Share this page
wata a rama akan nashi. To yau dai abun ya gagara domin daren jiya ma bai samu yayi bacci wadatacce ba saboda tsabar ciwon daya kwana dashi, yau kuma yayi zaton ko in ya shiga cikin mutane ko abun zai lafa sai dai kuma abunfa ba sauk'i. Ganin yana neman mutuwa ne fa yasa ya dawo gida a zaton shi ko Meenal bataje makaranta ba tunda ai da safe tace mishi bata da lafiya, So yayi yazo ya lallab'ata yau dai yaji ya gani ya kuma amshi auren sai dai kuma tun shigowar shi falon ya tabbatar da cewar bafa ta cikin gidan domin dai baiji kamshin girki ba dan dai yasan tana dawowa daga makaranta indai yana garin take fad'awa kitchen domin had'a mishi abincin rana, tanan wajen kam yana respecting dinta dan kai tsaye zaice abinda ya rasane a wajen Teemah ita yake samu a wajen ta, Yaso kwarai ya daure sai dai yaufa abinda yakeji a jikin shi bamai dannuwa bane ganin cewa zai iya cutar da kanshi domin dai har magani ya sha amma ba sauk'i hakan yasa ya yanke shawarar gara kawai ya kirata ta dawo gida in yaso komai ta fanjama fanjam domin dai aiba abun kunya zai aikata ba ta dawo kawai ta bashi hakkin shi, dalilin da yasa yayi ta danna mata kira kenan har zuwa sanda ciwon yaci k'arfin shi ya mulmulo ya dawo kasa yana jiran ta Allah ta kasance, Sama² ya dunga jin tana kiran sunan shi cikin kuka, sai kokari take ta d'ago shi daga inda yake kwance sai dai kuma inah! Wane ita ta iya d'aukar shi! Soja nefa tsayayye wanda ko a tsaye yake bazata iya ture shiba balle kuma yana kwance sharbam, Ba karamin salaamah ya samu a yayin da ya tabbatar cewa ita dince ta shigo dakin ba, domin ko babu komai bazaiyi wasa da wannan damar ba, zaiyi amfani da ita yanda ya dace dan yasan dai inba haka ba tofa koda ace macewa yayi sai dai yazam cewa ya mace a banza indai ta itane yayan shine kadai zasu zama marayu, tunda ita dai ba fad'in shi ta sani ba duba da cewar koda safen yau saida ta maimaita mishi cewar ya saketa kowa yaje yayi harkar shi. Sauran karfin daya rage mishi yasa wajen jawota ta fado cikin jikin shi, shi kuma yayi amfani da hannayen shi wajen nad'eta a jikin nashi ta yanda ya tabbatar bazata iya mikewa ba. kam² ya damketa damka bata wasa ba, yayinda zafin damkar yasa ta fasa ihu ita a zaton ta ko zafin ciwon ne yasa ya damketa, tunda itama in tana ciwon mara duk wanda ta samu damkewa takeyi, Iya kokarin ta tayi dan ta kucce daga jikin shi sai dai d'an bawan Allah keme me yakiya, sai ma k'ara mamaye ta da yakeyi yana cusa kanshi a cikin k'irjinta. "Ya'ya ka cikani inje dakina in kawo maka magani kasha, insha Allah kana sha zaka warke garas kamar ba kai ba" Shiru ba amsa sai ma hannun shi guda daya fara amfani dashi wajen shafo gadon bayan ta zuwa wajen kwankwason ta, Kamar wacce aka kwashe fuskarta da mari haka ta zabura jin yakai hannun shi kasa yana tattaro rigar jikinta data kasance doguwa yanayo sama dashi, "Innalillahi yaya dan Allah ka dena nice fa Meenal ba Maman boy ba!, nidai dan Allah ka cikani in kira wani ya kamamin mu kaika asibity dan kana bukatar ganin likita" Ta fadi hakan a yayin da take ta kiciniyar kwacewa daga jikin shi, Shiko kamar dutse haka ya koma mata dan yasan dai duk tsiyar ta bata iya kwacewa a hannun shi, dan haka sai ma ci gaba da yayi wajen ganin ya samar ma kanshi nutsuwa, Hannun shi data rike ya danne wanda hakan ne ya bashi nasarar jawo rigar har zuwa saman cikin ta, Dambe sosai take kokarin yi dashi dan ganin ta kwaci kanta a hannun shi fad'i take.... "Yaya kayima girman Allah dan darajar iyayen ka kayi hak'uri, Inma dan d'azun ban had'a maka abun kari bane yasa kake fushi dan Allah ka yafemin wallahi bazan kara ba, nidai dan Allah kayi hak'uri kaji wayata ke k'ara kuma wallahi Hajiya Innah ce ke kirana zata aiko a karb'a mata sak'o, nidai dan ka dena wallahi bana so" Sosai jikinta yaci gaba da rawa zuwa lokacin ko ai inda za'a auna jinin ta ba k'aramin hawa za'aga yayi ba, To jama'a fisabilillahi Ina dalili aure shekara sama da Biyar miji bai tab'a neman kaba sai yau kawai daga taimako yana neman haik'e mata, so yake yace mata tsayin shekarun nan mantawa yayi da hakkin ta wanda har hakan yasa mutane ke mata kallon tana shaye shayen maganin hana d'aukar ciki sai yau ya tuno da hakkin nata ko ya'ya abun yake, Da kyar ya iya fusgo kalmar bakin shi ya iya furtawa a fili da muryar shin nan da zafin ciwo yasa ta k'ara komawa masha Allah... "Ki tsaya fa karkisa inji miki ciwo!" "Iyyehh kuwa jama'a ku kawo min d'auki waiyo Allah Ya Sarki dan soyayyar ka da manzon Allah ka rufamin asiri wallahi tallahi ban shirya ba" Ihu sosai take mishi da kururuwar cewa itafa bata shirya ba, shiko mugun ko takan ta baibi ba illah ma maida hankali shi da yayi wajen ci gaba da cakuda mata jiki, sai dai kuma duk yanda yaso samun damar had'e bakin su saboda ihun da take tak'i yarda bori kawai take uwa wata wacce ke shirin tada aljannu tana neman dauki, Jin saukar bakin shi akan ajiyar da Allah yayi a kirjin ta yasata fasa wani uban ihu tana fad'in kalmar shahada kamar wacce ke gargaren mutuwa, "La'alaha illallahu muhammadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam, Shi kenan kwanan ki ya k'are Aminatu tun baki ga auren Besty din kiba, shi kenan Aminatun Malam zata mace tun bata zama cikakkiyar likita ba, Allah Sarki Malam za'a kashe makani tun ban gina maka gidan sama mai hawa biyu ba, waiyo Allah Yayan mu to aima ba haka akeyi ba, babu sallah ba kaza a farma amarya Sam wannan baya cikin shika shikan kwanciyar aure, ni wallahi bazan yarda ba ai nasan ita matar ka ba haka kaje mata babu kayan siyan baki ba, saini da ba'a so ne za'ama fashin budurci da rana tsaka, wallahi nidai tunda uwata ta haifeni banji inda aka tab'a nemar amarya da rana tsaka ba" (Nidai nace Meenal kila bakin nan bazai mutu ba sai an shiga daga ciki) Ture kanshi take ta kokarin yi dan sosai fa take jin ciwon yanda shiba jaririba amma ya wani kafa mata bakin shi dake cike reras da jerin hakoran shi a inda tunda tayi wayau take boyesu ga kowa, dan Allah jama'a maiya had'a babba da kayan da jarirai kesha, ga wani uban zafi da take jin suna mata wanda yasa babu shiru ta fara mishi k'ananun kuka a zaton ta wai ko zai tausaya yaji k'anta ya kyaleta, Sai dai mai makon hakan sai ma mirginata da yayi ya mai data kasan shi yaci gaba daya mutsa mata jiki, "Dan Allah dan Annabi karkayi a kasan tile's, ko wacce amarya a saman gado ake mata shi da lallashi shine ni za'a bajeni a tiles saboda dama ba sona kakeyi ba wato bari ka kasheni ka huta," "Zaki tsaya to in na mai dake saman gadon?" Ya tambaya ba tareda ya tsagaita da aikin da yakeyi ba, Kuka ta fashe dashi sosai. "Wai dan Allah da gaske kakeyi? Nifa Ina ce baka da lafiya ne shi yasa na shigo" "Maganin nike so ki bani ai!" Cak ya daga ta zuwa gadon, yana ko ajiyeta babu b'ata lokaci ta daka wani shegen tsalle ta dira ta d'ayan gefen tana sauke rigarta daya tattare, "Ina kike tunanin zaki gudu kije? Ke aiko wani ne yace miki zan barki ayau keda kanki zaki ce mishi k'arya ne kalli nan ki gani fa" Ya fad'i hakan yana mata nuni da gaban jallabiyar dake jikin shi daya taso, Ai da gudu ta maida idon ta ta rufe jikin ta na rawa taci gaba da rokon shi akan ya rufa mata asiri ya kyaleta, Komawa yayi ya duk'e dan tab'atan nan da yayi mai makon yaji sauki Ina sai ma k'ara kunnuwa yaji yayi, "Kizo nace" "Ai wallahi bazan zo ka kasheni da ranar Allah ba" Ta bashi amsa tun ma bai rufe baki ba, sannan ta d'aura da cewa... "Kuma wallahi kana k'ara tab'ani zanje in fad'ama Malam" Duk da yanda yake jin ciwo amma saida ta bashi dariya kuji fa wani shirme wai zata fad'ama Malam. "Me zaki ce mishi?" Ya tambaya. "Umm umm nidai kawai ka barni in tafi Ina ma ruwan ka da abinda zan ce mishi" Ganin tana k'ara ja mishi rai akan abinda baifi ya danneta ya kwata ta karfi bane yasa shi yunk'urawa da niyyar ya zafko ta sai dai kuma a dai dai lokacin cikin nashi ya k'ara mishi wani irin mugun kullin da dole sai da yakai kwance yana salati, Ita kuma a zaton ta wayau yake mata dan ta matsa kusa dashi, Da sand'a ta samu ta wuce inda yake kwance ta wani irin zabgaga da uban gudu ta fice a d'akin dan gara ta fita ta duba ko zata samu wanda zaizo ya fito mata dashi su kaishi asibiti, A bakin kofar falon ta suka kusan cin karo da Hajiya dake shirin shiga falon. "Ke kuma lafiya kike fitowa da gudu kamar wata wacce mutuwa ta biyo? " "Hajiya sarki ya Sarki ne baida lafiya wallahi mutuwa zaiyi in ba'a kaishi asibity ba dan Allah muje ki kamo min shi mu kaishi asibiti" Jan hannun Hajiyar ta fara da niyyar suje ciki, "Subhanallah meke damun shi? Tun yaushe ne bashi da lafiyan Ina ce yaune kukayi gurmin to yaushe ya fara ciwon" "Nidai Hajiya duk ban sani ba na dawo dai na same shi ya fado daga kan gado yana ta nishi kamar zai mutu" Matsawa baya kad'an Hajiya tayi tana k'arewa Meenal din kallo... "To ke kuma miya sameki haka naganki duk wani a yamutse kamar wacce ta kutto daga bakin kura? Kalle kifa duk kin wani yamutse" "To ba naje d'agashi mu fito bane kuma shine na kasa shi yasa na fito in kira masu gadi ai" "To ai ko yanzun sai mun nemo masu ceto Ina ni Ina iya d'aukar wannan mijin naki mai k'irar mutanen farko, koma daga ciki ki d'an gyara shi bari in ma Dan mai k'arfi magana yau ga ranar shi, dan nasan shi kad'ai keda zarrar d'auko shi ya fito mana dashi zuwa waje" Komawa cikin tayi kamar yanda Hajiya ta buk'ata yana nan kamar yanda ta fita ta barshi... "Ya'ya zamu tafi asibitin gasu Hajiya nan sun shigo" Hannun shi kawai ya iya mik'a mata yana mata ishara da cewa ta rik'ashi ya mik'e tsaye, "Ke takwara kuna ta inane? Ina d'akin mijin naki yake?" "Gamu nan Hajiya" Ta amsa ma Hajiyar tana fita daga d'akin. Hajiya ne a gaba shi kuma AK a bayan ta, fuska d'aure da alama dai dole Hajiya tayi mishi bawai da son ranshi ya shigo gidan ba, "To shiga daga ciki ka fito dashi ko! Ke kuma gyara mishi a hanya dan wannan aikin na maza ne ba iyawa zakiyi ba, nidai gani nayi da ace masu gadi da baku had'a komai dasu ba su shigo su gane miki sirrin gida ai gara shi koh? Naga dai ai koba komai shi d'an uwan kine, dan duniya yanzun ba gaskiya ka shigo da mutum yazo ga gama gane maka tsarin gida sai dare yayi a taho harda shi a yaye ka tass wallahi, nawa kuma akayi" Ita dai Meenal bata tsaya sauraron Hajiya ba itama tabi bayan shi cikin d'akin, Abunku da namiji yana zuwa haka ya d'ago shi ta gefe ya rataya hannun shi a kafad'ar shi sukaci gaba da taku sannu sannu har suka fice daga d'akin Hajiya na famar jera ma Sarki sannu da fatan Allah ya sawake, Motar da AK yazo da ita ya nufa dan dama kafin ya shiga gidan saida ya bude kofofin motar ya barsu bud'e, dan haka suna k'arasawa ya taimaka ma Sarki ya shiga, ganin fitowar sune kuma yasa sauran ma'aikatan gidan tasowa suna tambayan Lafiya, "Bashi da Lafiya"shine amsar da AK ya iya basu a takaice, gaban motar Hajiya ta shiga tayi ma kanta mazauni, ita kuma Meenal ta zagaya ta d'aya gefen da niyyar shigewa motar ita ma, "Keeee!!!! Gidan ubanwa zaki bimu a haka? da wannan shegen rigar na jikin ki kai ko kallabi babu karki sake ki shigar min mota na fad'a miki, k" Ya fad'a a matukar fusace, sai kuma ya juya inda ma'aikatan gidan sukayi cirko cirko "Ku kuma kuna iya komawa bakin aikin ku an gode" "To Ya AK dan Allah ka jirani in canzo kaya sai in fito mu tafi tare" "Eh na Jiraki mana tunda ga direban gidan ku, kinga kafin ki fito shi kuma ya mutu koh! Come on jare bace min anan" Hajiya ne tasa baki da cewa.. "Ah ah ka bari ta Sanyo ko hijabi ne sai mu tafi tare Ina zai yiwu mu barta ita d'aya" Jin Hajiya tasa bak'ine yasa ta samu kwarin gwuiwar falfalawa da gudu zuwa ciki, Shi kuma ya bita da kallo yana jin uwa zuciyar dake kirjin shi tana shirin fitowa, mai da duban shi yayi inda ma'aikatan gidan suke da ya tabbatar ba ita suke kallo ba sannan ya samu salama, Kamar yanda ta shiga da gudun hakan ta k'ara fitowa, Lokacin harya juya motar an ma bud'e mishi gate, Tun bata gyara zamanta a cikin motar da kyau ba ya gaza daurewa sai da ya furta, "Bana hanaki wannan yawan gudun da kikeyi ba? Ke me yasa har yanzun wai baki san kin girma bane, Abu kad'an gudu kamar wata shil shila" "Sorry" kawai ta iya furtawa, tana maida hankalin ta kan Sarki dake rik'e da cikin shi sai dai yanzun baya wannan nishin na d'azun bata sani ba ko ciwon ya ragune ko kuma ganin idon su Hajiya ne yasa ya kama jikin shi oho. "Wani asibity kuke zuwa?" "Dr Mubarak" Ta bashi amsa, Babu b'ata lokaci suka isa asibitin, kamar yanda ya tallafo shi daga cikin d'akin shi zuwa waje haka ya k'ara tallafa mishi suka fito a cikin motan kafin ma'aikatan asibitin su kawo kujerar da aka daura shi suka shige dashi ciki, Ganin an shige dashi ne hakan yasa Meenal nufa office din Dr Mubarak dan ta shaida mishi wanzuwar su a cikin asibitin, tunda ta mik'e yake binta da kallo ga mamakin shi sai yaga ta nufi office din da aka rubuta sunan maishi a saman kofar d'akin, "Keee" Ya d'aga murya yana kiranta, Juya tayi dan rainin wayau kuma wai sai itama take tambayar shi da cewa "ni" tana nuna kanta. "Eh kefa Ina zakije anan wajen?" Ya fad'a shima yana nuni da office din da take shirin shiga, "Dr zan gani" "Ke kadai?" Bata gane mai yake nufi ba dan haka bata iya bashi amsa ba. "Dawo nan ki zauna!" Kwabe fuska tayi kamar wata mai shirin yin kuka, "Hajiya kice mishi ya barni in shiga Dr din fa abokin Ya Sarki ne zan fad'a mishi ne saboda yaje ya duba shi" Kafin Hajiya tace wani abu sai ga Dr ya bullo da alama kiran shi akayi, "Dr Mubarak" Meenal ta kira shi tana k'arasawa inda yake tun bata jira ya amsa mata ba, "Ah ah Aminatu keda waye anan? Waye ba lafiya?" "Dr Ya Sarki ne babu lafiya yana can d'akin an shiga dashi nayi zaton ko kana cikin office din ka ne naso inje in sanar dakai sai kuma gaka" "Subhanallah Sufyan da kanshi! Tun yaushe ne bashi da lafiyan?" "Nima ban sani ba naje makaranta ne na dawo na sameshi a haka" "Subhanallah to bari inje in duba shi keda waye kuka zo?" Nuna mishi Hajiya da AK tayi, "Kakata da Yayan mu" Sai da ya gaisa dasu sannan ya juya zuwa duba halin da sarki ke ciki......... Ita kuma ta koma gefe AK ta zauna, "Ke saboda baki da kai shine zakije office din wani k'aton ke kad'ai koh?" Yayi maganar kasa kasa dan baya son Hajiya taji shi, "To ai shi d'in abokin mijina ne" Kamal saukar dalma akan gyambo haka yaji saukar kalmar a zuciyar shi, lallai ma yarinyar nan abun nata ya bunk'asa har shi zata cema wai wani abokin mijinta ne, Bayan ganin idon shi ai yaga abinda ke wahalar da mijin nata dan da taje gidan bai ganta ba amma yanda Hajiya ta dunga zabga f'ada tana ba Hajiya Jummai labari yasa ya fahimci komai tass................. To dai Sarki bai mutu ba masu mashi fatan mutuwa sai kuyi hak'uri ku cinye gumbar da kuka daka atoh. *ummiee Zaria*✍🏼[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 ~{{MY FAMILY}}~ *RUBUTAWA* *UMMIEE ZARIA* ````` *Page 41*.... "To ke yar nan ai sai ki kira mutanen gidan ku kona gidan su shi mijin naki dan su san abinda yake faruwa koh? Dan yanda muka kawo shi ranga rangan nan nasan indai likitocin nan na gaskiya ne tofa bazasu yarda su sallame shi ya koma gida ya mace a banza ba, dole rik'eshi zasuyi har jikin nashi ya dai'daita, Wai ke tsayama ! Shin ina kike cire rigar likitancin naki kika rataye wai da baki tsaya kin duba shiba? Kin daiji kunya wallahi kina likita a gida anma kin kasa tab'uka komai" "Uhmm nidai Hajiya dan Allah kiyi shiru asibiti mukefa ba gida ba, ke a ko ina ma sai kiyi ta surutu, kuma ni nama manta da wayata a gida ban d'aukoba da zamu taho sai dai ki bani Aron taki in kira dashi" "Kujimin wani zancen banza wajen yar wajen Jidda fa, to wallahi kiyi ta kanki dan nidai kin san da zarar naga ba dai dai ba tofa sai na tofa, daga cewa ki kira shine zaki hayayyak'o min kice sai dai in baki wayata salon kin cinye min katin wayar, badan halin kiba dai gata ki kira iyayen mijin na ki dan gara suzo su tsaya akan d'an su dan dai nida jikana ba zaman jinya zamuyi ba taimakon musulunci ne ma yasa na matsa mishi ya shiga ya fito dashi muka kawo shi asibitin nan, taimako dai ba wata abun tsiya ba to kin dai san sha'anin asibiti kar sugan mu da k'atuwar mota su fara lissafo abubuwan da zasu mishi amfani dashi dan nidai kudin jakata uzurin da zanyi dasu daban bana hidimar asibity bane, Atoh ina dalili za'a sani zubin adashin da babu kwasa bayan shi mijin naki ba gidana yake zuwa ba balle ince ya tab'a kawo min wani abun ko hakan zaisa yau in mishi kara, naki wasa ne yarinya bari ki gani uwarki zan kira ita tasa mayafin ta shiga gidan nasu fad'a musu" AK dake ta danne danne a waya ne ya amsa ma Hajiyar da cewa... "Ba sai kin kirata ba na riga na turama Sa'eed sak'o nasan zai kirani" AK ya bata amsa yana b'ata rai dan shima surutan ta sun fara sha mishi kai, inba abun Hajiya bama waye ya tambayeta ta bada ko kwabon tane, Kawai fa dan shi Sarki baya zuwa gidan ta balle ta samu damar more mishi aljihu shine yasa take duk wannan maganganun, Kiran Sa'eed daya shigo cikin wayar AK ne yasa shi tashi ya barsu a wajen yana nufar hanyan wajen asibitin dan ya tarbi Sa'eed din bayan ya amsa wayar. Dr Mubarak yad'an jima kad'an kafin ya fito daga inda Sarki yake, "Sannun ku da zama Hajiya" "Yauwa sannu Dr yamai jikin ya k'ara ji?" "Jiki alhamdulillah zai samu lafiya insha Allah dan zuwa anjima in ya k'ara warware wa ma kuna iya komawa gida dashi, amma Hajiya inba damuwa zanso mu d'an karasa daga cikin office d'ina domin akwai abinda nike so mud'an tattauna, akan ciwon nashi," "Ah ah dani kuma zaka tattauna? ai dai gara in ma wani abun ne ka jira har yan uwan shi su iso dan sune dolen shi, kaga nifa ba wata uwa na had'a dashi ba kawai dai ni uwar Jidda ce mahaifiyar matar shi amma bacin haka ni ban had'a komai dashi ba sai dai zumunta irin na musulunci da kuma auren shi da ke rataye a wuyan jikata, atoh Allah dai yasa ba wani abun bane ya taso, dan kaga ni dai bada shirin zuwa asibity na fito ba dan haka jakata ma yan kud'ad'en cikin ta basu taka k'ara sun karya ba," A zuciyar shi yace 😮 wow wanga tsohuwar daga gani yar jidalice, a fili kuwa dariya ya d'anyi, sannan ya daura da cewa.. "Hajiya dama ba wani abu bane domin maganar dama da ita matar nashi ya kamata inyi to amma tunda gaki a kusa shi yasa nike so kema kisa baki dan nasan zata fi jin maganar ki fiye da nawa inke kika fad'a mata" "Tooo subhanallah ciwon nashi kuma ya shafeta? Kai likita badai wani mugun ciwon yake dauk'e dashi daya gogama jikata ba dai koh?" "Ah ah Hajiya ko d'aya baya dauke dako wacce cutar da zai goga mata, mu k'arasa daga ciki dai sai mu tattauna da kyau" "Ke takwara tashi muje dan nikam gwuiwa ta ta fara sanyi kedai wannan aure naki dai toh Allah dai yasa kaffara ne, dan kina kan bautuwa" Tare suka jera har zuwa office din sannan Dr yayi musu nuni da kujerun dake gaban teburin shi suka zauna shima ya zagaya ya zauna. "Hajiya ko kina buk'atar wani abin a kawo miki? ruwa ko lemu wanne kike da buk'ata" "Ah ah wallahi na gode, kaga nikam da ruwan nan gara kayi gaggawar shaidamin abinda kenan dan insan wani sabon iftila'in ne kuma yake tunkarar jikata" Hannu ya mik'a ya zare glass din dake sanye a idon shi sannan yayi amfani da wani hankaci daya ciro daga aljihun rigar shi ya share fuskar shi, Kafin ya gyara zaman a kujerar da yake zaune kana ya d'aura da cewa.. "Hajiya a binciken da mukayi akan ciwon nashi mun gano cewar ba komai ne yayi sanadin ciwon ba face, hali na matsanan cin sha'awar da yake ciki domin ko rashin samun biyan bukatar da zai gusar da sha'awar ne yasa har ciwon ya taso mishi haka sosai, Abinda yasa nace ina son magana daku ba komai bane sai dan inyi ma ita matar shi nasiha, wala'allah ko sun samu sab'anin da yasa kila koda ya nemeta tak'i bashi had'in kai wanda hakan ne kila yakai shi a wannan halin da yake ciki, Domin dai inba haka ba wannan dole yaxam abun d'aure kai duba da cewa magidanci kamar shi ace yana fama da ciwon sha'awa alhalin kowa yasan yana da mace har biyu, na aure" Sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin yaci gaba da jawabin shi... "Nafi ta'allaka matsalar a wajen ita Aminatu duba da cewa anan dai itace a tare dashi" Juya gefen Meenal yayi ya fuskanceta da kyau, Ita ko Allah ya sani da tasan abinda zai biyo bayan shigowa office din kenan wallahi da bata shigo ba, kuji min sharri kawai zai wani ce wai laifin daga ita, ita ina ruwan ta da ciwon shi tuntuni bai san bashi da lafiya ba sai da yaga matar shi tayi komawar tane zai wani kama ciwo! "Meenal "ya kira sunan ta Bata iya amsawa ba tadai dago kanta kad'an, "Meenal meya had'aki da mijin ki wanda har yasa kike hanashi samun natsuwa dake?bayan kin san hakkin hakan a wuyar ki ya rataya! " Ji tayi kamar ace tayi wani siddabarun da zata bace b'at a wajen. To jama'a fisabilillahi wani amsa zata bashi? Hajiya ce ta amsa mishi da cewa, "Masha Allahu anzo inda nike so azo! Dan nan kace ciwon sha'awa ke damun shi koh?" "Eh Hajiya gaskiyar kenan" Waigawa tayi inda Meenal ke zaune sai faman mutsu² takeyi gaba daya ta kasa zama da kyau akan kujerar da take, "Ke takwara fad'amin shekarun ku nawa da aure yanzun?" Bata iya d'ago kanta ba ta amsa ma Hajiyar da cewa "shekara 6" "To kaji shekarun su 6" "Yauwa to fad'amin a tsayin shekarun nan sau

Chapter 36 of 92