Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da yake da coffee door, shi ba'a buɗe shi totally. for sure daga room ɗin take jiyo sautin, to anya kuwa daidai ta ke ji acikin kunnuwanta?, ai ranar har suka gama zaryarsu anan basu ji wani abu makamancin haka ba, ta tsaya tana Contemplating ta buɗe ko ta tafi, abunda kunnenta ke jiyowa dai ba na wasa ba ne, ba irin abunda mutum zaiji bane ya ƙyale ya tafi. sai kawai zuciyarta ta tsaya akan ta buɗe ɗin, ta sauke trolly daga kanta. tasa hannu ta murɗa handle na ƙofar room ɗin, door ɗin ya buɗe yana bada wani sautin ƙara. tsabar mamaki da tsorata Fillo sai taji kamar ƙafafunta ba zasu ƙara ɗagawa ba, tabi wurin da Turaki yake a yashe a ƙasan tiles dafe da ƙirjinsa, numfashinsa na fita da ƙyar. ruwan hawaye na sauka ta gefen idonsa, kawai sai taji kanta yayi wani irin nauyi, hawayen nasa ya ɗimautata, kamar wannan ace yana hawaye?, me ke damunsa?. bata san lokacin da ƙafafunta suka kaita gabansa ba gwiwoyinta suka durƙushe a saitin da kansa yake, ta kallesa taga kamar ma a sume yake, gabanta ya faɗi saboda yacca idonsa ya tsaya a wuri ɗaya cak baya ko motsi. ta kai hannu ƙasan hancinsa taji yana numfashi, sannan ta sauke wata nauyyar ajiyar zuciya. tausayinsa yay bala'in kamata, taya zata iya barinsa taje ta sanar da halin da yake ciki?, idan ta tafi me zai iya faruwa before ta dawo?, me zata yi don taimaka masa a wannan lokacin?, a yanzu kamin wani yazo?, sai taji cikin kanta kamar babu komai, dukkan wata dabara tata ta yanke mata, bata san me zata yi ba. acikin wani yanayin dake da wuyar fassaruwa tasa tafin hannunta me taushi ta shafa fuskarsa, sannan ta duƙo da kanta saitin kunnensa muryarta da rauni tace masa,"baka da lafiya? sannu, ka daina hawayen, bari naje na kirawo Maama". ta faɗi hakan tana ƙoƙarin miƙewa, ta yunƙura zata miƙe sai taji ya ruƙo hannunta ya dawo da ita. ƙwayar idonta ta faɗa cikin nasa a sanda hawayen ciki suka sami nasarar gangarowa kan kumatunta. a sanyaye tace,"zanje na kira maka Maama ne". sai taga ya girgiza kansa a hankali cikin ƙarfin hali. ta sake cewa,"to kana da magani a kusa na ɗauko maka?, aina zan ɗauko?". nan ma kansa ya girgiza mata a hankali. cikin dauriyar abinda yake ji acikin zuciyarsa. sai ta samu kanta da ce masa,"to me zanyi maka? me kake so?". sai taji ya ƙara damƙe hannunta sosai, ya sauke kallonsa daga kanta ya tsayar ajikin bangon dake facing nasu. ta tsaya kawai tana kallon gefen fuskarsa, tana jin yanda ruwan hawayensa ke ɗiga a saman skirt ɗin jikinta, tana jin yana ɗauke kansa daga ƙasa yana ɗorawa a saman cinyarta, tana ji yana ƙara damƙe hannunta, tana jin yanda wani abu ke fita daga tafin hannunsa yana shiga cikin nata, tana jin wannan zafin da ta tabbatar yana ji a zuciyarsa yana taɓa tata zuciyar. ta rumtse ido for few seconds sannan ta buɗe, ta buɗe tana bin inda yake kallo har sanda ta sauke kallonta gaba ɗaya akan ƙaton enlargement ɗin dake manne a bango. tayi mugun zabura da hoton da ta gani, ta tsayar da ƙwayar idanuwanta cak akan hoton tana ƙarewa dattijuwar matar dake jikin hoton kallo, ba sai an faɗa ba matar balarabiya ce, kallon matar take tana hango tsananin kamanni na Turaki dana Zaytuna a tare da ita, tun daga murmushinta har dimple ɗinta daya lotsa ciki sosai babu abinda ya banbanta daga na Turaki dana Zaytuna. _but who is she?_, tambayar da taiwa kanta kenan, kuma kafin zuciyarta ta raya mata wata amsa sai ganin Turaki tai ya miƙe tsaye yana toshe duka kunnuwansa biyu yana doka goshinsa a jikin glass da ƙarfi. tayi azamar miƙewa tana ruƙo shi tana faɗin,"ka daina, zaka ji ma kanka ciwo". ta faɗa cikin tashin hankalin da ta rasa na menene, kuma rufe bakinta kenan jinin dake fita a goshinsa ya zuba akan ƙirjinta. ta kalla jinin dake ƙirjinta, ta kalla jinin dake fitowa a goshinsa, idonta a waje tace,"ka bari". ta faɗa da wani mugun ƙarfi tana sa hannu da iya ɗan ƙarfin da take da shi ta fizgo shi daga bakin glass ɗin da yake tsaye, sai gasa a gabanta, taja hannunsa ta zauna da shi a ƙasa tana kunce ɗankwalinta ta ɗaure masa goshin. "menene? ka daina kukan to dan Allah, ka faɗa min me kake so?, me zanyi maka?, ka jira anan karka ƙara tashi zanje na kira Maama". ta faɗa kukan dake bakinta na fitowa. kuma sanda ta yunƙura zata miƙe lokacin ya janyota jikinsa ya rungume tsam yana kama hannunta ya toshe kunnensa da su. muryarsa na fitowa cikin muryar namiji mai rauni da faɗin,"don Allahhhhh, ki taimaka min". _Ayi Haƙuri dan Allah, mun shiga rububin biki, from this week har next week, babu zama kullum tafe ake, idan an zauna kuma hayaniyar ƴan taro ta hanaka sakat balle ka sami natsuwar typing, kuma kun san jiki da jini, mutum naso ya huta idan yay struggling. dalilin da yasa kuka jini ɗiff kenan, kuci gaba da haƙuri tare da min uzuri._ *Comment naku shi ne ƙwarin gwiwata.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *23* ya ƙara maimaitawa,"help me pleaseeee". ya faɗa yana ƙara ƙanƙameta. Fillo ta haɗiye yawun bakinta da ƙyar, ita bata taɓa jinta a jikin ɗa namiji ba ko da Yayanta Hamid. amma yau itace gaɓa ɗaya cikin jikin wani ƙaton ya ƙanƙameta, ƙanƙamar da tasa ta jin kasala, kuma tana ta ƙoƙarin ta fita a jikin nasa ta kasa. sai tayi shiru kawai tana sauraren yanda zuciyarsa ke bugawa, beat ɗin na fita da ƙarfin gaske, sai taji tana jin tsoro. muryarta a hankali tace,"taimakon me zanyi maka?". ta faɗa tana so ta raba jikin nata da nasa, lokaci ɗaya sai tsoronta ya ƙaru jin yacca jikinsa ya saki gaba ɗaya. ta fita daga jikin nasa a sanda ya tafi luu ya faɗi ƙasa, bata san lokacin da ta kurma uban ihu tana tallafo kansa da sauri. ta shiga girgiza shi tana cewa,"ka faɗa min taimakon me zan maka?, me kake so na maka?, Turaki ka tashi dan Allah". kuka take sosai tana cewa ya tashi, da dai ta tabbatar cewa ya suma sai ta miƙe a ruɗe ta fice daga ɗakin, har ta kai step na ƙarshe zata sauka daga stairs sai kuma ta fara tunanin idan ta tafi ta barsa shi ɗaya cikin wannan halin me zai iya faruwa da shi?. dan haka da sauri ta ƙara komawa har tana kusa zamewa, Allah ya taƙaita tsautsayi bata faɗo daga benen ba. yana nan a sumen har yanzu, tai kansa cikin kiɗima tana ƙara jijjigasa tana cewa,"ka tashi don Allah, ka tashi ka faɗa min duk abinda kake so zanyi, zan taimaka da ko menene ko da ace zan rasa raina ta sanadin hakan". duk wata dabara nata da tunaninta ya gushe a brain ɗinta, tayi dirshen a wajen tana ta kuka abinta, tsoronta Allah tsoronta ace mutuwa yayi, wa ya kashe shi?. sai kawai ta ƙara fashewa da kuka tana tallafo kansa zuwa kan cinyarta, tasa hannu ta share hawayenta tana ta maganganu ita ɗaya. "kar ka yi min haka dan Allah, kar ka mutu a sanda yake daga ni sai kai a wajen, za'a ce ni na kashe ka, wallahi haka zasu ce. kuma ni ban san komai ba, ban san me ya sameka ba, dan Allah dan Annabi ka farka karka mutu yanzu, ka farka ka faɗa min duk abinda kake so, ka faɗan duk kalan taimakon da zanyi maka, ni kuma nayi alƙawarin zan maka shi". ta ƙarasa maganar tana kifa goshinta akan nasa, sam sam bata san me ya kamata tayi a yanzu ba, abu ɗaya ta sani, shine ba zata taɓa fita ta barsa shi ɗaya a cikin wannan halin ba. can kawai sai taji zuciyarta na faɗa mata cewar ta kira waya, ta kira Maama ta sanar mata komai, to amma da wacce wayar?. ɗago da kanta tayi ta fara laluben aljihunsa dan ɗauko wayarsa, ta gama lalubenta bata ji komai ba sai wallet ɗinsa. tunaninta wayar ko tana cikin wallet ɗin ne, hakan yasa ta buɗe wallet ɗin da niyyar ɗaukowa, amma da mamakinta tana buɗewa taci karo da hoton mutum biyu, na Zaytuna da kuma Dattijuwar matar da ta gani a jikin wancan hoton. kanta ya ƙara ƙullewa ta rasa wanne irin tunani za tai akan lamarin dake yawo cikin ranta, yanzu ba lokacin buƙatar lallai sai ta san komai ba ne, yanzu lokaci ne na kuɓutar da Turaki da take ganin kamar rayuwarsa tana jingine da ita ne, warwarewar abunda bata sani ba shi yafi komai sauƙi a wajenta, idan ya farka zata zauna ta zana komai dake ƙulle cikin kanta a tsakiyar tafin hannunta, tukunna ta karance shi da zurfin tunaninta, idan lissafin nata yayi dai-dai, to ta tabbata daga nan zata warware komai a cikin sauƙi. cikin azama ta miƙe ta nufi hanyar fita sai Allah ya nufeta da ganin wayarsa akan locker, ta isa wajen ta ɗau wayar hannunta sai karkarwa yake. ba security a wayar, dan haka tana buɗewa kai tsaye lambar Maama ta laluba, bata ma san ta yanda akai ta iya wayar ba tunda ba taɓa riƙe waya tayi ba a rayuwarta, ko wayar Yami ma tsakaninta da ita in Amir ya kira Maijidda ta kawo mata tasa mata a kunne, amma ko ɗaga waya bata taɓa yi da kanta ba. scrolling kawai take a ɓangaren miscalls amma ta rasa lambar da ta dace ta kira, bata san wani Bello Ƙaraye ba, haka bata san lambobin biyun da babu suna a jiki na waye ba, fita tai daga ɓangaren call ta shiga contact, take taci karo da sunan My world, cikin sauri ta danna kiran ya tafi. daga can ɓangaren Hajiya Madina da ke zaune akan kujerar dake cikin ɗakinta. ƙafafunta a harɗe tana jin yanda zuciyarta ke matsewa, tana jin yacca zuciyarta ke faɗa mata kamar ba zata iya komai ba, tana jin yanda idanuwanta ke faɗa mata kamar ba ita ta haifi ƴaƴan dake zaune a gabanta ba, tana jin yacca ƙwaƙwalwarta ke faɗa mata rayuwar Turaki ita tafi cancanta da ta ingata sama da ta sauran, cikin kanta na lissafa mata kamar yanda take jin bata da kowa a duniyarta sai Turaki, haka shima Turaki ke jin ba shi da kowa a duniyarsa sai ita, ita ɗaya jallin jal. ƙwayar idonta ta wulƙita ta kalli Zaytuna, sannan ta kalli Nihal, tukunna ta sauka akan Samha, duka Yaran suna daga kan gadonta ne suna hira cike da soyayyar junansu. Samha kawai take iya gani a lokacin, kallon yarinyar take da irin kallon da ita kaɗai tasan ma'anarsa, ta kuma san manufarsa, ta kuma san lissafin da ƙwayar idonta ke yi akan yarinyar, ta kuma san ciwon da kallon nata ke hifarwa da ƙwayar idonta. da ace zata iya, tabbas da tace komai ɗin da take ji take gani ƙarya ne, to amma bata isa ba, bata isa ta kira abubuwan da tasan suna tafiya ba a matsayin ƙarya, ita gaskiya take bi, kuma gaskiyar ta sani, kuma gaskiyar zata bi. sanda ta rufe idonta tana sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya, sannan ne wayarta dake kan cinyarta tayi ƙara, ta ɗaga tana kallon screen ɗin da sunan THE BEST ke yawo ajiki. lokaci ɗaya taji duk wani ɗaci da ɓacin ranta ya gushe, tana jin wani ɓari na damuwar da take ciki ya yaye, fuskarta ta bayyana jin daɗin ganin kiran nasa, sai ta ɗaga tana faɗin. "Me Babban suna kana ina?, ina ta kiran wayanka baka ɗauka ba, na kira Bello yace bakwa tare, ina ka tafi?, Khalil yace baka je office ba yau, ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya, duk inda kake ka dawo gida yanzu kaji, ina nan na kasa samun nutsuwa tun kiran farko da nayi maka ban samu ba, yau na kiraka yafi sau goma kiran baka picking, tukunna dai kayi lunch?". maganar take muryarta na bayyana tsananin damuwar dake ƙunshe a cikin ranta, ba don komai sai dan rashin sanin halin da yake ciki tun safe da ya bar gida. haka take ita, indai ya fita a gida basa 1hour basu yi waya ba taji ya lafiyarsa, idan kuma yana gida to jiddan walahairan yana part ɗinta, suna tare ko a parlo ko kuma a bedroom ɗinta, sai dai idan ranar yana jin miskilancinsa har da ita to sai dai ita ta bisa part ɗinsu. ta kan tsokane shi da cewa,"Hamman'su kana juya ni kamar waina a tanda". Fillo da ke tsaye tana sauraren maganar Hajiya Madina, tausayin matar yay bala'in kamata, sai ta kasa yin ko da motsi, tai shiru ta kasa yin magana, tabi inda Turaki yake yashe kawai tana kallonsa, me yake faruwa da rayuwarsa ne?, me zata faɗawa Hajiya Madina yanzu?, ya zata yi idan taji a halin da ɗanta yake ciki?. sai ta tuno yacca Hajiya Madina ta shiga tsananin tashin hankali a wata rana da ya yanke da wuƙa yana yanka lemu, ta dinga kuka akan ɗan jinin da ya zuba daga jikinsa, ta tuna yanda Hajiya Madina ta koma bata iya nutsuwar minti ɗaya babu Turaki a kusa da ita a lokacin, ta tuna yacca duk bugawar sakan, duk wani motsi nasa sai tace,"menene me Babban suna?, me kake so?, me zan maka?, ciwon yana zafi?, sannu kaji, Allah ya baka lafiya". haka ta dinƙa ririta shi kamar jariri sabuwar haihuwa a lokacin. sai Fillo taji inaa ba zata taɓa iya kasassaɓar sanarwa da Hajiya Madina halin da Turaki yake ciki ba a yanzu, ba zata iya ba har ga Allah, bata son taga uwa ta shiga tashin hankali, balle kuma Uwa irin wannan da lokaci ɗaya take fita daga hayyacinta akan ɗan da ta ƙwallafa rai akansa duk kuwa da tana da wasu Ƴaƴan da Allah ya bata. Hajiya Madina ta rufe ido ta buɗe tana kallon agogo, ƙarfe biyar na yamma, yau watarana ce da ta kafa tarihi a tsakaninta da Turaki, rana ta farko da Turaki ya saɓa umarninta a iyaka tsayin rayuwarsa, to amma me yasa?. sai kawai ta rufe ido ta ƙara buɗewa tana sauke ganinta a daidai lokacin da agogo ya nuna biyar harda minti ɗaya, sai taji ranta ya ɓaci. kuma cikin nuna ɓacin ran tace,"baka taso a stubborn ba, kuma duk cikin ku shida kai nafi karewa daga duk abinda zai sa ka zama stubborn, amma me yasa sai daka girma?, kana so ka zama Stubborn kamar Khalil ko?. saboda nace duk sanda ka fita ya zama kuna tare da shi ko ina zaka je, ba wai ina nufin ka zama mara ji ba kamarsa, na sani da takurawa ace lallai duk inda zaka je sai da ƙaninka alhalin ka mallaki hankalin kanka, amma ka sani ni uwa ce da ba zan so wani abu ya cutar da ɗana ba, ya kamata ka tuna da akwai masu faraurar rayuwarka a kullum, dalilin da yasa nace duk sanda ka fita ya zam kana tare da Khalil ko Bello duk da nasan dabarata bata isa ta hana faruwar abunda Allah ya shirya ba. amma dai atleast kasancewarka tare da wani zai sa suke tsoron tunkararka. kuma sai da kayi min alƙawarin ba zaka saɓa umarnina ba akan hakan ba, Me Babban suna me yasa yau rana ta farko ka saɓa umarnina?, Khalil yace ko minti 2 baka yi a office ba ka fita, Bello yace kana ɗaukosa a airport kuka rabu. ina ka tafi tun bayan rabuwarku?, me yasa baka dawo gida kaci abincin rana ba?, me yasa kaƙi ɗaga wayata?, me yasa kake son haddasa ciwona ya tashi?, me yasa tun ɗazu ina maka magana kayi min shiru?, rashin maganar na menene?, lafiya?". tunani da lissafi dake a cikin kan Fillo ya tarwatse, gabanta yay dukan tara-tara, kallon Turaki take yi tana tuna irin tarin tasa soyayyar wa mahaifiyarsa, zuciyarta na faɗa mata taje ta same shi ta faɗa masa Maama ce, Maama na son yin magana da shi, zai farka idan yaji hakan, tabbas zai farka. ta isa gabansa tana jijjigasa a hankali daidai kunnensa tana faɗin,"ka tashi ga Maama". a zatonta ko jin hakan zai sa ya farka daga dogon suman da yayi, amma inaa kamar ma da gawa take magana. sai kawai wani kuka ya kubce mata. cikin kiɗima Hajiya Madina tace,"innalillaihi wa'inna ilaihi raji'un...". ko salatin bata ƙarasa ba Fillo tace,"Maama ki zo". ta faɗa tana kuka sosai. daga ɓangaren Hajiya Madina ta zabura ta miƙe daga kan kujera, cikin gigita da tsananin tashin hankali na farat ɗaya, me kunnenta yake ji ne?, kamar kukan wani take ji kuma kamar ana so ace mata tazo ga Turaki babu lafiya. "waye ke magana?, ina Muhammad ɗin?, ke wacece?". kukan Fillo ya ƙaru tace,"Maama ni ce, Hammah ɗin ya faɗi ya suma Maama kizo da sauri". wayar dake hannun Hajiya Madina ta nemi ta faɗi a ƙasa, Samha da idonta ya kai wurin tai saurin taro wayar sanda ta sauka daga saman gadon. ta taro wayar a lokacin da itama Hajiya Madina ke neman faɗuwa, Nihal tai saurin riƙota. Samha tace,"Lafiya Maama, menene?". Hajiya Madina ta kalleta ido a waje, a hankali ta kalli Nihal, sannan ta kai idonta ga Zaytuna wacce tayi tsaye ƙeƙam. sai kuma ta dawo da idonta ta sauke akan wayar tana kallon call ɗin dake tafiya, Hammah aka ce mata alhalin ga ƙannensa anan tare da ita. cikin neman fitar hayyaci tace,"to wace me magana a wayar?, wai Hammanku ya suma, to aina?, garin ya?". ta wurga tambayoyin ga Samha. duk su ukun suka maimaita,"Hammah ya suma?". Hajiya Madina ta ɗaga musu kai kawai hawaye na sintiri a saman fuskarta. "hello, dan Allah wake magana, ina me wayar yake dan Allah?". Nihal ta faɗa acikin wayar bayan ta amshi wayar daga hannun Samha. babu amsa sai kuka dake tashi kawai, Zaytuna ta silale a wajen, Nihal tayi kanta da sauri. Samha ta ɗau wayar ta kai kunne, dan tuni Hajiya Madina tayi mutuwar zaune, ta koma kamar me paralize idonta a wuri ɗaya kawai yake, jinta take kamar rayuwarta ta ƙare, kamar shikenan ta gama aiki. daga ɓangaren Fillo tace,"Hammah ne ya suma". Samha ta waiga taga sauran sisters ɗinta suna nan, ɗaya ta suma ɗaya na ƙoƙarin ganin ta sumen ta farfaɗo. to wace ke faɗin Hammah ya suma?. sai ta dakewa faɗuwar gaban da take ji tace,"to waye yake magana, kuma wanne Hammah ɗin?". Fillo na ƙara jijjiga Turaki tace,"ni ce Fillo, Hammah Turaki ne ya suma Maama, tun ɗazu yaƙi yay motsi kamar ya mutu". a matuƙar razane Samha ta miƙe tsaye tana faɗin,"what! mutuwa?, dan uwarki ke kina ina?, ta ya kika san abinda ya faru da Hamman'mu?". jin furucin Samha yasa jikin Fillo yin rawa a lokacin zuciyarta na faɗa mata shikenan tata kuma ta ƙare, ita dama ta sani ita za'a ɗorawa alhakin faruwar komai. "Fillo aina?, aina ya suma?". Hajiya Madina da ta amsa wayar take tambaya kuka na ƙwace mata. "Maama ɓangaren su Adda Zay...". bata ƙarasa ba taji alamun faɗuwar waya a ƙasa. kuma zata iya cewa rabin second ne ya kawosu, dan ganin su kawai tayi tsaye akanta. Hajiya Madina ta fizgo Fillo ta miƙe tsaye, ta zabga mata mari a fuska, marin da yasa jinta da ganinta suka ɗauke na wucin gadi. kamin ta dawo dai-dai ta ƙara ɗauketa da wasu marikan har uku. "uban wa ya buɗe room ɗin nan?". babu abinda Fillo ke ji a lokacin balle ta iya bada amsa. "ba magana nake miki ba, ban yi muku iyaka da wannan room ɗin ba?, bance duk sanda zaku yi aiki babu ruwanku da taɓa wannan ɗakin ba?, wa ya baki key ɗinsa?, me yasa baki hanasa shigowa ba?, kin buɗe baki kin yi min magana ko sai nasa ƴan sanda sun kamaki kin ƙare rayuwarki a bayan kanta?". Fillo na kuka tace,"wallahi Maama bani na buɗe ba, nazo wucewa ne...". bata barta ta ƙarasa maganar ba tasa bayan hannunta ta kifar da ita a ƙasa, Fillo ta zube a ƙasan tiles kanta na dukan bango, lokaci ɗaya taga giftawar wasu taurari acikin idanuwanta. abunda kawai zata ce ta ƙara ji shine Hajiya Madina ta mata gargaɗin cewa,"duk abunda ya sami ɗana, duk abunda ya sami lafiyar ɗana sai naga bayanki Fillo, tabbas sai kin ƙwammace ina ma baki zo duniyar nan ba". daga nan bata ƙara jin komai ba kamar yanda bata ƙara ganin komai ba na tsawon wucewar minti goma sha biyar. kuma sanda ta dawo hayyacinta daga buguwar kan da tayi, sai taga babu kowa a ɗakin sai ita ɗaya. tsawon minti biyar tana kuka, a hankali ta dinƙa kewaye ɗakin da kallo, babu komai acikinsa face shirgin takardu dake cikin locker, sai kuma gadon jarirai irin wanda ta taɓa gani a ɗakin Fulani, sanda Kaka ta zauna yiwa Gimbiya Zahra wankan jego. wanne abu ne acikin ɗakin da ya haddasa shigar Turaki situation ɗin da ta zo ta same shi aciki?, ina abunda yasa ba'a so a buɗe ɗakin?. ta kalli komai kuma bata ga komai ɗin da zai zama dalili ba. taimakonsa tayi, kuma taimakon take da niyyar yi masa, amma ga da abinda aka saka mata da shi, ya za'ai ta manta?, waye zai taushi zuciyarta akan abinda ta ƙudurce na ramuwa?, Amir ne kawai, kuma yanzu babu Amir a cikin rayuwarta, tsawon watanni huɗu sai taji tana kewar Amir a yau. sai ta runtse ido tana jin zafi a zuciyarta, ta miƙe tsaye da ƙyar tana dafa bango saboda hajijiyar da take ji, ko'ina na ɗakin take bi da kallo, so take taga illarsa, ba zata taɓa barin ɗakin nan ba sai taga illarsa da kuma dalili, wannan dalilin da ya haifar da komai. ta miƙe da ƙyar ta tafi tana jan ƙafarta dake yi mata zugi har ta ƙarasa gaban enlargement. kallon matar take yi da kyau cike da nazari da son gano wani abu amma ta kasa, abu ɗaya ta fahimta matar nan na da alaƙa me ƙarfi da Turaki, saboda tsananin kama, kamannin da suka zama kamar an tsaga kara, sai dai irin alaƙar da take tunani zuciyarta na faɗa mata cewa ba ita bace, wannan matar bata yi kama da wacce ta ajiye ɗa kamar Turaki ba, shekarunta kaɗanne, kuma ko da auren ƙauye aka mata baici ace ta haifi ɗa kamarsa ba balle har ta haife shi, ta haifi Zaytuna. ba ma wannan ba, idan ma tayi tunanin ita mahaifiyarsu ce to Hajiya Madina fa?. ta dafe kanta da take jin kamar zai fashe tana saurin dafa gadon jariran, bata buɗe idonta ba har sai da ta daina jin juwar, idonta ya sauka acikin gadon jariran, kan award frame dake kan bargon jariri, tasa hannu ta ɗauko tana kallon award frame ɗin, tayi concentrating akan hoton jiki da sunan jiki. *her Excellency RAMLA MUHAMMAD TURAKI*, sunan da yake rubuce a jiki kenan. wai wace wannan matar?, mene alaƙarta kuma da sunan Turaki?, *MATARSA!*, haka zuciyarta ta faɗa mata, kuma tabbas hakan yake, amma ina take?, mutuwa tayi?, rabuwa suka yi?, take anan zuciyarta ta warware mata dalilin da yasa ba'a son buɗe ɗakin, da kuma dalilin da yasa Turaki shiga critical condition. saboda wannan ɗakin na da alaƙa da ita shiyasa ba'a so a buɗesa, sannan ganin hotonta na fama ciwon da ta jiwa Turaki a zuciyarsa, wannan ciwon da tabonsa ya kasa goguwa daga garesa. wanne irin ciwo ne?, me tayi masa wanda ya kasa mantawa?. ta ƙara ƙulle idonta for 1minutes sannan ta buɗe tana ƙarewa gadon jariran kallon, ta tabbata wannan room ɗin shine silar komai, kamar yanda gadon jariran nan ke da alaƙar komai, kenan idan tunaninta ya bata dai-dai *ƊA* ne silar komai, jaririnsu!, to ina jaririn?, kuma itama uwar tana ina?, ta mutu ne?, ita ɗan da suka mutu?, kenan wannan shine ciwon dake manne a zuciyar Turaki?. sai kawai Fillo ta sauke numfashi tana hurar da iska a bakinta, ta koma ta isa gaban englargement din ta cirosa, sannan ta dawo ta ɗauko award frame ɗin ta fice da su daga ɗakin. *6hours pass, Miyyetti Hospital, Room 05.* cikin vip room ɗin, Turaki ne jingine a jikin pillow ɗin da aka saka masa a bayansa, goshinsa ɗaure da bandage, an naɗe wurin da ya ji ciwo da shi sanda yake dukan kansa ajikin glass. gefensa kuma wata farar tsohuwa ce kamar balarabiya a

Chapter 21 of 73