Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
abin da ƙwayar idonta ta haska mata irin hoton yaran a zahiri, ta gama ba su nono ta zo ta kwantar da su tana yi musu wasa, idan zata yi aiki sai ta saka musu karatun alƙur'ani kafin ta fita. yayin da suka girma su fara kiranta da Ummi, mahaifin su kuma su kira shi da Abie, ƙwayar idanunta ta ƙara haska mata lokacin da zata fara shirya su cikin kayan makaranta, ta ba su lunch box na abincin su, sannan tayi driving ɗin su zuwa makaranta, yayin da suka dawo ta zauna domin yi musu home work ɗin da aka ba su, idan weekend ya zo sai su dinƙa yada zango a field su na yin wasa tare da ita, ko kuma suke shiga cikin swimming fool. ita dai ta riga ta gama tsara yacca rayuwar jin daɗi zata kasance tsakaninta da ƴaƴanta, ba zata zamto ɗaya daga cikin irin uwayen nan da basa jan yaran su a jiki ba, ita zata zam yaranta na liƙe da ita ne ko da yaushe, ta dinƙa jin damuwar su suma su na jin tata, zasu zama manyan aminanta kamar yanda zata zame musu. sai taji kamar zuciyarta ta ƙara girma da tsiron wata sabuwar ƙauna ta daban, ƙaunar abinda ke cikinta ya mamaye dukka ilahirin jikinta, irin wannan ƙaunar ta ɗa da uwa, irin ƙaunar da zaka ji kamar zuciyarka na fitar da tiriri na son tabbatar da abinda kake so, Allah shahidi, shi zai yi mata shaidar irin son da take yiwa yaran, tana ƙaunar su fiye da ranta, a yanzu su ne rayuwarta, in har babu su tabbas babu ita. har ƙarfe uku tana ɗakin yaran a zaune, sallolinta duk anan tayi, abinci ma da aka kawo mata anan taci, ko ƙwalli ɗaya bata bari ya zuba ba gudun karta ɓata musu ɗaki. zuwa lokacin kuwa sun yi waya da Turaki yafi sau goma, bini-bini sai ya kirata yace ga shi nan yana hanya, kuma taji gaba ɗaya hankalinsa a tashe yake tun san da tace masa tana jin mararta na ciwo sosai, kamar dai zata fara labour. cikin mintunan da ba zasu wuce biyar ba bayan wayar su ta ƙarshe sai ga Turaki ya dawo, yana shiga ɗakin yaran ya ganta zaune akan darduma tana goge hoton enlargement ɗinsu ita da shi, fuskarta ta washe da murmushi, wani murmushi da Turaki zai iya cewa bai taɓa ganinsa a saman fuskarta ba. "welcome back". ya ƙarasa ya zauna a gabanta yana tankwashe ƙafafunsa, ya ƙura mata ido sosai yana ganin yanda take cije fuska, tana so ta ɓoye masa zafin ciwon da ke cinta, tana so ta ɗauko ƙarfin hali domin ta nuna masa babu komai, babu wani abu da yake damunta, babu wata matsala, duk saboda hankalinsa ya kwanta. "kin ci abinci?". "na ci, me ka taho min da shi?". ya matso da ledar da ya shigo kusa da ita yana buɗewa. "irin naman da kike so". ai ko nan da nan ta warci ledar, ta miƙa masa enlargement ɗin tace,"maƙala musu wannan, an manta jiya ba'a saka shi ba, mp3 ɗin su na karatun alƙur'anin ka bar shi a ɗakinka, ka ɗauko sai a ɗora musu a saman wancan table ɗin, ungo wannan diary ɗin sa min shi cikin wadrobe ɗin su, kasa shi ƙasan kayan Aayan". duk maganar tayi ne a lokacin da ta fara cin naman, Turaki ya miƙe yayi duk abin da tace, san da ya kammala har ta gama cin naman, ya shiga tsokanarta da kura, kasancewar naman yana da yawa sosai. sai da suka ƙara kimtsa ɗakin sosai sannan suka zauna a tsakiyar gadajen biyu, suka shiga hira, wata iriyar hira suke yi mai ratsa jiki, hira da zasu ce ba su taɓa irinta ba a tsawon zaman su, hirar da ta yiwa kowannensu daɗi matuƙa. kan Fillo na saman ƙirjinsa yayin da yake shafa gashin kanta, duk hirar da suke yi muryarta na fitowa ne tana ratsa dukkan ɗakin a hankali, cikin wani amo na rauni da ya gaza ɓoye dauriyar ciwon da ke cinta. ana sallar magriba ciwon naƙuda me tsanani ya ɓallewa Fillo, lokacin tayo alwala kenan ta fito daga banɗaki, tayi saurin dafa bango tare da duƙawa a wajen tana dafe bayanta, a lokacin wata azaba ta tsarga jikinta, sai taji numfashinta kamar ya tsaya cak a maƙogoronta, taji kamar duk wani ɓurɓushi na halittar jikinta yana barinta gaba ɗaya. ta rumtse ido na tsawon mintuna tana ambaton Allah cikin wata rarrauniyar murya, wani sabon bala'in zafi taji ya fara bin dukkan jijiyoyinta, sai taji ina ma ta kwasa a guje ta bar cikin ɗakin ta fita waje ko zafa sami sauƙi acan, sai dai ko yatsanta guda ta kasa motsawa, ji take yi tamkar an saka ƙaton dutse an danneta. muryarta tun tana fita da ƙarfi har ta zo ta daina fita, lokacin Turaki ya shigo ɗakin kamar an hankaɗosa, dama tun san da zai tafi masallaci yaji hankalinsa bai kwanta ba, yaji gaba ɗaya ba ya so ya tafi masallacin gwara yay sallarsa anan, amma sai ta hana shi, ta tilasta masa akan sai ya tafi masallaci ya sami jam'i. cikin tsananin tashin hankali ya ƙaraso in da take, cikin bala'in ruɗu na farat ɗaya yace,"kin gani ko, sai dai na faɗa miki ba zan fita ba". "ka kaini a cire min su Jannaty, ba zan iya ƙara kwana a haka ba, don Allah ka taimaka min, zan mutu...". Sauran harufan suka katse sakamakon wani sabon ciwon da ya murɗa mata, taji kamar an saka kibiya an soketa a tsakiyar cikinta da mararta. "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Fulani Nah daure mu fita". ta kalle shi cikin hasken da zata ce a matsayin mutum uku take ganinsa, ta tattaro dukkan sauran ƙarfinta da ya rage mata ta daure, ya kamata ta yunƙura ta miƙe tana dafa kafaɗarsa, zafin ciwon da ya ƙaru yasa duhu ya wanzu a cikin idonta, ta daina ganin komai, tabbas bata iya ganin komai harta mijinta da yake riƙe da ita, sai dai kunnenta na iya jiyo mata sautin muryarsa dake fita cikin tsananin tashin hankali. Allah ya taimaka musu a bedroom ɗin ƙasa ne, da basu san ta yanda za'ai su sauko daga saman ba. Turaki yaji tayi masa wata muguwar damƙar da zai rantse ba ita ba ce, domin ba ƙarfinta ba ne, bata da wannan ƙarfin ya sani. "ka ɗauko riyon Babies mu wuce asibiti". "ba zan iya tafiya na barki ba a haka". "zan iya Jannaty, zan iya daurewa, zan daure har ka dawo". nan da nan Turaki ya haye sama ya tattaro duk wasu abubuwa da za'a buƙata a asibiti, ya kira Ilham a waya ta taho part ɗin, tana shigowa parlon ta tarar da Fillo durƙushe a ƙasa tana ambaton Ya salamu, Ya Salamu ka kawo min da sauƙi, idan na kasa ubangiji ka bani dauriyar da zan iya. tayi kanta da sauri, Turaki ya sauko ya dire kayan hannunsa. "kira yaran nan su kai mota sai ki zo mu kamata". hankalin Ilham a tashe ta shiga ƙwalawa su Sakina kira, bata ma iya yi musu magana da baki ba sai nuni da tayi musu da hannu. fitowarsu compound Boɗejo ta iso gidan ita ma duk a ruɗe, tana ganin yanda suke tafiya da Fillon a hankali ta ɗaga murya wajen ce musu,"kai ai zuwa zaka yi ka kawo motar nan kusa, sai mun hanzarta kar ta haihu a mota". tsabar ruɗewa Turaki ya manta da tunanin hakan, don haka ya sakarwa Ilham ita ya wuce cikin sassarfa yana haɗawa da gudu. asibiti mafi kusa suka isa, su na zuwa aka karɓe su saboda ganin yacca Fillo ta gama galabaita cikin mintunan da gaba ɗaya ba zasu kai rabin awa ba, ƙari kuma da uban kuɗin da suka ji an sakar musu duk da cewa dama asibitin private ne. wucewar wasu mintuna da ba zasu wuce goma ba Dr ya fito yana shaida musu cewar ba zata iya haihuwa da kanta ba sai dai ayi mata CS. "in har zata haihu lafiya ku yi mata koma menene, ina da buƙatar matata don Allah". furucin ya fito daga bakin Turaki murya a kakkarye. Dr ya ba su takardar da za su yi signing akai, Turaki yay signing ɗin a san da hannunsa da jikinsa duka ke rawa. kafin Dr Yusuf ma ya karɓa yay sigining a ɓangaren signature na mahaifinta. cikin wasu ƙalilan ɗin mintuna aka shiga preparation ɗin yiwa Fillo tiyata. lokacin duk ƴan gidan su Turaki sun iso asibitin, da Ammi mahaifiyar Yusuf, da wasu ƙannen Hayyo mutum biyu da suke anan garin gombe Safna da Alawiyya. duk ɗinsu su na zaune a ƙofar labour room ɗin da aka shiga da ita tun ɗazu, kowa yay jugum jiki duk a sanyaye, babu wanda zaka kalla kaga kwanciyar hankali a tare da shi, mahaifiyarta sai kiran waya take yi ana faɗa mata ko tiyatar ma ba'a shiga ba har yanzu. Turaki kuwa zama da tsayuwarma sun gagare shi sai zarya yake tayi, time to time sai yasa hannu ya sharce zufar da ke saman goshinsa. motsin buɗe ƙofar labour ɗin da aka yi yasa duk suka tattara hankalin su gun, Dr ya fito cikin sauri ya nufi side ɗin operation thiater, a san da nurses biyu ke turo gadon da Fillo ke kwance akai, tana sanye cikin uniform ɗin da ake sawa na CS, nurses ɗin suka tsayar da gadon a san da suka ƙaraso saitin family ɗin nata. Mum ta fara duba tace,"Mum kun zo?". kallo ɗaya zaka yi mata ƙwalla ta cika idanunka, duk suka taso suka iso wajenta, ɗayan hannunta da babu canular shi ta dinƙa miƙa musu su na gaisawa tana amsa tarin adu'oin da suke tayi mata. tana duban Ammi ta ce,"Ammi Ummi bata zo ba?". "bata zo ba Fillo, muna dai tayin waya da ita, tana ta yi miki adu'a, tace kar ki yawaita raki kiyi ta adu'a". "Ammi ina ta daurewa amma na kasa yin nishin da suka ce, kamar dai ko ba zan haihu ɗin ba ne". "za ki haihu kar ki damu, insha'Allahu ƴaƴanki za su fito". "Allah yasa Ammi. don Allah a ki kira min Ummina". ta furta hakan ƙwayar idonta na mannewa akan fuskar Turaki da yake tsaye yana kallonta ya kasa tahowa wajenta. bayan sun gama wayar da Ummi, nurses ɗin su ka cigaba da tura gadon, suka tsayar da shi a gaban Turaki. duk sun kasa ɗauke ido daga na juna, ita da take cikin ciwo ita ce me ƙarfin halin yi masa murmushi, don a wannan lokacin Turaki baya iya jin ko murmushin menene zai iya yi, ko da ace kuwa haihuwar tayi, har sai ya ga ta koma asalin Fulaninsa da ya sani, ba wannan Fulanin da yake gani ba me ƙarfin hali. ta miƙa masa hannunta ya kama ya riƙe, ya zubar da gwiwoyinsa a gaban gadon yana ce mata,"sannu Fulani Nah, sannu ƴar aljannah". sai fuskarta ta juye zuwa tsantsar damuwa tace da shi,"kayi haƙuri Jannaty ba zan iya ba, nayi duk iya ƙoƙarina amma na kasa, Dr ɗin yace ƙugun maza gare ni ba zan iya haihuwa da kaina ba sai dai suyi min aiki". Turaki ya kasa ce mata komai, ya kifa goshinsa a gefen hannunta, ta ɗago ɗayan hannun dake da canular da ƙyar ta ɗora a kansa. "Ka kwantar da hankalinka don Allah Jannaty, babu abun da zai faru kaji?, lafiya lau za'ayi aikin nan da izinin ubangiji, kuma lafiya lau za'a fito maka da ni da ƴaƴanka". Turaki ya ɗago kansa ya kalleta, a san da yake amsawa da Allahumma amin. Fillo ta dinƙa kallonsa tamkar yaune ta soma ganinsa, mamaki take yi sosai, bata taɓa yi masa murmushi ba yaƙi mayar mata da martanin hakan, haka zalika bai taɓa kallon fuskarta ba, ba tare da tasa fuskar ta washe da kyakykyawan murmushi ba, a yau kuma a wannan lokacin fuskarsa na looking so hard, babu wani emotion da za ta ce ta tsinta a ciki, zatonta ranar yau ita ce ranar da yake ta jira, wan nan lokacin shi ne yake tsimayin jiransa saboda ƴaƴansa guda biyu za su fito duniya, don haka a wannan lokacin ya kamata ace taga yana farin ciki ko ya ya ne. amma tun a gida da ta fara ce masa ciwo, yay ɗan guntun murmushi yana tsokanarta da Lukutar gombe zata haihu zata sace a koma gidan jiya, zata dawo kamar muciya da zani. ta san tayi dariya a lokacin da yay wannan maganar, but ita a lokacin data tsokane shi da cewa haka aka gani a muciya da zanin aka nace sai da aka ɗauka, bata ga wani kuzari na martanin dariya daga gare shi ba, kawai dai ya miƙe ya ɗauko jarkar rubutu ya bata ta tasha cikin mutuwar jiki. ta lumshe idonta ta buɗe kafin tace,"ƙarfe nawa Jannaty?". zai iya cewa da ƙyar ya iya karantar agogon kafin yace mata,"takwas da rabi Fulani nah". ta sauke numfashi ta ce,"sun ce sai ƙarfe tara da rabi zamu shiga, da za su bani dama da na kalli gabas nayi adu'a". sai kuma tace,"ka ci abinci Jannaty?". bai iya magana ba illa girgiza mata kai da yay. "me yasa to?, kana so Aayan ya taso ya fika ƙiba ko?, mutane suke tsokanarka su na cewa ɗanka yafi ka ƙiba". sai ya daɗa riƙe hannunta kamar wanda za'a ƙwace masa ita yace,"ta ya zan iya saka wani abu a cikina alhalin kina cikin mawuyacin hali?". "Jannaty na faɗa maka ka kwantar da hankalin ka, lafiya lau za'ayi komai babu abin da zai faru". "zan ci abinci amma sai an fito da ke, wataƙila ma yau ba zan ci irin abincin da za kici ba, wan da zanci zai fi wanda zaki ci daɗi, ko don saboda nayi ƙiba a daina yi min gori". tayi murmushi,"to me zaka ci?". sai ya kai hannunsa ɗaya saman breast ɗinta ya taɓa yace,"madaran yarana zan sha, mu uku za kiyi feeding yau". "baka da damuwa guda ɗaya ma za'a bar maka, sai suyi shairing guda ɗaya". ta ƙara cewa,"ka yi min waƙar da kake yi min Jannaty". ya girgiza mata kai,"ban da waƙa sai dai adu'a". "to kayi min karatu cikin ƙira'arka me daɗi". a hankali kuma ya shiga biyo mata suratul shu'araa. har san da yazo kan aya ta ashirin da takwas,_wa'izaa maridhtu fahuwa yashfeeeen_. sai ta ji wani abu na bi ta ƙasan zuciyarta, ta kira sunansa da irin amon sautin da zai ce bai taɓa jinta da shi ba, ya kalleta idanuwansu suka sarƙe waje ɗaya, ya haɗiye wani abu da bai san menene ba kafin yace,"menene Fulani Nah?, me kike so?, ciwon yana raguwa?". ta mayar da murfin idon ta rufe ta ce,"hold me Jannaty, i want to talk to you". ta faɗi hakan tare da buɗe idanuwanta. "Jannaty duk da halin da nake ciki ina yi maka murmushi, please kayi min wannan kyakykyawan murmushin naka atleast ko da sau ɗaya ne, ko da bai yi faɗi da yawa ba, ka daure kayi min ko ya ya ne". shirunta ya haɗe da bayyanar haƙoran Turaki duka a waje, maimakon murmushin da tace tana so sai kawai ya sakar mata dariyarsa me daɗin sauti, dariyar da har ita ma sai da tayi irin tasa ɗin, dariyar da ta ratsa jijiyoyin Turaki ta zarce har cikin zuciyarsa ta huda wani waje. ta buɗe baki a hankali tace,"ko kai fa Baban biyu, please you take good care of our kids, ko babu ni na san kai uba ne na gari, na san yaran mu ba za su yi kukan maraici ba, kayi musu dukkan gatan da uba yake yiwa ƴaƴansa, ka ba su wadataccen ilimi, kaja su a jikinka ta yanda zaka dinƙa jin damuwar kowannen su, ka kula da tarbiyar su, tarbiyar su da iliminsu!, tarbiyarsu da ilimin su don Allah Jannaty". furucin nata yasa yaji kamar zai yi kuka, ya ƙanƙameta yana faɗin,"bana son magana irin wannan, you promise me that we will be together forever, so why talking like this?". "Allah ya baka haƙuri ba zan ƙara ba daga yau, ka yafe min". taja hancinsa laɓɓanta na motsa da murmushin ƙarfin hali tace,"i love you Turakin Fulani". sai kawai ya miƙe tsaye, ya manta da nurses ɗin da ke tsaye a gefe, ya manta da su Mum da ke tsaye su na kallonsu, ya manta da mutanen dake giftawa, yasa hannu ya ɗagota, ya haɗe bakinsa da nata yana kissing har tsawon minti biyu, kafin daga baya ya shiga kissing ko'ina na fuskarta sannan ya rungumeta tare da furta,"i love you morethan you do Fulanin Turaki". a lokacin ne kuma Dr ya bawa nurses umarnin cewa su wuce da ita ɗakin tiyatar. sai taji hannun Turaki na zamewa daga cikin nata, muryarsa na fito a mugun karye, yana yi mata adu'ar Allah yasa ayi cikin sa'a, Allah yasa ta fito lafiya. sai kawai ta rumtse idanuwanta gam, tana jin nurses ɗin na tura gadon nata su na barin wajen, tana jin kamar tana so tace musu su ƙyaleta ba sai an ciro yaran ba. Turaki yabi ta da kallo yana ganin yacca hawaye ke sauka ta gefen idonta, hawaye na farko da zai cewa ya gani a tare da ita tun a ɗazu da ta fara naƙudar. "don Allah kar kuyi min allurar bacci, ku yi min idona a buɗe, ina son ganin a yacca za'a fito min da Babies ɗina". ta faɗa idanunta na kallon likitocin da ke kanta tare da nurses, a lokaci ɗaya sai taji tausayin bawan Allahn da rayuwarsa take tamkar a nannaɗe da tata, Turakinta! Mijinta!, uban ƴaƴanta, wanda ta san a duk lokacin da tata rayuwar ta ƙare, lokacin da ta zama bata cikin rayuwarsa, to tabbas bata san ya duniyarsa zata kasance ba. sannan tausayin ƴaƴan da zasu fito daga cikinta yay mugun matse zuciyarta, bata san ya rayuwarsu zata kasance ba a yayin da babu ita, bata san ya tasu ƙaddarar rayuwar zata zama ba, bata san irin jarabawowin da za su fuskanta ba, duk da ta san babbar jarabawa a gare su shi ne na rashinta, za su taso ba tare da uwar da ta kawo su duniya ba, za su ta so ba tare da sun san wannan ɗumin jikin na uwa ba, za su taso babu wannan kulawa da soyayyar da yake a wurin uwa ba kaɗai. "bismillahir-Rahmanirrahim, bring the knife". haka taji likitan da ke tsaye akanta ya faɗa, kuma bayan wannan zata iya cewa jinta ya ɗauke na ɗan wani lokaci kafin ya dawo. a san da aka fara aikin, idanun Fillo a jiƙe suke sharkaf da hawaye, hawayen da ya hanata ganin komai sosai. a wannan lokacin dukkan tunaninta ya gama hargitsiwa da kowanne motsin dake faruwa a cikin ɗakin tiyatar, tana jin yacca sautin zuciyarta ke bugawa da ƙarfi acikin kunnenta. lokaci ɗaya taji sautin wata ƙara ta fita a jikinta, sautin da ta tabbatar na yanka ne, cikinta ake yankawa!, sai taji zafin ciwon da take ta daurewa ya ƙaru, zafinsa na ƙaruwa sosai da sosai, zafin da har ta kai ga kasa tantance cikinta ake yankawa ko kuma ruhinta ake zarewa. hawaye ya bi ta gefen fuskarta, ta ji kamar ta ɗago tasa hannu ta danne wajen da aka yanka ko zata sami sassauci, sai dai babu abin da zata iya, bata da ƙarfin motsi ko kaɗan, tamkar matacciya take. tsawon lokaci babu wani abu dake wanzuwa a cikin ɗakin tiyatar sai fafutukar da likitoci ke yi wajen ciro yaran daga cikin mahaifiyar su. kunnuwan Fillo sun ji lokacin da aka ciro Baby na farko, Babyn da taji Dr na cewa da nurses su yi ƙoƙarin su wajen ganin yayi kuka, sai taji wani farin ciki ya ratsata, farin cikin da taji tamkar an yi mata bushara da gidan aljannah. so take taga yaron da aka ciro, don haka cikin ƙarfin hali da dauriya ta karkata kanta gefe domin kallon jaririn da cibiyarsa kaɗai take iya hangowa, kuma a san da nurse ɗin ke juyowa zuwa sashinta, lokacin sabuwar azaba ta ƙara ratsata, tayi saurin rumtse ido tana ambaton innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. ambaton nata ya haɗe tare da kukan Baby na biyu da aka ciro, kukan da ya cika ɗakin gaba ɗaya, kukan da zata ce kamar ta tsinci sunan da take ta muradin ta haife su taji sun kirata da shi, Ummina!. a san da Babyn yay shiru sai taji jikinta ya tsaya a lokaci ɗaya, yay sanyi ƙalau, numfashinta mai nauyi na cigaba da fita, yayin da zuciyarta ke bugawa a hankali, hakan yasa ta fahimci cewa hargitsin azabar ciwon da take sha yazo ƙarshe, ƴaƴa biyun da ke cikinta an fito da su duniya, ta zama uwa, dukkan fatanta da burinta ya gama cika, atleast ta samu masu yi mata adu'a a kowacce daƙiƙa a yayin da komai ya riga ya kai ƙarshe. ta riga ta san abin da yake cikinta tuntuni, macece da na namiji ne ba sai an faɗa mata ba a yanzu. tana jin yacca motsin yaran da ake ta aikin gyarawa ke mutsutsu acikin kunnenta, tana jin yanda zuciyarta ke bugawa da son su da ƙaunar su, sannan a hankali ta fara jin komai na zamewa daga cikin kanta yana barin ƙwaƙwalwarta, cikin ranta tana adu'ar,_"Ya Rahman if you decide to take my soul at this time, i beg you Allah to give my husband and my childrens the strength to bear it, Allah kaji tausayin ƴaƴana, ka tausayawa maraicin su ka basu tamkar Hajiya Madina a matsayin wacca zata kula da su"._ da ga wannan furucin dake cikin ranta, sai kuma bakinta ya shiga maimaito kalmar shahadar da taji tana wanzuwa acikin kanta, hakan yasa idanuwan likitocin da ke ɗakin ya manne akanta, akan murfin idonta da ke barin kan twins ɗin da ake nuna mata amma ta kasa kallon su. kuma wucewar sakanni biyar komai ya zama ya ƙare, komai ɗin dake rayuwar Fillo, shikenan wa'adin da ubangiji ya ɗiba mata ya cika, alƙalaminta ya riga ya bushe, ubangiji yayi hukuncinsa. bayan wasu mintuna Turaki da ke tsugune a ƙofar ɗakin tiyatar yaji an buɗe ƙofar, bai motsa ba dan bai san ta yanda zai motsa ba, yana so dai ya buɗe idonsa yaga abin da ke wanzuwa, so yake ya buɗe ido ko ya samu zuciyarsa ta daina bugawar da take yi. acikin wata fargaba da ke tare da shi yaji an ɗora hannu akan kafaɗar sa, sai ya ɗan buɗe ido kaɗan yana kallon nurses guda biyun da ke tsaye akansa tare da likita, ba zai ce ga lokacin da ya miƙe ba, ya dai tsince shi ne tsaye akan ƙafafunsa yana kallon jariran dake hannun nurses ɗin, bai san me yake ji a zuciyarsa ba, amma dai ya san bakinsa ya kasa rufuwa, ya miƙa hannu ya fara karɓar namijin, sakanni uku yana kallon yaron me kama da shi sak kafin ya miƙa shi ga Dr Yusuf da ke tsaye a kusa da shi, sannan ya daɗa karɓar macen da ita ce ƙarama, kuma a lokacin da ya ɗora idonsa akanta a lokacin Doctor ɗin yace da shi,"I am very sorry to tell you that your wife is no more, Allah yayi mata cikawa, ina yi maka ta'aziyya Allah yaji ƙanta da rahamarsa". a maimakon rufewar da idanun Turaki ke shirin yi sai yaji sun maƙale akan jaririyar da ke kuka a hankali, jaririyar da yake hasko fuskar mahaifiyarta a fuskarta. sai kawai yaji furucin likitan na maimaituwa acikin kansa,_"your wife is no more"._ sai yaji kalaman likitan su na ƙara tafiya a hankali, yayin da yake ji su na barin cikin kunnensa har zuwa cikin kansa da zuciyarsa in da suka samu masauki, don ya kasa gane ta yadda zai karɓe su balle har su yi ma'ana a cikin ƙwaƙwalwarsa. Fulani ta mutu?, yana nufin Fulaninsa ta mutu, Fulani ta mutu!, Fulanin da suka yini tare yau, to ta ya zai yarda da hakan?. sai kawai ya kutsa ta tsakiyar mutanen da ke gabansa ya faɗa cikin tiyata room ɗin still yana riƙe da jaririyar, yana shiga ya hangota an rufeta, rufewa tana nufin lulluɓewa har fuska, irin lulluɓewar da ya gani akan Maamansa sati biyu da suka wuce, irin lulluɓewar da yasan mamaci kawai ake yiwa, irin lulluɓin nan da ake yiwa gawa kaɗai. Turaki ya tsaya cak tamkar mutum mutumi, idonsa na kallon gawar, yaji guiwoyinsa sun yi sanyi ƙalau, irin sanyin da suka kasa cigaba da ɗaukar sa, don haka sai ya nemi bango ya dafe gudun kar ya faɗi jaririyar da ke hannunsa ta cutu, haka ya dinƙa jan ƙafa yana dafe da bangon har ya ƙarasa gaban gawar, a lokacin ƙafafunsa suka kasa ci gaba da ɗaukarsa ya zube a wajen, ya

Chapter 70 of 73