Share this page
wacce ta matsa inda take suka mik'a mata gaisuwar kuma sukayi komawar su kan harkokin su domin ko acan baya ma fa suke hannunta babu wata shak'uwa a tsakanin su balle kuma yanzun day suke nesa da juna. Inda ace itad'in wata mai hankali ne tun daga yanda yaran data haifa da cikin ta suka wofantar da ita bayan tsayin lokacin da suka d'auka basu ga juna domin dai har an kai matakin dako ta shigo KD bata yarda Sarki yakai mata su a cewar ta bata son damuwa, wanda kamata yayi ace a yanzun da suka ganta su rugo da gudu cike da murnar ganin ta su rungumeta, amma ina ita shashashar ko a jikin ta dan K'annin Sarki ma da suka ma yaran magana cewar "bazaku je kuyi hira da mamar kuba, cewa tayi a barsu itama bata son suzo su dameta tana tare da gajiya, ****** Washe gari da safe kasancewar a gidan ta kwana, duk a kokarin ta na nunama Sarki cewan tana buk'atar kusanci da *Dangin shi* sannan dan ta k'ara tabbatar mishi da cewar tafa canza ba Teemar daya sani a shekarun baya bane wanna, Dan haka koda gari ya waye ma shigewa tayi cikin mutanen gidan aka cigaba da gudanar da abubuwa tare da ita sab'anin lokutan baya dako me za'ayi bata sanya kanta koda yaushe tana d'aki uwa wata sarauniya saboda tsabar jinkai da kuma kallon rainin da takema ahalin a ganinta tafi k'arfin shiga cikinsu sai dai ita su biyota. Sai dai kuma hakan da tayi yad'an sanyaya Uwar gida domin a yanayin yanda suka ga ta sake dasu wannan karon sai suke ganin kamar dai ba'a kyauta mata ba gashi tazo ta cimma bak'i cike da gida ana ta shirin bikin auren mijin ta wanda alamu suka nuna cewar bata da masaniya akan hakan! Domin sun san inda tasan ko taron me akeyi a gidan tofa daba wannan maganar akeyi ba a yanzun. Koda Uwar gida ta zaunar da ita tad'anyi mata yan nasihohi kafin ta shaida mata abunda ke faruwa, bata wani tada hankalin ta ba, illah ma nunawa da tayi ita bata da wani matsala da hakan, dan hakan ma k'arin arziki ne Allah dai ya basu zaman lafiya, da ita akayi ta shagalin biki domin tayi kokari matuka wajen danne wutar kishin dake ruruwa a cikin zuciyarta sosai kuma jama'ar gidan suka yaba da namijin kokarin ta harma da yawa daga cikin wad'anda suke adawa da ita fushin ta yad'an sauka a zukatan su, tunda ta ga an fara shirye² kawo amarya bayan magrib dan an shaida mata nan gidan za'a fara kawo yarinyar kafin a wuce da ita gidan ta, Kwarai taso ta tsaya a karb'i yarinyar da ita sai dai kuma a yanda takejin zuciyarta na yunk'urin biyowa bakinta yayo waje tasan bazata iya jure cigaba da basarwar da takeyi a cikin mutane bayan zuciyarta tana konewa a cikiba, kai bama fa lallai ta iya jure wa wajen hana kanta wafto wuyan yarinyar nan da za'a gabatar mata a matsayin kishiyarta ba, in hakan ko ya faru ai itake da fad'uwa domin ginin data fara ginawa ne zai rushe tun bata tabbatar da ingancin shiba. Dan haka ta d'auki excuse cewar bata jin dad'in jikinta ta koma Hotel d'in data sauka tsabar kishin dake nukurkusar tane yasa zazzabi ya sauko yayi mata rubdugun da dole sai da Sarki yaje ya zauna da ita domin dama koba zazzabin ta kuduri aniyar cewa Sarki bazai kwana a gidan shiba balle kuma har su samu daman keb'ewa da amaryar shi a ranar, to can dai Sarki ya lalace dan sosai suka raya daren cike da soyayya domin dai wani sabon amarci sukayi a karo na biyu aka bar Meenal da kwana da nata kawayen. *** Washe gari kuwa duk wani abunda ake gabatar ma wad'anda suke taya amarya kwana sai da aka gabatar ma su Meelat dashi kasancewar kuma abu ya zama unguwa guda yasa tunda gari ya waye sukaci gaba da amsar bak'i yan ganin d'aki, A gidan Malam ko bak'i na nesa kuwa tuni suka fara komawa garuruwan su, Ganin dai babu wani abunda ya canza domin dai bayan tabbatuwar aure gashi dai har an kawota gidan da koh a mafarki aka nuna mata shi a matsayin gidan mijin da zata rayu a cikin shi tofa saima ta tub'e kafin ta tattaro k'arfin da zata daku da duk ma wanda ya gabatar mata da hakan amma gashi wai a gaske hakan dai ya faru ba mafarkin da take ta tsammanin zata iya farkawa ko wani lokaci ba hakan yasa dole ta aro jarumta ta d'aura ma zuciyarta, to me yayi saura kuma hukuncin Malam nefa da dai ace wani daban ne ya d'auki nauyin shiryawa da gabatar wa ba shiba to da ta dage kwarai wajen nuna turjiyanta akan hakan dan tasan zata samu goyon baya daga Ma'am dan haka yanzun kam kuka ai bashi da amfani kuma sai dai ta zuba ido taga yanda rayuwa zataci gaba da juyawa, dan haka tuni ta hak'a rami acan k'ark'ashin zuciyarta ta bunne damuwarta harta da wacce ke kan fuskanta tayi kokarin maidashi ta aro ma kanta jarumta. Sai dai kuma har yanzun shiru take bakin nan nata kam ya mutu murus sai idanuwa da take bin mutane da shi ko abokan wasan ta da ta saba jansu suyi ta raha wannan karan kam ba dama, K'arin haushin kuma shine tun jiya da yamma taga an cire mata layukan ta dake cikin wayar ta sai fankon wayar aka bar mata, ita babban tashin hankalin ta shine so take taji wani hali dan gidan master yake ciki amma tasan hakan bazai yuwu ba domin dai ita ba jahila bace tasan hakkin dake rataye akan ta na auren wani yanzun, tana dai mishi fatan alkhairi Allah ya bashi wacce ta fita, tasan dai Allah ne kad'ai zai wanke ta akan kallon dazai dunga mata a matsayin wacce ta yaudare shi. *Bayan kwana biyu* Tun dai Meenal na zaman d'ar d'ar na jiran tsammanin shiga wata rayuwar sabuwa yanzun kam harta saba , domin dai yan biki duk sun koma gida jen su, domin dai zaman ta a wannan gida zamane na babu mai takura mata bamai sawa balle hanata domin dai abunda ransu ya raya musu shi sukeyi ita da kawayen ta, su dafa abunda suke muradin ci suci duk dakoh cewar kullum ana aiko mata da abinci daga gidan su Sarki dama nasu gidan amma indai su Moon sun shigo wajenta sai sun jata kitchen sun had'a wani abun wani lokacin ma har kusan 10 na dare sukan kai a gidan suna d'ebe mata kewa gari na wayewa kuma kannin Sarki ke shigowa suna tayata tsaftace gidan, dan haka sai kewar gidan su ya zama sauk'ak'ka a gareta domin tana samun masu shigowa dubata kuma kullum sai sunyi waya da sauran. Allah ma ya taimake ta da yike ana hutu hakan yasa gaba d'aya bata da wata damuwa miji dai ba ganin shi takeyi ba balle ta tsan gwami kanta, Shi dai ango tunda aka d'aura aure har yau Allah bai sa sunyi ido biyu dashi ba domin dai baya shigowa gidan in ma yana da bukatar wani abun da zai d'auka sai cikin dare ko kuma ya aiko Kwaro ya d'aukar mishi abinda yake bukata yana can ya b'oye fulawar shi a d'akin Hotel suna gwangwaje wa a filin wasa, dan jama'ar gidan su Sarkin ma har sunyi zaton ko ta koma ne babu sallama kamar yanda ta saba, sai dai ita a gefenta har yanzun bata saku kwarin gwuiwar da zata iya fuskantar amaryar nata bane, kwanciyar hankalin data k'ara samu kuwa ganin cewa gaba d'aya bataga d'aukin auren a wajen Sarki ba domin ko ya'ya ta d'auko zancen amaryar sai Sarki ya nuna baya bukatar zancen. °°°°°°° Zaune take akan kujerar 3sitter d'in dake cikin d'akin Hotel d'in da suka maida matsayin gida a yanzun, A yayin da ta d'aura duka kafafuwan ta dake mik'e sambal akan center table d'in data jawo zuwa gaban kujerar wayar tace a hannun ta guda 1 tana latse² yayinda d'ayar hannun nata kuma take amfani dashi wajen tausa mishi gashin kanshi, kasancewar shi kwance yayi pillow da cinyoyinta sala² dake waje sai shek'i sukeyi wanda hakan ke nuna zallar hutu da fatar ke d'auke dashi sakama kon kasancewarta sanye cikin kananun kaya wato gajeren wando da wata shed'aniyar half vest wacce an dai satane kawai amma bawai dan ta rufe wani abuba, Irin wadan nan shigar sune mafiya soyuwa a wajen sarki a duk sanda zai kasance tare da ita dan haka ita kuma tunda ta gane lagonshi ta rike mishi wuya taci gaba daci mishi uwa, Dan yanzun kam ta k'ara tabbatar da cewar mijinta nata ne ita d'aya. "Sarki ina son zan koma Lagos zuwa gobe fa domin akwai wani workshop din da zamu gabatar cikin satin nan kuma komai yana hannu na, sun kirani suna tambaya akan mai ake ciki kuma gashi ni ina nan, kaga kuma ya kamata dai kafin in tafi inje inga kanwata domin bai kamata ace har in koma baka gabatar damu a wajen juna ba, gashi kuma kai ka tare anan nasan tanacan cikin kewa" "Haba Gimbiya nayi zaton kin d'auki hutu ne zamu d'an kwana biyu a tare ashe kwalele kikazo kiyi min" Wata irin dariyar kissa take binshi dashi k'asa² cike da barikan ci tace "Haba Sarki na, ni harna isa inzo in maka kwalele kai da gonarka, sai dai ai kasan kodan saboda Boy dole in koma duk da dai nasan hannun dana barshi za'a kula dashi fiye da yanda zasu kulama da nasu dan kasan yanzun fa Boy ya doke matsayin kowa a gidan mu amma gara dai ace ina kusa da kayana, kai kuma dan ka bini mun koma tare aiba laifi bane! naga dai ko ka zauna ita amaryar taka ba wata tsiyar zata iya tsina na maka ba domin dai Sarki ai sai Gimbiyar shi" "Tunda haka kikace zan duba in gani ko bamu tafi a tare goben ba in yaso zanyi kokari in biyo ki a baya cikin satin nan dama ko ba'ayi haka ba akwai abunda zai kaini Lagos d'in balle kuma kinzo kin min d'and'ani haukaci gashi duk kin wani kasa sakewa ki kula dani da kyau" "Ah ah fa Sarki na bafa laifina bane domin dai kaine baka iya rik'e kanka da zarar an shiga filin wasa duk sai kabi ka rikice ka nemi fara kururuwa kaga kuma nan bafa gidan mu bane Hotel ne kasan kuma ina da kishi bazan so wani ko wata yajiyo muryarka a irin yanayin dani kad'aice ya dace naji shiba" "Ohh haka ne wato ma ni kadaine bana iya rik'e kaina to bari mu gani yanzun waye zai gaza iya rike kanshi a wannan karan" Ya fad'i hakan a yayinda ya yunkuro da nufin wawurar ta, gane nufin shi yasa babu shiri ta zabura suka fara zagaye d'akin daga karshe dai har yayi nasarar damk'ota yaci gaba da d'aura mata karatu. Da yamma liss kuwa suka shirya shida ita kamar yanda ta buk'ata suka kama hanyar zuwa wajen Amarya, Sai da suka fara shiga gidan su Sarki tayi ma mutanen gidan sallama wannan karan dai tsabar ta shirya ma abun harda gidan Malam sai da ta shiga ta kuma bi kaf sassan gidan suma ta gaishe su a karo na farko da dayawan sirikan gidan wadanda basu santa ba sukayi tozali da ita, ciki kuma harda sashen Mommy Hauwa saida ta shiga d'akin Malam shine na k'arshe inda ya had'asu ita fa Sarki ya musu nasiha akan suji tsoron Allah su kuma zauna da juna lafiya Allah kuma ya had'a kawunan su, Itako a cikin zuciyarta babu kalar tsinuwar da batayi ma Malam ba domin tsaf labarin komai ya dawo kunnen ta na cewar ashe yarinyar ma auren dole yayi mata Dan hakan tasan bazata sha wahala ba wajen ajiyeta a matsayin ta, shine dan bak'in munafunci ya ajiyesu a gaban shi yana karanta musu suji tsoron Allah, to shi d'in yaji tsoron Allah ne wajen auren ma mijinta yarshi akayi mata kishiya babu shiri? Ko wani shegen ne yace mishi ita d'in irin matan su na Arewa ne da ake jerawa kishiyoyi kuma harma a zauna lafiya, hummm badai aure ba bismillah ayi zaman auren ta gani indai da mijinta ne, Ummiee Zaria✍🏼 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!* 👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *It's a free book ga masu buk'ata daga zasu iya tuntub'ana kai tsaye*08061358462 """"""Page 34 Yauma dai kamar kullum gidan na Amarya Meenal ya samu ziyarar su Aisha, Maimoon, Maryam, Jameela harma da Rukayya, Tun jiya Meenal d'in ke magana akan faten shinkafa take sha'awa dan yau d'in faten shinkafan suka girka wanda Maryam ce ta jagoranci girkin kasancewar kaf cikin su hannun ta yafi fad'awa a wajen sarrafa abincin gargajiya, su dai sauran barsu wajen iya sarrafa kayan kwalam da makulashe, Zazzaune suke a kasan carpets d'in dake shimfide a tsakiyar falon sun zagaye farantin faten dake tsakiyar su, suna sha suna hira. Sai da Moon ta had'iye lomar dake cikin bakin ta sannan ta gyad'a kai gefe cikin kasalalliyar muryar da al'ajabi ya cika take cewa " wani dan Allah ku bakwajin mamaki kamar ya kashe ku?" Bata jira cewar su ba ta maida cokalin hannun ta cikin faranti tana mai k'ara gyara zamanta karamin murmushi ne kwance fuskarta sai da ta gama k'are musu kallo sannan ta bud'e baki tace, "wai Allah mai iko wallahi kullum in nazo kofar gidan nan na wuto bakin gate har na k'araso ciki na iske Meenal zaune sai inyi ta mamaki wai Meenalin Malam ne a cikin gidan nan Matar Sarki kuma! , kai jama'a dan Allah inba Allah ba waye ya isa ya yanke hukuncin nan kai tsaye ai sai dai shi,! " Kallon ta ta maida kan Meenal sannan ta had'e hannuwan ta guda biyun 🙏 alamun ban hakuri tana maida dubanta kan Meenal din taci gaba da cewa "Nidai please³ 🙏 sister kiyi hakuri da duk shiriritar da nayi a baya ba laifina bane sharrin yarinta ne duk wanda ya kalleni ai dama yasan girman jikine kawai ba shekaru, Allah kuwa girma ne kawai ya riga hankali zuwa inba haka ba ina ni ina Sarki ai kowa ya san yafi k'arfina" hannu wanta ta maida kan kunnuwan ta ta rike su suma sannan ta tashi daga zaunen da take ta tsugun na still dai hannayenta rike suke da kunnen ta saita d'an duk'e kamar zata kai goshin ta k'asa sai kuma ta d'ago zuwa ga tsugun nin da take "kiyafe min sister! Ki yafe min³!! Kar kici gaba da kallona a matsayin wacce ke son mijin auren ki wallahi ni dama ban sa shi a zuciyata ba duk abunda nikeyi inayi ne kawai a lokacin dan in tsokane ki tunda naga bakyason ana miki maganar shi, Allah ya gani ko a mafarki ban tab'a zaton zaki zama matar Sarki ba wata rana". Sake da baki Meenal ke binta da kallo yayin da su kuma sauran ke dariya k'asa² dan tun da aka gama biki babu wacce ta tada maganar yanda abun ya kasance dan babu wacce ke son ta kwanto ma kanta kura tunda ita uwar gayyar ta nuna musu bata son maganar dan haka sukaja bakunan su suka tsuke, Kallon Aisha Meenal tayi "Ke Aisha hala dai yarinyar nan ta fara zuk'e² da kurb'e²n kayan maye ba tareda sanin kowa bane? Ko kuma Ah² tsabar iskancin Lagos ne ya biyota har nan? Ashe ba k'arya Hajiya takeyi ba da tace kaji tsoron Allah ka kuma ji tsoron yan iskan Lagos, to na rantse in kika k'aramin maganar banza anan bazan k'ara kulaki ba har kibar garin nan tam! bama Sarki ba ah ah Saraki" ta k'arasa fad'in hakan a zuciye tana jan kwafa taci gaba da shan faten ta, Babu wacce ta k'ara tada maganar har suka kammala suka kuma gyara wajen sannan suka koma saman kujerun falon sukaci gaba da sha'anin su. //////Babu sallama balle ayi zaton neman izinin shiga Teemah ta bud'e kofar falon kai tsaye ta shige, kasantuwar dukan su hankulan su ya d'auku akan kallon film din da sukeyi hakan yasa basuji motsin shigowarta ba har sai da ta iso tsakiyar falon, kwas! kwas! Kwas d'in da takun takalmin ta yake badawa akan tile's d'in falon ne yajawo hankalin Meenal dake buga game da wayarta dan ita ba kallon film d'in take yiba, sai dai kallon matar kawai taci gaba dayi ba tareda ta iya ce mata komai ba, to jama'a me zata ce mata? haka kawai mutum ya fad'o maka cikin gida babu koh sallama sannan kuma yanayin shigar matar babu ta inda ya nuna cewar tana da tabuwar hankali balle tace ko mahaukaciya ce ta kutto daga wani wajen ta fad'o nan ko kuma to kila dai makuwa tayi! Dan haka da ido taci gaba da bin ta har zuwa sanda ta nemi d'aya daga cikin kujerun falon takai zaune tako d'aura kafarta d'aya kan d'aya abunta tana mai bin falon da kallon kurullah domin ai tunda aka gina gidan bata tab'a shigowa cikin shiba tadai ga gidan a hoto da video d'in da Sarki yayi ya kai mata a lokacin da ya so ta dawo gidan tak'i, Ganin zaman nata a falon bai wadatar ba yasa ta mik'ewa ta fara zagaye falon, da kallo duka su Meelat suka bita dan sai yanzun suka lura da ita suna tambayar Meenal da "wacece" ita koh dage musu kafad'a tayi alamun oho bata sani ba, Maryam ce tayi k'arfin halin gaisheta da cewa "ina wuni" amma ko alama matar nan bata nuna taji abunda Maryam d'in tace ba sai ma basar da ita da tayi ta k'arasa wajen dinning table din dake gefe tana karema wajen kallo domin yanda ya k'awatu a idon mai kallo kwarai gwanin ban sha'awa ga mai kallo, gaba tayi ta k'arasa hanyar da zai sadata da kitchen ta bud'e kofar ta tura kanta ciki ba tareda ta zura gangar jikinta gaba d'aya ba, shima dai sai da ta k'are mishi kallo a zuciyar ta tana mamakin dukiyar da aka narka ma yarinyar nan, anya ma ba kud'in mijinta suka samu sukayi facaka dashi haka ba? Inba haka ba ai ita bataga alamar cewa sun mallaki dukiyar da zasu kashe ma yarinyar mak'udan kud'i har hakaba! Bayan kuma ba ita kad'ai suka aurar ba waya sani ma ko baashi suka ciyo saboda gudun kar suji kunya dan ai daga ganin tsarin gidan duk wanda ya shigo dama yasan gidan yafi k'arfin a zuba mishi k'ananun kaya, to in ma dai baashin ne to su shirya maidawa mai kayan kayan shi in ya so a basu kud'in su su rage zafi, dan Wallahi babu shegiyar da zata zauna mata a gidan da aka gina da sunan ta, baza tayi saurin korata a yanzun ba domin hakan yana iya b'ata mata tsarin ginin ta data d'aura amma yanzun d'in ma sai dai yarinyar ta zauna mata a matsayin yar gadin gida badai matar gida ba. Fitowa tayi daga wajen taci gaba da zagayen d'akunan dake k'asa sai da ta gama ta juyo tana k'are musu kallo ganin su a tsatstsaye suna binta da kallo banda Meenal wacce ke zaune tanaci gaba da game d'inta kamar ma bata san meke faruwa a falon ba. Sai da ta k'are musu kallon tsaf Addu'ar ta d'aya shine Allah dai yasa ba waccan yarinyar bace dai kishiyar nata! Domin tun kallon farko data mata taji gaban ta ya yanke ya fad'i, Kallon su taci gaba dayi daya bayan d'aya kamar yanda suma suke kallon ta cike da mamakin karfin halin ta, sannan ta bud'e bakinta da wani irin girman kai da isa tace "Ita matar gidan bata iya fitowa ne a sanda bak'i suka shigo mata?" Babu wacce tayi zaton cewa Meenal zata bata amsa a dai² wannan lokacin har sai da kunnuwan su ya jiyo musu muryar ta a yayin da take ba Teemah amsa da cewa, "ita matar gidan takan tari b'akin da tasan da zuwan sune kad'ai bawai masu fad'owa daga sama babu gayyata ba," sai da ta d'ago kanta suka ma juna kallon ido cikin ido ita da Teemah sannan taci gaba da cewa... "baiwar Allah ina ganin kamar makuwa kikayi dan haka ki d'an koma ta gefen hannun damar ki inaga kamar tanan kika biyo koh? Bismillah kina iya komawa inda kika fito mun gode da gaisuwa" Zaburo wa Teemah tayi kamar mai shirin rufeta da duka sannan cike da jin haushin abinda yarinyar tace mata itama ta maida mata martani da cewa, "Ke din wacece da har zan shigo gidan mijina uban yarana kice wai in fita? gaki k'aramar yarinya dake amma alamu sun nuna baki da tarbiya" Yunkurowa itama Meenal d'in tayi domin sosai itama kalmar karshe na matar ya b'ata mata rai wai itace bata da tarbiya dan haka ta maida mata martani da cewa "tarbiyar ne yasa naga an shigo gidan matar aure babu sallama" Suna cikin wannan cacar bakin Sarki ya shigo falon Kwaro na take mishi baya, "Mike faruwa anan? " ya tambaya ganin su a tsaye kamar wasu zakarun dambe. Simi² su Meelat sukaja hannu wan juna suka shige d'aya daga cikin d'akunan dake kasan suka rufo kansu harda murza key, domin dai wannan ai family issue ne sukam basu da ruwa a ciki, ganin hakan yasa ita ma Meenal din juyawa da niyyar barin falon sai dai kuma tana takawa Sarki ya tsaida ta da cewa "dawo nan! ya ina magana daku kike shirin tafiya kuma" Teemah ce ta tari numfashin shi da cewa... "Baban Boy kar dai kacemin wannan mara kunyar yarinyar ce amaryar da ake ikirarin an aura maka?" Bata jira amsar tambayar nata ba ta d'aura da cewa.. "Sarki wani kalar abin kunya kake shirin jawomin, karasa matar da zaka auro ka had'amu kishi akan ka sai wannan yar kankanuwar yarinyar? ana ta cewa k'aramar yarinya nayi zaton zan ganta cikakkiyar budurwar da zamu goga zaman kishi da ita sai naga wannan abar... yanzun fisabilillahi a hakan ka iya nunata ma abokan ka yarinyar da a haife ka haifeta? Lallai yau na k'ara tabbatar da halin ku na ya'ya maza da kullum ake fad'a" Zagayen falon ta farayi takai gauro takai mari hannuwan ta duka a saman kanta kamar wata wacce aka aikowa sak'on mutuwar uwa da uba a lokaci d'aya. "Calm down please mana Teemah" Ya fad'a yana shirin kamota dan sai wani abu take kamar wata mai shirin tada aljannuh, ita koh tashin hankalin ta shine ganin abinda batayi tsammani ba, tabbas an bata labarin cewa k'aramar yarinya ce, to amma ita idanuwan ta abunda suka gane mata shine cikakkiyar budurwa mai mulmulallan jiki da cikakken dirin da bako wani namiji bane zai iya mata kallo guda ya d'auke kanshi, bayan wannan kuma ga wani irin masifaffen kyau data gano a fuskan yarinyar wanda ita kanta bata iya mata kallo guda ta d'auke kaiba ina kuma ga namiji irin mijinta da dama babu abunda yake bala'in burgeshi irin mace mai kyau kuma dirarra, wanda sanin kanta ne wad'an nan abubuwan su suka k'ara taimaka mata wajen shawo kanshi a lokacin data nuna tana son shi, domin shi dai mutum ne mai son matar fita kunya da hakan kuma take k'ara amfani da nata kyan da kuma salon kissa da kisisina ga kuma kulawa da kanta da takeyi duk dan kar dai ya hango wata a waje, shine yanzun aka wani d'auki wannan yarinyar mai siffan aljannun ruwa aka aura mishi gata kuma da kana nan shekaru, kai inahhh wallahi da sake dan bazata zuba ido aikin data fara ya lalace ba, ta sani sarai cewar babu kalar munafuncin da maza basu iyaba inhar ta barshi da yarinyar nan tofa yana iya mai data wata dankalin hausa a gefe yazo ya dunga

Chapter 30 of 92