Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
babu daɗi, bai san ya zai kimanta mata abinda yake ji ba, shi ta barsa yaje yaga kawai halin da Nuratu take sai ya fito ya kaita, hakan ne kaɗai zai basa natsuwar yin driving ɗin da take so, to amma yasan ko me za'ai ba zata yarda ba, kamar yanda ta faɗa ne ko mutuwa Nuratu zata yi, sannan kuma uwarsa ce, jayayya da ita ko bijire mata ya ɗaukowa kansa hanya ta taɓewa ne. dabara ta faɗo masa yace,"Ammi na bar motata a hospital". a fusace tace,"ko da motarka ma kazo ni ba zan shiga cikinta ba, ina da tawa a ita zaka kaini. motarka ai sai Falmata amma ba ni ba, kuma ni dai na faɗa maka ƙafarka ka ɗaga kayi cikin gida to ban yafe ba, idan kaga dama kai ta tsaiwa muna dragging muna ɓatawa junanmu lokaci". Yusuf ya kulle idonsa ya fesar da iska me zafi daga bakinsa, ya katse wayar yana kallon side ɗin Inna Wuro ya koma da baya ya nufa wurin motar. a cikin motar ya sameta a zaune, ya buɗe driver seat ya shiga, bai juya ya kalla back seat inda take ba yace,"Ammi ina yini, kuma ina zan kai ki?". Ammi tace,"gaisuwarka dai ka riƙe, inda zaka kaini kuma kowanne store ya kama, wurin dai da zan samu abinda na fita saya, dawowarmu kuma sai Allah yayi". tana yin shiru yay ma motar key, yay reverse har tayar motar na amsawa, wanda inda ace wajen da ƙasa sai ƙura ta tashi. suna fitowa daga cikin gidan kamar ance ta ɗago kai daga kallon wayarta taga motarsa. tace,"kace a hospital ka bar motar?". sai daya kulle ido sannan ya iya ƙaryar cewa,"dama nace da Mujahid ya kawo min ne". tai murmushi kawai tare da girgiza kai bata ce komai ba. store wurin huɗu suka je, ba dan tana rasa abunda zata saya a kowanne ba, sai dan kawai ta ɓata masa lokaci, dalilin da yasa ta dinƙa gutsira sayayyar kenan, har yamma tukunna suka ɗauko hanya. sai da suka shigo cikin anguwarsu sannan ta ƙara ce masa,"nace maka gida zamu wuce ne direct?, to kai reverse ka kaini gidan Kawun ka". shirunta ya haɗe ta kiran daya shigo a wayarsa, ya kalla sunan dake yawo akan screen ɗin, ganin sunan Inna Wuro ya kulle idonsa da yake jin yana masa zafi, zuciyarsa ta matse hankalinsa na ƙara tashi. minti goma sha biyar suka ɗauka kamin su iso cikin unguwar gargajiyan, da ƙyar motarsa ta shiga cikin layin, daga bayan gidan yay parking motar. yana kallon Ammi ta mirrow ta buɗe motar ta fita ba tare da tace masa ƙala ba, yaji kamar ya fashe da kuka. sai da ta kai ƙofar gidan tukunna ta sami yaro ta nuna masa mota tace yace da mai motar ya miƙo mata jakarta. a lokacin hannu kawai Yusuf ke jira ya ɗora akansa ya saki kuka, ya san da biyu ta manta jakar. jakar kawai ya bata ya juya ya koma mota, Yusuf tun yana kallon wucewar sakanni har ya koma yana kallon adadin mintuna, minti 1 zuwa 5 suka wuce har aka tafi goma Ammi bata fito ba, lokacin ne kuma ya ɗauko wayarsa da niyyar kiranta sai yaji anyi knocking glass, yana ɗaga kai yaga Kawunsu wanda yake Yaya ne a wurin Ammi me suna Malam Mudi. cikin sauri ya buɗe motar ya fito ya duƙa yana gaida Kawun kansa a ƙasa. "Yusuf gidan baƙonka ne daka ƙi shiga ka zauna a mota?". Yusuf yasa hannu ya sosa ƙeyarsa yana neman abinda zai ce, kan yay magana Kawun ya ƙara cewa,"ai Zainab ɗin ke cewa kai ka kawota kana waje, shiru shiru baka shigo ba shine nace to bari nazo naji ko munyi maka wani laifinne". Yusuf yace,"a'a wallahi Kawu babu komai, dama na ɗan tsaya ne muna waya da abokin aikina, shiyasa ban shiga ba amma dama yanzu nake niyya". tare suka jera suka nufa gidan, suna tafe suna tattaunawa akan wasu batutuwa har suka shiga gidan, da yake Malam Mudi mutum ne me sakin fuska. acikin gidan Umma Ladi taitawa Yusuf tsiya tana cewa ko dai sirikinta zai zama ne bata sani ba da ya maƙale a waje yaƙi shigowa, shi dai murmushi kawai yake har suka fito. da suka koma gida shi ya kwashi siyayyar da Ammi tayi ya kai part nata, sannan ya fito ya wuce na Inna Wuro, yana tafe yana duba agogo, daga lokacin da ta kirasa zuwa yanzu awa biyu kenan. hularsa ya ɗaga ya sharce gumin daya haɗo masa duk da cewar ba zafi akeyi ba, amma halin da yake ciki na rashin sanin a wanne hali Nuratu ke ciki yasa shi haɗa zufa. babu kowa a parlon lokacin da ya shiga, tsaye yayi kawai yana kallon trolly ɗin kayan Nuratu dake tsakiyar parlon a ajiye. mamakinsa ya tsaya akan Inna Wuro dake janyo ƙaramar trolley tana fitowa daga cikin ɗakinta tana maganganun ƙasa-ƙasa, har ta ƙaraso gabansa bai iya ɗauke idonsa daga kanta ba, amsar tambayar dake ransa kawai yake so ya samu tun kamin yayita. bata lura da shi ba saboda sababin da take tayi har sai da ta zo gabansa, shima warin asibitin da taji ne yasa tasan da tsayuwarsa a wurin. ta ɗago tai masa kallo ɗaya ta ɗauke kai. "ashe kazo, nai zaton ai ko ka zama tarihi da nake ta danna maka kira kana ƙin ɗauka. baka san ni ba wata tsiyar zance kayi min ba, idan ka manta na tuna maka ɗana me wannan ƙaton gidan ya tara abinda kai baka da shi, dan haka nafi ƙarfin roƙo a wurinka Yusuf". tasa ƙafa ta tura masa duka trollys ɗin gabansa tana cewa,"gasu nan, dama niyya nake na fita da su na ajiye su daga bakin ƙofa sai kuma Allah ya kawoka ka rage min aiki". Yusuf dai kallonta kawai yake yi, sai da tai shiru sannan yace,"kiran da kika min na mene?". jin yanda yay maganar ta ɗago ido ta kallesa ta taɓe baki sannan tace,"naga duk ka firgice kamar wanda ya tsarewa zaki. to ni dana kiraka ce ka ke me ya faru?, kasan dai haihuwa ba yanzu ba. gani nai nayi na Allah nayi na Annabi, to na gaji da rainon cikin da ba ni nayi ba, shi yasa na doka maka kira kazo kai awon gaba da ƙazamiyar matarka, ba zan iya da tofe-tofen yawu da amai ba, duk ta lalata min wuri da ƙarni. kai baka ji ba daka shigo?, ko da yake yanzu yarinyar can me aikin babarka tasa omo da turaren ƙamshi ta goge min ko'ina, wallahi da ba zaka iya shigowa ba daga bakin ƙofa zaka tsaya, amma matarka ai bata haɗu ba yasin, ciki sai kace akanki aka fara, sakan ɗaya biyu sai a tofar da yawu, can kuma sai dai kaji ana kyalayo amai". ta rufe ido ta dafe goshi tace,"wuwuwu abin dai ba kyan gani da kwatance". ran Yusuf idan yayi dubu ya ɓaci, idan da tasan muhimmancin aikin da tasa ya baro da bata masa haka ba. yaji kamar ya bige ta dan takaici, ya matsar da trolly ɗin gefe ya shige ɗakinta, yana shiga ya fito yana tambayarta ina Nuratun?. "yo ni ina nasan ma inda take, wannan dai fitsararriyar ƙanwar taka ita tazo ta ɗauketa bayan ta gama karta min rashin kunya...yo tsakani da Allah ina gani zan cutu kuma sai naƙi yin magana?, ƙarnin yawu da amai ne fa ke neman halaka ni. banda ma dai halin butulci irin na ɗan adam ina wani zai kallen ya gurza min baƙar magana, to akan Nuratu dai idan ba'a gode min ba ba za'a tsine min ba sai dai idan kuma son zuciya, wane zai iya ɗawainiyar da nai da ita, ce nake ita kanta ƙanwar Uwartata da aka kawowa ita guduwa tai ta barta ta wani fake da ta tafi umarah. haka nake hana idona bacci saboda yarinyar nan, tana bacci ina gefenta ina tofa mata duk kalar adu'ar da ta zo bakina gudun kar a haifi ɗa mara ƙafa, tunda naga alamar tana da mutanen ɓoye, Allah na tuba mene jinnu basa iya aikatawa sai dai Allah yay mana katangar ƙarfe da su kawai...ita dai waccen ƙanwar taka in kaje ka faɗa mata ɗibar albarkar da tai min taje dan kanta ni ba ramawa zanyi ba, kuma ba zanyi Allah ya isa ba tunda dai ina da hankali". Yusuf ya ɗauke idonsa daga kanta yaja trollys ɗin zai fice daga parlon kukan Inna Wuro ya dakatar da shi. ya juya yana kallonta da mamaki, kuka takeyi sosai tana faɗin,"wallahi karka daɗa karka raga ni ko zagin matarka banyi ba, kawai na gaji da ƙazantar ne na tofe-tofen yawu da amai shi yasa nace ta bar min wuri, kuma inda ace ta ban haƙuri ai zan haƙura, amma da yake butulu ce sai dai ta kalleni ta fashe da kuka duk dan wani ya ganta taja min masifa, nace to ta fita ta zauna daga bakin ƙofa idan kazo ba sai ka shigo min ciki ba tafiya kawai zaku yi, ashe taji haushi sai ta faki idona ta dannawa ƴar dabar gidan nan waya, ko minti ba'a ƙara ba sai gata kamar kububuwa ta faɗo parlon nan tana ta huci, da ace ban matsa baya ba da yanzu akan gawata kake tsaye, baka ga irin ɗiban albarkar da Yusra tai min ba, karka ji irin zagin da ta dinƙa surfa min Yusuf, harda kalar zagin da ban taɓa ji ba tunda uwata ta haifeni, wai akan matar Yayanta ba abinda ba zata iya ba, da zasu fita fa sai da ta bangaje ni, nai galantoyi zan kife a ƙasa bangon nan ya riƙeni, yo ka faɗa min ina zan manta da wannan cin mutuncin?, har da cewa fa idan an haifi yaron nan ba zan ɗauke shi ba sai dai kallo daga nesa, to dama ita ta haife shi?, matsalar ban iya haɗa husuma ba ne dana kai ƙararta gaban Amadu wallahi, amma duk da haka ka sanar mata inuwarta na ƙara gani a ɓangarena sai na buga mata duk abinda na raruma". Yusuf bai ce mata komai ba ya fice ya barta tana kukanta. sai da ƙyar Aliyu da ya shigo ya iya lallashinta tai shiru, amma har sannan bata bar maimaita maganar ba. Nuratu na kwance akan gado Yusra ta shigo ɗakin nasu, ta ajiye bowl ɗin dake hannunta akan dressing mirrow sannan ta isa gadon ta miƙar da Nuratu wadda duk jikinta yay weak, pillow ta saka mata ta jingina da shi, tukunna ta koma ta ɗauko bowl ɗin dake ɗauke da fruite salad da ta haɗa mata. "Anty please ki daure ki shanye wannan duka, kinga dai cikinki babu komai". Yusrah ta faɗa tana me cike da tausayinta. Nuratu ta karɓa tasa spoon ta fara sha, sai da ta kusa shanyewa tukunna ta ajiye, tunda ta tashi yau babu abinda ta iya ci, duk abinda tasa a baki baya zuwa cikinta yake dawowa, tayi amai yafi sau biyar, shi yasa Inna Wuro tace yau ba zata iya ba. Yusrah na waya da saurayinta da ta kalla ta ajiye bowl ɗin ta taso. "ina zuwa i will call you letter". ta faɗa tana aje wayar a gefen gadon. "Anty Nuratu ai babu abinda kika sha, gaskiya ni dai ki daure ki ƙarasa shanyewa". Nuratu kamar za tai kuka tace,"na ƙoshi Yusra". haka dai har sai da Yusra tasa ta ƙarasa shanyewa, a lokacinne Yusuf ya shigo, tana ganinsa kuma tasa kukan shagwaɓa, kamar wanda aka zarewa laka ya ƙaraso ya zauna a bakin gadon. Yusra ta gaida shi ya amsa murya a ƙasa, ya janyo Nuratu jikinsa yana shafa kanta yana lallashinta. ba tare da ya kalli Yusra ba wace,"what did she eat?". Yusra tace,"yanzu ta gama shan fruite salad". ya sake cewa,"ki gasa kaza ki kawon yanzu". "tom Yaya". ta faɗa tana fita daga ɗakin. Nuratu kuka ta ƙara sawa tana faɗa masa,"Excellency ni na gaji da wannan cikin, plss remove it for me". bai iya cewa komai ba ya rufe idonsa ya ɗora haɓarsa akan gashinta, hannunsa na kan cikinta yake bata haƙuri. ji yake da damar da zai mayar da cikin jikinsa da ya maida, tunda ta sami cikin nan bata huta ba, kullum a cikin wahalar laulayi take, ga shi yanzu aka fara ba'aje ko'ina ba, cikin ko 4 months bai kai ba. "ki daina kukan nan please". ta ƙara narkewa a jikinsa tace,"ka kira min Umma". ya ɗauko wayarsa a aljihu ya kira Umman ta vedio call, idon Nuratu na kan wayar tana jiran ɗagawarta. daga can ɓangaren Umma na kitchen lokacin ta ɗaga kiran, kallo ɗaya taima Nuratu ta hangi tarin kukan da idonta yasha ayau. da tsananin tausayinta tace,"what's wrong Nuratu?". "Umma ki dawo dan Allah, ki dawo ki kaini a cire min wannan cikin bana sonsa, na haƙura da samun Bilal ɗin". Umma ta sauke numfashi tace,"a'a Nuratu ba'a faɗar haka, babbar ni'ima ce fa Allah yay miki da ya azurtaki da samun cikin nan, wasu na nan basu samu ba suna cikin damuwa. adu'a kawai za ki Allah ya yaye miki wahalar laulayi ya kuma sa ki haihu lafiya. kar na kuma jin kince ba kya son cikin nan kinji ko". Nuratu ta ɗaga mata kai alamar taji, tana kwance a jikin Yusuf har lokacin, ko kunyar Umman basa ji. Umma ta kalla Yusuf wanda hankalinsa baya wajen, ta ƙara cewa. "am coming back next tomorrow insha'Allah, zuwa yamma in Allah ya yarda na dawo gida, ki daina kukan ya isa haka...irin wannan wahalar Mamanki tasha fama da ita lokacin da tana da cikinki, kamar ba zata rai ba, me ciki dama sai tai haƙuri ta jure". sun jima suna wayar Umma na lallashinta da kwantar mata da hankali kafin su yi sallama. sai magriba Yusuf ya fito daga ɗakin su Yusra shi da matarsa, har lokacin Ammi bata san cewar suna ɓangarenta ba. yasa Yusra ta kai kayan Nuratu motarsa, ba zai iya barinta a gidan ba tunda Umma bata nan, Inna Wuro kuma ta gaji, Ammi kuma ba sauraronta zatai ba, sisters nasa kuma kowacce na busy da study nata ba zai yiwu ya takura musu ba. so is better ya tafi da ita can hotel ɗin da yake kwana su kwana for 2days ɗin da ya rage masa ya koma aiki kano, in yaso sai yasa wata nurse din ta ke lura da ita. hannunsa riƙe da nata sukai parlon Daddy, sai da zasu shiga ya saketa, shi ya fara shiga sannan itama ta shiga. Daddy na zaune akan carpet lokacin, Ammi na kan kujera suna hira da shi, Daddy ne ya amsa sallamar tasu Ammi kam har ta buɗi baki zata amsa ganin Nuratu yasa tai shiru ta amsa a ciki. daga baya suka tsuguna dukansu, bayan Yusuf ya gaida iyayen nasa Nuratu ma ta gaishe su, Daddy ne kawai ya amsa mata, jikinta taji yay sanyi tasa hannu ta goge hawayen da ya zubo mata a lokaci ɗaya, har ga Allah bata son wannan ƙiyayyar ta uwar mijinta, kuma duk duniyarta idan aka cire mahaifiyarta aka cire Umma babu macen da take so irin Ammi, ko da ace ba ɗanta take aure ba tana son Ammi saboda tana ɗaya daga cikin mata da suke burgeta. Daddy ya kalle su yana smiling yace,"my daughter i hope there is no worries?". kan Nuratu a ƙasa a ladabce tace,"babu Daddy". yace,"to Allah yayi muku albarka, ya ƙara muku zaman lafiya da kwanciyar hankali, ya kuma rabaki da cikin jikinki lafiya". ita ta amsa a hankali Yusuf ya amsa da ƙarfi. Ammi dai tun amsa sallamarsu bata ce komai ba. Daddy ya ƙara cewa,"ina mara lafiyar da kace kuna ruƙo a wajenku?". Yusuf yace,"tana can gida muka barota, There was a widow's nurse who took care of her zuwa mu koma gida". Daddy yace,"but kana following situation ɗin da take ciki ko?". yace,"ehh Daddy, ko ɗazu ma munyi vedio call da ita, magana ce dai har yanzu bata yi amma she is getting better". Daddy yace,"masha'Allah, Allah ya bata lafiya, amma har yanzu baka sa cigiyar ƴan'uwanta ba ne?". Yusuf yay ɗan jim kamin yace,"ehh Daddy banyi hakan ba tukunna, saboda kaga ba mu san ma daga inda take ba, and if mukai mata zancen da ya shafi ƴan'uwanta da kuma inda ta fito, her mood was changing a lokaci ɗaya sai ta shiga state of frenzy, so thats the reason yasa muka daina mata maganar gaba ɗaya". Daddy yace,"Allah ya kyauta, Allah masanin gaibu, but there must be something about her gaskiya, kuma ko menene lokaci zaizo da zata biɗi komawa inda ta fito, kace da dukkan alama tana da ƴaƴa?, kaga kuwa ba zata ƙare rayuwarta haka bata nemi ta koma garesu ba, ku dai kuci gaba da bata kulawa da taimaka mata, Allah ya baku lada". a tare suka amsa da,"amin ya Allah Daddy". shiru ya gifta a parlon, Yusuf na taraddadin yanda zaima Ammi maganar tafiyarsu. da Daddy yaga shirun yay yawa ya katse abinda zuciyar kowa ke saƙawa yace,"or do you need anything?". Yusuf yace,"a'a Daddy, dama zamu tafi ne". yace,"ok ba anan zaka barta ba?". ya ɗan sosa ƙeyarsa da kunya yace,"ehhh Daddy". Daddy ya kaɗa kai yace,"alright to ku tashi haka dare nayi, amma dai ita da ka barna nan cikin ƴan uwanta ai yafi ka tafi da ita wani hotel". Yusuf yace,"da yake zamu je asibiti ne da safe". Daddy yace,"to yayi, Allah bada lafiya. ku tashi haka". Yusuf na kallon Ammi wadda ke zaune tana jinsu amma kamar ma hankalinta baya garesu, ta haɗe girar sama da ƙasa ta ɓata rai. yace,"Ammi zamu tafi". yana faɗar hakan Nuratu ta ɗago ido ta kalleta, yanda taga Ammi ta taɓe baki taji kamar an soka mata kibiya a ƙirji. Yusuf ya miƙe tsaye ita kuma ta rissinar da kai tana cewa,"mun gode Ammi da Daddy, Allah ya ƙara muku lafiya da nisan kwana me amfani". daga haka suka fice daga parlon zuciyar kowannensu babu daɗi. **** "kin tabbata ba kya jin ciwon komai?". Yusuf dake tsaye a gaban gadon Fillo ya faɗa, yayinda wata nurse dake kusa da shi ke riƙe da file. Fillo tace,"bana jin ciwon komai Dr". ya jinjina kansa, ya karɓi file ɗin hannun nurse ɗin yay rubuce rubucensa. ya ƙara cewa,"gobe da safe insha'Allahu zamu sallameki, Allah ya ƙara lafiya". Fillo ta amsa da amin sannan ta ɗago ido ta kallesa, ƙwayar idonsu ta sarƙe ana juna, Yusuf yaji zuciyarsa ta girgiza, yasan akwai kamanni, amma bai taɓa zaton cewar akwai tsananin kamannin da suka kai irin haka ba bayan na wanda suke identical 2wins, a tare da wa zaisa kamannin yarinyar nan?, idon, fuskar, yanayin komai iri ɗaya ne, sai dai ya rasa iri ɗaya da na waye, tunaninsa da hasashensa ya gaza basa. yayinda a wannan lokacin zuciyar Fillo ke ƙara faɗa mata tabbas tasan wannan fuskar ta Yusuf, sai dai ta kasa tuna aina ne, aina ta taɓa ganinta?. _Comment ɗinku shine ƙwarin gwiwata, rashinsa shi yake sawa na hutar da kaina._ *dont forget to share, comment and vote.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *20* bayan sati ɗaya jikin Fillo ya ƙara yin sauƙi sosai, yarinyar har wani fresh tayi hasken fatarta ya ƙara fitowa saboda kwanciyar da tayi a asibiti me kyau, da kuma irin cimar da take ci me rai da lafiya. na musamman Hajiya Madina ke yin lafiyayyan girki a kai mata, girkin da zai ji ganyayyaki masu ƙara lafiyar jiki da kuma hanta acikinsa, tunda aka kwantar da ita duk wani abinci da zata kai baki da hanta take yin lomarsa, fruite salad kam da bata taɓa shansa ba sai da ya ginsheta. kuma tunda suka dawo bata ci gaba da zuwa aiki ba sai Kaka ce ke yi, Hajiya Madina tace ta ƙara samun hutawa na sati ɗaya sannan sai taci gaba, har wannan lokacin kuma bata san Turaki ne ya kaɗeta ba, duk zuwan da yake yi akai akai zatonta halin karamci ne kawai irin nasu. sa fiya ce yanzu dan ko takwas da rabi bata yi ba, Kaka na daga falo tana sauraren Shaik Ibrahim Daurawa a radio, Fillo kuma na ɗaki tana shiryawa. Kaka tace,"wai ba zaki fito ki wuce ba ne?, kullum sai kin ɓatawa bawan Allah lokaci Fillo, Allah raina yana ɓaci da wannan abin naki". daga inda Fillo take ta ɗan gwame fuska tace,"Kaka fuskar hijab ɗin ce fa ta yage shine nake ɗinkewa". Kaka tace,"uhm haka dai kike kullum da uzurin da zaki bayar, to ki bar ganin saurayinki ne Allah sai nace ya fara yi miki bulalar makara, wataƙila ki fi maida hankali akan karatun". dariya kawai Fillo tai bata ce komai ba, amma har hangowa take wai Amir zai daketa, tana sonsa dan haka ba zata ƙi tsayawa ba amma shi ɗin tasan ba zai taɓa iyawa ba, ko wani me gangancin yaga zai gwada sai iyakar inda ƙarfinsa ya ƙare. ta fito daga ɗakin sanye da hijab ruwan toka, hannunta kuma tana riƙe ne da qur'ani izu sittin ta rungume shi a ƙirjinta haɗe da dardumar sallah. "na tafi Kaka". Kaka ta ɗago ta kalleta tace,"Allah ya bada sa'a, amma ku gama da wuri kinga Hajiya Madina tace ki koma aikinki yau, kya gaida Amir ɗin kice ina daɗa masa godiya Allah ya jiƙan mahaifa". tace,"tom Kaka". da haka ta fice. daga can bakin gate wurin da ya saba zama ta gansa, a durƙushe a ƙasa da alama ya gaji da tsayuwa ne. bakinsa na motsi yana latsa counter dake saƙale a yatsansa, baƙin yadi ne a jikinsa mai taushi mara tsada wanda ya karɓi jikinsa sosai. ya kuma fito da kyawunsa na usulin bafulatani, sumar nan tasa kwantacciya ta fulani tai luff sai ƙyalli takeyi, da takalminsa da agogonsa dai-dai na me rufin asirin ubangiji. tunda ya ɗaga ido yaga Fillo na tahowa zuwa gare shi kyakkyawan murmushi ya ɓalle a saman fuskarsa, zuciyarsa na ƙara cika da tausayi da soyayyar Halimatunsa, ruhinsa na ƙara buƙatuwa da ƙwaɗaituwar ta zama mallakinsa. a lokacin da ta iso wurin ta sakar masa nata sanyayyan murmushi da yake motsa zuciyarsa. ta durƙusa a gabansa ta gaishesa. Ya amsa yana kasa ɗauke ido daga dogayen yatsunta da ta rufe fuskarta da su, murmushinsa na ƙara faɗaɗuwa. sai da yay gajeriyar ajiyar zuciya sannan yace,"Barka da fitowa gimbiyar Amir, sarauniyar da ta kafa fadarta acikin zuciyar Amir, kazalika uwar ƴaƴan Amir". ta ƙara rufe fuskar da hijab ɗinta, wani daɗi na ratsata. Yay ƴar dariya yana jin tana ƙara burge shi saboda wannan kunyartata. yace,"duk da an hanani ganin fuskar hakan ba zai hana ni faɗin kinyi kyau sosai, matsalar guda ɗaya ce dai da bana so". ya ƙarasa maganar amon muryarsa na sauyawa, tai saurin buɗe fuskarta, so take ta kallesa amma ta kasa, ta sauke idanuwanta a ƙasa da rashin jin daɗi tana jan yatsunta tace,"wacce irin matsala ce?, mecece matsalar da baka so?, a shirye nake da gyara ko menene saboda kai?". ya murmusa kuncinsa sannan yace,"Kunya! itace matsalar kuma itace bana so, amma a iyaka tsakaninmu banda wani daban, sai dai na san ba zaki iya dainawa ba balle ki rage, tunda ba tun yau ba nake roƙon alfarmar a rageta ko ya ya ne saboda tana ƙwarata, amma kamar ma ba'a jin me nake cewa...ni kuma tsakani da Allah ina so ake a bani damar ganin cikin idanuwan gimbiya, ina sonsu, so me yawa ba kaɗan ba". Fillo na murnushi ta ƙara ƙoƙarin sake rufe fuskar sai taga ya haɗe hannayensa alamar roƙo yace,"dan Allah Fillo nah, ki tausayawa zuciyata, ki tausayawa idanuwana". haka dole ta haƙura da rufe fuskar, ba zata iya saka ƙwayar idonta a cikin nasa ba, amma ba zata hanasa ganin fuskarta ba, dan haka ta ɗago kai yanda zai kalleta sosai, amma bata iya barin idonta a buɗe ba ta kullesu. sai da Amir ya ɗauki kusan minti ɗaya yana kallon fuskarta ba tare da ita tai magana balle shi da ya shiga shauƙi. da yana da dama, da yana da yanda zaiyi da yau Fillo bata ƙara kwana a gidan nan ba, da yau Fillo a gidansa zata kwana, kusa da shi, kusanci sosai irin kusancin da zai ɗorata a saman ƙirjinsa ya dinƙa faɗa mata kalaman da zasu mantar da ita duk wani kalar ƙalubale da ta fuskanta a rayuwarta. "ina sonki, ina miki so me tsanani, ƙaunar da nake miki ba mai fasaltuwa bace, bana fatan na rasaki Halimatu, bana fatan Allah ya kawo abinda zai rabani da ke, ke ɗaya ce tal

Chapter 16 of 73