai gobe zatayi bori sosai ba.
A ranar da Meenal ta baro Gidan Hajiya shi kuma Sarki da Abokan shi isa gidan domin gabawa da ita, kamar yanda Uwar gida ta bashi umarnin zuwa ya gana da ita, Sanin cewar har zuwa wannan lokacin bata san da zancen auren ba kuma zuwan nashi na iya haifar da wani abun yasa Hajiya ta ha'da Meenal d'in da iyayen ta mata suka wuce da wuri domin sosai Hajiya ta shirya tarban angon Takwarar nata a cewar ta dole ta gindaya mishi dokar da mudun ya takata zata wanke kafafuwar ta taje har inda yake ta karta mishi rashin daraja, dan karma yaga an d'auki jikarta an bashi yayi zaton ko sun gaji da ita ne.
Misalin karfe 1 saura su Sarki suka isa kofar gidan koda suka isa an fara kiran Sallah a masallacin dake kofar gidan dan haka basu shiga ciki ba har saida suka gabatar da farali tukun,
Bayan sun idar da masallaci a kofar gidan bakin gate sukaja burki domin neman wanda zai musu iso zuwa cikin gidan kasancewar su na bak'i bazai yuwu su wuce ciki kai tsaye ba.
Fitowar Yusuf wase daga masallaci kenan yazo da niyyar shiga ciki Kwaro ya mishi sallama.
"Bawan Allah kamar cikin gidan nan zaka shiga koh? " ya tambaya bayan sun gama gaisawa dasu Sarki.
"Eh ciki zan shiga"
"Alhamdulillah tazo mana gidan sauk'i kenan, mu bak'ine ko kuma a tak'aice dai ince sirikin gidan ne yazo gaisuwa, inba damuwa zamu so kayi mana iso zuwa ciki duk da dai an san da zuwan namu amma kaga ai bai kyautu mu shiga kai tsaye ba! "
"Ba damuwa kuna iya shigowa ai"
Rufa mishi baya sukayi zuwa farfajiyar gidan, ganin cewa sunce su sirikan gidan ne yasa shi yanke shawarar kai su falon Hajiya tunda itace uwar kowa a gidan. Sai da suka karasa gab da falon sannan ya juyo garesu "bari in shiga in isar musu da sak'on isowar naku koh? "
"Ba damuwa muna jira anan" suka bashi amsa shi kuma yasa kai cikin falon.
Da sallama ya shiga, ya kumayi sa'ar samun Hajiya da iyalanta maza dukan su zaune a falon,
"Karaso daga ciki mana yusufa, ga wajen zama ai kadai zauna koh? ga kuma abinci duka in kana da bukata"
"Nagode Hajiya dama bak'i ne akayi suka buk'aci inyi musu iso, sunce sirikan gidan ne gasu a nan bakin kofa"
"To Allah ya musu isowa kenan barkan su da zuwa to ai ce musu su shigo kawai dan dama zaman nan daka gani zaman jiran zuwan su akeyi"
Ta fad'a tana jawo mayafin ta dake gefen ta ta rufe jikinta dashi,
"Larai! Ke larai!! Waini anya larai basai na dangana ki da asibitin ABU ba kuwa? Jama'a kayi ta ihu kana kiran sunan mutum kamar wanda yake cikin rijiya nan da kitchen ace mutum baiji kira ba, ah ² wallahi wankin kunne zan kaiki a miki waya sani ko dattin kunne ne yasa bakijin magana sai anyi ta miki ihu duk kisa makwogoron mutum ya tsatsage wajen d'aga murya"
"Ayi hakuri hajiya ina ta baya ne" Larai ta fad'i hakan a yayin da ta iso falon, "to ai sanin hali yafi sanin kama yar'nan yanzun dai fito da abubuwan da aka tanadar na taron bak'i domin gasu nan sun iso atoh kar suce sunzo gidan surukai ba'atare su da komai ba"
Tana rufe bakin ta bak'in suka fara sallama su uku ne sai Sarki angon cikon na hud'un su.
Bayan gaisuwa da yan tambayoyi dasu Baba Usman sukayi ma Sarki duk Hajiya na zaune tana karema Sarki kallo dan tunda abokanan shi suka gabatar dashi a matsayin Mijin takwarar ta take mishi kallon ciki da waje.
Jin sun fara sallama zasu wuce yasata dakatar dasu da cewa "Nace ba! "
Juyowa sukayi suna sauraron ta.
"Ku d'an bani Aron abokin naku na yan mintoci",
Ba damuwa Hajiya suka amsa dashi a yayin da suke ficewa, maida kallon ta kan su Baba Usman tayi "kuma ku bani waje sirri nike son yi da mijin takwara ta"
"To Hajiya" suka had'a baki wajen fad'a duk da basu so hakan ba dan suna gudun kartayi wani maganar daba ita kenan ba domin dai ko d'azun nan babu abunda ta mance bata fad'a ba akan shiga hakkin jikarta da akayi wajen yi mata auren wuri, amma haka nan dukan su suka fice suka bar mata falon ta suna fatan Allah yasa kartayi katobara.
"Kace sunan ka Sufyan ko? "
"Eh Hajiya Sunan kenan Sufyan Sulaiman Ladan"
"Masha Allah, sunce min matar ka d'aya da yara 4 koh? "
"Eh haka ne"
"To dama so nike in tambaye ka inji ya zaman naku zai kasance duba da cewar aikin ka a KD yake ita kuma uwar gidan ka ance tana can Lagos itama yanayin aikin tane ya hanata dawowa nan ta zauna a kusa da kai koh? "
"Eh Hajiya a Kaduna aikina yake a yanzun duk da dai yanayin aikin yakan d'aukeni zuwa wasu state d'in inje inyi kwanaki ko wata ma haka, kuma itama iyalin nawa kamar yanda aka fad'a miki yanayin aikin tane yasa bata dawo nan din ba amma in ta samu hutu takan zo nan din nima kuma duk karshen wata a can nike yin shi"
"Da kyau to dama abunda yasa na tambaya dan inji ainihin inda zaka ajiyemin jikane, anan Zaria ne ko a Kaduna inda kake aiki? "
" anan zata zauna Hajiya saboda a can d'in cikin barracks nike zaune kuma gaskiya ni bana da ra'ayin ajiye iyalina a cikin bariki dan haka nan zata zauna ni kuma zanyi kokarin in ringa zuwa dubata duk sanda na samu lokaci"
"To hakan ma ba laifi, Sai dai kuma gashi gidan ka na nan d'in daka ce jikata zata zauna naga gidan ginin zaman mace guda ne gashi kuma kace ita uwar gidan naka takan zo maka hutu nan, to yanzun daka ke shirin auren jikata ita kuma matar taka idan tazo a ina zaka sauketa kenan? Dan dai rashin adalcine kace zaka sauke ta a gidan da jikata take ciki! "
Sai da ya nisa dan Wallahi wadan nan tambayoyin da tsohuwar nan ke mishi sun fara hawa mishi kai, to fisabilillahi ina ruwanta da sha'anin gidan shi, inace dai gidan nan nashi ne koba matar shi ta aure ba yana da damar da zai sauke duk wanda yake so a gidan balle kuma matar shi da daman saboda ita ya gina gidan, amma dai dan su rabu lafiya sai ya amsa mata da cewa.
"Eh ai da yike ita Fateemah ko tazo a KD can tare dani take zama kota shigo nan d'in ba zama takeyi ba"
"Eh ba shakka to aini dai daman saboda gudun abunda ka iya tada wani fitinar a gaba nikeyi, koba komai dai kaga ita takwara ta bata da iko da gidan ka dake can lagos, na kaduna kuma tunda ka nuna baka bukatar matan ka su zauna a wajen nasan ba zaka d'auketa ka kai can ba, shine dama yasa nake so ince tunda abun haka ne karfa wata rana ita uwar gidan ka tazo nan kace zaka sauke ta anan inda jikata gudun wani abun ya biyo baya kaga ai gara ayima kowa adalci koh? Saboda a samu zaman lafiya kaga dai ita wannan karamar yarinya ce domin dai a haife wallahi tsaf nasan ka haifeta, in ma banda had'in dangi ai nasan ko kai ido da kunya ma ka kalleta kace kana so balle ayi zancen aure, to karamar yarinya ce dai dududu bata wuce 17 ba Inma fa takai kenan, sai kuma abu na gaba"
Ta fada tana mai mashi kallon ido cikin ido duk dashi d'in yana ta kokarin yanda zai cire nashi idon a cikin nata a mtsayin ta na kakar matar da ake shirin aura mishi.
"To dai rokon ka zanyi ko kuma ince alfarma zan nema, wato kaga dai ita yarinya nan wallahi kankanuwar yarinya ce in ma dai banda cewa yaran yanzun suna da kufan jiki wama zai kalleta yace ya kalli mace! To nidai dan Allah karkaga tayi saurin girman nan ko ina a ciccike kayi zaton wata uwar mata ne wallahi ba iyawa zatayi dakai ba, dalilin hakan nema yasa nace bari in roki arziki dan Allah ka daure ka d'auke idanuwan ka akan ta ka bari harta k'ara girma tayi kwarin da zata iya d'aukar dawainiyar ka kafin kace zaka haike mata dan nasan ku maza baku iya kawaici ta wannan gefen ba, ita kuma kaga yarinya ce karama zuwa d'aya zaka mata ka tasheta a aiki, to tunda har Allah ma yasa kana da wata matar inaga Ai komai zaizo da sauki ko? Ina fatan ka fahimci abunda nike magana akai domin dai magana na gaskiya bari in maka b'aro² yarinyar nan fa bason auren nan take ba ubanta Malam shine ya shirya ya kuma gabatar da komai ba tareda yayi shawara da kowa ba, harta ninan dana haifi uwar ta dama ita kanta uwar nata bamu samu labari ba saida ya riga ya zartar da komai in fad'a maka karewa ma hatta dai ita amaryar taka yanzun haka da nike magana dakai a matsayin gobe za'a daura mata aure tofa labarin auren bai kaiga isa kunnen taba, dalilin ma da yasa baka sameta a gidan nan ba kenan"
Yau dai Sarki shi yake ganin ikon Allah jama'a to wai ita matar nan bata san cewa ba iya jikarta ce kad'ai akama dole a batun auren nan ba harta shi da girman shi da komai biyayya kawai zaiyi ma uwar shi domin yaga sun rabu lafiya yasa dole ya amshi auren badan yana bukata ba!
Shine tun ba'a daura ba har an fara kafa mishi dokoki, shi aiko shaye shaye yakeyi to ba karamin sha zaiyi wanda har zai iya kaishi ga kusantar yarinyar nan ba, balle kuma shi rabon shi da zuke² ai tun lokacin da bai san ciwon kan shiba, dan Allah jama'a Inma yace zaijema yarinyar nan a matsayin miji ai zalinta kawai zaici hakan kuma ai shi gani yake bama karamin zunubi bane, yarinyar dakoh autar su ta girme mata sosai, yaso ya d'aga ido ya kalli Hajiya yace mata ke Hajiya nima fa auren nan ba dan ina so ake shirin daura min shiba, kamar dai jikar ki nima auren biyayya zanyi, amma ina bazai iyaba dan sa'insa da babba ba dabi'ar shi bace balle kuma su Sojoji da aka san su da biyayya komai sai dai suce *yes sir*
Dan haka sai ya kara dukar dakan shi kasa yana mai amsa mata da cewa.
"Hajiya insha Allah zanyi kokarin kula da ita bazan cutar da itaba koba komai ita d'in kanwata ce dan haka zan kula da ita kamar yanda zan kula da kannena ko kuma yarana na cikina"
"Kai madallah madallah kaji Allah dai yasanya Albarkha da alkhairi a wannan aure ya kuma baku zaman lafiya, to abu na karshe da banyi magana akan shiba shine batun karatun ta nasan ba lallai iyayen ta su tada maganar ba, amma ka sani tana da burin ganin ta zama likita kamar mahaifiyarta, kuma ni nayi mata alkawarin dafa mata wajen ganin cikar burin ta, nagode Allah kuma da yasa kaima mijin nata ba mazauni bane kaga hakan zai bata damar da zatayi karatun ta a tsanake cikin kwanciyar hankali, dan haka da zarar jarabawar su ta fito za'anema mata admission taci gaba da karatun ta ina fatan bazaka hana ba"
Ta karasa fad'a tana kallon shi dan so take ta fahimci shin zai amince ko k'ak'a,
"Ba damuwa insha Allah domin nima nasan dad'in karatu dan haka bazan tauyeta wajen hanata cikar burin taba".
"To Alhamdulillah yanzun kam kana iya zuwa ka samu abokan ka ku wuce Allah yasa ayi taron biki lafiya, a kuma daure a gunda yin Addu'a da yawan sadaka maganin bala'i dan makiya da mahassada ako ina suna nan wasu ma tare ake bacci dasu ayi tayin azkar ba gajiyawa kaji"
"Insha Allah za'a kiyaye Hajiya Nagode Allah ya kara lafiya da nisan kwana"
"Ameen ameen Allah ya muku albarkha muje in taka maka dan dama zuwan kune yasa ban fita ba nima aminyata ke aurar da jikanta matar da kanin ka Sa'eed dan wajen Malam zai aura kasan jikar Aminiya ta ce can nike son lekawa tunda nidai nan ba taron komai zanyi ba duk matan gidan suna can sun kwasa sun tafi unguwar naku"
A bakin kofa tayi karo da kwalayen su drinks da buhu nan kayan abinci, Larai ta kwalama kira tana tambayan wannan kayan kuma daga ina ya fito aka ajiye mata su a bakin kofa?
"Bak'inne suka kawo Hajiya" Larai ta bata amsa, "shine tun tuni baki sanar dani ba har saida suke shirin tafiya, fisabilillahi ai sai ki sanar dani inyi musu godiya koh, irin wannan dawainiya haka"
Ita dai Larai komawa ciki tayi tabar ta.
*WASHE GARI*
Meenal bata samu damar tashi ba har sai zuwa karfe 12 na rana kasancewar Mommy Hauwa tasan tana al'adah hakan yasa bata damu kanta wajen ganin ta tashin ba sai dai lokaci lokaci takan duba yanayin numfashin ta,
A yayinda ta farka abubuwan da suka faru a daren jiyane suka fara dawo mata amma sai take ganin inah wannan ai sharrin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 92