Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zuciyar kowa da abinda take saƙawa, daga ƙarshe dai Baffa yace su Zaytuna su kwaso kayan Kaka a taho da ita ɓangarensu, hakan kuma akayi suka ɗaukar mata abinda zata buƙata suka taho da ita wajensu ita da Maijidda da har yanzu ita ɗaya ce bata bar kukan fili ba. kuma ita kowa yafi jin tausayi bayan Kaka, tsabar kuka idonta sunyi luhu-luhu. ɓangaren Ameer kuwa har drip aka saka masa, dan lokacin da aka faɗa masa akan machine yake bai san ma sanda ya saki kan machine ba ya faɗa wani rami shi da machine ɗin, duk ya kurkurje yay rauni a duk jikinsa, ƙarshe sai wasu bayin Allah ne suka kaishi asibiti, a asibitin ya bayar da lambar Mahaifinsa aka kira nan da nan kuwa sai ga asibiti ya cika da mutane, abinka da me tarin ƴan'uwa. Innarsa na zuwa ya faɗa mata abinda ya faru, kuma take ta ƙaryata tace sai dai in ko yaranne a ƙuruciyarsu suke so su gwada shi da irin son da yakewa Fillo, sai dai itama ko da ta kira abinda Yami ta faɗa mata kenan, Amir dai nata kallonta with his all hope ace ƙaryar suke yi masa, gwada shi suke so suyi, kuma in har gwajin ne yasan yayi nasara, sai dai zai faɗa musu kar su ƙara yi masa irin wannan wasan gudun rasa rai wataran. sai dai tana ajiye wayar yaji tana faɗawa mahaifinsa halin da ake ciki, dan haka nan da nan brothers ɗinsa suka watse akayi gida dan fara karatu da adu'oi. faɗar dai tsananin tashin hankalin da Amir ke ciki ba zai misaltu ba, don lokaci ɗaya har ya faɗa kamar wanda ya jima yana jinya, Dr ma har yana cewa in ba'a kiyaye an nema masa abinda yake nema ba zuciyarsa zata iya taɓuwa. a daren wannan ranar dai Kamar yadda Fillo bata iya runtsawa ba, haka ma Hajiya Madina, Kaka, Maijidda da kuma Amir, dan Amir saura kaɗan ya rage ma ya bar asibiti a daren ya fita nemanta. Tashin hankali dai duk bai bar kowa ya runtsa ba, yaran Hajiya Madina kansu sun kasa bacci saboda halin da mahaifiyar su ke ciki, shi kansa Baffa har sannan yana kan matarsa yana bata baki. at the end dai Baffa yaga zaman kukan duk ba shi bane, dan haka yace kowa yay sallah ai adua, a haka suka raya wannan daren daga masu sallah sai masu karatun qur'ani sai masu tasbihi haka har asuba da tayi. bayan sunyi sallar asuba Anty Zulfa ƙanwar Hajiya Madina da tazo ita ta zauna tana jero Adduo'i kowa na amsawa, cikin adu'ar suna roƙon Allah ya kare Fillo a duk inda take, ya kuma dawo da ita garesu cikin amincinsa, da ameen suka amsa har ta idar suka shafa, suka shafa aduar a daidai sanda Baffa ya turo ƙofa ya shigo. ya zauna akan kujera idon kowa akansa, ya numfasa sannan ya shiga yi musu bayanin abinda police suka ce game da report ɗin da aka shigar. yace,"ku kwantar da hankalinku dan Allah tunda dai har Police sun riga sun shiga maganar, kuma yanzu zasu ƙara bazama gurin nemanta". ya kalli Kaka yace,"na basu hotonta da shi saurayin nata ya bamu, kuma duk an baza shi a lunguna da saƙunan garin nan, an miƙa cigiya gidajen rediyo da talabijin duk an baza hoton nata". cikin kuka Hajiya Madina tace,"to amma me yasa zasu shigo da tunanin cewar Kidnappers ne suka ɗauketa. Baffa idan sune ai da tuni sun kira waya, mun kwana na biyu fa kenan Baffa, Kidnappers ba zasu yi shiru har haka ba. dan Allah Baffa a dai ƙara bincikawa ƙila wani wurin tayi, idan kuma kidnappers ɗinne a nemo su, su faɗa mana abinda suke so". ƙarfin kukanta ya katse maganar tata. to wasa-wasa dai har tsawon kwana uku lamarin Fillo shiru, Kidnappers ɗin da aketa tunani suma shiru basu kira ba, wannan ya ƙara ɗaga hankalin kowa, aka kuma bar tunanin cewa kidnapping Fillo akai, dan idan shine tuni sun kira waya, abin dai yafi kama da ɓata, Kaka na batun ita gwarama taga gawarta ta huta. adu'a kawai ake ta ko'ina, sadaƙa kuwa a gidan Alƙali Dikko babu dare babu rana. Amir kuwa yana can ba ci babu sha saboda tsananin damuwa, musamman idan ya zauna yana tuna moments ɗinsu shi da ita. lamari fa ya ƙara ta'azzara, dan tun ana lissafin kwanaki aka daina aka shiga sati, to abu kamar wasa daga sati ɗaya sai gashi an tafi sati na biyu har an shiga na uku. daga nan kowa ya saddaqar da cewar an rasa Fillo har a bada, kuma duk wannan bidiri da ake Turaki bai sani ba, da ya kira waya Zaytuna kawai shaida masa tayi sunyi tafiya ita da Kaka zasu yi wata guda. amma tun ranar da sukai waya da Maama yaji hankalinsa bai kwanta ba, tace masa kar ya damu ciwon kai ne ba wata matsala ba, ya zauna yay concentrating kan sabon project ɗin da Baffa yasa su. haka kuma dole ya haƙura ya maida hankalinsa kan aikin da Baffa yasa su, sai dai zuciyarsa ta kasa natsuwa, rabin tunaninsa na kan Fillo, so yake yaji ko da muryarta ne, amma babu hali, tunda har Zaytuna yasa ta tambayi Yami ko suna gaisawa da su kaka ta waya, Zaytuna tace masa Yamin tace itama wallahi duk ta rasa ta inda zata same su. kuma randa Fillo ta cika kwana 21 cif, ranar kidnappers ɗin suka kira wayar Yami suka shaida musu suna buƙatar naira miliyan 5 cas,idan kuma babu to su yanka musu ƴarsu su turo musu da namanta a kwali, suka kuma bada gargaɗin cewa in har suka sanar da wani batun hakan to ko da sun kawo kuɗi lallai sai sun yake ƙafafun yarinyar, aka kuma saka musu muryar Fillo dake ta kuka tana roƙon Kaka akan azo aceceta zata mutu. wannan batun yasa Kaka da Yami suka yi ɗiff ko Maijidda basu bari ta sani balle su Hajiya Madina da sun tsab zasu iya sanar da police. Kaka ta kira Amir a waya yazo, ita da Yami suka bincike ɗaki tsab suka kwaso takardun filayen Fillo da Abdulhamid, filaye guda huɗu da kuma takardar wata gona, ta bawa Amor tace dan girman Allah yay shiru aje a siyar duka ayau azo aje akai kuɗin nan. cikin sa'a kuwa Amir na zuwa gaba ɗaya abinda aka saya filayen da gonar miliyan ɗari huɗu da hamsin. dan haka ko da ya kawowa Kaka kuɗin sai aka ƙara ɗauka shanu guda uku akaje aka siyar har kuɗin yayi making yanda aka nema. kuma Amir shi ya ɗau kuɗin yaje ya kai inda Kidnappers ɗin suka buƙata, bai dawo gida ba sai wajen biyu na dare cike da tsoron dajin da yaje ya ajiye kuɗin, har ya kasa bacci saboda firgici. su Kaka kuwa ana can anata zabga adu'a, Kidnappers ɗin sunce da an kai kuɗin zasu saketa ta dawo gida a lokacin, amma har sallar asuba har wayewar gari babu ko da inuwar Fillo. hakan ya ƙara ɗaga hankalin su Kaka, suka kasa tsaye suka zaune ita da Yami, sai zagayen ɗaki suke yi, ana hakan wayar Yami dake ƙugu a soke tayi ƙara, da sauri jiki na rawa ta ɗauko ta kara a kunne, abinda ya doki kunnenta a lokacin shine Kukan Fillo. tace,"Fillo kina ina?". tace,"Yami sunce ba zasu sake ni ba, wai kuɗin yayi musu kaɗan sai an ƙaro. Yami karku ƙara musu ko biyar, ni na saddaƙar mutuwa zanyi, ki faɗawa Amir kar ya ƙara zuwa dan sun ce zasu karɓi kuɗin kuma su kashe shi, He has done so much for me that I can not repay him, bana son rasa shi Yami, kar ya ƙara zuwa dan Allah, gwara ya rayu ni na mutu, Yami ki kula min da Kaka bata da kowa sai ni sai Allah". ta faɗa tana kuka sosai, kuma me taɓa zuciya. ƙit kamin Yami tace wani abu an kashe wayar. Amir yazo gidan jikinsa duk a sanyaye don tuni Kaka ta kira ta shaida masa, ko da ya shigo ɗakin zubewa yayi daga bakin ƙofa, har tsawon minti biyar ya kasa cewa komai, sai da ƙyar ya iya buɗe bakinsa yace,"Kaka ko dai mu sanarwa da su Hajiya?, tunda sunce a a shirye suke suyi duk abinda ya kamata". Kaka tai saurin girgiza kanta tace,"a'a Amir, ana faɗa musu zasu kai lamarin ga hukuma, su kuma mutane nan kaji abinda suka ce muddin hukuma ta sani sai sun kasheta". Amir ya haɗiye wani abu a maƙogoronsa da ƙyar sannan yace,"shikenan Kaka, zanje yanzu akwai wani filina acan ƙauyenmu zan siyar da shi, shima kuma gidan da zamu zauna zan siyar da shi. gaba ɗaya in Allah ya yarda za'a iya samun ko miliyan biyu ce, sai a haɗa a ƙara basu". daga yanayin yanda yake maganar in ka kalle shi sai kayi masa kuka, bakinsa duk ya bushe, gaba ɗayansa ya wani firgice ya zaftare saboda rama. Yami da Kaka suka haɗa baki wajen ce masa,"a'a karka sayar da komai Amir". ya miƙe kamar zai faɗi yace,"Kaka bamu da wata mafita da ta wuce wannan. gobe zan dawo in Allah ya yarda, kuma a gobe zasu saki Fillo da izinin Allah, fatana ku kwantar da hankalinku kuyi ta adua". Kaka tace,"to Amir a haɗa da sauran shanun can guda 5 da suka yi saura, akwai awaki ma guda 10 duk ka siyar sai a haɗa". da kansa kawai ya iya amsa mata sannan ya fice jiki duk a saɓule, yana tafe yana layi kamar wanda yasha ƙwaya, bacci ne fal a idonsa da wata azababbiyar yunwa da yake ji, amma baya jin cikin biyun ɗa zai iya samuwa, shi da cin abinci da bacci kuma sai Fillo ta dawo. kuma a safiyar ranar ne Turaki ya kira Khalil yake tambayarsa ga me da jikin Maama. dan shi har yanzu bai yarda da lafiyar da take ta faɗa dan bai ji a voice ɗinta ba, kuma taƙi yarda suyi vedio call. Khalil mutum ne shi da baida wani ɓoye-ɓoye, ko saƙon mutuwa ne kai tsaye yake sanar da shi, dan haka kai tsaye Khalil yace masa,"Hammah ai yau kusan 3weeks kenan ana cikin tashin hankali, zancen da nake maka yanzu haka Maama bata cikin hayyacinta, ta fita ita da ƴar aikin nan Fillo an sace ƴar, har yanzu shiru babu labarin yarinyar, shisa ka kasa jin Maama a yanda kake so". Turaki ya ɗauke wuta, ya daskare daga zaunen da yake, wayar ta silale daga hannunsa ta faɗo ƙasa, maganar Khalil ta shiga tariya acikin kansa. yarinyar ta ɓata, an saceta, 3weeks ba'a ganta ba, babu labarinta, ba'a san ina take ba. hannunsa ya dunƙule ya naushi kujerar da yake zaune, ya dinƙa karanto innalillahi wa'inna ilaihi raji'un har Bello yazo ya sa me shi a sanda idanuwansa suka kaɗa suka yi jawurr. _sorry for the late update. nepa ne suka yi tsiya wallahi, ko 1% da zan maku posting babu balle ma na typing ɗin, around 12pm kuma na gama typing ɗan banzan whatsapp yay min tsiya komi yaƙi tafiya, sai da na sake download nasa..i hope bkuyi fushi ba._ *Vote, Comment & Share.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _Avoid error mistakes._ *33* *Switzerland* sanya take cikin rigar sanyi mai kauri sosai, dogon wando ne fari a jikinta sai p-cap red colour da ta saka, wanda shigar ya amsa farar fatar jikinta sosai. yanayin fuskarta kaɗai zai shaida maka cewar bata cikin walwala da annuri, haka kuma ƙwayar idonta na shaida rashin nutsuwar da take da ita a zuciyarta a kullum a ko da yaushe. a tsaye take daga jikin window tana leƙan waje, tana kallon yacca ruwan sama ke sauka, sanyin garin na ratsowa har cikin ɗakin yana shiga jikinta. ta sauke dogon numfashi tare da ɗaga gorar hollandia ɗin dake hannunta ta ƙara kurɓa, ta buɗe lumsassun idanuwanta a sanda take juyowa ta fuskanci kyakykyawan farin bafulatanin dake zaune kan kujera yana danna wayarsa, shima fuskarsa kaɗai ta isa ta shaida maka cewar zuciyarsa a ƙunci take. Samha ta ɗauki tsawon daƙiƙu biyar tana kallon Sameer kafin ta buɗe baki tayi magana, muryarta ta fito acikin rauni da kuma damuwa. "tsawon shekaru masu yawa, har kullum, har yanzu na kasa haƙuri da juriya akan yacca nake ganin mahaifiyata ta fifita wani daban akan ni da ta haifa, tafi son sa fiye da ni da ta haifa, tafi basa kulawa fiye da ni da ta haifa, tafi kyautata masa fiye da ni da ta haifa, tafi damuwa da damuwarsa fiye da ni da ta haifa, hankalinta yafi karkata 100% akan ƴaƴan da bana cikinta fiye da wanda ta haifa acikinta. ka faɗa min ta yanda za'ai nayi farin ciki duk da cewar ban taso a tagayyare ba, ban taso a cikin talauci ba, ban taso da rashin gata ba, ban taso na nemi abinda nake so na rasa ba, ban taso na rasa soyayyar mahaifi da ta mahaifiya ba, sai dai wannan soyayyar tasu ce tayi min kaɗan, ba kalar wannan soyayyar nake so daga wurin mahaifiyata ba, kalar waccan soyayyar da take nunawa Turaki da Zaytuna ita nake so, ita nake da buri ita nake da muradi, amma tsawon shekaru masu yawa na rasata, na kasa samunta duk ta yanda na so...shi yasa ya zama dole na kawo ƙarshen wannan bambanci da iyayenmu ke nunawa ko ta halin ƙaƙa, ko da ace asanadin hakan zan rasa raina". ta ƙarashe maganar muryarta na bayyana wani irin baƙin ɗaci dake tasowa daga ƙasan zuciyarta. shirun da tayi yasa Sameer ya ɗago da kai yana kallonta, tana tsaye hawaye na bin fuskarta, ba ta da alamar zata hana su zuba balle tasa hannu ta goge su. ya rufe idonsa for few seconds ya buɗe yana sauke numfashi tare da ajiye wayarsa a gefensa. "ke kaɗai ce dama kika rasa dukkan abinda kika lissafa?, ko kuma ke ɗaya ke cikin irin wannan ƙuncin?". kanta na ƙasa tana kallon ƙafarta dake cikin black socks tace,"bani ɗaya bace, ko Hammah Khalil da Nihal na san basa jin daɗin haka, deep down there heart na san suna jin zafi, domin babu ɗan da zai so yaga iyayensa na nuna banbanci tsakaninsa da ƴan'uwansa...so amma abinda nake so ka fahimta Sameer inda ace hankalin mahaifiyamu na kan mutum guda acikinmu da ta haifa, to da atleast zamu sami sassaucin raɗaɗin zuci, ba wai take nunawa kamar ba ita tayi naƙudarmu ba". cikin zafin nama tai wurgi da hollandia ɗin dake hannunta tasa ƙafa ta murje, tana huci take cewa,"wani sa'in zuciyata na faɗa min Turaki da Zaytuna asiri suka yiwa Maama, ba haka suka barta ba, don babu uwar dake cikin hayyacinta zata ke nuna irin son kai tsakanin ƴaƴanta da na kishiyarta, but what ever lokaci yayi, wallahi a wannan karan babu fashi da tsiya tsiya sai na aika da su lahira, zanbi ta irin waccan hanyar da suka bi, ko duk bokayen duniya zan bi saina sa an kawo min ƙarshen su Turaki". Sameer ya hura iska a bakinsa sannan yace,"bin boka is not the best solution dear tunda aikin asiri na karyewa, and ba zan bari ma mu aikata shirka ba. abu ɗaya kawai da yake nan waɗan nan mutanen su zamu ƙara bawa kwangilar...". ai tun bai ƙarasa ba ta duki table ta katse shi da cewar,"kuɗina ba zai ƙara zuwa hannun gantalallun can ba". sai kuma ta nemi kujera ta zauna ta dafe kai,"Sameer ni abinda ma yake ban mamaki, me yasa duk sanda mukai wani shiri sai kaga Turaki ya kuɓuta daga wannan shirin namu?, ka duba fa kaga last da muka sa aka datse burkin motarsa, tsakiyar dare fa muka bi, wa ya ganmu?, wa yaji plan ɗin mu?, amma sai ga shi da safe yana batun bai key na motarsa ba, kuma tun daga ranar har yau bai ƙara hawa wannan motar ba, anya Sameer?, ga shi ba wani muka sa akan aikin ba balle muce ya munafurce mu, da kanmu muka yi aikinmu, kai na kasa ganewa gaba ɗaya". Sameer shima ya kwantar da kansa kan kujera yace,"ni kaina nayi mamaki sosai a wannan time ɗin, musamman da naga up to now baya hawan motar. amma mutumin da yake kwana yana sallah har sai gari ya waye sannan ya rumtsa, mutumin da yake driving yana sauraron karatun alƙur'ani yana bi, mutumin da baya rabo da ambaton Allah a bakinsa, mutumin da common magana ɗaya yayi sai ya ambaci Allah, to ki faɗa min ta ya ba zai kuɓuta daga haɗarinmu ba?, taya ba zai kuɓuta daga sharrinmu ba?, ai muma wasa muke, iyakar kuɗin da muka ɓarnatar ya kamata zuwa yanzu ace mun haƙura kawai, mu fahimci cewar Turaki yafi ƙarfinmu dan yana tare da kulawar ubangijinsa". Samha tace,"idan kai ka haƙura ni dai ba zan haƙura ba, dole ne ma sai na ƙwaci soyayyar mahaifiyata, dole ne ma sai na ƙwatarma kaina hakki. ka duba kaga banda mota guda ɗaya da kuma fili guda ɗaya me Baffa ya taɓa mallaka mana?. amma Zaytuna motarta biyu, bayan fili har gida tana da shi, Turaki kuwa an handame duk wata kadara an basa, komai Baffa yay yunƙurin yi mana sai Maama tace shi ya kamata a bawa saboda shine Babba, ko kuma tace ai su basu da uwa sai kace mune muka sa uwar tasu ta gudu". Shiru ya ratsa kafin Sameer yace,"to yanzu what next kike ganin zamu yi?". tace,"akwai wani dodo anan ƙasar, na faɗa masa zan basa kwangilar kisan mutum biyu, yace min zan ba shi 20ML, nace masa 10ML zan ba shi, da ƙyar dai muka ƙarƙare a 15ML, dan haka zan sayar da motata ɗaya da kuma sabon filin da Maama ta bani, sai muga abin yi". Sameer yace,"hakan yayi". daga haka ta wuce ciki ta barshi anan parlo. *Gombe.* a cikin parlon na Kaka, tana zaune ta zabga tagumi tana jan carbi, sai Yami ma a gefe ta zabga nata uban tagumin, sai Maijidda dake kwance akan ledar ɗakin, ba bacci take yi ba idonta ne kawai a rufe. dukkansu kallo ɗaya zaka yiwa fuskokinsu ka shaida bala'in tashin hankalin da suke ciki, duk sun rame sosai. tun a daren jiya Amir ya ƙara kai kuɗin da kidnappers suka nema amma shiru har safiyar yau babu wani labari na dawowar Fillo, tun kiran da suka yi na cewar sun ɗauki kuɗin zasu yi abinda ya dace to basu ƙara kira ba, haka su Kaka suka yi kwanan zaune kamar yanda Amir yay daga can gidansu, amma shiru-shiru babu wani bayani. to haka yau ɗinma tun 11 na rana Hajiya Madina tayo musu aiken abinci amma sun kasa ci. dan a inda Ɗausiyya ta ajiye flask ɗin tun ɗazu yana nan a inda yake babu wanda ya taɓa shi. Yami ce tace,"Ƙawata ki ɗanci abincin nan ko loma biyu ce dan Allah". Kaka ma tace,"ke ya kamata kici tunda kina da matsalar ulcer". Kaka ta dubi Maijidda tace,"tashi ki zuba abincin nan kici". bata buɗe idonta ba hawayen daya taru aciki ya sauko tace,"ba zan iya ci ba Kaka". dai-dai nan suka ga an ɗaga laben ɗakin, da sauri suka waiga kusan a tare suna kallon ƙofar, da fatansu ace Fillo zasu gani, but sai saɓanin hakan suka gani, sai suka tsaya suna kallonsa sun kasa ɗauke idonsu akansa. kamar yadda shima ɗin bin su yake da kallo ɗaya bayan ɗaya. kallon su yake yana so ya hango maganar da Khalil ya faɗa masa a fuskokinsu, babu wanda yasan da dawowarsa hatta kuwa Maama, dan ko driver bai kira yaje ɗaukansa ba, daga airpot napep kawai ya nema ya hau ya taho. ta gate ɗin ma'aikatan gidan aka sauke shi, kuma yana shigowa straight ɗakin Kaka yayo bai ko bi ta kan ma'aikatan dake gaishe shi ba, dan wata magana ma da yaji suna yi ta Allah ya sanya alkhairi duk bai fahimta ba. Kaka ta ɗauke idonta akansa tana cewa,"bismillah me Babban suna". baya jin zai iya ɗaga ƙafafunsa daga wurin da yake ya shigar da ita cikin ɗakin, dan ya riga ya gama samun amsar tambayarsa a fuskarsu, ta tabbata matarsa ta ɓata, har tsayin lokaci ba'a ganta ba. kuma sai ka lura sosai zaka hango uban hakin da yake yi tamkar wanda ya taho a guje tun daga El-Salvador. Yami ta yunƙura ta miƙe ta ɗauko darduman sallah ta shimfiɗa tana cewa,"bismillah ga wuri". Turaki ya ziro daguwar ƙafarsa ciki yana takawa tamkar wanda bai da jini a jikinsa. ya zauna hoton Fillo na haska masa acikin idonsa, tunaninsa ya katse sanda Kaka tace,"ina yini, an sauka lafiya?". Yami ma ta gaishe shi sannan ya buɗe baki yana jin kamar ba zai iya maganar ba yace,"lafiya lau". sai kuma duk sauran maganar tasa ta katse ya kasa faɗin komai. sai da Yami tace,"muna godiya da kulawarku, Allah ya bada lada". shirunta ya haɗe da fashewar kukan Kaka. Turaki ya juyar da idonsa kanta yana ta kallonta kamar yaune ya fara ganinta. kuka sosai Kaka take kamin tace,"ni da gawarta ne ma na gani hankalina zai fi kwanciya, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". furucin nata na ƙarshe ya haɗe da rufewar idanun Turaki yana dukan ƙirjinsa, for few seconds yana jin kukan Kaka acikin kansa da kuma hasashen halin da take ciki. ya buɗe idon ya sauke a ƙasa murya a sarƙe yace,"ki daina faɗar gawa Kaka, ganin gawarta ba yanzu ba insha'Allah, za'a ganta very soon aci gaba da adu'a Allah ya bayyanata". yanda yake yin maganar sai yaji kamar me koyon magana dan bai ma san ta yanda ya haɗa kalmomin ba ya faɗa. Yami tace,"Allah ya amince". Turaki yasa hannu ya shafa fuskarsa tukunna ya yunƙura zai miƙe sai yaji Yami da Kaka na maimaita kusan magana mai shigen wacca yaji ɗazu da yana shigowa. "ashe kuma lokaci yazo to ubangiji Allah ya sanya alkhairi". ana cikin wannan halin suke faɗar kalmar Allah ya sanya alkhairi!, to ko dai duk tsananin tashin hankali ne yasa kowa ya fita a hayyacinsa har yake faɗar abinda bai kamata ba. sai da ya isa bakin ƙofa sannan ya juyo yana kallon Kaka yace,"kuma babu gidan wasu ƴan'uwa da zata iya zuwa can?". Kaka tace,"babu, duk inda ya kamaci ace an bincika duk an duba. dan shi wanda ma zai aureta da kansa yaje can dangin mahaifinta ya duba, kwanansa ma biyu acan ɗin, amma ko da ya dawo yace wallahi bata can". Kaka ta faɗa tana sake fashewa da kuka. Turaki ya dinga kallonta kafin ya fice daga ɗakin ba tare da yayi musu sallama ba. ya wuce yana maimaiata kalmar wanda zata aura cikin ransa. daga nan kai tsaye ɗakin Maama ya wuce, lokacin da ya shiga zaune ya sameta a gefen gado ta zuba uban tagumi. har ya cire takalmansa ya shigo ya zauna kusa da ita bata sani ba, sai da ya janye hannun da tayi tagumi tukunna tai firgigit ta ɗago tana kallonsa. tana ɗago ido ta gansa sai ta fashe da kuka tare da kifa kanta a kafaɗarsa. ya rumtse idonsa sosai yana jin kukan nata na taɓa zuciyarsa tana ƙara matsewa da damuwar da take ciki, yasa hannu a kanta yana cewa,"innalillahi wa'inna ialihi raji'un, Maama whats wrong?, kukan me kike Maama?". ya faɗa dan yana so ya ƙara tabbatar da komai daga bakinta, amma da mamakinsa sai gani yay ta ɗago tana yi masa zancen da ya ɗaure masa kai matuƙa ya kuma rasa ina ta nufa. "Me Babban suna ka taɓa ce musu kana sonta ne?, ko kuma ita tace maka tana sonka ne da har ka amince musu?, yanzu shikenan ni ban isa ba, ban isa ai magana da ni akan abinda ya shafi rayuwar ɗana ba?, kuma a rasa a lokacin da zaa shirya bikinka sai lokacin da akaga ina cikin tashin hankali, me Fulani Azima ta shirya?". sai kukanta ya ƙaru sosai hakan yasa tayi shiru tana ƙara kwantar da kanta a kafaɗarsa. "Maama ban fahimci abinda kike son cewa ba, me ya faru?". sai ta ɗago da kanta ta kalle shi sosai, a ƙwayar idonsa ta gasgata cewa bai san duk abinda ke faruwa ba. saboda haka sai ta miƙe tsaye ta kamo hannunsa tace,"ka muje ka faɗawa Baffa da gatanka, kai ba maraya ba ne, dan haka ba irin wannan shirin kayi ba, ba irin wannan tanadin ka yiwa aurenka ba". bai iya cewa komai ba har suka fita daga ɗakinta suka bar part dinta suka nufa na Baffa still tana riƙe da hannunsa. suna shiga suka tarar da Baffa zaune a parlo yana kallon news ya ɗora hannunsa akan tumtum ɗin dake kusa da shi. Hajiya Madina ta

Chapter 33 of 73