Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kike buƙata". ya faɗa yana sakin hannunta, yana ganin yacca take ɓata fuska, bai tsaya sauraronta ba ya fita ya rufe ma ta ƙofar. tana ta faman ɓata rai tayi wankan, idonta duk ya taru da ruwan hawaye ƙiris yake jira ya zuba, ita fa kawai saboda ya kira ma ta Umminta ta yarda suka shirya, shi ne zai wani kawota toilet ɗinsa yace tayi wanka. sai bayan ta gama wanka ne sannan ta ɗaga towel ɗin zata ɗaura, sai ta gan shi ɗan ƙarami sai kace ɗan kwali kwatan yadi, idonta ya haska ma ta tana fita da wannan ɗan ƙaramin abun shi kuma yana ɗakin a zaune, sai kawai ta turo baki gaba tana kifa kai da bango ta saka kuka. sai da tayi me isarta tukunna ta ɗaga ido tana ƙarewa toilet ɗin kallo, daga jikin hanger ta kalli wani towel ɗin da alama ma sabo ne, bathtube ɗin ta taka ta ɗauko shi, ta sauke ajiyar zuciya dan ya fi wancan da ya bata abin arziƙi, kuma sai da ta ɗaura taga shima bai yi ma ta ba, taji kamar ta kurma ihu acikin toilet ɗin, sai kuma tsoro ya kamata babu shiri ta nufi ƙofa ta buɗe ta fita kanta a ƙasa. Turaki na zaune saman gado yana facing toilet ɗin, da ma jiran fitowarta yake tun ɗa zu, Nihal na ƙasa tana jiransa yaƙi fita. tun da Fillo ta ɗago ido tai masa kallo ɗaya sai ta maƙale a inda take, taƙi yarda ma ta kalle shi, ta rumtse ido tana yunƙurin juyawa ta koma toilet ɗin taji yace,"ki na komawa zan sa nepa su ɗauke wutarsu, ni kuma na fita na bar miki gidan". babu shiri ta dakata, ta rumtse ido sosai tana baro ƙofar toilet ɗin cikin tafiya me kama da sauri, dan duk ya saka ma ta tsoro, sai da ta kusa zuwa kusa da shi sannan ta tsaya ta rasa ya zata yi, ita ba zata iya zuwa wurinsa a haka ba, ta ɗaga kai ta kalli ƙofa tana tunanin fita, tsoronta ɗaya ne kar ta fita a ɗauke wutar da gaske. shi dai kallonta kawai yake yi from head to toe, towel ɗin jikinta ko rabin cinyarta bai kai ba, siraran santala santalan fararen cinyoyinta duk a waje, breast ɗinta masu. cika tsayayyu sun taso ta saman ɗaurin towel ɗin, ashe duk sirantarta ce take ɓoyesu a cikin kaya, but tana da su masha'Allah daidai misali, ya lumshe idanunsa yana sauke doguwar ajiyar zuciya, lokaci ɗaya hankalinsa ya nemi ya tashi, yasa hannu ya shafa fuskarsa yana kawar da abun da ke neman hargitsa lissafinsa. muryarsa ta fito a hankali sosai yace,"zo ki zauna". ya faɗa yana ma ta nuni da kusa da shi, sai taƙi yarda ta kalle shi balle ma ta zauna kamar yanda yace, gaba ɗaya sai yaji yana neman ya kasa jurewa, hakan yasa shi miƙewa ya nufeta. da sauri kuwa ta juya zata koma toilet ɗin ai ko yay saurin ruƙo hannunta, riƙo ta ɗin da yay towel ɗin jikinta ya kunce ya kusa zamewa, babu shiri ta tafi zata sunkuya but sai ya hanata hakan ya kama bakin towel ɗin ya ɗaure ma ta da kansa, ta fashe masa da kuka tana janyewa,"ni ɗakina zan tafi". bai saurari abin da take faɗa ba ya haɗeta da jikinsa yana hugging ɗinta very tight, ya ware duka five fingers ɗinsa a gadon bayanta, gently yake shafa very soft skin ɗinta, lokaci ɗaya yaji yanayin jikinsa na sauyawa gaba ɗaya, a hankali ya sunkuyo da fuskarsa yana neman lips ɗinta ya haɗe da na shi ya tsotsa, kamar wanda aka tsikara kuma sai ya fasa ya ɗago kansa yana girgizawa, ya buɗe idanuwansa da suka fara rinewa yana kallon yacca duk jikinta ya ɗauki rawa sai kuka take yi masa a hankali. ya sarƙe yatsunsu wuri ɗaya yana ɗora goshinsa a nata goshin, murya a kasalance yace,"sorry". ta gyaɗa kanta kawai tana ce masa,"ni ɗakina zan tafi". ba tare da ya buɗe idonsa ba yace,"bana so ki tafi, ki zauna anan yau muna tare". sai ta buɗe ido tana kallonsa, yanayin yanda yake maganar kamar ba muryarsa ba. bata san lokacin da bakinta ya suɓuce da tambayarsa,"menene?". a sannan ya buɗe lumsassun idonsa ya kaɗa ma ta kai,"nothing". ya faɗa yana sauke numfashi,"me za kiyi a ɗakin naki?, ko can zamu koma?, ni bana son zama ni ɗaya". tana ƙifta idanu ta ce,"tsoro kake ji?". ya ɗaga ma ta kai alamar ehh tare da cewa,"da kika shiga wanka naji kamar za'a kama ni". sai ta turo baki gaba ta ce,"ba wani nan". ya matsa hannunta ya ce,"me kike nufi?". ba ta ce da shi komai ba sai kare ƙirjinta take yi da ɗayan hannunta. yana riƙe da hannunta suka isa bakin mirrow, ya zaunar da ita akan stool, ita dai sai kallonsa take ta cikin mirrow ɗin yanda yanayinsa ya koma kamar na mara lafiya, ya ɗauko lotion ɗin da yake shafawa ya ajiye ma ta, baya tunanin zai iya aikin shafa ma ta dan za'a iya samun matsala, ba yanzu yake so komai ya kasance ba, zai ci gaba da daurewa zuwa lokacin da ya ɗaukarwa kansa. ta ga ya bar wajen ya isa gado ya ɗauko babban kwalban humra ya jiye a saman mirriow ɗin, tafin hannunsa a saman haɓarta ya juyo da fuskarta yana ma ta nuni da kan gado ya ce,"your dress". sai kawai ta bi kayan da ido kafin ta gyaɗa masa kai, ba tare da ce komai ba, kuma ba tare da ta kalle shi ba. tana kallonsa ya fice daga ɗakin jiki a saɓule kamar mara lafiya ko wanda aka yo aiken mutuwa, duk sai taji kamar yana neman bata tausayi, ko me akayi masa oho?. sai da ya fita sannan ta iya ɗaukar man ta shafa, tana mita ƙasa-ƙasa ta ɗauki humrar ta shafa, kawai yaje ya ɗauko mata sabuwa alhalin ga buɗaɗɗu nan har guda uku a ajiye, tana gama shafawa ta wuce kan gado, tunaninta ɗaya pant da pad, kuma da mamakinta tana ɗaga kayan sai ga pad ɗin haɗe da sabon pant, wata uwar kunya ta lulluɓeta, yaushe ma ya san tana period ɗin?. tana murguɗa baki ta shiga toilet ta saka, garin ɗauko brezier ɗinta ta zame ta faɗa cikin bathtube ɗin ta jiƙe, ta rumtse ido kawai ta fito bayan ta shanya, cikin sauri ta ɗauki kayan ta saka gudun kar ya dawo. tana saka rigar taji kamar ta kurma ihu, ya san kuwa kayan da ya ɗauko ma ta?, ita kam bata jin zata iya saka kayan nan alhalin yana nan, duk rigar tayi transparent, kuma iyakar gwiwarta fa, hannun ma irin na vest, kuma ma ko ya haɗo ma ta da brezier, sai kawai ta doki ƙafafu a ƙasa da ƙarfi kamar tiles ɗin sun ma ta laifi. ƙofa ta nufa zata fita sai dai tana zuwa taji ƙofar a rufe ya saka key ta waje, ta cije leɓen ƙasa ta juya ta koma toilet ɗin, ta ɗauko brezier ɗin sai dai ba zata saku ba don sosai ta jiƙe. fitowa tayi tana hawaye, gado ta nufa ta durƙushe a wajen ta kifa kai tana kuka, can jimawa taji an buɗe ƙofar, bata ko ɗago ba dan ita haushinsa take ji, shi ma kuma da ya shigo ɗin kallo ɗaya yay ma ta ya ɗauke kansa, ya wuce ya ajiye basket ɗin abincin dake hannunsa, ya fito da cooler ɗin ciki ya ajiye akan table. bakin gadon ya dawo ya zauna, ya ɗagota ya ɗaurata saman cinyarsa tare da zagayeta da hannayensa ya ce,"kukan na menene?, me Fulanin Turaki ke so?". ta ɗago da kanta, tana matse idanu tamkar baby ƴar 2years ta ce,"ni ɗakina zan tafi". ɗan murmushi ya yi yace,"naji to za ki koma can ɗin but tare zamu tafi ko?". tai saurin girgiza masa kai, ya ƙara cewa,"why?". "to ai kaima ga naka, kowa ya zauna a nasa ai". ya buɗe ido yana kallonta sosai kafin ya kwantar da kansa a kafaɗarta yana shaƙar ƙamshin humrar da ke fita a jikinta. da wani irin murya yace,"to ni yau tsoro nake ji, ba zan iya kwana ni ɗaya ba, in kin yarda na bi ki ɗakinki, na yarda ko a ƙasa ne zan yi shimfiɗa, but please karki tafi ki barni ni ɗaya bana so wani abun yazo ya kamani, ba zan iya ƙwatar kaina ba". Fillo ta dinƙa kallonsa kafin ta ce,"kai ne ɗin kake jin tsoro?". ba tare da ya ɗago kansa dake kafaɗarta ba ya ɗaga ma ta kai kawai. sai kawai ta tsinci kanta da kama hannunsa ta ce,"to amma jiyan nan ai kaine ka kori abun da yake biyo ni". "to ai jiya kika ce, yau indai yazo to sai dai ya cinyemu dukanmu, kuma da ma jiyan ma ai ƙarfin hali nayi na zama jarumi saboda bana so wani abu ya taɓa ki". tayi shiru ba ta ce masa komai ba, ya ɗago kansa ya kalleta ya ce,"shikenan ma kawai, zan tafi gidan su Bello". ta kalle shi suka haɗa ido ta girgiza masa kai da sauri, sai kuma ta sauke idonta ƙasa tana jan yatsunta. "ai dare yayi yanzu". hannu yasa ya ɗago haɓarta ya ce,"look in to my eyes". sam taƙi sai ma ido da ta daɗa rumtsewa. idanuwansa na neman lumshewa ya zura hannunsa cikin rigarta, tana jin hannunsa a ciki tayi saurin buɗe ido ta zabura zata miƙe ya riƙeta, flat tommy ɗinta ya shiga shafawa yana faɗin,"na san wannan shafaffan cikin na buƙatar abinci ko?". magana yake yi duk yay wani collapse. ta ɗaga rigar ta fito da hannunsa tana cewa,"ni ka bari". yay knooding ma ta kansa, ɗaukarta yay zuwa kan kujera ya ajiyeta, ya buɗe cooler ɗin abincin, nan da nan ɗakin ya karaɗe da ƙamshin ƙwai. ta bisa da kallo a sanda yake ɗauko plate ya zuba soyayyar doya da ƙwai da kuma miyar souse, bayan ya gama zubawa ya juyo ya fuskanceta, da hannunsa ya ɗauki doyan ya kai bakinta. "wa ye ya dafa abincin?". taji bakinta ya suɓece da yi masa tambayar. "Zaytun nasa ta kawo mana, i know ba ki da lafiya, and ba ki iya girki ba, so na roƙeta alfarmar take dafa abinci tana kawo mana before na kai ki catering school ki koya". ta tsuke fuska tana kallonsa ta ce,"ni ce ban iya girki ba?, wancan ranar da na dafa indomie ai kace na iya dafawa". ya ce,"amma ai bance yayi daɗi ba ko?". ta turo baki gaba ta kauda fuska gefe,"Allah na iya girki nima, kuma ka tambayi Maama kaji, Baffa ma da yaci wainar masar da nayi sai da yace yayi daɗi Allah yay min albarka, Adda Zaytuna ma indai zata yi baƙo in tana asibiti tana sawa nayi ma ta, kuma ka tambayi abokinka ɗin kaji, kuma ma ka tambayi Kaka kaji tun ina ƴar ƙarama nake yin girki". ya dinƙa kallon bakinta yana murmushi, har tayi shiru bai yi magana ba, jin shirunsa yasa ta juyowa tana kallonsa ta ce,"Allah na iya girki". ya rufe ido ya buɗe ya ce,"ai tun kina ƙarama kika ce". tai saurin cewa,"a'a nufina tun ina ƴar ƙarama nake yi, ko time ɗin ma da muna masarauta ina yi". "ohhh yanzu kenan ke babba ce?". kamar jiran tambayar take yi ta ɗaga masa kai, murmushinsa me sauti ya fito yana cewa,"to ni ban ga girman ba, you are still a Baby in my eyes, dan haka ni ba zan ci abinci ƴar ƙarama ba babu daɗi, rabi ya dahu rabi bai dahu ba, ko yay ta ƙauri, ko a cika gishiri". su ka haɗa ido ta haɗe gira waje ɗaya ta murguɗa masa baki, yasa yatsa ya ɗalle bakin nata. "oya ba rigima na ce ba, abincin za'a ci, buɗe bakin". saboda yunwar da take ji ta buɗe bakin tana karɓa, sai da ya gama bata sannan ya matso kusa da ita sosai, ya ce shi ma ta ba shi hannunsa ya gaji zai karye, yay ta narke ma ta yana koma ma ta ƙaramin yaro, da taƙi ya ta shi zai bar wajen yana cewa ya fasa kira ma ta Ummi ɗin, babu shiri ta ɗauka plate ta kamo hannunsa ya dawo ya zauna ta shiga ba shi, kuma yaƙi yarda ta ba shi da spoon dole sai hannu ta saka, duk kaiwa ɗaya sai ya cije hannun nata, har ta gama ba shi bata yarda sun haɗa ido ba kanta na ƙasa, sai dai tana ta murmushin da ta rasa dalilinsa. duk yanda Fillo ta cije ta noƙe akan ba zata bi shi toilet ba sai da yaja ta suka tafi tare, da kansa yay ma ta brush, sannan shi ma yay nasa, su ka fito yana ɗauke da ita rungume ajikinsa, ita kuma tayi laƙwas ta lafe a jikin nasa kamar mage, ya wuce yay switching light off sannan ya kunna deem light, tukunna ya wuce kan gadon, ita dai duk sai kunyarsa take ji. ko a kan gadon ma a jikinsa ya kwantar da ita, murya can ƙasa ya ce,"Fulani nah". ta ce,"uhmm". ya shafo gashin kanta da yake jin laushinsa da santsinsa na shiga jikinsa ya ce,"mu bari sai Allah ya kaimu gobe sai a kira Ummi ko?". ta girgiza kai da sauri,"a'a yanzu dai". "to ai dare yayi, kar tayi tsammanin wani abu ne ya faru". kamar zata yi kuka ta ce,"ni dai don Allah yanzu". ya sauke numfashi ya ɗauko wayarsa ya bata, ta miƙe daga jikinsa tana cewa,"remove the password". looking at her eyes da suka koma sexy ya ce,"your name". ta tsaya kallonsa kafin ta ce,"Halima?". ya girgiza kai,"no, the other one". "Fillo?". nan ma girgiza ma ta kai yay, ta shagwaɓe ta ce,"to which one?". daidai kunnenta ya ce,"cry cry Baby". fuska a tsuke zata yi magana yasa hannu ya rufe bakin, ita kuma taƙi saka sunan da ya faɗa, ai ta san bata kai wannan matsayin ba, dan haka sai ta saka sunayensa duka biyun bai yi ba, ta sa na Mum da na Maama duk bai yi ba, tasa na Zaytun shi ma bai yi ba, da ga ƙarshe kawai tasa yanda ya faɗa ma ta ɗin shi ma ta ga bai yi ba, tana sa Fulani Nah taga ya buɗe, kuma da tsantsar mamaki sai taga hotonta akan wallpeper, hoton da ba ta san da shi ba, kuma ba ta san lokacin da ya ɗauke shi ba, dan bacci take yi ya ɗauka, mutum dai in yana bacci muni yake yi amma ita kanta ta san tayi kyau, sai kawai fuskarta ta washe da murmushin da ya bayyana haƙoranta. ta kalle shi ta ga idanuwansa a rufe kamar ya yi bacci, a hankali ta ce,"ai ban san lambar Ummin ba". ya buɗe idonsa da bacci ya fara fizgarsa ya ce,"Ummi nah". yana faɗa ya mayar da idonsa ya rufe, kamar kuwa yanda ya faɗa ɗin gaban Ummi sai da ya faɗi da taga shigowar kiran, ta ɗaga wayar tana karawa a kunnenta cike da jin nauyi na sirikinta da kuma fargabar abin da zata ji, duk da cewa duk bayan kwana biyu yana kiranta su gaisa, but ba'a irin wannan lokacin ba, ta ƙara duba agogo taga ƙarfe goma har da ƴan mintuna. "Ummina". "na'am Autata". Ummin ta amsa tana sauke numfashi, sai yanzu taji ta samu natsuwa. da murna sosai haɗe da farin cikin jin muryar mahaifiyartata ta ce,"Ummi nayi kewar ki sosai". "ni ma haka Autata, ya kuke?, ina fatan duk kuna lafiya?". sai kawai Fillo ta saka kuka tana faɗa ma ta ita dai tana so ta ganta, haka Ummin tai ta fama da ita tana lallashinta, sun jima su na wayar, dan hira sosai suka yi, har Kaka ma sai da suka gaisa da ita, tace akai wa Dada su gaisa, Ummi ta ce ai tayi bacci yanzu. "Ummi to yaushe za ki zo?". ta ce,"yau kwananki nawa Autata?, ko 2weeks fa ba ki yi ba, ki bari sai an kwana biyu zan zo in ganku kinji, hope babu wata matsala ko?". ta girgiza kanta kamar tana ganinta ta ce,"to Ummi ba za ki dawo nan ɗin ba?". ta ce ma ta,"su Dada sun hana, muna nan sun riƙe mu ni da Dadana, an bar mana ɓangaren Kakarki, ba ki ga ba an gyara mana shi sosai yayi kyau, har ƙaton enlargement ma akayi mana aka kafe a parlon, da hotona da na Abbanku da naki da na Hamid, duka aka haɗa yayi kyau sosai". Fillo ta sauke numfashi tana jin soyayyar Umminta da kuma kewar Abbanta ta ce,"Ummi ina zuwa zan ɗauke shi Allah". Ummi ta ce,"ba zan bari ki ɗaukar min nawa ba, sai dai ki roƙi Hamid ya ba ki nasa, shi ma ya saka a ɗakinsu". da haka suka ci gaba da wayar har sai wajen sha ɗaya saura sannan suka yi sallama, sukai sallamar cike da kewar junansu. ta riƙe wayar a hannunta tana ta kallon hotonta, so take alallai sai ta tuna ranar da yay hoton, iyakar fuskarta ne kawai da wuyan balle idan taga kayan jikin nata ta iya tuna ranar. but kan gadon yay ma ta kama da ɗakinsa na can gida, its like kamar ma ranar da ta kwana a ɗakinsa ne. a hankali ta juyar da kanta tana kallonsa, zatonta ko bai bacci ba, sai taga yana sauke numfashi alamu ma ya jima da yin baccin. hannu ta miƙa ta ajiye wayar a inda taga ya ɗauko, sannan ta kwanta tana barin tazarar 4inches a tsakaninsu, taji ta kasa rufe ido tayi bacci, taji kamar tana buƙatar wani abu daga gare shi, ganin da alama yay nisa a baccin ta sami damar ƙarewa kyakykyawar fuskarsa kallo, tana jin wani abu me kama da sonsa tsantsa na taɓa zuciyarta. laɓɓanta suka tale da wani kyakykyawan murmushi, abu ɗaya ta sani yanzu shi ne tana sonsa, idan tace ba haka ba tayi ƙarya, and ta yaudari kanta, but ba zata iya cewa ga rana ko kuma lokacin da ta fara sonsa ba, idan har ma ta faɗi hakan to tayi ƙarya. kallon fuskarsa kawai take yi tana jin tamkar kar ta daina, tamkar yay ta baccin ita kuma tai ta kallonsa babu ƙifcen ido, ta tuna wata rana, ranar da ta fara tambayar Maijidda, _kin san wani Turaki a gidan nan?._, kuma amsar da Maijiddan ta fara ba ta ita ce,_ wani kyakkyawa ne ajin farko, in kyawun kowa na fasaltuwa nasa ba zai fasaltu ba, don ko kyau da kansa yay ƙaryar yace zai iya faɗin kyan Turaki._ amsar da Maijiddan ta bata kenan, kuma haka kawai sai taji haushin maganar a yanzu, wanda ta san ba komai ba ne face kishi, sai ta yamutsa fuska tana ɓata ranta, haka kawai duk ya bari kowa ya gama kalle kyansa ita an bar ma ta saura. ta rufe ido tana so ta sami sassaucin zafin da taji zuciyarta nayi ma ta, kafin ta buɗe ƙwayar idonta ta sauka akan gashin kansa, baƙi wuluk da shi, kwantacce kamar na larabawa, cikin ɗan hasken ɗakin sai sheƙi yake yi, sai taji tana sha'awar ta taɓa taji kalar sulɓinsa, ta ɗaga hannunta a hankali zata taɓa sai ta fasa, gudun kar taje ta taɓa ya buɗe ido ya kamata. ta mayar da kallonta kan pink lips ɗinsa, ƴan daidai da su masu ɗaukar hankali, a iya kallon kawai ta shaida masu taushi ne. ta rufe ido ta kai yatsanta ta taɓo lips ɗin a hankali, tana taɓawa tayi saurin ɗaukewa tana rufe fuskarta kamar wadda ya kamata tana taɓawar. sai da ta ɗauki kusan 3mints idonta a rufe, tana jin kamar ta kuma taɓawa taita shafawa lips ɗin, tana buɗe idon kallonta na sauka akan ƙirjinsa da ya wadatu da kwantacciyar gargasa me kyan naɗewa. sai taji tana buƙatar ta taɓata itama, tayi nisa a kallon chest ɗinsa, ba tayi aune ba taji muryarsa yana faɗin,"you want to hug me right?". ba ta san lokacin da ta waro idanu waje ba, ta kalle shi tai saurin kulle ido tana ɓoye fuska ajikin pillo, yay murmushi yasa hannu ya matso da ita kusa da shi a kunnenta ya ce,"stop being shy, hug me the way you want, i am all yours". ta tura baki tana jin kamar tayi kuka tsabagen kunya, ya sa hannunta a bayansa but ta kasa rungume shi ɗin duk da tana so tayi hakan, sai kawai ya ƙara matso da ita sosai ya ɗora kansa saman shoulde ɗinta, in a cool voice yace,"lets sleep". ta ce,"ai bana jin baccin". "but yo want to touch this right?". ya faɗa yana kamo hannunta ya ɗora akan ƙirjinsa, da sauri ta rumtse idonta jin wani abu ya ratso tun daga babban yatsanta har tsakiyar kanta. "oya ki ta shafawa baccin zai zo, or should i bring cumb kiyi masa kitso?". zata juya masa baya ya hana hakan, sai ta ɓoye fuskarta a ƙirjinsa, har yay bacci bata yi ba, sai da yay nisa sosai sannan ta shiga wasa da gashin ƙirjin nasa tana kuma shafa lips ɗinsa. *After 3Days.* ƙarfe shida da rabi a lokacin, Fillo ta sauko daga upstairs, english wears ne a jikinta, riga white sai skirt baby pink, sai hular chantaly itama pink colour, tayi kyau sosai acikin shigar. ta dubi parlon taga an gyara shi sai ƙyalli yake yi, duk da cewar da ma ba wai da datti yake ba, but ko ya wuri dai ya samu gyara kyau yake ƙara yi. wucewa tayi ta kunna burner ta zuba turaren wuta, nan da nan kuwa parlon ya karaɗe da ƙamshi, ta kunna tv tasa karatun ƙur'ani sannan ta wuce kitchen, tana tafiya kamar ba zata taka ba. yau da kanta take so tayi girki, kullum sai dai yasa Zaytuna ta dafa ta kawo musu, ta san akwai gajiyawa kawai dan ma dai ya haɗu da ƙanwa me biyayya ne, and kamar yanda ba zai iya cin abincin ƴan aiki ba haka ita bata tunanin zata barsa ci, ba ma ta fatan Allah ya kawo ranar da zai ci abincinsu. a kitchen ɗin ta sami Hannatu na feraye dankali, ta amsa gaisuwar da take yi ma ta da murmushi. "har kun tashi da wuri haka?, sannunku da aiki". Hannatu ta amsa ma ta da yauwa tana barin ferayar ta miƙe,"Anty akwai wani abu ne?". Fillo tayi ma ta wani kallo ta ce,"ni kam wai ba zaku bar faɗa min wannan sunan ba?". Hannatu ta ce,"ai Anty sai dai kiyi haƙuri gaskiya, amma ba zamu iya faɗin sunanki ba gatsal, ai in muka yi haka munyi rashin kunya, ke fa uwar ɗakin mu ce". ta gyaɗa kanta kawai ba tare da tace komai ba, Hannatu ta ce,"jiya na zo ɗakin naki da daddare na tarar kin rufe ƙofa, kin manta ba ki faɗi abin da za'a dafa da safe ba, sai Sakina ta ce taji kamar kince a soya dankali da ƙwai". ta ce,"in dai zaku ci dankalin ku dafa kawai, amma karku sa da mu". Hannatu ta dinƙa kallonta, so take ta fahimci wani abu, don kwana biyun nan ma sai gulma suke na rashin saukowar da bata yi, shi ma kuma me gidan baya fita, in sun ga ya sauko to masallaci zai wuce, har Sakina na cewa ta rasa uwar da suke yi a saman sai su wani koma kamar matattu, in banda ranar nan ma da akai baƙi taga sun sauko, har Fillon ta yini a ƙasa, sai shi da yake saukowa daukar abincin da ake kawo masa ya koma, wanda hakan ke ƙona musu rai, ba su san me ake nufi da su ba, ba su taɓa yin girki sun ci ba sai dai su dafa suci au kaɗai. Tunanin Hannatu ya tsaya cak sanda taga Fillo ta fito daga store hannunta ɗauke creat na ƙwai, ta tafi da sauri zata karɓa Fillo ta hanata tana faɗin,"bar shi Hannatu, kici gaba da aikinki". ta ce,"ai Anty da kin bari munyi aikinmu, ke da ba ki jima da tashi daga rashin lafiya ba". Fillo tayi murmushi kawai bata ce ma ta komai ba, ta ajiye ƙwan ta koma ta ɗauko semovita, shi ma ta ajiye sannan ta nufi friedge ta buɗe ta ɗauko ingrediant ɗin da zata yi amfani da su, butter, shredded coconut, youghurt, lemon juice syrup da almond seed. su ma duk ta ajiye su wuri ɗaya kana ta buɗe drower ta ɗauko baking powder, sugar da veg oil. semolina Cake take so tayi, wanda larabawa suke cewa Basboussa, tana sonsa sosai, dan lokacin da suka je umara yawancin kullum sai taci, hakan ne ma yasa ta zage ta koya a wajen kukun da ke dafa musu abinci, kuma yau

Chapter 58 of 73