Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fi ƙarfin zaman gidanka ba wai dan muna tsoro ko kuma muna gudun abunda zaije ya dawo ba, a'a wallahi fin ƙarfinka tayi in ma faɗa maka gaskiya, akan me zata zauna a gidan daƙiƙi da daƙiƙiya alhalin ita da iliminta, to dan haka idan da kana tunanin cewa bata da gata shiyasa ka maki giya kaje aka maku kalar wannan watsatstsen auren to yanzu ka sani da gatanta, mutuwar ubanta ta bankaɗo mata daraja da ƙima da mutuncin da take da shi, ita ba salwantacciya bace da za'a kaita gidan da wata figaggiyar tsohuwa can zata ke kallonta banza a wofi, gwarama in saboda matarka ce nace Fillo ta daka shegiya daidai gwargwadon ikonta dan babu matsoraci a zuri'armu. in taƙaita dai, Turaki kake ko waye yanzu da muke wayar nan ka rubuta takardar saki uku rerass ka yo min aikenta, idan kuma kaƙi sakar min jika aradun Allah zan sa a ɗaure kaff zuri'arku, dan bani da kyau, mutunci ba isata yayi ba". Turaki ya rumtse idonsa sosai, farar ɗaya ciwon kai ya kama shi, ya rasa me zaice da Dada, idonsa ya dinƙa haska masa irin jalalar da Boɗejo ta dinƙa yiwa Maama da Mum akan auren nan da zancen tarewar Fillo da akai, cin mutunci babu kalar wanda bata yi musu ba, har da cewa zata sa Baffa ya sakesu su kama gabansu, tana faɗin wai Ilham ba zata zauna da kishiya ba itama ai ita ɗaya ta zauna, in ace dai wata Turaki ya aura to in goma zai yi babu abinda ya dameta, amma akan Ilham zata iya cinnawa kowa wuta a ƙone, sai taga ta inda wata shegiyar ƴar aiki zata raba miji da Ilham, banda ma dai ana so a bar masu abin kunya ace za'a haɗa ƴar sarki da ƴar aiki, to ba'a isa ba, yanzu dai baida sukuni ta hanasa sakat, bini bini ta kira shi tace ya saki ƴar aikin da yaje ya aura a titi babu waliyi. ya furzar da iska daga bakinsa yana ambaton innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, in da yasan haka auren yake me zai kaishi yin auren duka biyun. Bello nata tambayarsa me ke faruwa bai iya ce masa komai ba, har sai da Dada taji shirun yayi yawa sannan tace da shi,"baka ce komai ba, sai fa ka sakar min jikata, kaima ai ba ƙaunarta kake yi ba munafiki algungumi, kayi zaton gata ne bata da shi kaje ka maki giyarka ka aureta ta yanda zaka wulaƙantata, har da wani cewa tausayinta da taimakonta yasa ka aureta, a gidan uwar wa kake tausayin nata, yaushe rabon da ka waiwayeta?, ai dama duk me hankalin da yaji kalar wannan auren ya san na cin mutunci ne, to aradun Allah ko ka sakar min jikata ko babbar kotun duniya ta rabani da kai". a hankali Turaki yace,"kiyi haƙuri dan Allah Dada...". ta ɗaga murya wajen saurin katse shi da cewa,"kai bafa sulhu na kiraka muyi ba, in sulhun zan nema in kira waccan jarababbar Kakar taka mana, to ka daina bani haƙuri dan babu shi a tsakaninmu kuma ba zanyi ba, ka sakar min jikata kawai, yanda ake jinka ɗan gwal kai da matarka itama haka take ƴar gwal ba daga sama ta faɗo ba". ya ƙara cewa,"Dan Allah Dada...". Dada tayi ɗiff ta kashe wayarta, ta jefar da ita a ƙasa tai ɗakinta, Raudha tabi bayanta da kallo cike da takaici, yaushe aka siya mata wayar amma tana neman ta kashe mata ita. *Gombe, 11:00am.* a sanda suka gama wayar da Dada, Turaki ya baro office ɗinsa yana jin kansa duk ya cunkushe. Bello dake driving ɗin yace da shi,"karka sakawa kanka damuwa, komai zai warware insha'Allah". Turaki ya kallesa da jajayen idonsa cikin ƙaraji yace,"fisabillahi saboda mace sai in rasa kwanciyar hankalina, ta ko'ina ji nake babu daɗi, haba dan Allah". Bello ya sauke numfashi yace,"ba mace bace rashin kwanciyar hankalinka MT, kai ne ka jawa kanka matsalar duk da kake ciki, yanda kayi gaban kanka a auren nan dole ka fuskanci ƙalubale, in ace da izinin iyayenka kayi komai wallahi wannan matsalar ba zaka shigeta ba". "shiyasa nayi deciding rabuwa da ita ai tunda itama bata sona, but Maama da Mum sun hana, to ni zan haɗa har ita Ilham ɗin na sakesu, ba zan iya da wannan damuwar ba". ya faɗa daidai da sanda suka ƙaraso bakin gate, Bello ya bushe da dariya, kafin yayi magana tuni Turaki ya fice daga motar ya shige gida. yana shiga yayi kiciɓis da Boɗejo a compound tana ta masifa akan bai bi ta kan Ilham da bata da lafiya ba, ta tsayar da shi bai ko bi ta kanta ba yay wucewarsa side ɗin Hajiya Madina, kai tsaye upstais ya haye, yana zuwa yay knocking door, daga ciki Hajiya Madina ta ɗaga ido ta kalla bakin ƙofa kafin tace,"come in". ya murɗa handle ɗin ya shiga gabansa na faɗuwa, yana saka ƙafa suka haɗa ido, ba shiri ta ɗaure fuska kamar bata san shi ba, ta ɗaga masa hannu da cewa,"go back". ya marairaice,"please Maama i want to talk to you, dan Allah kiyi haƙuri akan laifin da ban san nayi miki ba". ta ɗauke idonta daga kansa tace,"nace ka fita ko". ya ƙarasa shigowa yana ƙoƙarin zube gwiwoyinsa a ƙasa, ganin hakan yasa ta miƙe zata bar masa ɗakin ba shiri ya rigata fita, ya fita yana riƙe kansa da yake jin kamar zai bar jikinsa. part ɗin Hajiya Ramla ya wuce, tana ganinsa ta ajiye cup ɗin dake hannunta tana tambayarsa,"Babana lafiya?". ta tambaya duk da tasan yana cikin matsala, amma yau ɗin tana ganin ba irin yanda ta saba ganinsa aciki ba, damuwar ta girmama. ya zauna akan kujera yana daɗa riƙe kansa ba tare da ya ce mata komai ba, ta baro dining area da sauri tazo ta zauna a kusa da shi, ta dafa kafaɗarsa tana cewa,"what is wrong with you Babana?, kai da Boɗejo ne?". ya ɗago ido kamar zai yi kuka yace,"Maama ce". "me ya haɗaka da Maaman?". ya kwantar da kansa a kafaɗarta yace,"almost 1week fa Mum ko gaisuwana bata amsawa, ban san laifin da nayi mata ba wallahi, and taƙi bani damar ma da zan bata haƙuri, na mata sending apology through text message and letter duk tayi ignoring ɗina, kuma ina so nayi magana da ita Mum". Hajiya Ramla na kallonsa da tsananin tausayi tace,"and duk ina ina hakan ta faru?". ya kama hannunta cikin sanyin murya yace,"kinyi busy da yawa a office Mum, kuma kinga Baffa ya hanani zaman gidan nan". ta sauke numfashi tace,"tashi muje". yace,"Mum ko munje fa ba zata saurareni ba, korana take yi". ta kama hannunsa kawai suka fita zuwa side ɗin Hajiya Madina, suna shiga parlo tana saukowa daga upstairs, taiwa Turaki kallo ɗaya ta ɗauke kai ta wuce kan kujera ta zauna, yabi bayan Mum suka ƙarasa ya zauna kusa da ƙafafun Hajiya Madina. Hajiya Ramla tace,"ina bayar da haƙuri a madadinsa Madam". Hajiya Madina ta kalleta tace,"bai faɗa miki laifinsa ba?". yay karaf yace,"ki faɗa min Maama zan gyara". nan da nan ta fara masifa tana cewa da Hajiya Ramla,"yaron nan saboda baida mutunci yana so ya mayar damu ƙanan mutane yaje dubai ince idan sun tashi dawowa ya taho da trollys amma ya kawo min guda goma sha biyu kacal, ba wannan ba ma!, nace ya haɗo lefe but sai ya turawa Zaytuna 1ML wai ta siya abinda taga ya dace, wato gamu faqararru da miliyan ɗaya zamu haɗa lefe ko?, in tambayeka ma! zatonka Fillo ƴar aiki daka sani a baya zaka kaiwa lefe da zaka kashe 1ML kacal?, to in haka ƙwaƙwalwarka ke faɗa maka ta yaudareka, Fillo ƴar aiki daban Fillon da zaka kaiwa lefe daban, in ka manta ka tuna gidan da kaje kayi gaisuwar mahaifinta, ka tuna irin mutanen da ka samu, ka san da cewa kenan tafi ƙarfin naira miliyan ɗayanka, Fillon yanzu ƴar gata ce gaba da baya kuma ƴar gidan manyan mutane, beside wallahi ko da ace Fillo ta nan a yanda ka santa tun farko baka isa ka kawo min lefenta na miliyan ɗaya na karɓa ba, kai ka san da cewa taimakonka da tayi tafi ƙarfin dukka arziƙin ubanka har da naka. to make it short, kaje ka sami ubanka Alƙali Dikko ka tambayesa lefen nawa suka haɗawa ƴarsu daga nan sai kayi abinda ka san zai ɗaga mutuncinmu ba wanda zai ja mutuncinmu ya zube ba, dan mu ba marowata ba ne". kansa a ƙasa yace,"Maama kiyi haƙuri amma wallahi bani na tura kuɗin ba, time ɗin account ɗina ya sami matsala kuma kaina ya ɗau caji da damuwar Boɗejo shine nasa Bello ya tura mata, kuma wallahi sai da nayi masa magana yace ai hakan ya isa wai almubazzaranci babu kyau". Hajiya Madina ta zare ido tana doka masa tsawa tace,"rufe min baki shashasha, shi Bellon da zai haɗa nasa lefen da 1ML ya haɗa da har ya mayar da kai ɗan iska, me yasa baka tuna masa check ɗin dana basa yaje ya haɗa nasa lefen ba?, ko kuma baka faɗa masa gidan da kaje ka sami Fillo a yanzu ba?, to wallahi wallahi ba zan kai iyaka akwatu sha biyu ba, kuma ba zan kai lefen miliyan ɗaya ba, tashi ka bar min parlo". ya ɗago ya kalleta kamar zai yi kuka, ya marairace yana roƙonta akan tayi haƙuri. tace,"fitar min a parlo tun ina ganinka da gashin ido, ai ba iyakarta kenan ba, nace kaje ka gano lafiyar matarka kaƙi zuwa yau kwana hamsin da wani abu, wanne kallo kake so mutanen nan suyi mana?, amma na lura da hakan bai dame ka ba saboda kana tare da zaɓin ubanka acikin gidanka ko?, kai kasan maganganu marasa daɗin da Boɗejo tazo ta yiwa mahaifiyarka yanzu kuwa?, kuma duk akan Ilham, me ta-ke nufi da mu?, auren nan muma da muke iyayenka muka haƙura da yanda kaje kayi gaban kanka balle ita, ta bar yarinya ta tare a ɗakinta amma ta hana kowa kwanciyar hankali, ba'a zama da kishiya ita uwar yarinyar ta zauna da kishiyoyi, haba dan Allah tun yaushe ake abu ɗaya, abu mitsitsi yaƙi ci yaƙi cinyewa, comon tariyar da za'ai lokaci ɗaya a wuce wurin ta hana rawar gaban hantsi, tabi tasa mahaifinka ya takura maka saboda kai baka da uwar da zata baka umarni ko me?, but shikenan zan yiwa tufkar hanci, idan ta san wata ai bata san wata ba, yanda ɗanta yake bin umarninta haka kaima zaka bi umarnin taka mahaifiyar, ai uwa bata fi uwa ba". ɓacin ranta na ƙara tsananta ta waiga gefenta ta ɗauko jotter, ta falli takarda ta jefa masa da biro tace,"umarni nake baka ba ja'inja nace muyi ba, ka saki Ilham saki ɗaya". yay saurin ɗago kai yana kallonta,"Maama in saketa kuma?". ya kulle ido yana jan ajiyar zuciya,"Maama itama fa Fulani Kakarta tace sai na saketa". ta buga masa tsawa tace,"ba batun Fillo nake yi ba yanzu, ka fara sakar musu ƴa tukunna". sannan ta kalli Hajiya Ramla tace,"umarninki ne a matsayinki na wacce ta ɗau cikinsa wata tara ta kuma haife shi da wuya bata sauƙi ba, kamar yanda itama take jin ta ɗauki cikin wata tara ta haife bata sauƙi ba, idan ta cije ki fita cijewa, kin sa ya saki Ilham kuma ba zai saki Fillo ba". ta ƙara maida kallonta kan Turaki tace,"nace ka sakar musu ƴa ko". babu shiri ya shiga rubutu, _Ni Muhammad Habib Dikko na saki Rumana Hashim saki ɗaya._ ya gama rubutun daidai da faɗowar Boɗejo parlon, kuma daidai da shigowar kiran Dada a wayar Hajiya Ramla.... *Comment, share and vote.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _avoid error mistakes._ *45* Boɗejo ta ƙara ɗaure fuska a sanda take isowa kan Turaki ta tsaya. "mara mutuncin banza da wofi, kai har nawa kake da zaka raina ni?, har ni ina maka magana ka yi banza da ni ka ƙaro gaba wato ga ƙatuwar shashasha na yi maka magana ko?, ko da yake babu komai, ba ni karaina ba ubanka ka raina". ta gyara zaman gyalenta tana saka hannu ta ɗago kansa sama,"wallahi bari kaji na faɗa maka kayi kaɗan kace zaka wulaƙanta min Ilham, sanin kanka ne kaf jikokina na fi ƙaunarta, ba'a haifeka ba ba'a haifi uwar da zata haifeka ba, ɗan iskan banza yaushe kaciyarka ta girma har da kake jin kafi ƙarfin kabi umarnina da na ubanka. kai ka sa ni dai Ilham tafi ƙarfin wulaƙancinka, domin kuwa ta fika gata, ita ɗaya a wajen uwarta bata taso ta san wata aba damuwa ba, saboda haka baka isa kace zaka haɗata da kishiya ba, kishiyar ma mara aji ƙasƙantacciya wadda tayi aiki a gidanku, haba dai cin mutunci haka har ina!, a wanne garin mahaukatan ma ka taɓa jin an yiwa mace kishiya alhalin ko shekara bata rufa ba, ka tambayi uwarka kaji shekarun da ta rufa bata taɓa ɓatan wata ba kafin ayi mata kishiya, duk da dai na san cewa ba kowa ke zugaka ba illa waɗannan munfukan marasa yafiya da haƙuri". ta faɗa tana nuna Hajiya Ramla da Hajiya Madina da baki tana bin su da harara. "kuskure uban waye ba ya yinsa, haka laifi uban waye ba ya yinsa, ku waye ya san adadin laifin da ku ka yiwa ubangiji kuma ku ka roƙe shi ya yafe muku. dan uwar yarinya tayi masa laifi ai ba yana nufin yarinyar ce da kanta tayi masa ba, ku wa yasan kalar mutanen ma da ku ka yiwa sharrin da yafi wanda tayi masa, kuma naga dai anyi shekara da shekaru da yin abun, kuma ke Madina bace kika yi kun yafe ba, amma saboda dai zuciyarki baƙa ce sai yanzu za ki wani fa-ke da abunda aka riga aka manta da shi, saboda dama kina baƙin ciki da gatan da Allah ya yiwa Ilham wanda ƴaƴanki basu samu ba, to kuwa sai dai ki haɗiyi zuciya ki mutu domin gata da mulki da jin daɗi da ilimi da tarbiyya Ilham ta yiwa ƴaƴanki zarra, har a naɗe duniya kuma ba zasu samu abunda ta samu ba". ta maida hankalinta kan Turaki,"mara imani wanda bai da tausayi, yarinya bata da lafiya amma ka iya tsallaketa kasa ƙafa ka bar gidan saboda ga ka baƙin mugu azzalumi, to idan ba ka sa ni ba ka sa ni, akan Ilham ina iya ɓatawa da uban kowa, in nace uban kowa har da nata uban kuwa, ka ga kenan naka uban ba komai ba ne a idona. saboda haka yanzu tun muna ta lafiya lafiya ban ja abinda zai hana kowa kwanciyar hankali ba to ka miƙe ka wuce muje ka kaita asibiti, shege ɗan banza ka samu ka ɗirkawa yarinya ciki shi ne za ka watsar da ita, to miƙe mu tafi, alhakin kulawa da ita ai akanka ya ke yanzu ba'a kan iyayenta ba". shi dai kansa har lokacin na ƙasa yana ta kallon rubutun sakin da yay, ya rasa gaba ɗaya me ma yake ji a tare da shi, tsabar bala'in ciwon da kansa ke yi masa ji yake kamar zai bar jikinsa. sai da Boɗejo ta kai bakin ƙofa tukunna ta waigo tana ƙara cewa,"wai kuwa ba zaka taso ba?, ka san Allah in har wani mummunan abu ya sami Ilham sai nasa an ɗaureka". tayi ƙwafa tana bin su Hajiya Madina da wani kallo na ban haushi tace,"algungumai duk ku biyun da ba ku da aiki sai saka yaro agaba kuna kimtsa masa yanda zai bijirewa umarnin ubansa, yau zan gani sai dai ko ni ko ku acikin gidan nan muddin ba'ai abunda nake so ba, dan ya zama dole yau a saki waccan yarinyar, domin a yanzu dai Ilham ba zata zauna da ita ba har sai ta haife abinda ke cikinta, zan nuna muku na isa zan kuma nuna muku kaf a ƙasana ku ke, munafukai biyu masu son raba zumuncin ƴan'uwa, abokan sheɗ...". ba ta ƙarasa ba Turaki ya dakatar da ita a fusace,"ya ishe ki Boɗejo, zan lamunci duk kalar rashin mutunci amma banda cin zarafin iyayena a gaban idona. haba don Allah don Annabi, duk kin bi kin hana kowa kwanciyar hankali akan wata banza yarinya can, idan tafi ƙarfin a wulaƙantata me yasa kika na ce aka aurawa wanda ba ya sonta ba kuma zai taɓa sonta ba". bai san lokacin da ɓacin rai ya kaisa ɗaga ɗan yatsa ya na nuna ta da shi ba. "kina cin darajar kin kawo mahaifina duniya ne shiyasa nake ɗaga miki ƙafa akan irin cin kashin da kike yiwa Maama da Mum, darajarsa kike ci nake yi miki duk kalar wata biyayya da girmamawa, banda haka wallahi da comon inuwarsu aka ce ki yiwa kallon banza ba za kiyi ba, da tun na farko da kika yi ba za ki so ki ƙara na biyu ba. saboda haka yau ta zama rana ta ƙarshe da za ki ƙara ɗaga muryarki akansu in ba haka ba zanyi abunda ban taɓa yi ba". kai da ganin yanda yake maganar ka san ya fusata, kamar ma zai kaiwa Boɗejo hannu, Hajiya Madina ta kallesa ta sauke idonta ƙasa leɓenta na talewa da murmushi, alamun taji daɗin abinda yayi. Hajiya Ramla tai saurin miƙewa tana sauke hannunsa da yake nuna Boɗejo da shi,"me haka Babana?, kar fushi yasa ka aikata ba daidai ba, yi haƙuri komai yay farko ai zai yi ƙarshe...". yana kallon Bodejo da ta saki baki tana kallonsa da tsananin mamaki ta taho gare shi yace,"ai komai ɗin ma yazo ƙarshe, ba zan iya ci gaba da ɗauka ba". ya faɗa yana barin kusa da Mum ya ƙarasa gaban Boɗejo kafin ta iso gare shi, ya miƙa mata farar takardar da ke hannunsa yana cewa,"na gaji, na gaji da masifarki da neman tashin hankalinki, gaba ɗaya kin hana kowa sakat, to ina buƙatar Mum da Maama da Baffa su sami nutsuwa hankalinsu ya kwanta su huta da fitinarki, nima kuma ina da buƙatar nawa hankalin ya kwanta, ba cikakkiyar lafiya gare ni ba so ba za ki kwantar da ni ba". ya manna mata takardar ajikinta. "ga shi nan ki samawa kowa lafiya". Boɗejo tayi mutuwar tsaye ta kasa ko motsi, bin sa kawai ta-ke da ido, taji ƙirjinta na bugawa kafin ta iya ɗaukar takardar tana duddubawa, tayi masa kallon tsab sannan tace,"wannan kuma na menene?". bai ce da ita komai ba ya nemi kujera ya zauna yana dafe kansa, Khalil ya shigo a lokacin tayi saurin dakatar da shi daga hawa upstairs da yake shirin yi. "zo, zo nan Khalil". ya dawo ya tsaya gabanta, ta miƙa masa takardar hannu na rawa,"duba min mene aka rubuta a ciki". ya warware takardar, kalmar NI da ya fara cin karo da ita tasa shi ɗago ido ya kalli Mum sannan ya kalli Maama sannan ya juya bayansa ya kalla Turaki. Boɗejo ta doke shi,"na ce ka karanto min abunda aka rubuta ba wai ka bi su da idanu ba, sanin su ne baka yi ba komai". ya sauke gwaron numfashi yana murza idonsa da kyau sannan ya shiga karanto ma ta abinda ke jiki tiryan tiryan. Boɗejo ta lailayo wata uwar ashar ta yarfa a sanda ya gama karantawa, ta fizgi takardar da ga hannunsa ta isa gaban Turaki ta wurga masa. "kai ka isa, ka isa ka saki Ilham, to bilahillazi samun kwanciyar hankalinka da na iyayenka shi ne ka mayar da auren nan". Maama ta miƙe zata bar wajen tayi saurin dakatar da ita cikin hargowa,"tsaya baƙar munafuka, gidan uwar wa za ki je da kika miƙe sim sim za ki tafi?, ai na san ba kowa yasa yayi sakin nan ba sai ke algunguma, wallahi ban san Dikko annoba ya kawo cikin gidansa ba sai yanzu, Madina!, baƙin kaidin ki har ya kai haka Madina?, to kuwa tunda kika sa ya saki Ilham, sai kin sa ya saki ɗayar ko kuma ke ma in sa a sake ki". Hajiya Madina taji wani abu ya taso mata, tayi saurin haɗiye shi da ambaton Allah. Boɗejo ta miƙo mata takardar tana faɗin,"yanda kika sa ya saketa haka za ki sa ya mayar da ita, ungo nan ba shi". Maama na kallonta tace,"na san ina da babban matsayin da zan iya sawa ya saketa, amma ban yi hakan ba tun farko, ki daina alƙanta sakin jikarki da ni, ba ni na saka shi ba, wadda take ganin ta isa da shi kaf duniya itace ta ba shi wannan umarnin ba ni ba, kuma saboda gujewa fushin ubangijinsa da kuma taɓewar duniya yasa ya bi wannan umarnin". Boɗejo ta bi Mum da kallo kafin tayi ƙarfin halin ce ma ta,"Ramla kika sa ya saki Ilham?". Mum ta kawar da kanta gefe tana jan yatsunta tace,"kiyi haƙuri, amma abinda nake ganin ya dace shi na sa shi ya aiwatar, hakan shi kaɗai zai sa hankalin kowa ya kwanta, da ga mu har ke har kuma ita yarinyar". mayafin Boɗejo ya zame ya faɗi. "haka kike Ramla?". ta tambaya da tsananin mamakin Mum ɗin, wanda take tantamar da ƙyar idan ita ce tasa Turaki yayi wannan sakin. Mum ta fuskanceta tace,"ba zance haka nake ba ko ba haka nake ba, amma idan hakan bai yi miki daɗi ba Allah ya huci zuciyarki. naga masalaha ake ta nema tuntuni, wanda kuma ta hakanne kaɗai za'a samar da ita. kiyi haƙuri da abinda zan faɗa, ina son farin cikin ɗana, ina so ya sami kwanciyar hankali da nutsuwar da ya rasa tun daga ranar da ya auri Ilham...". "dakata! me kike so ki faɗa min?, so kike kice an aura masa annoba da har kike faɗar ya rasa kwanciyar hankali. to cikin ku biyun kar wadda ta ƙara ambatar min kalmar tashin hankali anan, tashin hankali na can wurin shegiyar yarinyar da yaje ya aura a titi, kuma tunda kika sa ya saki Ilham, to ya zama dole kisa shi ya saki waccan yarinyar da ban yarda da asalinta ba, ba zan taɓa yarda a kawo mana gurɓatacce cikin zuria'armu ba ku san da wannan, dan haka ba shi umarni ya saketa". Mum ta rufe ido ta buɗe sannan tace,"ina son rayuwar ɗana, ban shirya rasa shi a yanzu ba, kamar yanda nake tsananin son farin cikinsa, hakan yasa ba zan taɓa raba shi da abunda yake farin cikinsa ba. idan kika ce lallai sai ya saketa hakan zai zama barazana ga rayuwarsa, domin kuwa uwar gidansa itace rayuwarsa, rabuwa da ita dai-dai yake da rasa ransa, saboda haka ni ba zan sa ya saketa ba, dan Allah kiyi haƙuri a bar min yaro ya huta haka, kamar yanda ɗanki yake so ya rabu da ke lafiya haka shima yake so ya rabu da ni lafiya, sam ba zai iya ƙetare umarnina ba". Boɗejo ta nemi kujera ta zauna tana salati, ta dafe kai tana girgiza shi,"yau naga abinda ban taɓa gani da ji ba a tarihin rayuwata, ni yau ake bijirewa umarnina, ni yau ake ja-inja da ni. Ramla da Madina me ku ka taka?, me Azima tayi muku da ku ka tsani ƴarta haka?, zumuncin da ubangiji yace a yi shi ku ke so ku rushe yau?...babu komai bari Dikkon ya shigo". ta miƙa hannu ta ɗauko jakarta da ta tangarar a ƙasa ta ɗauko wayarta, da ƙyar ta iya lalubo lambar Baffa dan ta san duk wanda tasa ya nemo mata ayanzu ba zai nemo ba. ringing biyu ya ɗaga, ta amsa sallamar tana cewa da shi,"kana ina?". "ina gida". "kana cikin gidan naka ka barni da matanka suke min rashin mutunci suna gaggaya min maganganun da suka ga dama?, Dikko kana so ka gama da duniya lafiya kuwa?, to ka bar duk wani abu da kake kazo ɓangaren Mandina yanzu dan babu lafiya". tana faɗar hakan ta kashe wayarta, idonta akan Turaki da har yanzu yake dafe da kansa, dana sanin aurensa duka biyun fal cikin ransa. mintunan da basu wuce biyar ba Baffa ya shiga parlon Hajiya Madina, tun daga baƙin ƙofa yake kallon Hajiya Madina da Kuma Hajiya Ramla waɗanda ke tsaye sun kasa zama, ya ƙaraso ciki da sauri wajen mahaifiyarsa ya zauna a ƙasa yana cewa,"ranki ya daɗe gani, lafiya dai?". "ina kuwa lafiya Dikko". ta faɗa tana ɗauke ido daga kansa ta mayar kansu Hajiya Madina tace,"waɗannan marasa mutuncin matan naka sun sa yaron nan ya saki Ilham". with shock Baffa ya ɗago yana kallon Maama, Boɗejo tai saurin cewa da shi,"a'a ai ba ita ce tasa yay sakin ba, gata nan ita ta saka shi ya saki matarsa saboda bata tsoron Allah bata gudun girgizar al'arshin ubangiji". ran Baffa a ɓace ya miƙe yana kallon Hajiya Ramla. "kika sa ya saki Ilham?,

Chapter 49 of 73