ɗaya. a hankali kuma idonta ya rufe, cikin duhun idanunta na haska mata sunan Muhammad Turaki dake jikin farar takardar nan da babu zanen komai ajikinta sai na sunansa.
"tashi muje Maijidda".
"zuwa ina?".
"ina wannan baƙar ledar dana baki ranar bikin gimbiya Safiyya?".
"tana ɗakin Yami".
"je ki ɗaukota da sauri. ki sameni a bayan tanki cikin lambu, ki taho da ashana dan Allah".
_till we meet in the next page! Your Comment will make me to continue or stop._
dont forget to vote and share to other groups please🙏
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*2*
"Maijidda na kasa gane wajen".
Fillo ta faɗa a sanda ta ke ƙarewa babban filin wurin kallo. Dukkan tunaninta da hasashenta ta ɗora shi a wurin na fiye da daƙiƙa biyar amma sam ta kasa ta fahimci inda akai haƙan ramin.
Maijidda dake tsaye itama ta ƙarasa bakin kujerun wajen(resting chairs) ta zauna. Ta ajiye digar dake hannunta sannan itama tabi wajen da kallo cike da nazari da kuma son tunanowa.
"wallah Fillo nima na kasa tunawa kin san an kwan biyu...amma wai ajiyar me kikai ne a wurin nan?".
Fillo bata ce da ita komai ba, sai baki da ta zumɓura mata ta harareta kaɗan. ta zauna bakin tudun dake wajen tare da naɗe ƙafafunta, kamar wadda ta shiga ajin makarantar allo. Yatsanta manuniya akan leɓanta na ƙasa tana ƙarewa faɗin wajen kallo, da kuma tsirran ciyayin da suka firfito a ƙasar wajen.
Cikin zuciyarta tana ayyana ya za'ai ta manta wajen nan, bayan tasan tsawon watanni biyar da aka ɗauko bata ko zo wurin ba, hoton gun na haska mata acikin idonta a duk sanda ta tuno, abu ne da bai shafeta ba amma ta kasa mantawa da shi acikin ranta.
Ita dai tasan ta kuɗuri aniyar tarwatsa alƙadarin waɗanda sukai aikin dama wanda ya saka su. Abunda ta ke son sani ayanzu shine waima waye Muhammad Turaki?, mene alaƙarsa da waɗanda suke neman ganin bayansa?, wanene shi acikin gidan nan?, me yasa tsawon shekaru takwas da ta ɗauka tana rayuwa acikin gidan nan bata taɓa ganin ko da gimlawar inuwarsa ce ba?, me yasa bata taɓa jin zancensa ba a inda ya dace a dinga ambatonsa?, me yayiwa masu son kassara rayuwarsa?.
Bata da dukkan amsar waɗannan tambayoyin, sai kawai ta lumshe ido tare da hura iska a bakinta kamin ta furzar sannan ta sauke ajiyar zuciya. Bata manta da abunda ya faru ba a wajen, tsawon watanni biyar da suka wuce ba. Komai yana nan daki-daki acikin kanta, fuskokin mutanen da sukai aikin ne kawai ba zata iya shaidawa ba, dan a lokacin bayansu dakayan jikinsu kawai ta gani kamar yanda taga Muhammad Turaki a yau, amma ko muryarsu taji a yanzu zata nuna su ta rantse da Allah cewar sune.
MUHAMMAD TURAKI, harufan sunan da manyan baƙi suka ƙara haskawa cikin idonta, sunan da yake ajikin wannan farar takardar da babu zanen komai acikinta saina sunansa da jan penti. Sunan da ta kasa karantawa a randa tai arangama da layar, kuma haka taita ajiyar takardar har sanda Amir ya shigo cikin rayuwarta, ya fara koya mata karatu har tazo ta iya haɗa harufan a wata takarda ta daban ta maimaita rubutun sunan, sannan ta iya karantawa.
Ita dai bata san asiri ba, bata san ya ake yinsa ba, kuma bata san ya yake ba. amma zata iya rantsewa cewar aikin da waɗannan mutanen sukai asiri ne duk da bata ji sun ambaci wani abu da zai haska mata hakan ba, kuma babu tantanma asirin yana da alaƙa da sunan dake rubuce ajikin wannan farar takardar da aka maida ita laya.
Abu guda kawai tasan da shi, shine idan har ta manta wurin da akai haƙan aka binne, to ba zata manta maganganun mutanen ba a lokacin da suke aikinsu. Aikin da suka gudanar a sanda ƙafafu suka ɗauke acikin wannan babban gidan da baya rabo da shiga da fice ako da yaushe, ranar da akai naɗin Yarima Abbas zuwa wani matsayi da bata san wane matsayi bane, taji dai labarin irin rikicin da aka sha akan naɗin a wajen Kaka da Yami.
kuma zata iya cewa Allah ya nufeta da zuwa wajen ne saboda ta zama wata hanya ta tarwatsa mugun ƙudurin da ake shirinyi akan wani bawan Allah, tunda tsawon shekarun da ta ɗauka tana rayuwa cikin gidan bata taɓa zuwa wurin ba sai a ranar, lokacin kowa ya watse ana can masarauta ita kuma ta dawo dan ɗaukar ƙwaryar furar da ta dama zata bawa Amir.
A lokacin bata san taya ma akai ta kai kanta wajen ba. Ita dai kawai ta ganta ne ta ɓullo ta cikin lambu, ta durƙusa ta ƙasa bishiyan ayaban ta fito, kuma tana fitowa ne taci karo da wasu mutane su uku suna kalle kalle dan tabbatar da babu kowa a wurin da alama basu da gaskiya.
Bata kawo komai a ranta ba ta ɗau hanyar zata fito ta bar wajen sai kawai taji namijin cikinsu na cewa.
_"nan wajen ne, tace daidai inda tafukan ƙafarsa zasu taka kamin ya kai ga shiga cikin lambun"._
_maganar ta fito ne daga bakin bafaden dake tare da wasu mata su biyu._
_"andai ƙi aji shawarata, amma ni gani nake yafi ace an binne acikin lambun gaban kujerar hutawan da yake zama...amma anan wurin zai iya ma tsallakewa ya wuce"._
_Ɗaya daga cikin matan ta faɗa._
_Ɗayar muryar ta amshe da faɗin,"ni sai da muka zo gudanar da aikinma sannan nake jin zuciyata ta cika da fargabar abinda zai biyo baya, sai nake ganin kamar ba zamu yi nasara ba asirinmu zai tonu"._
_Ɗayar matar dake tsaye kusa da ita ta wurga mata harara tana faɗin,"to kuwa mugun tunaninki ya ƙare akanki ke ɗaya...wannan ma ai baƙin ciki kike mana, kina jin irin uban kuɗin da Shugaba tai mana alƙawari amma shine kike wannan mugun fatan...mtswww gaskiya ba ki haɗu ba, to ni kam dai akan wannan ɗaruruwan kuɗin da naji babu kasadar da ba zanyi ba"._
_"zafa ki iya samun kuɗin kuma ki kasa jin daɗinsu. Tunda idan aka kama mu banu da wani mataimaki sai Allah dan ko ita shugaba sanin kanku ba zata waiwayemu ba gudun kar nata asirin ya tonu...ni kam ina tsoro sosai wallahi jikina na bani wani abun zai faru, dan ba lallai muyi nasara ba sai da mu faɗi"._
_A ƙufele ɗayar ta kuma cewa,"to zabiya uwar zancen ai sai kije ki faɗawa Jakadiya ke ba zaki iya wannan aikin ba saboda ga abunda kike gudu...kinga sai ta musanya ki da wadda take ganin zatai mata aikinta ba tare data ji wani ɗar ba...mutum da shegen son kuɗi amma sai uban tsoro"._
_Rufe bakinta kenan Bafaden ya washe haƙoransa da faɗin,"yo ta jewa Jakadiya da wannan zancen ai sai dai wata ba ita ba. Dan tun a wajen zata zama tarihi kamin ma maganar ta kai ga kunnen Shugaba. Da farko da aka kirawo ki aka tambayeki za ki iya baki ce ba zaki iya ba sai bayan da kika gama jin sirrinsu saboda rashin hankali. To wa kike tunanin zai barki da rai?"._
_"ni fa ba wani abu nace ba, hankalina ne kawai yau ɗin naji bai kwanta ba. Dan duk randa asirinmu ya tonu, ko ita Shugabar da muke taƙama da ita ba zata iya ƙwatarmu ba, ƙila ma ta juya mana baya"._
-Da Bafaden da ɗayar matar sukai tsaki a tare. "to idan kin shirya rasa ranki da kuma dubu ɗari biyar ɗin da za'a baki kina iya juyawa ki tafi, mu ki barmu muyi aikinmu...akan kuɗi da kika ganmu babu kasadar da ba zamu iya ɗauka ba"._
_suna rufe baki Bafaden ya durƙusa ya shiga haƙe ƙasar dake wurin, wanda bai tsaya ba har sai da yayi rami mai ɗan zurfi tukunna. Sannan macen da bata da tsoron ta ɗauko gorar ruwa acikin jakar dake hannunta ta juye ruwan acikin ramin. Sannan miƙa hannu ta karɓi wata baƙar leda a hannun ɗaya matar ta zira acikin ramin. Duk abunda suke yi suna yinsa ne cikin saurari-sauri gudun kar azo a gansu._
_Kuma bayan sun maida ƙasar ne sun rufe suka tsaya suna tattaunawa, wanda yanzu da suke maganar Fillo bata jiyo komai da suke cewa saɓanin maganganun da sukai a ɗazu duk ta ji su._
_Alokacin zuciyarta na faɗa mata ne ta tunkari inda suke dan su san wani fa ya gansu, amma ɗayan ɓari na zuciyarta na hanata aikata hakan gudun karta fito suyi mata illa, duk da bata ga fuskar ko guda acikinsu ba amma tasan ba mutane bane masu imani a zuciyarsu ba._
_Cikin gudu mai kama da sauri suka bar wajen, sai da ta tabbatar sun bar wajen sannan ta fito, sai dai ko da taje wurin juyin duniya ta kasa gane inda akai haƙan aka binne, dan babu wata alama ta ɓurɓushin ƙasa da zai nuna maka anyi haƙan ƙasa a wajen, wannan ya nuna mata sun ƙware a iya aikinsu, kuma ba yaune farau ba._
_Ta ɗau kusan minti guda tsaye a wurin tana tunanin abinyi sai kawai taji gabanta ya yanke ya faɗi, ƙirjinta kuma na bugawa sosai, zuciyarta na faɗa mata tai hanzarin barin wajen tun wani bai zo ya ganta ba, dan idan akazo aka kamata ta ina zata fara bayani?, waye zai wanketa daga duk wani kalar zargi da za'a ɗora akanta?, gatanta Allah gatan ta Kaka, bata mantawa da lokacin da ɗaya daga cikin yaran gidan yaci abinci yayta amai ba, akace ai mai aikin data kai masa abinci ce ta saka masa wani abun, idan har yanzu tunaninta na jikinta, to ai ba zata manta ba tsawon shekara guda da akai abun har yau mai aikin tana cikin kurku a kulle akan laifin da ba'a da tabbacin ta aikata shi._
_Saboda haka bata san lokacin da siraran ƙafafunta masu kama da sillan kara suka bar wajen ba cikin sauri kamin daga bisani kuma ta haɗa da gudu, sai dai a lokacin da ta ke shirin barin harabar wajen gaba ɗaya tai tuntuɓe da dutse, ta tsuguna domin ɗaukewa kawai sai tai tozali da laya da kuma wata leda baƙa daure a wurin, cikin kanta bata kawo tunanin komai ba tasa hannu ta ɗauki layar da ledar sannan ta janye dutsen daga wurin._
_A wannan lokacin kai tsaye ɓangarensu ta koma, ta zauna ita ɗaya dan kowa yana can masarauta anata hidimar bikin naɗi, ita kuma duk tsoron kar ta fito a ganta ita ɗaya acikin godan a fara yi mata tambayar tuhuma. A ranar ma haka dole ta kashe haɗuwarsu da Amir._
"wai tunanin me kike?". Maganar Maijidda ta dawo da ita cikin duniyar zahirin da ta bari tsawon daƙiƙu masu yawa. Kallonta kawai tayi ba tare da tace da ita komai ba.
"Fillo kin san fa wurin nan ba wajen zuwanmu bane, ɓangaren masu gida ne. Amma kin kawo mu kin ajiye salon azo aganmu ace wani abun muke ƙullawa".
"Maijidda wuta zamu cinnawa wajen nan". Maganar ta Fillo tasa Maijidda zaro ido waje tare da hanzarin miƙewa tsaye. Da yake ita sarkin tsoro ce tuni jikinta ya hau makyartata.
Kuma bata kai ga ƙara magana ba, Fillo ta kai hannu ta ɗau ƙaramar galan ɗin petir ɗin da suka sato acikin gida ta shiga yaryaɗawa a wurin. Sai da ta juye shi tas sannan muryarta ta fito a hankali da cewar,"Maijidda matsa baya".
Cikin tsoro ba tare da mamakin abunda Fillo zata iya aikatawa ba tace,"ke wai me yasa ba kya iya kallo matsalar da zata faru a gaba, ke kawai abunda yazo cikin kanki shi kike yi. Yanzu mene amfaninki na cinnawa wajen nan wuta? salon kija mana barin gida".
"ai kin san dai ni ba mahaukaciya ba ce ko, duk abunda kika ga nayi ina da dalili...dan haka matsa da baya".
"wai na matsa da baya kike cewa, ke kuma fa?, kina kallo fa petir ɗin da kika zuba yana da yawa, kina kunna wutar nan fa tasowa sama zata yi".
"ni dai kija da baya kawai nace". Sautin muryarta ya fito cikin amo na ɓacin rai. Aiko babu shiri Maijidda taja da baya tai nesa da ita. Fillo kuwa tasa hannu a gefen zanen da bata iya ɗaurinsa ba har yanzu ta kunto layar da take ajiye da ita. tasa a tsakiyar tafin hannunta na dama tana ƙare ma ta kallo, kamin daga bisani ta shiga warware baƙi da jan zaren da aka naɗeta da su.
Sau uku tana duba sunan dake jikin layar, ranar farko data fara warwareta ta kasa karanta rubutun dake jiki alokacin bata iya karatu ba, da rana ta biyu da karatun da Amir ke mata ya fara zama akanta ta ɗauko ta duba dan haddace yanda harufan jiki suke, da kuma rana ta uku da ta rubuta harufan a wata takarda ta daban tai compairing rubutunta dana jikin layar dan tabbatar da tayi daidai, kuma a ranar ne ta iya karanta hurufan dake jiki, harufan sunan MUHAMMAD TURAKI.
To amma ga mamakinta sau ukun nan data buɗe bata taɓa cin karo da wani rubutun na daban ba bayan sunan Muhammad Turaki da yake jiki, sai ayanzu da take ganin wani rubutun sunan na daban da akayi shi aƙasan na turakin shi kuma da baƙar tawada amma ya fara disashewa hakan yasa ta kasa fahimtar kome aka rubuta.
Kawai sai taji wani dunƙulallan yawu ya wuce ta maƙogwaronta, tun a ranar farko da layar nan taje hannunta wani ɓari na zuciyarta ke gaya mata Halimatu karki jawa kanki bala'i, irin wannan abun mutum idan ya gani kauda idonsa yake akansa, amma yau kece da ɗaukar takardar da babu makawa anyi ne dan asirin wani.
Amma ayau sam zuciyarta bata yi mata wannan gargaɗin ba, illama ƙwarin gwiwar da take bata akan tayi iya duk ƙoƙarin da zata yi kan ganin ta karya wannan asirin, dan zata iya rantsewa wanda ake abun akansa ba shi da alhakin kowa, dan haka ta shirya yin jihadi akansa.
Saboda haka kawai sai ta cure takardar wuri guda ta jefar, ta ɗauki baƙar ledar da ta bawa Maijidda ajiya gudun kar Kaka ta gani, itama ta jefar a wurin.
Muryarta ta firo a fili tana faɗin,"har yanzu banda tabbacin asiri ne kuka yi ko ba shi, to koma dai menene sai dai yaci ku ku ɗaya, ga abinku nan ya koma kanku". Tana faɗar hakan ta ƙyasta ashana ta jefa, nan da nan ko wuta ta kama da wajen.
Garin tayi baya ta bige ƙafarta ajikin kujerar wurin har taji ciwo a babban yatsan ƙafarta. Amma ko tsayawa tabi ta kan ciwon ba tai ba.
Maijidda ko banda ambaton, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Babu abinda take. Har sanda Fillo ta risko wajenta ta kama hannunta dan su bar wajen. "ni kam na shiga uku dake Fillo, yanzu kin san iyakar inda wutar nan zata tsaya ne?, ba kya gudun abinda zai faru damu?".
"idan an tambaya sai kice mune muka kunna kinji". Fillo ta faɗa tana ƙara jan hannunta dan su bar wajen. Duk rashin iya gudu na Maijidda sai gashi har tana kusan kerewa Fillo saboda ita numfashinta ya fara ƙoƙarin tsayawa.
Kuma kan kace kobo hayaƙin wutar ya fallasu acikin gidan, saboda wuta ce ta tashi ba kaɗan ba sakamakon fulawoyin dake wajen, cikin mintunan daba zasu haura biyar ba sai ga fire service sunzo.
Irin tashin hankalin da wutar ta haddasa a zuƙatan al'umma Allah ɗaya yasan yawansa, an kewaye wajen anata salati, saboda irin tashin ƙarni dake fita ta cikin wutar yana shiga cikin hanci ya haura saman ka, ya haddasa faɗuwar mutane da dama a wurin.
Saboda wani irin wani ne da bashi da daɗi, dan asthmatic ma bai iya tsayawa a wurin. Haka ambulance tai ta shige da ficen ɗaukar mutane. A yayinda a wannan lokacin Fillo da Maijidda na can cikin uwar ɗakin Yami, hankalin Fillo kwance kamar ba ita tayi ba, Maijidda kuwa tai tsilli-tsilli da idanu kamar ta fashe da kuka.
Tana ta yiwa Fillo maganar amma kamar da dutse ta ke. Dan ita a wannan lokacin ma tunaninta na kan wani lamari na daban da take haskowa wanda take tunanin yafi wannan hatsari. Ƙarshe dai da Maijidda ta isheta da maganar da ba zata iya zaman jinta ta miƙe ta bar mata ɗakin.
Ta wuce ɗakinsu ta ɗauki littafinta ta hau assignment ɗin da Amir ya bata, wanda kusan kwana huɗu kenan da bata amma batayi ba saboda shiririta.
Don Allah share to other groups🙏
Youtube Channel-Sahaz Multimedia
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*3*
*Dare, 20:45pm.*
Ƙafafun Hajiya Madina suka shigo cikin ƙaton parlon, wanda ƙamshinsa ya haɗe da sanyin acn dake hurawa ya haɗu ya bada wani sanyin ƙamshi me motsa zuciya.
Jikinta sanye da ash abaya wadda taji adon stones ajiki, ƙyallin stones ɗin sai wurgawa suke ta cikin hasken fitilun parlon. Ganin Ƴaƴanta ya saka ta sakin murmushin da bata shirya masa ba, tana ƙaunar yaran fiye da yanda take son kanta, kowa yasan da hakan, abu ne ma da kamar tayi tambarinsa a goshinta.
Tana tsaye daga bayansu tana ƙare musu kallo cike da so da ƙauna, su kuma hankalinsu ya tattara kan tab ɗin dake kan cinyar Sameer suna kallon pixx ɗin da sukai ɗazu na birthday ɗin Turaki. Gyaran muryar da tayi ne ya ankarar da su zuwanta, suka ɗago a tare suna kallonta fuskokinsu na washewa da murmushi.
Ta zauna a kujerar dake fuskantarsu tana faɗin,"shine aka kasa jira nazo, wannan cin amanar har ina?". Tai maganar da sigar wasa kamar wadda ke tare da ƙawayenta.
Samha ta ɗauko tab ɗin ta nufo wurinta tana faɗin,"Maama kinga wanda aka maku ke da Hammah duk yafi kyau wallahi". ta zauna kusa da ita tana nuna mata hoton da aka ɗauka a sanda Turaki ke saka mata cake a baki.
Allah ɗaya yasan me taji cikin zuciyarta a wannan lokacin, dan shi kansa murmushin daya suɓuce a leɓenta bata san da zuwansa ba. Ta kai hannu ta shafa hoton, ƙwayar idanuwanta na haskawa da ƙyallin wata ƙauna dake tsakanin Uwa da Ɗa wanda Ubangiji kaɗai yasan girmanta.
"gaskiya munyi kyau, kamar ban haifi Hammah ba, kalle ni wata ƴar suwet a kusa da shi. Wannan idan sirikata ta gani ai sai tayi jealous idan bata san wacece ni ba". Ta faɗi hakan cike da raha, haƙoran makkan dake bakinta guda biyu suna bayyana duka a waje.
Taci gaba da scrolling har tazo kan wanda sukai gaba ɗayansu,"kai amma wannan ma yay kyau. 1 Family na Baffa kenan". Sanda tazo kan wanda Turaki yake shi kaɗai ta ƙara cewa,"wannan kam shima enlargement ɗinsa zan bada a ƙara min, Hammah yayi kyau sosai kamar wani magidanci".
Sameer yace,"Maama wai duk sai kin cika bangon ɗakinki da parlonki da hoton Hammah ne?".
"ƙila hakan ce zata kasance, dan sai dai idan bai yi sabon hoto shi ɗaya ba". Sai da suka zo ƙarshe a kallon hotunan sannan ta ƙara cewa,"gaskiya Hammah ya dawo ya fito min da matar aure, dan na ƙagu naga sirikata".
Aiko nan dukansu suka haɗa baki wurin faɗin,"aiko dai Maama ya kamata ace Hammah yayi aure, sai tsofewa yake yi".
Kallon da tai musu ne yasa babu shiri suka gimtse bakinsu, saboda kalmar tsufa da suka jinginata da Turaki.
"Hajjah nyamdu mae henyi". (Hajiya abinci ya kammala). Mai aikin data ƙaraso wurin a yanzu ta faɗa sanda take tsugunawa a gefen hannun kujerar da Hajiya Madina ke zaune.
Ba tare da ta juyo ta dubeta tace,"usema be habdugo". (sunnu da ƙoƙari)
"aha Hajiya Miyetti". (yauwa Hajiya na gode)
Daga haka ta miƙe ta bar wajen cikin azama dan barin musu wajen. Hajiya Madina ta ɗauke tab ɗin daga kan cinyarta tana ajeta kusa da ita, sannan ta kalla ƴaƴan nata tace da su,"my bloved ones dinner is ready".
Tare suka miƙa kaf ɗinsu suka nufa dining area, warm coolers na abinci ne zafafa masu kuɗin gaske, an jere akan dining table ɗin wajen kala shida, kowanne cooler da kalan abinci dake ɗauke acikinta, ta yanda kowa idan zaici abincin zai ci favorite nasa ne.
Zaytuna ta buɗe flask ɗin dake ɗauke da Mandi rice ta zuba a plate ta miƙa shi gaban Hajiya Madina, sannan kowa ya shiga zuba nasa abincin. Tunda suka fara ci babu babu wanda yay magana sai ƙarar cokula da kake ji har sanda suka kammala, wanda Hajiya Madina ce ta fara gamawa, ta yagi tissue ta goge bakinta.
"albishirinku". Ta faɗa sanda take jefa tissue ɗin cikin durstbin.
"goro Maama". Suka faɗa bakunansu a haɗe.
"this time Baffa yayi suprising namu, mo don dow lawol vartugo". (yana kan hanyarsa ta dawowa).
"na jam kam?". (amma dai Lafiya ko?)
"jam saliiman, mo vii mo yenwi Muhammad mako tan". (Lafiya lau. Kawai yace yana kewar ganin Muhammad ɗinsa ne)
"daɗin biyu kenan, to Baba ma yiidama to Dada ma kam yiidima". (Idan Babanka baya sonka to Mamarka na sonka).
Muryar Khalil dake shigowa cikin parlon a yanzu ta amsa lokacin da shima yake jan kujerar dining zai zauna.
Idon Hajiya Madina ya maƙale akansa tana cewa,"dume a tammi". (me kake nufi?)
Khalil yay murmushi kamin yace,"banda nuna launiyar warin fata kawai Baffa sai ya dawo gida saboda mutum guda, hala mu dama ya manta ya haifemu?". Maganar yake cike da zolaya.
Hajiya Madina tai murmushi kaɗan tace,"me yasa baka yi zuciya kazo a na farkon ba?".
Shima yana murmushin yace,"to yanzu dai ba sai ya dawo ba ya tarar Hamman baya nan. Dole dai ni zai gani ai".
"Jealosy". Ta faɗa tana binsa da wani kallo. A rayuwar Hajiya Madina babu abinda take so irin ta ganta cikin ƴaƴanta, kuma kowanne cikin farin ciki da jin daɗi ba acikin damuwa ba.
Suna cikin tattaunawa akan batun gobarar data kama ɗazu wajen ɓangaren Lambun gidan, take basu labarin aima har an sallami me gadin wajen, saboda sakaki da yake akan aikinsa. Inda dukansu suka ce hakan yayi daidai, duba da ko lokacin da akazo wajen bama ya cikin gida gaba ɗaya, baima san da kamawar wutar ba, balle yasan abinda ya haddasa kamawarta.
Wata matashiyar budurwa baƙa ta faɗo parlon cikin sauri me kama da sassarfa, kayan jikinta kawai zaka kalla ka shaidi itama ƴar aikin gidan ce. Wayar hannunta na ringing a karo na uku da kiran wayar ya ƙara shigowa. Ta ƙaraso gaban kujerar Hajiya Madina da sauri ta durƙusa tana miƙa mata bakinta na faɗin.
"kiyi haƙuri Hajiya, na ɗan matsa ne har kira na farko ya shigo ya yanke". Hajiya Madina ta bita da wani irin kallo, ƙwayar idonta na haskawa da ƙyallin ɓacin rai, ta karɓi wayar tana karawa a kunnenta. Kana iya jiyo sautin maganar dake tashi ta ciki, sai dai baka iya jiyo abinda ake cewa, tsawon wucewar 120second ta miƙe daga kan kujerar da ta ke, Zaytuna taja mata kujerar baya sannan ta fito ta nufi ƙofa.
Ba tai magana ba har sai data sanyo ƙafarta waje, kan step na farko da zai shigo da kai cikin parlon, sannan muryarta ta fito da wani irin amon sauti.
"Suite Eo5, 6th Floor Plot 1010 1st Avenue, By Shehu Shagari Way, Central Business District, Abuja".
Abunda ta faɗa kenan ta kashe wayar, kuma tana kan hanyar kaiwa ga ɓangaren Baffa sai jiyo horn tayi a baya, tana juyowa taga motarsa ce ke shigowa. Hakan yasa ta dawo da baya domin tarbar mijinta, inda wani farin ciki da annuri ya mamayeta.
*Dare, 20:45pm.*
"wai ha jonta a nyamae nyamdu mae na?". (wai har yanzu baki ci abincin bane?)
"mihari Kaka". (na ƙoshi Kaka)
"nde nyamuda dume?". (da kika ci me?)
"Kaka nafa ƙoshi ne kawai".
"bimi daga fajira wala ko metuda wukkugo nder reduma". (ce nake tun safe babu abinda kika ƙara sawa a cikinki).
"Kaka minanata bana mi nyaman kodume". (Kaka kawai bana jin daɗin bakina ne).
"To ko ananata beldum 6anduma?, nde an nyauma heftata'ke sae to guwallinima wakkati gotel.". (to ko ba kya jin daɗin jikinki?, Tunda ke ciwonki ba gane masa ake ba sai in ya kwantar dake lokaci guda).
"mi jamo Kaka. nane Amir waddiniyam mangoroje, daga mi nastai min njaride be Maijidda.". (ƙalau nake Kaka, ɗazu Amir ya kawo min mangoro, tun kamin na shigo muka shanye da Maijidda).
Kaka ta jinjina kai tace,"ni ai na iya fita a ban abin duniya na hana duk wanda ya gani na kawo maki saboda ina ƙaunarki".
Fillo ta ƙyalƙyale da dariya bata ce komai ba.
Kaka ta nemi wuri ta zauna tana gyaran man shanu, sallamar Maijidda ta ratsa cikin kunnuwansu a sanda take shigowa hannunta ɗauke da kwanukan abinci. Kaka da Fillo suka haɗa baki wurin amsa mata, ta ƙaraso kusa da Kaka ta aje kwanukan abincin.
"a'a me muka samu haka?". Kaka ke tambaya tana buɗe murfin tasar abincin. "masa'Allah tuwon dawa har haka. Aina Yami ta samo si?".
Maijidda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 73