Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da yay mata yana ƙara tamke fuskarsa yace,"aje nace". ta kallesa taga yanda idonsa ya kaɗa yay jawur, sai kawai ta kifa goshinta akan ƙafarsa ta fashe da kuka. ya waiga yaga har yanzu Ilham bata fito a kitchen ba, dan haka da azama ya miƙe ya ɗau ledan drugs ɗin sannan ya kama hannun Fillo ya jata suka fice daga parlon, tana ta tirjewa yaƙi sakinta har sai da suka shiga ɗakinsa, ya wurgata kan gado yana saka key ajikin ƙofar, sai dai abinda ya matuƙar bashi mamaki yana waigowa yaga ta buɗe roban malt ɗin tana zubar da shi a ƙasan tiles ɗin. _manage please._ *vote, comment and share.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _not edited._ *30* Turaki ya harɗe hannayensa a ƙirji yana ta kallon yanda Fillo ke juye malt akan tiles, sai da ta juye tass tukunna ta turo ɗan ƙaramin bakinta da ya ƙurawa ido, yaga ta tashi without looking at inda yake tsaye ta wuce inda wani ƙofa yake ta buɗe, waje ne kamar balcony, mopper ta ɗauko ta dawo tukunna ta shiga toilet ta ɗebo ruwa ta dawo ta goge wurin tas da turaren ƙamshi me daɗi. kamar yanda bai san me zai ce mata ba haka bai san abinda zai yi mata ba. duk tana jin yacca kallonsa ke shiga jikinta amma tayi kamar ta manta tare suka shigo ɗakin, in ace ba Turaki ba ne ba zata taɓa yarda ta ɗau tsayin sakanni ba balle mintuna tare da wani ƙato a ɗaki ɗaya, but shi ko da yaushe zuciyarta faɗa mata take yi he is a good person, he will not hurt you, sai dai ma ya kare mutuncinki da iyakar ƙarfinsa. kuma kamar yanda zuciyartata ta faɗa mata haka Hajiya Madina ta faɗa mata,_"me babban suna ba zai taɓa cutar dake ba Fillo, ko kaffara ba zanyi ba akan hakan, saboda haka karki taɓa jin ɗarr dan kun kasancewa wuri ɗaya tare da shi"._ kuma in the same day ne bayan ta koma ɓangarensu, da Kaka ta ganta a firgice ta tambayeta lafiya?, ta faɗa mata cewar tana ɗakin Maama ne Turaki ya shigo, kuma ya hanata fita yace taci gaba da aikinta shi kuma ya kwanta kan kujera. abinda Kaka tace mata a lokacin shine,_"ba'a shaidar ɗan kuturu sai ya kwana 100 da yatsa, to amma ni zan shaidi Turaki, ba wuri ɗaya muke kwana mu tashi ba, ban san halinsa ba, amma zanyi rantsuwa kan cewar Turaki ba zai cuci ƴa mace ba, ko da ace kuwa zasu kwana wuri guda. kawai dai ki kula sosai Fillo"._ sai da ta gama mopping en sannan tayi bakin ƙofar wurin da har yanzu yake tsaye, tai ƙasa da kanta sosai ƙirjinta sai bugawa yake yi, tana ta aikin jan yatsu shi kuma yay shiru kamar baya wurin. sai da ta gaji da tsayuwa tukunna tace masa,"dare yayi, Kaka tana jirana". tai maganar a sanyaye. ya sauke hannayensa ya zuba su cikin aljihu sannan yace mata,"kin gama shan malt ɗin?". da mamakinsa sai yaga ta ɗaga masa kai alamar eh, ya ƙara cewa,"ya isheki ko a ƙaro?". tace,"ya isheni". hannunta kawai ya kama suka koma zuwa ciki, har yanzu jikinta kwai zafi sosai. yay mata nuni da bakin gadon na alamar ta zauna, tace"don Allah". maganar ta katse dalilin haɗa idon da suka yi yana jifanta da wani kallo. babu shiri ta zauna hawaye na biyo kuncinta, yaja stool ya zauna yana ce mata,"tare aka haife ku da kuka ne?". tai saurin girgiza kai, yace,"to yi min shiru, in kuma anan kike so ki kwana karki fasa". babu shiri tayi ɗif tana goge hawayenta da gyalenta. shiru ya gimla cikin wasu ƴan sakanni, tana ɗago ido ta kallesa taga yana ɓallo magani, bata san lokacin da tace,"ni kam na shiga uku". yaci gaba da ɓallan maganin sannan yace da ita,"bani ruwa". cikin azama ta miƙe ta nufi ƙofa zata fita, a dabararta na in ta fita ba zata dawo ba, amma tana zuwa taji yasa key a ƙofan, ta waigo tana ce masa,"ƙofan rufe yake". ba tare da ya kalli inda take ba yace,"not necessary sai kin fita, ga ruwa nan akan drower". taji kamar tai ihu, sai kace wadda ƙwai ya fashewa a ciki haka ta wuce inda roban faro yake ta ɗauko tare da cup, ta kawo masa yace ta zuba ruwan a cup, ta zuba sannan ya kamo hannunta ya zuba maganin yace ta shanye. da ƙyar ta sha maganin tana sha tana hawaye, suma da guda ɗai-ɗai ta dinƙa sha, tana gama sha sai ga amai nan ya taho, ta miƙe da sauri tayi hanyar toilet taji yace,"idan kin gama aman sai ki kwanta anan". ya faɗa yana nuna mata gado da bakinsa, tare da miƙewa zai fice. kamar wacce aka dannawa pause haka ta tsaya tana sa hannu ta rufe bakinta, idanuwanta suka firfito waje dan ita ɗaya ta san me take ji, haka har sai da maganin ya koma, tana sauke numfashi tace,"na shanye". yay mata shiru ya fice ya barta, yin duniya ta buɗe ƙofan duk da cewar there is spare key amma ƙofan yaƙi buɗuwa, means ya bar key ta waje kenan, wucewar five minutes sai ga shi ya dawo da coolern abinci a hannunsa, tana kallo ya wuce sai dai at this time ta kasa attempting buɗe ƙofan, binsa tayi da ido kawai har ya zauna kan kujera. ya waigo da kansa yay mata kallo ɗaya, kuma take ta gane nufinsa a sanda suka haɗa ido, ta taho a hankali tazo ta zauna a ƙasa, ta ɗauko coolern dake kan table da plate ta zuba soyayyan taliya da vegetables ta zuba kaɗan, kuma kamar ance ɗago ta ɗago taga ya zabga mata wani nugun kallo, ba shiri ta ƙara abincin ya ɗanyi auki sannan ta fara ci. har ga Allah dama yunwa take ji, rabonta da abinci tun safe, hakan yasa ta zage tana cin abincin, ba ta ankare ba taga har ta cinye. son samu ace tayi ƙari to amma ba zata iya ba, Turaki dai idonsa na cikin glass yana operating laptop ɗin dake gabansa, tana ta kallonsa for almost 2minutes taji agogon ɗakin yayi ƙara, tana dubawa taga har 8:30. ta juyo tana ƙara kallonsa tace,"don Allah ka buɗen ƙofan na tafi, hakan babu kyau, Kaka tana can tana jirana". ya kalleta ya kalla coolern gabanta yace,"kin cinye?". ta girgiza masa kai,"na ƙoshi". yana ta kallon coolern yace,"buɗe na gani". ta buɗe yaga saura kaɗan bai fi spoon goma ba, ya galla mata harara yace,"juye ki ƙarasa cinye shi, wa kike tsammanin ya cinye sauran jagwalgwalonki?". ta marairaice tace,"cikina na ciwo". yace,"zo ɗau magani ki ƙara". sai ta rumtse ido sosai tana yin ƙasa da kanta, ta shiga afa abincin kamar me cin magani. kafin ta ɗago ta kallesa taga yanda idonsa ya sauya kala, haka ɗaya sai taji bala'in tausayinsa cikin ranta. kuka ta ke son yi amma bata so ta yi gudun kar ciwon kanta ya ƙaru, ga shi duk iyakar ƙoƙarinta ta kasa yi masa rashin mutuncin da ba zai ƙara sa shi shigo da ita ɗakinsa ba, infact kallonta ma ba lallai ya ƙara yi ba, to amma daga zaran tai attempt na yi masa wani abu sai wannan girman kwarjinin nasa ya tarwatsa duk plans nata. with breaking voice tace,"baka ci abincin ba, kuma ɗazu kace kana jin yunwa, ka cinye wannan ɗin". kai tsaye ya bata amsa da,"yara ne suka girka". yanda voice ɗinsa ya fita sai ta ƙara jin tausayinsa haka siddan. tace,"to haka zaka kwana da yunwa?". still ba tare da kallonta ba yace,"Maama tayi bacci". sai tai shiru tana kallonsa, taji ƙwalla ta cika idonta da tausayinsa, ta lura ba ya iya sakewa idan ba tare da Hajiya Madina ba, haka kuma magana ma baya iya yinta sai yana tare da Maama ko Zaytuna, da su kaɗai take ganinsa taga yana ta zuba magana har haƙoransa su dinƙa washewa da dariya, to randa kuma aka ce mahaifiyarsa ta dawo fa?, tunda ta fara aiki bata taɓa ji ko ganin yaci abincin da ba Maama ce ta girka ba in har a gida yake, ko office ya fita sai Maama tayi girki an bawa driver ya kai masa, to hana rantsuwa ita yasa ta taɓa dafa masa indomie ya kuma sha kunun da ta dama, wataran har Nihal ke tsokanarta da Fillo ƴar sa'a, Hammanmu yaci abincin hannunki. anan hawayen da suka cika idonta suka sami nasarar gangarowa, kewar tata mahaifiyar ya daɗa kamata, duk da Kaka na faɗa mata zuwa yanzu Ummi ta rasu, amma ita ajikinta ba ta jin hakanne, tana ganin kamin duniya ta tashi kamar zata ga Ummi, kamar zasu ƙara rayuwa tare da Ummi, kamar Ummi ta kusa dawowa gareta, amma sai zuwa yaushe zata ga Hammah Hamid?. wayar Turaki tayi ringing, bai ɗaga kiran ba sai da ya tsayar da duk abinda yake yi, daga yanda ya saita natsuwa zaka san da mutum me muhimmanci zai yi magana. ya ɗaga wayar yana rissinawa tamkar yana gabanta, yace,"kin tashi Maama?". daga ɓangaren Hajiya Madina tace,"na tashi me Babban suna". yace,"how are you feeling now?". tace,"feeling much better dear son. am sorry nayi bacci ban jira ka dawo ba, Zaytuna ta min allura ban san time da baccin ya ɗauke ni ba". Turaki ya sauke numfashi yana miƙewa tare da ce mata,"naji daɗin hakan ai, atleast kin samu kin huta. gani nan zuwa". tace,"i know you are tired, kayi kwanciyanka sai da safe tukunna. have you eaten your dinner?". yay shiru bai ce komai ba, tace,"na dafa maka tea, yana perlonku ka duba. ka tabbata kaci ka ƙoshi before you sleep". yace,"to Maama, thank you, Allah ya ƙara miki lafiya". tace,"yauwa bye bye, sleep tight. karka manta da adu'a". ya ajiye wayar yana kwantar da kansa jikin kujera. Fillo dai nata kallonsa tana jin wani tausayinsa na ratsata. gani tayi ya tashi ya fita yanayinsa na juyawa zuwa na marasa lafiya, kuma kamin ta yunƙura tabi bayansa sai ga shi ya dawo hannunsa riƙe da basket, ya wuce ya ajiye kan table ya shiga toilet ya fito. kaɗan ya zuba tea ɗin, soyayyan bread da ƙwai ne, slice biyu ya ɗauka yaci. zuwa lokacin bacci har ya fara ɗaukar Fillo, ta kifa kai a jikin gadon. a cikin baccin nata taji yana waya yana cewa,"haka fa, ai dalilin da yasa ma ba'a fiya son a tsaya ƙofar gidan ba kenan, both the two side, an ma fi samun wannan matsalar daga ta gate ɗin ma'aikatan gida. yes, ai kwanaki ma akwai baƙuwa da muka yi tana taɗi anan main gate so basu ankare ba sai jin abu tayi ya nannaɗe mata jiki, ana dubawa akaga ashe maciji ne. the same abinda ya faru da wata ƴar aiki ma, tana compound nasu ne ko tana bakin gate tana taɗi, na dai manta but itama ce akai abu kawai taji yana shiga cikin kayanta, ashe wani tsohon maciji ne yayi girmana, da ƙyar aka cire macijin nan a jikinta, ƙarshe ma mutuwa yarinyar tayi, shiyasa ai duk wanda ya san hakan yana kiyaye tsayuwa a compound ko bakin gate, don akwai ɓoyayyun macizai da yawa, shiga jikin mutum kawai suke kamar an aiko su, most especially masu tsayawa suyi zancen nan, suna tsaye sai dai suji maciji ya shige jikin...". ai bai ƙarasa ba Fillo ta kurma wani uban ihu tana haɗewa da salati, cikin second ɗaya ta tashi a ƙasa ta dire akan gado. ta cure a wuri ɗaya tana faɗin,"na shiga uku na lallace, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, maciji wayyo Allah na". faɗa take tana ƙara maimaitawa ataimaka mata maciji ne, maciji ya shige mata jiki, shi dai kawai yana zaune yana kallonta kamar tv, yay hanging wayar ƙaryar da yake yi, sai da ya tabbatar tsoron ya shigeta sosai ta yanda gobe ko uban Amir ne yazo ba zata sa ƙafa ta fita wajen ba, tukunna ya buɗe baki yace,"keee". ya faɗa da ɗan ƙarfi, wannan kiran sai ya ƙara tunzurata ta saki ƙara me uban ƙarfi tana dunƙulewa ta kai ƙarshen gadon ta cure wuri guda. "ka kore shi dan zatin Allah, wayyo gashi nan ya hau ƙafata, innalillahi Kaka kizo ki taimka min, Maciji ne ajikina gashi nan yana bina". tunda Fillo take bata taɓa tsorata irin yau ba, hawaye a fuskarta kam tamkar an kunna famfo, acikin blanket ɗin da ta rufe kanta da shi ta ɗan buɗe ido kaɗan sai taga duhu, nan ta ƙara sakin wani uban ƙaran da yafi wancan, ɗiff kuma sai tai shiru kamar ruwa ya cinyeta. wannan shirun nata sai Turaki yay zaton ko tsoronne yasa ta ɗauke wuta, saboda haka kawai ya ɗauke kansa akanta yaci gaba da aikinsa, computer yake kallo amma babu abinda ke haska masa acikin ido sai lokacin da Amir ya riƙe hannunta ya kuma ja hancinta. haka ɗaya kuma yaji ya kasa natsuwa, yaji kamar tsoro na so ya kamasa, yana typing a wayar hannunsa yana kallon kan gadon inda ta dunƙule, a ransa yaji kamar shirun nata ba lafiya ba, in bacci ne takeyi minutes ɗin da tai taking a haka tuni ta mirgina, in kuma tsoronne zuwa yanzu ai ya barta, sai yaji hankalinsa bai kwanta da hakan ba, ya ajiye wayarsa ya miƙe ya isa kan gadon yana dukan ƙafarta dake cikin blanket, shiru shiru bata motsa ba. sai yaji kamar zuciyarsa ta harba a lokaci ɗaya, ta-ke ya haye kan gadon ya yaye blanket ɗin, yana taɓata yaji jikinta ya saki ta tafi luu ta faɗa gefensa, tuni idonsa yayo waje yana furta innalillahi, kamin ya diro akan gadon ya shiga toilet ya ɗebo ruwa. tun bai haye kan gadon ba ya watsa mata ruwan a fuska sai gata ta farka a matuƙar firgice tana ƙwala kiran,"Umminaaaa". ta faɗa tare da fashewa da raunataccen kuka, irin kukan da duk wanda yaji sai ya taɓa zuciyarsa. tsakiyar gadon ya haye ya janyota jikinsa ya kewayeta da hannayensa duka biyun yana me rufe idonsa. wani abu da bai san menene ba yaji ya tsarga tun daga tsakiyar kansa har tsakiyar tafin ƙafarsa, sunan Ummina da ta ambata shi ya daki zuciyarsa, bai taɓa jin tausayinta ba sai ayau. "Ummina". ya ƙara jin sunan ya haska cikin kansa, kenan ta tsorata ainun, tsoron da ya kai gejin da har take ganin babu mai iya cetarta sai Umminta, ta tsorata ta kira sunan Ummin da bata raye akan tazo ta taimaka mata. idonsa ya buɗe ya sauke a tsakiyar kanta, tunawa yake da sanda Kaka ke shaida masa cewar,"marainiya ce Mahaifiyarta ta rasu, mahaifinta ma haka". to amma har yau neman dalilin da yasa Kaka ta ɓoye masa cewar mahaifinta ya rasu yake, sai dai tunaninsa na bashi ko don saboda Hayyo baida kyan hali ne. sai yaji ruwa ya cika idonsa kamar zai yi kuka, bata da Ummi bata da Abba amma tana da shi, tana da shi har abadan abadina, kuma alƙawarinsa ne zai tsaya mata kamar Umminta, zai tsaya mata ba kamar Hayyo da ya sani ba, zai tsaya mata ne kamar nagartaccen uba. sai ya ƙara rungumeta a jikinsa yana jin yanda zuciyarta ke bugawa kamar zata faso ƙirjinta saboda firgicin da ta ke aciki, numfashinta kuma na fita a wani fiffizga, tana ta kiran sunan Ummi a hankali. ya buɗe baki zai yi magana yafi sau uku duk sai yaji yama rasa me zai ce. can kuma a hankali ya kira sunanta dai-dai satin kunnenta,"Fulaniii". ya ambaci sunan kamar me koyon magana, haka kuma amon muryar kamar ba nasa ba. Fillo ta ƙara ƙanƙame shi tana daɗa tattarewa a jikinsa kamar me shirin shigewa jikinsa duka. he took a deep breath hugging her more, yasa hannu yana shafa sumar kanta a hankali ya kasa cewa komai. kusan 3minutes yana jin yanda heart ɗinta ke beating fast, a hankali yace"menene?, me ya tsorata ki?, kiyi shiru babu komai, am with you". ya furta cikin sigar rarrashi yana riƙe da hannunta guda. acikin fizgar numfashi tace,"Maciji ne". yace,"aina?". ta daɗa shigewa jikinsa sosai tace,"a ƙafata, ka kore shi please, gashi nan zai shige jikina". tai maganar duk a ruɗe tana daɗa ƙanƙamesa. ya sauke numfashin yana murza tafin hannunta murya can ƙasa yace,"babu wani maciji fa, buɗe idonki ki gani". ta girgiza kanta dake kan cikinsa tace,"a'a akwai, kai ne ka faɗa". yace,"to aini waya nake yi". ta ƙara girgiza kanta, yayinda Turaki ke rufe idonsa yana jin wani iri a jikinsa. tace,"ai sanda ka faɗa shine sai na jisa a jikina". ba tare da ya buɗe idonsa ba yace,"to ai ya tafi, buɗe idon ki gani babu komai, na kore shi". tace,"to ka kunna light". yace,"a kunne yake". ta buɗe idonta a hankali hasken ɗakin na shigewa cikin idonta, sannan ta zare jikinta daga nasa tana jin yanda gabanta ke faɗuwa har sannan, hannuwanta sai kyarma suke yi. Turaki yay saurin sauka akan gadon ya buɗe ƙofa ya fita, for few minutes sai gashi ya dawo da cup a hannunsa ɗauke da ruwa aciki me sanyi. har sannan Fillo na takure akan gadon waje ɗaya sai raba idanuwa take yi, motsi kaɗan take jira ta kurma ihu, ya ƙaraso gaban gadon fuska babu yabo babu fallasa, ya miƙa mata cup ɗin, ta kallesa ta kalli transparent glass cup ɗin a hankali tace,"dan Allah...". bai barta ta ƙarasa ba yace,"amsa Malama ruwa ne". ta ɗaga hannuwanta da har lokacin kyarma suke yi ta karɓa tasha sannan ta miƙa masa cup ɗin ya ajiye. "sakko ki tafi to". da sauri ta ɗago ta kallesa tace,"inje ina?". yay mata wani kallo kamin yace,"Kaka na can na jiranki". sai tayi narai-narai da idanu tana marairaice fuska ta leƙo da kanta ƙasa wai ta gani ko macijin yana nan har time ɗin. "ɗaure kanki". ta lalubo ɗankwalinta da yay can gefe ta ɗaure tujajjan gashinta. "oya to yafa mayafinki ki sakko ki wuce". tuni hawaye ya sakko mata muryarta na rawa tace,"wallahi ba zan iya sakkowa ba". looking at her yace,"saboda?". tace,"kamar na daina tafiya". wata dariya ta tahowa Turaki amma ya gimtse, babu me ganinta a wannan condition ɗin bai yi dariya ba. ya isa bakin ƙofa ya buɗe ba tare da ya kalleta ba raising his voice up yace,"zo ki fice". ta kallesa ta tuna zancen macijin da yay kawai sai ta fashe da kuka sose, ta shiga roƙonsa tana faɗin,"dan Allah don Annabi ka ƙyaleni anan, ba zan iya tafiya ba ƙafana ya daina aiki". sai kuma ta goge hawayen ta ɗago ta kallesa tace,"to ka ɗauko min wayan Yami a perlon Boɗejo sai na kira Kaka tazo ta ɗaukeni". ya haɗe rai ganin tana kallonsa yace,"Kakan ce zata zo ta ɗauke ki?, rashin imanin naki har ya kai haka?, and you even have the guts to send me right?, yaronki ne ni?". tace,"Allah baka haƙuri, kuma ni ba zan iya tafiya da ƙafata ba a yanzu, tsoro nake ji dan Allah ka barni sai da safe". ya zaro ido waje yace,"a ɗakin nawa?". ta gwame fuska tana jin komai babu daɗi a tare da ita tace,"to ni ya zanyi, idan na sakko fa majicin zai kuma bin ƙafata, dan Allah ka ƙyaleni anan sai ka tafi ɗakin Hammah Khalil". yace,"ke zo ki tafi can ɗin". tai shiru bata ce komai ba, yanda tai laƙwas tai mugun basa tausayi, yace,"to idan na barki anan ni aina zan kwanta?, kuma ai kince babu kyau". tana goge hawayen fuskarta tace,"ai nasan ba zakayi min komai ba. kuma ai ga kujera can sai ka kwanta akai, amma ka kira Kaka ka faɗa mata". ya maida ƙofan ya rufe ya dawo ciki ya wuce kan kujera ya zauna. har sha ɗaya na dare yana kan computer, kuma a lokacin suka yi waya da Bello yake faɗa masa flight ɗin 8 zasu bi gobe in Allah ya kaimu. a wannan lokacin Turaki bai iya amsawa ba har Bello ya gaji da hello hello ya kashe wayar. zuciyarsa kawai yake ji tana bugawa, kamar yanda gabansa ya tsananta faɗuwa, me ke shirin faru da shi?, tunda yake bai taɓa jin irin haka a tare da shi ba. doguwar ajiyar zuciya ya sauke tare da kwanciya akan kujeran, ya rufe idonsa da zummar yin bacci amma sai ya kasa, wannan faɗuwar gaban nasa ya tsananta har ya kai stage ɗin da baya jin zai iya yin bacci sai dai in ɓarawon bacci ya ɗaukesa. tashi yay ya shiga toilet yayo alwala yay nafila raka'a huɗu, ya ɗan jima yana ta adu'a kamin ya tashi ya buɗe closet ya ɗauko pijams nasa ya saka. gaba ɗaya ya manta da wata Fillo a ɗakin sai yanzu da zai hau kan gado, yasa hannu ya dafe goshinsa, me ya sa me shi ne?, agogo ya kalla yaga har 12 tayi babu damar ya tasheta yace zai rakata. ƙaramin tsaki yay ya hau gadon ya kwata ta gefe, ita kuma tana daga tsakiya ta dunƙule rufe da blanket sai baccinta take, baccin da bata san lokacin da ya ɗauketa ba. wasa-wasa dai har ƙarfe ɗaya Turaki na kwance idonsa a lumshe ya kasa bacci, ya miƙe zaune yana kunna deemlight. ya matsa tare da ɗago Fillo dan gyara mata kwanciyarta, amma sai yaji cewar ba hakan ya kamata yay ba, ya rufe ido yana cije fuska sannan ya ɗagota gaba ɗaya ya kwantar da ita a jikinsa. dai-dai nan ya ƙara hasken light yana ƙarewa innocent face ɗinta kallo, hawaye duk ya bushe akan fuskar, ta tsuke fuskan kaman wadda za tai dambe, ga zufa da ta ke haɗawa kaman an watsa mata ruwa. shi jikinsa ba me son sanyi bane dalilin da yasa bai fiya zama da Ac ba kenan, amma haka dole ya sauka yaje ya kunna Ac sannan ya dawo again ya ɗagota zuwa jikinsa ya kwantar, da hannunsa ya dinga goge mata zufar dake kan fuskarta yana jin zuciyarsa na matsewa da zafi zafi. sai yay hugging ɗinta tightly a jikinsa kanta na mannewa a chest ɗinsa, wani irin baƙon al'amari yake ji tare da shi, gefen fuskarsa ya haɗe da tata fuskar, ya kamo hannunta a hankali ya riƙe cikin nasa. ya bayar da sadakinta amma yau sai yake jin like he can't believe cewa wannan jaririyar mallakinsa ce, halalinsa, his wife, his only wife da ya gama tsarin rayuwarsa cewar da mace ɗaya zai rayu, ba tare da sanin cewar itan bace, ba kuma tare da ya taɓa lissafin cewa zai rayu da irinta ba ma, is he dreaming?. sai yaji wani abu me kama da farin ciki a tare da shi, ya ɗago da fuskarsa akan tata yasa hannu ya shafi gefen fuskarta, yana jin kwantaccen sajenta na burge shi, ɗaya hannun kuma na cikin nata hannun yana murzawa. maganganun da ta faɗa masa a mota ɗazu suka haska acikin kansa,_"ni me nayi maka a rayuwa ka tsane ni, ban taɓa cutarka ba haka ban taɓa munafurtarka ba, amma kai kullum burinka ka ƙuntata min, akan me?, saboda ina ƴar talakawa?, ina yi maka biyayya iyakar iyawana matsayinka na wanda nake a aiki a ƙarƙashin iyayensa, mahaifiyarka bata taɓa min kallon banza ba balle har ta nuna min tsana, amma kai ko da yaushe ka ganni burinka bai wuci kasa na zubar da hawaye ba, a wanne dalili?, idan har nayi maka wani laifi ne bisa kuskure da ban sani ba sai ka faɗa min na baka haƙuri, ba wai ka dinga muzguna min ba duk sanda ka ganni. yanzu ka karya min ƙashin hannu ka fasa min leɓe duk saboda me fisabilillah?"._ ya ɗora goshinsa kan nata yake cewa,"ban taɓa jin na tsani wani mutum ba balle kuma ke da kika taimake ni, kuma ta ya zan karya siririn hannun da nake kallo yana burgeni?, wannan bakin kuma ban san zai fashe ba Allah, but am so sorry, shinenan?". maganganun yake yi kamar tana jinsa. and for the very first time he felt her in his blood, he felt as if his life depended on her, ajikinsa yake jin kamar she needed him at this time, kamar ya fasa yin tafiyar just becouse of her, duk wannan faɗuwar gaban da yake ji akan zai yi nisa da ita ne, abinda bai taɓa ji ba tsayin rayuwarsa ko da akan Maama da Zaytuna da baya so yay nesa da su. A hankali ya kai fuskarsa daidai tata yana daɗa ƙarewa ramammar fuskarta kallo, fuskar rigima, fuskar kasada, sai yay murmushi yana kai babban finger nasa kan lips ɗinta yana shafawa. Fillo

Chapter 29 of 73