tace,"tace na faɗa miki Jakadiya babba ce tace a kawo miki. Wai kici ki ƙara ƙarfi da ƙiba".
Kaka tai dariya tana faɗin,"to sikenan, godiya nake sosai. Dama kinga duk mun kasa cin shinkafar ɗazu".
Rufe bakin Kaka kenan tambayar da Fillo tayi mata tai wani duka acikin kanta, inda har sai da ta zabura taja da baya.
"Kaka idan mutum ya tone asiri ko ya ƙone shi, wani abu yana samunsa ne?".
"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yanzu wannan tambayar daga ina?, Fillo kullum faɗa miki nake bakinki ya dinga faɗar alkhairi ko yay shiru, yanzu tsakani da Allah kamarki ina ke ina magana akan asiri?, yanzu inda baƙuwan fuska wajen ba sai ya tsammaci wani abun daban ba. Dan shi ba zai dubi rashin hankalinki ba".
"kai jama'a Kaka, ina batun rashin hankali anan, tambaya ne fa mabuɗin ilimi...amma shikenan tun baki amsa min zan tambayi Amir".
"aikuwa tambayarki gare shi dai-dai yake da rabuwa dake. Dan tsammani zai yi shi zaki asirce ko kuma kin yiwa wani ne. Kinga ni dai ki rabani da batun asiri, dama ya ya lafiyar kura? Ban gama fita daga tashin hankalin ɗazu ba zaki ƙara jefa ni cikin wani".
Maijidda tace,"Kaka tashin hankali kuma?, me ya faru?". Kamin Kaka tai magana Fillo ta amshe. "bafa wani abu bane. Akan wutar da ta tashi ɗazu ne wai shine take ta tsoro kar binciken da aka saka na gano musababbin tashin wutar ace ɓangaren masu aiki ne". Ta miƙe tana ɗaura ɗan kwalinta tana cigaba da cewa,"kuma na faɗa mata tunda dai tasan ba ita ta saka ba mene zaisa ta damu kanta".
Maijidda tace,"to taya ma za'ace ɓangarenmu ne mu ba zuwa wajen muke ba". Ta faɗa cikin dakiya, dan tunda akai zancen wutar jikinta ya fara ɓari, saboda ɗazu tana ji Yami na faɗin wai wutar sai data shiga har cikin lambu, dan ta kusa cinye rabin shuke-shuken ƴaƴan itatuwan dake ciki.
"to ma ace ma ɓangaren namu ne, dama ni na gaji da zaman gidan nan...kinga idan aka koremu ma koma rugarmu mu hankali kwance".
Kaka ta ɗauko murfi zata ƙwala mata tai saurin matsawa daga wurin tai bakin ƙofa tana dariya. "Kaka bara muje gaida Hajjah Gana, kwana biyu ban leƙa ba kar ta shigo tana miki ciwon baki".
"karki yi dare". Shine abinda tace da ita, sannan suka sa kai ita da Maijidda suka fita.
Tunda suka fito Maijidda ke ta surutunta, Fillo dai bata ce mata komai ba. Har sai lokacin da Maijiddan ta ankare da inda suke nufa sannan ta saurin dakatawa da tafiyan ta dubi Fillo tace.
"wai ina zamu je?".
"ina kika ga mun nufa?".
"cikin gida".
"to muci gaba da tafiya".
Maijidda tai shiru tana kallonta kamin tace,"idan kina wani abun kamar bake ba. Wane ɗan aiki ne kika taɓa ganin yaje ɓangaren masu gida idan ba Hajiya ce ta buƙaci zuwansa ba...ko kuma kin bawa wani ajiya ne?".
"babu wanda ya taɓa zuwa dan ko Kakata ma sau uku ta taɓa shiga. Ni kuma yau ina son shiga kuma tare dake zamu je, dan ke ɗaya ce hanyar da nake da ita tiryan tiryan da zata kaini ɗakin Turaki".
Ai shirunta sai ya haɗe da sauke hannunta da Maijidda tai daga saman kafaɗarta. Tai saurin juyawa a tsorace zata koma inda suka fito. Da azama kuwa Fillo tasha gabanta. "ke ban faɗa miki ba. ɗazu fa wutar dana haɗa asiri na ƙona". Ai kamin ta ƙifta ido ta buɗe Maijidda ta kwasa da gudu ta barta a wajen, dan ita har ga Allah ta fara tsorata da lamarin ƙawartata.
_Please don't skip any page without commenting or voting. Becoz thats the only way you will show your love and appreciation towards me. It encourage me to do more🥰._
Don Allah share to other groups fisabilillah🙏
Youtube Channel-Sahaz Multimedia
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*4*
*E9611, Ibb Way. Maitama Phase 1 Abuja.*
Ɗil 1,2,3,4,5, Adadin seconds ɗin da suka buga kenan ajikin agogon dake manne a bangon ɗakin, tagogin windon ɗakin a buɗe suke, iska ta busa inda ta shigo ta cikin windon ta ɗaga labulen tagar zuwa sama.
hasken rana ya ratso ta tsakanin labulen ya haska idon Turaki dake tsaye a gaban madubi yana saka agogo a tsintsiyar hannunsa. Wannan hasken yasa shi kanne ido tare da ɗagowa ya kalla tagogin da iskar ke ta busowa zuwa ciki, na tsawon seconds ɗaya sannan ya maida kansa ƙasa yaci gaba da ɗaura agogon.
haka kawai daren jiya da zai kwanta yaji baya buƙatar iskar bature, ko ta fanka ko ta Ac, dalilin daya sa shi buɗe window kenan, kuma ko da ya tashi sai ya manta bai rufe ba har ya kunna Ac, wanda sai a yanzu ya fahimci dalilin da yasa Ac ɗin taƙi yin sanyi yanda ya kamata.
Sanda ya gama taje sumar dake kansa ya miƙa hannu bakin gadon da hularsa ke ajiye zai ɗauka, yana ɗora hannu akai agogon ɗakin ya buga ƙara, sai ya ɗago kansa a kaikaice ya kai kallonsa ga inda agogon yake.
Ƙarfe 9 na safe shine lokacin daya buga, Mutumin da yazo cikin kansa a wannan lokacin shine Bello Ƙaraye, ko bai faɗa ba yasan yanzu yana can yana mita shi kaɗai na barinsa da yay yana jiransa. Sai kawai ya motsa leɓensa sannan ya ɗauki hular ya saka. Ya zauna a bakin gadon dan saka takalmi wayarsa ta shiga ƙara, inda ringtone ɗin i love you Maama ya karaɗe duka ɗakin.
Ya miƙa hannu ya ɗauki wayar kuncinsa na murmusawa. bai picking call ɗin ba har sai daya yanke tukunna yabi bayan kiran, bugu ɗaya aka ɗaga tare da yin sallama. Allah ɗaya yasan me yaji acikin zuciyarsa a wannan lokacin, bai amsa sallamar ba sai daya lumshe idonsa tukunna.
"Babana".
Sautin muryar Hajiya Madina tayi amo acikin kunnensa, Sunan da ta kirasa da shi ya fama masa wani ciwo dake zuciyarsa, ciwon da ba zai taɓa warkewa daga gare shi ba har sanda numfashinsa zai tsaya, ya riga ya san da wannan, kuma kowa ma ya san da shi.
Lokaci ɗaya yaji wani dunƙulallan abu ya tsaya a maƙogoronsa ya hana yawu wucewa, bai san lokacin daya ɗaga wayarsa ya daki goshinsa da ita ba. Irin hucin da yake jerawa ya ankarar da Hajiya Madina situation ɗin da yake ƙoƙarin shiga, dan haka da sauri tai ƙoƙarin dakatar da hakan ta hanyar kiran sunan da ita kaɗai ke kiransa da shi, kuma shi kaɗai ne sunan da za'a faɗa masa ya faranta ransa.
"Me babban suna, be patient please".
Lokacin da tai furucin kwanciya yay ajikin gadon yana fuskantar P.O.P, yatsun hannunsa na hagun a saman karan hancinsa yana murzawa da ƙarfi, yayinda idanuwansa ke a kulle har yanzu basu bar raɗaɗi ba.
"Ina kwana Maama".
"Ka tashi lafiya?".
"lafiya lau, ina fatan duk kuna lafiya?".
"muna lafiya lau, Ya wurin aikin naka?".
"Aiki mun gode Allah, yanzu nake shirin fita".
"Glad to hear that, Allah ya taimaka ya bada sa'a da nasara".
Daga kan dining ɗin da Hajiya Madina ke zaune, ta kai glass cup ɗin da ta ɗauka bakinta ta kurɓi lemun dake ciki na five alive, sannan ta ƙara cewa da Turaki. "When are you coming back home?".
"Ina kan hanya zuwa wani satin Insha'Allahu, munyi magana da Baffa jiya".
Jin yace mata sunyi magana shi da Baffa ta murmusa kuncinta kamin tace,"To shikenan Allah ya dawo min da kai lafiya".
"amin ya Allah Maama".
"ina fatan Baka da matsalar komai ko?".
"Babu Maama".
"to Allah yayi maka albarka...Make sure you eat your breakfast before you go to office".
Ya kai hannu ya shafo gefen fuskarsa inda gashin sajensa yake kamin ya amsa da,"insha'Allahu Maama".
Taso su tattauna wani batu amma saboda wani dalili nata sai ta fasa, Basu yi sallama ba sai da tai masa adu'a sosai tukunna. Kuma kiran nata na katsewa kiran Bello Ƙaraye ya shigo a lokacin, ya ɗaga da guntun murmushi a fuskarsa, sallamar da yay sai da Bello Ƙaraye yayi kamar ba zai amsa masa ba.
"Ba zaka fito bane yau?".
Turaki na dariya ƙasa-ƙasa yanda Bellon ba zai ji ba yace,"ehh kamar dai hakan".
"naga dukkanin alama". Yana faɗar hakan ya katse kiransa, bayan ya jawa Turaki tsaki na ɗan rainin hankali kawai.
Gaba ɗaya Turaki bai yi niyyar yin break fast ba, amma saboda abinda Maama tace haka dole yaja ya tsaya a sanda ya fito parlo. Ya nemi kujera ya zauna tare da janyo center table gabansa, dama already yasa wani ɗan aikensa yay masa order na chips tun 6, kuma da yaga zai yi late sai ya yanke shawaran idan yaje office yaci, to amma babu yanda zai yi tunda Maama tai magana.
Ya ɗauko chips ɗin zai kai baki sai ya dakata saboda Zaytuna da ta faɗo a ransa, duk da cewar tana cikin ransa a kowacce bugawar daƙiƙa. To amma dai a yanzun baya jin zai iya saka komai acikinsa idan har itama babu abunda taci.
Wayarsa ya ɗauko ya kira lambarta, kira na farko bata ɗauka ba sai ana biyu shima sai daya kusa yankewa.
"Hellow Hammah nah". Ta kira sunan nasa cikin muryar bacci.
Yatsun hannu basu isa sun ƙirga adadin farin cikin daya shiga ba da jin muryarta. Ya sauke numfashi sannan yace.
"ba za ki daina wannan malalacin baccin naki ba ko Zaytun?".
"Hammah nah jiya bamu kwanta da wuri ba ne, ka san Boɗejo tazo...to ta tsaremu da wannan hirar tata mara ƙarewa bamu ankarewa ba sai gani mukai lokaci ya wuce".
"yayi muku kyau ai, kuyi ta biye mata tana hanaku baccin kirki, bayan ita ta riga tayi nata tun yarinta".
Zaytun tai murmushi me ƙarfin sauti ba tare da tace komai ba, kasancewar ita ɗin ba mai yawan magana bace.
Turaki ya ƙara cewa,"dama i just call to check on you, I hope all is well?".
"komai lafiya Hammah nah".
Yay ɗan jim before saying,"idan kinyi breakfast let me know...amma yanzu fa za ki tashi bana son zama da yunwa, ki kalla time ki gani ƙarfe nawa".
Ba tare da ta duba komai ɗin ba tace,"Yanzu fa Safiyan yay Hammah". Tai maganar a shagwaɓe.
"shafo cikin ki sai ki faɗa min yanda yake".
Ta kai hannu kan stomach ɗinta sannan tace,"Hammah nan yana nan yanda ka san shi a shamule".
"to kinga alamar yana buƙatar abinci kenan, i keep telling you babu namijin da zai ɗauke ki alhalin yasan cikinki da bayanki a haɗe suke, he will think you can not bear him a child".
Tabbas ya faɗi maganar ne to entertain her, kuma hakan ce ta kasance, dan sai da tayi dariya sosai har baccin da bai bar idonta ba ya saketa lokaci ɗaya, ta miƙe zaune akan gadon tana ɗora pillow akan cinyarta, fuskarta cike da annashuwa tace da shi.
"ni da nake so ko da Allah bai azurtani da ƴaƴa da yawa ba, ya bani guda ɗaya tilo da zan saka masa sunan Hammah nah. Dan haka dole na tashi naje naci abinci ko da banyi niyya ba...ni Hammah idan ma kaga ana tallan maganin dake ƙara tumbi ka sayo min kawai".
Turaki yay siririyar dariya da cewar,"wasu na neman ragewa mu kuma muna nema". Yay maganar yana mai duban agogon hannunsa sannan yace,"zan wuce office na kusa late".
Daga haka sukai sallama cike da kewar juna.
*After 10minutes, Growth Stack Software.*
*Zone 5, 1st Floor Novare Central, Dalaba St, Wuse 900285, Abuja.*
Motarsa ta shigo cikin company ta ƙarasa zuwa wurin da aka tanadarwa ma'aikata domin aje motoci. Tun kafin ya ƙarasa buɗe murfin motar wani tsoho ya ƙaraso wajen cikin sassarfa.
"sannu da zuwa ranka ya daɗe".
"yauwa Baba sannunmu". Ya faɗa a sanda yake fitowa daga motar ya rufe.
Tsohon ya buɗe bayan motar ya ɗauki ƴar ƙaramar jakar laptop ɗinsa, sannan yay cikin office ɗin da ita. Shi kuma Turaki ya mara masa baya, tunda staffs ɗin wurin suka ganshi suke ta rissinawa suna gaida shi matsayinsa na Managing Director a ma'aikatar.
Bai shiga office ɗinsa ba kai tsaye ya wuce zuwa ofishin Manager, ya ɗauki kusan 5minutes sannan ya fito ya wuce nasa office ɗin bayan Manager ya shaida masa ya tsayar musu da lokacin da zasu shiga meeting ɗin.
Zamansa kenan akan kujerarsa sai ga Saktariyarsa ta shigo, ta aje record book ɗin dake hannunta a saman table ɗinsa, ya janyo shi zuwa gabansa yay rubutu ajiki sannan ya ƙara miƙa mata. Ta ɗauka sannan tace da shi.
"ranka ya daɗe PWC sun shigo tun aroud 8:30".
Ya ɗago daga kan computernsa ya kalleta, yana mai ɗan ƙanƙance idonsa cikin yin nazari kafin yace da ita.
"dama muna da Appointment ne da wasu this week?".
"a'a ranka ya daɗe, nima dai nayi mamakin zuwansu..to amma da suka ce min daga ofishin Manager suke sai na tsammaci shi ya turo su wurinka".
Ta faɗa tana buɗe wani file na daban dake hannunta ta ciro wani envelop aciki, sannan ta miƙa masa. "sunce na baka wannan".
Duk acikin harshen turanci ta ke maganar. Ya miƙa hannu ya karɓi envelop ɗin ya buɗe, cikin seconds ɗin da basu haura 10 ba ya gama karanta abinda ke jikin takardar. Bayan ya gama ya miƙa mata tare da cewa.
"ki kai office ɗin Manager, zamu yi waya da shi yanzu".
Ta rissina tare da karɓa sannan ta fita daga office ɗin.
Don Allah share to other groups🙏
Follow me on:
ArewaBooks-Halimahz
OkadaBooks-Halima_hz
Wattpad-Halima_hz
Youtube Channel-Sahaz Multimedia
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*5*
Fitarta da minti biyar akai knocking ɗin door, ba tare daya ɗago kansa daga kan system ba yace,"yes come in".
Muryar nasa ya fito a hankali yayin da hannunsa guda ke dunƙule a gefen bakinsa.
Bello ƙaraye ya shigo cikin office ɗin ya zauna akan kujera, ya fuskanci Turaki da har yanzu bai ɗago ido ya kalle shi ba yace da shi.
"sai yanzu ka ga damar fitowan?".
Turaki na typing a Laptop yace,"kai ma dai kasan ba mata gareni ba balle na sami me tashina da wuri".
Bello Ƙaraye yay masa wani duba yace,"tun yaushe ake cewa kai auren kaƙi. ni na rasa ruwan idon uban me ka tsaya yi da har yanzu ka rasa macen da tayi maka".
Turaki yace,"Lokacina ne bai yi ba, ko kaga nayi girman da za'a dinga tarata da maganar aure ne?".
Bello ya harare shi yace,"sannu motsin gado".
Turaki yace,"Yauwa, don haka sai a barni na sarara".
Bello ya ƙara cewa,"yanzu Asma'u ɗin ma bata yi maka ba?". "yes, she is not beautifull enough, and you know me well bana son abu mara kyau...idan kana sonta ka ƙara ata biyu na bar maka".
Bello dake masa wani kallo yace,"Baka da hankali...let close the charpter kamin ka ɓata min rai. kuma bari na faɗa maka, ka daina discouraging mutum akan abunda kai bai yi maka ba alhalin shi yayi masa, Ishaq told me you were telling him to get rid of that girl after all kasan yayi magana da iyayen yarinyar nan...tsaya ma! just because you think the girl was too local shikenan sai akace ba za'a aureta ba?".
Turaki yay guntun tsaki yace,"ka zo muyi magana akan aiki ne ko kuma zamu tsaya kan shirmen zancenka ne, da baku da aiki sai zancen soyayya, mace, aure".
Har yay shiru sai kuma ya ƙara cewa,"to for what reason ma yana da degree har biyu zaije ya ɗauko yarinyar da she didn't even finish secondary school".
"to kai ina ruwanka?, shi ai yasan da hakan yaje ya ɗauko ta ko".
Turaki yay tsaki, Bello bai ce da shi komai ba ya fiddo laptop ɗinsa dake cikin jaka. Yay danne danne aciki ya juyar da fuskar laptop ɗin yana nunawa Turaki.
"Na sami number'n contractor ɗin, zanyi waya da shi zuwa dare". Turaki ya faɗa a sanda ya gama karanta rubutun dake jiki, sannan ya miƙe daga kujerarsa zuwa gaban wata drower da tarin takardu suke a cikinta.
Bello Ƙaraye na binsa da kallo har sanda ya taka steps hannunsa ya kai cikin drower ɗin yana fito da wani file dake ƙunshe da takardu fal aciki. Ya dawo kan kujerarsa yana duba takardun cikin file ɗin. Bayan yay musu ɗai-ɗai ya kwashi wanda zai amfani da su ya wuce cikin madaidaicn parlon dake cikin office ɗin, daga bisani Bello ya mara masa baya.
Tsaye ya tarar da shi yana fuskantar gilashin windo, ya harɗe hannunsa guda ɗaya ta baya. Idanunsa na kafe ne akan glass ɗin kamar mai son ɗakko wani abu ajiki. Bello ya zauna kan kujera yana ƙarewa tsayuwar Turaki kallo, tsayuwar nan tasa mai cike da ƙasaita da taƙama, kana kallo zaka san an gaji sarauta cikin jini da asali.
Sanyin Ac yasa idanuwan Turaki lumshewa, muryarsa a kausashe yace, "tunda naji ana talking of billions tunanina ya bani da akwai wata a ƙasa".
Ya faɗa sannan ya juyo ya zauna kan kujerar dake fuskartar Bello, ya shafo fuskarsa da duka tafukan hannunsa biyu kamin yace,"dole ne ma ba zamu yi aiki da wannan company ɗin ba".
Bello ya dube shi da mamaki yace,"saboda me?".
"yanzu Accounter suka fita shi da mutanen nan".
"ta ina kai ka gansu?".
"a bakin gate suka tsaya, shi kuma ya fita da mota ya ɗebe su".
Ya faɗa ƙwayar idonsa na haskawa da dimbin ɓacin ran dake ciki, ya ɗora ƙafafunsa kan table ɗin dake tsakiyarsu, sannan ya koma ya jingina da kujerar da yake zaune.
Idanunsa a kulle yake cewa,"rayuwa cike ta ke da marasa halacci, ko kaɗan bana son mutum mara gaskiya".
"So now how are we going to tackle this problem?".
Bellon ya faɗa shima in astonishing at what Turaki had said.
"na san yanda zanyi tackiling ɗin abun, let's get out of the meeting first".
*Gombe, Dukku.*
*Alh. Ahmad Alfindiki Residence, 8:30am.*
"Kaima ai ka sa ni, it's either na kwana gida ko kuma na wuce gidan Khalid, na tsani kwana a hotel if not necessary".
Yusuf ke magana a wayan dake maƙale a kunnensa, yasa key ya rufe motan sannan ya wuce ɓangaren Inna Wuro wato Kakarsu, har lokacin daya shiga parlonta bai gama wayar ba.
Inna Wuro na zaune kan ɗaya daga cikin kujerun parlon ta kalli Yusuf daya duƙa yana cire takalminsa, ta taɓe baki ta ɗauke kai taci gaba da kallon tv da ta ke.
"yes kusan 2 weeks ma kenan, but i think i will be coming back next tomorrow by God willing. Becox akwai patient ɗin da nake da ita acan".
Yaci gaba da wayar yana ƙarasowa ya zauna kan 1 seater. "alright i will you call before then insha'Allah".
Inna Wuro dai dake kallo hankalinta ya rabu gida biyu, tun shigowarsa ta ke jera ƙwafa. Ji ta ke kamar ta tashi ta fizge wayar ta rotsa ta a ƙasa, sai taga ta tsiyan shigo mata waje babu sallama. Ta lura ma gaba ɗaya yaran gidan sun maida ita ƴar iska, kowa ya tashi shigo mata waje sai ta kaɗo masa yake shigowa da sallama, sun fi gane su shigo kullum suna ɓaɓatu a waya kamar dan su bature ya ƙera wayar.
Yusuf daya gama wayar sai da yay typing message a wayarsa kana ya sakata a aljihu, sannan ya kai idonsa kan Kakarsu yace,"Ina Kwana".
Ba tare da ta dube shi ba a fusa ce tace,"yana kwano".
Yay ɗan murmushi ya ƙara cewa,"kin tashi lafiya?".
"da baka ganni anan ba ai".
Yace,"to Allah ya ƙara lafiya".
Bata dai amsa mishi ba taci gaba da kallonta, kallon da gaba ɗaya ba fahimtarsa ta ke ba. Bakinsu kawai taƙe kallo tana yin dariya a inda ya kamata, ta kuma ja uban tsaki a inda akai mata ba daidai ba.
Ta gefen ido ta ke ta kallon Yusuf, wanda ya sauko ƙasa ya takwashe ƙafafunsa, ba tace da shi ƙala ba sai daya janyo flask gabansa sannan cikin hanzari ta dakatar shi.
"me haka?, kwanon abincinka ko nawa da zaka wani janyo shi gabanka?, ko kuma Uwarka ta dafa ta kawo min ne da zaka nuna min iko da shi?, salon dai neman magana irin ta bawa...ina ce da ka shigo ko sallama baka min ba balle na sami arziƙin gaisuwa, saboda ka maida ni abar banza shine sai da ka gama waya da wanda ya fini tukunna zaka durfafi abincina...to baka isa ba, kuma ba'ai wannan halittar da zata taɓa min kwano ba, ka tashi ka koma ka zauna ko kuma ka bar min parlo tun bamu samu saɓani da kai ba. Ni bana son tashin hankali haka kawai".
Yusuf ya miƙe ya koma kan kujerar ya zauna ba tare da yace mata komai ba, ta kalle shi kaɗan ta kwaɓe fuska kamin tace,"yafi maka dai".
"amma dai ina ce bayan na gama wayar na gaishe ki". Yace da ita yana kallonta. "bata yi min bane". "wa?". "ita gaisuwar taka". "ohh to Allah huci zuciyarki". Ta amsa da amin.
Yaci gaba da danna wayarsa, tsawon mintina kusan uku yaji maganar Inna Wuro na cewa.
"aiko ka akayi ne?". Bai zaton da shi ta ke ba, dan farko ɗagowa yay yana dube duben ta inda zaiga mutum, sai da yaga ba kowa sannan yace. "ba wanda ya aiko ni".
"to kuma zaman ma mene?, zuwa da sassafe haka, babu fa jimawa aka gama min gyaran wurin nan. bana son a ɓata min waje dan ni ba fiya son ƙazanta nai ba...da ba za'a bar mutum ya huta ba dole sai anzo ɗaukar magana".
Rufe bakinta kenan Aliyu ya shigo parlon, ta bishi da ido har sanda ya nemi three seater ya kwanta yana ɗora ƙafafunsa akan hannun kujeran. Haushi ya tuƙeta tace,"idan ka tashi Amadu ya gyaran wajen".
Shi dai bai kulata ba ya ɗauko earpice a aljihu ya saka a kunne, Yusuf na kallosa yana mamakinsa, shi dai a wannan zamanin bai ga namiji mara lissafi ba irin Aliyu, yana namiji tunda akai hutun ASUU shikenan ya zama kamar mace, kullum yana gida sai shegen aikin jin waƙoƙin banza, yaƙi sana'ar fari balle ta baƙi, idan anyi magana yace ai Babansa ya tara musu...kuma in ana faɗa masa gaskiya Ammi tace ba haka ba.
Ya jijjiga kansa kawai yana jan ƙaramin tsaki na takaici. Aliyu yace da Inna Wuro,"naga mutanen ƙauye sun zo".
Tace,"to su tsaya a iya ɓangaren ku bana son gayya". Yay gajeriyar dariya sannan yace,"ya za'ai su zauna a ɓangarenmu?".
Tace,"nima ya za'ai su sauka a ɓangarena?, Ni dai magana ta Allah idan kaje ka faɗawa Uwarka kar a soma turo min kowa, dan wancan karan banji daɗin zuwansu ba. Banda Amadu ya gina masai babba da ban san yanda zanyi ba, abunda ban taɓa gani ba sai a lokacin kashi har bakin masaina. Ɗoyi kuwa iri-iri babu kalar da ban guntsa ba, inda ace Uwarku ce kaɗai a gidan nan ai da warin kashin yaran ƙauyen nan shi zai zama ajalina. To sai Allah yasa akwai Falmata, tazo da kanta wallahi ta wanke min banɗaki nan ta sanya masa turaren wuta".
Aliyu yace,"itama Ammin ai zata yi miki, dan dai bata sa ni ba ne, kuma ai da sai ki faɗa mata".
Ta kama baki tace,"to ina ma ta ke zuwa waje na balle na sanar mata. ni fa idan kaga mun haɗu da ita Amadu ne zai yi tafiya mu haɗu a wajen masa rakiya kamar kishiyoyi, amma ni ina nake da wani arziƙi a wajen Zainabu...kana dai kallo ko gaisuwar safe".
Bai sake cewa da ita komai ba. Ta miƙe ta ɗauki flask ɗin abincin da aka kawo mata tun ɗazu bata ci ba ta wuce da shi kitchen, dan idan ta barshi Aliyu ma saka masa hannu zai yi, shi kuma ba jin magana yake ba.
Fridge ta buɗe ta saka yanda ma ko da wani ya shigo kitchen ɗin ba zai gani ba, har ta nufi ƙofa zata fita sai ta tuna ta dawo ta sakawa fridge ɗin key dan lemon da yake ciki sauran guda uku, Amadu bai san ya ƙare ba kuma cikin Ƴaƴansa babu mai ɗaukowa a ɓangarensu ya kawo mata, basu iya kawo mata komai ba amma sun iya suzo su cinye mata duk abinda aka ajiye mata.
Bata dawo parlo ba sai da tayi sallar walha, tana zuwa ta tarar da Yusrah ta shigo, ta bita da kallon sama da ƙasa ta ƙarasa bakin ƙofar ta jawo ta rufe tana faɗin,"kamin na huɗu ya shigo, ba dan ba dan ba sai nace Amadu gidan taron jama'a ya buɗe min".
Ta murza key tana mitar,"kai da ɓangarenka amma ba za'a barka ka huta ba". Sannan ta saƙala key jikin abin maƙale labule tana cewa da su. "idan zaku fita ga key ɗin anan, idan zaku fita nace ba wai idan kunji knocking ba".
Cikinsu babu wanda ya tankawa maganar da ta ke, dan haushi kamar ta rufe su da duka. ta kallesu su duka tace,"Amadu kuka share bani ba". Sannan ta juya ta koma ɗakinta.
Yusrah ta zauna kan kujerar da Inna Wuro ta tashi, ta buɗe jakarta ta ɗauko office pins tare da madubi, ta shiga
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 73