kujerar da take zama zata buga masa, babu shiri ya juya cikin sauri ya fi ce.
yana zuwa part ɗin Mum ya tarar da ita zaune a parlo ta zabga uban tagumi, zuciyarsa ta shiga lugude, ya tafi kamar munafiki ya tsuguna a gefen ƙafarta, bai san dai laifin da yay ba amma saƙon da Khalil ya ba shi ya san akwai laifin da ya aikata.
muryarsa a hankali ya ce,"Mum lafiya?". ya tambayeta yana ƙoƙarin cire hannun da tayi tagumin da shi, sai dai tun kan ya kai ga taɓata ta make shi da mugun zafi.
"matsa da ga kusa da ni".
ta faɗa tana sauke masa rikitattun idanuwanta da ke nuna zallar ɓacin rai, nan da nan hankalinsa ya tashi ya shiga tambayar laifin da yayi.
"wallahi tallahi idan har baka matsa da ga kusa da ni ba ko me na ɗauka sai na buga maka in yaso ka mutu in huta da baƙin ciki da takaicin rashin dacen haihuwarka da nayi".
ya buɗe baki ya furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yana kallonta zai ƙara yin magana a mugun tsawace ta dakatar da shi,"na rantse da Allah ka ƙara min magana a wurin nan sai na fiddo maka da nonona ka biya ni wanda na sha, banza mara mutunci shashasha butulu kawai wada bai saka halacci da halacci sai dai ya saka halacci da sharri, da ga ranar yau ina me tabbatar maka da babu ni babu kai har abada kuwa".
ta sauke yatsanta da ga kansa, ta ɗau wayar da ke kusa da ita ta kira Khalil, cikin mintina kaɗan sai ga shi ya shigo, tai masa nuni da kujera ya zauna a ɗarɗarce, ta ɗauki takarda da biron da ke kusa da ita ta wurgawa Turaki wanda ke dafe da kansa yana ta amabaton kalmar innalillahi a zuciya da fili, magana yake so yayi amma babu dama saboda rantsuwar da Mum tayi.
"mu ba matsiyata ba ne, kai tsiya ta yiwa ƙatutu, Allah ya hore mana yay mana arziƙin da zamu iya siye duk abin da ka mallaka har kake taƙama da shi, ka rubuta kuɗin matsiyaciyar wayar da kashe hannun ƴar mutane saboda ita, ko nawa ne za'a biyaka dan kai ne faqararre".
ta ƙyasta yatsunta biyu ta ce,"kuma ka sa ni, duk illar da hannun ƴar mutane yayi wallahi sai mun shiga kotu da kai".
ganin zai yi magana ta kuma doka masa tsawa,"kuɗinka nace ka rubuta".
yay taking deep breeth yana kulle idanuwansa yay rubutu ajikin takardar, da ido Mum taiwa Khalil nuni da ya karɓa, ya karɓa yana kallon abun da ya rubuta, Galaxy fold Z2 1.3ML tare da kuɗin gyara 700k. ya kalli Mum zai ma ta magana ta ce,"tura masa kayansa".
Khalil ya ɗau wayarsa in few minutes ya turawa Turaki kuɗin, seconds kaɗan sai ga ƙarar shigowar alert a wayar Turaki.
"Mum sun shiga". Khaleel ɗin ya faɗa yana dubanta. ba tare da ta kalle shi ba ta ce,"ka kira min Madam".
ya tashi ya fita, babu jimawa sai ga Hajiya Madina ta shigo fuskarta sam babu annuri babu walwala, ta tsaya cak da ga baya tana cewa da Mum,"ya za'ai ki kirani alhalin wannan ɗan banzan yaron yana zaune anan, ko kaɗan yanzu bana son ganinsa, zan dawo in sameki after ya fita".
ta faɗa tana juyawa Mum ta dakatar da ita da cewa,"so nake ki zame min shaida dalilin da yasa na kiraki kenan".
hakan yasa Maama dawowa tazo ta nemi kujera ta zauna, ta juyar da fuska yacca ko kaɗan ba zata fuskanci Turaki ba.
Mum tace,"ko bayan raina ban amince ba wannan ɗan banzan yaron yay aure, ina so ki zamar min shaida".
da sauri Turaki ya ɗago ido yana dubanta, me ya yi zafi shi ba wuta ba?, laifin me ya yi har haka?, yaji duniyar gaba ɗaya tayi masa zafi kansa na neman tarwatsewa, da ƙyar ya iya tattaro yawun bakinsa ya ce,"Mum me ya yi zafi haka?, wanne irin laifi na aikata muku?, idan abin da naiwa ƴarku ne na roƙeku don Allah kuyi haƙuri ni kaina na san nayi kus....".
maganar tasa ta yanke lokacin da yaji saukar jotter da biro a fuskarsa.
ya kalla Maama da ke kallonsa da tsananin ɓacin rai tace da shi,"ka rubuto min sauran sakinta shi ne zaka tabbatar min da kai isashshe ne, dan ba zan karɓi saki ɗaya ba domin kuwa Fillo ta gama aurenka har a naɗe duniya".
ya kulle ido yana sauke numfashi, sannan ya buɗe yace,"Maama ce muku tayi na saketa?".
"ba ka saketa ɗin ba ne?".
ya shiga girgiza kansa yana faɗin,"ni ban saketa ba Maama, idan ma haka ta faɗa muku to ƙarya take yi".
Maama ta dinƙa kallonsa babu ko ƙifce, kafin tace,"kai ko dai kayi hauka ne?, ko kuma shaye-shaye ka ke yi a ɓoye?".
ya ce,"Allah ni Maama ban san da wani batun saki ba a tsakaninmu, sai dai idan ita take buƙatar hakan shiyasa ta faɗa".
Mum na ta kallonsa ta kasa cewa komai dan kallon typical mahaukaci take yi masa, Hajiya Madina ta kira Zaytuna a waya ta ce taje part ɗinta ta ta zo ma ta da Fillo.
wucewar minti uku sai gasu tare, Fillo ta rakuɓe waje ɗaya tana rarraba idanu akan carpet, Turaki ya dinƙa kallonta yana ganin yanda fuskarta tayi jawur, da kuma uban bandage ɗin da ke hannunta.
Mum ta ce da ita,"karki ji tsoronsa ki saɓa shari'ar musulunci, faɗi ya sakeki ko bai sakeki ba?".
cikin dusashewar muryar kuka ta ce,"ya sakeni".
Maama ta ɗauki remote a kusa da ita ta jefawa Turaki sai ga shi a goshinsa, ya dafe wajen da lokaci ɗaya yayi malolo yana,"shhhh, Maama ni wallahi ban saketa ba ƙarya take yi".
Fillo ta ɗago ido ta kalle shi ta ce,"wallahi fa kake cewa?".
yanda tayi maganar dariya ta kusa fito masa amma sai ya dake ya zabga ma ta uwar harara ta yanda su Maama ba su lura ba, itama ta murguɗa masa baki tare da ɗauke idonta akansa ta kalli Mum ta ce,"tun a ranar da muka je asibiti duba shi ya sakeni, ni kuma na kasa faɗawa kowa, shi ne yau yace in dai ban bar masa gida ba sai na ƙwammace da ban taɓa saninsa ba har ma da ku".
ya kalli su Mum da duk idanuwansu ke kansa, da sauri ya ce,"Allah ban saketa ba". sai kuma ya juya ya kalli Fillon ya ce,"ni da bakina na furta miki hakan?".
ta harare shi tana fito da ɗayan hannunta da ga hijabi ta miƙawa Maama takardar hannunta.
ganin takardar idanuwansa suka fito waje da sauri ya kai hannu zai ƙwace a harzuƙe Mum ta sa masa ƙafa ta hamɓarar da shi gefe. ya ɗago da ga kifewar da yay yana ɗora hannu aka yana ambaton innalillahi da ƙarfi har sai da kowa ya kalle shi.
sanda Maama ta gama karanta takardar sai ta kalli Mum, ta miƙa ma ta Mum ta kau da kai tana girgiza kanta alamar ba zata karɓa ba.
Maama ta ce ma ta,"dan Allah ki karɓa your excellency, zuciyata zata fashe".
Mum ta juyo da sauri ta karɓa, ta kifar da takardar a cinyarta da ƙyar ta yarda da roƙon Maama ta karanta.
ta kalli Fillo a sanda ta gama karantawar ta ce,"yaushe ya ba ki wannan takardar?".
ta tsagaita kukanta ta ce,"ranar da muka je asibiti duba shi".
Mum ta ƙara cewa,"ruwan hawayenki ya shanye wajen adadin sakin, nawa ya rubuta?".
furucin Mum ɗin yasa idanuwan Turaki suka ƙawalalo waje fiye da ɗazu, ƙirjinsa ya ce taratsatsa.
Fillo ta buɗe baki wani sabon kukan na tahowa ta ce,"ai ban karanta ba".
Mum ta miƙa ma ta takardar tana cewa,"to karɓi".
Fillo ta karɓi takardar zata cusa a hijab Mum ta ce,"karantawa za ki yi ai, idan ba ki karanta ba sakin ai bai tabbata akanki ba, ki karanta sai ki nuna masa kuskurensa ki ɗau duk kalar matakin da kika ga ya dace da shi".
tana gama faɗa ta miƙe ta bar wajen, Maama ma ta fi ce, Zaytun ta haye Uptairs tabi bayan Mum, aka bar Fillo da Turaki kawai, ta ɗago kumburarrun idanuwanta ta kalle shi taga fuskarsa kamar baƙin hadari, hawaye na sakko ma ta ta ɗora ido akan takardar, sai taji fargabar yau tafi ta ko yaushe, ba ta san me yasa ba ko kaɗan ba ta ƙaunar adadin sakin da yay ma ta, sai dai kuma a sanda ta shiga karanta rubutun da ke ji sai taga saɓanin abin da zuciyarta ta faɗa ma ta tun ranar da ya bata takardar, idanuwanta suka karanta abin da yake daban da wanda take ta haskowa yana rubuce a jikin takardar.
wannan wani rubutu ne na daban, rubutun da ko kusa bai da alaƙa da abin da sakin da ta gama yankewa kanta anyi ma ta, rubutu ne take kallonsa da handwriting ɗin da ya burgeta, haka kuma taji kalaman da ke jiki na tafiya su na haɗewa da jinin jikinta, taji tana sha'awar da a karanta ma ta su a kunnenta.
ta karanta sau ɗaya ta kuma gane ma'anar but haka kawai sai taji tana ƙara buƙatar ta ƙara karantawa.
_my life depends only on you, i love you Fulani Nah, i love you up to the square of infinity, i promise you that i will take care of you morethan i will take care of my self, trust me when i say i can't do without you, Fulani Nah love me even just a bit._
ta rufe ido a sanda ta gama karantawa, taji bugun zuciyarta na sauyawa zuwa wani yanayi da bata taɓa riskar kanta a ciki ba a dai ga me da Turaki, ta sauke numfashi ta buɗe idon tana sauke akan Turaki.
tuni ya miƙe tsaye hannayensa na zube cikin aljihu, ta bi shi da kallo sanda ya wuce ta gabanta, sai da yaje bakin ƙofa sannan ya dakata ya juyo yana kallonta rai a haɗe murya a tamke ya ce,"kin taso ko kuwa".
ta ɗauke idonta da ga kansa ta mayar gefe, ya ƙara cewa,"ba za ki taso ba".
ta kumbura baki ta ce,"ai ka ce kar na koma maka gida".
Turaki ya saki baki yana kallonta, zai sake magana sai ga Mum nan ta sakko, ta yi masa kallo ɗaya ta ɗauke kanta ta isa kujera ta ɗauki wayarta, har ta juya sai kuma ta waigo ta kalli Fillo dake zaune ta ce,"tashi ki bi mijinki".
Fillo ta miƙe ta bi bayansa lokacin har ya kai bakin mota, ta buɗe baya ta shiga, ya kalleta ta mirrow ya ce,"do i look like your driver?".
ta hankaɗo laɓɓa gaba ta sunkuyar da kanta ƙasa tana shafa bandage ɗin hannunta, tsawar duniya ta dawo gaba tayi biris da shi kamar ba wannan Turakin da take tsoro ba, yay ƙwafa yaja motar suka bar gidan, sai da suka kusa zuwa gida sannan ya tsaya ya fito ya zagaya ya buɗe side ɗin take, yasa hannu ya yo waje da ita ya mayar da murfin ya rufe tukunna ya koma side ɗinsa ya figi motarsa ya barta a wajen.
tana kallo ya wuce gidansu da alama ba gidan ya nufa ba yanzu, ta juya ta kalla nisan da suka yo daga gidansu, sannan ta kalli kusancin da take da shi da na su gidan.
har ta juya zata koma can gidan sai taji yo haushin karnuka babu shiri ta tattare riga ta falla gida a guje, ta dinƙa buga gate babu ƙaƙƙautawa tsoro fal ranta, Baba me gadi kuwa na can toilet ya fito da sauri yazo ya buɗe yana cewa,"kai jama'a waye haka?".
yana buɗewa Fillo ta sunkuya ta ƙasan hannunsa ta shige da gudu, ya leƙo yana kallon waje bai ga komai ba, ya rufe ƙofar, yana juyowa yaga tuni har ta shige part ɗinta, ya buɗe hannu alamun ko lafiya?.
ƙarfe sha ɗaya Fillo taji ƙarar zuge gate, ta miƙe da sauri ta leƙa ta window taga Turaki ya fito a mota, ta ga sun tsaya da me gadi su na magana, idan ta fuskanta kamar Baban na labarta masa yanda ta shigo ɗazu ne, kuma da mamakinta sai taga ya wuce part ɗin Ilham as usual.
ta saki labulen windon ta koma kan gado ta kwanta da tunanin abubuwa kala-kala acikin ranta.
*Vote, share and comment.*
,*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*49*
washegari da la'asar Turaki na zaune a falonsa Bello ya shigo, kallo ɗaya Turaki ya yi masa ya mayar kan computer ɗin da yake dannawa, Bello ya ƙaraso gabansa ya ɗaga robar faro ɗin da yake hannunsa ya tuttule masa ruwan ciki akansa.
"Bello what kind of rubbish be this?".
"ɗan iska ma nan ya ganka ya ƙyale MT, yanzu na ƙara sarawa girman rainin hankalinka, kuma ban yafe ba zagin da ka ja min, akan kujera nake amma sai da na miƙe babu shiri tsabagen shigar zagin nan, har yau a jijjige nake da shi, sai kace kayi abu ni da banyi ba ni ke kwana aciki".
Bello ya faɗa yana zama kan kujera, Turaki ya dinƙa kallonsa da wani kallo kafin yay tsaki ya miƙe ya cire rigar jikinsa da ta jiƙe.
"tukunna ma ni ban gane maka ba har yanzu, ni ka rainawa hankali ko kuma su Mum ɗin ka mayar marainan wayonka?, sarai dai da iliminka ka san yarinyar nan ba ta da iddah akanka amma ka barta tana zama acikin gidanka".
Turaki bai tanka masa ba ya ci gaba da aikinsa, sai can Bello ya fara masa ƴar murya,"haba Aminina kar muyi haka da kai mana, faɗa min gaskiya don Allah. gudun ɓacin ran su Maama yasa ka ƙaryata sakin da kace min kayi ko kuma ni ɗin dai ka mayar sauna?".
"munafiki kawai". Turaki ya ce da shi yana hararsa.
Bello yay dariya sosai ya ce,"naji ka kirani da koma menene, ka san Allah idan baka faɗa min gaskiya ba to zanje na faɗawa su Maama gaskiyar abin da na sa ni, dan ni dai kace min ka saketa".
ya faɗa yana miƙewa.
da sauri Turaki ya ce da shi,"kai wai mara hankalin ina ne, yanzu sai kaje ka faɗa musu hakan?".
Bello ya ɗaga kafaɗa,"ofcourse, zan zuba maka ido ka ci gaba da zaman haramun da yarinya saboda kana gudun ɓacin ran iyaye, ai gwara a faɗa musu kawai su san gaskiyar abin da ke faruwa, yarinya ta tafi gidansu ta sami wani mijin tayi aurenta, kai kuma ai maka duk hukuncin da ya dace da kai. ko nufinka ka mayar da ita ne baka faɗa min ba?".
Turaki na daɗa ɓata rai ya ce,"ni dama ban saketa ba, ko da nace maka na saketa to wallahi tallahi ban saketa ba".
dariya ta zo wa Bello ya ce,"yau har da su rantse min?".
"saboda ka ƙyale ni na huta, kamar yanda ka barni na huta da takurarka na 7days".
Bello ya jijjiga kai,"amma kai dai anyi mugun ɗan rainin hankali, da ma saboda na ƙyaleka na 2days yasa kace min haka saboda ka san zanyi fushi?".
Turaki yay masa banza, sai kuma Bello ya ƙara cewa,"to kuma na ga har yanzu baka bar nan part ɗin ba?, ko kewar ta nan ɗin kake yi tunda ita ka ɗanɗana ka ji?, ko kuma ita ma baka saketa ba hankalin mutane ka raina?".
Turaki ya dire abin da yake ya dafe kansa, wucewar wasu sakanni tukunna ya buɗe ido ya zuba akan Bello ya ce,"in kana ƙaunar Allah da Annabi ka ƙyale ni, saboda fa wannan shegen sa idon naka yasa na barka a yanda itama waccan yarinyar ta ɗauka".
Bello ya gimtse dariyarsa ya ce,"tun da kace Allah da Annabi an wuce wurin. mu koma kan aiki, ɗa zu mun yi waya da financial sectary na IBTC company, ina wancan document ɗin da ka haɗa?,".
"shi na ke haɗawa yanzu?".
"what! ba jiya ka ce ka yi completing nasa ba?, yau fa ya kamata ace mun yi printing an kaiwa Baffa".
"to ya zan yi, after na gama wayar ta lalace, kano ma na kai gyaran a jiya, na so na tsaya na taho da ita Khalil ya damen da kira akan in taho gida ya ga kamar ba lafiya, but mun yi da shi me gyaran za'a kawo yau, ni kuma ganin ba su kawo tun safe ba naga gwara in haɗa wani kawai".
"wai wayar da ka siya last week ne ta lalace ko wanne?".
"ita ce".
"kaii! da ma ba original ba ce cutarmu suka yi, but tawa fa normal take, me ya sami taka ɗin da ma?"
Turaki ya ɗan kalle shi sannan ya ce,"fasata ta yi, gaba ɗaya ta tarwatsata ta koma fanko".
"ban gane ba, da ma ka haihu ne da har yara su ka fara yi maka babban ta'adi haka?".
"nop ban haihun ba dai tukunna, fitowa tayi da ga cikin ta fasa sai ta koma".
ya kalli Bello da kyau ya ce,"ka daina tambayar rainin hankali Bello, wataran sai ka haɗu da wanda zai rufeka da duka".
ya maida hankalinsa ga abin da yake yi, Bello dai sai cika shi da tambayoyin rainin wayo yake yi amma sam yaƙi responding nasa, da ya gaji kawai ya miƙe ya tattara komatsansa ya fice ya bar masa part ɗin gaba ɗaya.
part ɗin Fillo ya koma, lokacin tana kitchen su na aiki da yaran da aka aiko ma ta yau da safe, jiyo motsin shigowa parlon yasa tai saurin wanke hannu a sink ta fito, ganinsa ta yi zaune ya ɗora ƙafa ɗaya kan table ɗin, yatsansa ɗaya cikin baki ya kafawa laptop ɗin ido da alama nazarin wani abu yake yi, kafin ta ɗauke ido akansa taga ya miƙe da kayansa a hannu ya wuce upstairs, ta bi shi da kallo tana hararsa, sannan ta juyo ta mayar da idonta wurin da ya tashi tana faman ɓata fuska, haka kawai ya zo ya ɓata ma ta wuri, ya ɗauko table daga in da yake amma mayarwa ta gagara.
ta wuce tana ƙunƙuni ta ɗauke table ɗin ta mayar da shi ainihin in da yake, sai maganganunta take yi ita ɗaya har Bello ya shiga ma bata sa ni ba, sai da ta baro wajen zata koma kitchen sannan ta lura da shi. tai murmushi tana gaida shi, ya amsa ma ta yana tambayarta ya lafiyarta, ta ce,"Alhamdulillah".
yana kallon bandage na hannunta ya ce,"subhanallah ciwo kika ji haka?".
ta ce,"ehh jiya ne na yanke, amma da sauƙi".
ya ce,"ya salam to Allah ya sauƙe".
"amin na gode". sai kuma ta ce,"ka zauna mana".
ya ce,"nop ina sauri ne, MT fa yana nan ko yana ɗaya part ɗin?".
ta ce,"na ga ya hau sama".
Bello ya fito da flash da ga aljihunsa ya ce,"please ki ba shi wannan".
tana tsaye da ga in da take tace,"ka hau ka same shi mana".
ya ce,"no anata min waya daga office ne, ki ba shi yanzu please kice masa yay calling ɗi na".
ta wuce taje ta amsa, shi kuma yay ma ta sallama ya tafi.
kamar ta hau saman taje ta kai masa sai ta fasa tai wucewarta kitchen suka ci gaba da aikinsu, haka kawai yau ta tashi da kwaɗayin dambun gero, sanda ta shiga kitchen taga hannu ɗaya gareta har ƙwalla sai da tayi, kuma sai Allah ya taimaketa yaran suka zo a lokacin, nan da nan kuwa suka shiga kitchen ɗin tare.
kuma sai da suka kamma dambun kawai taji gaba ɗaya bata son cinsa, tun safe da ta tashi take jin mararta na murɗa mata kaɗan kaɗan, yanzu kuma ciwon ya ƙaru sosai, ta san ba komai ba ne illa period ɗinta, haka yake yi mata da ma, da zarar yazo kuma duk sai ya cika mata ciki taji bata son cin komai, fatanta ɗaya ne kar tayi wahalallan ciwon da ta saba.
ta kalli ɗaya cikin yara me suna Sakina ta ce ma ta,"kinga ɗauko wancan flask ɗin ki cika shi sai ki kaiwa Baba me gadi, idan kuma ba zaku iya cinyewa ba ki bawa Baban kice dan Allah ko da wanda zai bawa".
ɗayar me suna Hannatu ta ce,"Anty ke ba za ki ci ba?".
Fillo tai ma ta wani kallo ta ce,"na ce miki sunana Halima, bana son wani Anty. na ƙoshi naji ya fita a raina".
ta juya ta fita, Sakina da Hannatu suka shiga gulman wai ciki ne da ita, su na cikin ƙusƙus ɗin su sai gata ta dawo, ta ce da su,"yauwa yanda ma za'ayi, dan Allah ku kaiwa Kakata, ai kun san ɓangaren masu aiki ko?".
Hannatu ta ce,"anan gidan?".
ta ce,"no can gidan su me gidan nan".
Sakina tace,"ehh mun sani, kwananmu biyu ma a can".
haka kawai taji wani daɗi tace,"kun san Yami?".
suka haɗa baki wajen cewa,"ai a wajenta ma muka kwana".
"yauwa to ita zaku kaiwa, kuce ina gaisheta kuma don Allah ta sa Maijidda ta zo".
ta faɗi hakan ta fita a gaggauce saboda ciwon marar da ya fara tsananta ma ta.
tana hawa upstairs taji karatun qur'ani na tashi a room ɗin da ke kusa da nata, ta yi wucewarta ɗakinta sai faman yamutsa fuska take tana danne mararta.
har ta kwanta akan gado sai ta tuna da saƙon Bello, hakan yasa ta miƙe ta fito cikin ƙarfin hali ta wuce ɗakinsa, ta tura ƙofar tana sallama aciki-ciki, shi kuwa kamar bai ji sallamar ba dan bata ji ya amsa ba.
ganinsa babu riga yasa tai saurin rufe idonta, ta shiga ciki tana lalube kamar makauniya har ta isa inda taji kamar mudubi ta taɓa, ta ɗora flash ɗin da Bello ya bata akai sannan tai saurin ficewa ta bar ɗakin.
around 5 kiran wayar Maama ya shigo wayar Turaki, lokacin ya rufe laptop kenan, ya ɗaga da ga can ɓangaren Maaman ta ce masa,"ka na office ko gida?".
"ina gida Maama".
ta ce,"jiya Daughter ta manta magungunanta sai yanzu nake ganinsu, ka zo yanzun nan ka amsar ma ta dont waste time, ya hannun na ta?".
ya ce,"da sauƙi".
ba tare da tace masa komai ba ta kashe wayar, ba'a son ransa ba haka ya shirya, ba ya son wani faɗan dan haka bai tsaya ɓata lokaci ba, kuma ko da ya karɓo direct gidan su Bello ya wuce, Umma ya gani zaune a falo tana yiwa ƴan jikokinta karatun ƙur'ani, ya durƙusa ya gaishe da ita, tayi ta saka masa albarka kuwa tana jadadda masa akan ya gaida iyali.
ya ce,"Umma Bello ya dawo ne?, na kira wayarsa ban samu ba".
ta ce masa,"yana ciki bai jima da shigowa ba ma".
ya wuce ɗakin Bello, kuma yana zuwa ya tarar da shi kwance rungume da pillow yana waya, Turaki yaja dogon tsaki na takaici, ya jefa masa flash ya juya ya fice ba tare da yace masa komai ba.
bai koma gida ba sai bayan sallar magrib, yana shigowa parlo Sakina da Hannatu suka yi saurin durƙusawa su ka gaida shi, bai amsa musu ba illa bin parlon da yayi da kallo, ganin babu Fillo sai ya haye upstairs ɗin, yana buɗe ɗakinta ya ganta shame-shame a ƙasa sai murƙususu take yi, ya wuce ya dire ledar drugs ɗin akan stool, har ya juya zai fita sai kuma shashsheƙar kukan da ke fita a hankali ya dakatar da shi.
dawowa yayi ya durƙusa a gabanta, ya tsayar da ƙwayar idonsa akan fuskarta da hawaye ke ta zuba, ga uban gumi ta haɗa kamar an watsa ma ta ruwa, ga wani irin nishi kamar me naƙuda, sai ka kasa kunnenka sosai tukunna zaka ji kiran sunan Kaka da Ummi da take yi a wahalce.
ya ɗan taɓa hannunta yana cewa,"ke".
ta damƙo hannunsa ba tare da ta sani ba ta murgina tare fashewa da kuka sosai.
"wayyo Allah nah, wayyo Ummi nah, wayyo zan mutu".
ya sa hannu ya taɓa jikinta yaji zafi rau, sai kawai yaji ta ɗan ba shi tausayi, ya kamota zai ɗagota da ga kannanaɗewar da takeyi kamar miciji tace,"a'a".
muryarsa a hankali ya ce,"me yake damunki?".
sai a sannan ta iya buɗe idonta a wahale tana kallonsa a disashe saboda ruwan hawayen da ya cika ma ta ido.
shi kuma ganin tana kallonsa ya tamke fuska yana haɗe gira sama da ƙasa ya ce,"me?".
ta mayar da idon ta rufe tare da kamo hannunsa ta ɗora akan cikinta, ya kalli cikin ya ƙara cewa,"me ya sami cikin?".
cikin kuka ta ce,"don Allah ka kira min Kaka mutuwa zanyi, ko kuma ka kaini asibiti su cire min cikina don Allah".
yay shiru for some minutes sannan ya ce,"me kika ci?".
tai shiru ta kasa ce masa komai sai burgima take yi tana kuka sosai.
ya miƙa yaje ya ɗauko ledar drugs ɗin da ya shigo da su, ya fita ya ɗauko ruwa a ɗakinsa ya dawo, ya durƙusa yana ce ma ta,"tashi ki sha magani".
ta girgiza ma sa kai, ya ɗaga murya sosai,"na ce ki tashi ko".
ta ce,"Kaka ta hanani shan magani".
haushi ya kama
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 55 Chapter of 73