Share this page
sun gama yawace²n su a cikin gidan kitchen din Hajiya suka kaima farmaki suka dunga ci mata mutuncin madara da sunan yin tuwon madara da iloka bisa shawarar Meenal, sunfa mata ta'asa a kitchen ba kadan ba, amma basu tsira ba dan sun kammala sun bararraje suna rabama kansu ta dawo gidan Allah yasa kuma kai tsaye da shigowarta kitchen din tayo dan dazun da safe Mai Jama'a ya kawo mata kilishi a kitchen din kuma ta ajeshi gashi mutane sun ma gidan yawa tana tsoron kar a mata ta'asa dan haka ba shiri ta dawo gidan, to dai ba'a mata ta'asan kilishi ba an mata na madara da sugar domin kusan suman tsaye tayi bayan shigowarta kitchen din. Kai! Kai!! Jama'a me nike shirin gani? Uban me kuka shigo kuna min a kitchen? Larai! Larai!! Ke larai wai gidan uban wa kika shige kika barmin kitchen a bude wadan nan yaran suka shigo suna min ta'asa a cikin shi? yara da shegen fitina kamar sauro. Dan risinawa Larai tayi bayan ta iso "Hajiya ina kara kimtsa falon ne", kintsa falo shi yasa kika sakar musu kitchen ɗina suka shigo suke min abunda suke so? " ayi hakuri Hajiya ban san sun shigo ba " cewar larai, fita ki kiramin *Mai Jama'a* a waje kice nace yazo yanzun nan yamin maganin su, Ai ba shiri su Aisha da Moon cikin su ya duri ruwa suka fara bata hakuri, Hajiya dan Allah kiyi hakuri Allah kuwa zamu biyaki madarar ki, " ban hakuri sai kun fadamin ubanda ya turoku ku shigar min kitchen dan kunga bana gidan wato ma dakon fitana kukeyi koh? " cewer Hajiya a harzuƙe. Larai fa tuni har takai bakin gate dan tasan in ma tatsaya bama Hajiya hakuri laifin duka kanta zai komo sai dai koda ta karasa majalisar bata samu *Mai Jama'a* ba sai Sadeeq dasu Musty ta samu ganin bashi a wajen yasa ba tareda tayi ma kowa magana ba ta juyo cikin gidan suma dai basu lura da ita ba, har ta kawo kusa da falon Hajiya ta hango shi tsaye tareda Baba Usman suna magana dan haka ta karasa wajen su. *Mai Jama'a* kazo inji hajiya" tace bayan ta isa inda suke, " meya faru hala? " ya tambaya Uhmn mai sunan tane ta wajen Jidda da su Aisha bayan fitan ta suka shiga kitchen suka kwashe mata madara sukayi iloka da tuwon madara shine tace in kiraka", " muje cikin" cewar Baba Usman dan haka suka rankaya zuwa cikin sashen Hajiyar amma dai larai bata bisu zuwa can ba aikinta taci gaba dayi na gyaran falon Hajiyar. Duk wannan sababin na hajiya bai hana Meenal kwashe kason ta dana Meelat ta zuzzuba musu a leda ta cusa a cikin jakarta ba dan ta dauki aniyar komai zai faru tuwon madarar nan bazai taba zama haramiyar ta ba . yo ina dalili fisabilillah inba fitinar Hajiya ba madarar nan fa gashi nan a store din ta daga na gwangani na ruwa harda manyan gwana²n na gari kawai dan sun dan yi amfani da wannan shine zata wani zo tana neman tara musu mutane kamar wasu barayi harda wani aikawa a kira mata wani *Mai Jama'a* su kuma waɗan nan lusaran duk sun wani firgice sai wani hakuri suke bata ba Mai Jama'a ba a kira mata *Dangin* ma gaba daya. Muryan Mai Jama'an ne ya katsema su Moon ban hakurin da suke ta ba Hajiya ita ko sai wani cika take tana batsewa a dole fa an bata mata rai kamar ba iyayen su ke siya mata madarar suna tara mata a store ba. "Meke faruwa anan?" Ya tambaya, yau wa ɗan nan karaso daga ciki ka tam bayamin dalilin da yasa suka shigomin cikin kitchen suka kwashe min madara suka barnatar min dashi a banza!. "Bafa barna mukayi ba tuwon madara da iloka mukayi" cewar Meenal tana wani turo baki a sakalce kota manta wake tsaye a wajen ne oho. "Shi Ilokan ubanki Malam ne ya siyo madarar ya aikomin da ita da zaki baro gidan ku kizo kitchen dina? Hajiyar tace a zafafafe. Kai hajiya! Kai hajiya dan nazo nan gidan nayi tuwon madara shine zaki faramin gori naga dai ai gidan nan gidan kakana ne ina da damar yin abunda nike so kuma wallahi nasan da Baban su Momy na raye shi bazai takura min kamar yanda kikemin ba ai dama tunda nazo bakiyi murna da zuwa naba kawata tashi mu tafi" ta karasa tana kamo hannun Meelat data kasa cewa wani abu ita mamaki kawai take irin masifar da Hajiya keyi akan madara bayan ga madarar nan da yawa a store ko itama fa gani. "Koma ciki" Mai Jama'a yayi maganar a dake a yayin da suka kawo inda yake tsaye suna shirin ficewa, shidai Baba Usman yana ta bakin kitchen din a tsaye kuma har yanzun hajiya bata san da wanzuwar shi a wajen ba. Komawa tayi tana cika tana batsewa dan wallahi tayi dana sanin zuwan gidan da tayi yau haka kawai Hajiya zata kama mata fada a gaban kawarta Allah ma ya rufa mata asiri ta dade daba kawar nata labarin kalar masifar Hajiyar ai da tasa ajinta ya zube yau, kai jama'a ina ma amfanin masifa dan Allah, Baba Usman ne yayi magana "Zo ka amso ma Hajiya madarar, da madara dame kukayi amfani dashi? "Yace yana kallon su, Suga da man gƴaɗa Moon ta bashi amsa, a zafafe hajiya ta waiga dan bata san da wan zuwar shi a wajen ba tun farko sai yanzun dataji muryar shi. "Kai kuma waya gayyatoka nan? Nidai nasan nace Larai tamin kiran *Mai Jama'a* amma nasan ban ambaci sunan kaba, wato ku iyayen son ƴa'ƴa yaran ku bazasuyi laifi a musu fadaba shine ka taso zalo² ka taho to waima a magana ta kaji nace a biyani madara ne? Ko koh tsabar daure ma karya gindi shine wato kai ubansu bari ka biya to ai bance maka bani da madara ba ina da madara cike a cikin store dan haka koma inda ka fito ban gayyato kaba, ko kaine ka gayyato min shi? Ta fada tana kallon Mai Jama'a, shareta yayi bai kulata ba kamar yanda shima Baba Usman din yabar wajen yana dariyar rikicin Hajiyar nasu da ba'a mata gwanin ta, Kai ku tattara kayan ku kubar mata kitchen din ta" ya fada yana kallon su fuska a daure, ina zasu kuma basu dibar min ilokar ba? Kana ganifa sukayi kasafin abunsu iyasu! kuma ai dai ido guba tunda na gani sai su diba min, "ilokar zaki sha?" to wai kina bukatar tuwon madarar dama kuma kike fadar sun ɓata miki madara?. To ina ruwan ka? Naga dai ai madarar tawa ce kuma kitchen dina ne, karamin kwano ta dauka ta diba tuwon madarar da ilokar kafin ta fice a kitchen din tabar shi da binta da kallo baki bude cike da mamaki girgiza kanshi kawai yayi ya juya shima ya fice daga kitchen din dan bashi da abun cewa kuma. Hajiya cefa inka biye mata sai ku wuni kuna jidali ita bata gajiya. #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ _Bazan taɓa mantawa da ku ba aminan ƙwarai,ina kuma alfahari da kasancewa ta cikinku,ko ban kira suna ba kun san kanku,mutanen Family House. Na gode³ ƙwarai da ƙarfin gwuiwar da kuka bani,wajen rubutun littafin *DANGINA* ubangiji ya biya da aljannah._ *MOM TEEMAH* *AISHA HUMAIRA* *JIKAR HAJIYA* *CHIDA* ```Page 7 Falo ya sameta zaune ta daura kafarta ɗaya kan ɗaya hankalin ta kwance take cin ilokarta, tsaye yayi mata akai hannun shi bibbiyun dafe da ƙugun shi ba tareda ya zauna ba yake mata kallon kasan ido cike da jin haushi yace " kinga hajiya gaskiya ki dena min irin haka, wannan ai salon kijamin raini a wajen yarane zaki wani sa a kirani akan wani soki burutsun zance, yanzun fisabillahi ko kunya wai abunda kika gama bala'i akanshi shine kika wafce musu kika dawo nan kika gyara zama kike ta sha, haba Hajiya gaskiya nidai bana so" ya fada yana ƙyacci. "Ah² kai ban gane ma wannan muzuran da kazo kamin tsaye a saman kai kana min ba, yo rashin kunya da rashin ta ido harna kaika, kaida kullum kake laya min jerin ƴan mata sahu² da anyi magana kuma kace ba wacce kake so cikin su ruwa tun bai tafasa ba har zai kone, wallahi dakai da suɗin lokaci nike nema na musamman da zan ci muku uwa, kai nidai Allah ya isana wallahi waɗannan shegun mata dai sun cuceni duk gashi nan sunsa gaba ɗaya baka ganin mata da gashi, ooooh tsaya ma wai kai nan saboda rashin imani zuwa kayi dan ka jibgar min jikokin ko ƙaƙa??? Iiiyee naga sai wani zakalkalewa kake faman yi, toni shike nan saboda gani Aminatun mahaukata kawai sai inyi kira akan kazo kasa min su a gaba da bugu kamar wadanda suka kashe mutum? Kawai dan na kiraka ka tambayan min su dalilin da yasa zasu shiga min kitchen bada izinina ba, kenan kai nan zuwa kayi ka kakkarye min su ko me ka raya a zuciyarka? To nidai ba hauka nikeyi da zan baka damar dukan wadancan kananan yaran ba fisabillahi yaushe har sukayi girman da zan kira Iliya ɗan mai karfi kamar ka ya hukunta su ah'ah wallahi da hankali na , yo ita waccen ƴar Jiddan in ka taɓata kuma ai ka janyo min jangwam, kana ganin yau Allah ya karya alkadarin ubanta da kafarta tazo gidan nan fa kai yaushe rabon da kaga haka? to in ka bugeta kuma ai ka maidamin hannun agogo baya duk sallah fa sai nayi addu'a Allah ya karkato min da hankalin ta kan mu ah'ah wallahi jeka kawai na yafe in ma sunyi laifin da yakai matakin duka nikam mai zai gagareni insa a zaromin zabori in zazzane musu jiki dashi. Ciki da waje," ta karasa fada tana hararar shi,baki sake yake binta da kallo cike da mamakin yanda ta rufe idanu take masifa kamar ba ita ta aika a kira mata shiba amma yanzun so take ta maida laifin kanshi. "Da zaborin ne zaki dake su? " ya tambaya, "kwarai miye a ciki? Ta bashi amsa. Ah lallai to ai ba laifi nidai na fada miki karki kara kirana dan yaran nan sun miki laifi inba haka ba hummmm, yafada yana ficewa daga falon rai bace. Duk abinda ke faruwa a falon suna daga kitchen suna jiyosu dan Hajiya bata iya fada da karamar murya ba, dan haka ta kofar baya suka fice daga kitchen din, kai tsaye sashen Momy Hauwa suka wuce domin dai itama din kamar sauran yaran gidan tana da sashen ta daban da take sauka idan tazo gidan kamar lokacin biki haka ko kuma wani sha'ani daya zamana dole saita kwana dan Hajiya ba ta yarda wani ya sauka a side dinta, har gara² ma jikokin ta yan mata suna da ɗakunan data ware musu suke sauka a ciki idan sunzo ba tareda iyayen suba, suma dai ba kasafai suka fiye son sauka a wajen taba saboda takuran ta dan in har ka kwana a side din Hajiya tofa tashin asuba dole babu fashi da zarar kun idar da sallah zata ware ma kowa aikin shi masu shiga kitchen daban , haka ma masu gyaran side ɗin da zarar an gama kuma sai wanka ko wani irin sanyi ake bata yarda mutum ya zauna mata baiyi wanka ba dan ita bata shiri da kazami. Khadija suka samu tana shirin fitowa daga side din hannun ta rike da wani ƙaton basket da aka jera wadansu kyawawan kuloli masu daukar hankali gwanin burgewa kai daga kallon su kasan masu tsada ne, "Khadi ina zuwa? " cewar moon, ita kuma ta amsa da cewa " Zan kaima Ƴa Abdul abincine, lah Meenat yaushe kikazo? " ta tambaya tana karasawa kusa da ita fuskarta cike da fara'a, "tun yaushe kikazo? Ta kara tambayan ta. Keni tun tuni nike cikin gidan nan kawai dai nan din ne bamu shigo ba muna sashen Al-masifatu" ta karasa fada tana harare² dan har yanzun bawai takaicin abinda Hajiya tayi musu ya saketa bane dan Allah ya gani yau hajiya ta gama kwance musu zani a kasuwa ta rasa wanda zata musu sai wancan ɗan damben bayan batun yauba tasan shi da shegen karfin tsiya dan bata manta wani zuwa gidan datayi lokacin baya ba, musun ƙwallon ƙafa ya sarƙe a majalisar shi abun har saida ya kaisu ga dambatuwa, a gaban idonta fa yama abokin faɗan nashi duka ɗaya wallahi kawai sai ganin kato tayi a kasa kwance bai kara motsi ba saida aka yayyafa mishi ruwa dan tsaf ya aika shi duniyar somammu in kukaga wanda ya somar din wallahi a tsaye da girman jiki duk ya fishi, shi wanda ya somen yayi zaton zai daki banza ne dan anata rirrike shi ana son a raba faɗar shi yana kwacewa sai kunfar baki yake akan a sake shi ya koya ma Mai Jama'an hankali yagan shi da kirar madara yayi zaton bai iya faɗa ba, atoh kun san yaran yan gayu ba wani son wahala suke ba . Ai ko shi da kanshi Mai Jama'an yace "dan girman Allah su sake shi yakaraso" mugun ashe ya shirya sumar dashi ne to dai mutumin nan bai dawo daga duniyar suma ba saida suka feshe shi da ruwa, fisabillahi shine zata wani aika a kira mata shi wato yazo ya kakkkarya kasusuwar su dama gasu kamar kudin guzuri duk kan su babu mai auki, gashi ɗazun nan dama ya gama hararar ta ita dai Allah yasa ma ya manta hummm lallaima Hajiyar nan tasan matsayin da zata ajiyeta daga yau, ita hajiya ko kunyar bakuwar fuska bataji ba jama'a a gaban ƙawarta fa ta kwance mata zani a kasuwa....... "Miye a cikin kulan hala? " Aisha ta tambaya "kema kin sani ai tuwo ne" Khadi ta amsa mata, hummm Allah ya kyauta da yamman nan inci tuwo ai shi yasa kullum yake kara murdewa bashi da abincin ci sai tuwo nikam ina tausaya ma matar shi dan ta shiga uku da tukin tuwo safe rana dare" cewar Moon Khadi kam cewa tayi " nidai ku karasa bari in mika mishi in dawo kafin ya biyo sahu ta fada tana ficewa zuwa side din samarin gidan. Bayan anyi sallan la'asar ne Anty Hassana ta aike su saman layin sukai mata sako, wasu kaya ne zasu kaima kawarta daga nan kuma ta musu umarnin su shishshiga makota su gaishe su kamar yanda suka saba duk in sunzo zasu shiga gidajen unguwan su gaishe su sannan sukai musu tsaraba domin duk yawancin mutanen unguwan zuri'a ɗaya ne, a lokacin ne kuma Meelat ta samu kira daga gida dan haka ta roki dasu rakata ta samu abun hawa ta wuce. Dan bazata samu damar binsu gidajen ba, bayan su Moon sun tabbatar mata da cewa Insha Allah suma bazasu kwana anan ba dazarar sun dawo zasu hado kayan su zasu taho tareda Meenat gida kamar yanda suka saba, suna shirin fita sukayi kicibus da ƴa Musty zai shigo gidan "ah² jikokin Hajja sai ina kuma? ya tambaya, zamu raka Meelat ne zata koma gida cewar Aisha, waiga wa gefen da take boyewa a bayan Meenal yayi "yanzun fisabillahi da ban ganku ba haka zan laluba inji kin wuce ba sallama kanwata? " ko ba'a dauke ni a matsayin ƴa'ƴan bane iyeh? " to ni dai da gaske nike dan haka muje in sauke ki dan bazan bari kije kiyi tsaye a bakin titi kina neman abun hawa ba" ya fada yana juyawa. (Cinyewa kin yake mu) suka haɗa baki wajen fada da karfi Moon ne mai cewa "bebs bana fada muku ba wallahi ko tantama banayi ƴa Musty ta zurma kunga irin kallon da yake mata kuwa? mutumin da in yana gaban mata yake daure fuska yana wani cin magani amma kuga yanda yake mata magana da kwantacciyar murya wai Allah dadi muma mun zama an mata", Iiiii huuu huuuu jama'a Alhamdulillah Allah nagode maka" Meenal tace da karfi tana tsalle cike da murna saida ta gama raye²n sannan ta dawo gefen da Meelat ke tsaye dan ita gaba ɗaya ma ta rasa na cewa, "ke wallahi kawata tsaya kiji karki yarda ki jefar mana da wannan damar da muka samu, ban kuma ce kiyi gaggawar bude zuciyar ki dan ki cusashi ba NO sai munja zaren mu, Wallahi in kika mishi sakwa² kikayi saurin kware mishi ba uban dazai hana ni in tube mu daku dake, mutanen da kullum mata ke musu layi suna binsu kamar ƙuda da mangwaro dan haka ba ɗagin ƙafa zuciyar shi zaki rikemin dakyau so nike mu banbance musu Banbancin kana nan yan mata da wadancan sakarkarun da kullum suke layin taya su zaman majalisa barima ki gani"ta faɗa tana bude jakarta ta fiddo kwalbar turare ta kama fashe Meelat din dashi, me su Moon zasuyi ai sai suka fara ihu suna kara kuranta ta, "Allah kuwa naku wasa ne bakusan irin bakin cikin dake kamani duk sanda nazo naga mata zaune a kofar gidan nan ba, kai Allah dai ya isa an zubda mana daraja wai mace ke zuwa neman soyayya muna nan daku duk sai nacicci musu uwa, Dan Allah karki bari wannan damar ta kubuce mana" inji Moon ita kuma Aisha ta daura da "karki bamu kunya kawata" ke in kika bani kunya wallahi kai tsaye zan miki Allah ya isa dan kinja mana asara ne babba cewar Meenat basu barta ba saida suka gama fanfata sannan suka fito, koda suka fito daga gidan ƙasa kaɗan suka hango motar shi a fake da alama su yake jira dan haka ba ɓata lokaci suka karasa inda motar ke fake Meenal ce tayi saurin bude mata gaban Motar tace ta shiga basu wani tsaya ba suka musu fatan sauka lafiya suka juyo. Cikin gidan suka koma a farfajiya suka tadda su Anty sadiya da Anty fati duk dai yan matan gidan sun fito "ina kukaje? " Anty fati ke tambayan su, rakiyar Meelat mukayi ta tafi gida' suka bata amsa to ai sai ku juya muje ko ma samu mu dawo da wuri, juyawa sukayi da niyyar fita "kai ina kuma zaku" cewar Anty Sas, ba tafiya zamuyi ba? Aisha ta tambaya to waye zai kwashi kayan nan? Anty Sas din ta kara tambaya, Kai dan Allah baga yara nan ba su dauka mana" ku dai zaku dauke shi dan badasu zamuje ba, suna kunkuni suna komai haka suka dauki kayan ita dai Meenat makalewa tayi a gefe a cewarta bata ma kowa dakon kaya haka dai suka rankaya suka fito sun kumayi sa'a majalisar kamar anyi ruwa an dauke dan ba mutane sai tsiraru, haka dai suka tafi duk inda ya kamata su shiga sun shiga kuma sun raba musu tsarabar gidan karshe da suka shiga shine gidan ƙawar Anty Hassana kuma gidan su Nusaiba masoyiyar Mai Jama'a koda suka isa gidan haka ta dunga rawar jiki tana nan² dasu ina ka saka ina ka aje ita a dole ga kannin saurayi sunzo gidan su batasan wannan rawar jikin nata haushi yake ba su Moon ba su dai su Anty Sas da basu san miye a kasa ba sunyi zaton ko tsabar son jama'a ne yasa ta sake dasu haka basu san tana kamun kafa bane, duk inda tayi haka Meenal ke binta da ido so take saita gano munin ta sai dai kuma Masha Allah Nusaibar fa tana da dan kyanta ba laifi kuma yar masu kudine dan tun daga bakin gate in ka shigo gidan zaka san an tara ba laifi duk ta gama karanceta tsaf amma duk wannan kyan cewa tayi wai Nusaibar bata haɗu ba, jira take subar gidan ta samu damar fesar da abunda ta kunsa, dan haka ta riga kowa tashi dan ko kayan ciye²n da aka jera musu bata yarda taci komai ba haka kuma ta hana sauran ci dan dama su Anty fati sunce suna da koshi, "ku muje koh" tace bayan ta mike "Haba dai da wuri haka ku zauna mu danyi hira mana gashi ma bakuci komai ba" cewar Nusaiba, Ah ba komai muna da koshi gashi magrib ta kawo kai gara mu koma Anty Sas ta amsa mata, to bari in sa muku a leda kuje dashi gaskiya in kunje gidan sai kuci"Nusaiban ta kara fada tana shigewa ciki saida ta kira mamanta cewa zasu wuce sannan ta dauko leda ta juye musu duk kayan dake wajen ita kuma Mamanta kayan zaki ta hada a wata ledar ta mika ma Aisha "ku ce mata nagode nima gobe zan shigo gidan in Allah ya kaimu nagode kunji ku gaida gida". Suna fitowa a gidan tun basuyi nisa ba suka fara gulmar Nusaiba Meenal ce mai cewa "ke Moon wai da gaske ita wannan figaggiyar itace keson wancan Iliya ɗan mai karfin? Kai innalillahi gaskiya dai girma ya fadi yanzun ita duk kyanta kawai ta rasa wanda zata so sai Mai Jama'a" "Wacece? " su Anty Sas suka tambaya, kawar ku mana cewar Meenal "ke kawar wa Anty Fati ta tambaya tana kallon Anty Sas a zaton ta ko wata kawar Anty Sas din suke magana akai Aisha ce ta basu amsa da cewa" Nusaibar nan fa da muka fito gidan su ita ce keson Ƴa AK kuma harda danbe ma sukeyi akan shi haka naji hajiya tana fada" "Meee" suka fada cike da mamaki, "waiyo Allah yarinya ta kamu da mugun abu innalillahi wallahi harta bani tausayi ita wani hau din ne ya hauta ta rasa abun so sai Ƴa AK mutumin da gida da makaranta kullum mata kebi" cewar Anty Sas. gata kyakyawa da ita tubarkhallah" cewer Anty fati cike da jimami "to Allah ya yaye mata dan ko

Chapter 6 of 92