Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gidan Fatima anjima kaɗan zasu dawo". Dada ta ɗanyi tsaki tace,"ma za kirawota ta dawo ta zo ta duba jikin yarinyar nan, tayi ma ta allura yanda zazzaɓin zai fi saurin sauka kinga ajima akwai taro, ba'a tara jama'a babu amarya ba, ko kuma an gayyota jama'a kuma su zo ace musu ba taro". Ammi tace,"bata da lafiya ne?". "yo gata can dai tana neman kashe kanta ai, ciwo yana cin ta babu wanda ta faɗawa saboda shegen nurƙufanci da miskilanci da baƙin hali irin na Hayyo". Ammi ta ɗauki waya ta shiga kiran lambar Yusrah, tana ɗagawa ta ce da ita ta dawo yanzu sai ta koma. Dada ta sa aka kira ma ta Ummi, tana zuwa Dada ta ɗaga sandarta ta rafka ma ta a ƙafa. Ummi ta ɗan ja da baya tana bata haƙuri tun bata ji laifinta ba. "ki shiga ciki kiji damuwar ƴarki tun da ke dai soluwar uwa ce". ta faɗa tana bin Ummi da harara. Fillo dai na zaune tun da su Dada suka fita, tana riƙe da farar takardar da Turaki ya bata ranar da suka je dubo shi a asibiti bai da lafiya, kallon takardar ta-ke tana juyata gudun hawayenta na ƙaruwa. ta jinginar da kanta jikin bango idanuwanta a rumtse tana ƙoƙarin danne kukan dake neman cin ƙarfinta, babu abin da ke haskawa cikin ƙwayar idanuwanta sai rubutun dake cikin takardar, kawai sai ta kasa riƙe kukan ta sake shi ya fito da ƙarfi a sanda Ummi ke shigowa ɗakin. hankalin Ummi tashe ta yo kan gadon tana tambayarta lafiya, bata ma san ta shigo ba sai a yanzun, da sauri ta cusa takardar a cikin rigarta. Ummi ta kwantota kafaɗarta tana lallashinta da ban haƙuri. zatonta duk kukan ba na komai ba ne sai irin kukan da wasu amare ke yi idan zasu bar gida. Fillo ta samu ta rarrashi zuciyarta da ƙyar saboda bata so Ummi ta san abun da yake faruwa, bata san irin damuwar da zata shiga ba in har taga takardar sakin da ke hannunta, ba lallai ta iya ɗaukar wannan ƙaddarar ba, zata ga kamar itama bata yi dacen samun miji ba ne kamar yanda ita ma bata yi sa'ar miji ba a sanda ta auri mahaifinta, dalilin da yasa ta ɓoye kenan kuma ba ta tunanin za ta faɗa, ai tun da har ana zaman idda a gidan miji zata yarda su kai ta, ranar da ta gama iddarta acan sai ta sanarwa da kowa abun da ya faru, amma ba a yanzu ba da ba ta san wanne irin hali Ummi zata shiga ba akan hakan. Yusrah ta shigo tayi ma ta allura, aka kuma ɗebo uban magunguna a first aid da aka ɗauko a ɗakin Innah aka bata. Ummi ce da kanta ta bata abinci taci, sai da taci da dama sannan ta ƙyaleta. "ki daina kukan haka nan kinji Auta ta, bari naje ana ta baƙi daga ɓangarenmu, idan kika ji daɗin jikinki sai ki zo ku gaisa da su Yaya Murja". tana kallon Ummin ta ce,"wace ita?". "da babarta da Kaka ubansu ɗaya, su na can sun zazzo ma fa da yawansu, sai tambayarki suke yi, nayi zaton kuna can gidan Asma'u shiyasa ai". ta gyaɗa kanta kawai, Ummi ta fita daidai da shigowar su Maijidda, waɗanda suka shigo suna ta masifa akan ɗinkin da tela yayi musu ba daidai ba. AmaturRahman na faɗin,"na rantse da Allah in ace ba yau zamu sa kayan nan ba sai ya biyani zan baro shagonsa, ɗan iska me kama da ɗan daudu". Maijidda tayi watsi da nata akan gado ta ce,"ai ni idan kinga na saka waɗannan kayan to sauya ni aka yi, gwara idan na koma gida na dinƙa saka su idan zanyi aiki amma ba'a bikin Hussaina tah ba, ban da rainin hankali ɗinki sai kace ance masa tsofaffi ne zasu saka". Amatullah ma ta shigo ta jefar da ledar hannunta, Raudha ma haka, duk in ka kalla fuskokinsu ka san ransu babu daɗi. Raudha tayi tsaye jikin wadrobe tana fuskantar Fillo, ta harɗe hannaye tana cewa,"kin ga yanda fuskarki ta kumbura kuwa?". ta rufe idonta kawai ta kwanta tana juya musu baya, Amatullah ta ce,"ai ɗa zu Hammah Hamid ce yay idan ya dawo ya tarar ba ta daina ba sai ya zaneta babu ruwansa da matar aure ce". Raudha ta sauke numfashe ta ce,"i never see such a kind person me shegen kuka ma irinta, da muna saudia zatona ko dan Dada ta ce sai an saketa ne, da muka dawo kuma na kasa fahimtar auren ne bata so ko kuma kukan barin gida ne". "kin taɓa ganin amaryar da take kuka irin haka dan zata bar gida?, ita dai barta dan ta ga ƴar auta ce shagwaɓa tayi mata yawa shiyasa". AmaturRahman ta faɗa tana wucewa toilet. Raudha ta zauna kusa da Fillo tana kamo hannunta ta riƙe, ta ɗau wayarta tana kiran lambar me makeup da zata zo ta yiwa amarya anjima da za su yi Fulani Day, bayan sun gama wayar suka ci gaba da maganarsu ta abubuwan da zasu yi anjima. ƙarfe uku na rana aka fara shirya amarya, wata cousin ɗin su da ta zo daga benue tana ta complain akan rashin zuwan ango da aka ce ba zai zo ba, har sai da aka ce ma ta ai baida lafiya tukunna ta sarara ta hutar da yawun bakinta daga masifa. ita dai Fillo duk babu walwala, ƙwayar idonta na manne a cikin mudubi kai kace kanta take kallo, nan kuwa hoton ranar da suka je asibiti ne kawai ke haska mata. ta tuno sanda suka shiga room ɗin da Turaki ke kwance an saƙala masa oxygen, ga wasu abubuwa da akayi masa connecting, kallo ɗaya dai zaka yi masa idonka ya cika da ƙwalla haka kuma kaji tsoron Allah ya kama ka. ita da ta gansa ma sai da tayi mugun tsorata saboda kumburar da ya yi kamar an hura shi, a yacca yake ma zaka ce gawa ce, har yanzu ta kasa kwatanta abin da taji a lokacin da ta gansa da kuma abin da take ji zuwa yanzu. kawai sai ta rufe idonta tana hasko lokacin da ta gyara masa zaman hannunsa akan gadon a sanda ya buƙaci hakan, lokacin da taji ta kasa rabuwa da hannun nasa ta riƙe tayi masa irin riƙon da bata taɓa yiwa hannun wani mahaluƙi ba, har yanzu tana jin sautin muryarta a kunnuwanta da suka dinƙa fita da amo na tsananin tausayi suna jera masa kalmar sannu tamkar yawun bakinta zai ƙare, kuma a sanda take ji a jikinta kamar yana buƙatar wani abu daga gareta sai taji ya riƙo ɗaya hannunta ya zura ma ta farar takarda, wannan farar takardar da ke ɗauke da baƙin rubutu me ɗacin ɗanɗano, rubutun da take ji gwara a soketa da mashi akan abata karatunsa kuma a alaƙantata da shi, rubutun da taji ya tsayar da wani dunƙule abu a maƙoshinta ya hana ko da yawu wucewa, ita dai ta san ko kaɗan bata son Turaki, daidai da bugawar sakan na agogo ba ta taɓa jin wani abu me kama da sonsa a cikin zuciyarta ba, tausayinsa kawai take ji wanda shi ma daga Allah ne, amma ta rasa dalilin da yasa ta damu da sakin da ya yi mata, ta rasa reason ɗin da yasa take jin kamar ta mutu akan wannan sakin. ƙwayar idonta ta ƙara haska mata san da ta ɗauki tsayin daƙiƙu uku tana kallon takardar kafin ta iya ɗauke idonta daga kai ta sauke su akansa da yake kallonta da wani rauni da zata iya cewa ta gani acikin ƙwayar idonsa, ta san lokacin da idonta ya manne acikin ƙwayar idonsa, amma ba zata ce ga sanda hawaye masu azababben zafi suka shiga sauko ma ta ba, ta san dai ta ɗau tsayin lokaci tana kallonsa har sai da shi ya ɗauke nasa idon akanta ya kauda fuskarsa gefe, kauda fuskar da yasa taji kamar an tsikareta, tayi saurin miƙewa tana sakin hannunsa da ta riƙe ta fita da ga room ɗin tana danne kukan da yake cinta, kukan da har yau kowa ya rasa na menene har da ita kuwa, kuma kukan da har yau yaƙi tsagaita ma ta. hawaye su ka sauka akan foundation ɗin da me makeup ke blending ma ta, me kwalliyar taja tsakin ƙorafi tana matsawa da baya da cewar,"haba ke kuwa don Allah, haka fa jiya ma kika yi mana ki kasa akai ta westing time. idan ba za ki iya daina kukan ba kice a fasa yi miki mana ki daina wahalar da ni, ni wallah ban taɓa ganin amarya me masifaffan kuka ma irinki ba". tai maganar da muryar ɓacin rai. kowa sai ya hayayyaƙowa Fillo akan kukan da take yi sam bai dace ba, ran kowa ya ɓaci aka fara fita daga ɗakin ana barinta, Maijidda da tsananin tausayinta ta kamata suka shiga toilet ta wanke ma ta fuskar sannan suka dawo, me kwalliyar taƙi tasowa, duk da kuɗi za'a biyata masu yawa bata jin za tayi ta yin aikin wahala haka, har sai da Ammi ta shigo tayi magana tukunna ta miƙe tana jaddadawa Fillo akan kar ta ƙara ɓata ma ta aiki. sharp sharp akayi kwalliyar da tayi bala'in haska Fillo, ta dawo tamkar ba ita ba, aka fito da ita cikin shigar fulani kamar ka saceta ka gudu, Maijidda ta dinga roƙonta akan ta daure tayi murmushi ta kore damuwar fuskarta kar tayi musu irin ta jiya, duk ta yanda ta so ta yi hakan ta kasa, har sai da suka shiga parlon Maudo taji Dada na ba da labarin. "ehh mana, ai ni ban taɓa ganin ƴar banza mata ba irin wannan tsohuwar, ke ni da naje asibitin ma ban san sanda na tofar da yawu ba da na ganta, kin ganta kuwa a fige kamar figaggiyar kazar da bata kama abinci ba, naji haushin kaina ma da na zauna waje ɗaya ina ta masifa banje munyi ido huɗu da ita ba tun farko ta raina kanta, muna haɗa ido ta zabga ma ta harar da ta fi tata, tana ta maganganunta ni dai na kirawo likita nace masa ga sabuwar patient nan". ba ta san lokacin da siririyar dariya ta suɓuce ma ta ba, kuma cikin sa'a Nuratu ta ɗauketa hoto a lokacin, hasken camerar yasa ta ɗago ido karaf camera woman ma ta ƙyasta ma ta, sai kawai taji abun ya burgeta hakan ya bayyanar da dukka kyawawan fararen haƙoranta, suka fito cikin wani salo na burgewa da ɗaukar hankali, idanuwanta su ka yi wa ta lumshewa suka buɗe ta kalli me hoton da irin kallon da ke tsuma zuciyar duk wani lafiyayyan namiji. tafin da aka fara ana waƙa irin ta su ta fulani sai taji a lokaci ɗaya yana tafiya da damuwar da take ciki, yana tafiya da wannan tarin hawayen da ke cikin ƙwayar idonta yana musanya shi da murmushi me faɗi. *Gombe.* "ka yi wankan?". Bello ƙaraye ya tambayi Turaki lokacin da ya sakko daga upstairs. Turaki bai ce da shi komai ba ya wuce dining, da ga yacca yake tafiya zaka san bai gama warwarewa ba, har yanzu jikin nasa da saura, duk ya bi ya rame, Bello ya taso shi ma ya isa dining ɗin yaja kujera ya zauna. "me za ka ci na zuba maka?". ba tare da Turaki ya kalle shi ba yace,"mene aciki?". Bello yana nuna masa flask na abincin guda biyu yace,"nan fried suppagetti ce, nan kuma tuwan shinkafa miyan agusi". Turaki ya sauke numfashi yana kwantar da kansa jikin kujerar dining ɗin ya ce,"couscous na ke so da miyan hanta". Bello yay ta kallonsa before yace,"akwai data a wayarka?". Turaki yay masa wani kallo, kallon da ya shaidawa Bello abin da yake nufi, hakan yasa shi cewa,"to ni dai duk da ba'a ji da ni a gidanmu irin yanda ake ji da kai, na rantse da Allah ban taɓa shiga kitchen da sunan girki ba sai dai in shiga in kwasa, to tsakani da Allah ta ina zan san yanda ake dafa wani couscous balle miyar hanta, yunwar dare dai ta taɓa sawa na dafa ƙonanniyar taliya, idan kuma za ka ci irinta yanzu in shiga kitchen ɗin". Turaki ya harare shi tare da jan tsaki. Bello yace,"to ai shiyasa nace ka ban wayarka sai in yi dowloading vedio, ina ce ai kuna da komai ko?". jin Turakin bai tanka masa ba yace,"yanzu dai tun da babu wanda kake so ɗin ka daure kaci tuwon shi ma ai ɗan uwan miyar hantar ne, kafin a kira Maama a faɗa ma ta, kaga tun safe baka ƙara cin komai ba kuma Dr ya hanaka zama da yunwa". Turaki ya ture plate ɗin da ya ajiye masa a gabansa, Bello ya ɗaure fuska yana cewa,"ban da ma dai girma irin na rashin lafiya me zai sa in zauna ina biyewa ƙaton gardi irinka ina yin nan nan da kai kawai saboda baka da lafiya, ehh tou sai kuma girma irin ta ƴan'uwantaka, kuma itama gaskiya na ga zaka cutar da ni sai a koma abota irin ta haɗuwar gate rabuwar bakin gate". yay tsaki,"haka kawai mutum Allah yay masa gata ya ba shi mace ya ta shi ya korata gidan iyayensu, Allah ma ya rufa maka asiri da wata billahi da ka ɗanɗana kuɗarka, ka bar ganin ina tare da kai ba komai zan iya yi maka ba kamar yanda matarka zata yi maka, banda ma rashin tunani da rashin shawara irin naka, da ka san Baffa yayi maka gate da gidansa ai da ka dawo sai kace ka mayar da ita, da tuni yanzu kana gaban Maama ana tarairayarka kamar ƙwai, abincin ma a baki ake baka ni kuwa duk abinka wallahi sai dai kaci da kanka ko kuma mu koma asibiti aci gaba da zaman jinya". Turaki ya kalle shi da takaici ya ce,"Bello when za ka zama me cikakken hankali?". Bello yana kai lomar tuwa ya ce,"ka siyo min kawai maganin jiran lokaci". Turaki zai yi magana akayi sallama a parlon, Bello ya kai idonsa kan Hamid, yay masa bismilla da ya ƙaraso, ya iso wajen nasu suna ta cewa ya zauna yana ce musu a'a. yana kallon Turaki ya ce,"akwai room guda ɗaya da babu key ɗin sa". Turaki ya rufe ido ya shafo wuyansa, kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce,"wanne room ne?". Hamid yace,"wanda ke downstairs". Turaki ya sosa girarsa sannan ya ce,"bari na dubo maka". ya ta shi ya shiga bedroom ɗin Ilham da ke nan ƙasa, ya buɗe drowern madubi ya ɗauko makullayen da suke ciki duka, ya dafe kansa da yaji yana mugun sara masa, kafin ya fito ya bawa Hamid ya ce su gwada dan bai san wanne ba ne aciki. Hamid ya fita bayan yay musu sallama, Bello ya kalli Turaki da damuwa ke fito masa ɓaro ɓaro me haɗe da tsoro ya ce,"Dr ya kawo maka result ɗin ne?". Turaki ya ce,"bai kawo ba, ya dawo ranar kuma sai ya tarar mun tafi hospital, but ya kira ni ɗazu ya ce she is not pregnant, ni dama na san zance ne irin na Boɗejo kawai, da na kusanceta ai ban bari sperm ya zuba a ciki ba". Bello ya tallafe haɓa yana dubansa ya ce,"ɗan ƙara min haske mana MT, kaga ni ma na kusa shiga da ga ciki and bana so na fara tara ƴaƴa da yawa, anyway before kace min ɗan iska, ni dai tsakani da Allah ban ga abin ƙi ba a tare da yarinyar nan Ilham ba da har ka yi kuskuren sakinta MT, Mace irin cikakkun matan da ake so da suka haɗa komai, waccan kam ta zo sai kama sha wahalar raino kamin jikintaya ginu". Turaki ya cika bakinsa da iska sannan ya ce,"a wurina sakin ta da nayi ba shi ne kuskure ba, babban kuskure a wajena shi ne da bana iya sirrinta abuna dole sai na faɗa maka". Bello ya ƙyalƙyale da dariya bai ce komai ba, for few seconds sannan ya ce,"yanzu ma ai na san akwai abin da ka ke so ka faɗa min tun ranar nan amma ka kasa, kuma na tabbatar ba dai-dai ka aikata ba shiyasa ka ke shakkar faɗa min, yanzu dai ina jinka me ka ƙara zuwa ka aikata da babu shawara balle zurfin tunani, dan na lura da kai tun da masu jeren kayan nan suka zo ka bi ka rikice kamar mara gaskiya". Turaki ya dafe kansa, sai da ƙyar ya iya faɗawa Bello abin da yake ransa, furucin farko Bello ya ce da shi,"totally MT baka da hankaliii, what are you telling me?, kai wai mistake ɗin farko ba ya zamar maka izina sai ka aikata da yawa?, har yanzu fa baka fita da ga matsalar da kake ciki ba shi ne zaka ƙara saka kanka a wata?, ko kuma ɓacin ran iyayen ne ba ya damunka?". ya daki dining table ɗin da hannunsa yana nuna shi da yatsa ya ce,"sam sam babu hankali a tare da kai, abubuwan da kake aikatawa masu lafiyar ƙwaƙwalwa basa yinsa". Turaki ya ture yatsan nasa yana cewa,"karka ƙara nuna ni kuma karka ƙara ce min banda hankali, damuwata nake faɗa maka matsayinka na aminina, mafita na ce ka tayani nema ba wai ka tsaya faɗa min baƙaƙen maganganu ba". ran Bello a ɓace ya miƙe tsaye,"an faɗa baka da hankalin, ka yi abun da za'ai maka kallon me hankalin ne?, har yaushe ka zauna ka zartar da wannan hukuncin akan yarinyar da gaba ɗaya ba ta cancanci haka da ga gareka ba?, kai da ba zaka zauna ka yi shawara da mutum ba sai bayan ka aikata abun da zai zame maka damuwa, kai ko da wani ma ya ce ka saketa ma ai sai ka zazzage shi, amma saboda toshewar basira irin taka yarinyar da banda taimakon Allah da kuma taimakonta da yanzu ka zama tarihi ko kuma da yanzu kana nan acikin lalurar da aka kasa maganceta, asiri fa!, asiri fa ta dinga ɗaukewa akanka MT, akwai wanda zai iya sa kansa a haɗari ne just becouse to save some'ones life irinta, sunanka fa kawai ta sa ni ba kai ba kuma tayi helping ɗinka har kake raye zuwa yanzu kuma cikin ƙoshin lafiya". takaici yasa Bello yin shiru yana rasa ma a wanne sahu zai saka Turaki, sai ya ƙyasta yatsunsa biyu ya ce da shi,"to bari kaji na faɗa maka, fushin Baffa akanka ba komai ba ne akan fushin Mum da zaka gamu da shi, sarai dai ka san da cewa tana son yarinyar nan. kuma in ƙara faɗa maka abu ɗaya, ba zan waiwayeka ba a sanda ka faɗa cikin cakwakiya ta biyu, ban san ka aikata ba kuma ba kai shawara da ni ba a sanda zaka aikata ba, dan haka karka kuskura ka neme ni". yana gama faɗar hakan ya fice, Turaki ya bi bayansa da kallo kafin ya tashi ya wuce ɗakinsa. babu abin da yake so yanzu irin yaje gidan su, amma Baffa ya ajiye ƙaton soja a bakin gate ya ce duk ranar da yaga wata fuska ko da mai kama da tasa ne a kama shi a ɗaure. washegari da safe yana kwance a ɗaki aka murɗa handle ɗin ƙofar ɗakinsa, motsin ƙofar yasa shi buɗe ido yana kai dubansa ga me shigowar, ganin Maama yasa shi miƙewa zaune da sauri, ta iso wajensa tana jin tausayinsa na ratsata, ta zauna a kusa da shi ta dafa shoulders ɗinsa ta ce,"ya ƙarfin jikin naka". ya ce,"da sauƙi sosai". ta bi shi da kallo sosai tana lura da yanayin jikin nasa, babu kumburin ko kaɗan duk ya sace, ramar ce dai kawai da tayi masa yawa. ta sauke numfashi ta ce,"Bello ya ce min ba ya gari shiyasa na taho, ina drugs ɗin naka?". yana kallonta ya ce,"ƙarya yake yi, fushi yake da ni shi ne ya tafi". Maama ta girgiza kai tana murmushi ta ce,"Allah dai ya kyauta muku, anjima ne za ku shirya ai". ta miƙe tana isa table ɗin da yake tsakiya ta ɗauko magungunansa ta dawo ta zauna, ta ɓallo ta zuba masa a baki. "ka sha ka ƙara jin ƙwarin jikinka, anjima akwai dinner. su ma suna kan hanya sun taho kawo Fillo, amma ba nan ɗin zasu kawota ba direct, za su sauka a wurinmu after an dawo da ga dinner sai mu kawo maka ita, hakan ai ya yi ko? baka da lafiya ban zauna nayi shawara da kai ba me babban suna". shi dai bai iya cewa komai ba, Samha ta shigo ta dire basket na kayan abinci, ta zuba a plate kamar yanda Maama ta umarceta. kamar wani ƙaramin yaro haka Maama ta dinƙa feeding nasa, bayan ya gama ci ta cika masa bathtube da ruwan zafi ya shiga yay wanka, sanda ya fito ba ta ɗakin, bayan ya gama shiryawa zai fita sai gata ta dawo. "ai ba fita zakayi ba, koma ka kwanta ka huta. alfarma ɗaya nake so a wurinka me babban suna, ka cire damuwa don Allah, ka ɗauko rigar walwala da farin ciki ka saka, yau babbar rana ce a wurinka, ranar da ta ke zaɓinka". ya ce,"Maama Baffa...". ta dakatar shi tana faɗin,"sau nawa zan faɗa maka in dai batun Baffanku ne ka ajiye shi a gefe, kai fa kujera ne a wurinsa kana zaune zai neme ka, duk wannan hawa saman da ya yi na ɗan lokaci ne, tsohuwarsa na hucewa zai huce, space kawai yake buƙata, kai ma kuma da ma kana buƙatar space ɗinsu, mu kanmu da ka gani ba ya kula mu, jiya ma ya bar mana gidan ya kaɗa inda bamu sa ni ba". Turaki yay ja ajiyar zuciyar zai yi magana ta ƙara katse shi,"Bello zai zo maka da kayan da zaka saka anjima, Khalil zai riga ku zuwa can wajen dinner ɗin". ya gyaɗa kansa kawai kamar yaro bai ce komai ba har ta fi ce. *Taraba* tun safe da Fillo ta tashi tana yin sallar asuba ta shiga toilet ta rufe kanta, a ƙasan tiles ta zauna tana ta kuka ta damƙe takardar sakinta a hannunta, so take ta yi musu bayani amma ta rasa ta inda zata fara. Sai da Ummi ta shigo sannan da ƙyar ta buɗe toilet ɗin ta shiga ta fito da ita, ta bi su Maijidda da duk suke kwance kan gado suna ta baccin gajiya, dan ba su tashi a event ba sai 11 na dare, kuma suka dawo gida suka ƙara ɗorawa da wani ba su suka kwanta ba sai 3, shiyasa sallar asuba ma duk da ƙyar suka yi. Ummi ta zaunar da ita akan darduma ta ɗauko Alqur'ani ta bata ta ce,"kiyi ta karantawa za ki ji sauƙin koma me ke damunki. tun da dai ni da nake mahaifiyarki ma ban isa ki faɗa min matsalar da ke damunkin ba, to ga maganin kowacce kalar damuwa nan ki ta karatu, ƙarfe sha ɗaya naji Dada na batun jirginku zai tashi". Fillo dai kallonta kawai take yi, har Ummi zata fita sai kuma ta ƙara cewa da ita,"in ma kina tsoron faruwar wani abu ne a auren naku ki yi ta ambaton innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, Allah zai sanya komai ya zamo mafi alkhairi a gare ki, ni dai har zuciyata bana jin komai a game da tarewar nan taki ba, kullum adu'a nake ina faɗawa ubangiji, kuma na gamsu da son da yaron nan yace yana yi miki". Ummi ta fita ta barta, ita kuma ta buɗe suratul Yusuf ta shiga karantawa, kamar almara sai ta fara jin duk wata damuwa da fargaba da komai yana tafiya yana barinta. ƙarfe takwas Ummi ta dawo ɗakin, hannunta riƙe da tray wanda ke ɗauke da kayan breakfast, ta ajiye a gaban Fillo, ita kuma ta aje alqur'anin hannunta ta miƙe ta shiga toilet ta wanko bakinta ta dawo, tare suka yi breakfast ɗin ita da Ummi, su na ci Ummi na yi ma ta ƴan nasihohi akan sabuwar rayuwar da zata tsinci kanta, da maganganu tausasa da duk suka sanya sauran damuwar da ke tare da ita barinta. ƙarfe tara Ammi ta shigo ɗakin nasu tare da me makeup, ta tarar su Maijidda da Amatullah sun sa Fillo a gaba sai tsokanarta su ke, saboda ta daina kukan da ta ke yi sai su ke cewa ashe dama so take yi akaita gidan miji shiyasa ta ishe su da kuka, yau kuwa ga idonta nan ƙyam sai ƙyallin farin ciki da yake yi, ita dai tana zaune babu wanda ta tankawa. Me makeup ɗin ma sai da ta tsokaneta,

Chapter 51 of 73