Share this page
tasan za'ayi haka, wai mema ya sashi biyota har makaranta ne? "Lafiya lau Dr ya kike, ya school d'in naku?" "School Alhamdulillah barka da zuwa ya hanya?" "Alhamdulillah na iso lafiya, hanya kuma yana can mun baro musu, Me kuke shiryawa ne haka naga kina tayin dogon list?" "Surprise zamuyi ma amaryar ku, abubuwan da muke buk'ata na program din da muka shirya zamuyi anan cikin school ne nike rubutawa saboda karmu mance da wasu abubuwan, Me za'a kawo maka ?" "Ni bana buk'atar komai naci anan wajen balle kuma kafin in fito ma sai da Hajiya ta bani abinci naci, ke kawai nazo gani dan bazan iya jira har sai kin koma gida kafin in samu damar kallon wannan kyakyawar fuskar taki ba tashi muje wajen nan babu dad'in zama sam!" Ya fad'a a yayinda ya kai yatsar shi ya lakaci gefen kuma tun ta, "Ina zamu kuma?" "Kaiki zanyi in siyar dake" "To ni ai nazo cin abinci ne anan yunwa fa nike ji!" "Naga alaman hakan shi yasa nake son in kaiki inda zakici abincin a tsanake ba nan wajen da yake da hayaniyar mutane da yawa ba, Yama zaki zauna cin abinci anan bayan ga maza nan da yawa duk sai kallon ki sukeyi, Baki san hakan yana da had'ari ba ai baima dace ki zauna kina tauna abinci a bakin ki maza na kallon yanda bakin naki ke taunar abincin ba dan ba kowa bane yake da tsarkakakkiyar zuciya ba, kenan haka kike zuwa nan kullum da sunan cin abinci? " K'asa yayi da murya sosai ta yanda bai zama lallai taji mai zaiceba kafin ya k'arasa maganar shi da cewa, "Yarinya baki san wani jarababben daga kallon yanayin yanda bakin ki ke motsi ma kad'ai yana iya samun gamsuwa ba" "Na'am me kace?" "Cewa nayi kenan kullum anan kuke zuwa cin abinci?" "Ah ah ba kullum ba lokaci lokaci dai" "To na kashe zuwa wajen nan da sunan cin abinci daga yau, Bazan hanaki kizo kiyi take away ba amma dai ban yarda kizo ki zauna kici anan d'inba kinji na fad'a miki" "To saboda me zaka ce haka ai bani kad'ai nike zuwa ba, in ma kallo ne ba gashi nan ba kaima daga zuwan ka duk kabi ka d'auke hankalin yan matan wajen kalle su ka gani fa dukan su idanuwan su akanka yake ni ban san ma mi yasa ka biyoni nan ba" Ta fad'a tana juya idanuwan ta gefe da gefe harda wani tura baki, "Koma ke da waye ni dai ina rokon alfarma kiji tausayina ki rufamin asiri ki dena zaman cin abinci a wajen nan, Nifa inda hali ma gara ki dunga zuwa da abinci daga gida kinga nifa in abun ya zama haka zan ma Hajiya magana ta d'auki wata sabuwar mai aikin da zata dunga tashi da sassafe tana had'a miki abincin da zaki dunga zuwa dashi makaranta tunda naga aikin yana son yama Aunty Larai yawa amma bazan yarda kici gaba da zuwa irin wajen nan cin abinci ba nagode Allah ma kun kusa kammala karatun madai mutum ya huta " Yana karasa fad'in hakan ya mik'e ta bayan kujeran ta ya koma ya tsaya kafin ya sanya hannayen shi yaja kujerar da take kai din a zaune baya, Zabura tayi ta mik'e tsaye daga zaunen da take dan tasan dan k'ank'ani ne cikin aiyukan da zai iya aikata wa wato yace zai kama kafadar ta ya mik'ar da ita tsaye ko kuma dai wani abun makamancin hakan, "Ina zaka kaini to? Nidai ban zuwa ko ina gida kawai zan tafiπŸ˜’" "Ni kuma nace ba gida ba wani waje zaki rakani" Jakarta ya mik'a hannu zai d'auka tayi saurin d'auke Jakar ta rataya a kafad'a, "Ok muje to tunda bazaki bari in rik'e miki Jakar ba" Karasawa inda su Maryam suke sukayi, Sultana ce ta fara gaishe shi da cewa, "barka da zuwa Brother ya hanya?" "Alhamdulillah Sultana ya kike?" "Ina lafiya! " Ganin haka yasa sauran yan matan dake wajen suma suka dunga tasowa suna mik'o gaisuwa bai damuba haka yaci gaba da amsa musu sai dai tsaf yake lura da yanda yanayin fuskar Meenal ya canza dan haka sai kawai ya waske da cema Sultana d'in idan ta gama abinda takeyi tazo su tafi, "Ah ah Brother kuje kawai nida Maryam zamu wuce unguwar Malamai ne daga nan zamuyi amfani da motar Meenal din kai sai ka wuce da ita" "Alright to ba damuwa sai kun dawo muje koh! "Nidai dan Allah ka tafi nima zan bisu muje can din tare kaji" "Ai kinji abinda Sultana tace dan haka kodai ki taka mu tafi ko kuma in nad'e hannun rigana in miki irin d'aukar da akema Jarirai, wai bana ce miki saboda ke na shigo cikin school din nan yauba, to wallahi in ma bakya so su kawayen naki su gane alaqar dake tsakanin mune gara tun wuri ki bini mu tafi salin alin sab'anin hakan kuma bazan bar nan ba har sai na tabbatar da nabar musu labari mai armashin da zasu dad'e suna tattaunawa akai kafin in tafi," Bata da wani zab'i wanda ya wuce ta bishi d'in, Dan haka badan taso ba haka su Sultana suka musu rakiya har zuwa inda yayi parking motar shi, shi da kanshi ya bud'e mata gidan gaba ta zauna kafin ya zagaya ta gefen driver yaja motar suka fice daga cikin school din. Maryam da Sultana dake tsaye a wajen har yanzun sun juya da niyyar komawa dan akwai sak'on da Maryam zata amsa kafin su wuce juyawar da Maryam tayi idonta ya sauka akan Bash jingine da motar dake gefen su kad'an hannuwan shi rungume a k'irji idanuwan shi kyar a kansu, Basarwa taso tayi ta nuna kamar bata ganshi ba sai dai kuma shi d'in duk da halin shock d'in da yake ciki na ganin Meenal hakan bai hana shi kiran sunan ta ba domin koba komai yana buk'atar tabbatar wa akan abunda idanuwan shi suka gano mishi, "Maryam" Ya kira sunan yana takowa da d'an sauran karfin daya rage mishi zuwa inda take, Bata iya amsawa ba har ya cin musu, "Maryam fad'amin dagaske Meenal ne idanuwa na suka gane min ko wata daban? Meenal na gani yanzun nan fa tare da wannan yayan nasu me nene ma sunan da ake kiran shi dashi? Uhmm uhmm mai jama'a, eh mai jama'a shifa, wallahi da idona na gansu yanzun nan ya bud'e mata murfin mota bayan ta shiga shi kuma ya shiga gefen direba yaja motar suka tafi, Mai yake faruwa ne? Dama shine mijin da aka aura mata ko ya abin yake shin ko dai gizo ne ko kuma mai Kama da ita na gani? Fadamin dan Allah kicemin ba ita bace mai kama da ita na gani ayau, inba haka ba mai zaisa inga Meenal anan bayan an tabbatar min da cewa wani d'an uwanta soja aka aura mata kuma ba anan zasu zauna ba?miye had'inta da mai jama'a kuma? " Juyawa tayi bayan ta damk'o hannun Sultana da niyyar subar wajen ganin yana shirin janyo hankalin mutane kan su, Da sauri yasha gaban su yana had'a hannuwan shi, "Please Maryam dan Allah ki tsaya kibani amsar tambayoyi na kaina ya d'aure da yawa, Meenal fa idanuwa na suka gane min bayan tsayin shekarun dana d'auka ban sata a cikin kwayar idona ba" Sultana ce ta katse shi da cewa, "Da kata dan Allah bawan Allah ya zaka zo ka taremu a hanya cikin mutane haka, duba kaga yanda kasa jama'a ke kallon mu in ma maganar da kake son yi da ita ya zama dole ai ba anan ya kamata ka tsareta da tambayoyin ka ba sai dai bari ni in sauk'ak'a mata wasu rud'anin da kake ciki a yanzun, Eh ita Meenal din dai ita ka gani sun fita tare da mijin da zata aura a yanzun duk yanda akayi alamu sun nuna cewa kana cikin samarin ta da aka kasa a shekarun baya, to ko yanzun din ma bana tunanin zaka samu galaba ko nasara a kanta domin kamar yanda wancan karan d'an uwanta ne yayi nasara a kanka wannan karan ma hakan ce zata k'ara faruwa dan haka gara ka shafama kanka lafiya Kaje kaci gaba da zama da yar matar ka ina ga hakan zaifi, Meenal ba rabon ka bace shi yasa take ta kucce maka, Maryam idan kin gama abinda kikeyi muna iya tafiya." Kusan sumewa yayi a tsaye bai iya motsawa ba har suka kule ya dena ganin su, "Ke wai waye wancan d'in?" Sultana ta tambaya, "Bash ne bash din da nace muku mun had'u dashi s kofar doka shine tsohon saurayin Meenal kafin auren ta da Sarki, Ban san meya shigo yi cikin makarantar nan yauba gashi duk addu'ar da mukeyi na kar Allah yasa ya bayyana to yau dai gashi ya ganta, na kuma tabbatar da cewa wallahi sai ya nemo ta" "Bash.... " Sultana ta maimaita sunan tana jin jina kai, "To ai ya riga ya makaro ko yanzun muke da nasara akan duk ma wanda zai bayyana bayan shi, Domin dai koda bata riga ta furta ma AK cewa itama tana son shiba ina tabbatar miki da cewa akwai son shi a cikin zuciyar ta dan haka kowa ya iya allon sa ya wankeπŸ€·πŸ»β€β™€οΈ" Basu b'ata lokaci mai tsayi a makarantar ba suna amsan abunda Maryam zata amsa suka bar makarantar, kamar yanda shima Bash yabar makarantar ba tareda yayi abinda ya kawo shi ba, dan ganin daya ma Meenal yasa komai ya kwance mishi, Tsayin shekarun nan yayi hakuri da sonta ne kawai tun daga ranar da akace an d'aura mata aure da wanin shi, Ba k'aramin gwagwar maya yayi tsakanin shi da zuciyar shi kafin ya samu damar mai da son Meenal din can k'asar zuciyar shi ya nemi waje ya birne son nata a ciki ba, Yasa wuya yasha jinya yasha fama har sai da yayi jinya na watan ni saboda yanda batun auren ta ya mishi mugun bugun da dole ya kaishi k'asa war was, Yaci buri akan ta burin auren ta wanda a wancan lokacin shine buri mafi girman da yake kwana ya kuma tashi dashi a cikin zuciyar shi, sai gashi kwatsam wai bai tashi jin cewa ita d'in za'a d'aurama aure da wani ba har sai ranar d'aurin auren, Da badan yana da tabbacin cewa ita ma kanta bata da masaniya ba toda tabbas zaice babu namijin da aka ma mummunar yaudara irin shi, Saurayin daya riski labarin auren budurwar shi a yayinda ya shirya zuwa wajen d'aurin auren a matsayin zashi auren kannen ta, Kai shifa wallahi bai taba jin labarin soyayya irin nashi ba. Bayan fitar AK ba dadewa Ya Sa'eed ya isa gidan Hajiya, Bayan sun gaisa ne yake ce mata, "Hajiya akwai sak'on da Sarki ya wakilta ni in ba takwarar ki, Sai dai halinta dana sani shi yasa nace gara in fara zuwa wajen ki muyi shawara kafin in gabatar mata da sakon, nasan ke zakifi ni sanin yanda zan shawo kanta!" "Too sak'o kuma?" Gyara zama yayi kafin ya d'aura da cewa, "Hajiya nasan kin san burukan da Meenal take dasu a rayuwarta, Zuwa yanzun Alhamdulillah zamu iya cewa biyu daga ciki sun cika to cikon na ukun ne shi yake son cika mata, Gidan data tashi da burin ta ginama Baba Malam ne shi Sarki ya siya da sunan ta, Babu wanda yasan da batun siyan gidan daga shi saini daya damka ma amana saboda baya son kowa yasan cewa shi ne ya siya gidan, sai kuma ke da yanzun nike fad'amawa, Na fara zuwa wajen kine dan nasan ke zaki san dubarar da zamuyi wajen ganin Meenal ta amsa dan nasan halin ta tana iya cewa bazata amsa ba dan tuntuni take tarin kud'ad'e saboda ta siya filin da zata gina gidan. *UMMIEE* [9/15, 10:36 PM] Ummiee Zaria: βšœοΈπŸ”±πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *DANGINA*πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ”±βšœοΈ *BOOK 2* *PAGE 29* Babbar magana! Ashe dai yaron nan d'an kwarai ne kawai rik'on sakainar kashin da yayi ma auren su ne ya hanani gano kyawawan halayen she, to wai dama can haka yake da hannun kyauta amma ni ya wofantar dani ko kodai yanzun ne ya canza? Allahu akbar in ba d'an daya gaji arziki tsiya na kwance kwancin kwana ba wani mijin ne zai dunga bin macen daya saka da alkhairi kashi da kashi a jejjere irin haka? Kaga fa dank'areriyar k'atuwar motar daya bata a ranar daya kawo mata takardar freedom d'inta,wanda nasan wannan toshiyar baki ne bayan shi ga kuma wasu miliyoyi daga zuba mata a k'atuwar envelop su wad'annan dai tuni na canza su na tura can Saudiya wajen matar kawunta suka siya mata zinare suna can banki na kai ajiya, Shine kuma bai gaji ba yanzun ya biyota da wani alkhairin har gida, kai yasa wannan abu dai wallahi dan an riga anyi an gama ne amma da koni ina iya yin tsaye a maida mishi matar shi,kaga shi yasafa ake cewa gaggawa aikin shed'an, To aikin shed'an ne mana inba haka ba dubi kaga tsayin shekarun da sukayi da aure amma duk bai iya kyauta ta mata irin haka ba balle nima in gani in yaba, Inda hakan yakeyi tun farko ai da tuni kila sunyi haihuwa uku ko hudu kamar dai ku da kukayi auren tare dasu, ko yanzun ma kuma bazan mishi bak'in ciki ba wallahi tunda shima baiji bak'in ciki ba yake ta hidima da takwarata ubangiji Allah dai ya saka mishi da aljannah mafificiya Allah kuma ya bashi damar yin wani auren dan inbai k'ara aure ba tofa sam bai more rayuwa ba wallahi dan dai waccen shegiyar matar tashi Allah na tuba tooo Allah dai ya shirye ta in tana da rabo a aljannah kaga ko a ciki da falo ta zauna kasan ko ciki da falo a aljannah ai tayi girman Kaduna state da kewayen ta badan halin taba, Badai zan mishi baki ba amma dai zanje har gida inba ita uwar shi shawara ta k'ara dubawa tacan gefen ta ta nemo mishi wata matar tunda abun ya zama haka, ga dai ku da kanne mata a gida amma nasan ubanku bazai yarda ya k'ara bashi wata yar da sunan aure ba nikuma kaga duka jikokina basa kusa ai da na mishi had'i da wata ko za'a dace ko nima ba sai inyi ta dangwalan arziki ba! , Kai koh anyi kyautar gida da mota mai ya rage, next agenda kuma ai sai dai kaji anyi kyautar kujerar makka ina fad'a maka wallahi" Sosai fa Hajiya ta zage tana ta faman zugagama Sarki ruwan addu'a da sanya albarkha, duk ta mance komai da suka faru a baya alkhairin shi a yanzun duk ya goge komai. Shidai Sa'eed tunda Hajiya ta fara rattafo zantukan ta dariyar ta kawai yakeyi k'asa kasa, shi din ba bak'on ta bane yasan halin ta ciki da bai, "Hajiya to yanzun ya za'ayi?" "Ya za'ayi kuwa d'an nan wannan kyautar ai tunda har ta shigo gidan nan kuma ai bata fita wallahi, Dafari dai ka fara bani takardun in tabbatar na jimk'e su a hannu na tukun dan gara in jisu a tafin hannu na ta yanda ko addu'a na sun isa sama nasan bazasu dawo k'asa ba, Maganar Meenal kuma kadai ce amana shi Sarki ya baka baka son kowa ya sani koh?" "Kwarai Hajiya saboda ya yarda dani shi yasa ya damk'a min amanar komai a hannuna dan ko k'anin shi da suka fito ciki d'aya bai yarda yasan da batun siyan gidan ba saboda baya son maganar ta fita ta koma kunnuwan dangi" "Ya kyauta kuma nima ina mai tabbatar maka da cewa zancen nan zai tabbata ne a tsakanin ni da kai sai kuma ita mai gidan da zan shaida mata gaskiyar cewa Sarkin ne ya siya mata gidan daga baya, Yanzun abunda za'ayi kasan dama nace maka kayan d'akin ta da kud'in dashi Sarkin ya bata sune na siya mata gwala gwakai koh? To idan tazo zan damk'a mata takardun nan a matsayin cewa da wancan kudin ne nayi amfani aka siya mata gidan, Kaga daga baya idan ta gabatar ma da Malam gidan sai a fad'a mata gaskiya nasan zuwa lokacin in taji gaskiya ba zatayi bori sosai ba, amma yanzun in har aka ce mata Sarki ne ya siya gidan kachokan ba lallai nema ta amsa ba dan wani zubin itama tana tab'a bak'in hali na gado atoh" "Eh kuma fa Hajiya kema kina da gaskiya, in haka ne ai gara in yi saurin barin nan d'in kafin ta dawo da dai naso in jirata dan akwai maganar da nike son yi da ita?" Takardar ya mik'a mata ita kuma tasa hannu biyu ta amsa da bismillah, "Allahu Akbar kabiran Allah mai maida Sarki bawa, bafade kuma ya zamo sarki yau dai gani rik'e da takardar gidan takwara ta a hannu na, ko ya zatayi idan taga takardar nan, Amma fa Sa'eed wannan harkar naku akwai son kai a ciki, Banbanci zallah ake nuna min ganin idona, Wato yar nan dai tun tashin ta duka burin ta na duniya akan Malam almu ya k'are ni kuma ko oho, da alama dai mantawa takeyi cewa ni dai nice na haifi uwarta Yar banza kullum kuma nan take zuwa tana amshe min yan kud'ad'en da d'iyana suke bani na kashewa, zata zo ai yau dai duk tsiyar ta sai ta bani tukwuici wallahi kafin in bata takardar nan nima," "Kwarai ina bayan ki Hajiyar mu dan tabbas kin cancanci tukuici mai girma wannan karon, kinga idan ta baki nima sai ki fincino min kad'an kaga ciki insamu nasa mai a mota" "Kai tafi can wani rashin tsoron Allah ne zai sa in baka kud'ina kuda kud'i basa isan ku iyaye sun tara muku amma kuma kun kasa hak'ura kullum cikin neman su kuke in anyi magana kuce wai kogi baya k'in k'ari, To ai sai kuyi ta faman tara su a account sai kun mutu a kasa lissafi wasu kudin ma baza'a tab'a sanin inda kuka kai kuka boyeba, yanzun dai jirani in kawo maka sak'o ka kaima jikokina a toh," Da kanta ta ciccib'a ta mik'e ta nufi kitchen d'inta bata fito ba sai data shak'o k'atuwar leda taf da kayan kwalam da mak'ulashen da Meenal takeyi ta ajiye musu. "To gashi kuma ban yarda ka bud'e ba nima amana na baka atoh karma kace ban fad'a maka ba, Amma dai tunda kazo gara ka jira dawowar nata dan nasan ta kusa dawowa tunda kaga yamma tayi, Kaga na tuna kuwa, nace injin dai shi Baban naku bai riga ya fara amsa tayin mutane akan ta ba?" "Wa kike magana Hajiya?" Shima ya tambaya dan bai gane kan maganar nata ba, "Ina nufin manema auren ta mana!, dan kasan halin uban nan naku kar azo ni ina nan zaune da yarinya a gabana azo a k'ara mai maita min abunda ya faru sai aure ya rage kwana kad'an azo a shaida min" "Anya kuwa gaskiya da wuya dai, Na daiji ana maganar su Fauxieyerh da sauran yaran amma banji an ambaci sunan ta ba, Sai dai kuma koni ta nan gefe na akwai mutum biyu da suka min magana a kanta, yana daga cikin dalilin ma da yasa nike son yin zama da ita, saboda dukan su suna son gabatar da kansu a gaban Malam nine na dakatar dasu saboda nasan in sunje shi zai sasu a sahun mane ma ne, Amma in suka fara gabatar da kansu a wajen ta kinga ita zata tantance da kanta zata zab'arma kanta wanda ya cancanta," "Babbar magana wannan shine ake cewa ana wata ga wata! Kungani koh, ai dama nasan za'ayi hakan shi yasa nike ta son ganin ta mai da hankali ta tsayar da tsayayye dan nasan mai hali baya fasa halin shi, To ai ba iya gefen ka ni kaina nan ina da tsayayye gangariya anan gefe na sai dai ita kuma yar tutsun ne har yanzun ban gane ina ta dosa ba, Abinda za'ayi yanzun su biyun nan da kace, Nan dai zaka fara turosu suzo su gabatar da kansu a wajen ta, saboda wani dalili nawa, sannan karka yarda koda wasa ka bari zancen neman da suke mata ya isa kunnen Malam zanfi so zancen ya tsaya a iya nan," Hajiya sun dad'e suna tattaunawa da Sa'eed duka maganar kuma akan Meenal ne da samarin da suka fara kunno mata kai dan ta gefen Sa'eed din dai mutum biyun da yake magana dukan su yan uwanta ne, Aliyu yaron Maman kano ne shike bin Abubakar tsohon saurayin Raheenat a Yola yake aiki zuwa gaisuwar nan na mutuwar mijin Raheenat ne yaga Meenal d'in, Sai kuma Hashim shi kuma yaron yayan innar yara ne in baku manta ba a baya na fad'a muku cewa duka matan malam biyu auren zumunci ne dan haka suma Hashim da Aliyu dai dukan su yan uwan Meenal ne na kusa, Su kuma abinda yasa suka fara tunkarar Sa'eed da zancen son auren Meenal din saboda shiri da sukaga yana yi da Meenal din sosai shi yasa suke son suyi kamun k'afa, Hajiya ta dade zaune tana cigaba da nazarin yanda zata bullo ma al'amarin nan bayan fitar da Sa'eed yayi zuwa gidan su Billy, Duka dai wadanda Sa'eed ya gabatar mata yan uwan Meenal din ne na jini kuma dukan su biyun a cikin su babu na yarwa, To su biyu gashi sun fara bayyana tun yanzun a hakan ma iya su ta sani bata sani ba ko a gefen iyayen ta maza wasu ma sun kai nasu k'ok'on baran akan su ko yaran su, Idan fa tasa ido tabbas abubuwa zasu lalace ne zuwa gaba kad'an, kuma dai ai duk dad'in inuwar gemu bai kaiga mak'ogoro ba, Dan haka zatayi amfanin da wannan damar na zuwan da su Baba Usman zasuyi bikin Musty gara su tura su kawai suje su nemo ma AK auren Meenal din a wajen iyayen ta maza kafin abubuwan su cab'e dan tasan har wad'ancan suka gabatar da kansu tofa shi malam nashi yan uwan zai d'auka ita nata jikan ko ohoπŸ€·πŸ»β€β™€οΈ" A gefen AK ko duk yanda yaso yaga Meenal ta saki jiki dashi abun ya faskara, dan tunda ta shiga motar duk surutan da ya saki baki yanayi bata wani amsa shi daga umh sai umm umm sune amsar da take bashi, Dan itafa gaba d'aya a takure take saboda ita sam bata saba irin wannan rayuwar a tsakanin su ba, Ita dashi sun saba kullum ne da zarar sun had'u fad'ane abunda yafi yawa a cikin hirar su, yau kuma ya d'auko ta yana ta faman yawo da ita ta ina zata sake fisabilillahi ga wani Mayan kallo mai kashe jiki da yake binta dashi dan haka ba k'aramin takura tayi da zamar motar ba, "Ya'ya dan Allah nidai muje gida, Allah bana ma jin yunwar a yanzun idan munje gida zanci a can" Ta fad'a ganin yana shirin yin parking a kofar wani k'aton restaurant, "Karki damu ba shiga ciki zamuyi ba zanyo miki take away ne sai mu wuce gidan, ai na fasa zuwa sai dake d'in kuma dan haka ki kwantar da hankakin ki Dr zamu rayu a tare har tsufa insha Allah, Yanzun fad'amin mai kike son ci? Ko duk abinda na amso miki babu damuwa?" Ya tambaya yana kashe mata ido d'aya, Ita gaba d'aya ta rasa gane dalilin da indai suna tare bashi da halin da zaiyi magana da ita kai tsaye har sai ya had'a da d'age mata gira, Shi bai san hakan da yakeyi kunya yake bata ba gashi kuma a d'an lokacin itama ta koya ko magana sukeyi

Chapter 66 of 92