Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya tsince a sanda na faɗa cikin wani hali, kusan shekara yanzu suke bani duk wata kalar kulawa". nan da nan kuma duka Families biyu sai suka manta da damuwar da ake ciki, a shiga babin farin ciki. dan kamar yanda su Hajiya Madina suka mance da lamarin su Fillo haka suma su Kaka suka manta da lamarinsu, dan suma waje suka samu suka zauna, Kaka sai kwarara adu'a take yi da godiya ga su Yusuf, tunda Ummi ta shiga faɗa mata irin alkhairan da suka yi mata. da ƙyar iyalan Dikko suka safafawa Hajiya Ramla suka bar jikinta, ta bisu da kallo tana cewa Hajiya Madina,"ranki ya daɗe yanzu duka waɗannan yaranmu ne?, har waɗannan samarin?". ta faɗa tana nuna Khalil da Sameer. Hajiya Madina tace,"ƙwarai kuwa". nan da nan ta shiga nuna mata su Nihal tana faɗa mata sunayensu, tai mata nuni da Ilham dake gefe ɗaya ta rakuɓe sai kallonsu take tana murmushi. tace,"ga inlaw ɗinmu can". Mum tace,"really?". Maama tace,"ga zahiri na kunya nan kina gani". ai nan da ko Mum ta buɗe mata hannu tace ta taho gareta, ta rungumeta da tsananin farinciki sai saka mata albarka take yi. kuma sai a lokacin Mama ta lura da rashin Zaytuna, sai ta miƙe tana dube dube dan dama tuni ta san da ƙullatar da Zaytuna tayi da Mum. ta ganta tsaye can gefe ta haɗe rai fuskarta a gefe ɗaya, ranta ya ɓaci sosai taji tama kasa magana, hakan ne yasa Hajiya Ramla fahimtar komai musamman da ta ɗaga ido ta kalli photocopy ɗinta, ba sai an faɗa mata ba ai tana kallonta tasan itace jaririyarta da ta tafi ta bari. Turaki ma ya dinƙa kallon Zaytuna yana tuna lokuta da dama da take ce masa,"ka daina damuwa da ita Hammah tunda ai itama bata damu da mu, ni fa Hammah Allah ko ace ta dawo inda take ba zan kalla ba balle na raɓeta". sai kawai ya miƙe ya nufi wajenta, yana jin Maama cikin muryar ɓacin rai tana cewa,"wannan ba itace tarbiyar dana baki ba Zaytuna, kuma ko ki ɗago ƙafa kizo mahaifiyarki tasa miki albarka ko kuma wallahi in ƙaraso nan inyi miki duk abinda zuciyata ta sani, dan ba ki isa ki lalata mana farin cikin da muke ciki ba". Tayi shiru a sanda Turaki yaje gaban Zaytuna ɗin ya kamo hannunta, har ta cije tana neman ƙwacewa, ban san me ya faɗa mata a kunne ba yasa ta biyo shi. suna zuwa gaban Mum Turaki ya zube duka gwiwoyinsa a ƙasa, yaja hannun Zaytuna da ta tsaya ƙiƙam itama ta zube nata gwiwoyin, dama wannan ranar ya daɗe yana jira, dama wannan lokacin yake ta jira, dan haka kawai sai ya haɗe hannayensa duka biyu alamun neman yafiya cikin amon sauti me mugun ban tausayi yace,"Mum dan Allah dan Annabi ki yafe mana, ki yafe min dan girman Allah, wallahi tallahi ban san ta yacca akayi wutar ta kama ba, da sanina ba zan haddasa gobara ba Mum kema kin san banda fitina, amma ina neman yafiyarka dan Allah Mum". yay maganar hawaye na sakko masa hoton komai na wancan lokacin na haska masa musamman a sanda yabi Mum ta hankaɗo shi ta rufe ƙofa ta tafi ta barsu. Hajiya Ramla ta fashe da kuka, kukan da ya tafi ya shiga kunnuwansu ya daki zuciyar Turaki da Zaytuna, suka yi saurin ɗago ido suna kallonta, a ɗazu zai faɗi duk wani saukar hawayenta da sunan hawayen farin ciki, amma wannan kukan da ta kasa riƙe ƙarfin sautinsa na shaida masa so take ta yishi iyakar gwargwado, ta yanda zata samu ta rage raɗaɗi da baƙin cikin wani abu dake ranta. to me ya kawo hakan?, shi da yayi mata laifi. kuma kafin ya gama karantar dattin baƙin cikin dake saman fuskarta sai yaga ta sauko daga kan kujerar, itama ta zube nata gwiwon a ƙasa ta rungumo su jikinta tsam. tana kukan sosai tana faɗin,"Babana babu abinda ka yi min, baka min laifin komai ba Babana. ni ce nayi muku laifi wanda har ba zan yafewa kaina ba sai in kun yafe min, dan Allah, dan Annabi Babana kai da Zaytuna ina baku haƙuri, ina roƙonku ku yafe min da nisanta daga gareku da nayi, sharrin shaiɗan ne". Zaytuna ta fashe da kuka tana shigewa jikin Mum ɗin sosai, cikin muryar kuka suka haɗe baki ita da Turaki suka ce,"Mum ke fa Uwa ce akan me za kike neman yafiyarmu bayan baki yi mana komai ba. to ma idan kinyi ɗin menene ai girmanki ne da cancantarki, balle ma har duniya ta naɗe ba za ki taɓa yi mana abinda zamu kallesa a matsayin kin mana laifi ba". furucin nasu sai ya zama kamar haɗin baki ko kuma tun can dama sun tsara hakan. sukai shiru suna barin jikinta, Turaki yasa hannunsa na hagu a gefen fuskarta ta ɓarin da yake, itama Zaytuna haka. suka ƙara haɗa baki da faɗin,"muna miki tsananin so, farin cikinki shi ne muce mun yafe ko?, to mun yafe miki Jarumar mata". sukai kissing nata a goshi suna jin wani irin shauƙi na daban da basu taɓa jinsa ba mara misaltuwa na bin jinin jikinsu. gaba ɗayansu kuma har Mum ɗin sai suka saki murmushi me faɗi, har haƙoransu duka na bayyana a waje. Hajiya Madina da su Neehal sai suka koma ƴan kallo, dukkansu sai murmushi suke yi, kuma har sannan Hajiya Madina bata bari Baffa ya sani ba saboda sanin irin fushin da yake da Hajiya Ramla, ta bari ne kawai sai dai ya gansu a gida. Zaytuna taƙi sakin mahaifiyartata tace,"Mum yau a jikinki nake so na kwana, yau ba zanyi bacci ba Mum zan zauna inta kallonki". suka riƙo hannunta ta miƙe ta koma kan kujerar ta zauna, sannan ne ta kalli Hajiya Madina da zolaya tace,"Madam kisa ƴaƴanki su sakeni in tafi wurin sabuwar ƴar da nayi". aiko karaf Neehal tace,"ki tafi ina Mum?". ta faɗa tana turo baki tai saurin zagayowa ta zauna kusa da ita tana kama hannunta da cewar,"ai mu daga yau kina manne wajenmu kuma". bata bar murmushi ba tace,"to zanje in duba patients ɗina, a ban izini dan Allah". Kusan duk a tare suka haɗa baki wajen faɗin,"patient kuma Mum?". tana kallon Hajiya Madina tace,"wata yarinya ce da ta taimaka min muka fito daga cikin jeji mota ta bigeta, tun ɗazu munfi 1hour amma shiru, tace min ƴar aikin gidanmu ce, dan tunda ta ganni ma take cewa muna kama da Zaytun". a lokacinne kuma sai ga Fillo nan tazo wajen kamar tasan zancenta akeyi, tana riƙe da hannun Ummi ta ƙaraso da kumburarriyar fuskarta da taƙi barin murmushi. ta saki hannun Ummi ta nufi wajen Hajiya Madina wacca ta buɗe mata hannu, ta shige jikin Hajiya Madina ita kuma tana rungumeta tare da faɗin,"hasken gidan Alƙali Dikko, haƙiƙa ke ɗin haske ce a tare damu Fillo". Fillo tace,"Maama nima ga Ummina na gani, ashe bata mutu ba". ta saketa tana faɗin,"haba dai". tabi Ummi da kallo kafin ta isa wajenta da sauri tana gaisheta suna yiwa juna barka da farin cikin da suka tsinci kansu a ranar yau. Turaki dai sai yabi Fillo da kallo, ba wai ya manta da ita bane, tun ɗazu hankalinsa na kanta, kawai dai ba zai iya barin Mum bane, amma Allah Allah yake yaga Dr Yusuf yazo wajen. ji yake kamar yaje ya sunkuceta ya ɗauketa ya kaita inda zai zama daga shi sai ita, silent place ɗin da ba za'aji sautin komai ba sai na dariyarta, dan tabbas zai ƙara yalwata wannan annurin da yake gani shimfiɗe a saman fuskarta. zai ajiyeta akan cinyarsa yayi mata godiya da irin salon da ba'a taɓa yiwa wani mahaluƙi shi ba duk girman matsayinsa da mulkinsa kuwa. Mum ta dubeta tace,"zo nan ƴata". Fillo ta isa wurinta zata tsuguna tace,"a'a zo nan". ta faɗa tana yi mata nuni da kusa da ita, yayinda take kallon Turaki tana cewa,"Babana matsa". Turaki ya matsa Fillo ta zauna, Mum na kama fuskarta tace,"how are you feeling now dear?, ina ke miki ciwo?". tace,"feeling much better Mum". ta faɗa da ƙyar saboda yacca take jin babban yatsan Turaki na ƙafarsa na yawo akan ƙafarta. ga shi yana matso da fuskarsa saitin kunnenta kamar baya ganin kowa da komai a wajen, ita al'amarunsa tukun before yay tafi sun fara bata tsoro, kuma kawai sai ji tayi ya ratso da hannunsa ta baya ya matsa cikinta, ta ɗanyi zillo tana jin kamar ta fashe da kuka. a hankali ta yanda ko kaɗan Mum ba zata ji ba balle ta gane yace,"tanks immeasurably". ta ɗan kallesa kaɗan ta ɗauke idonta. a sannanne suka jiyo guɗa ta karaɗe cikin asibitin, Boɗejo ce ta taho sai rawa takeyi, take kuma wuri ya ƙara kacemewa da murna. Inna Wuro dai na gefe da sakakken baki cikin ranta tana faɗin ashe haka aljanu ma suke da haɗin kai. daga bige musu ƴa har sunyi cincirindo haka da wannan uban daren, sai dai babu hankali sam dan taga kamar murna suke yi. ta ratsa ta gefen su Kaka da suke tsatstsaye da ƴan gidan su Yusuf, ta tafi da sauri zuwa reception, ta sami wasu nurses su huɗu a zaune suna hira, tayi musu sallama suka gaida ita. tace,"ku ana can anata haska film kunan zaune da farin kaya kamar sabababbin gawa, a'a to ni dai da kuka ganni kujerar zama nazo ɗauka. wata ƴar arziƙin tazo ta kai min kujera dan Allah in samu wajen zama tunda naga abin bana tsayuwa ba ne". Nurse ɗaya ta taso tana cewa,"Hajiya kawo Babyn". ɗayar kuma da mamaki tace,"film kuma Hajiya! a asibitin?". Inna Wuro ta gyara zaman mayafi tana riƙe Farha da kyau tace,"a'a babu zancen wani in kawo Baby, sunanta Farha ba Baby ba, kuma yanzu ina ni ina baki jaririya alhalin ban sanki ba?, inje ki cuceta in shiga uku, to wallah uwarta a kotu take yin aiki tsab sai ta iya sawa a ɗaure ni ba mutunci ne da ita ba, a hannuna ta san ƴarta haka kawai in baki ki yiwa ƴar allurar tetanus ki jamin jafa'i, yo banda ma tana can tana kallon Film ina zata bar min ita, ai basa bani ita nima kuma bana karɓa saboda sunan Zainabu Yusuf ya saka mata, ummm wai ko dai sunan uwarsa yasa bacin yasan Uwar ba mutumiyar ƙwarai bace, Allah yasa ma dai kar ƴar ta yo gadon hali, dan naga irin goshinta iri ɗaya dana Zainabun". Nurse ɗin tai murmushi kawai. Inna Wuro tace,"yanzu dai ɗaukar min kujerar muje, ko kuma sai an biya kuɗin ɗaukar ne?". Nurse ɗin tai ƴar dariya tace,"a'a Mama, kula daku ai aikinmu ne, muje". ta faɗa tana ɗaukar kujerar. Inna Wuro tace,"a'a in ma kince sai an biyaki ai sai a biyaki, albashin da ake baku dudu nawa yake, kuɗin fa abincin rana ɗaya ne da Amadu yake kashe mana, muje wallahi sai in sa ya baki wani abin ai ɗana yana da kuɗi, shisa ma kaf nabi Malaman duniya nace suke masa adu'a kar a sawa kuɗin ido su ƙare da wuri mu shiga uku mu gantale acikin ɗumamen safe, shayi kuma ba madara balle isassan sikari". Nurse ɗin tayi gaba tana ƙunshe dariyarta, Inna Wuro na lura da hakan tace,"a'a wallahi dawo ki ajiye in ɗauka da kaina, sam bana haɗa hanya da ƴan banza irinku, shisa kaf ƴaƴan Amadu da Kursum ce bama shiri saboda irin wannan munafukar dariyar, sai inyi magana a wani ƙunshe dariya saboda ga taɓaɓɓa na magana ko?, to Allah ya isar min dan ba yafe miki zan ba, yanzu tsakani da Allah wani yazo wucewa ya gani ai sai yace min sannu, to sannu ina lafiya ƙalau ai zagi ne da cin mutumci, gaskiya ajiye kujerarki bana so na ɗauka da kaina, dama ku yaran asibitin nan duk ƴan banza ne sam baku da mutumci wallahi, kullum sai mutane sun kai ƙararku radiyo tsabar ba kwa so ku gama da duniya lafiya, to wallahi ni babu ruwana a lahira kuna kallo zan yi gaba in shige aljannah salin alin ku kam kuna baya ana ramawa talakawa abinda ku kayi musu". Nurse ɗin tace,"yi haƙuri Mama bada ke nake ba". Inna Wuro ta haɗe rai tayi mata wani kallo tace,"wato ke harda halin ƙarya irin na Aliyu kina da shi kenan, ina ganinki da idona kina ce min bada ni kike ba, to kawai na barwa Allah abar zancen bana son sabuwar fitina bacin wadda nake ciki". tasa ƙafa tayi fatali da kujerar, ta nemi wata ta ɗauka tayi gaba sai masifa take yi. sai da zata bar wajen kuma sai ta dawo murya ƙasa-ƙasa tace,"ba zaku zo kallon ba ne?, ai ko dai zaku yiwa kanku dan zaku rasa na ɗorarwa, kunga yanda jama'a suka cika wajen akayi maƙil da ƙyar ake numfashi, to dai za'ai babu ku wallahi indai baku zo ba dan faɗan aljanu da mutane ne, ɗana Aliyu ne ya kashe musu ƴarsu suka zo cin Uwassa Zainabu, ni dai du Allah kuzo ina gayyatarku kallo, ku taho da kujeru kuma ku sami na takawa dan anyiwa wajen rumfa nima sai na taka zan hango abinda ke faruwa, dan baku ga yacce suka zo da makamai suka yiwa wajen ƙawayen ba, ni yanzu so nake ma suce ba akan Aliyu zasu ɗau fansar ba akan Zainabu zasu ɗauka, ni dai da nayi sati ban bacci ba saboda tsabagen murna". jiyo tashin hayaniya ta tafi da sauri,"kai kai kai na tafi kar ayi babu ni, kar a shanye ƙafar Aliyu banga ta yanda akayi ba in kasa bada labari". Nurses ɗin na dariya suka biyo bayanta da sauri suma, ita dai sai jan kujera take tana ɗaga ƙafarta me ciwo da ƙyar, ɗayar nurse ɗin ta dage sai da Inna Wuro ta tsaya ta bata Farha, ta bata ita tana cewa,"ni da ace da jakar goyo ma sai ku ara min in sakata aciki kar inje tashin hankali yay tashin hankali nayi ta kaina in yasar musu da ƴa a wajen ban sani ba". suka gimtse dariyarsu Nurse Raliya tace,"zan riƙe miki ita Mama". tace,"aiko dai Allah rabaki da sharrin zaurawa ya haɗaki da saurayi me irin zuciyar ɗana Amadu, ya rabaki da sharrin samarin zamani masu munin hali irin na Aliyu". ta amsa da amin. tana tafe sai faman sauri take tana cewa nurses ɗin,"amma fa kuyi shiri ku riƙe takalmanku a hannu dan da zarar an fara sare-sare ta kaina zanyi in barku, dan ba zan tuna ma ni na gayyatoku ba, ku taho da sauri dai kar ayi a gama babu mu". kuma duk bakin room ɗin da Inna Wuro tazo wucewa sai ta leƙa tace,"jama'a ku fito ana faɗan aljanu da mutane ana can ana faman shanye ƙafafu, dan Allah ku fito jama'a ku taimaka mana kar a kashe jikana Aliyu, wayyo na Annabi ku taimaka jikana yana cikin masifa ya kashe ƴar aljanu, ku kawo mana ɗauki dan Allah, jama'a da yawa sun taru an rasa yanda za'ai da su kowa yabi su da kallo ana zazzare ido". jin wannan yasa mutane aka dinƙa fitowa ana ta faɗin subhanallah da innalillahi, dama tun ɗazu suna ɗan jiyo hayaniyar, kan kace me wannan wuri ya ƙara ɗinkewa da mutane kamar cinema, Inna Wuro ta rasa wajen ratsawa ta wuce sai ta tsaya daga gefe ta ƙwalla wata razananniyar ƙara da tasa a lokaci ɗaya akayo kanta. kamin a rufeta tayi saurin jan kujerarta tabi ta gefe ta wuce ta samu wurin da zata bawa idonta hakkinsa, ta zauna tana ɗaga kai sai kalle-kalle take tana kiran,"ƙawayena masu farin kaya dana gayyato kuna ina?, gani anan tsakiya idan kun jini ku ɗaga hannu in zo in shigo da ku, ga sarauniyar aljanun nan duk an rungumeta ku hasko waya ku ɗaukarwa duniya". wani takaici ya turnuƙe Dr Yusuf, ya dinga kallonta yana jin kamar ya kai mata duka, Aliyu da ya dawo hayyacinsa ya ɓata rai yazo yana ce mata,"wai ke dan Allah mene haka?, jifa yanda kika tarowa mutane jama'a, ke ko ina akaje sai kin yarfa mutane, kinga tashi kawai mu tafi gida kamin ki gama ɓararwa da Daddy mutunci". ko kallonsa bata yi ba tasa hannu tana turesa gefe. "yo Aliyu tunda dai ba naka mutuncin zan ɓarar ba me kuma ya shafeka". ganin yaƙi matsawa ta zabga salati tana nuna masa can gefe da cewar,"mun shiga uku ga Zainabu can ta yanke jiki zata faɗi". Aliyu yay hanzarin matsawa yana wurga idanuwa, ta kallesa tai dariya tace,"ɗan ƙwal uba addababbe". ta buɗe idanuwa duka tana ƙara kallon su Hajiya Madina da su Kaka waɗanda a yanzu suka haɗe wuri ɗaya, waje ya zama kamar gidan biki, Hajiya Madina na rungume da Fillo tana cewa,"tabbas ke ɗin alkhairi ce, kin zama haske a cikin rayuwarmu tunda kika kusance mu, insha'Allahu nayi ɗamarar faranta miki Fillo har ƙarshen rayuwata". Daddy ya ƙaraso inda Inna Wuro take zaune tayi ƙyam da ido a waje ɗaya tana ta aikin kallon bidirin da har yanzu bata fahimci kansa ba ma. in zaka yanka wuyanta ba zata ce ga abu ɗaya da taji an faɗa ba tun ɗazu, balle tace maka ga akan ainihin abinda yasa ake wannan murna, ita dai abu ɗaya ta barwa kanta dukansu aljanu ne kuma uban Aliyu suka zo ci. Daddy ya rissina yace,"mu tafi gida Inna dare yayi sosai, ƙarfe uku har da rabi, alhamdulillah yarinyar ta samu sauƙi dan Yusuf ma yace gida zasu wuce". ta kallesa tace,"to su kuma waɗancan da suka cunkushe waje ɗaya tafiya zamu yi mu barsu bamu gama kallonsu ba?". Daddy yace,"ai yanzu su ma zasu tafi". tace,"kai Amadu bana son halin Aliyu a tare da kai, ni kawai kayi tafiyarka ku ƙyaleni anan idan an gama na biyo motar haya, haka kawai yaran can da basu sami zuwa ba su rasa me basu labarin irin aratabun faɗan da aka sha, kai kasan halin ƴarka Yusra da gulma bata ƙi ta zageni tass ba akan ban kai musu rahota ba, ta dinƙa ɗaga min murya tana me amfanin zuwana wajen, to gwara ka barni in samu na kai musu, ni ƙafar Aliyun ma banga ta yanda aka shanyeta ba, yanzu dai ɗau wayarka kawai ka kayi musu hoton vedio me motsi sai akaiwa sauran ƴan gidan da basu ga tashin hankalin da akai ba". Daddy yace,"wayata na barta can gida kinga a halin da aka taho ai". tayi shiru dai bata ce masa komai ba, dai-dai da ƙarasowar Nuratu wajen tace,"Inna Wuro ashe matar da muka riƙe a wajenmu babar yarinyar da Aliyu ya buge ce, shekaru da yawa basu haɗu ba sai yau Allah ya haɗa fuskokinsu". Inna Wuro ta daki ƙirji ta dafe, babu shiri ta miƙe da sauri tana cewa Daddy,"tarkata yanamu yanamu mu wuce Amadu, daga nan kai tsaye Kano zamu wuce wuce ko gida ba zamu koma ba, gwara muje wurin Malam Ahmad Sulaiman ya haɗo mana turaruka azo ake bankawa juna, ina dalili haka irin wannan ibtila'i na rainon Aljanu, to Allah yasa dai bata shiga jikin wannan ƴa Farha ba". Daddy dai yay shiru, tashin hankalinsa ɗaya ta botsare tace sai anyi kano a tsakiyar daren nan, dan aka ƙi zuwa shi abin zai zamewa tashin hankali ta dinga kuka kenan tana ita ya biyata nononta da yasha kawai sai ta san nayi. Inna Wuro ta dinƙa bi tana cewa mutane ahalin Amadu Alfindiki kuna ina, mutane kuzo mu tafi gida ƙarfe uku ta dare tayi. Ammi tace mata,"Inna kiyi musu sallama, ki ɗan ƙara basu haƙuri sai mu wuce". ta daki cinya ta riƙe baki tace,"niiii, ba dani ba wallahi, akan me in bada haƙuri bani na kashe musu ƴa ba, ke dai da ya zamar miki dole da fitinannan ɗanki yaja miki masifa". har sai da suka je bakin mota sannan aka kula da babu wanda ke riƙe da Farha, Nuratu tace,"Inna wa kika bawa ita?". Inna Wuro ta fashe da kuka tana faɗin,"na shiga ukuna, wallahi ban san wanda ya amsheta ba, a hannuna fa take ƴar nan ban san garin ya ta bar hannun nawa ba, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, to aini sai yanzu ma na kula babu abu a hannuna, to dama abu ka ɗauka kamar baka ɗauka ba, Amadu kira Malam Ahmad ya buga mana istikara ko aga hannun wanda ta faɗa". tana yin shiru sai ga Yusuf nan ya fito ɗauke da Farha, ya wuce ta gabanta ko kallonta baiyi ba ya miƙawa Nuratu ita yace,"karki ƙara bawa tsohuwar can ƴata tunda ba'a kasuwa naje na siyota ba, ke ma kuma ba buɗe ido kika yi kika ga an ajiye miki ita kusa dake ba, sai da kika sha baƙar wuya kafin samunta". yay maganar ransa a ɓace. Inna Wuro na jinsa tace,"nima halina yaja min na shegen shishshigi da ƙwala kai a faranti, in ban damu da ɗaukar ƴarka ba ai baka zagar min iyaye har haka ba Yusuhu, iyayen da sun jima a ƙasa, tunda suka mutu babu uban da ya taɓa buɗe ƙazamin bakinsa yay musu irin wannan ƙazamin zagin sai kai Yusuhu, kamar bani na haifi ubanka ba?, amma babu komai Allah yana ji kuma yana gani, ranar gobe ya bi min hakkina. ƴarka kuma ni da ɗaukarta har abada, kai kallonta ma ba zan ƙarayi ba indai na cika ƴar halas, shegen banza kawai da yayo kama da dangin uwassa duk munana". tai gaba tana goge hawaye da gefen zani. "Amadu zo mu tafi kafin jinina ya hau". tafiyarsu ba jimawa su Hajiya Madina ma suka fito, da su da su Kaka aka kwashesu duka a sienna har biyu. cikin dare ne amma kace tsakar rana saboda yanda suke ta hanyaniya a mota. dan lokacin har an kira Granny a waya vedio call, itama duk wannan fushin da take yi sai ta manta da shi, tana ganin Mum ta fashe da kukan farin ciki, tana faɗin gobe-gobe zata taho, yanzu Adil zai je ya yanko mata ticket. taraddadin Hajiya Madina ɗaya ne su kuma Baffa ya lanƙwashe. kuma suna gab da isa gida Baffa ya kira wayar Hajiya Madina yake shaida mata cewar,"Fulani Azima tayi mummunan accident, su wuce masarauta kawai ba sai sun koma gida ba". *Vote, Comment and Share.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *38* *Massachusetts General Hospital, Philippines.* acikin silent ward ɗin babu abinda kake ji yana tashi sai sautin kuka me ban tausayi. wata tsohuwa baƙa na sanye cikin les me tsada milk colour, ta baro inda take tsaye ta dawo kusa da Ilham ta zauna. ta janyota zuwa jikinta cikin sigar lallashi da ban haƙuri tace da ita,"Ilham wannan kukan naki da kika shafe kusan awa guda kina yinsa ba shine zai bawa Mahaifiyarki lafiya ba, saboda haka ki sha re hawayenki ki mata adu'a dan ita tafi buƙata a halin yanzu". maimakon Ilham ta daina kukan sai sabo ya ƙaru fiye da wanda take yi, kuma Kakar tata Hajiya Shema'u wacce take mahaifiya wurin Azima bata ƙara ce mata komai ba, sai bubbuga bayanta da take cike da matsanancin tausayin Ilham ɗin. a lokacinne kuma Ahlan ya iso wajen, ƙani ne a wurin Azima daga ita sai shi. ya zauna akan kujerar kusa da mahaifiyarsa, shima da ka kalla fuskarsa zaka hangi damuwa acikinta. yace da ita,"Umma me likitan ya ƙara cewa?". ta sauke numfashi ruwa na kawowa cikin idonta tace,"tou Me Martaba dai ya tafi wajensa tun bayan da suka fito da ita daga theater room ɗin, ban san yanzu kuma ya ake ciki ba". Ahlan ya sauke numfashi sannan yace,"nima jiya muna tare da jami'an tsaron da suke ta bincike akan accident ɗin nata, kuma har yanzu fa Umma babu labarin driver'n da suka fita tare. anje wurin iyalinsa su kansu sunce satin biyun nan cif ba su saka shi a idonsu ba nemansa suke, itama kuma jakadiyar tata fa har yau ba labarinta". da damuwa sosai Hajiya Shema'u tace,"to Allah masanin abinda ya faru, kuma ni gani nake idan lamari ne na ƴan garkuwa ai ita zasu ɗauke ba drivern ko Jakadiyar ba, kuma idan kidnappers ɗinne da tuni sun kira waya, amma koma mene dai mun barwa Allah, fatanmu Allah ya tashi kafaɗunta". sai kuma ta fashe da kuka sosai tana cewa,"da banyi niyyar faɗa muku ba saboda kar hankalinku ya tashi, sai dai faɗar ya zama dole ko don a tayata da adu'a. likita yace ta kamu da paralyse, ɓarin damanta ya mutu ya gama aiki Ahlan, idonta guda ɗaya ma shima ya mutu wai ruwan ciki ya tsiyaye gaba ɗaya, ƙafar hagun ma

Chapter 40 of 73