Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya ƙarasa rugujewa, don tana rasuwa kowa ya kama gabansa, da yake dai shima Yarima Adam Allah ya rubuta dole zai riƙi sarauta haka ya zuba uban dukiya aka ba shi sarautar yankin Funakaye, yankin da Babban ɗansa ke mulka a yanzu tun bayan rasuwar Sarki Adam. sai a wannan lokacin Sarki Lateef ya samu lafiya, aka sarara da bi masa ta ƙarƙashin ƙasa, kwanciyar hankali ta samu a gare shi. Allah ya azurta Sarki Lateef da yara huɗu, babban ɗansa Abubakar wanda yaci sunan Kakansa Sarki na biyu a wancan zamanin, suke kiransa da Yarima Babba, sai dai a yanzu Ƴaƴa da Jikoki na kiransa da Alhaji Babba, kuma a yanzu shi ne Hakimin Kaltungo. sai ɗansa na biyu da yaci sunan mahaifinsa Hashim suke kiransa da sarki na uku, kuma Hashim shine wanda ya gaji sarautar mahaifinsa Sarki Lateef tun bayan rasuwarsa. a lokacinsu ba'ai wannan tashin hankalin ba na nuna son mulki ga kowannensu, hasalima mahaifiyarsu Sarauniya Rumana ita ta bada zaɓin cewar shine zai maye gurbin mahaifinsu, kuma daga wannan maganartata babu wanda yaja balle a tsaya ja'inja aka tsaya akan abinda tace. sai ɗansu na uku Habib suke masa alkunya da Dikko, wanda yake babban alƙali a cikin ƙasa da wajenta, wanda gwamnatin tarayya ke ji da shi, kuma mahaifiyarsa ke alfahari da shi saboda gaskiyarsa. Falmata(Faɗima) itace autar Sarauniya Rumana(Boɗejo), wacca aka haifeta bayan rasuwar mahaifinsu daya tafi ya bar Rumana da cikinta. ya kuma bar wasiyyar cewar indai an haifi mace a saka mata sunan mahaifiyarsa Falmata, kuma kar a ɓoye mata suna a dinga kiranta da wannan sunan. hakan kuma akayi sai dai Ƴaƴa na sakayawa suce mata Inna Falmata, mahaifiyarta kuma tace mata Sarauniya. bayan biyo ɗan shirun da aka samu a falon na Hakimi wato Alhaji Babba, akan faɗan da yake ta yiwa Turaki na batun ƙin amincewarsa akan auren da iyayensa suke so yayi, yaci gaba da cewa. "to mu ba mutanen banza bane ya kamata kasan da hakan Turaki, babu yacca za'ai ace mu ƙyaleka akan ra'ayinka na cewar kai ba zaka yi aure ba, wannan ma zancen banza da wofi ne...idan ka manta to ka tuna su waye mu, saboda haka wallahi ƙaryarka ka bar mana abin kunya a tarihin sarautarmu...na san idan ta ra'ayin mahaifinka ne sai da ya zuba maka ido, to mu ba zamu zuba maka wannan idon ba kaji ni da kyau". A wannan lokacin idanuwan Turaki a kulle suke, kansa a duƙe yake, yana zaune ne a gefen ƙafafun macen da duk duniya baida kamarta Hajiya Madina. itace ta kawo ƙararsa ba kowa ba, aure take so yayi ya riga yasan da wannan batun ba tun yau ba, ya sa ni shine burinta akansa. to amma me yasa?, me yasa a matsayinta na wadda ta isa da shi bata gindaya masa umarnin hakan kai tsaye ba sai dai ta kawo ƙararsa gaban wanda cin mutumci shine abin yinsa?. wani dunƙulallan abu yaji ya tsaya a maƙoshinsa, zuciyarsa ta katse da raya masa abubuwa a sanda Hakimi ya ƙara yin magana. "Turaki ko dai baka da lafiya ne?, idan kasan akwai wannan matsalar a tare da kai to ka faɗa tun wuri a maganceta, duk da cewar abu ne da kamar wuya namiji kamarka ace yana da matsala makamancin hakan". Boɗejo dake gefe tace,"ah tou dai nima shi na gani. wannan zance dai na batun ba shi lafiya ma ƙarya ne, ni nafi ga wani algungumin ne ya jefe mana shi, tunda dai kaga maitar ibadar nan da yake ma yanzu fa duk ya daina, kuma wallahi ko waye Allah ya isa bamu yafe ba...yanzu duk wani dogon zance ba shi bane, a tashi tsaye a nema masa magani kawai idan aka biye ta uwar tasa da uban nasa ba zasu yi masa wannan abin arziƙin ba". Turaki ya buɗe idanuwansa ya zube akanta, magana ta ke tana ƙara kambaba zancen asiri ne akansa. bai san lokacin da bakinsa ya buɗe ya katseta da faɗin,"Boɗejo ke kuma komai ya faru shikenan sai kice aikin asiri asiri". tayi masa wani kallo ɗaya sannan ta maida kallonta kan Hakimi tace,"me na faɗa maka Yarima Babba tun kamin ayi zaman wannan kotun?, ai sai dai idan ban faɗa ba amma yaron nan sai ya tanka, baka ga kallon da yake min bane kamar ma zai tashi ya rufeni da duka...haka fa ubansa ya koya masa kuma alhalin ni ba irin rainon da nayi muku ba kenan, wallahi duk irin son da yake ma yaransa bai kama ƙafar wanda Ubanku Allah ya jiƙan rai ya nuna muku ba, amma ku dai baku san wani abu wai shi raina na gaba ba, hasalima wallahi baku san babba na magana ku saka baki ba, amma su dai Ƴaƴan Dukko halinsu kenan Babba na magana su nuna bai kai ba...to alhamdulillahi daɗin abin Turaki bani na kawo ƙararka ba Uwarka ce gata nan a kusa da kai, kuma billahillazi da ace lokacin da nake sarauniya ne sai kasan na faɗa ka saka baki". Turaki yay ɗan guntun tsaki, ya ɗago kai ya kalli Hajiya Madina, suka yi ido huɗu da ita. a kallon da yay mata ya gano expression ɗin dake tare da ita. sai yayi saurin kai hannu wuyansa ya shafo shi, ɗabi'arsa ce hakan. yawanci Boɗejo kance wani ƙullin yake shafowa. ya sauke numfashi, muryarsa ta fito a hankali, cikin girmamawa da biyayya yace da Hajiya Madina. "Maama ba sai kin kai ƙarata wani wurin ba. kin isa da ni, kin isa ki bani umarni na bi ko ina so ko bana so, kin isa kija layi kice kar na shata na haƙura dan dole na, bin zaɓinki dole na, yacca kike so nayi haka zanyi muddin hakan zai faranta ranki...". bai ƙarasa ba amon muryarta ya fito da faɗin,"aurenka nake son gani Me babban suna, ina so kayi aure tun ina da rai Hammansu, ka sani ina sonka fiye da numfashina, babban burina a yanzu shine naga aurenka, naga matar da zaka aura, naga jikana, naga kalar rayuwar jin daɗi da kwanciyar hankalin da zaka shimfiɗa da iyalinka...Hammansu wannan auren da baka so shine mutumcin mutum, kuma shine ƙarshen jin daɗin rayuwa...ita rayuwa nan guda ɗaya ce Hammansu, haka ran ɗan adam guda ɗaya ne. lokaci tafiya yake baya jira, so kai enjoying rayuwarka tun lokacin bai ƙure ba, ya zamana kazo baka mori dukkan jin daɗin rayuwar ba...babu wanda aka yiwa alƙawarin kaiwa gobe a wannan duniyar, tsari kawai muke da hange, kuma zata iya yiwuwa mu matu a lokacin da muke ta shirin tsare-tsaren gobenmu, and that will be the end of us, ni kuma ina so mu tafi ne a lokacin da muka bar masu tunamu a kowacce daƙiƙa. da zarar ance babu kai shikenan duk wasu memories daka bari suma sun tafi, amma ɗa fa?, shi ɗaya ne memory da zaka tafi ka bari a kasa mancewa da kai, hakan yasa nake so kayi aure tunda sauran lokaci, auren nan daga zuriya mai ƙarfi irin zuriyarmu, *SARAUTA*, ta yadda zaka bar bayanka, wannan kawai shine burina akanka Hammansu". idanuwan Turaki a ƙasan carpet suke, amma ƙwayar idonsa wasu yatsu ta ke hangowa sirara da suke karkarwa kamar waɗanda ake girgiza su. ya haɗiye wannan yawun dake saman harshensa zuwa cikinsa, sannan ya rufe idonsa ya buɗe a lokaci ɗaya. laɓensa na sama dana ƙasa suka tale, harufan bakinsa suka fito da faɗin. "Aure! zanyi aure Maama, zanyi yanda kike so, kuma insha'Allahu sai na cika miki dukkan burinki akaina, kuma insha'Allahu ba za'a wayi wata rana da za'ace kin rigani tafiya ba, ni nake so na rigaki tafiya Maama, ni nake so, bana so ki tafi ki barni, rayuwar zata yi min tsanani, zan daina jin daɗinta kwata-kwata, zan dinga jinta ne kamar ana min feshi da ruwan dalma, dan Allah Maamaaaa". maganar yake da kakkaryewar kowanne harafi, kuma maganar tasa ta katse gaba ɗaya a sanda yaja sunanta wajen faɗi. lokaci ɗaya ya nemi ya fita hayyacinsa. sautin kuka kawai yake ji acikin kansa, wannan sautin kukan na yarinta dana jarirai, saboda haka yay saurin saka duka hannayensa ya toshe kunnuwansa, tare da kifa goshinsa akan ƙafafun Hajiya Madina dake zaune tana hawaye. har zuwa lokacin da ya daina jin ihun kukan acikin kunnensa sannan ya ɗauke hannunsa, ya shiga sauke numfarfashi, gaba ɗaya yanayinsa ya sauya, kamar ma ya burkice ne, hannayensa masu rawa a yanzu suka damƙe zanin Hajiya Madina. a jikinta ta ke jin irin rawar da jikinsa yake yi, jikinsa na rawa amma ita a wannan lokacin tata zuciyar ce ta ke rawa, so take itama ta taya shi kukan, irin kukan da yake yi, so take ta taya shi ko yaya ne, ko da sau ɗaya ne. Zaytuna dake kusa da Boɗejo ta taso cikin kyarmar jiki, ta dawo gabansa ta durƙusa, sannan ta shige jikinsa gaba ɗaya itama nata kukan na ƙara ƙarfi, Turaki yay mata wata runguma da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma na riƙe ne da zanin Hajiya Madina da yake jin kamar a lokacin ƙwace musu ita za'ayi. wani tausayi ya ratsa zuciyoyin duk wanda yake zaune a parlon banda zuciyar mutum ɗaya dake ƙissima tarin abubuwa acikinta. lissafi take, lissafin yanda komai zai tafi, lissafin yanda komai zai warware, lissafin yanda baya ba zata taɓa gogewa ba, lissafin yanda komai zai tafi akan nata tsarin lissafin. **** Komai na ɗakin abin kallo ne, ko da ace baka san kuɗin kaya ba kallo ɗaya da za kai ma ɗakin da kayan da suke cikinsa zaka san cewa tabbas an narka dukiya wajen siyan kaya da kuma tsara ɗakin. ko da ace za'a ɗauki tsawon shekara 10 zuwa sama ba'ai renovating ɗakin ba, ba za'a gane cewar komai da yake ciki ya jima ba. lokacin da Fillo ta buɗe ɗakin zata gyara shi, tsayawa kawai tayi tana mamakin abinda za'a gyara, ina ƙurar da Hajiya Madina ta ke faɗi?, babu, infact irin ƙamshin dake tashi a ɗakin ko ɗakin da ake gyarawa kullum albarka, saboda haka ne tama rasa ta inda zata fara, gani ta ke sai dai ta ɓata ba dai ta gyara ba, dan komai tsaf tsaf, ɗakin yafi ƙarfin basirar gyaranta. amma a hakan dai ta gyara dole, tunda umarni aka bata, kuma sai bayan da ta gyara ne ta fahimci ashe da gasken yana biɗar gyaran. komai ya ƙara zama fes-fes, adon ɗakin dark blue and silver ne, kalar da ta burgeta kuma tasan ta dace da mamallakin ɗakin. a sanda ta gama gyara komai, sai ta shiga binciken abinda ta daɗe tana roƙon Allah yayi sanadiyar shigowarta ɗakin, wannan asirin da akace an saka shi a ɗakinsa, ba ɗakin da yake kwana ba, wannan ɗakin da zai koma da kwana bada jimawa ba, yes taga asirin, ta ganshi a inda taji sunce sun ajiye, ƙasan gadon, a mulmule yake kamar yanda taji sun faɗa, sam ba wari yake ba, wani irin daddaɗan ƙamshi yake yi, irin ƙamshin nan da ba zaka so ka daina shaƙarsa ba, irin ƙamshin nan dake motsa zuciya ta faɗa cikin wani yanayi mai wuyar fassaruwa. hasalima da ta ɗauko sai ƙamshinsa ya gauraye duka ɗakin, ya kore ƙamshin air freshner da turaren wutan da ta yiwa ɗakin. tunaninta guda ɗaya ne a lokacin asirin na menene?, to dama asiri yana ƙamshi?, ai tayi zaton asiri wari yake yi?, anya wani bai ganta ba a lokacin da ta laɓe yasa suka faɗi wannan maganar domin a ɗana mata tarkon ɓera?. ta tsorata da wannan tunanin, amma ko menene dai ba zata taɓa barin wannan dunƙulallan abin ya ƙara zama a ɗakin ba balle har Turaki ya kwana tare da shi. saboda haka cikin hanzari ta yunƙura ta miƙe zata fice, kwatsam idanuwanta suka sauka akan takardun da suka faɗo ɗazu da zata shiga ƙarƙashin gadon tace sai ta fito ta mayar da su. ta kama gefen zanenta ta ƙulle wannan abin da har yanzu zuciyarta taƙi yarda da cewar asiri ne, babu ko ɗigon tsoron zai iya cutar da ita, ta durƙusa ta kwashe takardun ta buɗe drower ta zuba su, sai dai cikin rashin sa'a wata takarda me duhu ta faɗo. daga tsayen da take kawai ta tsaya tana kallon takardar, baƙa ce, duk da duhunta hakan bai hana hoton abinda ke jikin takardar bayyana ba. dai-dai take gani ko kuwa gizo ne idanuwanta ke yi mata?, kalmar Tashin hankali dai tayi kaɗan wajen kwatance da halin da ta shiga a lokaci ɗaya. ƙafafuwanta suka tafi a hankali gwiwoyinta na zubewa a ƙasa gaban takardar, waɗannan siraran yatsun nata na rawa ta ɗauko takardar, sai bayan ta ɗauko ne taga ashe harda wata ƙaramar takarda anyi stapling ɗinta ajiki. ƙwayar idonta ta manne akan ƙaramar takardar dake ɗauke da sunan asibitin *As-Salam International Hospital*, Assalam ɗin kawai zuciyarta ta iya karanta mata banda international Hospital ɗin. *Nile Corniche, Athar an Nabi, Old Cairo, Cairo Governorate 4220501, Egypt.* kamar haka address ya biyo bayan sunan asibitin, bin kowanne rubutu ta ke da ido ba don zata iya karantawa ba, har tazo inda ta ke da ilimin karantawar, karatun da ta samu daga wajen Amir, *NAME* zuciyarta ta faɗa, sannan ta ƙara faɗar sunan daya ke rubuce akan siririn dogon layin da aka zana dan rubuta sunan majinyaci, *MUHAMMAD TURAKI HABIB*. ƙasan sunan kuma wani dogon layin ne da aka rubuta *KIDNEY FAILURE*. A duk cikin tarin rubutukan da takardar ke ƙunshe da su, suna uku zuciyarta ta iya karantawa, As-Salam, Name da kuma Muhammad Turaki Habib. kuma ta ke zuciyartata tayi wani girgiza da karanta sunan nasa, ba kamar ranar farko ba da bata ji komai ba sanda ta karanta sunan nasa. sai kuma ta maida idonta ga haƙiƙanin hoton dake jikin baƙar takardar, ta taɓa riƙe irin takardar nan, wasu shekaru baya da suka wuce, kamar haka ne ba zata manta ba, likita ya basu takardar dake ɗauke da hoton ƙodar da akayi. _"tana ɗauke da ciwon ƙoda"._ ba zata manta ba haka likita yayi musu bayani a wancan lokacin. allon ƙirjinta ya girgiza lokaci ɗaya, me hakan ke nufi kenan?, shima wanda sunansa ke rubuce ajikin wannan takardar yana ɗauke da irin ciwon daya kashe mata Adda?. bata san lokacin da ta shiga girgiza kai da sauri ba, ai bata manta ba ta faɗa a baya, anyi an gama, ba zata ƙara rasa wani mutum da ya samu gurbin motsi a zuciyarta ba, kuma wannan alƙawari ne ta ɗaukarwa kanta. kuma shikenan sai ta shiga rera kuka, zaman durƙushen da bata tashi daga shi ba kenan har zuwa yanzu, tunda ta tuna irin baƙar wuyar da Addanta tasha kafin ta mutu, bayan sun gama sa rai da cewar ta sami lafiya, a wankin ƙoda na arba'in da huɗu(44) da akayi mata, ashe tsawon lokacin da ta ɗauka tana fama ciwon ajali ne. Hawayen dake bin idanunta ya gangaro ya sauka akan takardar dake riƙe a hannunta, wadda ta tsirawa ido babu ko ƙifce. _"Mutuwa zai yi shima"._ wani ɓangare na zuciyarta ya faɗa mata hakan. a lokacin idan ka ga Fillo zaka iya rantsewa hankalinta ya gushe gaba ɗaya daga jikinta, dalilin ambatar kalmar mutuwa da zuciyarta tayi mata, allon ƙirjinta ya ƙara yin wani duka a karo na babu adadi, wata tsawa ta ziyarci cikin kanta, tsawar da ta haɗe da kiran daya shigo ta cikin wayar ɗakin wadda ke manne ajikin bango. _Idan Ayyukan da suke gabana na ɗaya daga cikin abinda ke hana ni yin typing, to tabbas rashin comment ɗinku shine maƙusin abinda ke saka na ɗauki tsawon lokaci banyi ba...ko dana zo yin typing ɗin ma sai naji banda wannan ƙwarin gwiwar, tunda ko da nayi babu masu tarbarsa hannu biyu, saboda haka ku daina ganin laifina, har da naku laifin...amma idan har kun gyara la shakka nima zan gyara...sai dai ban sa ni ba ko kunfi so aci gaba da tafiya a littafin kuɗin?._ *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *14* Fillo tasa hannu ta goge hawayen dake fuskarta, ta ɗaga kai tana bin wayar dake ringing da ido, tunani takeyi akan taje ta ɗaga ko karta ɗaga, ɗaya ɓari na zuciyarta ya rinjayeta akan taje ta ɗaga ɗin. saboda haka ta yunƙura ta miƙe tsaye jikinta a mace, bata ma ko iya ɗaga ƙafa sai janta take yi har ta ƙarasa inda wayar take manne a bango. ta kai hannu ta ɗaga wayar, daga ɓangaren Hajiya Madina ta kaɓe abinda ke jikin zaninta sannan tace,"Fillo". jin muryarta acikin wayar yasa Fillo saurin saita natsuwarta, sai da ta gyara muryarta sosai sannan ta amsa kiran. "Na'am Maama". Hajiya Madina tamkar tana kallonta ne a lokacin, don tana jin muryartata tunaninta ya bata kamar da wani abu, apple ne a hannunta a lokacin, amma cikin wani irin zullumi ta ajiye tana tambayar Fillo,"kuka kike yi?". Fillo ta haɗiye wani abu sannan ta ƙara gyara muryarta tukunna tace,"a'a Maama". Hajiya Madina tace,"but how comes naji muryarki some how?, wani abu ya faru ne?, ko ba kya jin daɗi?". ta jero tambayoyin ga Fillo muryarta na fita da sautin dake nuna damuwa da kulawa. kamar tana gabanta ta girgiza kanta tace,"a'a Maama lafiya lau". ta faɗa cike da mamakin yanda akai Hajiya Madinan ta gane kuka acikin sound ɗinta farat ɗaya, dan har sai da ta kai ga ta kalli wayar ko dai tana kallonta ne. Hajiya Madina ta ƙara cewa,"tiles ɗin nan yana da tsantsi sosai i forgot to tell you that, Allah yasa ba faɗuwa kika yi ba wajen yin mopping?". duk da cewar bata fahimci ɗan guntun turancin ba amma ƙarashen maganar ya fahimyar da ita dukkan maganar. tace,"a'a Maama nayi takatsantsan, har na gama ban zame ba". Hajiya Madina tace,"to yayi kyau, kin gama aikin?". tace,"ehh yanzu nake shirin rufe ɗakin". Hajiya Madina tace,"me amsar saƙon da na baki yazo yana ta jiranki, kije ki kai masa sannan ki ƙarasa aikin...muma mun kusa dawowa muna jira Boɗejo ta shirya ne tare zamu taho". tace,"tom Maama Allah ya dawo daku lafiya". da haka wayar tasu ta katse, Fillo tabi wayar da kallo tana jin son Hajiya Madina har cikin ranta, a iya ɗan zaman da tai ta gama karantar matar, zata rantse duk wanda ya faɗi aibun Hajiya Madina to ɗan hassadarta ne. macece da bata da ɗagawa ko kaɗan, bata tunƙaho da arziƙinsu, bata wulaƙanta talaka, bata da ƙasƙanci, kowa nata ne, kowa ganinsa ta ke ɗaya suke, kowa sonsa ta ke yi, mutumta duk wanda yake tare da ita takeyi babu tozarci. ƙasa ta duƙa ta tattara takardun ta mayar cikin file ɗin da suka faɗo, sannan ta mayar cikin wata drower daban da wadda suke ciki da. ta fita daga ɗakin jiki a saɓule, da ƙyar ma take yin tafiyar tamkar me ƙarancin jini a jiki, tana saukowa daga upstairs ɗinne cikin tsautsayi ta gurɗe ƙafa. bakinta ya furta bismillah kafin ƴar ƙarar da ta saki ta biyo baya. cikin jin zafi da raɗaɗi na lokaci guda ta riƙe ƙafar tana cije fuska. gurɗewar ba ƙarama bace, dalilin da yasa idanuwanta suka cika da tarin hawaye kenan, wani sabon kukan ya ƙaru akan wanda zuciyarta bata gama yinsa ba, sai da ta ɗauki kusan 4minutes sannan ta tashi ta sauko da ƙyar sai ɗingisa ƙafar takeyi, sai da ta kashe light na parlon tukunna ta bar side ɗin. a ƙofar ɗakin me gadi ta tarar da mutumin, baƙi ne kamar yanda Hajiya Madina ta sanar mata, yana da curar ƙasumba, fuskarsa kuma sam babu fara'a. me gadi dake jin radio ganinta yasa shi yin murmushi, ta rissina ta gaishe shi ya amsa mata yana tambayarta ya aiki, ta amsa masa da lafiya. sannan ta tsuguna a gaban mutumin da ko inda take bai kalla ba tun zuwanta, bata sani ba ko haka yake ko kuma ita yakewa hakan dan ta ɓata masa lokaci oho. "ina yini". ya kalleta ta wutsiyar ido, kamar ba zai amsa ba can kuma yace,"lafiya". ta fito da hannunta daga cikin hijab wanda ke ɗauke da file ta miƙa masa tace,"ga shi wannan tace a baka". sai da yayi mata wani kallo kafin ya warta, dan ba zata kira hakan da karɓa ba sai dai warcewar, hakan kuma ya ɓata mata rai, ta miƙe cikin ɗaurewar fuska. tafiyarta zata yi, ba zata ƙara ko da ɗigon minti anan ba, cewar ita ƴar aiki ce hakan ba yana nufin a dinga wulaƙantata ba. ta sani ita ba wata bace, ba ƴar wani bace, amma wallahi tafi ƙarfin wulaƙantawar kowanne kalar mahaluƙi, talauci ai ba hauka bane, dan haka yanda bata wulaƙanci haka ba zata yarda a wulaƙanta matsayinta ba ko da wasa, ita ƴar mutunci ce kuma da darajarta, aiki suke ake biyansu ba wai roƙo suke ba. saboda haka yanda ya warce bai karɓa da arziƙi ba, haka itama zata bar wajen ba tare da ta jira nasa saƙon ba inma yana da shi, ai dama ce akai kawai ta ba shi, to idan ma yana da wani abin faɗa sai ya jira Hajiyar ta dawo ya bata, amma ba dai ita Fillo ta jira saƙonsa ba. abunda bata sa ni ba a wannan lokacin shine, tun yunƙurawar da tayi zata tashi shi kuma ya bar wajen, saboda haka ko da ta kalli inda ya zauna taga babu shi bata yi wani mamaki ba, tayi tsammanin faruwar hakan. tace da me gadi,"Baba kayi haƙuri dan Allah ban miƙo maka abincinka ba, wallahi ina cikin aiki ne sai yanzu na samu sarari amma bari naje na kawo maka yanzu". Tsohon ya washe bakinsa da duk haƙoran da suka ɓaci da goro yace,"laa babu komai ƴar nan, karki damu". juyowar da zata yi kawai taga mutum tsaye a bayanta ya harɗe hannaye a ƙirji, da tsananin mamaki ta ke kallonsa from head to toe, baki buɗe ta kasa rufewa, what would she call the situation she got into ?, tasan dai gefe ɗaya farin ciki ne ya lulluɓeta, to amma ɗaya yanayin fa?. idan tace ba ta kewarsa tayi ƙarya, idan tace bata yi murnar ganinsa ba tayi ƙarya, idan tace bata son ganinsa ta yaudari kanta. cikin wani irin emotions da ta ke jin kanta tayi saurin saka tafukan hannunta ta rufe fuskarta, murmushi kawai take yi, irin murmushkin nan me faɗi dake fallasa kyawun fuska, wani daɗi ne kawai ke ziyartarta, ji take yi tamkar an mata albishir da kujerar makka. tana son ganinsa, tana ta so ta kasance da shi amma babu dama, lokaci yayi mata ƙaranci tunda ta fara wannan aikin, rabon da ta saka shi a ido tafi sati uku, har Kaka ta gama ciwonta ta gama basu haɗu ba duk da cewar kullum sai yazo dubiya, sai dai idan ta koma Kaka ta bata sallahun saƙon gaisuwarsa daya bar mata. Allah ya sa ni sai yanzu da ta gansa take jin tamkar ta ɗauki shekaru bata gansa ba, kuma Allah ya sa ni a yanzu ji take yi kamar ta rungume shi don tsananin farin ciki, ta ya ya?, ta ya ya zata nuna masa irin jin daɗin da ta yi na ganinsa?. ta ramin yatsunta take hango fuskarsa da gaba ɗaya babu walwala, lokaci guda tasha jinin jikinta, wanne irin bayani zata yi masa ya fahimta?, ko me zata ce ba lallai ya gane ba, abu ɗaya kawai tasan yana ransa shine yanzu ta fifita aiki akansa. sai kawai jikinta yay sanyi, still hannunta na rufe da fuskarta tayi ƙasa da kanta tana jin kamar tayi kuka. bata yi aune ba taji faruwar al'amarin da bai taɓa faruwa ba a tsakaninsu ita da shi, hannunta ya ruƙo, wannan hannun nata da bai taɓa riƙewa ba tsawon lokacin da suka ɗauka tare, me zata yi yanzu?, zata sakar masa hannun ne ya sauke kamar yanda taga yana ƙoƙarin yi ko kuwa zata hana hakan?, domin gani ta ke kamar ba zata iya haɗa ido da shi ba, kunyarsa ta ke ji sosai, kunyar riƙe ma ta hannu da yayi, tana ganin tamkar sun aikata wani babban alfasha ne. idanuwanta suka ciko da ruwa, ta shiga ƙiftasu a hankali, dai-dai lokacin kuma da ya sauke hannun nata daga kan fuskarta, kallonta yake har yanzu, ya kasa ko da ƙiftawa, ji yake kamar ya ɗauketa, ji yake kamar ya sureta ya kaita duniyar da babu kowa aciki daga shi sai ita. a ƙoƙarinta na zame hannunta daga nasa ta ɗago ido tana kallonsa, kamar ruwa ta ke gani anasa idon shima?, kamar yana so yay kuka ne?, kamar rauni ne take gani a ƙwayar idon nasa?, kenan shima yayi kewarta har irin haka?. shi kuwa kallon da

Chapter 10 of 73