Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya matsa kusa da makarar, Baffa ya kalle shi, zuwa yanzu idanuwansa ƙamas babu alamun danshi na hawaye, haka fuskarsa tayi fayau babu wani abu da zaka tsinta a ciki illa tsananin tashin hankalin da yake ciki. haka shi ma Khaleel, wanda tun ɗa zu sai ayanzu da ya ɗora hannunsa akan makarar sannan hawaye yay nasarar gangaro masa, sai dai yay saurin saka gefen rigarsa ya goge. hannun Turaki ya shiga cikin maƙarar, ya tallafo kan gawar, yasa ɗaya hannun ya yaye linkafanin ya tsayar da shi daidai wuyanta, inda fuskarta kawai suke iya gani, fuskar da suke gani tamkar zata yi musu magana. muryarsa ta fito cikin sanyi, ya shiga jero tarin adu'oin da ya san su na cikin kansa, yi yake yi yana ƙara maimaitawa, har tsawon lokacin da bai san ya ɗauka ba me tsayi, har sai da Baba Nafi'u yasa hannu ya dafa kafaɗarsa yace,"ya isa haka Turaki". shi kaɗai ne ya iya yi masa magana domin ko Baffa ba zai iya ba a wannan lokacin, shi kansa ya kifa kansa yana hawaye kamar yanda Hajiya Ramla da ƴaƴan suke yi. "ke kam taki tayi kyau Madina, tabbas ke ɗin ƴar aljannah ce, ki yafe min Madina, don Allah don Annabi ki yafe min". muryar Boɗejo suka ji ta amsa acikin ɗakin, a sanda take isowa wajen, kuma kukan da yaci ƙarfin ya hanata ƙarasa abun da zata faɗa. har aka yi sallar jana'iza Turaki da Khalil basa cikin hayyacinsu sosai, a tsaye kawai suke, hannayensu sarƙe dana juna, yayin da idanunsu ke kafe akan makarar da ke ɗauke da gawar dake gabansu. da ga bayan su kuma tarin ɗumbin jama'ar da ba zasu ƙirgu ba ne, don jama'ar gari yara da manya sun halarci jana'izar. ƙarfe shida na yamma aka kai Hajiya Madina ƙabarinta, inda ɗumin jama'ar da suka fi ƙarfin ƙirga suka yi mata rakiya zuwa gidanta na gaskiya. acikin shirun da ya ratsa maƙabarta, babu sautin muryar da kake ji na tashi sai na manyan mutanen dake cewa. "yauwa bismillah ku biyo ta nan". "yauwa jama'a a ɗan gyara". "ku riƙeta sosai". "to ku miƙota nan". "yauwa to ku ajiyeta nan, masha'Allahu!". mutanen da suka ratso ɗauke da gawar ta cikin tarin ƙaburburan dake jere a cikin maƙabartar. suka ajiye makarar a bakin ƙasar da aka tone, kusa da ramin da yake gida matabacci, kuma gida na ƙarshe ga kowanne bawa, gidan da ke jiran duk wani mai rai, gidan da yake iri ɗaya da na me kuɗi dana talaka. Turaki da Khalil na tsaye kusa da juna, tsayinsu kusan ɗaya, zuciyar kowanne na tunani kala-kala a game da mutuwar da ta riske su a yau. abun da basu taɓa zato ba, abun ba su taɓa kawo shi nan kusa ba, mutuwar ma da gaba ɗaya basa hasashenta. "Bismillah". Muryar limamin masallacin unguwar ta janyo Turaki da Khalil daga dogon tunanin da ƙwaƙwalwar su ta faɗa, suka juyo a tare suka kalle shi, sannan suka kalli gawar dake gabansu, wadda aka fito da ita daga cikin makara, a lokaci ɗaya suka tsinci kansu da tarin ruwan hawayen da ya bar idon su tun ɗazu. a hankali Turaki ya durƙusa daidai kan gawar ya tallafo kan, Khalil da Samir da Baffa da Wan Hajiya Madina da Liman suka tallafi sauran jikin, sannan suka haɗu wajen zura gawar a cikin ramin ƙabarin. lokacin da suka zura gawar acikin rabin ƙabarin, zuciyar kowannen bawa dake wurin ta matse da ƙarfin imanin dake ƙaruwar a ƙirjinsa, tabbas duk wanda bai yarda da Ubangiji ba yayi asara, asara mai girma kuwa, haka duk wanda bai tuba ba kafin mutuwa tabbas yay babbar asara. idanuwan Turaki suka tsaya cak akan farin likkafanin, yana kallon yacca ake mayar da ƙasar da aka haƙe ana rufe gawar gawar da ke ciki, har sai da hasken likƙafinin ya dusashe, yayin da tukwane da tudun jar ƙasa suka shafe shi gaba ɗaya. daga wannan lokacin kuma ƙwaƙwalwarsa bata ƙara wani tunani ba, komai da ke cikin kansa ya zame yabar shi. abin da zai ce yana iya jiyowa a duniyar da yake jinsa kamar ba'a cikinta ba, tarin adu'oin dake fitowa daga bakin liman, kafin a hankali kuma ya fara jin sautin wani abu na shiga kunnensa, sautin takun ƙafafu su na juyawa su na barin wajen. sai ya kalli nasa ƙafafun, sai yake ganin tamkar ba zai iya ɗaga su ba, tamkar sun ƙame anan kenan har sanda tasa mutuwar zata zo ta riske shi. yaji an riƙo hannunsa, da ƙyar ya iya ɗauke idonsa akan ƙabarin, ya juya ya kalli Baffa da Khalil, kafin ya ɗaga ƙafarsa a hankali ya fara tafiya da baya, a haka ya dinƙa tafiya da baya har ya bar cikin maƙwabartar, yana tafiya yana barin Hajiya Madina, yana kusantar gidan da zai koma a yau rana ta farko ya riske bata cikinsa, rana ta farko da zai koma bai ji muryarta ba na kiransa da wannan sunan da ita kaɗai ta raɗa masa, kuma ita ɗaya take kiransa da shi, Me Babban Suna!. yaji wani uban gumi ya keto masa, ya wanke masa dukkan ilahirin jikinsa, a hankali kuma ƙwaƙwalwarsa ta karanto masa kalmar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. shikenan sun yi tazara, tazarar da ba zasu ƙara kusantar junansu ba. a lokacin da suka koma gida, tsakanin Khaleel da Turaki sai aka rasa wanda ya riga wani shiga ɗakin Hajiya Madina, an dai gansu sun shigo sun tsallake tarin mutanen dake zazzaune. a cikin ɗakin na Hajiya Madina, Khalil na zaune a ƙasa, idonsa na manne akan gadon inda tayi baccin ƙarshe a duniyarta, yau rana ta farko da ya shigo ɗakin bai ganta ba kuma ko da ya zauna zaman jiranta ba zata shigo ba, shikenan ta tafi tafiya ta har abada, sun zama marayu, yanzu ba su da uwa, wannan jigon na jin daɗin duniya. a hankali yaji hawaye na sauka akan kumtunsa, masu ɗumi da yawan da yaji kamar an buɗe bakin famfo, kukan da bai yi ba tun a ɗazu shi ya taho a yanzu, kawai sai ya ajiye dukkan dauriyarsa, yay ƙasa da kansa, ya runtse idonsa da yake ganin hoton mahaifiyar tasa na haska masa, don haka saiya shiga rero kuka babu ƙaƙƙautawa, kuka tamkar ƙaramin yaro. a wannan lokacin kuwa Turaki ya kifa kansa akan gadon, ƙamshin Maamansa na fitowa daga kan gadon na ziyartar hancinsa, yayin da yake damƙe da wannan ƙaton zanin da take cewa zanin goyon jikanta ne. _"kwana ashirin da biyu ya rage Edd ɗin nata ya cika ko?, to Allah ya raba su lafiya. kaga Me Babban suna waɗan su gadaje na jarirai na gani da suka fi wanda na siyo kyau, mu sauya shi ko?"._ maganartata ta haska acikin kansa, shekaran jiya suka raba rana su na hira da ita, kuma yawancin hirar duk akan jikokin da taƙe ta burin ganin zuwan su ne, har daga ƙarshe ma take ce masa. _"to ni ina ta lissafina ma, wa ya sani ko ba lallai ba ne na kai wannan lokacin, Allah dai ya san adadin shekarun da ya ɗiba mana a rayuwa, ni dai idan na tafi ku yafe ni Me Babban Suna ko da nayi muku laifi bisa kuskure"._ sai kawai yaji ya rasa dukkan dauriyarsa, ya manta shekarunsa, yana tunawa cewar shi fa ɗan Maamansa ne, kuma Maaman ta rasu a yau, bai san lokacin da wani matsanancin kuka ya kubce masa ba, ya shiga rero shi tamkar yaro sai dai gaba ɗaya babu sauti, illa tarin ruwan hawayensa da ke sauka su na jiƙa bedsheet ɗin. har aka tura ƙofar ɗakin aka shigo tsakanin Turaki da Khalil babu wanda ya sani balle ya ɗago. Fillo ta ƙarasa ta zauna akan gadon, tana zama kuma Turaki ya ɗago kansa ya ɗora akan ƙafafunta, ya damƙe cinyoyinta yana wani irin girgiza. sai taji sabon kuka yazo mata, tunawa da tayi Nihal na can an rirriƙeta sai surutai take yi. saboda haka sai ta nutsa yatsunta acikin kansa tana motsa yatsun. *BAYAN SATI BIYU.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *60* *Jarabawa daga Mahaliccin mu.* Rayuwa tana cike da nasara da kuma faɗuwa, kuma akwai lokutan da gwaje-gwajen da ake yi mana kamar ba za su ƙare ba. A cikin Alkur’ani me girma, akwai ayoyi da dama da Allah ya yi magana a kan hanyoyi daban-daban da za a gwada mu, amma kuma ya ba mu ƙunshin kulawa da zai taimaka mana mu bibiyi waɗannan lokutan masu wahala a gare mu. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce:“Babu wata musiba da za ta samu musulmi face Allah ya kankare masa wani abu daga cikin zunuban shi, ko da kuwa tsinuwar ƙaya ce”. (Bukhari Wa Muslim). haƙiƙa jarabawa ba azaba ba ce daga Allah, tana daga cikin rahamarsa marar iyaka. Musulmi ko wanda ba Musulmi ba, babu makawa kowannen mu yana fuskantar jarabawa a rayuwarsa. Rayuwa ba gadon wardi bane ga kowa, Akwai mutanen da ke fama da talauci, akwai masu fama da lafiyarsu, sannan akwai masu fama da danginsu, akwai masu fama da mutuwa a jere a jere. Jarabawar ubangiji ta bambanta ga ɗaiɗaikun mutane daban-daban, an yi su ne bisa la'akari da irin ƙarfinmu da rauninmu. Abubuwan da suka zama kamar gwaji a gare ni, wataƙila ba za su dame ku ba, nima akasin hakan. tambayar gama gari da kowa ke yi a lokacin da ya shiga wani hali shi ne; me ya sa Allah ya sa na shiga cikin wannan halin? Me ya sa ba zan iya zama mai farin ciki a ko yaushe ba?, Menene na yi don cancantar wannan jarabawar? Me yasa Allah ya jarraba ni?. kuma rashin sanin amsar waɗan nan tambayoyi wani lokacin yana iya nisanta mutum daga imaninsa. jarrabawa na iya haifar da mummunan tunani mai tayar da hankali wajen mutum ya aikata saɓo, kamar faɗin Allah ba ya so na!. ko ma mafi muni mutum yace Allah ba ya yi mini adalci(astagfrullah). Amma Allah shi ne Al-Adl, Mai adalci, kuma shi ne Ar-Rahman, Mai jin ƙai, wanda ba ya ya nufin cutarwa ga bayinsa, face yana son alheri a gare mu. Akwai hikima a yanayin da ya ke sa mu a ciki, duk abin da muke buƙata mu yi shi ne haƙuri. Akwai dalilai da yawa a cikin Alqur’ani da hadisi da suke taimaka mana wajen amsa tambayar dalilin da ya sa ake jarraba mu. An halicce mu ne domin mu bautawa Allah, wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da yasa ake jarabtar mu. tabbas an halicce mu ne domin mu bautawa Allah, kuma dukkanmu mun yi alƙawarin yin haka kafin a aiko mu a duniyar. Jarabawa hanya ce a gare mu don cika wannan alƙawarin. jarrabawa ita ce hanyar da Allah ya ke bambanta mu, domin tana taimakawa wajen bayyanar da imani da rashin imani. Allah yana jarrabar mu, ya tsarkakemu ya kuma wanke mana zunubai. jarabawa gwaji ce ta maye gurbin wani mummunan bala'in, tabbas da munsan musibun da Allah yake kare mu, da ba za mu taɓa rasa sallah ba, kuma ba za mu taɓa son ɗauke goshin mu daga sujjada ba. Gwaje-gwajen da ke ɓata mana rai na iya zama nau'i na kariya daga wani abu mafi muni da wataƙila ya same mu. Allah yana so ya tsarkake mu, daga soyayyarsa da rahamarsa, domin mu samu ba Aljanna kaɗai ba, har ma da mafi girman darajar Annabawa da salihai. Gwaje-gwaje su na fallasa kurakuran mu da kasawarmu, kuma sanin hakan yana ba mu damar mai da hankali da himma wajen gyara waɗannan ɓangarori na halayenmu. Allah yana jarrabar wanda yake so. Annabi(SAW) yana cewa: "Duk lokacin da Allah ya nufi mutum da alheri, sai ya sanya shi cikin tsanani".[Bukhari]. me yasa?, domin idan bawan ya amsa jarabawarsa da haƙuri, da gamsuwa da hukuncin ubangiji, hakan yana kusantar da bawa zuwa ga Allah, Kuma Allah yana son masu haƙuri. Ibn Al-Qayyim (rahimahullah) ya ce idan aka yi mana jarrabawa, muna fuskantar zaɓi guda biyu; muyi haƙuri ba rashin haƙuri ba. muke sauraren Alqur'ani da yawaita ambaton Allah saboda wadatar zuci, domin karanta alƙur'ani yana ba da wadar zuciya, addu'a don neman taimakon Allah, da ƙarfinsa, da samun sauƙi daga jarrabawa. mu tunatar da kanmu jarrabawar da Annabawa suka yi, sun ba mu kyawawan misalai na juriya. mu tuna cewa kowanne mutum guda ana gwada shi ta hanyoyi daban-daban. mu tuna babu wani abu a cikin wannan rayuwar da ke dawwama, don haka jarrabawar za ta ƙare insha Allah. domin ko acikin alƙur'ani Allah yace,"Lallai ne tare da kowane wahala akwai sauƙi". ubangiji ba ya ɗaurawa wani rai face abin da zai iya ɗauka, Allah ya amince da mu, don haka mu ma muna buƙatar mu amince da iyawarmu ta cin jarabawa. Allah yasa mu da ce!. ƙarfe goma na safe a lokacin, Ilham ta fito daga ɓangarenta tare da wata yarinya da ba zata wuce shekara 8 ba. yarinyar ƙanwar Fulani Azima ce, aka bata ita kafin akaita makaranta, kasancewa yarinyar ta gama primary a halin yanzu. yarinyar na riƙe ne da jakar Ilham, tabi bayanta zuwa baƙar motar da taga ta shiga, sabuwar motar da me martaba ya bata kyautarta. a san da suka iso bakin gate domin fita, a sannan ne Fillo ke baro wajen Baba Me gadi da turtsetsen cikinta, da lokacin haihuwarsa kawai ake jira. Ilham ta zuge glass su na gaisawa da Fillo, da siririyar dariya a fuskarta tace da ita,"kin ga kuwa yacca kika koma?, Allah each and every day cikin nan kumbura ki yake ƙara yi". Fillo na kallonta tace,"ban da sharri dai". "Allah babu zancen sharri, jiya da muka ci dinner ba ki kumbura haka ba". Fillo tayi murmushi ta ce,"in ace ana mayar da cikin jikin wani ai ke zan mayarwa, ke ma ki ɗanɗana, ko da yake kwana nawa ne Allah na tuba, ina daga balcony zan ke hango ki a field kina aikin patrol". Ilham tayi dariya sosai tare da cewa,"Allah dai ya raba lafiya, ni ban ma fidda ran ba za ki haihu ba a yau". sai kuma ta nunfasa ta ce,"zan je gida ne, an yi min waya jikin Mami ya ƙara tashi". jikin Fillo yay sanyi tana me tunawa da halin da suka riski Fulani Azima a shekaranjiya da suka je dubata. cikin sanyin murya tace,"Allah ubangiji ya bata lafiya, ko in je in shiryo mu tafi tare?". "a'a ke da kike fama da kan ki, na faɗa miki bana fidda ran ba za ki haihu ba a yau, ƙila ma sai dai ai min waya ace Baby ya sauka. ɗa zu da asuba ai ina tayi miki dariya ta window". Fillo ma tayi dariyar ta ce,"hmmm aikin mijinki ne, haka kawai duk ya jigatar da ni da safa da marwa, ke kinji yanda ƙafafuna ke ciwo kuwa. ai ana kaiwa gobe sai dai kuga na kai kaina asibiti sun yanka ni sun ciro muku yaran ku". "da kanki ma za ki haihu insha'Allah, bari na tafi sai na dawo". "to a dawo lafiya, ki yiwa Mamin sannu don Allah". motar Ilham ta bar compound ɗin gidan, ita kuma Fillo ta shige part ɗin ta. a ɗaki ta sami Turaki zaune yana rubutu a takarda, tun safe yake aikin rubuce rubucen office, tayi wurgi da hijab ɗin jikinta akan gado, kafin ta nemi waje ta zauna ta miƙe ƙafafu. "Jannaty please come and massage my legs, Allah ciwo suke min sosai". ya ɗago ya ɗora idanuwansa akanta, matuƙar tausayinta ya kama shi, in ace yana da ikon da zai fito mata da Babies ɗin nan babu abin da zai yi masa shamaki da hakan, ya ƙagu ta haihu haka ko don ta huta. ya tattara takardun a gefe tukunna ya taso, kafin ya zauna a gabanta ta dakatar da shi da faɗin,"sorry ba ni riyon kayan su Maama". ya ce,"me kuma za kiyi da shi?". tayi masa wani kallo kafin tace,"kaji min mutum, me ake yi da gyara?, yau tun tashina ban gyara musu ba". sai yay zamansa kawai, ta ɓata rai tana faɗin,"zan yi maka kuka". ta faɗa a shagwaɓe. ya ɗago ido ya kalleta, sarai ya san zata aikata hakan, don haka ya miƙe yaje ya ɗauko ƙaton riyon da ke ɗauke da uban kayan Babies a ciki, ya ajiye zai zauna ta ƙara dakatar da shi. "diary ɗi na". ya rufe ido tare da karyar da kai, zai yi magana tayi kalar tausayi tana haɗa hannayenta ta ce,"yi haƙuri Baban Ƴan biyu, ai don Allah nace". sai da ya lakuce mata kumatu kafin ya fita ya bar ɗakinsa zuwa nata ɗakin, san da ya dawo tana waya da Boɗejo wacca ta kira tana tambayar lafiyar jikin nata. ya zauna kawai ya shiga matsa mata ƙafafun, yana tsokanarta da lukutar gombe, bayan sun gama wayar da Boɗejo ta harare shi tare da fizgar diary ɗin tace,"ka duba min sirrina ko?". "oho ke kika sani, ni me zan duba acikin diary ɗin da ake ɓoyewa kamar ana ƙulla munafurci a cikinsa, to ta ina ma zan iya gane watsaltsalun rubutun lukutar Gombe?, rubutun da ba iyawa aka yi ba". dariya tasa Fillo dakatawa daga rubutun data fara,"oho dai duk abin mutum ba zai ga me ke ciki ba, ah tou! sirin mu ne ni da ƴaƴana" "sirri ko munafurci?, yara tun basu zo duniya ba an fara koya musu hali mara kyau, ni dai gaskiya nake faɗa miki ki sauya hali, wannan ba halin zama mother ba ne". ta ƙara yin dariya,"magana ce bata isheka ba sarkin ƴan sa ido, sirrin uwa da ƴaƴa ne dai ba zaka gani ba". ta faɗa tana yi masa gwalo, sai ya sakar mata ƙafa suka shiga kokawa akan sai ya karɓi diary ɗin, ta ƙwalla ƙara babu shiri ya ƙyaleta yana aikin zaro ido da jera mata tambayoyi a hargitse. "menene ya faru Angel?, na bige miki wani wajen ne?". ta kashe masa ido ɗaya da cewa,"kasan idan baka daina takura min ba zan kaiwa Ilham jinginar ka, ka kwana dubu saba'in baka ganni ba". "Allah ya baki haƙuri yallaɓiya ranki shi daɗe me girma uwar gida, da ki hora ni da rashin ganinki ai gwara ki zane min ɗuwawu na kasa zama, rashin ganinki ai azaba ne a gare ni". "idan na mutu fa?". sai ya ɗago yana kallon fuskarta da ta ƙara kyau yace,"ban hana ki yi min zancen mutuwa akan ki ba". "Allah ya baka haƙuri ranka ya daɗe". ta faɗa da murmushi a fuskarta. bayan ta gama gyaran kayan Babies ɗin take ba shi labarin irin satar kayan da akayi ranar zaman sadaƙar bakwai ɗin Hajiya Madina. "Daddyn Maama ka san me?, ina sabon less ɗin dana ɗauki zaninsa nace za'a ɗinkawa little Maama riga da shi?, to wallahi har da shi aka ɗauke, daga in ɗauko in ajiye kan gadon Mum in shiga toilet, ai kuwa na jera Allah ya isa babu adadi, saboda les ɗin nan Maama na sonsa". yace,"Allah ya kyauta, rashin tsoron Allah ne duk yake saka sata a gidan mutuwa, Allah ya shirya masu yi kawai". ta amsa da amin kafin ya kamata ta yunƙura su miƙe tare, toilet suka shiga domin yin wanka, acikin banɗakin sai da aka ɓata tsawon awa guda ana shan soyayya, sannan suka fito su na dariya, ita tana faɗin idan ya ɗauketa a yanda take yanzu ƙasusuwansa duk sai sun ɓalle, yayin da shi kuma ke faɗin ya sani, hannun lukutar gombe tsaf zai ɓalla shi ya ɓalle gaba ɗayansa.. kamar kullum yauma suka shirya kansu, ita ta saka wata ƙatuwar bubu da ta ɗauka acikin kayan Maama, kuma rigar sai tayi mata kyau sosai, saboda girman cikin jikinta sai awon yayi daidai da ita. "amma dai ba zaka jima ba ko?". amon muryarta ya fito a lokacin da take ɓalle masa maɓallin rigarsa. ya ce,"No yanzu zan dawo babu jimawa, takardun nan kawai zan kaiwa Khaleel, don't be lonely, am always with you, ina cikin nan". ya faɗa yana pointing saitin zuciyarta. tayi wani kalar murmushi tana kamo fuskarsa cikin tafukan hannunta biyu ta ce,"ina sonka mijina, ina ƙaunarka". "ni ma ina yi miki tsananin so matata, Allah yayi miki albarka, yasa ki haihu da ranki da lafiyarki". "amin amin Daddyn little Maama". furuncin nata ya saka shi yin murmushi me faɗi, tare da duƙawa ya ɗage rigar jikinta ya yiwa cikin kiss, sannan ya ɗago suka yi kissing juna. da ƙyar ya iya sakinta yaje yana tattara takardun cikin sauri, ita kuma tana bashi labarin cewa,"Jannaty ka san me?". ba tare da ya juyo ba yace,"ban san me ba sai dai june". murmushin tayi sannan yace,"to ka san june?, tunda nake a rayuwarta ban taɓa hango kaina a matsayin uwa ba, ban taɓa tunanin zan ɗauki ciki ba balle har akai lokacin da zan haife shi". sai tayi shiru, yace,"ehen ina jinki lukutar Gombe". murmushi ya kasa ɗaukewa a saman fuskarta, tana kallon bayansa ta ƙara cewa,"sai ga shi Allah ya ƙadarta min ganin samun cikin, har zuwa watan haihuwarsa, zan haife ƴaƴa biyun da nagartaccen mijina ya bani su, na ƙagu in haife su Jannaty, ina tsananin son su fiye da kaina". cikin sigar zolaya yace,"har ni kin fi son su akaina?". ta ɗan taɓe baki tana kallonsa, da irin wasan da ke tsakanin mata da miji tace,"waye kai?". ya ƙaraso ya zauna kusa da ita ya mintsinin leɓenta, ya ɗora hannunsa a saman nata dake kan cikin. "yau kin ji sun juya?". ta ɗaga masa rigar tana faɗin,"kalla fa yanda suke ta ƙiriniya, duk sai duka suke kai min ta ko'ina, suma ai sun gaji da zaman". Turaki bai iya cewa komai ba illa shiru da yayi yana ta kallon cikin dake motsi, yana jinjinawa girman ƙudirar ubangiji. gaba ɗaya sai yake jin tamkar yasa hannu ya buɗe cikin ya ɗauko yaran, Fillo kuwa kallon cikin kawai take yi a gefe guda zuciyarta na saƙe-saƙen yacca rayuwar zata juya, yanda komai zai koma saɓanin tunanin su da hasashen su, yacca komai zai faru anan gaba kaɗan, nan da ɗan lokaci kaɗan ba me yawa ba, hakan take taji a jikinta. "ba fa na so yarana su yi kama da mijin lukutar gombe saboda bana so su yi muni, ka daina kalle min su". ya rungumota jikinsa yana cewa,"wallah ki roƙi Allah su yi kama da ni kiga yanda za'a dinƙa miki layi a ƙofar gida, in kuwa su kai kama da ke to kin shige su, ƙila sai dai mu ke kulle su a store". bayan fitarsa ta zauna a gefen gado, ta rufe idanuwanta a hankali, yayin da hannayenta ke ɗore akan ƙaton cikinta, ita ɗaya ke ta saƙawa wai yanzu halitta ce a cikin cikinta, halittar da ya girma kuma zai fito nan ba da jimawa ba, shikenan da zarar sun fito ita ma ta samu nata babies ɗin, irin wanda take gani daga nesa don bata iya ɗaukar jariri, za su fito a matsayin nata, yayin da zata amsa wannan sunan mafi daraja na Uwa, ƴaƴan su ita da Turaki, Ƴaƴan su ikon su. sai taji ƙwalla na neman taruwa a cikin idonta, ƙwallar da take ta zallar farin ciki da wani bala'in jin daɗin da ba zai misaltu ba. ta lumshe idanunta, ƙwaƙwalwarta na haska mata hoton yaran acikin kanta, ana jibi Hajiya Madina zata rasu ana scaning sai taji tamkar ta ɗauko su a wannan lokacin, babies ɗin su na kwance a cikinta gwanin sha'awa, ga sunan clearly a jikin screen cikin hoton black and white, kansu a haɗe su na ta watsal-watsal yayin da hannun kowanne ke gefen bakinsa, idanunsu a buɗe tarr tamkar kayi musu magana su amsa maka. kawai sai ta fara hasko yanda kammanin babies ɗin zai kasance, bata san ya Allah ya tsara halittar kamannin nasu ba, wataƙila su yi kama da su, wataƙila kuma su ɗauko kamannin su daban, sai dai a son samunta duk su ɗauko kamannin Turaki, ta yan da zata dinƙa kallonsa a fuskarsu idan baya gida, ba ya ga hakama idan suka ɗauko kamanninsa zasu fi kyau, irin wannan kyan da sai ta dinga tofe su da adu'a a kaɗawar kowanne sakan na agogo. tashi tayi akan gadon, ta isa gaban dressing mirror ta ɗauko diary ɗinta, sannan ta duƙa ta ɗauki riyon kayan babies, ta fita a ɗakin Turaki ta isa zuwa nata. wadrobe ta buɗe ta ɗauko wasu set ɗin kayan sanyi da Hajiya Ramla tayo mata aiken su a jiya, sannan ta fita ta nufi ɗakin kusa da na Turaki, ɗakin da suka ware domin yaran su, ɗakin da Turaki ya rufe mata ido ya shigar da ita sannan ya buɗe yana nuna mata yana faɗin for our coming kids. ɗakin tamkar already dama yara na rayuwa acikinsa, domin anyi decorating ɗinsa da duk wasu kayan wasan yara, komai na cikinsa pink and white, kayayyakin da almost siyayyar Marigayiya Hajiya Madina ne, sai ta isa gaban gadajen guda biyu, a wannan lokacin babu

Chapter 69 of 73