Baba, amma motan kamar bana gidan ba, ban dai sani ba". Me gadi ya fice da sauri, ganin ba motar gidan bace yasa shi ƙarasawa don ganin waye.
Turaki ya gani aciki fuskarsa kamar an aiko masa mutuwa, ya tabbatar da AC kunne a motan amma yana ganin yacca zufa ta tsatstsafo a goshinsa.
Me gadi ya rissina yana faɗin,"ranka ya daɗe ashe kaina, kayi haƙuri na shiga banɗaki ne. motar kuma ban shaida ta waye ba shisa, bari inje in buɗe".
da ƙyar Turaki ya iya buɗe baki saboda yacca yake jin kansa kamar zai fashe yace,"ba gate zaka buɗe ba, yarinyar da ta shiga yanzu zaka kira, da sauri".
cikin sauri me gadi ya koma, lokacin Fillo na dab da entrance na side ɗin Boɗejo taji me gadi na ƙwala mata jira.
"ki zo da sauri yallaɓai ne ke kira". ita da yace yallaɓai sai tayi zaton ko Baffa yake nufi. don haka ta ɗago ƙafa tana cewa,"tom". shi kuma yana ƙara cewa,"yace kije da sauri". Fillo ta ƙara saurin tafiyarta har tana jin kaman za tayi tuntuɓe.
tunda ta fito jajayen idon Turaki ke kanta har ta ƙaraso ta ɗayan glass ɗin, ya sauke glass ɗin ba tare da ya waiga ya kalli ko da inuwarta ba.
dan a yacca zuciyarsa ke tafarfasa zai iya shaƙota ya shigo da ita ta cikin glass ɗin.
Fillo ganinsa yasa gaba ɗaya ta tsure, da ƙyar ta tattaro yawun bakinta tace,"gani".
ta faɗa kamar me koyon magana, bala'in tsoro na kamata saboda yanayinsa da ta gani, ita ko babu yanayinsa ma tana jin tsoronsa.
"buɗe ki shigo". haka taji amon muryarsa tamkar saukar aradu aka.
zata tsaya tunanin maganar tasa taga ya juyo a fusace ya zuba mata rikitattun idanuwansa da suka koma kamar na tiger.
babu shiri ta nufi ƙofar baya zata buɗe a tsawace taji yace,"kika shiga nan babu abinda zai hanani ɓalla ƙasusuwanki na zubar a wajenan".
take ruwan hawaye ya sakko mata ta dawo tana buɗe gaba ta shiga da tsananin ruɗewa, duk ta firgice ta gigice.
ta rufo ƙofar motar tana kifa kai akan cinyarta ta fashe da kuka. Turaki ya dinƙa kallonta babu ko ƙifta ido, a hankali kuma ya mayar da ƙwayar idonsa kan hannun hagunta da Amir ya riƙe for morethan 2tyms, yaji zuciyarsa ta ƙara tamkewa, trying his best to be very calm gudun kar ya illata ƴar mutane, ya damƙo tsintsiyar hannunta dake rawa yana mata mugun riƙo kamar zai karya ƙashin wajen.
ta ɗago da kanta a gigice tana kallonsa da tsananin jin zafin riƙon. cikin muryar kuka tace,"me nayi maka?". tambayartata yaji kamar ya tsinka mata marin da zai yi sanadiyar ɗaukewar jinta da ganinta gaba ɗaya, wataƙila hakan yasa tasan laifinta.
acikin rishin kukan da take yi tace,"jiya fa kace ka haƙura, amma tunda baka haƙura ba i will give you half of the money now, ending month sai na cika maka sauran".
shi dai kallonta kawai yake yi yana tunani iri iri cikin ransa, tana batun ta basa 25k now, aina ta samu 25k?, wanda ya tafi ne ya bata?, me tayi masa ya bata?. sai ya rumtse ido gam yana ƙara damƙe hannun da mugun ƙarfin da yafi na ɗazu har sai da ƙashinta yayi ƙara, idan ce masa akayi an ganta da wani ba zai taɓa yarda ba don ba tayi kama da wadda zata tsaya da namiji ba, amma with his own 2eyes ya ganta tsaye da namiji a inda babu kowa sai su kaɗai, ƙofar gidan da babu masu wucewa, sama da rabin awa suna hira cikin nishaɗi har tana wage masa all her 32teeths.
which kind of purnishment did he supposed to give her?, shin ya ɗimautata da sanar da ita cewar akwai igiyoyin auren wani akanta guda uku reras?, ko kuma yayi mata abinda ba zata ƙara kallon wani namiji ba a rayuwarta?, balle harta bari ya riƙe mata hannu har tai masa dariya har ta barsa yaja hancinta.
"wallah zan baka 25k daga baya zan cika maka sauran, amma kayi haƙuri ka sakar min hannu da zafi wallahi, ƙashina ma har ya ɓalle ina jin".
tsabar ƙuluwa Turaki bai san lokacin da ya dunƙule hannunsa ya daki bakinta ba ya fashe, shi zata faɗawa ya sakar mata hannu bayan ita halalinsa ce?, and ta iya barin wani ƙaton banza can daban da ba muharraminta ba ya riƙe mata hannu ba tare da ta hanasa ba?.
Fillo ta fashe da kuka sosai tana sa gefen mayafinta ta danne leɓenta da ya fashe. "ni me nayi maka a rayuwa ka tsane ni, ban taɓa cutarka ba haka ban taɓa munafurtarka ba, amma kai kullum burinka ka ƙuntata min, akan me?, saboda ina ƴar talakawa?, ina yi maka biyayya iyakar iyawana matsayinka na wanda nake a aiki a ƙarƙashin iyayensa, mahaifiyarka bata taɓa min kallon banza ba balle har ta nuna min tsana, amma kai ko da yaushe ka ganni burinka bai wuci kasa na zubar da hawaye ba, a wanne dalili?, idan har nayi maka wani laifi ne bisa kuskure da ban sani ba sai ka faɗa min na baka haƙuri, ba wai ka dinga muzguna min ba duk sanda ka ganni. yanzu ka karya min ƙashin hannu ka fasa min leɓe duk saboda me fisabilillah?".
kuka take sosai tayi maganar, idon Turaki manne akanta yana hasko tsayuwarsu da Amir, cikin jin zafi a heart ɗinsa ya kulle idonsa, yaja motar with high speed kamar duniya zata tashi, tayoyin motar suka bada sautin ƙuuuuu akan kwalta, wannan ƙarar ta haddasa tsoro na bala'i a zuciyar Fillo, kuma tsananin tsoron yasa farat ɗaya ta ɗago da kanta dake kan cinyarta, ganin yanda yake zabga mugun gudu akan titi tayi jikinsa a rikice ta riƙosa tana faɗin,"kayi a hankali dan Allah zamu yi accident fa, ka daina nufar bishiyan can".
*Please vote, comment and share.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_not edited._
*29*
motar Turaki bata tsaya a ko'ina ba sai a compound na cikin company ɗin su, ƙarfe biyar na yamma a lokacin, and at that time an ma yi closing, bai san exact abinda ya shigo da shi ba, kawai ɓacin ransa ya kaisa.
yay parking yana daɗa tabbatar da duka glasses na motar a rufe suke, ya kunna karatun qur'ani sannan ya buɗe lock. ya kalli Fillo da har lokacin kanta ke kife a gefen kafaɗarsa, tun sanda ta ke roƙon yay driving nasu a hankali taga baida hankalin dainawa shikenan sai tayi shiru, kuma tsoron da takeji shi ya hanata ɗagowa a kafaɗar tasa.
wucewar 20seconds yana kallonta, yana jin yanda numfashinta ke sauka a hankali, a tunaninsa duk bacci ne take yi, nan kuwa tsabagen zuciya ce tasa tai luff kamar wadda baccinta yay mugun nisa, wani irin zafi take ji a zuciyarta kamar ana rura wuta, in ace ta ɗago a ɗazu da tabbas babu abinda zai hana hannuwanta shaƙe Turaki, in yaso suyi accident ɗin da gasken gasken.
kafaɗarsa ya janye nan take kanta ya ƙwalu da kujeran, ta buɗe ido a hankali tana kallon inda suke, bata ko motsa ba har ya fice daga motar, tana kallo ya saka lock ya wuce ya barta, ita kuma ta rakasa da ido.
tana ganin yacca ƴan tsirarrun staffs da basu wuce ba kowa na gaida shi, shi kuma yana ɗaga musu hannu.
duk ƙoƙarin da tayi don ganin lock ɗin motar ya fita ta kasa, kenan rufeta yayi a motar ya tafi ya barta?, koma me zai faru da ita ya faru da ita?, to me yake nufi da ɗaukota ɗin?, ga shi ya kashe Ac balle ta samu sauƙin zafin gari da na zuciyarta da take ji.
wani malolon baƙin ciki ya tokare mata zuciya, sai ta kifa kai da gwiwa ta fashe da kuka, kuka take sosai har tana jin kamar zata shiɗe, ga kanta na uban sara mata, ga zufa duk ta wanke mata jiki, sai da tayi me isarta tukunna ta ɗago tana goge hawayen, tana jan majinar hancinta ta ƙara trying buɗe motar amma taƙi buɗuwa.
sai kawai ta jinginar da kanta jikin kujerar ƙirjinta sai bugawa yake, ta cikin glass ɗin ta fahimci magriba ta gabato saboda yanayin yacca garin ya lulluɓe, zuwa lokacin duk staffs sun ɗaɗe sai me gadi kawai da take iya hangowa ta cikin mirror. ta rufe idonta tana bin suratul Yusuf dake tashi cikin ƙira'ar Yousuf Kalo.
Turaki kuwa tunda ya shiga office ɗinsa zama yay kawai ya rufe idonsa, yayi hakan ne kawai saboda temper ɗinsa yay cool, dan in yci gaba da kasancewa tare da ita a yanda yake mugun jin haushin abinda tayi ba abinda zai hana sa illata. sai da ya ɗauki tsawon awa guda bai motsa a yanda yake ba, yana kallon kira daga different numbers na shigowa wayarsa amma babu ɗaya da yay picking.
Fillo dai har sannan tana zaune sai wurga idanu kawai take yi, Allah ɗaya yasan yanda take ji a cikin ranta, taja Allah ya isa tafi kai ashirin, in ace da wani abu da zata iya fasa glass ɗin tuni ta fasa ta fita ta windown.
tana cikin tunani a ranta sai taga Turaki ya fito daga wani building daban da inda ya shiga ɗazu, cikin sauri yake tafiya yana sauke hannun rigarsa dake tattare, da alamu alwala yay zai wuce masallaci tunda ga ruwa nan a fusakarsa.
bata ɗauke idonta akansa ba har sai da ta daina ganinsa, bayan minti goma sai taji lock ɗin motar ya fita, kuma kamin ta kai ga buɗe murfin idonta taji ƙofar side ɗin da take ta buɗe.
"come out". taji muryarsa ta shiga kunnenta sanda take buɗe idonta duka.
kamar tai banza da shi sai kuma taji tana tsoron yin hakan, Allah shahidi bata tsoron uban kowa a duniyar nan amma tana mugun shakkar Turaki.
ta tattaro mayafinta tana ƙudundune jikinta sannan ta fito a cikin motar ta tsaya a gefensa, tana fitowa ya rufe yay gaba yana cewa da ita,"follow me".
tabi bayansa tana ɗan kalle-kalle, sai yaba kyan company ɗin take yi, daga waje ma kenan ina kuma ga an shiga ciki.
suka shiga cikin office ɗinsa sannan suka wuce ciki inda wani ƙaton parlo yake, inda anan ne yake Turaki ke hutawa.
"kiyi sallah". abinda yace mata kenan ya wuceta ya zauna inda ƙaton farar cushion yake.
Fillo ta kalla haɗuwar parlon ta ƙara kallo tana me jinjina uban yawan dukiyar da aka kashe wajen ginin company ɗin da kuma abinda aka zuba acikin office ɗin, wato kuɗi dai suna inda suke, talaka da baida su ne yake ganin kamar babu su kwata-kwata.
kanta a ƙasa ta fuskanci kujerar da yake zaune, muryanta a hankali tace,"banda alwala".
yanda tayi maganar kawai yasa shi ɗago da kansa yana kallonta, ko kurma yaji sautin murayar nata yasan da ɓacin rai aciki. sosai yake kallonta da son gano abinda yasa tayi uban hasken da yake gani ajikinta, ba haka yasan asalin hasken fatarta ba, to daga ina wannan mugun farin?.
jin yay shiru ta ɗago kanta karaf suka haɗa ido, ta tsuke fuska da baki tana ƙara ɓata rai. shi kuma yay mata nuni da hannu yana mata nuni da inda toilet yake.
bata motsa ba kawai ta tsaya, ita ba zata iya shiga toilet yana zaune a wurin nan ba, sai dai in su shekara a haka, in yaso daga baya ta rama sallolin.
da kansa ya gane manufarta, hakan yasa ya miƙe ya fice bayan yace mata,"don't waste my time".
yana fita ta shiga toilet ɗin, cikin toilet ɗin kansa mugun ƙamshi yake kamar ba'a shigarsa. tai alwalan ta fito, mayafinta ta yafa ta tayar da sallah akan darduman da ta gani.
la'asar da magriba tayi a haɗe, bayan ta idar ta duƙar da kanta saboda mugun sarawar da taji yana yi, ga jikinta ya fara zafi alamun fever na son kamata. ita kanta ta san ma dole tayi zazzaɓi da ciwon kai ko saboda kukan da tasha a yau.
minti 1,2,3 har minti ashirin suka wuce Turaki na zaune office yana jiran fitowarta amma shiru. cikin ransa ya ayyana duk yanda akayi jira take ya koma yace mata ta fito, tsaki yaja ya tashi ya koma cikin parlon.
zaune ya ganta har sannan akan darduman kaman me lazimi, to amma jin motsinsa bai sa ta ɗago ba, alhalin ya santa da shegen tsoro, ya tsaya yana kallonta yaga dai durƙushen kanta kamar ba na lafiya ba tukunna ya ƙarasa ciki ya zauna kan kujerar dake kusa da ita.
yasa hannu ya ɗago kanta looking at her innocent face da yay ja, with the other hand ya taɓa forehead nata yaji zafi rau. ya rufe idonsa kaɗan ya buɗe yana ganin yacca hawaye ke suntiri akan kumatunta, kallon hawayen yake yana hango lokacin da yake zaune a gaban Hayyo yana faɗa masa cewar,"ehh kamar uba nake a wurinta amma ni ba mahaifinta ba ne, wannan yarinyar da kake gani ai ƴar zina ce, ƙwarai ƴar gaba da fatiha ce ranka ya daɗe, mahaifiyarta ma mahaukaciya ce, garin haukar nata ta gudu shekaru da yawa har yanzu bamu ganta ba, kuma har yanzu ni ban saketa ba. amma dai saboda a rufawa yarinyar asiri indai da gaske kake sonta ranka ya daɗe kawai ka biya sadakinta yanzu a take, batun sauran kayan al'ada da ake yi duk ba sai kayi mata ba, tunda dama ba faɗar addini bace, sadakin dai nata kawai ka kawo itama idan an bata babu hankalin riƙe su, tunda dama ni ne maɗaurin aurenta, babu wanda ya san danginsu tunda a titi na tsinci uwar naji tausayinta na aureta. ita kuma tsohuwar da kake cewa Yarinyar na hannunta gaskiya to ban ma san wace ba, ƙila ma ko irin tsaffin nan ne macuta".
ya ƙara hasko lokacin da yasa hannu a aljihunsa dan ɗauko kuɗi, amma sai yaji babu komai. sai ya ƙara kallon Hayyo wanda ya gano tsananin kama ta Fillo a tare da shi, ya sauke numfashi yana me jin wani iri a ransa, zuciyarsa na ƙara ƙarfafa masa miƙa sadakin Fillo, ko da bai aureta saboda taimakon da tayi masa, tabbas ta cancanci a aureta saboda rashin dace na uba da tayi, dan ko kaffara ba zai yi ba Hayyo shine mahaifin Fillo.
to amma da me zai bayar da sadakin nata?, yay shiru yana tunani cikin ransa, ko kaɗan baya so ya miƙe daga kan tabarmar nan ba tare da ya mallaki yarinyar da ta dinƙa cusa kanta a haɗari ba saboda kawai ta cece shi, ba don komai ba sai dan ba zata iya ganin an cutar da wani ba.
yana iya tuna yacca ya dinga jin kallon da Hayyo keyi masa, yana tuna furucin da Hayyo yayi masa kan cewar,"ranka ya daɗe in har babu sadakin yarinyar nan kazo ayau, to ina mai tabbatar maka da cewar ba rabonka ba ce, domin kuwa tun tana ƙarama akwai wani tsoho da ya roƙi a bashi ita, to banda ma dai tasa ƙafa ta gudu da maganar da nake shaida maka yanzu tayi ƴaƴa kusan uku. dan haka kana tafiya zan yi masa magana ya bada sadakinta, in yaso tunda Allah yasa kai kasan inda take, sai kayi mana jagora muje mu taho da ita".
"zan bayar da sadaki, amma sai naga shedu". haka yasan ya faɗa masa, kuma minti goma ba'a ƙara ba sai ga Hayyo ya dawo tare da mutum huɗu, ya shaida mutum ɗaya wanda Hayyo ya nuna masa yace shine limamin babban masallacin anguwarsu, saboda lokacin da ya shigo unguwar ya tsaya yayi sallah a masallaci, dalilin da yasa ya gane shi kenan, sai mutum ukun da bai sansu ba, amma daga tsufansu ya san ba mutanen banza bane.
yana tuna sanda Liman ya buɗe baki ya tambayesa ina waliyansa, kuma a lokacin magana ɗaya ya faɗa wadda daga ita ba wanda ya ƙara cewa komai Liman yace ya miƙo sadakin. "ni maraya ne, bani da kowa sai Allah".
hakan ya faɗa musu, kuma daga faɗar hakan babu wanda ya ƙara masa wata tambaya aka ce ya ajiye sadaki. still idonsa na kan Hayyo yace,"banda kuɗi yanzu". kuma tun bai rufe bakinsa ba Hayyo yace,"kana iya tashi ka tafi, yarinya dai ba rabonka ba ce".
zuciyarsa ta faɗa masa cewar in har Fillo zata iya sadaukar da ranta da kuma lafiyarta akan ta kuɓutar da shi daga wani ƙulli, alhalin ba dangi iya bare na Baba, to baya jin shi zai kasa iya sadaukar da komai nasa don ganin ya mallaketa, mallakarta kaɗai shine sakayya mafi kyautatawa da zai yi mata. saboda haka take a wurin a ajiye key ɗin motarsa a gaban Liman yace,"na bayar da motata a matsayin sadakinta".
ba zai taɓa mance yanda Hayyo ya dinƙa kallon maƙullin motar ba with so much expression, har ƙwayar idonsa irin ta Fillo na yin kamar zata faɗo waje. amma duk da haka sai da yasa aka shiga cikin gida aka kira masa wani saurayi, saurayin shima me kama da Fillo sak, idan bai manta ba sunan da Hayyo ya kira saurayin da shi shine,"Hamid". saurayin ya amsa masa da,"na'am Abba". sannan Hayyo ya ɗago kai ya kallesa yace ya zagaya baya, ya gano masa motar dake wajen kuɗinta zai kai nawa.
and abinda Hamid ya dawo ya sanarwa da Hayyo shine,"kuɗinta zai kai miliyan hamsin ko sama da haka". kuma ba tare da ƙara yin wani bincike ba Hayyo ya kalli ƙwayar idon Turaki yace masa,"kaje yarinya ta zama mallakinka, aure ya ɗauru".
haka ya baro garin Taraba a train zuciyarsa cike da tarikan mamaki iri-iri a game da lamarin Fillo da mahafinta, duk da cewar yaso ya keɓe da Hamid to amma bai samu dama ba.
Fillo ta buɗe idonta dake yi mata zafi tana kallonsa, idonsa a rufe yake, har sannan kuma bai saki kan nata ba.
in cool voice nata tace da shi,"please ka daina taɓani any how babu kyau. kuma dan Allah ko kuɗin napep ne ka bani na koma gida, Maama da Boɗejo zasu neme ni, turarenka kuma zan biyaka insha'Allah".
a sannan Turaki ya buɗe idonsa yana ɗauke hannayensa akanta. yana kallon gefe daban kamar zai yi magana sai ya fasa ya miƙe.
ya nufi ƙofar fita yana cewa da ita,"biyo ni". ta tashi cikin sauri tabi bayansa.
tunda suka hau titi take ta kallon hanya har suka iso asibitin Miyetti, fita yay a motar ya barta ita ɗaya ya shiga pharmacy ya sayo magunguna ya dawo, sannan suka ɗau hanyar gida.
ko da suka ƙarasa gida Turaki yay parking a parking lots sai Fillo ta kasa fitowa a motar, ta tsinci ƙafafunta da kasa yin motsi su fita daga motar. tana kallo ya fice ya barta aciki, sai ta bisa da ido tana kallo ya wuce side ɗin Boɗejo, gaba ɗaya ta rasa me take ji a tare da ita, tasa hannu zata buɗe motar ta fita sai ga motar Samha tayi parking kusa da ta Turaki.
da dukkan alama tun fitar safe da tayi sai yanzu ta dawo, Fillo tai saurin maida ƙofar tana rufewa a hankali gudun karta ji ƙara, kasancewar tend glass ne amotar hakan yasa babu me hangota aciki sai dai ita ta ga na waje. tai ɗuff ta ɗauke wuta dan ji take kamar zasu iya jiyo numfashinta.
Sameer taga ya fito daga driver seat sannan Samha ta fito ta ɗayan seat ɗin, ta zagayo ta side ɗin Sameer ta karɓi roban Maltina a hannun Sameer, sun ɗauka atleast 2minutes suna magana kamin su saki murmushi, tukunna suka bar wajen suna wucewa cikin gida.
Fillo taji ta wani girgiza, bata san wannan shirin nasu kuma na menene ba, bata ji su ba, bata san me suka ce ba. taja nunfashi ya ɗauka ledar maganin da Turaki ya tsaya ya saya ta fita daga motar, cikin saurin tafiyarta tai side na Boɗejo cikin zuciyarta tana ta fatan kar Allah ya bawa Samha ikon ganin Turaki, haka kawai zuciyarta ke faɗa mata wannan roban malt ɗin ba malt bane kawai aciki da akwai wani mugun abin aciki, haka kuma ba don kowa aka shigo da shi ba sai don Turaki, tafiya take tana harɗewa tana ƙara jin tsoron mutum acikin ranta, idan ba a film ba bata taɓa tunanin za'a iya samun siblings ɗin da zasu iya kashe ɗan uwansu a gaske ba, sai ga shi yanzu ta gani a zahiri, abin na faruwa a inda take rayuwa.
maganar Hajiya Madina ta haska cikin kanta, santa take ce mata,_"ba halina ba ne, ba haka zuciyata take ba, tunda Allah ya halicceni banda mugun nufi akan kowa, zuciyata bata da tsatsa ko kaɗan, kullum roƙon Allah nake kar yasa na cuci wani a rayuwata, amma ban san a ina Samha da Sameer suka ɗauko wannan mugun halin ba, ban sa ni ba, dan ba halin mahaifinsu ba ne..."._ kasa ƙarasa maganar tayi a lokacin saboda kukan da ya ƙwace mata.
kamar wadda tayi gudun famfalaki haka Fillo ta shiga parlon Boɗejo, gaba ɗaya ma sallamar ta mance da ita. babu kowa a parlo dan haka kai tsaye bedroom na Boɗejon ta wuce, ta san ba zai wuce can Turaki yayi ba, ta buɗe ƙofar tana shiga da sallama.
Ilham dake gefen Turaki a zaune ta amsa sallamar tana faɗin,"bismillah".
gaba ɗaya Fillo sai taji ƙafafuwanta sunyi matuƙar sanyi, bata san dalili ba amma haka kawai taji gabanta ya faɗi da ganin Ilham da tayi da kuma yacca ta ganta zaune manne ajikin Turaki.
zuciyarta taji na faɗa mata cewar kawai tayi reverse, amma sai taji ta kasa gaba ta kasa baya.
Ilham na kallonta sosai tace,"ki shigo mana, ba aiki zaki yi ba?".
kan Fillo a ƙasa tace,"ehh". Ilham tace,"to bismillah".
Fillo ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta, ta shigo ciki idonta a rufe tana jin kamar jiri ne ke neman ɗibarta ya zubar.
Ilham na riƙe da hannun Turaki tace,"to Hammah ba sai mu tafi tare ba, tun fa dana dawo ban ƙara zuwa ko'ina ba, Mami sai tace wai a'a, kuma ni ko dubai ina so naje na sha iska, please Hammah zan bika".
ya kama hancinta yaja ba tare daya ce komai ba, wucewar 3seconds ya miƙe ya fita Ilham tabi bayansa, Fillo kuma dake tsaye gefe guda ta bisu da kallo.
suna fita ta jefar da ledar dake hannunta akan kujera, taji kamar tana so tayi kuka, amma ba zata yin ba saboda har yanzu kanta ciwo yake yi mata. ta rumtse idonta sosai, da ƙyar ta iya gyara abinda zata gyara a ɗakin cikin few minutes ta fice.
tana fitowa parlon ta tadda Turaki zaune a kan kujera shi ɗaya, da remote hannunsa yana sauya channel. ta tsaya tana kalle-kalle ko zata ga Ilham, sai dai da dukkan alama bata nan.
table ɗin dake gabansa tabi da kallo, fruites ne acikin plate sai roban malt a gefen plate ɗin.
tai tsaye daga inda take sai kallon roban take yi, kamar me son ganin wani abu aciki.
taiwa Turaki kallo ɗaya ta ɗauke kai, bata san me yasa ba haka kawai taji tana mugun jin haushinsa for the first time. inda yake ta ƙarasa ta aje ledan maganin kusa da shi tana cewa,"ka manta a mota". sannan ta kai hannu kan table ɗin ta ɗauke roban malt ɗin zata bar wajen.
yay saurin riƙo hannunta ya dawo da ita,"ɗauka ki tafi da su".
ta waiga ta kalla ledan sannan ta kallesa, tace,"maganin da ka saya ne fa". shima ɗin yana kallonta yace,"nayi miki kama da mara lafiya?". sai ya galla mata harara yace,"ɗauka ki wuce da shi".
kamar zata yi kuka tace,"shi maganin dama haka kawai ake shansa?, kawai daka sami magani sai kace dole sai na sha. ka barni na wuce please Kaka na can na jirana". ya janyota ta zaune kan kujerar kusa da shi. zai ƙwace roban malt ɗin ta damƙe da kyau.
ya dinƙa kallonta da mamaki kafin ya iya buɗe baki yace mata,"aje". ta maƙe kafaɗa ba tare da tace komai ba. ya ƙara ware idonsa yana kallonta, ta rufe ido ta cije fuska tana son janyewa a kusa da shi ta tashi.
jin ba zai saketa ba ta buɗe ido ta kallesa tace,"ni wannan nake son sha ba magani ba, don Allah ka bar min".
bai san time ɗin da ya saki baki ba yana kallonta, in bai manta ba lokacin da aka kwantar da ita a asibiti uban malts ɗin da aka ajiye ai duk ƴan dubiya aka dinƙa bawa saboda bata sha, hasalima ko anyi forcing nata tasha sai tayi amansa, amma yanzu shi take ce malt take son sha.
sai ya sassauta riƙon
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 28 Chapter of 73