ɗauko wasu sabbin kaya irin na ƴan turkey, kayan da Baffa ya tahowa da Nihal ne tsaraba, ta ciro set biyu aciki ta bawa Fillo tace,"ungo kiyi maza kije ki shirya yana parlon baƙi yana jiranki tun ɗazu".
Fillo ta kalla kayan sannan tace,"Maama zanje da waɗannan ma". ta girgiza mata kai tace,"daga wurin suyar waina fa kika taso, haka zaki je wajensa kina tsami?, salon ya raina min ƴar tawa tun yanzu...a'a je ki gyara jikinki shaf shaf kije ki samesa dan ya jima kusan 15minutes, in kin dawo kizo ki min list na abinda kike so na siya miki".
Fillo ta amshi kayan tana ta zuba godiya ta fita, fuskarta kawai ta ɗauraye ta ɗauki turaren Ɗausiyya ta fesa, sosai tayi kyau acikin kayan kamar dama dan ita aka siyo.
haka kawai sai take jin sam bata ƙaunar zuwa wurin Amir, alhalin tun randa aka kawo kayan sa rana ta ke ta so ta gansa, kwana 5 tasan tayi kewarsa sosai da soyayyarsa, tunda in sunyi waya ma faɗa suke, bata saka mayafin kayan ba tasa hijab saboda yanda ta jita uncormfortable a riga da wandon.
ta tafi tana ta ɓata fuska, ji take kamar har yanzu bata huce daga haushin Amir ba, kamar ranar nan da ta kulasa ba ita bace, kamar yau idan taje zata yi masa wulanci ne wanda zai sa ba zai ƙara dawowa ba.
sanda ta shigo parlon ya miƙe a zuciye zai tafi, ganinta kuma yasa ya tsaya yana sauke ajiyar zuciya cike da farin cikin ganin nata.
tun daga kan yatsun ƙafarta yake kallonta har zuwa kan fuskarta, last da yazo ta fita da mayafi bata yi masa kyau irin yau ba da take acikin hijab. ta tsaya daga bayan kujerar da yake tana cin magani bata ce masa komai ba.
ya harɗe hannayensa a ƙirji yace,"nai zaton ai ba za'a barki ki fito ba dan naga wani iko ake nunawa dake a gidan nan, ko basu san tawa bace?". tai masa shiru tana ƙara ɗaure fuska tana jin kamar ta juya ta koma.
sai taji yay ƙasa da murya cikin amo na shauƙin so yace,"fushi ake dani har haka da ba za'a min ma smiling ɗin nan dake melting heart ena ba?, zunubin me na aikata wanda ban sa ni ba gimbiya?".
sai kuma ya kama kunnensa yace,"am sorry, ba zan ƙara ba insha'Allah, kar a kuma yi min horon da zuciyata ba zata iya ɗauka ba this time around".
ba tare da ta kalle shi ba tace,"tunda nace maka ka bari zan saka maka ranar zuwa ai sai ka bari ko, ba wai ka ɗauko ƙafa ka taho ba notice ba".
yay murmushi yana zagayowa inda take tsaye, ji yake kamar ya rungumeta a duk sanda yake tare da ita.
yace,"kiyi haƙuri nayi kuskure, kasa haƙuri nayi wallahi, 5days ɗin nan ji nai kaman an shekara 5".
ta daɗa ɓata rai tace,"to ni aiki nake yi yanzu, Baffa ne zai yi baƙi anjima kaɗan muna aiki".
ta faɗa tana ƙoƙarin barin wajen, zai riƙo hannunta tayi saurin janyewa tana cewa,"bafa kyau ka daina min irin haka, ni ban ma san yaushe ka lalace irin haka ba na taɓani".
yay dariya sose yace,"tsabar ƙauna ce, amma ba zan ƙara ba daga yau, zan jure zuwa ranar da za a kai min ke...yanzu dai kafin ki tafi dan Allah kiyi min murmushi ko zan sami sauƙi".
ta ƙara cin magani tace,"ba zaka samu ba kam, kaga tafiyata".
ta faɗa tana wucewa sai ya daɗa dakatar da ita da cewa,"sorry na manta. Kaka tayi min magana akan siyar da filayenki guda biyu saboda hidimar biki da zata yi da su, to na faɗa mata cewar za'a bada takardu tace suna wurinki ke kika adana su, yanzu ya za'ai?, saboda an sami wanda zai siya da tsoka dan kowanne zai iya siyansa 1Ml".
ta juyo ta kallesa tace,"Kakan tace maka za'a sayar min da fili saboda hidiman biki?".
ya ɗaga kafaɗarsa,"yes, in kin koma zata daɗa miki bayanin hakan. ko na kira Yami sai kiji daga bakinta?".
tace,"tabɗijam, ashe gwarama da Allah yasa na ɓoye takarduna, to aiko babu me sayar min da fili ko guda ballantana har filaye 2. ayi haƙuri kamin lokacin Allah zai bada yanda za'ayi duk wata hidima...ka gaida su Inna sai anjima".
ta faɗi hakan tana ficewa daga parlon ta bar Amir da sakin baki yana binta da kallo fuskarsa na nuna damuwa da rashin jin daɗi.
in ya lura kamar yanzu bata son auren nasu dan ƙarara yaga hakan a fuskarta, me ke shirin faruwa ne?, wani ne ya hure mata kunne a lokacin da sukai faɗa da shi?, waye shi?, aina yake?.
sai yaji wani bala'in kishi ya tokare masa zuciya, a fusace yabi bayanta dan jin amsar tambayoyinsa sai dai yana fitowa compound ɗin ya tarar babu ita, haka ya bar gidan zuciyarsa na masa ƙunci.
da daddare Fillo na kwance a ɗakinsu wajen 9 na dare, time ɗin sun gama karatu ita da Ɗausiyya, suna hirar duniya Fillo kuma cikin ranta tana ƙudurcewar gobe zata cire tsoro taje ɓangarensu, ta kuma bawa Kaka shawaran kar a sayar da fili ko ɗaya gwarama a sayar da dabbobinsu.
wayar ɗakin tayi ƙara Ɗausiyya ta miƙe tana mita tai picking call ɗin.
daga ɓangaren Zaytuna tace,"Ɗausiyya Fillo tayi bacci ne?". tace,"a'a". "to ce mata tazo da sauri please". tace,"tom Adda".
ta ajiye wayar tana kallon Fillo da har ta rufa bacci ya fara ɗaukarta, tace,"kije Adda Zaytuna na kiranki".
ta sakko daga kan gadon tana yamutse fuska saboda baccin dake cinta, veil ɗin da ke ɗaure akanta ta warware ta yafa ta fita.
cike da tsoro ta fito compound, tana tafe tana dube-dube har ta ƙarasa sashen su Zaytuna, ta buɗe ƙofar ɗakin Zaytuna ta shiga bakinta ɗauke da sallama, ganin Zaytuna bata ɗakin ta tsaya gefe tana jan yatsun hannunta, bacci sai daɗa fusgarta yake, Zaytuna kuma na toilet tana wanka, jin sallamar fillo yasa ta ƙwanƙwasa ƙofar toilet ɗin, wannan yasa Fillo neman kujera ta zauna tana ta jera hamma.
wayar Zaytuna dake kan gadonta tayi ringing har sau biyu, ana ukun ta leƙo a toilet ɗin tace da Fillo,"ɗaga please ko waye kice bana kusa".
Fillo ta miƙe tana layin bacci taje ta ɗau wayan, dai-dai lokacin kiran ya katse, sai kuma ya ƙara shigowa, sai da zata yi picking tayi noticing vedio call ne, ta ɗaga murya wajen faɗawa Zaytuna cewar Vedio call ne.
Zaytuna tace mata,"wane sunane jiki?". tace,"DH". tace,"just pick".
Fillo ta gyara zaman gyalenta tai picking call ɗin tana kauda fuskarta daga kan screen ɗin wayar, call ɗin nayin connecting tace,"bata kusa, idan ta dawo zata kira".
daga hotel ɗin da Turaki yake zauna kan gado ya lumshe idonsa sannan ya buɗe yace da ita,"ke kuma kina ina?". tace,"ina ɗakinta ita kuma ta fita".
Turaki dai so yake ta haska fuskan nata gaba ɗaya amma taƙi, sai side face ɗinta da yake kallo, ita ba ta ɗauki muryarsa ba ma, ya san halinta zata iya tai droping wayar ko kuma ta bar wayar a haka taƙi haska fuskan ba tare da ta ƙara cewa komi ba har sai Zaytuna ɗin tazo.
ya miƙe daga kishingiɗen da yake ajikin pillow ya zauna sosai sannan yace,"bata ɗakinta ta fita, ke kuma kika shigo har kike ɗaga mata waya. what those that means?, stealing or snatching or what?".
ai furucinsa na ƙarshe yasa Fillo bata san ma sanda ta haska screen ɗin wayar gaba ɗaya ba a fuskanta, ta cune tana ɗaga gira duka biyun sama tace,"banyi kama da ɓarauniya ba balle in tsaya ɓata lokacina kan snatching, kuma ai ita me wayan da kanta tace in an kira na ɗaga, if not ba zan taɓa picking ba ko za'a dawwama ana kira".
tai maganar tana murguɗa ƙaramin bakinta, dan ko waye ya bata haushi ya ɓata mata rai, duk da ba'a son ranta ta faɗi hakan ba, stealing fa!, ya san mene ma'anar danganta wani da sata?
Turaki yay murmushi sai kuma ya ɗaure fuska yace,"ni kike faɗawa haka?, sa'anki ne ni?". sai a lokacin ta ɗauki muryarsa, a tsorace ta murza idanuwanta tana ƙifƙifta su, ta shiga uku ita ce kalmar da ta ambata cikin ranta. sai taji ƙirjinta na duka a lokaci ɗaya, ta marairace fuska tana yin kamar zata yi kuka tace,"kayi haƙuri ban san kai bane".
ya ƙara tamke murya yace,"ɗago kanki ki kalle ni". ya faɗa muryarsa a ɗage. ta ɗago kanta tana dab da fashewa da kukan dake ƙasan ranta, ta tsana, ta tsani wannan ɗaga muryar da yake mata. kuma a yau babu abinda zai hanata faɗa masa kar ya ƙara raising mata wannan voice ɗin nasa.
so tayi itama ta ɗaga murya wajen faɗa masa ta yanda zai shaida gargaɗinta garesa, amma sai taji muryarta tayi sanyi tana ce masa,"bana so kake ɗaga murya haka dan Allah".
Turaki ya shafo wuyansa yace,"are you commanding me?". ta girgiza kai ba tare da tace komai ba tana sa hannu ta goge hawayen da ya sakko mata. sannan tace,"Adda Zaytuna ɗin wanka take yi, zan faɗa mata idan ta fito".
ta faɗa tana ƙoƙarin kashe wayar yay saurin dakatar da ita, shin bata san tun randa ya taho ba ya rasa natsuwarsa saboda tunaninta, tunanin halin da take ciki, bata san tun ranar da ya taho ba yake jin fargaba akanta ba, kuma tun da ya sauka a kowanne bugar sakan na agogo so yake ya ganta, yaga motsinta, yaga yacca lafiyarta ke ciki, bata san a daren yau ya rufe ido yafi sau 5 ba amma ya kasa baccin duk saboda yana so ya ganta, ko ya samu hankalinsa ya kwanta, ko wannan faɗuwar gaban ta bar shi.
ya tausasa muryarsa yace mata,"ce nayi ki ɗago ido ki kalle ni bawai ki kashe wayar ba".
da ƙyar ta iya samun courage ta ɗaga ido ta kallesa tana jin ƙirjinta na ta duka, sai dai kallo ɗaya da tayi masa sai ta kasa ɗauke idon nata gaba ɗaya, wannan tsoron ganinsa ɗin da take ji sai taji ya yaye, taji tana so ta kalle shi tai ta kallonsa.
kallonsa take yi ta kasa ɗauke idonta a kansa, zata iya cewa kamar ya rame, kamar yana cikin damuwa, kamar yana buƙatar wani abu.
ya katse tunaninta da faɗin,"kina da matsala ne?".
har yanzu idonta na kansa tace,"me ka gani?". yace,"me ya sami idonki?". ta lumshesu tukunna tace,"bacci nake ji".
muryarsa na ƙara yin ƙasa yace,"bayan bacci fa?".
tace,"ba komai".
yace,"are you sure?".
tace,"yes".
ya ƙara kallonta sosai sannan yace,"daga tuesday zuwa yau faɗa min kalar fitinar da kika yi".
ta waro ido waje taje,"fitina kuma?, ai ni bana fitina, da hankalina".
ya murmusa kunci sosai yace,"kuka fa?".
sai ta sami kanta da ba shi amsa kai tsaye da cewar,"ai dama kaine kake sa ni kukan, kuma baka nan".
yace,"really?". tace,"yeah".
leɓensa ya tale da murmushin da bai shiryawa ba yace,"magani fa?". ta cune fuska tace,"wannan ma ai kaine kake min dole, kuma da baka nan duk bana sha".
yace,"abinci fa?". ta juya idonta tana jin baccin na ƙara zuwa tace,"ina ci mana". ta faɗa tana ɗan shagwaɓe fuska.
Turaki yay shiru bai ƙara cewa komai ba, tsawon 30seconds kallon siraran yatsunta kawai yake da ta tallafe haɓarta da shi.
sanda ya buɗe baki zai ƙara yin magana sai ta riga shi da cewar,"yaushe zaku dawo, Maama duk ta damu".
yace,"ba yanzu ba sai next year". jin hakan bata san sanda ta ɗago ido ta kalle shi ba ta maimaita abinda yace,"next year kuma?".
ya ɗaga mata gira,"yes, Maama zata zo idan tana son ganina, also Zaytun. ko bayan su akwai wanda ya damu da rashina ne?".
tayi shiru bata ce komai ba duk da tana so tace wani abu ɗin.
Turaki yace,"oya kashe wayan, dare yayi Kaka na can na jiranki". ta ɗan kalle shi tace,"to naga duk ka rame, baka da lafiya ne?, ko wani abu yana damunka?".
yace,"lafiyata lau, ina dai kewar Mum ne".
tace,"wacece haka?". ta tambaya as if bata san komai ba.
yace,"Yayar Maama ce, ta daɗe da ɓata bamu ganta ba har yanzu, ki tayamu da adu'a Allah yasa mu ganta very soon. ko idan na dawo za ki taimaka min mu nemota?".
yanayin yacca voice ɗinsa ya fito sai taji tausayinsa sosai, tace,"ka san inda za'a ganta ne?".
yace,"a'a, kawai dai jikina na bani kamar ke za ki ga inda take". tace,"sai dai na tayaku da adu'a, amma ni ban san aina zan ganta ba".
yace,"adu'an ma mun gode. bye". da sauri tace,"da gaske sai next year?". ta tambaya tana tsare shi da ido. sai taga kamar yayi murmushi sannan ya ɗaga girarsa alamar ehh. ta sake cewa,"to kana kula da kanka?". ya girgiza mata kai alamun a'a ba tare da yay magana ba.
tai ajiyar zuciya kamar zata ce wani abu sai ta fasa, haka ɗaya take jin bata so ya yanke kiran, haka ɗaya take ji kamar idan ya kashe wayar shikenan ba zata ƙara ganinsa ba, hakama kamar ba zata ƙara jin voice ɗinsa ba.
ya katse shirun nata da faɗin,"kin daina jin baccin?". ta ɗaga kanta,"ehh ya tafi. ba zaka jira Adda Zaytuna ɗin ta fito ba?". ya girgiza mata kai baice komai ba. tace,"tom shi abokinka ɗin da kuka tafi tare fa?".
yace,"ba sa wayar zanyi?".
ta tura baki gaba tace,"ince masa me?, tambaya nayi ko yana kula da kai".
Turaki na murmushin leɓe yace,"ai ba wanda ya biyasa kuɗin kula da ni. shima ta kansa yake".
tace,"to magani fa?". yace,"haka kawai ake shan magani da ma?". tace,"ai kai baka da lafiya".
daga ita har shi ba wanda ya ƙara cewa komai, tana ta gyangyaɗi riƙe da waya yana kallonta, ƙarshe sai kashe wayar yayi ganin kaman tayi nisa a gyangyanɗin. Zaytuna na fitowa ta sameta akan gadon ta ɓingile tana bacci riƙe da waya a hannu, ta tasheta ta gyara kwanciyarta akan gadon.
washe gari Fillo dai bayan sun gama aiki, leeson teacher nasu ya tafi ta kama hannun Ɗausiyya tayi mata rakiya ɓangarensu.
tana shiga ta faɗa jikin Kaka ta rungumeta cike da murna, Kaka tace,"ai ce nake kin koma can gaba ɗaya?".
Kaka tayi maganar itama cike da jin murnar ganinta, kamar sun shekara basu ga juna ba.
Maijidda ta kama hannunta ta jata zuwa cikin ɗaki tana cewa,"yarinya zo kiga kayanki. wallah sunyi kyau harda irin shaddar ƴar gidan Mamu aciki".
Fillo dai tunda ta zauna gaban ƴar ƙaramar akwatin, kallon yacce Ɗausiyya da Maijidda ke aikin fito da kaya kawai takeyi. ita dai ji take kamar bata murna bata farin ciki da ganin kayan, kuma kamar tana farinciki ta dai rasa taƙamemen abinda take ji ɗin.
har la'asar suna zaune, Maijidda da Zakiyya itama Jikar Yami da tazo hutu har Ɗausiyya suna ta tsara abubuwan da zasu yi lokacin biki. Zakiyya na cewa,"ke Fillo kike cewa ai kar a fara shiri yanzu, lallai baki san halin lokaci ba. to wallah yanzu za kiga wata biyun tayi, gwara duk abinda kika san zaki yi ki fara shi tun lokaci bai ƙure miki ba".
Maijidda ta janyo Fillo jikinta ta raɗa mata abu a kunne tana dariya, Fillo tayi tsaki tana tureta. Maijidda suka tafa ita da Zakiyya suna tsokanar Fillo da cewar,"an matan Amir an kusa shiga sahun manya". Fillo dai babu wanda tanka.
Yami ta shigo ta ƙwalawa Fillo kira ta fito, tazo ta durƙusa tana gaida Yamin, itama Yami na tsokanarta da cewar ai tayi zaton kunyar ba zata ƙara barinta shigowa ba har ai auren.
kunya ta ƙara kama Fillo, Yami ta miƙa mata robar wani magani tace,"shanye wannan yanzu". ta karɓa ta shanye da ƙyar duk ba wani rashin daɗi ne da shi ba.
sannan Yami ta ƙara ce mata,"kun gama jarabawar?". tace,"za dai mu fara Yami". tace,"to za ki ke samun shigowa kullum ko na haɗa miki magungunan ki tafi da su?".
tai shiru bata ce komai ba tana kallon tulin wasu takarcen magani iri-iri, dama tun washe garin da aka kawo kayan Maijidda ta fesa mata labari wai Yami tasa a kawo mata magungunan da zasu gyarata tun daga sokoto da niger, ita dai haushi ne ya tuƙeta a lokacin saboda taƙi jinin taji ana cewa,"maganin mata ko kuma maganin gyara mace".
Yami ta ware wasu ta zuba a leda tace,"gasu nan ki tafi da su, basu da ɗaci babu bauri babu komai, su zama sune ruwan shanki kinji ko. wannan kuma haɗin zuma ne itama kike sha akai-akai, dan Allah Fillo karki mana asarar kuɗinmu, in kin mayar da hankali kinyi amfani da su kanki kika taimaka".
ita dai Kaka na daga gefe tana jinsu, bata ce komai ba har sai da Yami ta gama sannan tace,"da ki haɗa mata da wannan ruwan tsarkin ko, tunda naji Babuwan tace shima da wuri zata fara amfani da shi".
Yami tace,"kinga kuwa na manta, shi da tace ma ya rage wata biyun zata fara amfani da shi".
nan dai Yami ta haɗa mata duk abinda ya kamata ta kuma yi mata bayani.
wajen biyar da rabi na yamma Hajiya Madina ta kira Fillo tace taje ta ɗauko mayafinta tazo ta rakata anguwa. wata sabuwar shadda da Maama ta ɗinka musu ita da Ɗausiyya ta saka, shaddan ash colour me duhu, an mata ɗinki me kyau ajiki kai ba kace ɗinkawa akayi dan a bawa ƴan aiki ba.
tana zaune a parlo Hajiya Madina ta sauko daga stairs, waya ce riƙe a hannunta suna vedio call da Turaki, tana faɗa masa irin yacca kowa ke missing ɗinsa har Baffa, tana basa labarin Ilham ma jiya ta ke cewa zata biyo shi sai taji cewar baya Hong kong yanzu.
irin yacca suke hirar kamar ba ɗa da uwa ba. Bello a gefensa yace,"Maama ni ba kuyi missing ɗina ba kenan, alhalin ni ke kulawa da shi".
cike da tsokana Maaman tace,"Bello ke kuma wa acikin kayan miya, a'a Hammanmu dai shi muka sani, hatta ƴan aikin gidan nan sunyi kewarsa, yaushe rabon yay nisa damu irin haka, wlh gidan duk ba daɗi".
ta miƙawa Fillo jakar hannunta tana cewa da Turaki,"tom zan fita ne, zanje wajen wannan matar da na faɗa maka nasa ta nema min marayun da za'a ke taimaka musu kullum, to shine zanje naga inda take da zama".
Turaki yace,"ok to Allah ya taimaka ya bada lada, Nihal ce kusa da ke?".
tace,"a'a su duk sun fice ai, ana bikin ƙawar Zaytuna sunje dinner party, ka san Baffanku ba so yake ba shisa nace suje mata da wuri su dawo da wuri, yafi ace basu je ba gaba ɗaya".
Turaki ya sauke numfashi kaɗan yace,"Maama ke ɗaya kuma za ki fita?, ki bari mana gobe sa raka ki".
tace,"ni da Fillo zamu je, bani ɗaya zan tafi ba me Babban suna".
yace,"yauwa hakan yafi ai".
sai kuma ya shafo wuyansa yace,"Maama please ko za ki bata ta kaiwa Salihu(me gadi), akwai saƙo dana bar masa, ina so naji ko yay concluding abin".
ta miƙawa Fillo wayar tace,"kaiwa me gadi da sauri".
Fillo ta miƙe tana ajiye jakar hannunta akan kujera, Hajiya Madina tace,"no tafi da jakar ai yanzu zan fito".
Fillo dai tunda ta amsa wayar ta fito bata kalla screen ɗin ba, tafiyarta kawai take yi shi kuma yana ta kallon fuskarta da ta haska.
ta kaiwa me gadi wayar ta dawo bakin mota tana jiran Maama, wucewar minti biyu sai ga me gadin ya dawo mata da wayar ta karɓa tana kallon screen ɗin, ganinsa yasa ta gaida shi.
ya amsa yana ƙarewa kwalliyarta kallo duk da ba wani kwalliya tai ba, farar powder kawai ta sha sai lip balm. tace,"in mayarwa da Maama wayan?".
yace,"no, i just want to say ki kula da kanki sosai kinji, hakama ki kula min da Maama, karki barta kuyi dare a inda zaku ɗin".
ta amsa da,"to". he have alot to say to her but dole ya taƙaita, at last kawai ya tambayeta,"kina da wata matsala ne". ta girgiza masa kai alamar a'a. shi kuma ya kashe wayar, Fillo tabi wayar da kallo tana jin kamar wani abu a tare da ita na tafiya da katsewar wayar. ta tuna yanda yake kallonta yana tambayar kamar yana magana da matarsa.
ko da suka je gidan Asabe Ƙuli, basu jima acan ba, kan hanyar su ta dawowa Hajiya Madina ta tsayar da driver a ƙofar wani store. a mota ta bar Fillo da Drivern bayan tace mata,"Fillo bari yanzu zan fito kinji. rigar jarirai kawai zan sayo inda muka je ɗin nan ne jikarta ta haihu".
Fillo tace,"tom Maama sai kin dawo". har Hajiya Madina ta fita a motar sai kuma ta dawo ta miƙowa Fillo wayarta tace,"bana son zaman shiru riƙe wayan ko ƙur'ani kya karanta, ko kuma za ki biyoni ne?".
Fillo ta girgiza kanta tace,"a'a Maama sai kin dawo ɗin". ta faɗa tana amsar wayar.
game ɗin da take yawan ganin Maama nayi ita ta shiga, tana cikin yi sai ga kira ya shigo wayar, ganin sunan,"My Husband". na yawo jikin screen ɗin yasa ta fita daga motar tace da drivern bari ta shiga ta kaiwa Maama.
sai da ta fito taji garin so silent, babu ma inuwar mutane dake giftawa, tana shiga ta bawa Hajiya Madina wayar ta fito.
duk da tana hasko motarsu dake tsallake haka ta taho a ɗan tsorace ta tsallaka, sai dai sanda tazo bakin motar ta buɗe ƙofar motar zata shiga taji wani abu mai sanyi a wuyanta, sanyi irin na ƙarfen wuƙa.
da sauri tayi yunƙurin juyawa bayanta jin numfashin mutum akanta, nan da nan taji numfashinta na seasn, sai kuma taji murya dai-dai kunnenta cikin raɗa da kakkausan amo ance,"wallahi kina ihu ko wani motsi sai na yanka maƙoshinki da kaifin wuƙar nan dake wuyanki".
ai sai tayi ɗiff ta fasa yin ihun da tai niyya, idonta ya maƙale a driver seat sai taga drivern baya ciki, dan haka ayanzu bata da wani zaɓi da ya wuce umarnin da aka bata.
tayi tsilli-tsilli da idanu tana jin yadda sanyin kaifin wuƙar ke wucewa har cikin zuciyarta. ta runtse ido sosai zuciyarta na tsananta bugawa, cikin kanta ya haska da kalmar mutuwa!, sai kuma gefen ƙwaƙwalwarta ya karanta mata ya ya Kaka zata ji labarin mutuwarta?, wanne hali Amir zai ji a sanda aka faɗa masa ta mutu?.
tana ji mutumin yasa tsumma ya toshe bakinta sannan ya shiga janta har suka bar bakin motar, ita dai idonta wurgawa yake yana kallon ƙofar store ɗin da Hajiya Madina ke ciki, so ta ke ta hango fitowarta in yaso ta san ta yadda zata ƙwace bakinta ta ƙwala mata kira, sai dai har suka baro bakin motarsu aka zo da ita wajen da bata san ina ne ba, bata ga kowa a wurin ba ko da kuwa Maama.
taji an buɗe motar da suke kusa da ita a yanzu an buɗe ƙofar baya. tana jin sanda wata murya daban da wacce ke riƙe da ita yace,"sakata aciki".
duk wannan abin da ake har yanzu wuƙar na wuyanta motsi kaɗan suke jira tayi su fille kan.
suka zirata acikin motar, tana kallon wanda ke front seat fuskarsa lulluɓe cikin bakin ƙyalle, wanda ke riƙe da ita yana shigowa ya rufo ƙofar, sannan ya ɗauke tsumman da ya rufe mata baki da shi, daidai da buɗewar bakinta zatai ihu, daidai kuma da juyowar na gaban ya danna mata wani tsumman da ya rufe hancinta da bakinta.
take ta shaƙi ƙamshin wani abu a jikin tsumman, bata da ilimin sanin chloroform balle a yanzu da taji ƙamshinsa tayi ƙoƙarin ɗauke numfashinta, kuma wannan ƙamshin abin da ta shaƙa ya wuce har cikin kanta sai taji kamar zata mutu, ƙirjinta kamar ana rura wuta tana ci bal-bal, lokaci ɗaya kuma sai taji numfashinta ya sarƙe gaba ɗaya, ta kasa shaƙar iska, a hankali kuma sai jinta da ganinta suka ɗauke duka, nan take kuma tai laƙwas ta tafi luuu tana faɗawa jikin na kusa da ita.
ba tare da ɓata lokaci ba motar ta bar wajen cikin speed ɗin da ba za'a taɓa zargan muggan mutanene acikinta ba. har sanda zasu wuce driver da ya dawo daga fitsarin da yaje ya bi motar da kallo, yana jin kamar bai yarda da motar ba har ta ɓacewa ganinsa. dai-dai nan kuma ya ɗaga kansa yana ganin me tahowa daga bayansa...
*LULLUƁIN BIRI.......*
*comment, vote and share.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_Avoid error mistakes._
*32*
ganin Hajiya Madina yasa drivern tafiya wurinta da sauri ya karɓi ledan kayan dake hannunta, a gaban mota ya aje manyan ledan kayan kusan guda 5, da gani kasan ba siyayya bace ta jarirai kamar yanda ta faɗa, siyayya ce ta musamman tayita don
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 31 Chapter of 73