Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
adu'a sannan suka baro su. kamar yanda sunnah ta koyar Turaki suka yi nafila tare da matarsa, bayan sun idar ya kama kanta yayi adu'a, sannan ya gabatar mata da abinci. ita taci dan shi bai iya cin komai ba, sai bayan da ta kammala ya tashi ya bar ɗakin ya wuce parlo ya zauna, tunda ya fito kuma yake ta tunanin Fillo, Allah kaɗai yasan me yake ji a zuciyarsa. ya jima zaune anan daga baya ya tuna fa cewar aure aka yi masa and amayar tana ɗaki, ko kaɗan baya ƙaunar ganin Ilham, kuma baya jin zai iya haɗa jiki da ita su kwana a shimfiɗa ɗaya, amma kuma ba shi da yanda zai yi, ba shi da wani hope, dole ne zai bi koyarwar addini, zai yi amfani da ilimin da yake da shi dan ganin bai kaucewa addininsa ba kuma bai ƙi yin koyi da sunnar ma'aiki ba a daren farko. babu zancen ya ƙauracewa shimfiɗarta a yau dan zai iya jefata a halaka, tunda addini ma ce yay ka ƙauracewa shimfiɗar mace a sanda tai maka laifi in har kayi wa'azi taƙi dainawa, Maganar kauracewa a shimfida sai idan har ta yi wani laifi ne , kuma kayi wa'azi taƙi dainawa, abinda musulunci yace kenan game da ƙauracewa shimfiɗar mace. dan haka a wannan dare dai Turaki ya mayar da Ilham cikakkiyar mace, ba dan ya so ba, kuma ba dan yana farin ciki ba, kuma ba dan yayi farin ciki ba da samun budurcinta ba. haka kuma rashin sonta bai sa ya zalunceta ba wajen kusantarta, ya tafiyar da ita a hankali ta yanda yasan ba zai ƙuntata mata ba, sai dai hakan ba shi ya hana Ilham kuka sose ba a wannan daren. *Vote, Comment & Share.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _Shafin gaba ɗayansa sadaukarwa ne ga duk wani makarancin littafin *LULLUƁIN BIRI*, ina jin daɗin yanda kuke bibiyar littafin nan, alkhairin Allah ya isa gare ku._ *34* da asuba Turaki na dawowa daga sallan asuba kira na shigowa wayarsa, babu suna ajikin lambar dan haka ya tsaya yana kallonta da son ya fahimceta, ganin ba lambar da ya taɓa sani bace ya ɗaga. yana karawa a kunnensa Gimbiya Aisha ta kwaɗa sallama cikin dodon kunnensa da irin muryar da kana jinta kasan tasha uban kuka. banda koyawa ta addininsa da babu abinda zai sa shi amsawa, dan sarai ya shaida muryarta, kuma ko ba komai taji daɗin amsawar saboda muryarsa nan me daɗi, daɗin da take jin yafi na sarewa tsuma zuciya. daga kan gadon da ta ke tasa tissue ta ƙara goge idonta, with littile courage tace masa,"barka da asuba. ya amarci?". tsabagen mamaki ma bai san me zai ce mata ba, last kira da tayi masa Bello ne ya karɓi wayar ya keta mata rashin mutuncin da ko kare ba zai shinshina ba, kuma in ace Bello gaban fadawa yay hakan abu ne me kamar wuya idan ba'a fille masa kai ba, dan tsananin shock na irin maganganun da ya dinƙa yaɓa mata matsayinta na ƴar Sarki tsayawa tayi kamar statue, and a zaton Turaki ko ace shi ɗaya ya rage namiji a duniya Gimbiya Aisha ba zata ɗauke shi ba saboda abinda Bello yayi mata, amma shine yau take daɗa kiransa?. dama bata tsammaci zai amsa mata ba, saboda haka maganarta kawai taci gaba da yi. "ƙawata Ilham bata faɗa min zancen aurenku ba kwata-kwata, amma na gani a duniya, naga the best couples in the year of 2022, na jima banga perfect match couples irinku ba. duk da kai babu farin ciki a tare da fuskanka but hakan ba shi ya hana fiddo da ainihin kyawun surar da ubangiji yay maka ba, and wannan rashin bayyanar annuri da fara'a na fuskanka ya shaida min cewa auren dole ne akayi maka, kai baka so but ita tana so dan tata fuskar ta bayyana hakan 100%, but duk da haka fa duniya zata judging rashin walwalanka da a haka kake, amma to me da na riga na san fuskan da bai rabo da murmushi na san sam auren ba so yake ba. Anyway i congratulate you dear, Allah ya baku zaman lafiya. sai dai you have to know one thing, ni Aisha Sanusi M2 ni ce zan zama uwar ƴaƴanka, keep this in your mind". Turaki dai tun sanda ta fara maganar ya kunna TV yana sauraron karatun alƙur'anin da aka saka a channel ɗin saudi tv, abubuwan da ta faɗa ma ba komai yaji ba banda na ƙarshen. bai bari ta ƙara cewa komai ba ya datse kiran da ya haddasa masa ciwon kai. ya wurgar da wayar a gefensa yana daɗa jin ransa duk babu daɗi. yana gama bin azkar ɗin da yake sauraro ya jinginar da kansa da kujera, lokacin tuni gari ya waye har 6:30 ta kusa. idonsa a lumshe hoton Fillo nata haska masa, lokacin ne Gimbiya Ilham ta fito daga bedroom tana takowa da ƙyar har ta ƙaraso wajensa, abaya ne yello colour jikinta me bala'in kyau, ta ɗora hular chantly akan kwantacciyar sumar kanta, tayi kyau sose da light makeup ɗin da tayi sai zuba ƙamshi take yi, ta ɗauke hannunsa akan kujerar sannan ta zauna a kusa da shi ta kwantar da kanta a kafaɗarsa, hannun nasa kuma ta ɗora akan cinyarta. muryarta a sanyaye kuma a shagwaɓe tace,"Hammah fever na son kamani, kaina yana ciwo sosai, jikina ma duk ciwo yake yi". ta ƙarasa maganar yana jin saukar hawayen nata a kafaɗarsa, yana jin yanda ɗumin hawayen ya tsarga fatar jikinsa, yana kwatanto shi da zafin hawayen Fillo, wacce ya san a duk inda ta ke yanzu kuka take yi. bai ce da Gimbiya Ilham komai ba har wucewar daƙiƙa ɗaya, lokacin wayar dake kusa da shi tayi ringing, yana kallon new number ne ajiki yaƙi ɗauka. har sau biyu kiran na katsewa tunaninsa duk Gimbiya Aisha ce, sai kira na uku ya shigo da lambar Inna Falmata, kamar ba zai ɗaga ba sai kuma ya ɗaga yana yin sallama. daga can ɓangaren Boɗejo ta amsa sallamar tasa tana ɗorawa da faɗin,"ban kiraka da lambata ba saboda nasan ba ɗagawa zaka yi ba, ashe sabuwar lambar ma baka ɗagawa, sai ka ɗaga ta Falmata da yake kasan ta ƙanwar ubanka ce, ko ba komai halin girmama manyanka na burgeni, duk uban miskilancinka ka san manyanka". yaji kamar ya kashe wayar dan mugun haushinta yake ji, amma sai bai yi hakan ba. a daƙile yace,"ina kwana". tace,"lafiya lau, kun wayi gari lafiya?". yace,"lafiya lau". tace,"yauwa dama zan tambayeka ne ya ka sami Ilham ɗin?". ta faɗa tana yin ƙasa da murya. yace,"lafiya lau, ba ki da lambarta ne?". tace,"ya salam, baka gane nufina ba ne?, ita yarinyar a ya ka sameta nake nufi?". ya ƙara cewa,"lafiya lau, ba ki da lambarta ne?". Boɗejo taji kamar ta kai masa duka ta cikin wayar, dan in kusa gareta yake ma ba abinda zai hana faruwar hakan. cike da takaici ta ƙara yin ƙasa da murya tana faɗar,"ya zanyi tunda kai farin shiga ne, sai nayi opalli-opalli tukunna zaka gane. dama haka zancen ya zancen budurcinta?, ya ka same shi?, fatan dai ta kawo shi lafiya?". da ƙosawa yace,"gata ki tambayeta". ya faɗa yana direwa Ilham wayar akan cinyarta. ta buɗe idonta da ke rufe bacci na so ya ɗauketa, ta kalla wayar da call ke tafiya, da sauri ta ɗau wayar ta saka a kunne tana cewa,"Inna ina yini". Boɗejo tace,"Ilham ni ce, lafiya naji muryarka haka, kuka kika yi?, ko ba kya jin daɗi?, mene matsalar faɗa min, Turaki ne ya gaya miki magana babu daɗi?". Ilham tace,"a'a". ta faɗa tana sakin sabon kukan shagwaɓa. hankalin Boɗejo a tashe tace,"ni bana son kuka, ki buɗe baki ki min bayani, ko sai na zo?". cikin muryar kuka Ilham tace,"Boɗejo jikina duk ciwo yake min, zazzaɓi ne ajikina. kaina kamar zai cire, kizo dan Allah". Boɗejo tace,"bawa mara mutuncin wayar". Ilham ta kai hannu ta ɗora masa wayar a kunne, da masifa Boɗejo tace,"daga mugu sai kai Turaki, yanzu yarinyar babu lafiya shine dan tsabar zalunci baka wuce ka kaita asibiti ba?, haka kaga ubanka na yiwa Madina?. gaskiya ban yafe ba sai Allah yay mana sakayya tsakanina da kai. kuma dan uwarka Madina ka amsa min tambayar da nayi maka tun ɗazu, in kuma sai nazo har gidan kaga tsayina inji". Turaki yay guntun tsaki yace,"ni dai karki ƙara zagar min uwa. amsar tambayarki kuma ta kawo shikenan, karki ƙara kirana ki kira wayarta idan kina son magana da ita, ni ban haɗa komai da damuwa ba so ki barni inji da abinda ya damen". bai jira cewarta ba ya kashe wayar yana miƙewa ya bar wajen, Ilham tabi bayansa da kallo tana jin hawaye na sakko mata. yanzu shikenan irin wannan zaman zasu dinƙa yi da shi?, ana aure dan farin ciki amma tun ba'aje ko ina ba ta fara fuskantar ƙalubale, tana ji ana faɗar tun daga daren farko mace ke fara samun kula da tarairaya daga wajen mijinta amma ita nothing like that, ya sameta a virgin ɗinta amma kamar wadda ta zo masa a fafe, sai faman haɗe rai da kumbura yake ba, duk uban kukan da ta sha daren jiya sannu wannan bata samu ba, balle taimako daga garesa. and cikin ƙarfin hali ta gyara kanta duk da zafi da raɗaɗin da take ji amma hakan bai sa yaji tausayinta ba a sanda ta tabbatar da yaji uban zafin dake jikinta sanda take kwantar da kanta jikinsa, yanzu shikenan ita wannan soyayyar da take ta kwaɗayi a gidan aure ba zata samu ba kenan?, dama haka illar auren wanda baya sonka yake?. sai kawai ta kifa kanta a hannun kujerar ta fashe da kuka mai ban tausayi. daga can masarauta kuwa tuni ko'ina ya ɗauka da batun Gimbiya Ilham ta kai budurcinta gidan miji, kowa kuma sai ya shiga saka kyautukansa acikin wata ƙatuwar kwalla da ke dire a ƙofar turakar Fulani Azima, guɗa kawai kake ji na tashi da tafi ana son barka ana yabon Fulani Azima da tarbiyar da ta bayar. ƙarfe goma sai ga manyan motoci ƴan ubansu na jiniya a ƙofar gidan Turaki, mota guda biyu ɗauke da hadimai mata, suka fito suka isa inda wata baƙar mota ta ke cike da sassarfa. acikin motar ne aka shiga fito da manya manya coolers na abinci, wasu coolers ɗin abinci ne cikinsu irin na gidan saurata, sai wasu coolers ɗin kuma uban kayan gara ne kamar hauka. dan Gimbiya Ilham tsab zata shekara da su indai ba cin abinci aka dinƙa musu ba. haka suka dinƙa shiga da coolers ɗin suna fitowa suna kuma ɗibar wasu, sai da suka gama shigar da su tas sannan kuma sai ga ma'aikatan kamfanin Arewa culture Decoration suna shigowa ɗauke da kayan aiki a hannunsu suna nufar can baya inda ƙaton haraba yake wajen filoti guda, a wajen harda swimming pool irin tafkeken nan. suka baje kayan aikinsu kuma cikin ƙanƙanen lokaci suka shiga gyara wajen da decoration irin na gidan sarauta bango zuwa bango, haka ƙasan wajen ma duk an malale shi da uban carpet me taushi an baza uban tumtum sai ka rantse ko fadar mai martaba ake haɗawa. wata ƙawar Fulani Azima na zuwa taga irin yacca decoration ɗin ya haɗu sai tayi tsaye ta kasa motsi ta saki laɓɓa tana bin wajen da kallo cike da burgewa. "wow, la'ila ha'illahu, dan Allah aina aka samo waɗan nan masu iya aikin. kan uba ke kiga wuri kamar dama can a haka aka ƙera shi, na rantse da Allah wanda bai sani ba yazo wajen nan sai yace gidan sarauta ya shiga". sai tayi saurin zaro waya a jaka tana miƙawa ɗaya daga cikin ma'aikatan tana cewa,"ungo maza lafta min lambarku a wayata, ina zanyi saken wannan azababben decoration ɗin da bikin ƴata, habawaa ai dole jama'a suzo suyi kallo na kece raini ma, ta yanda gobe ba zasu ƙara ɗaukan gajigarin masu decoration na musu aikin wofi suna asarar kuɗi ba". ma'aikacin na murmushi yace,"Hajajju bari na karanto miki kawai". Hajja Balkisu tace,"yi da sauri, ai ni duk a tsume nake. yanda kasan in ɗauke wajen nan in tafi da shi". Ma'aikacin still da murmushi fuskarsa ya shiga karanto mata lambar yana rubutawa,"08067261323". tace,"me zan saka a sunan?". yace,"kawai rubuta Arewa Culture Decoration". daga cikin gida kuwa Gimbiya Ilham na zauna tana ta bin Hadiman dake kaiwa da komowa wajen kimtsa kayayyankin da suka shigo da shi. sai taji suna tafiya da zaman kaɗaicin da ta ke ciki, dan Turaki tuni ya fice daga gidan ko sallama ɓata haɗa su ba. can kuma sai taji parlon ya karaɗe da wata uwar guɗa kamar gidan zai tsage, ta rumtse idonta for the first time da hawayen farin ciki ya sakko mata tun kawota, ko ba komai tasan duk wannan abin da akeyi na murnar ta kai budurcinta gidan miji ne. Boɗejo ta fito daga bedroom ɗin da suka kwana riƙe da farin bedsheet ana haskawa mutane ɓacin da yay dan su shaida, ta bawa Jakadiya Hanne tana barin wajen da rawa. ta isa wurin Ilham ta rugumeta tana ƙara sakin wata uwar guɗa ta musamman, sai kuma kowa yayo kanta ana cewa,"barka Gimbiya, sannu Gimbiya, sannu sannu, Allah ya huce gajiya, ubangiji ya kawo albarkar ɗaki, sannu. Fulani Azima na cewa agaisheki, a gaisheki, ayi miki gaisuwa irin gaisuwar da babu mahaluƙin da ya taɓa samunta". daga nan Boɗejo da Inna Falmata suka kamata sukai cikin ɗaki da ita. bayan an yiwa Gimbiya Ilham gashin ruwan ɗumi mai kyau, sannan aka haɗa ruwan lalle da turare Boɗejo tayi mata wanka da shi, aka fito da ita sai zuba masifaffan ƙamshi take yi. duk wannan hidima dai da akeyi Boɗejo ƙwafa kawai take jerawa tana tunanin irin rashin mutumcin da zata yiwa Turaki tunda yasa ƙafa ya bar ɗanyan amarya ita ɗaya kamar mayya. kwalliya aka yiwa Ilham ta gani ta faɗa, tayi azaban kyau, aka fito da ita a lulluɓe da alkyabba fara tas me adon red ajiki, babu ta inda ake ganinta harta ƙafarta kuwa dake sanye cikin wani half conver na sarauta, akan cushion na babban parlon gidan aka zaunar da ita tayi zama irin na masu mulki, Mutum uku daga dangin mahaifiyarta suka zo suka ɗaga hular alkyabbar nata ana fasheta da turare me bala'in ƙamshin gaske, suna yi ana tafi ana busa shantu ana rera mata waƙa na son barka da kawo budurcinta lafiya lafiya, after sun gama bajakolin fesa turaren sai wasu bayi guda biyu suka zauna kusa da ita gefe da gefe suna mammatsa mata ƙafafunta. acan ɗaya ɓangaren kuwa Turaki na fita gida ya wuce, kaitsaye part ɗin Baffa ya nufa don zatonsa ko suna can suna breakfast, sai dai ko da yaje duk basa can Baffan ma bai tashi ba, dan haka ya taho side ɗin Maama, time duk sun zauna zasu yi break fast, kallo ɗaya Maama tayi masa tasan baici abinci ba, hakan yasa ta miƙe ta shiga kitchen ta dama masa kunun gyaɗa shap shap ta soya irish, duk da cewan akwai soyayyan irish ɗin amma tasan ba zai ci ba. sai after break fast ɗin ne Maama ta zaunar da Turaki a ɗaki tai masa nasiha sosai akan yanda zai zauna da matar da ba sonta yake ba, ta nusar da shi in har yay haƙuri ya kyautata mata to tabbas zai ga ribar hakan, tunda har yayi biyayya Allah ba zai barsa haka ba. tace,"Me Babban suna ko ni zan iya zaɓa maka Ilham matsayin wacce zaka aura, saboda yarinya ce me hankali da tarbiyya, ita kaɗai ta fita zakka acikin yaran Mai Martaba, to nasan dan ka aureta ba faɗuwa kayi ba ka sami uwar ƴaƴa ta gari. but ni ta yanda akazo da lamarin aurenne ya ɓata min rai, shiyasa duk naji na tsani auren wallahi, to amma ya zamu yi tunda ubangiji ya shirya faruwan hakan tuni. adu'ata Allah ya baku zaman lafiya ya kauda fitina tsakaninku, ya kuma baku ikon fahimtar junanku ta yanda ɗaya ba zai cuci ɗaya ba". sannan ta ƙara cewa,"ka dai ji me nace maka ko?". ya ɗaga kansa kawai tabbacin yaji, dan bai jin zai iya magana. suna zaune da ita suna ta hira kiran Boɗejo ya shigo wayarsa, yana kallo yay banza da kiran, da ya ƙara shigowa ya kashe wayan gaba ɗaya yana jan tsaki tare da kwanciya kan gadon Maama. ita dai tana kallonsa amma ko kusa bata yi magana ba, saboda tasan irin ɗacin da yake ji a zuciyarsa, and beside ta lura kamar yana da wata damuwa acan ƙasan ransa, sai dai bai faɗa mata amma tasan duk runtsi zata sa ni. miƙewar Maama kenan zata shiga toilet taji an banko ƙofar ɗakin, kallon wajen da zatai taga Boɗejo a fusace ta shigo, ta bi Turaki dake gadon idonsa a rufe ta ƙarasa wajensa tana ta zazzaga masifa kamar zata bankawa ɗakin wuta. Hajiya Madina kam dama tana ganin itace ta shige toilet ta rufe ƙofa, haushin duk wanda ke da sanya hannu akan lamarin aurenan take. bata fito a toilet ɗin ba sai da taji Boɗejon ta fita, ta fito a ranta tana jin haushin irin zagin da Boɗejo ta dinƙa mata ita da Turaki, cikin ranta tana jin ina ma ace akwai ƙasar da babu wanda ya sa ni sai ita, da ba abinda zai hanata ɗauke Turaki a gobe ta kaishi can yaje ya huta na kwana biyu ko zuciyarsa tayi sanyi. acan gidan Turaki dai sabon biki ne ya tashi, dan yana zuwa ya tarar da danginsu da dangin Fulani Azima an cika gidan sai tashin busar algaita ta ko'ina, ta dole Boɗejo ta shirya shi har da cewa wallahi idan baiyi wasa ba sai tayi masa wankan da kanta. ya fito cikin dakakkiyar shadda fara da ta saje da alkyabbar Gimbiya Ilham, yayi azababben kyau har yafi na ranar ɗaurin aurensa. kamar dai wancan kwanakin haka yau fuskarsa duk babu walwala har akai taron aka gama, sai da Boɗejo ta tabbatar sun gama cika al'adarsu sannan hankalinta ya kwanta. jama'a sunci sun sha an bar arziƙin abinci a inda yake, bayan kammalawa Inna Falmata ita tayi jawabin godiya ga duk waɗanda suka zo da kuma tarin adu'oi wa ma'auratan, daga nan kuma sai aka shiga ɗaukar hutuna kamar hauka, kowa burinsa bai wuci yay short vedio yana hasko gidan ba ta yanda duniya zata gani ta shaida gidan arziƙi. ƙarfe biyar na yamma Turaki ya wuce police station kan sabon report da ya shigar tun a ranar da ya dawo, suka kuma tabbatar masa da cewar suna kan yin bincikensu, bai dawo gida ba sai 6 kuma ba gidansa ya wuce ba wurin Maama ya wuce, inda yaje ta tarar ta wuce wajen Kaka anzo ance tana can ta suma. *Kidnappers.* ga duk wanda ya san Fillo a yanzu zai iya rantsewa ba ita bace, saboda yanda ta fita a hayyacinta, abinka da mara ƙiba, kallo ɗaya zaka yi mata ka zubar mata da hawaye saboda yanda ta fige, idanuwan nan sun ƙara ɓurmawa ciki. zaune take akan ƙasan simitin wajen an ɗaure ƙafafunta da igiya, haka ma hannayenta an ɗaure su ta baya, yanda fuskarta tayi jawur da yanda jini ke fita daga bakinta kaɗai zasu shaida maka irin azababben dukan da ta sha a iyakar yau. ƙaton mutumin dake gabanta ya ƙara buga mata bindigar hannunsa a fuskarta, take bakinta ya ƙara fashewa kanta ya lanƙwashe. cikin burkitacciyar hausarsa yace,"muddin baka daina yi mana gardama ba, to wuya yanzu ka fara shanta. in bakayi wasa ba sai mun kaseka ayau ɗin nan". da ƙyar Fillo ta miƙar da wuyanta ta ɗago tana kallonsa da idanonta guda ɗaya da bata iya gani sosai da shi. kallonsa take yi tana hango ranar da suka tsareta suka ce ta bayar da lambar wanda za'a kira, lambar Amir kaɗai ta haddace a duniyarta kuma bata tunanin zata iya bayar da shi, saboda tsoronta kar ya cutu da jin halin da take ciki. sai da tayi da gaske tukunna ta iya haɗa lambar Yami ta bayar dan ba wani haddaceta tayi sosai ba, kuma sai da aka gwada lambar kusan sau uku duk ba correct ba sai ana huɗun Allah ya taimaketa kiran na shiga taji muryar Yami a sanda aka ɗaga, da wannan ta samu ta kuɓuta daga wahalar da suke bata. kuma tun a ranar da aka kawo kuɗin suka ƙirga suka ga harda ƙarin dubu ɗari biyar akai amma hakan bai yi musu ba suka ce fiye da wannan suke so, idan bata manta ba tana jin shi ƙaton na cewa,"wato iyaye naka suna sonka sose, tunda har gashi suna ƙara mana kuɗi akan wanda muka nema. wannan ya nuna mana sewan sun tara kudi da yawa, don haka ba zamu sake ka ba sai an cika mana kudi ya zama miliion goma". tunda taji ance ƙarin dubu ɗari biyar tasan Amir ne kaɗai zai yi hakan duk da bata san ta yanda akayi su Kaka ma suka sami wannan kuɗin ba. dan a ranar da suka kira waya aka sawa su Kaka muryarta tana cewa azo a ceceta, the first abinda Kaka ta faɗa mata shine,"ki daina kuka Fillo, kiyi ta adu'a kinji za ki kuɓuta, banda ƙarfin da zan kawo musu amma Amir zai zo ya tafi dake kinji". ta sa ni a irin son da Amir yake mata zai ƙara fiye da haka ma in har ace yana da shi, kuma tun a ranar ta ƙara jin Amir ya sami wani waje na daban a tare da ita, in ace da sonsa ya ragu da 85%, to a yanzu wannan son nasa zata ce ya ƙaru da morethan 1000%, saboda shi ɗin mai sonta ne kuma me ƙaunarta, dan haka a duniya bata da wani wanda ya fishi. dukan cikinta da akayi da ƙafa shi ya dawo da ita daga duniyar tunani. ta saki kukan da bata jin zata iya riƙe shi, ta shiga ambaton Allah a fili da kuma zuciyarta. ta buɗe bakinta wanda leɓenta suka riga suka zama ganda tace,"ku kasheni kawai, dan Allah ku kasheni ko na samu na huta. kunce sai an ƙara muku kuɗi an ƙara still kuna faɗin bai isheku ba, na faɗa muku bamu da wani gata sai Allah, dan Allah dan Annabi ku kasheni kawai". ƙaton ya jawo jakar kuɗi na biyun da Amir ya kuma kawowa naira miliyan biyu, sai dai basa tunanin da naira miliyan bakwai da rabi kacal zasu iya sakin yarinyar, sun jima suna kidnapping su yanke kuɗaɗe masu uban kauri, amma basu san me yasa akan wannan yarinyar ba suka buƙaci kuɗi kaɗan. cike da rashin imaninsa yasa ƙafa ya ta-ke ƙafarta yace,"ka san menene yaro?, ko iyaka motan gidanku da muka ƙwamusoka daga wajen da muka ganka ranar idan siyar da shi za'ai ya haura sama da miliyan asirin, saboda haka ku daina ce mana baku da shi. for the last time zamu kira waya ka faɗa a gida kace aciko mana miliyan uku, ana cikawa mu kuma munyi alƙawarin zamu sake ka". cikin tsananin azaba da wahalar da take ji tace,"ni Kakata kawai nake da ita a duniya, bayan ita banda kowa. wannan motar ba tamu bace ta gidan da nake aiki ce, dan Allah ku taimaka min, na tabbata Kakata duka gadonmu na wurin mahaifiyarmu ta siyar aka sami wannan kuɗin, a yanzu kuwa na san babu wani abu da zata ƙara ɗagawa ta siyar, kuyi min rai dan Allah". shirunta yay dai² da shigowar wani mutum dogo kamar sanda, ya ƙaraso gaban ƙaton mutumin yana miƙa masa waya yana cewa,"oga ka duba news ka gani". Ogan ya shiga kallon shafin facebook da yake nuna masa yana karanta bayanan dake jiki na ɓatan Fillo ƴar aiki a gidan Judge Alƙali Dikko, da kuma hotonta a ƙasa sanye da hijab. sai ya bushe da dariya yana sa ƙafa yayi fatali da kujerar dake kusa da shi, ya mayarwa da mutumin wayar yana faɗin,"ashe kamu muka yi me soka bamu sani ba, har muna ɓata lokacinmu wurin amsar 5million only". sai yay shiru yana ƙara sakin dariya yace,"Hardo kaje ka nema mana numban waya na gidan Alƙali, wannan yaro yana da taurin kan jaraba ba zai bamu wani number ba...kayi sauri ka kawo min in the next few minutes, yanzu ba miliyan 10 muke nema ba, miliyan 200 zamu karɓa". ya faɗa yana miƙewa daga kan kujerar yana ƙara sakin dariya cike da nishaɗi. sannan ya ƙara kallon ɗaya acikin

Chapter 35 of 73