ni shirya nace nida kaina zan daukota zuwa asibiti dan so nike likitocin sumin Karin bayani akan ciwon nata dan gaskiya abun bana wasa bane, ita kuma uwar gaba daya banga alamar ta damu da wahalar da y'ar kesha ba dan har yanzun banji gamsas shiyar bayani daga gareta akan ciwon ba"
Sai da ya dan goge zufan daya tsatstsafo masa wanda take nuna alamun cewa shima din a dame yake kwarai kafin yaci gaba da cewa,
"Tun tashin yarinyar nan ita bamai yawan laulayi bane shi yasa in ciwon ya tashi duk sai tabi ta firgice, Allah Kadai yasan azabar da take sha yar karamar yarinya da ita"
Fitowar daya daga cikin Nurse din dake kula da Aminatun ne yasa su Maryam mikewa sukayo wajen ta suna mai tambayar ta da cewa...
"Ya jikin ta?
Ta tashi kuwa?
Meya sameta? "
Haka sukaci gaba da jero ma nurse din tambayoyi ba kakkautawa,
"Ah ah sister's ku kwantar da hankalin ku ya'r uwar ku zata samu lafiya nan bada jimawa ba Insha Allah dan yanzun hakama ta farka"
Karasawa wajen Sarki tayi.
"Ga wannan abubuwan da ake bukata ne ku amso zamuyi mata amfani dashi kafin Dr ya fito daga labour room"
Alamu ya mata da hannu cewar ta mikama Kwaro takardar,
Mikewa Sa'eed yayi "bani takardar in anso!
Tana mika mishi takardar ita kuma ta koma ciki,
Jin cewa Meenal ta farka yasa suka danji sa'ida a cikin zukatan su, nan da nan Sa'eed ya dawo, Nurse din dazun ne ta Kara fitowa ta amshi kayan ta koma ciki,
Ba'a dauki lokaci ba su Aunty Murja suka iso asibitin gayya guda kamar wadan su masu kai Amarya,
Da mamaki Malam yake kallon su, inba haukaba ya zasu kwaso iyalan gida gaba daya su taho suzo su tare a asibiti subar gida ba kowa alhalin yaran su na gab da dawowa daga makaranta, yanzun kuma Idan yace zaiyi magana sai sugar laifin shi suce ya fiye fada ko yanzun dai sunci albarkhacin Sarki,
ne amma Ana basu damar ganin Aminatun zai korasu su koma gida asibiti aiba gidan biki bane, dan haka bai iya ce musu komai ba illah kauda kanshi ma da yayi ya mike da niyyar barin musu wajen, sai dai kuma har yayi taku daya biyu ya juyo garesu,
"Ina fatan cewa babu wacce tayi gigin kiran Hauwa'u ko auta a cikin ku? "
Dukan su dukar da kansu sukayi aka rasa mai bashi amsa dan ba wacce Zata so ya sauke haushin ganin su diyyy din da yayi a kanta, shifa Malam mai iya mishi sai Allah dan wallahi ko shakka babu da basu biyo bayan su ba ko ace wasu suzo wasu su zauna tabbas saiya samun abun magana cewa dan ba cikin yaransu ne d'aya ke ciwo ba shi yasa suka zauna a gida wato inta mutu ma oho,
Amma gashi yanzun sun kwaso jiki sunzo sai wani daure fuska yakeyi Malam ho.
Uwar gidan shi ne ta wakilci sauran da cewa,
"Bamu kira Auta ba itama kuma Jiddan mun kirane dama muji ko Aminatun nada sauran maganin da take sha a gida dan mu taho dashi sai dai kuma bamu samu wayar nata ba har muka taho, ya jikin nata? ta farka kuwa? "
Bai tsaya bata amsa ba yasa kai ya fice su kuma sauran matan suka samu wajen zama suna tambayan su Maryam yaya jikin na Aminatu,
Bayan zaman shiru da jiran tsammani da sukayi na wani lokaci Sannan ne wannan Nurse din ta Kara zuwa take fada musu cewar an canza ma Aminatun daki sai dai kuma sun mata allurar bacci basu so kuma hayani ya yasa ta farka da wuri ba,
"Zamu iya ganin likitan daya kula da ita? "
Sarki ya tambayi Nurse din,
"Eh to bari in mishi magana, ku biyoni in nuna muku inda aka maida ita"
Tace a yayin da ta juya zuwa wani hanyar daban ba wanda ta fito daga ciki ba.
"Kira Baba sai muje yaga likitan koh? "
Sarki yace da Sa'eed,
"To Ya'ya"
Ya amsa a yayin da ya juya zuwa waje, su kuma su Meelat tuni suka rufama Nurse din baya zuwa dakin da aka kwantar da Meenal.
Babu bata lokaci su ka dawo Malam ne kan gaba kamar zai hada da gudu Sa'eed kuma yana biye dashi a baya,
"Ya jikin nata ta farka din kuwa mai likitan yace?
#Ameenatu. 🧕🏻
#Team Sarki. 🤴🏼
#Team Mai Jama'a. 🤵🏻
#Sheikh Naseer.👨🏻💻
#Ummiee~Zaria[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*
*👨👩👧👦DANGINA!👨👩👧👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_
ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._
*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}
*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._
*Ga masu tambayar littafin daga farko zaku iya tuntuɓata kai tsaye da wannan number ɗin 08061358462,*
Karku manta littafina kyauta ne banyi shi dan in siyar ba dan haka karkuji ɗar kuba duk wanda kuke so.
Free book ne yan bati a dage da karatu a daure a dunga comment atoh.
```Page 21
°°°°°°°°°°°°° £h ta farka dan har ma sun canza mata d'aki, sai dai kuma sunce sun mata allurar bacci saboda ta samu wadatac cen hutu ana saran idan ta farka zataji saukin ciwon insha Allah "
Cewar sarki,
"To sai mu karasa can din koh! Kai kuma ina ganin ya kamata ku wuce tunda gasu Hadiza sun karaso,kar a tauyeka da yawa sannu da kokari kaji Allah dai ya saka maka da alkhairi Allah yayi Albarkha , "
Su Kwarone suka amsa da ameen.
Shi kuma ya amsa ma Malam da,
"Eh zamu wuce so dai nike muga likitan tukun inji idan babu wata damuwa , dan namayi kokarin Kira wayar Dr din bai amsa kiran nawa ba,"
Cigaba da tafiya sukayi zuwa d'akin da Meenal ke ciki, suna isowa Dr din yana fitowa daga d'akin.
"Soja mazan fama wai dama kana gari ko dai shigowar kenan? dan kai ana cewa gida biyu maganin gobara kai kam naka gidajen ba iyaka, yanzun gaka a Zaria anjima Kaduna gobe Lagos gata kuma sai yanda hali yayi"
Ya karasa fada a yayin da ya iso inda su Sarki ke tsaye,
Hannu ya mika musu sukayi musabaha fuskar shi cike da fara'a yake tambayar su cewa,
"Ah² shin kodai kune kuka kawo Amina Mukhtar? "
Ya karashe tambayar yana mai nuni da hannun shi zuwa dakin da ya fito,
"Dalilin ma da yasa nayi Kiran ka kenan".
Sai da Dr din ya duka har kasa ya gaishe da Malam kafin yace "Baba harda kai suka taho? ai da kayi zaman ka a gida jikin da sauki ai"
"Likita ai ban iya zama gida uwata na asibiti gara dai in taho ayi komai a gaban idona, ya jikin nata? "
"Jiki Alhamdulillah Baba muna saran samun saukinta da zarar ta farka, bismillah mu karasa ku ganta"
Jagora yayi musu zuwa cikin dakin inda suka sameta kwance akan gado ga karin ruwan da aka daura mata,
Karasawa wajen gadon Malam yayi yana mai binta da kallo,
"Sannu uwata, sannu kinji wannan ciwon Allah yasa ya zama kaffara a gareki, Allah ya kawo sanadiyar rabuwar ki dashi ki huta"
Ya karasa fada yana gyara mata zaman hijjab din dake wuyan ta ya rufe mata kafadunta da suke waje sakama kon zamewar da kafadar rigarta yayi.
"Sarki mu karasa office dina, nurse ikleema tace kuna son gani na"
"Ok" kawai Sarki ya amsa mishi dashi, juyowa gefen da Malam yake yayi yanda yaga Malam ya tsare Meenal da kallo ne yasa shi jin ba dadi dan yasan haka Malam zai takura kanshi har sai sanda yaga ta warware tukun kafin shima ya samu salama,
kauda kanshi daga kan Malam yayi zuwa kan Meenal din, kallo daya ya mata ya kauda kai dan shi kullum mamaki yake akan hukuncin da uwar gida ta yanke waishi ne za'aba auren wannan karamar yarinyar dan a kallon daya mata yanzun ba abunda ya hango illah zallar kuruciyar ta daya kara fitowa.
"Muje koh"
Dr ya fadi hakan a yayin da yake barin d'akin wanda hakan ne ya yanke ma Sarki sakar zucin da yakeyi.
"Baba mu karasa office din Likitan"
"Toh Madallah Malam Sufyan bismillah"
Malam ya fada yana binsu a baya duka suka fito daga cikin dakin, fitar nasu shi yaba matan daman shiga cikin dakin bayan Malam ya kora musu gargadi akan kar suyi hayaniyar da zasu tasheta a bacci.
Malam da Sarki ne Kasai suka isa office din likitan,
Dr yayi kokari sosai wajen kwantar ma Malam da hankali akan ciwon na Meenal,
duk da Malam ya mashi bayanin tsayin lokacin data sauka tana fama da ciwon da kuma irin yanda take wahaltuwa da ciwon, harda ma irin yanda suke fad'i tashin neman mata magani amma Allah baisa an dace ba,
Ganin da likitan yayi cewa babu bukatar wani boye ² tsakanin Dr da mai jinya balle yanda yaga Malam duk ya damu yasan ya shi fadama Malam gaskiyar cewa lalurar ciwon mara irin na Aminatu gaskiya maganin shi d'aya ne cikin biyu idan kuma har ba'a dace ba to sai acigaba da neman magani har zuwa sanda Allah zai yaye ma mace ciwon,
duk da dai a ganin shi sosai Aminatu tayi kankanta da aure a shekarun ta da kuma irin kalubalen da auren wurin kan haifar ga matan da ake aurar dasu basu kai matakin ba,
Amma hakan baisa yakiyi ma Malam bayanin cewa Aure shine sahihin maganin da yake sarai cewar in akama ta zata rabu da ciwon,
duk da cewar wasu matan ko sunyi auren ciwon baya saurin tafiya sai dai yakan ragu har zuwa sanda mace zata fara haihuwa a hankali kuma sai a nemi ciwon a jikin mace a rasa.
Malam ya jinjina wannan al'amari matuka bawai dan bai son aurar da itan bane ,
sai dai kuma sanin kanshi ne yanda kullum take cin burin yin karatun likitanci, yasan Aminatu tana da burika da yawa wanda bata tab'a kawo cewa akwai wani abu dazai shiga tsakanin ta da burikan nata ba,
To amma kuma da irin wannan wahalar da take sha duk wata yana ganin ai gara auren duk da shima Allah ya gani bai so ya aurar da ita din da wuri ba .
dan hakan nema yasa kaf cikin maneman da suka fito nata yaki bama kowa dama har yanzun sai dai kuma yana tsoron kada rashin yin mata auren yasa su rasata wata rana duk da a kwanakin yaga yanda aketa fuskantar kalubale ga matan dake kamuwa da ciwon yoyon fitsari a sanadin auren wurin kamar yanda likita ya fad'a,
A takaice dai wani damuwar kuma Malam ya kara shiga Wanda zamu iya kira da ga koshi ga kwanan yunwa,
daga karshe dai ya yanke shawarar zaije yaci gaba da istihara in auren ne mafi alkhairi to Allah ya tabbatar.
Bayan sun fito daga wajen likitan Malam da kanshi yama iyalan nashi umarni akan su koma gida haka, dan likitan yace koda ta farka bazai basu sallama yau ba har sai sunga yanda jikin nata ya karaji dan haka su koma gida ita Innar su inta koma gida saita hada abubuwan da zasu bukata na zaman jinya, sai ta dawo ta zauna da Meenal din,
Fatan samun sauki suka mata sannan suka Kama hanya dan har dasu Jamila Sarki yace kwaro ya mai dasu makaranta,
cikin dakin Malam ya koma yayin da shi kuma Sarki ya koma office din Dr sai da yayi settling din komai da yasan zasu bukata a zaman da zatayi a asibitin sannan ya baro office din.
Harabar asibitin ya koma, koba komai ya kamata ya kira Uwar gida dan tasan cewa har yanzun yana cikin Zaria bai wuce kaduna kamar yanda ya mata sallama a yayinda yabar gida ba.
Da fara'a a muryar ta ta amsa sallamar daya mata,
"Sarki badai har kun sauka ba? amma dai gudu kasa Ibrahim yayi da motar koh? Kuma kullum Ina fada maka ka dena sa d'an mutane yana gudu da Mota, atoh ba fata ba ai gara kai ko yanzun ka mace kabar baya shiko har yanzun ko auren farko baiyi ba ! "
Sai da yayi murmushi sannan ya bata amsa da cewa
"muna cikin Zaria ai bamu samu damar wuce wa bama"
"Subhanallah to meya faru kuma? "
anan ne ya mata bayanin abinda ake ciki kana ya kara da cewa yanzun hakama yana cikin asibitin shida Baba Malam.
Daga yanayin yanda yake jiyo muryar ta cike da annashuwa yasan cewa koda bata fito fili ta fadaba hakika tayi farin ciki da abunda ya aikata.
"To kai babban mutum haka akeyi ai kamata yayi ka kirani tun dazun ka shaida min muma mu taho asibitin to amma ko yanzun bata baci ba bari insa a hada abinci sai in taho musu dashi,
Kai kuma kayi abunda ya dace Allah ya maka albarkha, kafin kabar asibitin kuma sai kayi musu cefanen kayan jinya koh yan kayan tea dasu kayan marmari haka,"
Jin yayi shiru yasa ta kara da cewa
"kana jina kuwa?"
"Eh inaji"
ya Bata amsa,
"To nace ba,
inaga tafiyar ka dole zaka barshi sai zuwa yamma kenan dan dole ka zauna muga yanda jikin nata zai kara ji zuwa yamman! "
"To amma Hajiya tun dazun fa Malam yake cewa ya kamata in wuce haka tunda dai kinsan yasan yau zan koma dama kuma akwai shirin dazan karasa idan na isa"
Bata bari ya karasa ba ta katseshi da cewa
"to kai kuma dan yace ka tafi shike nan saika kama hanya gilu² ka tafi ka barshi da dawainiyar Aminatun?
Sarki Ana magana nefa akan yarinyar da ake nema maka da aure! To in baka nuna kulawarka a kanta ba fisabilillahi kana ganin zai samu kwarin gwuiwar baka ita ka aura ne? Kar kayi la'akari da cewa itadin kanwar kace yasa kayi zaton cewa Malam zaiji nauyi na kona mahaifin ka wajen daukar Aminatu ya baka muddin baiga alamar cewa zata samu kulawar daya dace a wajen kaba, dan haka kafin ma in iso ka tabbatar ka aiwatar da abunda na saka kuma suma sauran yan uwanka zan fada musu suzo su dubata"
Tana gama fadin hakan ta yanke wayarta dan tasan dai tabbas bazai bar asibitin ba har sai yamman kamar yanda tace,
Kuri yabi wayar da kallo yana kara mamakin Uwar gida yanda ta fututtuke wai shi da girman shine ake shirin yima auren dole fisabilillahi shida yake da kamar Teemah mai zaiyi da wannan karamar yarinyar.
"Allah ka bani mafita mafi alkhairi "ya fada a bayyane.
Malam ko zaman shi a dakin Baba Adamu da Baba Auta ya fara kira ya shaida musu abinda ke faruwa kafin yaci gaba da kiran sauran dangi, sai dai duk kiraye²n da yayi bai kira Mommy Hauwa ba dan yasan matan gida zasu Kira su fada mata, koda lokacin sallah yayi saida ya Kira nurse din dake kula da Meenal din ta zauna da ita Sannan ya wuce masallacin.
shiko Sarki mortar Dr Mubarak ya ara ya shiga gari dan aikata umarnin da uwar gida ta bashi na siyo kayan jinya haka ko ya kwaso harda su drink dasu ruwa duk wani abunda yasan zasu bukata sai da ya siya koda ya dawo Malam yana Masallaci, sai dai ya cimma Kwaro da Sa'eed a d'akin,
su yasa suka kwaso sauran kayan suka kawo dakin sai da ya kirga kudade yaba Sa'eed da sunan ya rike a hannun shi koda za'a bukaci wani abun sannan yaja mishi kunne cewa karya fadama Malam sannan yace ma Kwaro ya tashi su kama hanya dan bazai so Uwar gida ta iso asibitin ta iske shiba dan tana iya kara ballo mishi wani ruwan kuma.
Sai da sukama Malam sallama tukun kafin suka kama hanya, tafiyar su babu dadewa su uwar gida suka iso tare da sauran matan gidan Malam Ladan din.
A wannan rana dai su kansu yan asibitin sun san an kawo musu yar dangi jinya domin tako ina haka ake zuwa dubiya cikin yan dubiya kuwa,
harda Hajiya Innah da nata gayyar wadanda suka samu isowa asibitin da dare bayan ishsha'i zuwa lokacin kuma su Baba auta sun Samu sun lallaba Malam ya koma gida Mommy Hauwa da Innar yara sune a asibitin kuma Alhamdulillah koda Meenal din ta farka jikin nata da sauki sosai domin period din yazo mata,
Dama in ya riga yazo ciwon yakan ragu, har ta Samu ma tayi wanka ta canza kayanta daga na makaranta zuwa na gida.
mota guda Hajiya sukayo ita da ahalin gidan ta gefe Guda kuma gasu Mai Jama'a, Musty, da kuma Sadeeq. Koda suka iso sun Samu Mommy Hauwa da Innar yara a waje ne suna fira ,
yayin da suka bar Maryam da Meelat a ciki tareda Meenal din a Cewar su wai su zasu kwana da ita.
Bayan gaisuwa ne suka dunguma zuwa ciki dan duba mai jikin,
sun same su duka su ukun zaune akan gadon mai jinya suna hira,
sai da Hajiya ta kare musu kallo tsaf sannan ta rike hab'a tana kallon Mommy Hauwa "Jidda nace mutum nawa ne ke ciwon hala?
nidai mutum uku na hango a gadon marar lafiyar ko an fara hada mutum uku a gado daya ne? "
Sauka daga gadon su Maryam sukayi suna dariya yayinda ita kuma Meenal ta koma ta kwantar a maimakon zaunen da take haka kafin Hajiya tayi magana, ita dai Allah ya gani ta gaji haka mutum zaiyi ta zama a asibiti mutane suna mishi jele da sunan gaisuwa , itafa Allah ya sani wallahi ta tsani zaman asibiti dan da za'aji ta nata da gida zata koma tunda dai aiko yanzun taji sauki inyaso sai taci gaba da shan magani ta warware a gida abinta, dazun ta fara magana Malam yace a'ah, haka kawai ka kwanta asibiti maye da mayya suyi ta maka jele salon a lashe maka kurwa,
Sannu takwara ya jikin? Kekam wannan girma naki baizo miki da sauki ba sam wallahi, ace mace in zatayi al'adah sam ba sirri "
Dago idonta tayi da niyyar kallon Hajiya bakinta cike da magana sai akayi sabani idonta ya fada cikin na Dan Mai karfi aiko ta daddage ta watsa mishi hararar da tayi niyyar bama hajiya ita akan Sari,
"Kai" ya furta cine da mamaki yana nuna kanshi da yatsa.........
#Ameenatu. 🧕🏻
#Team Sarki. 🤴🏼
#Team Mai Jama'a. 🤵🏻
#Sheikh Naseer.👨🏻💻
#Ummiee~Zaria
[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱
~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~
*©®UZ-2023.*
*👨👩👧👦DANGINA!👨👩👧👦*
_{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_
ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳.
*ZAINAB USMAN*
_{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳*
_Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._
*₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳*
_Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._
*JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}}
*HAUWA MUH'D USMAN*
{{Real Smasher}}
*H UMAR*
{{Admin Beneficial}}
&
*SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}}
*₮Ʉ₭Ʉł₵ł*
_Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen.
```Page 22
"Kaiii"
ya furta a fili yana mai zaro ido cike da mamaki ya nuna kanshi da yatsa.
Ita kuwa yallabiyar kauda kanta tayi kamar ma bata san da wanzuwar shi a wajen ba tawani gyara kwanciyar ta abunta ta juya musu baya,
Zanyi maganin kine yarinya baki san nidin maganin tsageru bane irin ki,
Yake aiyanawa a zuciya yana mai dage kafadun shi duka biyu alamun ke zakiji a jikin ki,
Karasawa wajen gadon yayi kamar abun arziki ya nemi gefen gadon ya zauna, bai tsaya wata² ba ya cusa hannun shi cikin bargon data rufe jikin ta dashi ya manna mata wani irin shegen tsunguli mai dan Karen zafi,
Bata tab'a tsam manin cewa shine ya zauna a kan gadon ba sakamakon juya bayan da tayi.
tsananin azabar zafin mintsilin daya tafi kai tsaye ya kai sako zuwa kwakwal warta a bazata ne yasata sakin firgitaccen kara a yayin da ta wani irin zubarar da bata sauka akan kowa ba sai akan shi,
Cacume shi tayi da kyau tana burgima da kiran ta shiga uku kunama ta cijeta,
"Waiyo Allah kunama ta cijeni,
ku cire min ita karta shigemin cikin jiki,tana wannan ihun take cigaba da yakushin shi a wuya,
waiyo Allah Baba Malam"
Haka ta dunga ihu tana burgima tun tanayin burgiman akan gadon har ta sauko kasa duk ta yamutsa gadon ta watso komai a kasa,
Amma fa dan walakanci irin na Meenal duk wannan ihun da haukar tsalle tsallen da take rike take gam da jikin Mai Jama'a riko kuma bana wasa ba,
Bawan Allah duk ta gama cimimiye mishi shaddar jikin shi duk ta yamutsa shi dan dole ya koma kamar wanda yayi fada da zaki, dan ba rikon wasa ta mishi ba abundai kamar da gayya ko kuma daukar fansa,
dan kuwa duk yanda yake tsammanin zai iya yakice ta a jikin shi abun ya faskara,
Sai fadi yake
"ke! ke!!
ke ki tsaya a duba mana, dallah ni sakeni kinbi kin wani shakemin wuya in mutuwa kike muradi ki mace ke daya mana amma kin wani shakeni in baki sakeni ba sai na karya miki hannuwa"
"ke yar nan kunama kuma ana zaune kalau daga zuwa dubiya kuma sai ace kunama ta halbi mai jinya,
Haka kawai salon ace mune da muka shigo yanzun mukazo da ita salon kisa a dunga nuna ni da baki anayi damu a gari?
Ah ah
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 92