kuma wallahi bani bace".
Hajiya Madina ta sauke numfashi, calmly tace da ita,"nutsu Fillo ki juyo ki fuskance ni". tana fizgar numfashi ta juyo ta fuskanceta kanta a ƙasa tana cewa,"wallahi Maama bani bace, wasu ne su uku, kuma ban sansu ba".
Hajiya Madina tace,"kuma kin tabbatar asirin ne?".
tai saurin ɗaga kanta,"ehh Maama haka suka ce, Allah ne shaidata".
"amma me yasa baki taɓa faɗa min ba?".
tace,"Maama ban san ta yanda za'a yarda da ni ba, kuma da naga duk na kwashe waɗanda naji sun faɗa shisa ban faɗa miki ba, kuma bana so ku shiga damuwa ma".
Mum ta fashe da kuka sosai tace,"idan na yafe na wa ba zan yafe na Babana ba, sai mun tsaya a gaban ubangiji da ko waye yake da hannu akan lamarin nan, me yarona yayi mata tsakani da Allah?".
Maama na kallon Baffa tace,"kai kam har wanne kalar zunubi ka aikata da ake bibiyarmu da asiri?".
zai yi magana ta ɗaga masa hannu,"wait Baffa, ya kamata mu fara sauraran maganar da yarinyar nan tayi, ni na san wacece ita fiye da tunaninka, tunda ta faɗi hakan tabbas haka ɗinne, beside ka duba ƙarancin shekarunta ta ina zata iya haɗa ƙarya irin haka farat ɗaya?, kai fa alƙali ne kayi nazari akan furucin nata mana".
ta dafa shoulders ɗin Fillo tace,"yi min bayanin komai kinji, karki ji tsoro".
Fillo ta shiga basu labari tiryan-tiryan tun daga ranar farko har zuwa rana ta ƙarshe da tayi wannan accident ɗin da Turaki ya bugeta, al'amarin yay matuƙar girgiza su, suka dinga salati suna maimaitawa, Mum dai kuka kawai take yi magana ma ta kasa, banda Hajiya Madina dake ta aikin tsinuwa tana jan muguwar adu'a akan duk wanda ma ya san da zancen za'ai asirin ba iya wanda yay ba.
Ummi dai kallon ƴarta kawai take yi da mamakin da yaƙi barinta da kuma tsoron kar ace aljanu ke aiki a jikinta, dan jefa kai a irin wannan haɗarin sai mutanen ɓoyen.
Mum ta sauko daga kan kujera ta rungumeta tana yi mata godiya da saka mata albarka, haka ma Maama, sun ma rasa kalar godiyar da zasu yi mata, kamar zasu haɗiyeta saboda son yarinyar da suka ji ya shigesu, matsayin da take da shi a zuciyar Hajiya Madina ya nunku a sa'i guda.
Baffa dai yay shiru saboda abin ya ɗimauta shi sosai, abinda yaji yana faruwa a film da kuma wata nahiyar yau shi ne akan ɗansa har ma da matarsa.
Turaki ganin yacca idon Baffa ke kansa yace,"kayi haƙuri Baffa, da na zauna nayi nazari shine naga babu da abinda ya dace na saka mata da shi sama dana aureta, kuma ni banje wurin mahaifinta da niyyar aurenta ba a lokacin, tausayi ne yasa na amince aka ɗaura auren babu shiri, kuma Baffa ina tsoron kar da kuce min baku amince ba shisa ban faɗa muku ba nayi gaban kan nawa, amma dan Allah dan Annabi kayi haƙuri ka yafe min".
Baffa yace,"to wa yay maka waliccin auren?".
yace,"ba kowa Baffa, ni da naje wurin Baban nata izinin auren naje nema shine yace sai dai na aureta a lokacin in ba haka ba zai bawa wani ita".
Baffa yace,"kai kuma ba zaka iya rayuwa babu ita ba?".
ya girgiza kansa da sauri yace,"a'a Baffa, kawai naji ina da son ta zama mallakina a sanda na san waye mahaifinta".
Baffa ya girgiza kansa,"har yanzu labarin film kake ban Muhammad, waye zai ɗau ƴarsa ya aura maka babu waliyi kamar dai wani mahaukaci irinka?".
yace,"idan baka yarda ba zan iya kai ka wurin limamin masallacin da ya ɗaura so you can believe me".
Baffa yace,"why not wajen mahaifinta daka ce ka damƙawa sadakin?, ko kuma da limamin ku ka haɗa bakin ƙarya?".
Turaki ya kalla Fillo da yake jin kukanta na taɓa zuciyarsa yay ƙasa da murya sannan yace,"saboda yana da son zuciya ba lallai ya faɗi gaskiya ba idan akaje wurinsa, mugu ne zai iya cewa ma bai san da maganar ba".
Baffa yace,"kamar yanda kaima baka da gaskiya ba, becoux i cant believe cewan kaje kaima kanka aure ba tare da saninmu ba kawai saboda zuciyarka na ganin abinda ya dace kayi kenan, da ta taimaka maka kana so ka saka mata ba akwai hanyoyin kyautatawa da yawa ba? dole lallai sai ka aureta sannan zaka biyata da abinda tayi maka?".
Turaki yay girgiza kansa yace,"kayi haƙuri Baffa, gani nayi ko duka dukiyarmu aka bata ba'a biyata ba".
sannan yay saurin ɗauko wayarsa ya shiga file manager ya lalubo record ɗin da yayi yace,"kuma Baffa zaka yarda da ni in kaji wannan".
su Maama sukai shiru suna sauraron Hayyo dake cewa,"ni idan har ka tafi ba zan yarda da cewa iyayenka zaka je ka kawo ba, ka ajiye sadakinta kawai shine nasan da gaske aurenta kazo nema, duk da ba ƴata bace amma zanyi abinda uba na gari ya dace yayi a matsayina na wanda yaga an haifeta a titi na taimaka musu ita da uwarta, in kuma ba sadakinta a yanzu ina mai tabbatar maka kana barin wurin nan zan aurawa Malam Mudi ita tunda nasan inda take, sai muje da hukuma aje wurin tsohuwar da ta saceta mu karɓota".
haka suka dinƙa sauraron maganganun Hayyo har zuwa sanda Liman yace da Turaki ya ajiye sadaki, ya jiye maƙullin motarsa bayan ya shaida musu cewa shi maraya ne baida iyaye, Hayyo kuma yace ya ba shi ita sai su haɗu can su zama shege da shegiya su haifi ƴaƴan sunnah.
Baffa ya dinƙa kallon wayar Turakin kamar Hayyo yake gani acikin wayar, Kaka ta zabga salati tana faɗin,"wallahi tallahi wannan muryar Hayyo ce gata nan tarrr, yanzu lalacewar tasa har ta kai ya sheganta yarsa?, kai jama'a wannan duniya ina zaki damu?, ina azzalumai suke so suje da ɗumbin alhaki?, me ya sami Hayyo ni ƴar nan?, ni da nake uwar matarsa ma yana cewa bai sanni ba?, to wallahi tallahi Fillo ƴarsa ce ta sunnah ma kuwa, mutuwar zuciya ce kawai irin tasa da yake cewa a titi ya tsinto su, amma ai Allah yana ji yana gani".
Ummi na kuka sosai tace,"akwai Allah, akwai ranar hisabi, ko da na yafe zaluncin da Hayyo yayi min a zaman aurenmu ba zan yafe sheganta min ƴa da yayi ba, ba zan yafe masa ba sai Allah ya saka min".
Fillo tai jikin Ummi tana kuka sosai da jin maganganun Hayyo da suke yi mata zafi, kukan da duk ya taɓa zuƙatan wajen.
Kaka na kuka tace,"waye kuwa zai so haɗa jini da Hayyo banda ƙaddara".
Baffa yace,"shi waye shi ɗin ne?".
Kaka tace,"Hayyo ai sheɗani ne, ba zaka tabbatar da hakan ba sai ka aura masa ƴarka, matansa sunfi goma kuma duka babu wacca ya saka, kowacce gajiya take tayi da muguntarsa ta bar masa gidansa, da zarar ya sami abinda yake so a wajen mace shikenan kuma ta zama abar banza a wurinsa tun balle ki sami ciki saboda baya son ƴaƴa, ba ya aje abinci a gidansa kuma baya bari a fita a nema kuma baya yarda masu taimakawa su kawo masa".
ta numfasa ta ƙara cewa,"kaga wannan". ta faɗa tana nuna masa Ummi, tace,"maraicin uba ne yasa tayi zaman gidan Hayyo, har ta haifi wannan ƴa bai daina dukanta ba, saboda kawai ta haihu har sau biyu kuma taƙi tayi zuciya ta bar masa gida, ita kuma ƴaƴanta kawai take tausayi duk da tana da ɗan banzan haƙuri, akan dalilin barinta gidan ma abinci aka aika mata daga gidan wata ƙawata yana zuwa ya haɗa da ita da wadda ta kawo abinci da wannan ƴa yay musu duka, sannan yay mata zagi na ƙare dangi irin zagin da ko dabba ba aiwa shi ba, mahaifinta dake ƙasa kansa na san sai yayi baƙin cikin wannan aure saboda kiran sunansa da yay yana zaga, kuma wallah banda wannan yaro yay jihadi ya aureta ina me maka rantsuwa da Allah siyar da ita zai yi, dan manyan ƴaƴansa mata 3 wallahi tallahi duk siyar da su yay, bafa siya irin ta abayar da sadaki ba, a'a! a taya ɗan mutum a ɗau kuɗi a bashi ya ɗauko yarinyar ya bayar a tafi da ita, kuma da bakinsa zai faɗa yace ya siyar da wance shi baida hurumin rayuwa da ƴaƴa".
kowa ya furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, zuciyar Baffa na tafarfasa yace,"siyar da ƴaƴa kamar ba ɗan mutum me daraja ba, ƙwarai ya zama dole hukuma ta kama shi".
Kaka tace,"waye hukuma zata kama?, Hayyon?, yo iyaye nawa ne sukai ƙararsa kuma da anje station yake fitowa, ai lamarin Hayyo sai dai a barwa ubangiji kawai".
Baffa yace,"lamarinsa bana ƙyalewa ba ne, kafin ya bar duniya dole ya gane kurensa, hukuma wacca ta san aikinta ita zata kamasa a wannan karon, ba irin hukumar cin hanci ba".
Kaka ta girgiza kanta kawai dan tasan hukuma ta kama Hayyo ba abu ne me yiwuwa ba, yo a cikin mugun halayen Hayyo wanne ta faɗa babba aciki?, ai bata faɗi komai ba dan wani abun dole sai an sirrinta.
Baffa ya katse shirunta da faɗin,"gobe insha'Allahu zamu je tare da ku".
tace,"to ai ya tashi daga gidan da muka sani, ance yayi kuɗi sun bar unguwar ne ma ko garin Allah masani".
Mum tace,"indai ɗan garin ne sai aje gidan iyayensa, a kama mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole zai kawo kansa".
Ummi tayi wani murmushi me ciwo, Kaka ma haka sannan tayi ƙarfin halin cewa,"ai babu wanda ya san iyayen Hayyo balle danginsa, duk iyayen da yake amfani dasu wajen neman aure na bogi ne, hayarsu yake yowa, kuma wallahi duk binciken mutum ba zai san ba iyayensa ba ne, hmmm Hayyo fa sai Allah, wanda ya sansa kawai shi ya sansa".
su Hajiya Madina suka shiga jijjiga kai tare da jinjina lamarin, tausayin Ummi ya kama su da ita kanta Fillon.
Baffa na kallon Turaki yace,"you did the right thing my son, auren yarinyar nan da kayi jihadi ne babba, and i am proud of you for that tun da har kai tunanin tsamota daga hannun azzalumin uba, kana da lada a wurin Allah insha'Allah, Allah yayi maka albarka, don't worry komai ya wuce, ina shaida maka naji daɗi ƙwarai da gaske da ya zamana mugun halin mahaifinta ka fara dubawa, ko ni me iya aura maka itace a sanda naji halinsa, but hakan ba yana nufin next time ka ƙara yin gaban kanka ba tare da ka sanar damu abu ba".
Turaki yace,"insha'Allahu Baffa i won't repeat such a mistake again".
yaji muryar Baffan yana sa ke cewa "na yarda da aurenku na kuma saka masa albarka, idan mahaifiyarta da kakarta sun amince kana iya tarewa da ita a yau, i will call Hakimi and inform him, and i will try all my best to make Boɗejo to understand so that ba za'a sami matsala ba...fatana ɗaya ka zama adali a tsakanin matan da ubangiji ya ƙaɗarta maka aurensu, Allah yay ma rayuwar aurenku albarka".
Wani irin Relaxation breath Turaki ya saki tare da faɗin Alhamdulillah ƙasa-ƙasa kafin ya ɗaga murya yace da Baffa,"thank you Father, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana, ya bani ikon faranta maku iyaka ƙarshen rayuwata".
sai ya kusa bawa Baffa dariya, kamar ba shi bane ya firgice a ɗazu ba, tun balle da yace ya saketa.
Baffa ya kalla Kaka yace,"to Kaka ban san ku a yanda zaku ɗauki wannan auren ba, kun yarda da auren ƴarku da yay babu saninku ko baku yarda ba?".
Kaka tace,"wanne irin rashin yarda Alhaji, wa zai ƙi haɗa jini da nagartattun mutane irinku ai sai dai idan bai samu ba, kuma wa zai ƙi yarda ya aurawa ƴarsa mutum kamar me babban suna, yaro me hankali da sanin yakamata, ai ni sai dai nace Allah ya albarkaci auren kuma mun gode sosai dan ka yiwa wannan ƴa babban taimako a lokacin da ya dace dan inda baka yarda ka amince da auren ba Hayyo siyar da ita zai yi wallahi, babu wani wanda yaywa alƙawarin aurenta".
Mum na kallon Ummi tace,"Maman Fillo baki ce komai ba?".
Ummi ta kalli Fillo dake jikinta tana kuka tace,"to ai ni gani nake yaronku yafi ƙarfin auren wannan ƴa, abun kamar kwata-kwata babu haɗi, ina shi ina auta?, but ba zanƙi ba dan nasan ƴata hannun na gari zata shiga insha'Allah, kawai dai akwai abunda nake dubawa ne".
Ummi tana kallon Turaki tace,"amma me Babban suna zaka iya zama da ita?, kasan tausayi daban so daban, karka ƙwari kanka kace zaka zauna da ita saboda ta taimaka maka, shi aure dan so da ƙauna ake yinsa, in akace za'ayi aure dan taimakon juna kawai ba lallai aji daɗin zaman ba, anfi so ayisa in har da so da ƙauna ta yanda duk za'aji daɗin zamantakewar har ƙarshen rayuwa".
Turaki ya shafo wuyansa bai ce komai ba, Mum tace,"kayi magana, dan ba zai yiwu mu baka ƴa ba alhalin baka shaida mana kana sonta ba, dan haka in har ka san ma baka sonta to a miƙo maka takarda kawai".
da sauri ba tare da shiri ba yace,"ina sonta Mum".
Hajiya Madina tace,"a ina ɗin?, ina son yake?".
ya ƙara shafo wuyansa cike da kunya yace,"Allah ina sonta Maama".
Hajiya Madina ta miƙe ta kamo hannun Fillo dake ta aikin kuka, tana dubansa take cewa,"ina buƙatar lefen ƴata nan da 3days kafin na fara tunanin ko zan baka ita".
sai yanzu hankalin Fillo ya dawo jikinta, ta waiga ta dubi Turaki sannan ta kalli Maama tace,"Maama ai ni bana sonsa, ba zan iya aurensa ba".
Mum ta kalleta tayi murmushi, ganin ba wanda ya saurareta ta fashe da sabon kuka tana cewa,"Allah Maama ni bana sonsa, ba zan iya aurensa ba dan Allah kice ya sakeni, ni taimakonsa da nayi saboda Allah nai, dan Allah ya sakeni".
Ummi ta buga mata tsawa,"kul kar na ƙara jin furucin nan daga bakinki".
Hajiya Madina tace,"a'a yi mata a hankali, da gaskiyarya ai, dan shi yana so kuma shikenan ita ba za'aji ta bakinta ba?".
ta kalli Turaki tace da shi,"ka zo ka nemi yarda ƴata da amincewarta akanka, kwana biyu na baka, idan ba kai nasara ba za ayi duk abinda take so".
tana faɗar hakan taja hannun Fillo suka fita, wacca ke ta faɗa mata ita dai asa ya saketa yanzu ba zata zauna da shi ba.
bayan fitarsu Baffa yay adu'a aka watse, ya rage daga shi sai Turaki, on serious note Baffa ke kallonsa kamin yace,"kenan ita Fillo itace uwar gida?".
kansa a ƙasa yace,"ehh Baffa".
ya numfasa ya sake cewa,"to ya zaman nasu zai kasance?, haɗe su zaka yi ko ya?".
yay ɗan jim kamin yace,"yanda kace Baffa".
"ahh wannan kuma ai kai zaka yi making decision, sai dai in shawara ta kama sai in baka".
yace,"tom Baffa ka bani shawarar".
"ka bari sai mun zanta da hakimi tukunna, now you can leave, sai da safe".
*Vote, comment and share.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_Avoid error mistakes._
*42*
Jar mota ƙirar rangerover ta sauka daga kan titin ta gangara gefe tayi parking a gaban tebur ɗin masu sayar da fruites.
matashin saurayin dake daga cikin motar ya zuge glass yay wa me siyar da pineapple sallama, mutumin ya amsa yana barin wajensa ya ƙaraso gun motar. zuwan nasa yasa Hamid miƙa masa hannu suka gaisa, me pineapple ɗin yace da shi,"ta nawa za'a zuba yallaɓai?".
Hamid yace,"sako guda goma, kar a yanka kowacce". mutumin ya juya yaje ya zubo pineapple ɗin a cikin leda har guda biyar ya dawo, Hamid ya buɗe masa booth ya saka a ciki, kwata-kwata ba ita yay niyyar siya ba kawai dan mutumin ya rigada ya saka rai ne.
mutumin ya dawo yana goge hannunsa da durster yace,"ranka ya daɗe an gama sakawa".
Hamid ya juya bayan motar ya kalla mahaifinsa dake daga kishingiɗe kamar me bacci amma ya san ba bacci yake ba, sannan ya juyo ya ƙara cewa da me pineapple ɗin,"bamu apple". cikin sauri yaje ya dawo.
Hamid yace,"nawa ne kuɗin?". yace,"ka bada dubu takwas". Hamid yasa hannu a aljihu ya ɗauko ya basa, yana shirin barin waje ya tsayar da shi da cewan,"yauwa kaga dan Allah tambaya nake dama".
mutumin yace,"to Allah yasa na sani".
Hamid yace,"gidan Alƙali Dikko nake nema".
mutumin yace,"ohh gidan uban marayu zaka ce". sannan ya shiga yiwa Hamid kwatance yanda zai gane, Hamid yay masa godiya sannan yaja motar ya bar wajen bayan ya ɗau apple ɗaya ya miƙawa Mahaifin nasa yana roƙonsa akan ya daure yaci ko ya ne.
tafiya kaɗan ta kawo su ƙofar gidan Alƙali Dikko, dai-dai lokacin da motar Maama ta shiga gidan, Hamid ya fito yana ƙarewa girman gidan kallo sannan ya ƙarasa yay knocking gate.
me gadi ya buɗe ƙofar ya fito suka shiga gaisawa da Hamid, bayan sun gama gaisawa Hamid ke tambayarsa dan Allah ko akwai Hajiya Bilkisu anan gidan.
Me gadi yace,"a'a wallah babu Hajiya Bilkisu, wani yay maka kwatance da nan ɗinne?".
Hamid yace,"ehh tou, daga can gidan sarki aka kwatanto mana nan ɗin, da tana aiki acan sai akace ta dawo nan gidan".
Me gadi yace,"ohh ai nan ɗin main gate ne na gidan, da yake ɓangaren ma'aikatan gidan daban, daka zagaya ta baya zaka ga gate ɗin irin wannan ne".
Hamid yay masa godiya sannan ya koma mota, yana zagawa ɗaya gate ɗin ya faɗawa me gadin sunan Kaka na ainihi shima yace gaskiya bai san wannan sunan ba, sai dai bari ya kira masa shugabar ma'aikatan.
ba jimawa Yami tazo wajen, tana kallon Hamid tace,"kar dai jikanmu ne kai". ta faɗa saboda tsananin kama da Fillo da ta gani a fuskarsa kamar an tsaga kara.
yace,"ehh to indai wadda nake nema ɗin ita kike nufi to ni jikanta ne".
Yami na murmushi tace,"Allah sarki, ai da yake ma ta kwana biyu da tashi daga nan ɗin, amma bari sai muje yanzu na raka ka gidan da suka koma dake ba anan unguwar ba ne".
Hamid ya jira Yami ta koma ta sanyo mayafi sannan suka tafi, ita bata ma lura da wanda ke bayan motar ba saboda tana nufar shiga baya Hamid yace da ita ta dawo gaba.
sunyi tafiya me nisa kamin su isa gidansu Fillo, motar tasu ta shigo layin a sanda Fillo ke fita daga layin tana sanye da uniform da kuma niƙab zata wuce islamiya.
ƙofar gate ɗin a buɗe take dan haka bata tsaya knocking ba, Yami ta shiga dan sanarwa da Kaka, a parlo ta sami Kaka ita ɗaya tana kallo, suna gaisawa tace da ita,"taso ƙawata, taso taso".
Kaka na bin ta da kallo tace,"lafiya dai Ƙawata?".
Yami tace,"lafiya lau Ƙawata, ke dai fito da sauri kiga abin mamaki abin farin ciki".
cikin azama Kaka ta miƙe akan kujerar ta ɗauka hijab ɗin Ummi dake kan kujera tabi bayan Yami da sauri hankalinta duk ba'a kwance ba dan taga Yami duk a hargitse take.
Fitowarsu bakin gate Kaka tai saurin dafe ƙirji asanda tayi tozali da Hamid jingine a jikin mota.
"me idanuna suke gane min?". wani farin ciki da jin daɗi suka mamaye Hamid ya baro jikin motar yana zuwa ya rungume Kaka.
ta ɗan ture shi a jikinta tana faɗin,"Hamid kaine ka zama mutum haka?, dama zan ƙara sanyaka a idanuwa na?, Hamid dama kana raye baka taɓa nemana ba?".
Hamid ya sauke numfashi yace,"kiyi haƙuri Kaka Allah ne bai nufa ba, amma wallahi kina raina, ta ya zan manta dake bayan kece silar zuwan mahaifiyata duniya".
Kaka ta share hawayen farin ciki tana bin motar da kallo kamin tace,"to ya akai kazo nan Hamid?, kar dai wani abu ne ya faru mara daɗi?, wannan motar kuma ta waye?".
Hamid yace,"Kaka ai ban manta da kina aiki a gidan sarki ba, na faɗa miki tsawon shekarun nan Allah ne kawai bai nufa ba sai yanzun".
tace,"dan dai kaga bana tare da abu me muhimmanci a wurinka ne shisa ka kasa nemana".
yaga tana kallonsa tana ƙara bin motar da kallo yace,"mota ta ce, ba zai yiwu mu shiga daga cikin gidan ba ne?".
Kaka na kallonsa tace,"zai yiwu mana Hamid, ai shiga cikin gida ma dole, gidanku fa kazo taho muje".
ta faɗa tana juyawa ya dakatar da ita,"Kaka mota ba zata shiga ciki ba ne?".
tace,"to sai dai ka duba tunda mu ba mota garemu ba, tun zuwanmu dai ta wannan ƴar ƙofa muke shiga".
ya ƙarasa ya duba yaga gate din yaga ba me zugewa ba ne, hakan yasa yace mata,"Kaka to bari na fito da shi".
tace,"waye?".
yay ɗan jimm damuwa na bayyana a fuskarsa sannan yace,"tare da Abba muke, ba zai iya tafiya ba sai na taimaka masa".
idanun Kaka a waje tace,"kana nufin Babanka Hayyo?".
ya ɗaga mata kai,"ehh Kaka".
da mamaki sosai tace,"to me ya sami ƙafar tasa da ba zai iya takawa ba, ko wani mulkakken ya zama?".
ya sauke numfashi yace,"jarabawar ubangiji".
Kaka ta taɓe baki tace,"Alhaki dai yake bibiyarsa".
bai ce komai ba ya ƙarasa mota ya buɗe booth ya ɗauko wheelchair sannan ya buɗe bayan ya taimakawa Hayyo ya fito ya ɗorasa akan kujerar, tun fito da shi Kaka tayi masa kallo ɗaya taji mugun tsoro ya kamata kamin bala'in tausayinsa ya biyo baya, indai gani take yi da kyau ya rame kamar me cutar ƙanjamau, mutumin da yake jayent son kowa ƙin wanda ya rasa, mutumin da bama a gane girmansa ko ada amma yanzu girma ya bayyana ajikinsa sosai kace me shekaru ɗari.
Hamid ya turo shi suka ƙaraso inda Kaka ke tsaye cike da tsoron duniya, hoton abubuwan da suka faru a baya suna ta haska mata a ido, ita dai banda Hamid ya faɗa mata yace Abbansa sai ta rantse tace ƙarya ne ba shi bane, dan gaba ɗaya ya fita daga kamanninsa tsabar wahala, kamar ba wannan ƙaƙƙarfan namijin da ke zage dukkan ƙarfinsa ya zane mata ƴarta ba.
ta girgiza kai tana ƙara jin tsoro na al'amarin sakayyar wanda aka zalunta, a hankali tace da shi,"Hayyo". ya ɗago da wuyansa da ƙyar wanda ya laƙwashe.
ya kalleta ya buɗe baki yace,"nannnnaaammm Daddddda". ya faɗa cikin ƙinƙinar da sai kayi da gaske zaka gane, kuma cikin murya kamar ta masu koyon magana.
kawai sai Kaka ta fashe da kuka sosai tana ambaton,"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". ta ƙara kallonsa tace,"Hayyo kai ne ka koma haka?". ta tambayesa tana tuna zaƙin maganarsa ada, wanda daɗin amon muryarsa na ɗaya daga cikin abinda yake jan hankalin mata garesa, dan ƙarya ne Hayyo yayi magana kana wajen baka ce kaji daɗin muryarsa ba.
hawaye ya sakko a idonsa yace,"Kakkkkaaa dddddaaa Allllahhhh kikkki yaaafeeee miiiimmmmnn, dddda Allllahhhh kiiii neeemmmooo minnn Haliiimaaaattttuu".
sai da aka ɗauki cikakken minti ɗaya da ƴan kai sannan ya iya faɗar kalmar da za'a faɗeta cikin sakanni biyu, yana maganar bakinsa na rawa, haƙoransa na daddatsewa akan harshensa.
Hamid yasa handky yana goge masa uban yawun da ya dalala ajikinsa ya ɓata gaban babbar rigarsa kamar an sheƙa masa ruwa.
ƙafafunsa suka shiga rawa akan wheelchair ɗin ya kamo hannun Hamid yana faɗa masa,"zaazzzzzannnn saukkkkkaaaa innnneeee miiii yaaaaaffiyyarrrr Dddddaaaada".
kaman yanda Kaka ke hawaye haka ma Yami, saboda ƙarya ne ace kaga halin da Hayyo ke ciki baka zubar da hawaye ba.
Hamid na kallon Kaka yace,"wai yana so zai sauko ya nemi yafiyarki". tace,"Hayyo ba sai ka sauko ba na yafe maka, ni baka min komai ba dama". ta dubi Hamid tace,"mu shiga". tai gaba suka biyo bayanta, Yami ta tura ƙofar. suna nufar entrance na parlon gidan Ummi ta fito, Kaka ta fara gani wadda ke aikin goge hawaye, bama ta lura da sauran ba, tai saurin ƙarasowa wajenta tana faɗin,"lafiya Dada?, na fito naga ba kya parlon me ya faru?".
Kaka bata iya magana ba dan har yanzu a girgiza take, kuma kamin tayi mata nuni dasu Hayyo, Ummi taji hannayen mutum a ƙafafunta da ɗigar ruwan hawaye.
ta kai idonta kan Hamid dake zube a gabanta ya riƙe ƙafafunta, ba fuskarsa ta kalla ba, saman kansa kawai ta kalla ta shaida ɗanta, sai taji wani abu ya tsarga mata, ta kulle ido tana jin taruwar ruwan hawaye aciki.
"Hamid". ta kira sunansa da amon sautin da ya tafi ya taɓa har zuciyar Hayyo. "me kake nema a ƙafafuna Hamid?, laifin me kayi min?, tashi tsaye na ganka ɗana".
Hamid ya miƙe yana hawaye, Ummi ta rungumosa jikinta suna kuka tare, wucewar daƙiƙa biyu Hamid ya zare jikinsa daga nata yana bin mahaifiyar tasa da kallo, wadda yaga ta ƙara kyau da girma kamar ba ita ba.
"ya akai kazo nan Hamid?, wa ya faɗa maka inda muke?".
tambayoyin da tai masa kenan, kuma kamin ya bata amsa idonta ya sauka akan halittar da duk lalacewar da tayi ba zata kasa ganeta ba a kallo ɗaya, tai saurin ɗauke ƙwayar idonta daga kan mutumin da take jin ta tsane shi tsana mafi muni.
Hamid ya buɗe baki
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 45 Chapter of 73