Share this page
da su Sultana sai tayi ta wani d'age musu gira kamar wata yar iska, "Ka bari dan Allah! Kana sawa ina jin wani iri wallahi," Bayan shi ya maida kan kujerar motar yayi relax kafin ya bude baki murya can k'asa yana ci gaba da kallon ta yace, "Mai zan bari kuma?" Dage girar da kashe idon ta kwatanta mishi, kafin tace hakan da kakeyi, Tana k'ara d'age giraren ta, Ba kad'an ba hakan da tayi ya k'ara tsatso mata kyan daya k'ara tafiya da hankalin shi, Shidai wallahi komai tayi k'ara kyau take a idanun shi dan haka bayajin gajiya ko damuwa sam a duk sanda zai kasance tare da ita, "Kina da kyau πŸ‘ŒπŸ»" Ya fad'a yana kwatantawa da hannu, ita kuma sai tasa hannu ta rufe fuskarta saboda kunya ma ya bata wallahi, Dariya yayi kafin ya tashi ya zauna ya bud'e k'ofar motar, "Ki zauna a cikin motar karki fito fa, yanzun nan zan dawo" Da kallo ta bishi tana jin wani irin abu wanda a tsayin rayuwarta bata tab'a jin wani abu makamancin hakan idan tana tare da wani ba sai shi, Shi kad'aine namijin da idan tana tare dashi a cikin zuciyar ta takejin kamar an cire mata ko wani kalar damuwa, Nutsuwa takeji da salama a duk sanda suka kasance tare ba kuma zata iya cewa ga dalilin da yasa takejin hakan ba, amma tana jinta a yanayin da zuciyata ce kad'ai sheda akan yanda takejin bata sani ba ko hakan yana daga cikin alamun kamuwa da soyayya, in ko hakan ne sai tace akwai matsala dan itafa wallahi bata shirya ba, Sam sam sam bata shirya maida hankali akan soyayyar ko wani namiji ba, tana buk'atar isashshen lokaci kafin ta kamu da son wani, Ta sani cewa idan har tayi saken da AK yayi galaba da sauri haka a kanta tofa itace zata sha wahala, Natsuwa take fatan samu bayan aurenta bawai auren da zatayi ta gwabzawa da wasu matan akan mijin auren taba, "Ya dai tunanin me kikeyi haka ne?" Ya tambaya jin yayi mata sallama har sau uku bayan shigar shi cikin motar amma bata amsa ba, duk da idanuwan ta suna rufe yasan cewa bai isa ace daga shigar shi zuwa yanzun har tayi bacci ba, Jin shiru bata amsa bane yasa ya mik'a hannun shi duka guda biyun ya ware yatsun shi manuniya ya dannasu akan kuma tunta dai dai inda dimples dinta suka lotsa, "Auch" Ta fad'a tana ware idanuwan ta akan shi, "Ke dai raguwar likita ce wallahi kawai daga shigana shine kafin in fito har kinyi bacci, ko bakya da lafiya ne dan nasan yawon shirin bikin nan bazai barki ki zauna ki huta ma ranki ba" Sai da ta gyara zaman ta kafin ta amsa mishi a shagwab'e da cewa, "Ai tun d'azun sai da nace maka ka kaini gida kak'i" Waiyo Allah yarinyar nan wai me yasa bata neman zaman lafiya ne ita, Fisabilillahi sai ta sashi a gaba tayi ta mishi shagwaba tana kassara shi da salon ta, Wannan ma ai d'aukar alhaki ne wallahi, "Ki dena min wannan abun idan muna tare!" Ya fad'a yana sauke ajiyar zuciya a jejjere, "Me nayi😳? " Ta tambaya tana zare ido, "Ba komai, zaki iya tuk'amu zuwa gida?" "Ni kuma? To ba kai ke tuk'in ba tun d'azun" "Eh nagaji ne yanzun bazan iya jan motar ba, ki daure ki mai damu gida" Bude k'ofar gefen ta tayi ta fita ta zaga zuwa driver seat shi kuma tsallakowa kawai tayi ya koma inda ta tashi ba tareda ya fita daga cikin motar ba, Ruwa mai sanyin daya shigo motar dashi ya bud'e ya kafa kai sai da yasha kusan rabi sannan ya zuba wani ruwan a cikin hannun shi ya dunga zuba su ta saman wuyan shi suna gangarewa cikin jikin shi ita ta tuk'a motar har gidan Hajiya a yayin tafiyar su ta komawa ko zaman shiru akayi a motar shi dai lafewa kawai yayi yana binta da mayun idanun shi, har sai da ta gaji ta mishi magana akan kallon yayi yawa kafin ya juya ya maida fuskar shi gefe yana kallon mutanen dake kai da kawo a titi. *Ummiee ce* [9/18, 2:40 PM] Ummiee Zaria: βšœοΈπŸ”±πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *DANGINA*πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ”±βšœοΈ *BOOK 2* *PAGE 30* Bayan ta faka motar a inda ya dace ta yunk'ura tana shirin bud'e k'ofar gefen ta dan ta fita a motar shi kuma yayi azamar rik'o hannun ta wanda hakan ne yasa dole ta dakata ta maida kallon ta kanshi, Girar ta d'aya ta d'age mishi tana juya yan yatsun ta alamun tambaya ba tareda bud'e bakin ta tayi ko wani furuci ba, "Saurin me kikeyi ne wai? Duk kin wani k'osa ki shige ciki ki barni ko! saboda kin gaji da ganina? " Ya fad'a batareda ya saki hannun ta daya rik'e ba, Kauda kanta gefe tayi tana basarwa, "Nace ba!" "Kace me?" Ta tambaya batareda ta kalleshi ba, "Ina son mu had'u anjima after sallan isha'i, Ok ok ina nufin zanzo hira anjima in kin bani dama please πŸ™ karkice min No kinji Dr" "Hira...?"ta tambaya cike da mamaki, "Eh tad'i nike son zuwa mana ko kuma shikenan sai akace miki dan muna gida d'aya bani da daman zuwa hira wajen budurwa ta?" "Niba budurwar ka bace, ka bari har in amshi tayin soyayyar ka kafin ka kirani da suna budurwar ka"ta fad'a tana murgud'a mishi baki, "Nidai tunda har nace ina son ki ni a wajena tuni kika zama budurwar tawa dan haka idan an idar da Sallah zan nemo yaron da zan aiko ya kiramin ke ki fito muyi hira koba haka akeyi ba? Ke kuma in zaki fito sai kiyomin kwalliyar da zan yaba kafin fitowar naki koh?" "Uhumm uhmm " Sautin murmushin ta yafita a yayinda ta juyo fuskarta tana kallon shi, "Ba haka akeyi bane?" Ya k'ara tambaya yana kallonta shima fuskar shi da murmushi . "Ah ah mu a gidan mu ba haka akeyi ba," "To ai ba damuwa ki fad'amin yanda akeyi a gidan ku d'in nima sai inyi, mai nema ai baya fushi " "to mudai a gidan mu idan kaga yarinya kana sonta to iyayen ka zaka fara turawa wajen Baba Malam su tambayar maka izini daga wajen shi, Shi kuma idan yayi bincike a kanka yaga cewa ka cancanci ya baka yarshi ka aura a lokacin ne zai baka damar zuwa ku gana kaida yarinyar da kake so, bayan kun gana da ita ne za'ayi batun sa ranar aure dan mu gidan mu ba'a d'aukar lokaci ana jeka ka dawo kafin d'aurin aure! Kai kuma duk kabi wad'annan dokokin ka takesu ka wuce " "Oh my God ashe ma abun sauk'ine dashi har haka ban sani ba! To indai haka ne ni ai ta kwana min a gidan sauk'i tunda haka ne yau zan k'ara tuntub'ar Hajiya da maganar ta tura kawai a tambayo min d'in," ya fad'a yana bayyana jin dad'in shi dan baiyi zaton cewa abun zaizo mishi da sauk'i har haka ba, ashe daya tura manya shike nan sai dai ayi batun sa ranar d'aurin aure, "Nidai ban baka damar ka kai maganar nan gaban kowa ba, ai nace muku niba yanzun zanyi aure ba, indai kana son aurena dole sai dai ka jira har zuwa sanda zan kammala karatuna gaba d'aya, in kuma bazaka iya jira ba ka nemi wata" wai kina nufin cewa dole sai nabi wannan matakin kafin in gabatar da kaina a wajen iyayen ki? Ok na fahimta yanzun na gane kenan dai na riga na samu karb'uwa a wajen ki shi yasa kike son in gabatar da kaina a wajen su Baba Malam koh? Wow I really appreciate it Baby I really love you a lot " Ya fad'a a yayin da yakai bayan hannun ta kan bakin shi yayi kissing. Kwace hannun tayi tana yarfewa kamar wacce kiss din ya manne ma a hannun, "Nidai ka dena tab'ani bana so, kawai kai sai ka wani dunga rik'ema mutum hannu kuma ni karka k'ara gigin sumbatar hannuna daga yau bana so" Ta fad'a tana hararar shi, "Oh Baby its just a single kiss" ya fad'a batareda nuna damuwa ba shifa a wajen shi gani yake hakan ba wani abu bane duba da irin rayuwar da yake ganin wasu couple din sunayi idan suna πŸ’ dating shifa hannun ta kawai yayi kissing kuma bada wani manufa ba kawai dai so yake ya nuna mata son da yake mata, bai d'auka cewa hakan zai b'ata mata raiba, "Oh is just a kiss kake cewa ma? Amma dai ai kasan niba matar ka bace koh?" "But i wish ki zama matar nawa some day, Ok ok ok am sorry ban san hakan zai b'ata miki raiba,amma zan dunga kiyayewa daga yanzun" Bud'e murfin motar tayi ta fita ta wuce fuuu batareda ta k'ara kulashi ba duk da yanda takejin yana kiran sunan ta bata waigoba harta shige side d'in Hajiya Jummai wanda takejiyo hayaniyar yara a ciki tun d'azun da alama bak'i akayi a gidan tasan kuma bazai wuce Rukayya ce tazo gidan ba, "Ya rabb, badai wai har yarinyar nan tayi fushi ba? Kenan na kwafsa Tunda nayi kissing hannun ta?" Ya tambayi kanshi cike da jimami kafin yaci gaba da cewa "Oh Allah to wai ya yarinyar nan take so inyi ne? Ita bata san cewa ni ban saba da irin wannan rayuwar na tsayawa gaban mace inyi ta surutu kamar wani sakarai ba, duk k'okarin da nikeyi dan in faranta mata rai kawai nikeyi a kullum amma banga alaman hakan yana aiki a kanta ba, wai ya take so inyi ne? Neman izini wajen iyaye, Bada izinin ganawa da budurwa, Neman aure bayan sun gana tsakanin saurayi da budurwar," Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke kafin ya kwantar da kanshi a jikin kujerar motar "Kenan dai hakan yana nufin cewar ta yarda in gabatar da maganar aurena da ita a gaban iyayen ta?" Murmushin fuskar shi ya fad'ad'a, "Yarinya tunda haka kike so nima kuma hakan zan gabatar, zan tura iyayena su nemo min izinin kamar yanda kika buk'ata sai dai kuma hakan baya nufin cewa zan iya nesan ta kaina daga gareki, Bazan tab'a sararawa ba har sai kin zama mallakina," Ledojin ya kwasa ya shigar mata dasu sashen na Hajiya har sama ya haura ya bud'e d'akin ta ya ajiye mata nata kasancewar koda ya shigo bai samu kowa a falon ba shi yasa ya haura saman, dakin Hajiya ya lek'a itama bata ciki dan haka sai ya sauko da sauran ledojin a hannun shi, "Yanzun ka shigone hala? Dan muna cikin kitchen nida Larai shi yasa bamuji motsin shigowar naka ba, miye kuma wannan a cikin leda naji sai kamshi yakeyi wallahi," K'arasawa inda take yayi yana mai amsa mata da cewa, "Eh yanzun na shigo da ban ganki a faloba nayi zaton ko kina d'akine shi yasa na haura saman," Yana mik'a mata ledojin ya fice daga sashen ya k'ara shiga motar shi yabar gidan domin kamar yanda ya fad'ama Hajiya ne d'azun wajen birthday din wani Abokin shi yake son zuwa. Hira ke gudana tsakanin Meenal da Ya Sa'eed tun bayan baro warta sashen Hajiya Jummai ta shigo ta same shi a falon na Hajiya, sama ta haura a gurguje ta canza kayan jikin ta d'auko ledojin data tabbatar cewa AK ne ya ajiye mata su a d'akin ta fito itama, Baice mata komai akan maganar da yace mata yana son yi da itaba har sai da suka fito zai tafi bayan ya shiga cikin motar shi ya zauna ne kuma ya bata umarnin cewa ta shigo motar suyi magana, Bata musa ba ta shiga ta zauna, "Meenal "ya kira sunan ta yana maida hankalin shi gaba d'aya a kanta alamun dake mata nuni da cewa koma mene zai fito daga bakin shi yana da mahimmancin da yake buk'atar ta bashi hankalin ta yayin tattaunawar nasu, Babu abinda gabanta yakeyi sai fad'uwa dan bata saba ganin kamewar fuska daga wajen Yayan nasu ba domin dai shida ita kullum cikin wasa da dariya suke, yanda yaga tana ta faman binshi da kallo ta kasa amsa sunan nata daya kirane kuma hakan ya sashi k'ara kiran sunan a karo na biyu, "Meenal! " "Na'am ta amsa dashi gabanta yana ci gaba da fad'uwa, "Meenal kin san nayi miki magana akan cewa akwai maganar da nike so mu tattauna dake koh?" Baijira jin amsa daga gareta ba ya d'aura da cewa, "Wannan maganar ne yasa yau na baro duk abubuwan dake gabana nazo nan dan in samu damar yin magana dake" "To Ya'ya ina jinka allah yasa dai ba wani laifin nayi maka ba?" girgiza kanshi yayi kafin ya amsa da cewa, "Bakimin laifin komai ba zuwa nayi dai domin mu tattauna akan abunda ya shafi rayuwar ki, Meenal ke yanzun ba k'aramar yarinya bace kin riga kinyi girman da zuwa yanzun ya kamata ace kin san duk wani abunda yayi dai dai da tsarin rayuwar ki ba sai wani ya sanyaki a hanya ba domin duk wani hankalin da yakamata ace d'iya mace mai adadin shekarun ki ta mallaka kema kin mallake shi, Abunda nike so in miki nuni akan shi shine, Karkiyi tunanin cewa wai dan kinyi auren farko Allah bai had'a zuciyoyin ku keda mijin naki kun gudanar da zaman auren yanda ya dacr ba kiyi zaton cewa sauran maza suma haka suke nuna rashin kulawar su akan matan da suke aure! Ah ah ina sone ki gane cewa tun farko Allah ya nufa cewa zaman da zakuyi a matsayin miji da mata takaitaccen ne shi yasa duk abinda ya faru ya faru, Yanzun kuma da kuka rabu hakan bazai zama dalili a wajen ki ta yanda zaki tauye kanki ki hana wasu mazan tun karar ki da batun neman soyayya a wajen kiba , ko kuma ke ki k'untata kanki wajen hana taki zuciyar bata damar samun kusanci da wani a cikin su, A sanda kika bud'e zuciyar ki ma wani namijin ne kad'ai zaki gane abinda zuciyar ki take so dama wanda bata so, Karki yarda ki k'untata kanki ki kuma tauye masoyan ki wajen hanasu tunkaro ki,domin bazai yuwu ki cigaba da zama haka babu aure ba Kin sani koda ace iyayen mu basa raye mu yayyen ku maza zamuyi tsayuwar daka akan ku domin muga mun cigaba da kula da tarbiyar ku, abinda nike son ki gane anan shine bazai yuwu mucigaba da zuba miki ido kice zaki zauna haka babu aure ba domin hakan yana iya tab'a daraja dama mutuncin ki wanda ba iya kanki abun zai tsaya ba harmu makusan tanki abun zai shafa, Zuwana yau nazo ne saboda in baki shawara Meenal karki yarda kiyi sakaci ta yanda abinda ya faru dake a shekarun baya zai k'ara maimaita kanshi a yanzun, Domin dai yanzun haka maganar nan da mukeyi dake ina mai tabbatar miki da cewa akwai wad'anda suka fara kai maganar son auren ki wajen Baba Malam bayan su kuma nima haka akwai mutum biyu da suka gabatar min da kansu a matsayin suna son in shige musu gaba wajen kai maganar su wajen iyayen mu, a zahiri gaskiya kuma dukan su babu wanda bazanyi farin cikin ace ya zama mijin auren kiba, Sai dai kuma ko kad'an bana fatan a k'ara tauyeki wajen yi miki auren da baki shirya ma zuwan shiba ko kuma a zab'ar miki mijin da baiyi dai dai da zab'in zuciyar ki ba, Nasan a hakan kuma kema baza'a rasa masu tunkarar ki da batun soyayya ba, dan haka kece zakiyi ma kanki yak'i kiba zuciyar ki damar tantace mijin da kike son ki rayu dashi ni kuma zan shige miki gaba wajen gabatar dashi, Naba Aliyu da Ya Hashim number d'inki na kuma basu harda address din nan gidan domin su gabatar da kansu a gareki, Dukan su yan uwanki ne na jini sai dai kuma duk da kasancewar su dangin ki hakan baya nufin ki cusa ma zuciyar ki abunda bata muradi, zanso inji ra'ayin ki akan kowannen su bayan sun gabatar da kansu, in kuma kinsan cewa akwai wanda kika riga kikaba zuciyar ki zanso ki sanar dani tun yanzun ni kuma zan dakatar da zuwan su nan d'in nasan zasu fahimce ni, Karkiga har yanzun babu wanda ya tankamiki kiyi zaton ko an sa miki idone, ah ah na tabbatar da cewa shi kanshi Baba ya sa miki idone saboda ki sarara akan abinda ya faru, dan haka ina mai k'ara baki shawara gara tunda wuri ki gabatar da wanda kike so a gaban iyayen mu, ki bashi dama yaje ya gabatar da kanshi a wajen iyaye kamar yanda aka saba gudun abinda ka iya biyowa baya kin daiji na fad'a miki, ni zan wuce yanzun ki koma ciki ke kuma Na kuma ba Sultana sak'on sabbin kud'in da kikace kina buk'ata na lik'i ni zan wuce sai naji daga gareki" "Nagode Yaya insha Allah zanyi abinda kace d'in amma dan Allah ka dakatar da zuwan su Ya Aliyu da Ya Hashim gidan nan ni ban shirya ganawa da kowa a cikin suba" "Kiyi hakuri hakan bazai yuwuba dole ne suzo na riga na gama magana" "Amma Yaya.... " D'aga mata hannu yayi alamun dakatarwa, Ki wuce ciki nace tafiya zanyi aina baki dama idan basu miki ba kece zaki dakatar dasu daga kai maganar zuwa can gida bawai niba, ni shawarar da nike ganin itace zata fishsheki kawai na baki dan haka saida safe" Jiki a sanyaye ta bud'e k'ofar motar ta fita shi kuma yaja motar ya fice daga gidan, Sanyi kafafun ta sukayi dan dole ta nemi wajen zama ta zauna tana jin wani irin tashin hankali yana lullub'eta ta, Zufa kawai ke yanko mata tako ina uwa irin wacce aka tsare gaban Sarki tayi k'arya, Wani irin tashin hankali ne wannan yake shirin tunkarota kuma? Ita da take gudun masu mata shine saboda tsabar rashin mutunci su kuma wad'ancan dan suna ganin cewa su d'in suna da alaqa ta yan uwan taka da ita suke son yima rayuwarta kutse ba tareda ta shirya ba? Waiyo Allah ita, kenan da ace shi yaya sa'eed bai dakatar dasu akan tun karar malam da maganar ba kenan da tuni sun kai kansu wajen shi, Ita fisabilillahi ina ita ina k'ara wani auren zumunci kuma fisabilillahi, wai a hakan ma kuma dukan su masu mata shi Ya Aliyun fa matar shi ko haihuwar farko ma batayi ba dan duka duka auren su baifi shekara biyu da watanni ba shine tun yanzun yake batun k'arin aure, wato ya aureta ya had'a da wancan itama bayan dan lokaci yace wata kishiyar zai k'aro mata lallai ma, Shi kuma Ya Hashim da kyar mafa aka samu shawo kanshi yayi auren dan duk ya girmi su Ya Sa'eed yasin har Sarki ma ya girma matan shi biyu aka aura mishi rana d'aya amma da yike matan nashi gasar haihuwa sukeyi tuni suka suka cika mishi gidan da yara kusan 7 ita wani tsautsayi da rashin rabon ne zai sata aure shi, in ma ta aure shi da kishiyoyi zataji koda yaran su? Gidan da kusan kullum sai anyi damben bura uba a cikin shi aiko da maganar nan taje kunnen Malam da yaci amanarta ba kad'an ba, Waiyo Allah wai dama abunda mata ke fuskanta kenan aduk lokacin da auren su ko mazajen suke aure suka mutu? Shi kenan ko wani namiji sai yayi ta kawo musu hari ko wani mara ta ido ke dai zaice yana so, Tayi zaton cewa Salman ne kad'ai mara hankali shi yasa ya iya tunkarar ta kai tsaye, to ashe akwai manyan shi a gefe da ace sun kai maganar nan wajen malam ai da shi kenan sun shek'eta da ranta wallahi sai dai kuma wannan karan koma me zai faru ya dade bai faruba amma bazata zauna tanaji tana gani a k'ara mata wani auren dolen ba balle kuma har ace za'a aura mata mai mata. Koda akayi sallan isha'i ita fa gaba d'aya tama manta da cewar da AK yayi wai zaizo hira, To jama'a hira kamar dai wani saurayin arziki gida d'aya fa suke zaune, to in yazo hirar ma mai zaice mata? Ga kuma damuwar hirar da sukayi da Ya Sa'eed wannan damuwar duk sune sukayi mata katutu a cikin zuciya. Wani daga cikin yaran makotar sune ya shigo falon na Hajiya da Sallama, bayan ya gaishe sune Hajiya ke tambayar shi da cewa, "Ya akayi ne Khalid ko Maman kace ta aiko ka?" "Ah ah Ya Mai Jama'a ne ya aikoni wai yana kiran Aunty Meenal" Cewar yaron, "Mai jama'a dai na nan gidan nawa?" "Eh shi Hajiya" "Yana ina ne shi din daya aiko ka kiranta?" Hajiya ta k'ara tambaya, "Yana can a zaune wajen bakin gate" "To jeka kace mishi tana zuwa" "Ni babu inda zanje kai kace mishi nayi bacci" Cewar Meenal *Ummiee ce*✍🏼[9/18, 9:54 PM] Ummiee Zaria: βšœοΈπŸ”±πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *DANGINA*πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ”±βšœοΈ *BOOK 2* *PAGE 31* Khalid yi tafiyar ka gida kaji" Cewar Hajiya, bayan fitar yaron mik'ewa itama Hajiyar tayi ta wuce sama bata k'ara bi takan Meenal akan maganar ba dan ta k'uduri aniyar cewa bazata k'ara shiga maganar soyayyar su biyun ba, sai dai suga ta yanke hukunci kawai, Daga kan minutes ya fara lissafi sai gashi mintunan suna ta wuce wa shiru ba Meenal ba labari, wayar shi ya d'auka ya fara kiranta sai dai yarinyar nan dan wula walan walakanci haka tayi kunnen uwar shegu da kiran nashi duk da cewa yana da tabbacin taga kiran, Musty daya shigo gidan yanzun ne ya hango shi zaune sai faman latsa waya yakeyi, "Baa'ba yadai me kakeyi anan zaune kai kad'ai kuma?" Dogon tsaki AK yaja yana barbaza gashin kanshi, "Ya dai ko mutuniyar ce ta tab'o mana kai?" Musty ya k'ara tambaya, "Wai haka kuke fama da yaran nan dama? Da kyar fa na samu yaron dana aika cikin gidan nan akan ya kiramin ita amma wai sai cema yaron tayi ya fad'amin cewa tayi bacci alhalin kuma Hajiya tace ma yaron yace gata nan zuwa, kasan mintuna nawa na b'ata anan zaune ina jiran fitowar ta?" Bai jira Musty ya amsa mishi ba yaci gaba da cewa, "Kusan awana d'aya fa a wajen nan zaune na kira wayarta nasan kuma ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba cewa taga kiran nawa kin d'auka dai tayi saboda ta raina ni" "Calm down mana ya kake so ka b'ata ranka akan wannan d'an k'aramin damuwar, Menene ma na wani b'ata ma kai lokacin dahar sai ka wani nemi yaron aike cikin gidan a sanda kake buk'atar ganin ta? Gidan kune fa nan d'in kana kuma da damar da zaka iya shiga cikin shi a duk sanda kayi ra'ayi, oh wai nan dama kai kazo tad'ine kana jiran ta fito?" Musty ya fad'a yana nuna AK din yana kuma mishi dariya, "Zanci uban ka a wajen nan idan ka nemi matsamun kasani" "Miye laifina ni kuma daga baka shawara, kawai ka tashi ka bita cikin gidan tunda yau mulki takeji bazata yarda ta fito ba, kuma ai mai nema baya fushi kuma yasin ko nine ita ina da saurayi a gida bazan yarda in fito hira a harabar gida duk Sauro su gama cizona a banza ba" Gefen da AK d'in ke zaune shima Musty ya rab'a ya zauna,yana mai cigaba da cewa, "Baa'ba sai kayi hakuri fa indai yan matan nan ne duk haka suke da shegen jan aji amma na lokaci ne kaci gaba da tara ta kawai indai rabon kace duk zaka fanshe in kaso a rana d'aya" ya k'arasa fad'a yana dafa kafadar AK din ya jinjina alamun tabbaci. "Wai kai kasan cewa har yanzun yarinyar nan tak'i bani hankalin ta yanda

Chapter 67 of 92