Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba. kusan minti biyar sannan ta miƙe tana cewa,"wanko fuskarki tare da Yami muke, saura idan munje kiyi wawtar gaya ma ta abin da kika faɗa min, dan naga kamar hankali ya bar jikinki, wallahi kici uban faɗa in ta kama ma a haɗa miki har da duka, ki ce ma ta kawai ba ki da lafiya, in ya so ma ai tsammanin ciki kika ɗauka da wuri haka". ta ƙarashe maganar cike da tsokana tana ƴar dariya, Fillo ta harareta ta nufi toilet, ita dai dariya take tana ƙara faɗin,"Allah kina cewa ba ki da lafiya abin da za'a fara tunani kenan, nan kuwa ba'a san ko shimfiɗa baku taɓa haɗawa ba, balle ayi me kankat". su na sakkowa da ga step Maijidda na ƙara faɗin,"ni dai gaskiya nake faɗa miki kuma shawara nake baki, ki ajiye shegen taurin kanki da tsinannan miskilanci a gefe ki kama mijinki, billahillazi tsiwa da rashin mutunci ba naki ba ne a gidan nan, ki nutsu ki yiwa kanki karatun ta natsu, in kuwa ba haka ba na rantse da Allah sai kin yi kukan da yaci uwar wanda kike yi, sarai kin san dai ba ke ɗaya ba ce, matarsa na dawowa zai jefa ki a kwandon shara, ya mance da ke da batunki, ba kowanne kalar iskanci namiji ke ɗauka ba a wajen mace komin son da yake yi ma ta kuwa, yanda kishiyarki take wayayyiya sai ki zama ke da bola ɗaya acikin gidan nan in kika yi wasa. ke idan ma ita ba ta dawo ba ga ƴan aiki nan an ajiye miki cikakkakun ƴan mata masu buɗaɗɗan ido, inda rabon sun ƙwace miki miji sun barki da sakakken baki ne ke kika jiyo, dan wallahi ni ban wani yarda da ƴan aikin nan ba, son samu ma duk ki saita musu hanya kiyi aikinki ke ɗaya, mene abin wahala anan, haka kawai ƴan aikin yanzu da suke ƙwace maka miji". ita dai Fillo jinta kawai take bata ce mta komai ba, tun sakkowarsu Yami ke bin su da kallo har suka ƙaraso suka zauna kan kujera, Fillo ta sauko ta gaishe da Yami, ita dai Yami sai kallonta take yi cike da nazari da son gano wani abu, kuma cikin hikima ta iyaye manya ta fahimci abin da yake faruwa ba tare da ko ta tambayi Fillo ɗin ba, ai kuwa nan da nan Yami ta shiga yi ma ta nasiha sosai, da ƙara koya ma ta dabarun riƙe miji gam a tafin hannu, ita dai Fillo ji kawai take yi, don ba ta tunanin zata aiki ko da abu guda indai akan Turaki ne. lokaci ɗaya Fillo ta sake, su Yami su ka ɗebe ma ta kewar da take ciki, hira sosai kamar sun shekara ba su haɗu ba, tana ta zumuɗin za ta ji muryar Ummi ta tambayi Yami wayarta tace ai ta lalace, ɗoki da murnar da take ciki duk sai taji sun gushe, har la'asar su Yami su na nan ba su tafi ba. su na cikin kallo Turaki ya shigo, ita ta fara kai kallonta kansa, haka kawai sai taji gabanta ya faɗi, tayi saurin ɗauke idonta a kansa ganin wani kallo da ya yi ma ta fuskarsa a tamke. ya shigo ya zo ya gaida Yami, suka gaisa sosai tana sanya masa albarka tare da yi musu adu'a sannan ya wuce sama. bayan tafiyarsa Yami ta kalli Fillo ta ce da ita,"ban ji kin yi masa sannu da zuwa ba, ba ki tashi kin karɓi jakar hannunsa ba, duk lafiya?". ta turo baki gaba tana faman ɓata fuska, ai kuwa Yami ta shiga yi ma ta faɗa sosai kamar zata duketa. "ta shi ki bi bayan mijinki". murya a kumbure ta ce,"ai sai kun tafi zanje Yami". tai maganar alamarta na shaida ko sun tafi ɗin ba zuwa zata yi ba. Yami ta taso mata da faɗan da yafi na ɗazu, ba shiri ta miƙe kamar zata yi kuka ta wuce sama fuuu, tana hawa ta shige ɗakinta, sai kuma taji kamar Yami zata hawo saman, hakan yasa tai saurin fitowa ta wuce ɗakinsa. ta buɗe ƙofar ta shiga babu ko sallama, ta nemi bakin ƙofa ta maƙale tana jan yatsu sai kace munafuka, Turaki ya buɗe idanuwansa da ke rufe ya bi ta da kallo, ƙwayar idonsa kawai za ka kalla kasan akwai abin da ke damunsa, akwai abin da yake buƙata sosai, ta ɗago ido karaf suka haɗa ido da shi, sai ta saurin juya masa baya, ya miƙe zaune da ga kishingiɗen da yake ya ce,"is there anything?". ta juyo tana turo ba ki gaba cike da zallar yarinta tace masa,"Yami ce ta ce na biyo bayan ka". babu shiri murmushi me kama da dariya ya suɓuce a leɓensa, sai ya tallafi haɓa yana kallonta kawai, ganin hakan yasa ta ɗan duki ƙafafu a ƙasa ta ce,"ce tayi ka kira min Ummi a waya". sai ya ɓata fuska ya mayar da kansa jikin pillow yace,"ba ki faɗa ma ta kin tarwatsa wayar ba?". kamar zata yi kuka ta ce,"ai na faɗa maka bana sa ne". "to sai ki jira sai kin gyaro sai kiyi kiran". kawai sai ta saka kuka tana faɗin,"to wayan naka ai ba guda ɗaya ba ne, dan Allah ka bani in kira Ummina, yau kwanana 9 banji muryarta ba fa". ya galla ma ta harara, banda tana kuka tsab sai tayi dariya saboda yacca idanunsa suka yi a hararar, ta ƙara dukan ƙafafu a ƙasa da shagwaɓa sosai tace,"don Allah ka ba ni kaji, to ni ka bani lambar sai inje wajen Baba me gadi ya ara min tasa". ya kasa ɗauke ido akanta, sai yaji tana cewa,"kuma kai fa kace za ka zame min kamar Abba nah". sai ya sauke numfashi ya ce,"zo ki ɗauka". ta taho kamar wadda ta yiwa ƙasa laifi, tana zuwa bakin gadon taga duka wayoyi biyun akan bedside locker har ma da keypad, tana kallon wacca ta fasa ta gane ta, kenan an gyara ma shi ne yake ta yi ma ta ciwon baki, ta ɗan waigo kaɗan ta kalle shi taga hankalinsa bai kanta, sai ta kai hannu zata ɗauki wayar, caraf taji ya riƙo hannunta ya janyota jikinsa ya zaunar da ita kan ƙafafunsa da ke tankwashe. "da kika fasa ai ba ki iya ba da haƙuri ba, shi ne saboda rashin kunya yanzu an gyara za ki zo ki ɗauka, to ba ni sai kije can wajen me gadi ya ara miki". ta shiga kokawar ƙwace hannunta tana faɗin,"to ai kaine kace in zo in ɗauka". "ehh ai ƙarshen rashin kunyarki zan gani kuma na gani, ba ni wayata ba zan bayar ba, kije shi me gadin ya ara miki tunda dama wajensa kike zuwa aron abu". ta ce,"to ka ban lambar". kawai ya fizge wayarsa sannan ya ɗauketa da ga kan ƙafar tasa ya dire a ƙasa, yasa wayoyinsa a aljihu yay shigewarsa toilet, after 3 minutes ya fito yana goge hannu da ƙaramin towel, mamaki yasa shi tsayawa yana kallon Fillo da ke durƙushe ta kifa kai akan gadon tana kuka bilhaƙƙi, yau rana ɗaya da ya tambayi kansa shin hawaye basa ƙarewa ne?, ko da yake in su na ƙarewa ai da tuni ya sami salama da wannan kukan, ya girgiza kai ya koma toilet ya mayar da towel ɗin sannan ya fito. ya dawo ya koma kan gadon yay kwanciyarsa ya juya ma ta baya, taji yana waya yana cewa,"oak gani nan, ki ajiye ki wuce, na bawa Samha saƙonki". ta ɗago kanta lokacin da yake sakkowa akan gadon yana barin ɗakin, ta bi bayansa da kallo, after few minutes sai ga shi ya dawo ɗauke da basket ɗin abinci, ya wuce ya ɗora akan table, sannan ya zauna akan kujera ya shiga zuba abincin da ke cikin flask, duk tana kallonsa yadda yake yi tamkar bai san da halittarta a ɗakin ba, ita kuma tana yi ana yana shareta shi yake daɗa tunzurata, hakan na ɓata ranta, har ya kammala cin abincin bayan ya tsarga masa ya taso ya dawo kan gadon, yay kwanciyarsa kamar mai bacci. can yaji ta riƙo hannunsa, ya juyo yana kallonta, ta kifa goshinta akan hannun nasa, hawayen idonta ya sauka akan fatarsa, ɗumin hawayen ya wuce ta cikin jijiyoyinsa har zuwa ƙirjinsa, tausayinta ya wanzu a zuciyarsa, gaba ɗaya jikinsa sai yay sanyi, Allah ma ya sa ni yana tsananin tausayinta, basarwa kawai yake yi, ko shi da yake namiji ba ya jin zai iya ɗaukar 2days bai ji muryar Mum da Maama ba, balle har akai ga kwanaki tara, ai sai rashin lafiya ta kama shi. but sai ya ƙara ɗauke kansa akanta, ya tamke murya ya doka ma ta tsawa yace ta fitar masa a ɗaki, ta miƙe jiki a sanyaye kamar wacca ƙwai ya fashewa a ciki ta fita, kai tsaye ƙasa ta koma wajen su Yami fuskarta duk caɓe caɓe da hawaye, sai da taje ta tarar su har sun wuce, sai ta dawo ta koma ɗaki ta rufo ƙofa, ta hau gado taci gaba da kukan gado. sai bayan fitarta Turaki yaji gaba ɗaya bai kyauta da abin da yay ma ta ba, ko babu komai mahaifiyarta take ta roƙon ya kira ma ta, duk sai yaji ransa babu daɗi, kasa daurewa yayi ya ta shi ya bi bayanta, a dunƙule ya ganta a tsakiyar gado, ya girgiza kai ya ƙarasa ya hau kan gadon gaba ɗaya. ya ɗagota zuwa jikinsa ya kewaye yana ɗora haɓarsa a saman kanta, yasa hannu yana goge ma ta hawayen fuskarta, ya shiga hura ma ta iska a kunne yana faɗin,"cry cry Baby what the cry for umm?". cikin kukan ta ce,"ba kai ba ne". ya ce,"OMG! laifin me nayi da har ya sa kike kuka?". tana motsi a jikinsa kamar zata shige jikinsa gaba ɗaya ta ce,"ba kai bane sai kake yi min tsawa bayan ka san bana so". yaja dogon numfashi ya sauke sannan yace,"to ai kece Fulani nah ba kya ji, duk yanda na so nai controlling anger na akanki sai kinja na ɗaga miki murya, phone ɗina fa kika fasa min da abubuwa masu muhimmanci a cikinta, but shikenan daga yau insha'Allah ba zan ƙara ba in dai tsawa ce". ya faɗa yana ɗago kanta daga ƙirjinsa ya ɗora goshinsa akan nata, ya hura iska a idonta suka lumshe yace,"shikenan?". kamar jiran tambayar takeyi ta girgiza masa kai da sauri tana cewa,"a'a". ya buɗe ido yana kallonta da shirin jin abin da yake tsammani, but sai yaji saɓanin haka. "ka bani haƙurin kukan da kake ta saka ni to, har ma da ciwon da kaji min". ba shiri ya tsura mata ido yana kallonta, sai yau ya ƙara ganin yarinyartarta ta fito sosai, ya ƙara tabbatar da muguwar rigimammiya ce, bakinsa yaƙi rufuwa da murshin da yake me haɗe da mamakin halin rigimarta. tana buɗe ido suka sarƙe a nasa, sai kawai ta tsuke fuska ta kai masa duka a ƙirji tana mayar da kanta ta kwantar, ya shafo gashinta yana cewa,"ni ne zan baki haƙuri ko da wani daban kike?". "kai ne mana, ai kaine kaji min ciwo, kuma kake min tsawa, kuma kake sa ni kuka, kuma kake share ni". ya ƙara ɗago kanta yana kallonta ya ce,"duk ni ɗaya!, to yanzu tsakani da Allah baki ji kunyar cewa in baki haƙuri?, ke fa kika fasa min waya me tsada, ni bance ki ban haƙuri ba sai ke". ta zumɓura baki ta ce,"to ai kaine ka janyo na fasa ban sa ni ba". "ni kuma?". ta ɗaga masa kai kawai. "to da nayi mene na janyo?, sharri kika fara?". sai kawai ta ƙura masa ido, kukan da ya tsaya ya dawo sabo, ya kwanto kanta jikinsa yana faɗin,"subhanallah!, ni kam naga ta kaina, Fulani wai me yasa kuka ba ya miki wahala?, wallahi Allah bana son hawayenki its hurts me alots amma kinƙi ganewa. kin ga ni dai yanzu mu bar ma zancen in dai kuka za kiyi, kin min laifi na miki laifi kowa ya rama anyi 1-1, yanzu dai mu shirya don ranar yau ba zata wuce ba sai anyi sulhu". ta kamo gaban rigarsa ta riƙe har sai da maɓallin ya cire, a hankali tace,"ni ba zan shirya da kai ba sai ka bani haƙuri". ya shafo wuyansa ya ce,"ya zanyi, bada haƙuri ai ba zai sa na ragu da komai ba, kiyi haƙuri". ta ɗauke hannunsa daga bayanta ta ɗago tana kallonsa, a shagwaɓe ta ce,"ba'a haka ba". sai ya lanƙwasar da kai yana kwaikwayon shagwaɓarta ya ce,"to a ya ya?". "ka kama kunnenka sai ka sakko ƙasa ka tsuguna". ganin bai da niyyar yi yasa ta juya masa baya tana faɗin,"to kayi tafiyanka kawai". ta faɗa tana sakin kuka kaɗan. wannan kukan ya sa shi saukowa ƙasa ya durƙusa, ya kama kunnensa da hannu ɗaya sannan ya kamo ɗayan hannunta ya ce,"to look at me mana". ko da ta juyo ta gan shi sai ya kusa bata dariya ganinsa ya koma kamar ɗan yaro. ya sarƙe yatsunsu wuri ɗaya wanda hakan yasa ta jin wani abu ya tsarga ma ta, shi kuma ya lumshe ido ya buɗe sannan ya ce,"we should ask for forgiveness if we make a mistake, I made a mistake and i am asking for your forgiveness, and i know you will forgive me, please am sorry for all my wrong deed, am so sorry Fulani Nah, promise you not to repeat such a mistakes insha'llah". kamar ya ƙara tunzurata sai hawaye sha, ya dafe kansa yana faɗin,"ya Allah! what again Fulani nah?, Is there anything else you want me to do after this?, ko kalar ba da haƙurin ne bai yi miki ba na sauya?". ya faɗa duk a ruɗe dan Allah shaidarsa ko kaɗan ba ya son irin wannan kukan nata, yana taɓa zuciyarsa, kawai dai dan babu yacca zai yi ne ma yake dakewa ya nuna kamar bai damu da ita da lamarinta ba, amma can ƙasan zuciyarsa shi ɗaya ya san me yake ji. cikin kuka sosai kamar zata shiɗe ta ce,"don Allah...". sai kuma tayi shiru ta kasa ƙarasawa. yay saurin komawa kan gadon ya riƙe hannayenta duka biyu cikin nasa ya ce,"don Allah what?, say it please, i am ready to do whatever you want". sai ta faɗa jikinsa tayi masa tight hug ta ce,"don Allah kar ka auro Aisha, bana sonta karka aureta don Allah, kace baka sonta, i will do whatever you say, but for Godsake don't marry her". he took a deep breath closing his eyes ya ce,"wacece Aisha?". "wadda kace zaka faɗawa Baffa zaka aureta". "when did i say that?". "ranar da ka ji min ciwo, kana faɗawa abokinka zaka aureta wai kana sonta, har na fasa maka waya bana sane, kuma ni bana sonta don Allah karka aureta". ya cika bakinsa da iska ya fesar, ashe plan ɗinsa yayi, ya shiga shafa gadon bayanta da gashin kanta in a romantic way ya ce,"the crying is enough, kinga ba ki da lafiya". tana sassauta kukan ta ce,"to ka fasa auren nata?". ya ce,"ba zan iya fasa aurenta ba". "saboda me?". ta faɗa tare da fashewa da sabon kuka tana zamewa da ga jikinsa. "saboda tana so na, ni kuma ina so na auri wacca take so na, kuma tunda tana so na idan na aureta zanji daɗi, zata ke yi min duk abin da nake so, zata kiyaye ɓacin raina, ba zata barni da yunwa ba, zata ke yi min soyayya me daɗi. to kuma kinga yanzu ke ɗaya ce matata, ke kuma ba kya so na balle duk kiyi min wancan abubuwan...". bai ƙarasa ba ta katse shi,"who told you i don't love you?". "ke fa kika faɗa a gaban su Baffa ranar da nace na aureki, kuma ma fa har kika dage sai na sakeki, to ni bana so in takura miki shiyasa zan aureta saboda ina so in zauna da wacca take so na". sai kawai ta ƙara faɗawa jikinsa ta ƙanƙame shi tana faɗin,"Allah ina sonka, kuma zan ke yi maka koma menene, but don Allah karka auro ta". ya janyeta ajikinsa yana faɗin,"ba zan iya ba fa, Aisha tana so na sosai, ba zan iya butulce ma ta ba, kiyi haƙuri". lokaci ɗaya tari ya sarƙe Fillo, ta dafe ƙirjinta da take jin yana yi ma ta mugun zafi kamar ana hura wuta, ta damƙe hannunsa ƙam jikinta sai shaking yake yi, hawaye tamkar an buɗe famfo, abu kamar wasa kan gadon sai ya ɗauki rawa kamar yanda jikinta yake yi, sai juyi take yi da kanta tana sosa ƙirjinta da yake yi ma ta wani mugun zafi. Turaki ya ruɗe ya kamota, yanda yaga tana yi da ƙirji da yacca numfashinta ke neman yankewa sai ya tuna da maganar doctor na heart failure ɗin ta, hankalinsa ya tashi ya shiga ambaton innalillahi yana kiran sunanta, ya kasa janyota jikinsa saboda yacca ta sarƙafe, ta riƙe hannayensa sosai ta tsayar da ƙwayar idonta akansa, hoton yacca za su dinƙa shairing ɗinsa su uku ne kawai take hangowa cikin idon nasa, kamar ba zata iya jurar ganin faruwar hakan ba, kamar gwara ta mutu, kamar gwara ya rabu da ita kawai. "Fulani nah, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". maganar yake yi a kiɗime, ya sauko akan gadon ya bar ɗakin, ɗakinsa ya nufa cikin hanzari ya ɗauka drugs ɗinta da ya siya ya ajiye su safe gudun ɓacin rana, ya ɓallo ya buɗe bakinta ya zuba ma ta, sannan ya shiga tayata shafa ƙirjinta da take ta cewa zafi. a hankali taji ta fara samun relief, sai ta kai hannunta gefen fuskarsa ta kama tana faɗin,"Allah ina sonka, i am saying this from the bottom of my heart". ya shiga ɗaga ma ta kai yana faɗin,"yes i know, na fasa auren Aisha, ba zan aureta ba na yarda kina so na, kuma za ki min ko me nake so". ta sa babban yatsanta a gefen bakinsa ta ce,"i love you much, but ai kai baka so na, ka daina so na, ka na sa ni kuka da yawa". yana murmushi ya kamo hannunta ya ɗora a ƙirjinsa daidai saitin zuciyarsa ya ce,"i wish i had the chance to open my heart to you, you would have seen that you are the only one inside without anyone else, kece fa zaɓin Muhammad Turaki, kuma zaɓin Hajiya Madina, kuma zaɓin Hajiya Ramla". sai ya tattaro ta jikinsa ya rungume tsam,"Fulani nah i promise to you insha'Allah zan saka ki murmushi more than yadda na saka ki kuka, ki kwantar da hankalinki babu wata Aisha da zan auro, wasa nake yi, i say it just to see your reaction". sai ta janye a jikinsa tana tsayawa da kallonsa as if she have never seen him before, har yaushe ya gane tana kishinsa da ya nemi yay wasa da rayuwarta haka?, duk yacca ta ke ɓoyewa da ma sai da hakan ya bayyana ta wani ɓangaren bata sani ba, sai ta tura baki gaba zata kau da fuska yay saurin saka hannu ya tare hakan, ya marairace yana kama kunnensa ɗaya kamar a ɗazu ya ce,"am so sorry ƴar lelen gidan su Zaytun, ki ce kin haƙura kar Hajiyoyin gidan Alƙali su ƙara min tsinin goshi da remote". daga ita har shi murmushi suke son yi but kowanne sai ya cije, ta kai yatsanta kan goshinsa tana shafa ƙullutun wajen da bai baje ba har yanzu, sai kawai ta ƙyalƙyale da dariya, wanda hakan shi ma ya sa shi dariya, yana kama hancinta yaja. "kayi sabon ido a goshi". yasa haƙori ya ciji hancinta,"zan rama ne akanki". sai kuma ya kwanta itama ya kwantar da ita a jikinsa yace,"shikenan mun shirya?, an daina kukan?, an daina min tsiwa an daina share ni?, an mayar da aurena?". ba tayi magana ba kawai ta ɗaga masa gira, yace,"thank you". ya faɗa yana shafa sajenta ita kuma tana so ta ɓoye fuskarta a ƙirjinsa. bakinsa a saitin kunnenta yace,"to sai yaushe kuma". a hankali ta ce,"what?". ta faɗa yana jin saukar ɗumin iskar bakinta akan ƙirjinsa, wanda ya nemi ya haifar masa da kasala, jin yay shiru ta ƙara tambayarsa, sai ya sosa gefen fuskarsa yana faɗin,"just forget, not now". ya mirgina yana riƙe da ita a jiki yace,"ke yanzu da na baki takarda kawai sai kika ɗauketa as divorce paper?". kunya ta kamata ta ce,"to ai na ɗauka idan aka bawa mace farar takarda sakinta aka yi". yana wasa da hancinta ya ce,"tunda kin ɗauka ai sai ki sauke...oya bani labarin kukan da ki kai tayi, duk da na san rabi kukan shagwaɓa ne, to sauran rabin na mene?, na son Turaki da kishinsa ko na mene?". tasa tafin hannu ta rufe masa baki da ido, sannan ta ce,"i want sleep". ya sauke hannun da yake kan idonsa sannan ya ɗora nasa hannun akan nata da ke bakinsa yace,"its after 4 babu kyau baccin yamma". ta shagwaɓe tana cewa,"ɗan kaɗan zanyi". bai ce komai ba ya ɗora kanta a ƙirjinsa, take kuma bacci ya ɗauketa, da kukanta da baccinta su na ba shi mamaki, abu ne da duk basa yi ma ta wahala, ita dai shekarun ne kawai da ita but komai da take yi na ƴan 4-5years ne. ya kamo hannun da ke da ciwo zai warware bandage ɗin sai yaji ta motsa, hakan yasa ya ƙyale yaci gaba da looking at her innocent cute face. *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *51* sai da aka fara kiran sallar magriba tukunna Turaki ya iya zame Fillo daga jikinsa, sanin cewa ba sallah zata yi ba kawai yaja blanket ya rufeta, yay kissing forehead nata sannan ya fita, yana zuwa ɗakinsa yay alwala ya wuce masallaci. a masallaci ya zauna har sai da akayi sallar isha'i tukunna ya dawo, for the first dawowarsa gida bai wuce ɗakinsa ba kai tsaye, bedroom ɗin Fillo ya wuce, yana shiga ya tarar har yanzu bacci take yi, ya girgiza kansa yana mamakin irin baccinta. durƙusawa yayi a gaban gadon yana yaye blanket ɗin ya kamo hannunta, ɗayan kuma yana shafa fuskarta sai kallonta yake yana murmushi, fuskar baccin nata kaɗai ya isa ya shaida maka rigimammiya ce, haɗe gefen fuskarsa da tata yayi, ya lumshe idonsa for some minutes ya buɗe, yasa hannu yana jan hancinta yace,"Fulani nah baccin ya isa haka". ta buɗe idonta a hankali, cikin baccin da yake cinta ta dube shi ta mayar da murfin idon ta rufe tana juya masa baya. murmushi yay ya miƙe tare da hawa gadon ya cicciɓeta ya fita da ita zuwa ɗakinsa. direta yay a ƙasa yana kama hannayenta ya ɗaga sama, sak irin yacca akewa ƙanan yara idan za'a tashe su, ta buɗe lumsassun idanuwanta ta kalle shi tana sakin kukan shagwaɓa,"ni fa bacci nake ji". ya rumgumeta yana kwaikwayon muryarta shi ma yace,"ni kuma i want you to wake up, kin barni ni ɗaya i feel lonely, ki tashi ko rigima ce muyi". haka yay ta damunta har sai da ta wartsake tukunna ya ƙyaleta, ya kama hannunta suka isa wajen gado, ya zauna a gefe yana ƙoƙarin ɗorata a saman cinyarsa sai taƙi, taƙi zaman becose she is not feeling comportable saboda period ɗin da take ciki, tana jin ma kamar tayi staining. "mene amfanin ƙafafun nawa idan ba ki zauna akai ba?". ta ɗan kauda fuska tace,"ɗaki zanje". yaja hannunta har sai da ta juyo ta kalle shi yace,"nan ba ɗaki ba ne?". "to ai toilet zan shiga". ya miƙe tsaye yana faɗin,"nan ma ai akwai toilet ɗin, muje let me escort you". ya faɗa yana kama hannunta zuwa toilet, sai ta maƙale a bayansa taƙi shiga, ya janyota zuwa gabansa yana kallonta, ta kifa kai akan cikinsa tana cewa,"ni toilet ɗina ba wannan ba, ina so zanyi wanka". ya ce,"nan ma ai ana wankan". tasa taɓara,"ni ba wannan ba to, nawa zanje please leave me". ta faɗa tana ta maƙalewa a bayansa, bai kulata ba ya buɗe toilet ɗin suka shiga ciki duk da faman tirjewan da take yi, tana kallo ya kunna ruwa a bathtube har sai da ya cika sannan ya dawo da idonsa kanta, su na haɗa ido ta ɓoye fuska a bayansa, ya juyo da fuskartata yana cewa,"kiyi wankan anan". sai ta shiga dukan ƙafafu a ƙasa cike da kukan shagwaɓar da ke neman juyewa zuwa na gaske tace,"to ai..". ya katse maganartata ta hanyar ɗora yatsansa saman lips ɗinta,"ba na son musu, kiyi anan nace". tayi narai-narai da idanu hawaye na sakko ma ta tace,"to ai zan ɗauko abu ne". bai kulata ba ya janyo towel ya bata,"ko kiyi da kanki ko nayi miki". ta saurin karɓa ba tare da ta yarda ta kalle shi ba. "zan ɗauko miki ko me

Chapter 57 of 73