Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zai yi magana tayi saurin ɗaga masa hannu cikin fusata, ta kulle idonta tana huci na tsawon daƙiƙa ɗaya, ta buɗe su a sanda ƙwayar idonta ta kaɗa tayi jawur, wannan damuwar da take tare da ita na tsawon shekaru ta taso tun daga can ƙuryar zuciyarta ta mamaye saman fuskarta. da tsananin ɓacin rai a muryarta tace da Hamid,"tunanina duk sanda zan ganka zan zama ina me farin ciki ne". ta faɗa tana ƙara ɗaga muryarta da faɗin,"me yasa kazo min da wannan abin cikin gida?, to idan baka sani ba ka sani, bana so kuma bana ƙaunar sake haɗa ido da azzalumin mahaifinka har in bar duniya, dan haka tun ina shaida kai ɗana ne ka fitar da shi daga gidan nan". tai maganar cikin zafin rai tana yi masa nuni da gate, Hamid ya dubi mahaifinsa da tausayi wanda ke ta kokawa da wheelchair yana so ya sauko, ya koma ya kalla Ummi yace,"dan Allah Ummi...". bata barsa ya ƙarasa ba ta doka masa tsawa. "Hamid ka fita da shi na faɗa maka, ka fita da shi tun ina iya kallonka ina shaida kai ɗana ne, Hamid ina me rantse maka in baka fitar da wannan matsiyacin mutumin daga gidan nan ba zan tsine maka". Kaka tayi saurin shiga maganarta da cewa,"kul, kul Halimatu, shi me yayi miki da zaki nemi ki sauke fushinki akansa". Ummi tace,"wallahi tallahi in har don inci gaba da kallon wannan azzalumin mutumin a inda nake ne to gwara in yafe Hamid ko kuma in tsine masa muddin bai fitar da shi daga gidan nan ba, na tsani mutumin nan na tsani ganinsa, inata roƙon Allah kar ya ƙara haɗani ko da ace da inuwarsa ne shine Hamid saboda baya ƙaunarta zai ɗauko shi ya kawo shi inda nake salon zuciyata ta buga". Yami tace,"kiyi haƙuri Ummin Fillo, ki tsaya ki saurare shi har yanzu shi ɗin mijinki ne, kuma karki manta shi uban ƴaƴanki ne, Allah ma muna masa laifi ya yafe mana, to kuma ina laifin wanda ya gane kurensa yazo neman yafiyarka". ta girgiza da kanta cike da takaici da ƙunar rai,"Yami baki san waye wannan mutumin ba, wannan da kike ganinsa azzalumi ne, mugu ne, macuci, dan Allah ku fitar da shi daga gidan nan tun ban faɗi na mutu ba". sai kawai ta fashe da kuka me cin rai, tana jin wani abu me ɗaci na taso mata, tana jin kamar ta shiga ciki ta rarumo duk abinda ta gani tazo taita rotsawa Hayyo. faɗowar Hayyo daga kan wheelchair yasa hankalinsu ya kai kansa, Hamid ya tafi da sauri ya ɗaga kujerar da ta danne shi, jikin Hayyo duk karkarwa yake, yana jan jikinsa a ƙasa yana so ya ƙarasa gaban Ummi, Hamid ya fara hawaye ya ɗagosa ya mayar da shi kan kujerar, sannan ya turasa ya kaisa gaban Ummi. gwanin ban tausayi hawaye ke sauka akan fuskar Hayyo ya haɗe hannayensa alamar roƙo, bala'in nadama da danasani shimfiɗe a fuskarsa, cikin ƙinƙina mesa zuciyar mutum ta tsinke yace,"dan darajan Allah ki yafe min Halima, ki tausayawa halin da nake ji, ke kaɗai kika rage ki yafe min acikin waɗanda suke raye, kuma muddin baki yafe min ba nasan ba zan gama da duniya lafiya ba, domin nasan na aikata miki abubuwan da Allah ba zai barni ba, dan Allah ki yafen ko na samu sassaucin bala'in da nake ji a tare da ni". Ummi na kallonsa da tsantsar tsana tace,"kai yanzu Hayyo har kana da idon da zaka kalleni ka buɗi baki kace in yafe maka?, yaushe kasan Allah da yau kake roƙon wani da shi?, to bari kaji na faɗa maka, banda idon da zan dubi halin da kake ciki in tausaya maka balle na yafe maka, ka cire batun yafiya tsakanina da kai dan ko da ace yafiyata ta rage maka shiga aljannah Hayyo ba zan yafe maka ba". Kaka, Yami da Hamid sukai ta roƙon Ummi akan ta yafe masa, amma sam taƙi, ƙarshe ma sai ciki ta shiga ta ɗauko mayafi ta fito tana kallon kowa tace,"in har ba zaku ɓadda shi daga inda nake ba to ni zan bar muku gidan". sannan ta kalli Hamid tace,"kai kuma ko a mafarki ka ganni karka nuna ni a matsayin mahaifiyarka, tunda kaima baka tausayina". tana zuwa bakin gate Fillo na turo ƙofa ta shigo, niƙab ɗinta a hannu tana yamutsa fuska alamun ta gaji, farat ɗaya hankalinta ya tashi ganin Umminta na kuka, gabanta ya faɗi tana tunanin me zaisa mahaifiyarta kuka a yanzu kuma?, ai tayi zaton zubar hawayenta ya ƙare kuma tunda har ta rabu da Hayyo. sai ta ƙanƙance ido tana bin kowa da kallo, ta tsayar da idonta bayan Hamid da bata ga fuskarsa ba, zuciyarta bata gama tunanin ko waye ba ya juyo, ta ware ido tana faɗin,"Hammah". ta faɗa murmushi na ƙwacewa a fuskarta, harta ɗaga ƙafa zata wuce wurinsa sai kuma idonta ya sauka akan mahaifinta dake kallonta yana murmushi da hawaye, alamun na yaji daɗin ganinta, lokaci ɗaya ta haɗe rai ta ɗauke idonta daga kansa. ta kalla Ummi dake ƙoƙarin raɓata ta wuce, ta kama hannunta zasu fita maganar Hamid ta tsayar da ita. ta juyo tana kallonsa tace,"Hamma dana ganka sai naji farinciki ya kamani, amma da naga wannan masifar a tare da kai sai naji kamar in haɗiyi zuciya in mutu, saboda na san ba komai ya samin Ummina kukan da ta jima bata yi ba ba sai shi, dan haka gwara mu bar muku nan ɗin dan ba zamu ƙara zama da masifar da zata hanamu farinciki da jin daɗin rayuwa ba". tana rufe bakinta Hamid ya ɗauketa da mari, kuma bai sauke hannunsa ba Ummi ta zabga masa marin shima. "ƙarya tayi ba masifar bane shi da har zaka ɗaga hannu ka marar min yarinya, to wallahi ka kiyayeni kar kaja ɓacin rai yasa bakina ya zama silar lalacewarka a duniya, kuma na fasa tafiyar kaje ka gangaro shi kuzo ku fita a gidan nan tunda ba uban wani ya gina mana ba". maganar Hayyo ta shiga kunnen Fillo a sanda yake cewa,"dan Allah dan Annabi ƴata ki yafe min, ki tausayawa halin da nake ciki, wallahi na san alhakinku ke bibiyata shisa na faɗa cikin wannan mawuyacin halin". Ummi tace,"ai baka ga komai ba, kaɗan ma ka gani, kuma insha'Allahu nan gaba maganar ma sai ta gagareka, da izinin Allah sai kowa ya gujeka ya barka kai ɗaya a halin da yafi wannan muni". Hayyo ya kulle idonsa yana ƙara roƙon su Ummi su yafe masa, tasa tazo ƙarshe su taimaka masa kar ya tafi lahira da alhakinsu, Fillo na kallonsa cikin ƙunci tana tuna voice ɗinsa da taji a wayar Turaki tace,"mu yafe maka kake cewa?, ka manta sanda kake saka Ummina a ɗaki ka kulle kayi ta dukanta?, ko kuma ka manta sanda kake bin ta har waje ka duketa a gaban mutane kana zaginta?, ko manta yacca ka azabtar damu da yunwa kayi?, ko kuma ka manta sheganta ni da kayi da har kake kirana da ƴarka?, to idan ka manta duk waɗannan abubuwan mu ba zamu manta ba, kuma tsakaninmu da sai Allah, da yardar Allah ba zaka mutu ba sai kaga shiga matsanancin halin da yafi wannan". a tsawace Kaka tace da ita,"kul ɗinki Fillo, karki ƙara wani furuci anan, wannan lamarin tsakanin iyayenki ne, duk lalacewar uba uba ne shi, uba ba abin wasa bane ki san da wannan, kamar yanda kike ganin mahaifiyarki da mutunci ya zama dole shima ki gansa a mutumce muddin kina son gamawa da duniya lafiya, ke ba dan shi ba ai da baki zo wannan duniyar ba, ki iya bakinki akansa kafin duniya tayi watangaririya da ke". Fillo tasa kuka tana faɗawa jikin Ummi tace,"ni wannan ba Babana bane, shi da ya sheganta ni a duniya ta ya za'ai ya zama ubana, mutumin da ya kasa bani ilimi da tarbiyya shi ne zai zama mahaifina?, ni dai ba Babana ba ne kuma ba zan taɓa yafe masa abunda yay mana ba". tarin da Hayyo ya fara babu qaqaautawa yasa Fillo haɗiye sauran maganganunta tayi kansa da sauri, Kaka tace da Hamid ya tura shi su shiga daga ciki, Ummi na tsaye tana jin zuciyarta nayi mata wani iri tabi bayansu da kallo. cikin ƙanƙanan lokaci dai Hayyo ya fita a hayyacinsa, tari kawai yake yana a basa ruwa ya sha, Fillo ta ɓare jarkan faro jikinta sai rawa yake yi ta zuba a kofi ta tallafi kansa ta basa ya sha, Kaka ta ɗauka lambar Dr Yusuf ta kirasa a waya yace gashi nan zuwa nan bada jimawa ba. cikin mintunan da basu wuce biyar ba Hayyo yasha ruwa yafi roba huɗu, da yasha zai kuma cewa a ƙara masa, kuma duk Fillo ce take basa, idan ta kai kofin bakinsa sai ya haɗa harda hannunta ya kama tukunna yake shan ruwan, hawayenta kuwa dake zuba ajikinsa jinsu yake kamar wuta, in ace ya san haka Ƴaƴa suke da tausayi da jin ƙai da bai wulaƙanta ƴaƴan da Allah yabasa ba balle ya wofuntar da su, bai san Ƴaƴa rahama bane sai da ya shiga wannan halin, lokacin da babu macen da zata kula da shi, haka kuma babu ƴaƴan da zasu zauna su basa kulawa, in ace babu Hamid bai san kuma ya zai yi ba, wataƙila da tuni ya mutu ya ruɓe ba tare da kowa ya sani ba. sai a yanzu da tasa tazo ƙarshe yaji sonsu da ƙaunarsu matuƙa na bin jinin jikinsa, sai yanzu yake jin ina ma ace baya zata dawo da ya kyautatawa iyalinsa, babu abinda yake buƙata a yanzu irin ubangiji ya basa aron lokaci, sannan ya ara masa lafiya ko ta ɗan kaɗan ɗin lokaci ne dan ya faranta ran iyalinsa, ya gyara halinsa, ya gyara lahirarsa, to amma ya san ƙarshensa yazo, ba zai ƙara samun wata dama ba a wannan duniyar balle kuma lokaci. yana ta kallon Fillo yana kuka sosai yace,"na karɓi sadakin aurenki tuntuni, na san da cewa hakkinki ne, dole na baki hakkinki, amma saboda son zuciya nawa ban nemeki ba balle na baki, sai na gina kaina da kuɗin motar dana siyar, ban ko fara morarsu ba Allah ya jarabceni da shiga wannan mawuyacin halin, dan Allah ki yafe min kar in mutu da hakkinki akaina". ya faɗa yana kuka sosai. "na san ƙwarai na zalunceku, ba'a taɓa mugun mutum irina ba da ya ƙuntata rayuwar iyalinsa, ban baku ilimi ba balle na baku tarbiya, hasalima duk naƙi karɓarku a matsayin ƴaƴan dana haifa, alhakinku kaɗai ba zai barni in ƙare da duniya lafiya ba, dan Allah ku yafe min ko na sami sassuaci a ƙabarina, kuce kun yafe min ko naga da kyau a ranar gobe". ya kamo hannun Hamid yace,"haƙiƙa banda tamkarka ɗana, Allah ubangiji yay maka albarka, Allah ya saka maka da mafificin alkhairin, ya baka masu kayatata maka fiye da yanda ka kyatata min, fiye da yanda ka dinga kare martabata da mutuncina, na san ba zan ƙara wani lokaci me tsayi ba, idan na mutu ka ɗauki wannan Atm ɗin dana baka ajiya kaje ka ciro miliyan hamsin ka bawa ƴata, hakkinta ne". ya faɗa yana shafa fuskar Fillo, sannan yace,"ka nemi adalin alƙalin da zai raba maku gadonku babu zalunci, duk wata kadara dana mallaka taka ce Hamid na bar maka, na rubuta hakan a takarda ta nan cikin kayana, abinda kayi min ba zan taɓa iya biyanka ba Hamid, na gode, na gode, na gode Hamid, baka taɓa fushi dani ba, baka taɓa guduna ba saboda mugun halina, matana da ƴaƴana sun guje ni amma kai ɗaya namiji da Allah ya bani kana liƙe da ni, kana faɗa min gaskiya a lokacin da nake da dama amma naƙi saurarenka, Allah yasa ka gama da duniya lafiya, dan Allah yayin da babu ni ka zama uba a wurin ƴan'uwanka, karka bari zumuncinku ya yanke, kayi musu gatan da ni banyi musu ba, ka zama na gari Hamid, ka zama na gari, mutum baya dana sanin zama mutumin ƙwarai har mutuwarsa, amma idan ka zama mutumin da wasu suke kuka da kai zaka yi dana sani a sanda kazo mutuwa har bayan mutuwarka, Allah yasa ka gama da duniya lafiya". Hamid ya kasa cewa komai yana dai riƙe da hannunsa yana hawaye, Hayyo na shaƙuwa ya kalla Fillo yace,"zan ƙara ruwan me sunana Umminta". Fillo ta ɗago kansa ta kuma basa ruwan yasha, a lokacin sai da ya shanye jarkan guda, yana kallon Fillo yana murmushin ƙarfin hali yace,"ki tayani roƙon yafiyar mahaifiyarki, ki faɗa mata ina sonta, ina sonta fiye da yadda baki zai furta, dan Allah ta yafe min ko na na samu naga haske a ƙabarina". yana faɗar hakan kansa ya langwaɓne gefe yana shaƙuwa sosai, ya dafe ƙirjinsa yana jin tsananin azaba na ratsa shi, magana yake so yayi amma shaƙuwa sam ta hana shi, can kuma sai ga jini yana fita daga bakinsa kamar zubar yawu, ya damƙo hannun Fillo da Hamid yace,"tawa tazo ƙarshe, ba zan ƙara ko da minti uku ba, mutuwa zanyi ƴaƴana, bana so na tafi na barku amma ban isa na hana mutuwa ta ɗaukeni ba, ba'a son raina zan rabu daku ba sai don mutuwa ta zama dole a gareni ko ba yanzu ba, idan na mutu ku nema min gafarar Allah, karku gushe face kuna me nemar min gafararsa a ko da yaushe, haƙiƙa ni ɗin me laifi ne a gare shi, mutuwa zanyi babu makawa, iyayena sun rasu tun ina saurayi, baƙin cikina ya zama ajalinsu, ku nemi dagina a ƙauyen Ngurore-Jabu under local government ɗin Karim-Lamiɗo, Wurkum district gidan Hakimin Wurkum, nanne gidanmu, Allah yayi muku albarka, dan Allah kuce da mahaifiyarku ta yafe min, la'ila ha'illahu muhammadurrasulillahi sallahu alaihi wassalam". ɗif kamar ɗaukewar wuta haka numfashin Hayyo ya ɗauke, hannunsa ya saki ya faɗi daga riƙon da yaywa yaransa, Kaka ta fashe da kuka tace,"shikenan, Hayyo Allah ya jiƙanka yay maka rahama yasa can tafi nan". Fillo ta ƙwala wata ƙara tana jijjiga shi,"Abba nah, Abba don Allah ka tashi, Abba karka mutu, Abba karka tafi ka barmu muna buƙatarka, wallahi mun yafe maka duk abinda kayi mana, dan Allah ka tashi Abba nah, muna sonka a yanda kake Abba ka tashi please". Hamid dai kukansa a hankali yake yi, shi ɗaya yasan me yake ji a zuciyarsa, Kaka ta tashi ta fita dan kiran Ummi idan bata yi nisa ba, tana fitowa ƙofar parlo ta tarar da ita a tsaye tana goge hawaye da mayafinta, ta kalleta tace,"ya mutu ai". wasu sabbin hawaye suka ƙara zubowa a fuskar Ummi, Kaka ma ta goge nata tace,"ki shigo ciki asan abin yi kafin dare yayi, anan za'ai jana'izarsa ko sai mun koma can?, in sai mun koma can dole sai gobe za'a kai shi tunda kinga daren yayi, in kuma nan ɗin ne to na shiga masallacin can na faɗa in yaso ko bayan magriba sai a kaishi". kukan da Ummi ke ta riƙewa ya kubce mata, ta fashewa da kuka sosai ta shiga parlon da gudu ta tafi kan gawar Hayyo, wanda take kallonsa kamar zata yi masa magana ya amsa mata, ta kifa kanta a ƙirjinsa tana riƙe hannunsa, kukan da bata taɓa yi ba a duniyarta yazo mata, da ƙyar muryarta ta samu ta fito acikin kukan tana cewa,"na yafe maka, Allah ya yafe maka, Allah yasa ka huta, ubangiji ya lulluɓeka da rahamarsa". lokaci ɗaya parlo ya karaɗe da kukan uwa da ƴaƴanta, zuciyoyin da su kaɗai suka san me suke ji, duk rashin kyan halin mutum yayin da akace babu shi mutuwa ta ɗauke shi sai mutuwarsa ta taɓa zuciya musamman makusantansa, ji suke yi inama zasu iya dawo da shi suci gaba da rayuwa tare da shi a yanda yake. kukan da Fillo da Hamid ke ya ƙara tsinkar da zuciyar Ummi, kuka sosai babu me iya lallashin wani, lokacin kuma Dr Yusuf ya shigo parlon, da Yami ya fara cin karo, yana kallonta jiki a sanyaye yace,"lafiya Yami?, waye babu lafiya?, ba dai jikin Ummi bane ya tashi?". tana goge hawaye tace da shi,"a'a ba ita bace, wanda ma aka kira ɗin kazo ka duba shi Allah ya karɓi abinsa". ya kalla wurin da su Ummi suka kewaye gawar sannan ya kalla Yami yace,"ban gane ba Yami?, waye mutu?". tace,"Baban Fillo ne yazo, kuma ashe ajali ne ya kawo shi". Yusuf ya isa wajen da sauri, sai dai yana zuwa fuskar da ya gani ita ta matuƙar basa mamaki har ya razana yaja da baya, ya kalla Ummi ya kalla su Hamid yace,"waye wannan ɗin?". babu wanda ya iya basa amsa acikinsu, ya dinƙa kallon Fillo dake aikin girgiza Hayyo tana faɗin dan Allah Abba ka tashi, ka tashi mun yafe maka karka mutu yanzu. Yusuf ya zube a wajen hoton gawar Hayyo da hoton Kawunsa Muhammad da ya sani na haska masa a ido. a fili ya furta,"Kawu Muhammad". sai kuma yasa hannu a aljihu ya ɗauko wayarsa ya kira lambar Ammi, har ta ƙare ringing bata ɗaga ba sai daya kira lambar Aliyu yace ya kai mata. murya a daƙile tace da shi,"ya akai?". yace,"Ammi Kawu Muhammad". tace,"me ya sami Kawu Muhammad ɗin?, ganinsa kayi?". kamar yana gabanta yace,"Ammi ya mutu". a matuƙar razane ta miƙe jiki na kyarma tace,"ya mutu?, aina ka gansa da zaka ce ya mutu?, yaushe rabonka da shi ma har da zaka ce ya mutu?, wa ya san inda yake?". yace,"to ban sani ba Ammi ko idona ne yake gane min ba dai-dai ba, amma tabbas gani ga gawar Kawu Muhammad, zan tura address kizo yanzu ki gani ko shi ɗinne, amma na tabbata gawar Kawu Muhammad ne a gabana". Ammi ta jefar da wayar Aliyu tayi cikin ɗaki da sauri ta ɗauko mayafi tace da shi,"muje muje Aliyu, duba wayarka Yusuf zai turo da address". cikin mintunan da basu haura ashirin ba sai ga su Ammi sun ƙaraso gidan, ta shigo parlon duk a rikice tayi kan gawar da aka lulluɓeta a yanzu, ta kalla Ummi dasu Fillo da babu abinda ke tashi a parlon sai gunjin kukansu, ta kai hannunta na kyarma ta ɗaga zanin da aka rufe shi da shi, tana kallon fuskarsa ta saki zanin ta zabura taja da baya tana ambaton ƙalu innalillahi... sai kuma ta fashe da kuka sosai tana faɗin,"ashe rabon ba zamu ƙara ganawa ba sai bayan ka mutu zanga gawarka Yaya". ta kalli Ummi tace,"mijinki ne da gaske?". Ummi da mamaki take kallonta ta ɗaga mata kai kawai, Ammi tace,"Yayana ne uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya, tunda ya zama ajalin iyayenmu shikenan kuma ya kama gabansa bai ƙara waiwayon kowa ba, rabona da shi tun Yusuf bai fi shekara goma sha ɗaya ba, yazo gidana sau ɗaya lokacin ko sauraronsa banyi ba". tayi shiru tana bin gawar da kallo tana kuka sosai, "Allah ya jiƙanka Yaya yasa ka huta, Allah ya yafe maka zunubanka, ya haskakaka ƙabarinka, Allah ya sadaka da manzon Allah SAW". nan da nan kuma sai ta ɗauki waya ta shiga kiran ƴan'uwanta waɗanda suke uba ɗaya, dama su biyu ne a wurin mahaifiyarsu daga shi sai ita, duk da irin fushin da aka ɗauka da Hayyo hasalima wasu sun manta da shi, amma kan kace mene wannan waɗanda ke zaune anan Gombe har sun zazzo. saboda manyan yayyansa dake can taraba dole aka fasa kaisa a ranar akace a bari sai gobe, a washegari da safe kuwa ƙarfe takwas na safe gida ya cika maƙil da ƴan'uwan Hayyo maza da mata, lokacin har anyi masa wanka jira ake babban wansa yazo ai masa sallah. lokacin da aka ɗauko gawar Hayyo za'a fita da ita a lokacinne mutane da dama da basu sami damar kuka ba suka saki nasu, saboda bala'in tausayin Fillo wacce ke ta kuka tana kiran a bar mata Abbanta dan Allah, sai da ƙyar Ammi ta iya riƙota Hajiya Madina ta ƙwace hannunta daga kan makarar da ta yiwa mugun riƙo, sannan ne aka samu aka fita da gawar Hayyo daga parlon, kuma lokacinne Fillo ta yanke jiki ta faɗi bayan ta ƙwalla wata razananniyar ƙara da ta masa a gidan gaba ɗaya. aljanun da ba'a santa da su ba suka tashi.... *Vote, Comment and Share.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *43* *Taraba Satate, Wurkum district, Late Alhaji Aminu Barkinɗo Residence.* tafkeken gida ne me irin ginin gidan sarauta, sai dai ginin irin na zamanin da ne bana yanzu ba, but an ɗan sabunta shi ba kamar yanda yake ainihinsa ba. ƙofar gidan na marigayi tsohon Hakimin Wurkum danƙare yake da jama'a kace ɗaurin auren wani babban mutum ake ko kuma za'a ƙara yin naɗin sarauta ne. daga cikin rumfar tempol ɗin da akayi, Maudo ne zaune akan kujera yasha rawani yana amsar ta'aziyya daga bakunan mutane da dama, shine Babban ɗa a wurin marigayi Alhaji Aminu Barkinɗo, kuma shine wanda ya zauna a hannun mahaifiyar Hayyo a lokacin da ta na raye, domin shi tasa mahaifiyar ta rasu, kuma tun bayan rasuwar mahaifin nasu ya maye gurbin kujerar tasa har zuwa wannan ƙarni da muke ciki. daga cikin gidan, ɗumbin mutane ne ƴan gaisuwa ke ta hada-hadar shige da fice a ƙaton tsarkargidan da yay kusan filoti guda, kana kallon yanda aka kakkasa ɓangare ɓangare zaka san family house ne. wata farar tsohuwa tukuf ta fito daga wani ɗaki tana dogara sanda, sai da suka ƙaraso tsakiyan tsakargidan sannan ta tsaya tana kallon mai yi mata hidima wadda ke biye da ita a baya tun fitowarta, hannunta riƙe da ƙwaryar fura babba, ita ɗaya ta rage acikin matan Alhaji Aminu Barkinɗo, cikin su uku da ya aura ita ɗaya tayi tsawo rai haka. cikin yaren fulatanci tace da Hadimar,"ki nemo Gaji ki basa furan ya kaiwa Dottijo, tun ɗazu ya aiko Manga kuma ba'a samu an kai masa ba, kuma ƙila zai sha tare da baƙi ne, yi maza du Allah". Hadimar ta wuce da sauri tabi dogon soron da zai kai ka wani babban fili kafin ka fita zuwa waje. Dada ta waiga tana kallon masu fitowa daga ɓangaren Hakimi, ta ƙwala kiran,"Munyoɗo". sai da ta kira sau biyu tukunna wata farar dattijuwa ta fito da sauri tana amsawa, tazo gabanta ta rissina tana faɗin,"Dada gani, lafiya kika fito ke ɗaya?, kuma kin tsaya ai a rana, me kike da buƙata?, ina Petel din?". tai maganar tana kamata ta matsar da ita daga cikin ranar. ta kalleta ta cikin glass ɗinta tace,"ina wannan shike, amnn mata na wurin Hayyo?". Munyoɗo tace,"wacce daga ciki Dada?". Dada ta ɗan ɓata fuska da muryar ƙorafi tace,"wannan yaro dai Allah ya jiƙan shi kawai, du yaje ya haɗo mata da yawa in ka tashi neman ɗaya sai kayi ta faman kwatance". tayi tsaki sai kuma tace,"wasu sun ƙara zuwa ne?". Munyoɗo tace,"ai Dada jiya duk sun gama zuwa, su bakwai ne yanzu sauran huɗun ance sun rasu, suna babban parlo yanzu haka". Dada ta girgiza kai alamar Allah ya kyauta sannan tace,"to wannan Balarabiyar za ki kirawo min". Munyoɗo tace,"tom Dada bari na duba". ta faɗa tana juyawa ta nufi ɓangaren da yake nanne na mahaifiyar Hayyo, ta shiga babban parlon da ya tara ƴan zaman makoki, ta dinƙa wuce su har ta ƙetara inda Ammi da Ummi suke zaune tace da Ummi,"Dada tana kiranki". Ummi ta amsa da to tana yunƙurawa ta miƙe, Ammi ma ta miƙe tana faɗin,"kin san Allah na sha'afa gaba ɗaya Dada tana nemana". tare suka fito gaba ɗaya, suka tadda har an ajiyewa Dada kujera ta zauna akai, suna zuwa ta ɗaga sandar hannunta ta bugawa Ammi, Ammi ta kauce tana faɗin,"kiyi haƙuri baƙi ne suka tsayar da ni". Dada ta harareta ta cikin glass bata ce mata komai ba, ta mayar da dubanta ga Ummi dake tsugune a gabanta tace mata,"kije ki sako mayafinki mu wuce asibiti, ance tun shekaranjiya baki koma wurin yarinyar nan ba, ban sani ba ko isashshen hankali ne baki da shi". Ummi ta miƙe cikin sanyi jiki ta wuce, Dada ta kalla Ammi tace,"kije ɓangaren Giɗaɗo kice da matarsa ta bayar da ferfesun kaji da nace ayi, na santa da ɗan banzan cin yajin jaraba, idan ta san yayi yaji da yawa to ta zubar da shi ba mayu ne zasu sha ba, ta ɗora sabo na mara lafiya ne". har Ammi ta wuce sai kuma ta ƙara tsayar da ita,"kice da Belɗo ya fito da mota zai kai ni asibiti, yace da Safara'u taje ta haɗa min kayana a kawo min yau can ina kwana". tana tafiya sai ga wata hadima daga bangaren

Chapter 46 of 73