Share this page
gamida cewa "ni din? " "Kwarai kedin fa ko cemiki akayi bana lura dake a duk sanda zamu hadu?" Bata da amsar bashi dan haka tayi shiru, saima dukar da kanta da tayi tana wasa da ledar dake hannun ta, "Uhummm ke nikejira" "To... to.... toow nidai kayi hakuri, ba kai bane duk sanda mutum zai ganka kana cikin jama'ar ka, in ma an ganka kai kadai to waya kakeyi ni kuma shi yasa nike wucewa bana gaisheka" "Wato in mutum yana cikin mutane bazaki gaishe shiba kenan? amma ai a hakan kike gaisheda su Musty su kuma miye alaqar ki dasu? Bata bashi amsar tambayar farko daya mata ba sai ta biyun, inda tace "to ai shi Musty sunan Baba Malam yakeda" Saida ta gyara zaman takalmin kafarta ta kuma rike ledar hannun ta da kyau sannan ta daura da cewa, "Kuma su ai dukan su suna da sakin fuska suna ma mutane dariya kai koh fuskarka kullum kamar ta shanu" Tana gama fadar hakan kamin kiftawar ido ya hangota ta falfala da gudu zuwa sashen Hajiya. Baki da hanci ya bude yana kallon ikon Allah, Wato ma shi yarinyar nan ta Kira da mai fuskar shanu, Da gaske dai kenan abokin wasan nata ta dauke shi. Girgiza kanshi kawai yayi fuskar shi dauke da karamin murmushi, "Allah ya shirye ki" Baiyi yunkurin bin bayan ta ba sai ma sashen shi daya wuce dan koba komai hakika yana bukatar hutu dan haka zaije yadan watsa ruwa kafin yaci abinci. Sai dai me? Yana bude d'akin nashi anan bakin kofar ya tsaya ya cire takalmi da safar dake sanye a kafar shi, sai dai kash domin ko baiyi taku mai nisa ba Allah ya hadashi da gamon shi, wato k'afa yar hutu wacce bata dauke da faso ko kauje ga kuma danshin safa ne ya hade da santsin tayes sakama kon ruwan da har yanzun bai gama bushewa ba, aiko dai kafin ya ankara ji kake suuuuu tabb duwawun shi ya maku da kasa dan ainihin faduwar da ake kira faduwar yan bori shi yayi, "Innalillahi Wa'innah Ilaihir Raju'un, waiyo Allah na wash bayana subhanallah" Kalmomin daya dunga maimaita wa kenan cike da azaba dan wallahi yafa maku da kasa da kyau bawai faduwar wasa ba, bai iya tashi a wajen ba saida yaji rad'ad'in da jikin shi ya dauka ya ragu tukun na, sannan ne ya lallaba da rarrafe ya karasa cikin dakin shi, wajen wardrobe din shi ya wuce da niyyar ya ciro kayan da zai canza domin na jikin shi dai sun gama nad'e sauran ruwan dake wajen, sai dai me? Yana bude kofar kayan da dama jira suke a bud'e kofar su zubo suka biyo kofar gaba daya haka suka danne shi da yake a duke yake, Kaya! kaya haka dai ya samu yayi watsi da kayan a gefe, cike da jin haushi ya koma gefe ya zauna ranshi a bace can kuma ya fara bin d'akin da kallo dan ya tabbatar ba haka ya fita ya barshi ba to waye Hajiya taba key din dakin shi har aka shigo mishi, dan yasan dai Wallahi wannan ba aikin Larai bane, to " waye? " ya tambaya a bayya ne, zuciyar shice ta bashi amsa da cewar "yarinyar nan", kai anya kuwa? Yes itace dan tabbas dazun yaji kamshin turaren shi a jikinta, "To kenan ita ta shigo min d'aki? Meya kawota dakina? Aiko zata sani wallahi" Ganin sakar zucin bazai fishsheni bane hakan yasa shi daddafawa ya mike, dan gara yayi sauri yaje ya ritsata kafin tabar gidan, bai jira komai ba ya wuce gefen Hajiya hannun shi daya dafe da kwankwason shi. ***** Da gudun ta tafado falon na Hajiya dan a zaton ta yana iya biyota, Kiririf ta maida kofar falon ta rufe harda murza makulli. Ke! Ke!! Ke uban waye ya biyo ki kika fadomin falo haka kamar wacce mutuwa ta biyo, ah gaskiya baki da kyakykyawar d'abia wallahi nidai kin dauki alhakina haka kawai ana zaman kalau zaki fadomin daki kamar an jeho ki mtws Kuma ki koma ki budemin kofa dan ina kallon masu min shiga da fita ne tunda mutanen gidan basa nan, Ita dai bata kula Hajiyar ba saima karasawa inda jakarta yake da tayi, "Ita Turan da kika kai mata dambun sunan ubana ta kira ta zaga koh ya'ya ? dan banji kince min tace ta gode ba! " "Kai Hajiya ba yanzun na shigo ba ko zama fa banyi ba, ai kin san dai dole zatayi godiyar kuma harda ma kaya Aunty Billy ta bani Dadah kuma ta bani wani sak'o wai in kaima diyarki" "Wacece kuma Aunty Billy a gidan? Bakuwa sukayi? " "Hajiya Bilkisu fa nike nufi ba wata ba" "Allah Sarki itace ta baki kyautar kaya? " "Eh Hajiya wai telan ne ya matasu sun matseta shine ta bani kin gansu! " Ciro kayan tayi daga cikin ledar tana nuna ma Hajiya, "Ah lallai kinsha godiya kuma kayan masu tsada ne, to Allah ya mata albarkha Allah kuma ya dubi zuciyarta ya fito mata da miji na kwarai tayi aurenta ta huta, dan nidai tausayi take bani yarinya bata rasa komai ba na diya mace amma ace miji ya gagara samuwa, aini dai dan kar inyi shish shigi ne dana nema mata miji wallahi, to yanzun abun alkhairin nema baya dorewa kar in hadata da wani in abu baiyi dad'iba ace nice sila, amma inba haka ba aiko yaron kirkin nan Saddeequ nace ya nemi aureta nasan bazai kiba tunda masha Allah yarinya ce mai kyau wallahi sak kakarta turai to tsoro nike shi yasa ban mishi maganar taba" Katseta Meenal tayi da cewa "Hajiya Ya' Sa'eed ke neman tafa, kuma aurenta yake sonyi" "Kai madallah, madallah too kice duk mune aiko na mata murna wallahi miji irin Sa'idu ai idan ka samu saika rike abinka kayi ta riritawa, to aiko zan samu Dadah da batun gara ace ya fito a musu aure tun kafin shima a neme shi a rasa" Kwankwasa kofar da akeyi ne ya katse musu hirar da suke. "Kinji koh? Shi yasa nace ki budemin kofata dazun amma da yike kunnen kashi gareki kikamin kunnen uwar shegu yanzun ai kya bude" "Waye? " Meenal ta tambaya a yayinda take bude kofar, bata samu amsar tambayar nata ba idon ta yayi tozali da AK da tambayar nata ya kara fusata shi, Zaro ido tayi ganin shine, "Waiyo Allah dan Allah kayi hakuri wallahi bazan kara ba" Baice mata komai ba illah janyo hannun ta da yayi suka koma cikin falon. "Hajiya me yarinyar nan taje yimin a d'akina? " Ya fada a sanda suka karasa inda Hajiyar ke zaune tana kallon su, "Mai kuwa zai kaita banda ta gyara maka d'akin tunda ba kowa a gidan, wani abune ya faru? " Bai iya bata amsa ba illah juyawa da yayi ya jawo Meenal zuwa gaban shi baiyi wata wata ba ya sauke mata wani irin lafiyayyen rankwashin da sai da yasa takai kasa bayan ta fashe da k'ara nan kuma kukanta ya cika d'akin, "Kai Abdul ka kiyayeni fa wani irin rashin mutunci ne zaka kawo yarinya har gaba na sannan kaci zalin dinta, na tambaye ka meta maka baka bani amsa ba shine kake kokarin bula mata kwakwalwa da gudumar hannun ka? To kasan dai ko banyi Allah ya isaba sai Allah ya saka mata tunda dai ni na ce taje ta gyara dakin....... Share Please #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen. Ina ma d'aukakin al'umman musulmai barka da sallah tareda fatan Allah ya maimaita mana🥰 Here is your sallah gift, kuyi karatu har ku gaji😂😂 ```Page 26 Ai kasan dai ko banyi Allah ya isaba sai Allah ya saka mata, tunda dai ni nace taje ta gyara d'akin, shine dan bak'in mugunta zaka kama musu yarinya kana neman kwankwashe mata kwalwa , zonan takwara in gani Allah yasa dai bai rusa miki kai ba? Ke dama gaki nan kullum kamar wata kalallab'a". ta fad'a tana janyo Meenal din dake ta kwarara ihu tana murje² a kasan tile's kamar wacce ake yankawa zuwa jikin ta, "Yi hakuri kinji barshi da halin shi ai tsabar mugunta ne ke damun shi to jama'a inba mugunta ba mai zai d'iba a jikin wannan lab'ub'uwar yarinyar ? in mutum tak'amar shi karfi basai ya fita cikin maza ko yaje gidan damben dake Sabon Gari ya tub'e su daku da mazan ba, shine zai huce haushin shi akan jikata, yi shiru kinji uban shi zan kira yajama d'an shi kunne ya shata layi tsakanin mu in kuma ba haka ba wallahi koni ina iya mishi kud'in jirgi in tarkata mishi kaf kayan tsiyar shi dake gidan nan in kuma had'a shi da police su rakamin keyar shi zuwa airport ya tafi can inda iyayen shi nima in huta atoh haba Jama'a ina ma dalilin wannan kwazzaba nikam." Har ya juya da niyyar barin falon jin abinda Hajiya ta fad'a yasa shi juyowa yana mata wani irin kallon dashi ba harara ba shi kuma bai rufe idanun ba, kasa² dai yakeyin kallon. "Hajiya! Hajiya!! Hajiya kin san dai bako yaushe nike son ana shiga gonata ba koh, kuma kud'in jirgin da zakimin ki tsakura a ciki ki siyama jikar ki paracetamol" Yana gama fad'in hakan yasa kafa ya fice ko waigen su bai karayi ba, Astagfirullahi ya Allah kasa inga annabi jama'a me nike shirin gani yau ni Aminatu? Ke takwara kinga abinda ya faru a falon nan nawa yau kuwa? Nagode Allah a gaban ki akai komai kema kin isheni shaida dan babu abunda zai hana ni kiran uwar shi dan dolenta ta baro Saudi tazo ta dauki takadirin d'an ta dan wannan shara'ar tafi karfin ayita a cikin waya sai ido da ido, dan in ban mike tsayeba zuwa gaba yaron nan yana iya shigomin har falon nan ya kashemin fuska da mari" Hajiya duba min kaina Allah kuwa ya rotsamin kai! " gyale da hular dake kanta dama tuni suka kama gaban su, "Ke da Allah ba wani fa shafewar da kanki yayi ni banason haya gaga irin naki, tashi maza ki shirya ki koma gidan ku Allah ya bada ladan zumunci ameen" Diff kukan Meenal ya dauke a yayin da ta tsaya tana kallon Hajiya cike da mamaki, "Hajiya" Ba wani Hajiya zoki wuce ai tun d'azun nike fama dake kikayi kunnen uwar shegu dani, kinga yanzun ai kya nemi inda dare yayi miki" sai da ta turo baki gaba tana mutsts tsuke idanu sannan tace "Hajiya kaina!" Ita kuma hajiya tace "to ina ce dai nayi miki sannu? naga dai shi mugun ko kallo baki isheshi ba ya fice bayan ya gama kwashemin albarka" "To aini maganin ciwon kai zaki bani inba haka ba kaina rabewa biyu zaiyi" "Ah ah wallahi ba'a gidana ba, bari in ma tarwatsewa zaiyi ya tarwatse d'in bayan kin koma gidan ku kafin kisa a farayi dani a radio cewa jika tazo gidan kaka kanta ya tarwatse a'ah wallahi badani ba, maganin ciwon kai dai ai bazan rasa shi a gidan nan ba jirani in d'auko miki" ta fadi hakan a yayin da take mikewa zuwa ciki. "Nidai kud'in zaki bani idan na fita in siya maganin" "Me naji kin ambata? Kamar kud'i naji kin kira yarnan! Oh kice fashi zakimin da ranar Allah to kama gaban ki yarinya,dan banci nanin ba nanin bata cina ke tsaya ma! Wai mema kika aikata mishi a cikin d'akin daya harzuka shi haka? " "Ni banyi komai ba" Inma kinyi ai jikin ki dai ya gyaya miki" Ciki Hajiya ta wuce bata jima ba ta dawo da maganin ciwon kan, saboda yanda take jin ciwon kan yasa batayi jayayya da Hajiyar ba ta amshi maganin tasha, "Muje wajen in ma daya daga cikin samarin nan magana su kaimin ke gida" "Ni bana so bazan hau motar kowa ba, zan je bakin titi in samu mota" "Kedai kika sani mutum na miki abun arziki kina gwasale shi" Shiru Meenal ta mata ganin Hajiyar ta koma Ciki da niyyar dauko mayafine yasa ta ficewa a falon da sauri ta karasa wajen fulawoyin nan da ta ajiye shower gel d'in data kwamuso a d'akin shi ta dauke su ta cusa a cikin ledar kayan da Billy ta bata can kasa ta yanda babu mai gane cewar akwai shi a ciki, yanzun nan fisabilillahi da ace batayi sama da fad'i da turaren shi da wannan shower gel d'inba dashi kenan fa ya rankwashi banza kenan? "Kut ai wallahi bai isa ba koba dad'e koba jima saina rama" ta fad'i hakan a bayyane, Hajiya ce ta karaso wajen tana mita, "ke kuma daga in shiga in dauko mayafi shine kikayi fitowar ki? Nayi zaton kin wuce ne ai? "To aini na fad'a miki ni bazan hau motar suba tafiya na zanyi tunda basu suka kawoni ba dama" "Kyadai ji dashi!" Hajiya ta bata amsa. Koda suka fito kofar gidan Yusuf wase da Mai Jama'a ne kad'ai a majalisar sai kuma wasu bakin fuska. "Kai Abdul taso ka mikamin yarinyar nan gidan su in samu mu rabu lafiya da ita! " "Dama ni na kawota ne dazan mai data? tunda ta kawo kanta ai tasan hanyar komawa, kuma ni ko man petroleum ma babu a motana" Baki bude Hajiya ke kallon shi, "Kai Abdul Khareemu ashe bakajin tsoron kwanciyar kabari cikin duhu? da girman ka da komai kake kallon tsabar idona kana shekamin karya, ince kazo ka maida musu Y'a gida kacemin motar ka ba mai, to ai da hakan gara ka fito gaba gid'i kace min ke Amina bazan kaita ba kiyi abinda zakiyi" Bai gama sauraren abunda take cewa ba ya mike ya wuce zuwa cikin Restaurant d'in dake wajen. "Kai kai kai Abdul ina kuma zakaje me zakayi anan , karfa kamai dani wata shashasha, in tashi tunda farar safiya in had'a abinci shine saboda baka tausayi na kake neman zuwa wajen matar nan mai shafe² wai can zaka cin abinci to wallahi Allah dai yana kallon ka atoh dan bazaka mai dani wahalalla ba, aiko dan wahalar da nayi ka dawo kaci dambun nan, mutane da yawa ke son shi amma na hanasu na aje maka shine dan iskanci kake neman kwance min zane a kasuwa" Juyowa yayi ba tareda yace mata komai ba ya kama hannun Wase suka wuce cikin gidan. "To ya daifi kam ke kuma Takwara ki jira ya fito da motar saiya mik'aki gida" Sai dai me? Koda ta juya wayam babu Aminatu ba alamarta domin ko dama tun fitowar su ta kama hanya tayi tafiyarta tabar Hajiyar na b'ab'atu ita da bakin ta baya gajiya da surutu. Wannan rankwashi shi yayi sanadiyyar da sai da Meenal ta kwana da ciwon kai dalilin hakan yasa basu samu damar zuwa gidan su Zulaihat d'in da sukaci alwashiba, To kuma dan Allah shine saboda tsabar rashin imani yau ya wani biyota har gadon asibity ya mintsileta, tab ai wallahi su zuba shida ita hege ka fasa dan halak sai yanka, Kwana hud'u Meenal tayi a asibiti suka sallameta a kwana 4 nan kuwa tab'ara sai kalar data manta, sannan kullum Malam da Hajiya sai sunzo asibitin suma da nasu kalar wasan kwaikwayon dan Malam dai zuwa dubiyar ta haka ya maidashi kamar biyan bashi akan kowa, tsaf yake lissafe da wadanda basuzo sun duba mishi uwaba. Itako Hajiya innah nata idon akan masu zuwa dubiya babu kayan dubiya yake haka dai akayi ta fama har sanda akayi sallama kowa ya koma kan harkokin shi. ***** Dalilin ciwon laulayin cikin da Teemah keyi a wannan karan yasa dole Sarki ya zauna da ita,abunda take da bukata kenan dama domin koh sosai ta tubure mishi akan cewa rashin sone yasa yanzun bai damu da damuwarta ba, dan haka ita bazata iya wahala ba domin a gaskiya sosai takejin jiki dalilin hakan yasa duk abubuwan ta suka tsaya tadai fada mishi in bai zauna da itaba to hakika zuwa zatayi ta cire cikin dan bata iya wahala da cikin da uban cikin bai damu da itaba, To kun san dai dama can sai ya ciza da kyar yake iya daure zuciyar shi ya mata babu dad'i balle kuma yanzun da take shirin bashi sabon Baby dan haka dole ya d'auki hutu dan ya samu ya shawo kanta to dai suna can suna ba fulawa ruwa. Bayan wani lokaci........ Abubuwa da dama sun faru wasu sun tafi dai² bisa tsarin da yayi dai² da zuciyoyi wasu kuma sun kasance akasin hakan , A yanzun haka dai saura yan watan ni su Meenal su zana jarabawar gama secondary sunfa zama yan mata sosai Masha Allah komai yaji, Dan haka nema wasa² dai samari suka fara rububi a kanta sai dai da yike ta iya takunta da kuma kasancewar akwai waya a hannun ta yasa babu wanda ya fahimci halin da take ciki, domin dai duk kwakwar nacin mutum bata tab'a yarda yasan unguwar suma balle kuma gidan su saboda tsabar gudun tonuwar asirinta komai a cikin tsari take binshi, Alfarma daya dai takema wadanda take ji dasu a cikin samarin shine idan suka matsa da son ganin ta zataje can Tudun wada gidan Hajiya su had'u acan kuma ko hajiyar bata san da hakan ba, wato dai duk yanda zata raina ma mutune hankali ta b'atar musu da tunani a kanta ta sanshi, domin dai kullum a gida ikirarin ta shine likita zata zama dan haka babu batun wani soyayya da aure, hakan yasa babu wanda zai zargeta cewar tana kula samari. Sai dai bata san cewa tana shuka a idon makarwa bane, domin ko duk halin da take ciki na janyo samarin ta zuwa gidan Hajiya Mai Jama'a tuni yake ankare da hakan domin har farfajiyar gidan na Hajiya take shigo da samarin su zauna suyi hira, Shi mamakin shi a kullum shine, su samarin da suke biyon tan mahaukatan wani kasa ne? Su basa ganin kankantar tane dahar suke iya tsayawa da ita da sunan zance? , Kome ma suke cewa in suna zancen oho, dan yasan shirme da yarinta dai shi zatayi ta musu kala² dan rawan kanta yayi yawa. Jama'a fisabilillahi in soyayyar cema ka nemi cikakkiyar mace mai hankali mana ba wannan yar birin wasan ba. Kuma zai same tane wallahi in bata dena kawo musu maza gidan suba saiya had'a ita da samarin yacicci musu mutunci tunda ita bata da kunya wallahi, Dan shifa sosai abun yake bashi takaici dan cikin samarin nata inka duba zakaga bawai irin yan kuca kucan yaran nan bane, ah ah cikakkun samari take samu wayayyu dan alama ya nuna saita darje kafin ta baka damar zuwa inda take, Barin ma wani sakarai daya lura da cewa yafi sauran dake zuwa rawar k'afa a kanta, kuma yasan gayen Lukman Dan gidan Master ne, sosai yaron suke da arziki a gidan su to zaija mishi kunne ne kar yayi amfani da arzikin shi yama yarinyar mutane wayau. yadai tsaya sosai yayi nazarin cewa saboda taga ta fara zama budurwa shi yasa kullum take k'ara raina shi,domin da gaskefa ta maidashi abokin wasan nata dan ko bai takaleta ba ita sai ta takaleshi, domin dai har yanzun kullum babu shiri a tsakanin su sai dai in bata zo gidan ba, inshi yaje gidan su wajen Mommy Hauwa tofa bata da katabus, domin yafi samun damar cin zalin d'inta acan da kyau dan datayi wani motsi da niyyar ramawa Jidda ke taka mata burki akan bata son raini aishi yayan ta ne, amma in a gidan Hajiya ne yana mata itama take huce haushi a d'akin shi dan dai shi baya buguwa, kuma ita dai bazata mishi Allah ya isa ba sannan ba zata yafe ba wallahi, dan tuni saida tayi yanda tasan inda Hajiya ke ajiye key din d'akin shi, dazarar ya mata ba dai² ba take sace key din taje d'akin ta huce haushin ta akan kayan shi. Tsaf yasan cewa ita ke daukar mishi turare da sauran abubuwan dan kullum a jikinta yakejin kamshin da ba irin turaren shi su Sadeeq ke amfani dashi ba, sai dai yana nan yana dakunta duk ranar daya kamata a hannu dumu² zata gyawa aya zakin ta. Gefen Meelat da Musty ko soyayya suke zubawa ruwa² domin tuni aka san da zaman shi a gidan su Meelat d'in duk da akan soyayyar nasu har fad'a saida sukayi da Ak a cewar Ak din shi Musty yana haukane duk cikin Nigeria ya rasa yarinyar dazai nema sai wannan yar jaririyar, wato ashe shi yasa yaran nan suke mishi gani gani dan haka wallahi duk ranar da giyar soyayya ta kwashe shi yaje zance wajen yarinyar nan inhar ya sake ya kira sunan shi a wajen to bai yafe ba. Maryam dai itama irin na Meenal take duk samarin ta a iya waya hirarsu take karewa dan ita dai tasan a gidan su koda wasa ma a kasan tana kula wani jikinta ne zai fad'a mata. Su Moon da Aisha ma ko wacce tana inda take sai dai kullum Moon ta kira Meenal saita tambayeta ya labarin mai gidan yan gayu dafatan yana lafiya, tofa daman da zarar ta ambato shi hirar su ta wannan rana ta kare sai kuma wani lokacin, da alama dai Moon fa ta kamu 🤔 yarinya keda Teemah dan wannan fadar yafi karfina. Batun ciwon marar ta kuwa Alhamdulillah duk da cewar badai ta warke bane amma in ya tashi mata yanzun akwai wani taimako da Malam ya amso mata wanda da zarar ciwon ya taso in tasha bacci zai dauke ta, hakan yasa wahalar nata ya ragu. A gefen Malam kuma kullum cikin istikhara yake akan maneman Aminatun da zuwa yanzun suke ta kara yawa, domin a yanzun haka wadanda sukayi mashi magana akanta a da din su ya haura mutum goma sannan dukan su babu wanda inda hali bazai iya hanashi bashi auren Aminatun ba, dan haka dole yaci gaba dayi mata Addu'a domin neman zabin Allah a cikin al'amarin dan ya yanke hukuncin gara ya aurar da ita d'in kawai kodan samun lafiyar jikin ta itama, in yaso karatun nata tayi shi bayan aure. ************ A gefen Masoya biyu kuwa wato Sarki da Sarauniyar shi zamu iya cewa duniyace sabuwa ta bud'e musu domin dai tuni mutuniyar tashi ta tashi tsaya wajen ganin ta shiga ta fita ta gyara tsakanin ta da mijin ta kuma sosai yanzun kam ta samo kanshi take kuma juyashi yanda take so harma fiye da

Chapter 21 of 92