ba...duk wata writer bata ƙin yin typing haka ɗaya wallahi sai da babban dalili, this typing da kuke gani is not easy at all, a barku da rubuta comment kaɗai ya kuke ji? to balle kuma a barka da rubuta readmore sama da 3?...duk a bar wannan, ina tunanin a page kusan uku na faɗa muku biki muke yi, biki muke bana karere ba, bikin ƙannena biyu a cikin sati biyu duka a haɗe, amma a haka na dinƙa squeezing ina muku typing, har akazo gabar da duk yanda naso na samu chance na yakice nayi muku ko da babu readmore wallahi na rasa, akace Babbar Yaya Magajiyar Uwa to kuna tunanin bikin zaizo min da sauƙi ne?, sai monday muka kammala biki, to ya kuke so nayi da raina tsakani da Allah?, i think ko da aka kammala biki ku masu iya bani hutu ne kuce na huta sbd gajiya, jiki da jini...amma har aka iya samun wasu suna faɗa min magana ta private da masu kirana a waya suna faɗa min abinda suka ga dama as if umarnin wani nake bi nayi typing ɗin, to ko yau nace na daina rubuta novel ɗin nan ta zauna wallah tunda ni nasa kaina ba wani yasa ni ba...so for Godsake muke yiwa juna uzuri a lamuran rayuwa na komai ba lallai sai a rubutu ba, yanzu in ace mutuwa nayi baku da labari fa?. kuma fisabilillah da naku zafin zanji ko da na ƴan youtube😫duk kun saka kaina ma zai fashe😫😫....and ina baran adu'anku wa sisters ɗina da suka shiga da ciki, Allah yasa anyi kenan sai mutuwa zata raba, ya kuma basu zuri'a ɗayyiba._*
*kuma duk da haka ina jiran azo ai min gashin ƙugu da ƙafafuna😂😂, hannun ma sai kunyi gashi dan a gajiye yake shima.*
*Comment, Share and Vote.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_not edited._
*26*
Ilham ta shigo parlon Yarima Abbas bakinta ɗauke da sallama da wani irin emotions a tare da ita. tun shigowarta kanta ke sunkuye a ƙasa kamar ta shiga fadar Me Martaba.
ta ƙarasa gaban table ɗin dake tsakiyar su Yarima Abbas ta ajiye ƙaramin tray dake hannunta, bayan ta ajiye ta ɗago ido ta kalli ɓangaren da tasan anan ne zata yi tozali da Turaki, tunda from there hancinta ke jiyo mata ƙamshinsa, wannan ƙamshin turaren da ita ta basa kyautarsa har ya zama choice ɗinsa.
idonsa da nata suka haɗu wuri ɗaya, kuma ba tare da ƙwayar idonsu ta fita ata junansu ba suka saki wani sanyayyan murmushi wa juna. wanda hakan ya wanzar da jin kunya a tare da ita, Turaki kuma da har sannan murmushin bai ɗauke masa ba yace,"zo nan".
Yarima Abbas dake cike da jin girma na izza yace,"kafi kowa sanin bana son yara suke zuwar min sashina ko, amma duk sanda kazo sai ka dinƙa wani kiransu suna shigo min da dattin ƙafafu".
ba tare da Turaki ya dube shi ba yace,"da wa kake?". rai ɓace Yarima Abbas yace,"yaushe wannan rainin hankalin zai bar jininka Turaki?".
Turaki ya ɗauke idonsa akansa yay masa banza bai tanka masa ba.
Ilham ta zauna akan hannun kujerar da Turaki yake, ya kamo hannunta ya riƙe yana cewa,"wai ni wannan Kunyar tawa da kike yi tun sanda kika dawo ta mene?". kanta na ƙasa tace,"kunya kuma Hammah?". yace,"ehh mana, kuma ni ban haihu ba, balle nace ɗana kike kamu".
ta ke fuskanta yay turning zuwa na shagwaɓaɓɓu tana ɗan dukan ƙafa a ƙasa tace,"yanzu Hammah ka rasa da wa zaka haɗani sai ɗanka".
murmushi kawai yayi yana shafa beard ɗinsa. idonsa akan tray ɗin da ta aje yace,"mene wannan?". tace,"your favorite, since morning na dafa idan zan tafi na kai maka...". sai ya katseta da cewan,"have you forgotten?". sai ta ɗan ɓata fuska tace,"ban manta ba, but ai naga ada ne". ya gyara zamansa yana faɗin,"ba da bane har yanzu Ilham. girkin Maama da Zaytun kawai".
wani irin rashin jin daɗin ya ziyarci Ilham, fuskarta ta nuna hakan, Turaki ya kalleta yace,"fushi?". ta girgiza kanta da sauri,"a'a". yace,"to saki fuskan". ba tare da tayi hakan ba tace,"to har girkin matarka ma ba zaka ke ci ba Hammah?". yace,"dalilin da yasa zanyi aure na zauna a kusa da Maama kenan". tace,"amma Hammah akwai...". ya tari numfashinta da faɗin,"akwai mutuwa ko?, na san da hakan. ki tayani adu'ar na riga Maama mutuwa ba naga tata ba". Ilham tace,"to Allah ya ƙara mata lafiya ya kuma bata tsawancin kwana me albarka". ya amsa da,"amin lelen Boɗejo". ya sauke numfashi sannan yace,"ina gyalenki?".
tace,"na barosa kan bed ɗin Mami saboda kace na hanzarta".
hannunsa akan fuskarta yace,"je ki ɗauko ki dawo, ki faɗawa Mami zaki min rakiya".
fuskarta ta washe da murmushi tana tambayarsa,"ina zamu je?". ya shafo wuyansa sannan ya bata amsa,"perfume zamu sayo".
idonta ya ƙanƙance a sa'ilin da take kallonsa. "ƙarewa yayi?, in ɗauko maka nawa?".
yace,"a'a wani zan sauya". idonta na ƙara ƙanƙancewa tace,"canjawa kuma?, perfume naka ɗin? your best choice ɗin?".
ya ɗaga gira ɗaya,"yes, bana son ƙamshinsa yanzu". tayi knodding kanta sannan ta miƙe ta fita.
Yarima Abbas ya rakata da harara, yayinda Turaki ya tsayar da ƙwayar idonsa akanta har sanda ta fice, bai san dalilin da yasa yake tausayin yarinyar ba, ko dan ta kasance ita ɗaya a wurin mahaifiyarta ne?, ba hakan bane, hakan kuma ba zai zama dalili ba. yana son Ilham kamar yanda yake son Nihal, Samha da kuma Zaytun. yana ƙara sonta da burin faranta mata saboda yanda itama take sonsa tun yarintarta, ta ke masa kallon jininta fiye da yanda take kallon su Yarima Abbas.
ya sauke numfashi yana jinginar da kansa jikin kujera tare da rufe idanuwansa, baya manta alkhairi a rayuwarsa ko da ace daga baya zaka saka masa da sharri, wannan alkhairin naka garesa zai mantar da shi girman sharrin da kayi masa. sai dai har yanzu ya kasa mantawa da sharrin da Mami tayi masa, tsawon shekaru da yawa har yau neman dalili yake na ƙala masa sharrin sata da Fulani Azima tayi.
idan ya tuna cewa bayan da mahaifiyarsu ta tafi ta barsu, a cire Hajiya Madina a gefe, babu wata mace da ta nuna musu ƙauna tsurarta gami da tausayi tare da kyautatawa irin Fulani Azima. ta so shi shi da Zaytun kamar zata haɗiye su, tayi sa'insa da Mai Martaba duk akansu. ya faɗa rijiya Fulani ta bisa cikin rijiyar an ɗauko su tare, a matsayinta na matar Mai Martaba ta zubar da gwiwoyinta gaban mahaifinsa tana roƙonsa akan ya bata Turaki zata kula da shi fiye da yanda zata kula da ɗan cikinta har zuwa ranar da Ramla zata dawo.
to amma sai dai me?, a lokacin da ya shaƙu da ita, ya saba da ita, ya shaƙu da ƴarta, yake ganin ta zamar masa uwa, sai Fulani ta rikiɗe ta koma kalar wata mace ta daban, mace me cike da tuggu da makirci, ta shiga muzguna masa tana goranta masa akan zaman da yake yi acikin masarautar alhalin ita ta rabosa da Hajiya Madina, ba wani ya ɗaukosa ya kawosa ba.
ta ƙala masa sharrin satar gwal a lokacin da baiji ba bai gani ba, ta ƙara da faɗin ya satar mata kuɗaɗe, kuma ba tare da wani tunani ko bincike ba Mai Martaba ya yanke masa hukunci daidai da abinda ya aikata, hukuncin da Hajiya Madina tayi tsalle ta dire agaban Mai Martaba tace muddin aka ga an saka ɗanta a prison to wallahi sai dai idan bata numfashi. ta kuma fuskanci Baffa gaba da gaba tace ya sani, idan har matsayinsa na alƙali bai shigar da ƙarar Fulani akan ƙazafin da ta yiwa ɗanta ba, to la shakka babu kaffara sai ya rabu da ita, kuma ya rubuta ya ajiye, rabuwarsu ba yana nufin zata tafi ta bar masa Turaki da Zaytuna bane, a'a zata tafi da gaba ɗayansu ne ta kowanne hali, ko da zai dinƙa yankar naman jikinta yana goranta mata ba ita ta haife su ba.
asalin samo gaba me ƙarfin gaske kenan da ta shiga tsakanin Hajiya Madina da Fulani, har tsawon shekaru masu yawa, har sai lokacin da Turaki ya kammala degree ɗinsa na biyu sannan gabar tasu ta ƙare, bayan Hajiya Madina ta tambayi Turaki ya faɗi kyautar da yake so tayi masa yace mata yana so ta daina gaba da Fulani, domin gaba abar ƙyama ce tunda Allah baya so, kuma ma'aikin Allah yace kar mutum ya rama sharri da sharri dan haka ta bar batun ɗaukar fansa da tace zata yi akan abinda Fulani tayi masa, ta yafe mata kamar yanda shima ya yafe mata.
a duk sanda ya nemi abu a wurin Hajiya Madina take a wurin take yi masa ba tare da ɓata lokaci ba muddin bai fi ƙarfinta ba, amma a wannan roƙon da yay mata sai da ta ɗauki tsawon kwana biyu shi kansa bata shiga sabgarsa ba, wai sunan shawara take tayi da zuciyarta taga idan zata iya yafewa wanda ya ƙalawa ɗanta sharrin sata. daga baya kuma sai komai ya warware tunda suka ƙara tausarta shi da Khalil da Bello, daga nan kuma Hajiya Madina ta sauko ta ci gaba da bawa Fulani girmanta na matsayin da take da shi.
yana zaune cikin tunanin abubuwan da suka faru a baya Ilham ta dawo, sai da ta taɓasa tukunna ya buɗe idonsa ya sauke akanta. tayi kyau acikin shigar da ta sauya na sky blue ɗin code less me shegen tsada, ya miƙe yana ɗaukar key ɗinsa ya kalli Abbas yace,"babban Yarima zan wuce".
ba tare da Yarima Abbas ya ɗago daga operating laptop nasa ba yace,"ka gaida Maama da Zaytun".
fitowarsu daga sashin Yarima Abbas suka ci karo da Fulani Azima ta fito daga turakarta kuyangu uku na biye da ita. haka kawai Turaki yaji gabansa ya faɗi da ganinta, lokaci ɗaya kuma ƙwaƙwalwarsa ta shiga karanto wasu ayoyi na kariya dake cikin alƙur'ani, ba wai yana nufinta da mugun abu bane, a'a haka kawai tun a ranar da taje asibiti dubasa yaji zuciyarsa ta kasa kwanciya da ita, kuma yana ta ƙoƙarin yakice abinda zuciyarsa ke raya masa akanta amma hakan yaci tura, in yayi ƙoƙarin watsarwa sai maganar Fillo ta dinƙa dawowa cikin kansa na batun asirin da tace ta ɗauke akansa.
*ASIRI!* har yau kalmar nan tsaye take a cikin ransa. kenan inda Allah bai shigo da Fillo cikin rayuwarsa ba shikenan duk kalar asirin da yaji ta ɗauke akansa sai ya kama shi?.
ya rufe ido ya buɗe yana kawar da wani tunani dake shiga sashen tunaninsa.
Fulani Azima ta tsaya da tafiya tana kallon Turaki da Ilham dake tafiya, wai Turaki ne tare da ƴarta?. lokaci ɗaya zuciyarta tayi wani mugun matsewa. taji kanta ya sara mata, lallai bata ga ta zama ba, sai ta sake sabon shiri, dole ne ma ta koma wurin boka, zata faɗa masa ya sauya tsarin aikinsa, sannan kuma yayi mata duba akan duk shegen dake lalata mata aiki.
a harzuƙe ta juya ta koma ta fasa zuwa inda ta nufa.
cikin motar Turaki dake tafiya akan titin zuwa PERKY FRAGRANCE STORE, wayarsa dake hannun Ilham tayi ringing a karo na huɗu, kuma a karo na huɗun ta ƙara ce masa,"Hamma ya kamata kayi picking call ɗin nan".
shima a karo na huɗun ya ƙara bata amsa da cewar,"picking ɗin ba ya da wani amfani".
a karo na biyar da kiran ya ƙara shigowa Ilham ta tsaya tana kallon lambar da babu suna ajiki. kasancewar kiran ba huruminta bane dalilin da yasa tun farko bata bi ta kan lambar ba, sai a yanzu da idanuwanta ke kallon lambar cikin kanta kuma na karanto mata lamabar ƙawarta Gimbiya Aisha.
har sanda kiran ya katse Ilham bata bar kallon lambar ba, haka ɗaya sai taji kamar an soketa da kibiya a ƙirjinta. kenan dama da gaske Aisha take yi mata.
conversation ɗin su na last haɗuwarsu ya shiga yawo acikin kanta. ranar buɗe company ɗin su Turaki, ranar da Turaki yay kwalliyar da babu macen da zata kalle shi bata kwaɗaitu da ya zama mallakinta ba. kuma a sannan Aisha ke bata labarin ta taɓa ganinsa a asibiti sanda taje duba wata cousin sister ɗinta, taso tayi masa wulaƙanci irin wanda kare ba zai shinshina ba amma sai ya juya ya tafi ya barta da zummar zaije ya dawo ya bata haƙuri, ashe juyawa yayi ya tafi da zuciyarta.
ya tafi da dukkan nutsuwarta da tunaninta, don haka a ranar buɗe company da ta ƙara ganinsa ba zata yi saken da zai suɓuce mata ba. a lokacin Ilham faɗa mata tayi kai tsaye cewar indai Hammah Turaki ne ba zai sota ba, hasalima ko kulata ba zai yi ba talkless of batun soyayya har ta kaisu ga aure. ta faɗa mata bai taɓa soyayya da wata mace ba.
sai dai buɗar bakin Gimbiya Aisha ce mata tayi,"Ilham, ni kuma ki rubuta ki ajiye, zan sauke duk wani jin kai dake kansa, zai soni, zai nemi aurena, zai aure ni a sanda ya gama haukacewa akaina".
Ilham tace mata,"asirce min ɗan'uwa zaki yi?". Gimbiya Aisha na murmushi tace,"bana fatan watarana tazo da zan aikata saɓon ubangiji Ilham, amma ki sani, zan haukata ɗan'uwanki ne kawai da salon soyayyata me zafi, irin wacca zai hanaku sakat har sai kunzo kun ɗaukar masa ni kun kai masa gidansa. da gaske nake miki Ilham ina son Brothernki sosai wallahi, kuma ina adu'ar Allah yasa ya zama mallakina, nasan kuma zan samu tunda dai har sarauta ce ta haɗu da sarauta".
Ilham ta rumtse idonta sosai tana jin wani iri a ƙasan zuciyarta wanda ta rasa dalilin hakan. ta wutsiyar ido take kallon Turaki dake driving cikin ƙwarewa, yana bin karatun ƙur'anin da ya kunna. ta mayar da murfin idonta ta rufe tana jin a ranta kamar zata yi kuka.
Turaki ya kai sanyayyan hannunsa ya taɓa goshinta, lokacin ta buɗe ido tana miƙewa zaune.
yace da ita,"did anything happend?". ta girgiza masa kai,"ba komi Hammah". "kuma kika yi silent bayan na san wannan bakin baya rabo da labari".
tai murmushi tukunna tace,"to ai naga kana bin karatu ne". Turaki ya kai hannu ya kashe karatun sannan yace,"ina jinki, bani labari".
"wanne iri to?". yace,"irin fitinar da kika dinƙa yi da kina yarinya bayan na koma Europe wurin Granny".
tasa hannu ta rufe fuska tana cewa,"to ai kasan wannan time en, kaga babu batun a baka labari". ya ɗan waigo ya kalleta yana cewa,"give me my phone". ta miƙa masa yay dialling numba ɗin Zaytuna ya kira.
sai da kiran ya kusa katsewa sannan tai picking, bayan picking ɗin shiru yay baice da ita komai ba. sai itace tayi murmushi daga inda take tana duban Fillo dake bacci hankali kwance akan gado tace,"bata tashi ba".
Turaki yace,"up to now?, lafiya kuwa?".
Zaytuna tace,"lafiya lau, rashin bacci ne da bata yi ba jiya". "why is that?".
tace,"naje wurin Kaka nace mata ko da zata ji shiru Fillo bata dawo ba zata kwana a wurina, saboda naga kaman bata jin daɗi tun ɗazu tana ta bacci...so Kakan sai take ce min ai jiya ma kwana tayi bata rumtsa ba tana ta kuka, kuma tayi tambayar meke damunta bata sanar mata ba, ta dai bar hakan a rigimarta kawai...dana dawo kuma naji jikinta da zafi, kukan da tayi ma zai iya sa mata zazzaɓi".
Turaki took a deep breath with out saying anything, hakan yasa Zaytuna kwantar da murya tace,"i will prescribe some drugs sai ka taho da su saboda ciwon yatsanta. like da fever ma a jikinta".
yace,"oak send it to me right now via message".
sai kuma yace,"Bello fa?". Zaytuna tai dariyar da ya bayyana haƙoranta tace,"he left since, da ƙyar na taushe shi wai sai yaje wurin Maama anyi wacca za'ai".
tsakin Turaki ya fita da ƙarfi yana cewa,"mahaukaci ne ai...don't pick up his calls again".
Zaytuna na murmushi tace,"na hannun daman naka Hammah?". yace,"ehh shi". ya faɗa yana katse wayan.
ya kashe kiran yana parking a ƙofar store ɗin da suka zo. suka fito a tare da Ilham wacce ya zagaya yana tambayarta dalilin sauyawan mood ɗinta alhalin ba a haka suka fito ba.
****
a hankali Fillo ta buɗe idonta daga ɓaccin da ta tashi, ta sauke ƙwayar idonta akan gadon da ta san ba katifarsu bace ita da Kaka.
tayi wani mugun zabura ta tashi zaune tai saurin durowa daga kan gadon, cikin ranta tana faɗar kalmar innalillahi.
ta rasa ma da wanne irin tunani zata yi amfani wajen tuna komai. bakin ƙofar da ta san ta riƙe handle tana kuka kawai take bi da kallo, da yaushe tayi baccin?, kuma ya akayi tazo kan wannan gadon?. kawai sai ta duƙe a wurin ta kifa kai da gwiwa tana fashewa da kuka, lokacin kuma taji kiran sallah ya shiga cikin kunnenta wanda ko ba'a faɗa ba tabbata na magriba ne.
ta miƙe da sauri ta wuce ƙofa zata buɗe taji ƙofar a rufe, ta dawo a hargitse ta shiga duba keys acikin drowers bata gani ba, taji zuciyarta ta ƙuntata. shin Turaki wanne irin mutum ne shi mara uzuri da yafiya a rayuwarsa, akan kawai ta fasa turare zai kulleta a ɗakinsa ita ɗaya?. kawai sai maganarsa ta dawo mata sanda yace idan ta fita a ɗakin nan to biyansa turarensa tayi.
kulle idanuwanta tayi tana jin hawaye na biyo kuncinto da tsananin jin haushi da takaicin kanta. me ma ya kaita?, har sai yaushe ne zata daina shiga hurumin da bai shafeta ba bai shafi wani nata ba?, dan ana so a cutar da Turaki doesn't mean ana so acutar da Hammah Hamid ne. ina ruwanta da Turarensa ma da har zata fasa kawai saboda bata so?. bata taɓa jin taji haushin kanta a wani abu da ta aikata ba sai a yau.
ta san turaren me tsada ne kamar yanda ya faɗa, to yanzu da wanne kuɗin zata biyasa?, shekaranjiya Kaka ta kwashe ƴan kuɗaɗenta ta bayar an siya tumakin da suke kiwo. kawai sai ta ƙara durƙushewa a gaban mudubi tana kuma sakin kuka, ko na misƙala zarratan Turaki baya da tausayi kuma baya da imani, sam baiyi gadon mahaifinsa ba, kuma bai yi gadon mahaifiyarsa ba kamar yanda taji labarinta a bakin Maama ɗazu.
tana cikin wannan kukan ne taji an buɗe ƙofar, ko bata ta ɗago ba tasan shine, hakan yasa taƙi motsawa, saboda so take yi ta taushi zuciyarta gudun aikata abinda zata zo tana dana sani, dan tasa a ranta sai Turaki yasan ya kulleta a ɗaki.
yau zata masa abinda zai sa ya koyi haƙuri da yafiya, in ba haka ba kuma ta barsa da sharrin waɗanda suke neman rayuwarsa, wannan ma kaɗai ya isa ya shiga hankalinsa.
Turaki ya shigo ciki yana mayar da ƙofar ya rufe tare da ƙara saka key, zaton Fillo bai saka key bane, hakan yasa ta miƙe da azama cikin dabarar data tsara cewar zata bige shi ta buɗe ƙofar ta fice da gudu, irin gudun da ba zai iya kamota ba. kuma ba zata ƙara yardar ma tazo ɓangarensu aiki ba sai dai in Ɗausiyya.
Turaki ya tsaya yana kallonta da mamakin yanda ta wani taso a sukwane kamar wacca taga mugun abu, ya ɗan matsa zai bata hanya gudun karta bigesa daidai nan ɗakin ya gauraye da uban duhu sakamakon ɗauke wuta da akayi.
babu shiri Fillo ta cakumo Turaki ba tare da sanin inda ta nufa ba tana kurma uban ihu tare da ƙanƙame shi.
"wayyo Allah nah, na shiga uku, Kakata". ihun take yi tana ƙara ƙanƙameshi kafin kuma ta shiga roƙonsa,"dan Allah ka kunna fitilar, wallahi ba zan ƙara ba, na bi Allah na tuba insha'Allahu ba zan ƙara yi maka ta'adi ba, kuma zan biyaka turarenka amma kaima Allah ka kunna hasken bana son duhu".
maganar take tana ƙara cikwikwiye shi, Turaki yasa hannu ɗaya ya riƙeta sosai ajikinsa, ya duƙa ya ajiye ledar hannunsa sannan yasa ɗayan hannun a aljihu ya ɗauko wayarsa ya kunna tourch. idanuwanta a rumtse suke gam hakan yasa ba zata shaida hasken fitalar wayar ba, kuma har lokacin bata bar roƙonsa ba akan ya kunna fitilar tana ƙara shigewa jikinsa. ya leƙa fuskarta ya kalla yanda duk take a tsorace, sai haɗa uwar zufa take, ya girgiza kai kawai yana mamakin bala'in tsoro irin nata.
yayi ajiyar zuciya a daidai lokacin da wutar ɗakin ta dawo, yay guntun tsaki na ɗan jinkirin da aka samu before a kunna generator. shi kansa baya son wannan ɗauke wutar duk da ba kasafe aka cika ɗaukewar ba, dalilin da yasa ya dami Baffa kenan akan kawai a haɗa transformer a gidan a huta.
cikin sheƙar kuka Fillo ta ƙara cusa kanta cikin ƙirjinsa wanda tuni maɓallin wajen ya cire. karan hancinta na gogar fatar ƙirjinsa tace,"dan darajan Allah Turaki kayi haƙuri, idan na kuma yi maka ta'adi kayi min duk abinda kaga dama, ni ba da gangan na fasa maka turare ba suɓuce min yayi a hannu. kai ma Allah da ma'akinsa ka kunna hasken zan biyaka".
"kinyi alƙawarin zaki biyani?". da sauri ta ɗaga kanta,"ehh zan biyaka amma ba irin naka ba".
guntun murmushi ya sauka akan leɓensa yana bin tsakiyar kanta da ɗankwali ya zame da kallo. kansa ya ranƙwafo saitin kunnenta yace,"to ki sakeni sai na kunna hasken". da sauri ta girgiza masa kai,"a'a ka kunna a haka, idan na sakeka wani abun zai kamani".
yace,"wanne abu ne zai kamaki?". Fillo taji kamar tasa masa duka, sai kawai ta daɗa sa kuka tana cewa,"ni dai ka kunna don Allah, duhu tsorata ni yake wallah".
ya kai hannu kamar zai shafi gefen fuskarta sai kuma ya fasa yace,"to idan na kunna ta ina zaki sani bayan kin rumtse ido. ki buɗe idonki tuni aka dawo da light".
jin hakan yasa a hankali ta shiga buɗe idonta, sai da ta tabbatar idan ta buɗe duka idonta zata ga haske sannan ta buɗe, ta buɗe idonta duka tana saukewa ajikinsa. take ta zabura ta sake shi tana fita a jikinsa tare da ja da baya, sai aikin rarraba idanuwa take yi. sai kuma tayi saurin dafe kanta da taji yayi mugun sara mata a lokaci ɗaya, jiri ya nemi ya ɗebeta ya yasar, Turaki daya lura da hakan yay saurin kamo hannunta ya janyota ta dawo gabansa, ƙarar bugun ƙirjinta tarr a kunnensa.
yana riƙe da hannunta da take son ƙwacewa ya sunkuya ya ɗauki ledar, ya jata suka zagaya zuwa ɗaya side na gadon. cikin fargaba da tsoron matakin da zai ɗauka akanta na yadda tasa rigarsa ta cikwiwiye kamar an ƙwato a bakin jaki.
idanuwanta sukai rau-rau tasa hannu tana ture nasa tana cewa,"kayi haƙuri dan Allah, ba zan sake ba".
bai ko kalleta ba fuskar nan a haɗe ya zaunar da ita a gefen gadon. sannan shima ya zauna kusa da ita yana janyo table gabansa, ya buɗe coolern abincin dake kai yaga dambu ne na cous-cous da yaji hanta acikinsa sai ƙamshi yake. daga buɗewa duka wajen ya baɗe da ƙamshi.
ya juyo da kansa kaɗan ya kalleta tana ta matsar ido, ya tamke murya yace,"when did you wake up?".
taja majinar hancinta cikin muryar kukan da bai barta ba tace,"kayi haƙuri dan Allah". Turaki ya daki gefen gadon yayo kanta gaba ɗaya yana sakar mata tsawa,"nace when did you wakeup?".
da bala'in tsoro tasa hannu ta kare kanta jikinta sai kyarma yake yi, cikin rawar murya tace,"ban jima ba".
bai ƙara bi ta kanta ba ya tashi ya fita, after few minutes sai gashi ya dawo riƙe da wani ledan daban. ya ajiye akan gadon ba tare da ya kalleta ba yace,"ci abinci".
tsananin tsoron yanayinsa da ya rikiɗe bata tunanin zata yi masa musu, don haka da azama ta sauka a gefen gadon, hannu na rawa ta ɗauki plate ta buɗe coolern ta zuba abincin ta ajiye a gabanta.
tunda ta zuba taji idanunsa akanta, hakan yasa ta kasa sakewa, kuma ta kasa ɗagowa ta kallesa balle ta nemi izininsa taje ta wanke hannu, shi kuwa ciwon hannunta kawai yake kallo da Zaytuna ta ƙara dressing.
sai da ta ga ya yunƙura zai tashi sannan tayi saurin cewa,"zan wanke bakina". yay gaba abinsa bayan yace,"karki je ki wanke kici a haka".
yana fita a ɗakin ta miƙe ta shiga toilet, bakinta ta wanke da macline sannan ta ƙara wanke toilet ɗin tukunna ta fito. har lokacin kuma hawaye bai bar sauka a fuskarta ba, ita tsoron da take yi kar Maama ta nemeta, duk da tasan zuwa yanzu Kaka na can tana jiran dawowarta.
ba zata iya cewa ba zata ci abincin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 73