Share this page
atoh" Zagawa gefen da Hajiya ke hakimce uwar gida tayi, "Barka da yammaci Hajiya" "Barka kadai yame jikin?" "Alhamdulillah Dr ma yace zuwa anjima zasu bashi sallama saurin da nike tayi kenan dama in iske ku" "Allah sarki ai kuwa da kin b'ata lokaci bazaki same muba, ina fatan kuma shi likitan ya shaida miki komai kamar yanda nima ya fad'amin?" "Kwarai Hajiya na samu labarin komai, kuma banzo nan dan in hanaki tafiya da ita ba, nazo ne dai dan in banki hakuri wallahi ban san duk abubuwan da suke faruwa ba kenan tsayin shekarun nan, Kuma insha Allah tunda har ya nuna baya muradin ta ni nan da kaina zan amso mata takardar ta kamar yanda na zama silar had'a auren" "Ah ah to madallah! Madallah!! Abu yayi kyau dan dama nima shawarar dana yanke kenan, yanzun dai in Allah yasa ya rubuta sakin sai kibayar a kawomin can gidana, in kuma babu hali nima da kaina ina iya dawowa gobe in amsa tun da kince anjima zai dawo, kuma kiyi iya bakin kokarin ki ki hana iyayen su maza jin batun nan dan nasan tsaf zasu hana suce bazaiyi sakin ba, kuma in hakan ta faru nidai ba hakuri zanyi ba daga karshe ma ina iya ganin laifin ki wallahi tunda dai kece uwar shi, jikata dai hakuri iya hakuri tayi shi to allah ya bada lada ya kuma had'a kowa da rabon sa, ke Meenal tuk'a mota muje yamma na dad'a yi" Ficewa sukayi daga gidan ita kuma uwar gida ta karasa wajen masu gadi, Gargadi ta musu sosai akan koma waye yazo gidan karsu barshi ya shiga indai ba mai gidan bane, sannan karsu sake su fadama kowa cewar Meenal bata gidan....... *Ummiee Zaria*✍🏼 πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° Son so my people [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: πŸ”±βšœοΈπŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *DANGINA!*πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦βšœοΈπŸ”± ~{{MY FAMILY}}~ *FREE BOOK* *RUBUTAWA* *UMMIEE ZARIA*✍🏼 ````` *Page 43*..... Bayan Uwar gida ta koma gida wayar Salman ta kira ta fad'a mishi cewar da zarar an sallame su su taho nan gidan ne kai tsaye bawai gidan Sarki ba, Sauran yaranta dake nan gida wadanda basu gama komawa nasu gidajen ba sun so su kawo suka akan dalilin da yasa Meenal tayi tafiyar ta tabar Sarki a asibitin a matsayin ta na matar shi, ganin suna son suga laifin Meenal din data biyema kakarta ta tafi, hakan yasa ta taka musu burki akan cewa ita ma Meenal din bata da lafiya ne shi yasa bata zauna ba, wasu daga cikin su sunyi Na'am da hakan wasu ko sun daijita ne kawai, domin dama dai ba komai ne in kayi zaka burge wani ba. Bayan isar su Hajiya gida, masu gadin gidan tayima magana suka kwaso mata kayan Meenal zuwa cikin sashen ta, dakin dake kusa da nata suka sa kayan, Ita ko Hajiya tun bata zauna ba ta d'auki waya ta fara kiran Turai (kakar billyn ya Sa'eed in baku manta taba). Babu b'ata lokaci bayan Turai ta d'auki wayar hajiya tace "Turai komai kikeyi dan Allah ki sake shi ki taho gidana ina buk'atar ganin ki da gaggawa" Bata tsaya jin ta bakin Turai ba ta yanke wayar, Hajiya Jummai ne ta shigo sashen da sallama. "Hajiya barkan ku da dawowa, ina daga falona naga ana sauke kaya daga motar Meenal shine ma yasa nace bari in taho in gani ko bak'i mukayi?" "Bari! Bari!! Bari kawai Jummai aini yau ni naga abinda yafi zare tsayi, ai dama ko baki shigoba nida kaina zanyi kiranki ki taho muyi jimamin tare, To gata nan dai na taho da abata gida tunda zaman gidan mijin ni dai banga ranar shiba" Tunda Meenal taji Hajiya zata fara rattaba zance ta mike tsam, ta haye sama, dan haka nan sai take jin zuciyarta Sam ba dad'i, "Banfa gane ba Hajiya! Auren nata ne ya mutu bayan barin ta nan gidan d'azun ? Ina ce d'azun nan tabar gidan nan, to koma warta gidan ne har akayi saki ko yaya?" "Ji Jummai da wani batu, toni in sakin akayi har zan damu kaina ne! Kawai mugunta da bak'in hali irin na soja mutumin nan yaje ya kafe min jika a gida yana kallon ta kamar hoto" "Banfa gane ba wallahi Hajiya" "Aifa Jummai ba ganewa zakiyi ba tunda ban miki bayani ba, ke dai nemi wajen zama dan in kin ji abinda ya faru kina iya yanke jiki ki fad'i," In kunga yanda Hajiya keyi zakuyi zaton wani k'aton zunubi Sarki ya aikata🀣. Wurjanjan haka Turai ta iso falon na Hajjaju ko damar yin sallama bata samu ba, "Innah lafiya kuwa meya faru kingan nifa haka na fito daga gida zuwa nan takalmi na wari da wari? wane ne ya mutu hala? dan daga yanda naji kina magana na tabbatar ba lafiya ba" Wajen zama Hajiya ta nuna mata da hannu batareda ta ce k'ala ba, Zaman ko tayi a gefen data nuna mata. "To masha Allah anan kusa dai gidan duniya kune kad'ai zan kira da shakikai na wadanda zan fad'amu duk wani abun da ke damuna in na kuka ne muyi tare haka ma in dariyar ce muyi tare, Nasan dai dukan ku baku manta yanda auren Takwara ta yar wajen Jidda ya kasance ba?" "Kwarai bamu mance ba" Suka had'a baki wajen bata amsa, "Masha Allah, kuna dai sane da yanda aka munafunce ni aka bayar da jikata har a kasa ranar aure ban samu labari ba sai da biki ya rage saura sati 3, ku biyun nan ku kukayi tsayin daka a sanda naso in botsare cewar ban yarda ayiwa jikata auren dole ba, kuka bani hakuri inaji ina gani aka d'auki karamar yarinyar nan aka aurama Soja mai mata harda yara 4 a lokacin dan kawai ya kasance dan uwanta" "Kwarai kuwa haka akayi" Turai ta fad'a tana kara gyara zaman ta dan sosai ta k'agu taji me ya faru. "To dai yarinyar nan a hakan kowa ya shaidane domin dai taba marad'a kunya wajen yima iyayen ta biyayya ta kuma amshi auren duk da bason mijin take ba, hasali ma ashe tana da wanda take so daban amma burinta nayin karatu yasa ta kasa bashi dama ya gabatar da kanshi, To ku bud'e kunne kujini da kyau, wai kun san cewa tsayin shekarun nan 6 da watanni da auren su amma shi mijin bai tab'a kusantar taba!" "La'ilah ha'ilallahu muhammadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam, innalillahi wa innah ilaihir raju'un, lahaulah wala kuwwata illah billah to shi dama bashi da lafiya ne kuma ya yarda aka aura mishi ita, ko ya abun yake?" Jummai ta tambaya cike da jimami, ita ko Turai salati kawai takeyi tana sanar ma ubangiji, "Ke Innah wai wannan maganar naki gaskiya ko wasa?" Turai ta tambaya itama dan wannan batu kam ai yafi kama da tatsuniya, jama'a inba tatsuniya ba a ina za'a kaima namiji mace kamar Meenal ace wai shekara da shekaru bai tab'a taba, "To dai kuma zaku gama jimami ne ku fuskanci gaskiya, domin ni tun shekarun baya na san da batun, to a lokacin tsakani da Allah na ta'allaqa hakan ne da sharrin matar shi dan kowa dai yayi mata shedar tsafe tsafe, bayan na qara binciken ita Meenal din ta tabbatar min da cewa ko d'aki guda basu tab'a had'awa ba sai na fara neman musu maganin karin asiri dana tsarin jiki, Bayan ni na saki jiki cewar ita tayi musu amfani da maganin kamar yanda na fad'a mata ashe ita shashashan iya wanda na ware a matsayin nata kawai tayi amfani dasu sauran kuma ta ajiye a gefe, to nidai tun sannan ban K'ara tambayan ta ya ake ciki ba, tunda dai kullum na tambayeta ya suke zaune cemin take lafiya lau, to indai yanke muku zance, Ke Jummai ai wajen ki ta fara sauka data shigo d'azun daga makaranta koh?" "Eh kwarai kuwa wajena taci abinci tayi sallah ma kafin ta iso nan" "Madallah to ashe wai bikin da akayi na k'annen mijinta ita kishiyar nata tazo kamar yanda ta saba...... Kaf abinda ya faru a yau din na zuwan Teemah gidan da kuma komawar da tayi gida ta cimma Sarki ba lafiya dama abinda likitan ya shaida musu harda had'uwar su da uwar gida kafin su baro gidan meenal tsaf ta kwashe ta rattafa musu " Koda ta gama koro musu bayanin shiru tayi suma ta basu damar tofa nasu albarkacin bakin, "ku dakata ban san ko kun hango abinda ni nike hasashe ba,"jummai ta fada, "Me kike hasashe ne?" Suka tambaya suna kallon ta dason jin me hasashen nata ya k'unsa, "A nawa hangen sai nike ganin wannan abun fa ba haka banza bane ya auku, tabbas akwai wata a kasa, tunda tun farko dama kowa yasan cewar matar shi matsafiya ce, bakwa ganin kamar itace ta aikata wani abun ta yanda shi bazai tab'a jin sha'awar ita Meenal din ba?" Turai ne ta amsa da cewa, "Ah ah Jummai babu wani batun asiri rashin soyayya ne kawai tunda gashi har likita ya tabbatar da cewa ciwon sha'awa ne ke damun shi, ita dai Meenal din itace ya jingine tunda ai gashi nan baro baro cewa da lafiyar shi" "Banki ta naki ba Aunty Turai amma nima nawa maganar tana kan hanya, saboda dai komai kiyayyar da miji yakewa mace akwai ranar da in sha'awa ta kamashi dole zai ture zancen wannan kiyayyar a gefe ne ya nemeta domin itafa sha'awa bata san yaren rashin soba inba haka ba dan me ake cewa ruwan kashe gobara basai mai kyau ba, Ko kun manta ne cewa in ana son a shiga tsakanin ma'aurata babu ta inda ba'a bi, *misali* *Wasu zakuga an sakar ma ita matar warin jiki*, *Wata matar kuma jini ake sake mata* *Wata ko tsoron mijin za'asa mata ta dunga kallon shi kamar dodo*, *Shi kuma wani mijin a duk sanda yaje kwanciya da matar sai ya rasa kuzarin shi na d'a namiji ta yanda bazai iya kusantar taba*, *Ko kuma ita mace a mata asirin da in mijin yaje neman ta sai gaban ta ya koma irin na namijin ko kuma wajen ma ya shafe gaba d'aya*, akwai hanyoyi da yawa da ake amfani dashi wajen dakushe alaqar aure tsakanin mata da miji, To ita dai Meenal din ina ganin in ba'a samu daya daga cikin abinda na lissafa a kanta ba to sai dai insha mijin ne akayi nasarar cire mishi sha'awar ta a duk sanda yake tare da ita.bari in kira Meenal din muji ta bakin ta" "Meenal" Hajiya ta kwalama kira, Jin shiru bata amsa bane yasa ta kiran Larai, "Larai haura sama ki kiramin Meenal ku sauko tare" Taren ko suka sauko. "Meenal zoki zauna anan tambayar ki zanyi" Hajiya Jummai tace, Zaman Meenal tayi kamar yanda ta buk'ata, "Ke takwara ina fatan dai baki kira kowa kika shaida mishi cewa kina gidan nan na d'auko kiba koh? " Hajiya innah ta tambaya tana kallon Meenal din. "Ban fadama kowa ba" "To kin kyauta ma kanki, kuma ki jini da kyau koda uwar kice ta kiraki bance ki d'auka ba dan nasan suna samun labarin bakya gidan zasu fara kira suji ba'asi kin san kuma ba uzuri zasu miki ba iyakacin suce ki koma, in kin koma koh kin san abinda kika baro nedai zaki tarar dan yanda shi mijin bai damu dake ba suma iyayen naki bana tunanin sun damu dake tunda har suka iya banzatar dake tsayin shekarun nan babu wanda a cikin su ya damu da sanin yanda kike rayuwa a gidan mijin da suka zab'a miki, gaba d'aya ma sun manta cewar auren dole suka mashi, to wallahi kinji dai na fad'a miki dan haka ko malam nema ya kiraki karki sake ki koma, in kuma kinsan kasa zaki watsanin a ido kina son mijin ki to tun kafin dare yayi ko kuma kizo daga baya ki kullaceni gara ki shaida min gasu Jummai nan su mai dake gidan ki atoh, dan ku yaran yanzun wani abun za'ayi dan a muku gata ku kuma sai kuga kamar cutar ku akeyi" "To ni Hajiya nace miki zan koma ne dama?" "Baki ceba amma ai gara in kara tabbatar wa a gaban su Jummai dan sumin sheda in magana ya tashi dan yanzun na tabbatar laifin duniya akaina kowa zai daura gani zasuyi kamar nice keson kashe miki aure, nasan babu wanda zaiyi la'akari da zaman da kikayi a gidan ba tareda wani abu ya gifta tsakanin ki da mijin ba, Kaini ai nagode allah da Allah yasa kaf cikin yarana da jikokin babu dan iska, Ku duba ku gani fa yanzun dan Allah in wata yarce aka ma irin auren nan hakan ya biyo baya mai kuke zaton zai faru? Ai wallahi tikitin iskanci ta samu kyauta, sai gashi jikata ko karar shi bata tab'a kaiwa wajen wani dan ya danne mata hakki ba, matan yanzun da ko mijin suka samu baya kai musu yanda suke so sai dai ku tsinci maganar a kotu anje gaban alkali batun kashe aure, in Kuma hakan bai samu ba shi kenan sai mace ta fara rab'e rab'e tana bin wasu mazan, allah dai ya shirya mana zuria" Ameen duk suka amsa mata dashi baki daya. "Meenal nace wani irin zama kikayi da mijin ki tsayin shekarun nan? So nike ki fad'amana komai bakin gaskiyar ki munan dukan mu babu wacce bazatayi tsaye wajen kwato miki hakkin kiba in munga za'a tauye ki, Fad'amin shi din kina jin tsoron shine shi yasa koya neme ki bakya yarda ko ya abun yake" Jummai ne ke tambayar ta. "To aini bai tab'a nema na ba wallahi, abinda shekarun baya ma ko sashena baya shigowa daga baya nefa inya shigo ya fadamin abinda yake buk'ata sai ya koma d'akin shi," "To ke da baya zuwa mai yasa bakya binshi can nashi d'akin?" "Kai" Meenal ta fad'a tana zaro ido waje, "Eh baki san in miji baizo inda mace take ba ita macen ba laifi bane dan ta bishi, ai babu laifi akan hakan ko kin tab'a zuwa ne ya koroki?" "Ah ah ni gaskiya ban taba zuwa ba, Kuma fa ko abu yace in kawo mishi da nakai yake cemin Ina iya tafiya" "Kenan dai kina so kice baku tab'a samun kusanci dashi ba kwataΒ²? " "Eh gaskiya bamu tab'a ba" "To me ya faru ayau da har yayi sanadin da ciwon shi ya tashi tunda dai likita yace ciwon sha'awa ne ya kama shi" Shiru Meenal tayi ba amsa. "Karkiji kunya ki fadamin gaskiyar abinda ya faru" A daburce ta fara ba da labarin yanda ta iske shi a kwance a kasan tile's yana murgine murgine dama yanda yaso kusantarta tak'i duk da bawai ta bud'e musu komai bane amma haka take magana kunya duk ya gama rufe ta. "Tashi ki koma d'akin ki" Jummai ta bata umarni bayan ta gama sauraren ta, aiko kamar jira take dama domin tuni tayi bacewar b'at a wajen. "Kun fahimci wani abu a labarin ta" "Yo mu me zamu fahimta ko , bayan kinsata a gaba kina mata tambayoyi irin naku na tsofaffin lauyoyi," Cewar Hajiya Turai, Yar karamar dariya Hajiya tayi sannan ta d'aura da cewa, "Kamar dai yanda na fad'a muku ne d'azun ni nafi zargin akwai shiga tsakani a zaman auren yaran nan to hakan ne, domin dai a bayanan ta na gane cewar kwata kwata shi mijin nata baya son kusanci a tsakanin su, yanzun Kuma da aka samu canji ina da tabbacin cewa tabbas akwai inda aka samu tangarda kodai asirin ya karye ko kuma an canza sabon salo," "Ba shakka hakan yana iya zama gaskiya, to yanzun wani mataki za'a d'auka?" Turai ke tambayan Jummai. "Da farko dai zanso a fara kokarin karya komai dake tareda mijin, sannan sai a d'aura shi akan magunguna na kariya, koda yake magani baya aiki sai mutum ya had'a da addu'a gashi shi kuma bamu san ya yake ba wajen kula da ibada, babbar damuwar ma yanzun yanda Hajiya ta d'auko Aminatu daga gidan ta, kunga koba komai da tana can komai zaifi zuwa mana a sauk'ake," "Ko yanzun bazai gagara ba dan jikata dai na d'auko kayata kuma bata komawa gidan nan, magani kuma tunda dama nayi niyya da zuciya d'aya nida kaina zai kai in damk'a a hannun uwar shi ita sai tasan ta yanda zatabi dashi har yayi amfani dashi, saki ne dai sai ya saki takwara ta karma kowa ya bani hak'uri" "Aunty Turai bakice komai ba" "To me zance Jummai bayan aikin gama ya riga ya gama! Tunda tace sai yayi sakin ai sai muyi fatan ita yarinyar Allah ya mata canji na alkhairi shi kuma allah yasa iya wahalar kenan, ita kuma matar indai ya tabbata ita keda hannu allah ya shirya ta" Sun tattauna sosai kafin taron ya watse, *** Salman bai d'auko sarki sun dawo gida ba sai bayan ishsha'i zuwa lokacin kuma jikin na Sarki alhamdulillah sosai yaji sauki kamar ma bashine aka kwasa ranga ranga zuwa asibiti d'azun ba, D'akin shi dake sashen Teemah ya shiga sai da yayi wanka sannan ya samu damar jero sallolin da ake binshi, Ba kowa yasan yana gidan ba sai iya yan d'akin su, sai da uwar gida ta tabbatar yaci abincin da tasa aka kai mishi ya kuma huta sannan taje d'akin ta same shi. Bayan sun gaisa ta mishi ya jiki ya kuma amsa mata da jiki yayi sauki ne ta miko mishi takarda da biron dake rike a hannun ta wanda dasu dama ta shigo d'akin, D'aure fuska tayi sosai dad'e duniya bata tab'a sanin yanda akeyin dariya ba. "Sufyaan Β³" Sai da ta kira sunan shi sau uku yana amsawa da "na'am" Sannan ta daura da cewa, "A duniyar nan kana da wata uwa data fini matsayi a wajen ka?" Duk da yanda zuciyar shi ke dakan lugude bai gaza amsa mata da cewa.. "Babu Hajiya" "Da kyau, kenan ina da ikon da zansa ka abu kayimin kenan?" "Kina da ikon kisani komai kike so inyi miki shi kai tsaye Hajiya indai hakan bai sab'awa shara'a ba" Kara bata tayi sosai alamun ba wasa, sannan ta matsar mishi da takardar da biron zuwa gaban shi, "Gashi nan sau nike in k'ara baka umarni kamar yanda na baka a lokacin da naso auren ka da yar uwar ka, yau ma ni din dai mahaifiyar ka ina mai baka umarni daka rubuta ma Aminatu takardar saki, domin yanke alaqar auren dani nayi silar had'ashi a tsakanin ku daga k'arshe kai kuma ka nuna min ban isa ba dalilin hakan ka ajiye yar mutane a gidan ka tsayin shekaru ba tareda ka tuna hakkin auren ta dake kanka ba, dan haka yauni zan sauke maka nauyin daka kasa d'auka, rubuta mata sakinta yanzun ka bani, bakuma nason saki d'aya ko biyu saki uku reras nike so ka zana a takardar gaban ka ka miko min nan, inyaso gobe sai ka had'a kayan ka kabi bayan matar so, na kuma gode maka allah ya saka maka da alkhairi ubana, ni dai bazan tab'ayi maka baki ba sai dai ina son in tuna maka cewa kana da yara mata gasunan saiti bida bi har su uku, ina fatan kar zunuban ku kaida uwar su ya shafi rayuwar su" Shiru gaba d'aya Sarki ya d'auke wuta dan bai tab'a hasaso ko tsammanin zuwan wannan ranar ba. "Ya ina magana dakai kamin shiru?" "Dan Allah Hajiya kiyi hak'uri ki gafarceni, insha Allah na miki alkawarin gyara tsakanina da ita, karkice in saketa ban san da wani idon zan kalli Baba Malam ba........ Kuci shi da hak'uri in anci karo da mistake a tsallake dan banyi editing ba, *UMMIEE ZARIA*✍🏼 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: πŸ”±βšœοΈπŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *DANGINA!*πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦βšœοΈπŸ”± ~{{MY FAMILY}}~ *FREE BOOK* *RUBUTAWA* *UMMIEE ZARIA*✍🏼 ```` *Page 44*..... "Dan Allah Hajiya hakuri ki gafarceni,nasan ni mai laifine a gareku,na kuma cancanci amsar hukunci daga gareku na abinda na aikata,amma insha Allah na muku alkawarin gyara tsakanina da ita,zanci gaba da zaman aure da ita a matsayin cikakkun miji da mata, ina rok'on alfarman ku karkuce zaku shige gaba wajen raba auren nan, in hakan ya faru ban san da wani idon zan kalli Baba Malam ba." Katse shi uwar gida tayi a fusace jin wani sabon salon rainin wayau da yake shirin bijiro mata dashi, inba rainin wayau ba da can daya ajiye d'iyar mutane a gidan nashi ya kuma wofantar da ita da wani idon yake kallon iyayen ta? "Oh sai yanzun ne ka tuna da wani idon zaka kalli shi wanda ya baka ita a matsayin matar?, Ka daiji kunya wallahi Sufyaan ka fad'i kasa ba nauyi, a zatona koda ace ni banci darajar haihuwar kaba shi Malam zai iya cin darajar da Allah ya bashi na zamowa tamkar uba a gareka duk da cewa bashi ne ya haifeka ba, yarinyar nan kowa ya shaida kaunarta da Malam keyi amma a cikin jerin maneman da suka fito neman auren ta duk ya shallake sauran ya baka ita, Kasan tsayin shekaru nawa mukayi nida mahaifin ka mukayi muna bibiyar shi akan ya baka auren ta kafin ya amince? Nayi zaton cewa ba Aminatu da take matsayin yar uwa kuma kanwarka ba koda ace acan gefe na koma na d'auko maka wata nakasasshiya kai mai tara hannuwan ka bibbiyu ne ka amsa ka kuma riketa da amana, Kullum akayi haihuwa a cikin Dangi sai anyi batun Aminatu wasu na ganin cewar Allah ne bai kawo nata haihuwar ba yayinda wasu suka ta'allak'a rashin haihuwar nata da tsarin rashin haihuwa takeyi, Surutai babu irin wanda ba'ayi ba yakai tun anajin kunyan ayi shi a gaban makusan ta sai gashi ya koma harta da uwarta mahaifiya bata tsira ba, Kasan meye abun takaicin? Ni din nan da kaina nasha zuwa inje in amso taimakon neman haihuwar in kai mata har gida, wanda ni a nawa zaton ko ciwon da kowa yasanta dashi na mara shine dalilin jinkirin haihuwar nata, Idan na tuna hakan a yanzun har kunyar kaina nikejin yana kamani, idan ba ita d'inba wace yarinyar ce zata yarda a zauna a gaban idon ta a yad'a mata maganganu irin wanda yan uwanka ke mata akan cewar tak'i haihuwa, Amma yarinyar nan da yike takance matar rufin asiri ko sau daya bata tab'a tunanin cewar zata tona abinda ke binne a tsakanin ku na tsayin shekaru ba ta gwammaci tayi ta had'iye komai ita d'aya, dan haka wallahi bazan k'ara yarda in jagoranci cin zalin d'in daka mata a baya ba domin ko inda ace d'aya daga cikin k'annen Kane hakan ya sama kaima nasan bazaka bari ba, Ba kuma nazo jin ra'ayin bakin ka bane ko kuma ban hakurin ka nike buk'ata ba! Ah ah takarda dai zaka rubuta min yanzun basai an kwana gari ya waye ba, in yaso daga goben kana iya bude kofa ma masu zuwa maka jaje domin kaine ka tafka asara ita kam murna ya dace aje mata dan ina mata fatan samun wanda ya fika kodan albarkacin biyayyar da ta d'aure tayi ma iyayen ta na zama a gidan ka tsayin shekaru ba tareda ta nuna gazawa ko kuma ta ce zata bud'e sirrin ta ma wani, kai koh ni bazan maka baki ba sai dai ka sani yan magana kance ruwa cikin cokali ya isa mai Hankali wanka" Duk yanda Sarki yaso ya k'are kanshi da son ta fahimce shi Sam uwar gida ta rufe ido tama hana shi magana, to me zaice mata bayan ya gama nunawa duniya cewar ita din bata isa ba, domin ai d'an daka isa dashi bazai maka haka ba, Saki d'aya ya zana a takardar sab'anin ukun data buk'ata, copy biyu tasa ya rubuta ta rik'e daya a hannun ta d'ayan kuma tace ya rik'e a hannun shi gobe in gari ya waye yayi sammakon zuwa Tudun wada yakai ma Meenal d'in domin dai tuni tayi gaba Allah kuma yasa hakan shine mafi alkhairi a garesu, bata bar d'akin ba sai da ta k'ara jaddada mishi cewar karya sake wani yaji zancen sakin nan har sai bayan ya isar ma Meenal da takardar ta, kuma ko bayan hakan bata yarda in magana ya tashi iyaye sunce ya maida ta ya amsa cewar ya mayar da ita d'in ba gara ma ya h'ada ina shi inashi yabar garin a goben, Wannan dare a wajen Sarki da uwar gida kai tsaye zamu iya kiran shi da bakin dare, Domin dai kaf a tarihin rayuwar ahalin su ba'a tab'a samun kaddarar data gifta na sakin aure

Chapter 38 of 92