Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Baffa yana nan kawai ake amfani da su. ta buɗe ƙaramin coolern taga irish ne da miyar hanta da soyayyan ƙwai, ƙamshin ya ziyarci hancinta har sai da ta lumshe ido, ai ko bata jin yunwa sai taci balle kuma uwar yunwa na ƙwazafarta a ciki, mamakinta ɗaya ne da yaushe aka kawo abincin?, zuciyarta ta faɗa mata tana can tana bacci. ta ɗauko plate ta fara zuba abinci sai taji ana knocking, adu'arta ɗaya ne a lokacin Allah yasa su Dadda ne suka zo, ta miƙe da sauri taje ta buɗe door sannan ta zuge glass, idanuwanta suka sauka akan Bello da ke tsaye hannunsa ɗaya a aljihu ɗaya kuma yana maƙale da waya a kunnensa. taja da ba ya tana ba shi hanya tare da yi masa sannu da zuwa, ya shigo yayin da yake amsawa, ya wuce ya zauna kan kujera ita kuma ta durƙusa har ƙasa ta gaida shi, ya amsa ya ɗan kallonta da son fahimtar wani abu, sai dai ya gagara fahimtar komai ɗin. tana tsugune tana jan yatsun hannunta har wucewar daƙiƙa biyu sannan ya kalleta ya girgiza kai ya ce,"MT bai ta shi ba ne?". tai ɗan jimm tana nazari, kamar ta ce bai tashi ba kamar kuma ta ce masa ya fita, a wannan shirun na ta Bello ya samu amsar tambayarsa, tausayin yarinya ya kama shi, a irin hallacin da tayi masa sam sam ba ta kamaci wani abu wulaƙanci a wurin Turaki ba balle tozarci, dan babu tozararci irin sakin da ya yi mata tana ƙarama da ita, ya miƙe yana cewa da ita,"idan ya dawo kice masa nazo, ina ta kiran wayarsa bata shiga ya yi ƙoƙarin kirana". ta amsa da,"toh". sannan ta ce,"ba ka sha ruwa ba, ga tea zan kawo maka". bai kalleta ba amma yanda voice ɗin ta ya fito ya tabbatar ruwan hawaye sun cika idanuwanta, kuma so ta ke ta zubar da su, ya sauke numfashi ya koma ya zauna tare da cewa,"oak kawo min tea kawai, kisa nescafe idan ba takurawa". ba wai yana yin yunwa ba ne, a'a kawai ba zai iya ƙin tayan da tayi masa ba, dan sosai shi dai yake bala'in tausayinta. ta wuce cikin sauri ta ɗau mug anan kan ƙaton family dining table ɗin, ta cika shi da ruwan tea sannan ta ɗauki plate ɗin da ta zuba irish da miyar hanta taje ta kai masa, shi ya tayata janyo center table gabansa dan yaga kamar mug da plate ɗin da ke hannunta su na neman rinjiyar waɗannan sillan karan hannayen nata, kar yaje ata dalilinsa ƙashin yar mutane ya karye. ta na kallon carpet ta ce masa,"nescafe ɗin ne dai babu sai na bayar an siyo, kuma mai gadi ya fita bai dawo ba". da mamaki Bello ya ce,"sai an siyo?". ta ɗaga masa kai kawai tana sa hannu ta goge hawayenta. yay ta kallonta da mugun tausayinta ya ce,"kuma kin duba ko'ina a kitchen ɗin babu?". ta yi shiru, sai taji ya ƙara cewa,"tsaya tukunna!, faɗa min gaskiya kar ki ɓoye min komai, ke ɗaya kika kwana a nan ko?". da sauri ta girgiza kanta alamar a'a. yay guntun murmushi na takaici ya ce,"karki rufawa MT asiri, ɗan banza ne bai da hankali ko kaɗan, tunaninsa ba irin na mutane ba ne, gwara ma ki fayyace min komai dan ko kin ɓoye min shi ba zai ɓoye min ba. ki faɗan gaskiyar amsar tambayar da nayi miki". hawaye su ka ƙara zubo ma ta bata ce da shi komai ba, a wannan hawayen ya karanto duk wata amsar tambaya da yake son yi ma ta. ya sosa girarsa yana tunanin ta yacca zai shawo kan wannan lamarin, tun jiya yake tunanin ta yan da zai yi convincing Turaki akan ya mayar da aurensu, shikenan su zauna lafiya salin alin babu wanda ya san anyi, to amma ya san shegiyar gardama da rashin ɗaukar shawara irin tasa ba lallai ya amince ba, shi abun da yake gudu ma kar silar zaman nata a gidan azo a aikata kwaɓa, yay guntun tsoki ya ƙara trying lambar Turaki amma bai samu ba. ya ce da ita,"ƙofar tsakiyar nan anan kitchen ya ke, ki kawo min nescafe ɗin". sai ta juya tana kallon ƙofar da ta buɗe ta shiga ɗa zu har tafi ƙarfin minti uku tsaye aciki, ta ƙara juyo da kanta gare shi ta ce,"babu ai kitchen ɗa zu duk na duba". yay gajeran murmushi ya ce,"ai na za ki dinƙa girki idan babu kitchen?, ko kin taɓa ganin gida babu kitchen?". ta ce,"a'a ƙila haɗe mana ya yi da ita, anjima na ke son zuwa part ɗin nata". Bello ya kaɗa kai,"kina uwar gidan zai tafi bangaren wata ya yi kitchen?, to ba haka ba ne, kowaccenku da nata kitchen ɗin, duba in da na faɗa miki". ba ta iya jayayya da Babba ba, amma ita ta san babu wani kitchen, ta tashi taje ta buɗe parlon, yana ta kallonta a san da ta shiga ta tsaya da ga bakin ƙofar, yay smiling ya ce ta buɗe ƙofar ciki, ta ƙarasa shiga ciki ta isa wa ta ƙofa da ta gani ta buɗe, jimawa kaɗan sai gata ta dawo riƙe da ƙaton gwangwani na nescafe, ta ajiye masa ta koma dining ta zauna, yana shan ruwan tea ɗin yana ɗan janta da hira sama-sama, har da tsokanarta wai an bata award na amaryar da tafi kowacce amarya kyau tun da aka fara aure a nigeria. ita dai murmushi kawai take yi, kuma sai taji hirar tasa na yi mata daɗi musamman da yana bata labarin yarintarsu, irin yanda suke faɗa akai akai kamar ƴan tsaki, da yacca Baffa ke cin ƙaniyarsu, har ya ce yana basu purnishment ɗin yin dariya da haƙori ɗaya ko su ciji hancinsu in ba haka ba a dafa su a bawa mage ta cinye, sai suyi ta kuka su na bada haƙori in Baffa yaƙi haƙura sai su ɓuya a lambu, sun sha kwana acan yafi a ƙirga saboda basa son faɗan Baffa da dukansa ko kaɗan. sai ta sami kanta da yin dariya sosai, sai da ya ɗeba ma ta kewa tukunna yay ma ta sallama ya tafi, bayan tafiyar tasa duk sai taji babu daɗi, ta dawo ta koma upstairs tai kwanta zuciyarta cike da son ganinta a gida, yanzu ta san su Dadda sun ɗau hanya, tana ta so ta yi waya da Umminta taji muryarta, tun da ta tashi take mugun kewarta. ban da tunane tunane babu abin da takeyi har ƙarfe goma, sai lokacin ta tuna da aiken da ta bawa Baba, hakan yasa tayi saurin saukowa ta fita, tana fitowar kuwa ta tarar da Baba me gadi yana isowa entrance na ɓangarenta, ta tafi da sauri dan karɓar masa kayan, sai dai kamin ta ƙarasa Turaki ya rigata, ta ƙaraso wajen Baban a sanda Turaki ke miƙa masa hannu alama na ya ba shi kayan ba tare da ya ce masa komai ba. Fillo ta haɗe rai kamar ba ita ba, ko kallon in da inuwarsa take bata yi balle kuma shi kansa, tana yiwa Baba sannu da zuwa ta miƙa hannu za ta karɓi kayan taji saukar muryar Turaki a tsakiyar kanta. "idan har kayan nan suka je hannunta, to ka nemi wani gidan ka ci gaba da aikinka". ta dakata da karɓar ledar tana kallon hannun Baba da ke aikin karkarwa, taji mugun tausayinsa ya kamata, tana kallo ya kalleta fuskarsa nayi ma ta nuni da tayi haƙuri ta rufa masa asiri, ta gyaɗa kanta kawai shi kuma ya bawa Turaki ledojin, ya karɓa ya juya ya bar wajen, itama zata bar wajen Baban ya ce,"Hajiya ga canjin ki". ta waigo tana yi masa murmushi ta ce,"ka riƙe Baba". ya waro ido waje yana cewa,"dubu biyar ce fa Hajiya". ta ce,"babu komai Baba". ta faɗa tana barin wajen tare da goge ƙwallar idonta, shi kuma ya bita da kallo yana ta zazzaga ma ta adu'a yana sa ma ta albarka. kai tsaye parking lot ta nufa in da ta ke hango Turaki a wajen motarsa ya buɗe ya shiga ƙafarsa ɗaya a waje, ya ajiye ledar kayan da ya amsa, ɗaya a ƙasa ɗaya a saman murfin booth, ta ƙarasa wajen motar cikin sanɗa ta durƙusa ta kwashi kayanta, ta yi saurin barin wajen kamar za ta kifa ƙasa, fatanta ɗaya ta isa har ƙofar part ɗin ta bai fito da ga cikin motar ba, abin da ba ta sa ni ba shi ne, tana ɗaukar kayan ta juya shi kuma ya fito da ga cikin motar, mamakin ƙarfin hali irin na ta shi ya tsayar da shi kawai yana bin bayanta da kallo, ya kasa yi ma ta magana balle ya cimmata ya karɓe, shi kallon ma da yake yi ma ta tun jiya kamar da akwai abin da takala. ya jijjiga kansa, koma me take ji da shi zai saitata ne within wani ɗan lokaci. bayan sallar azahar tana zaune kan darduma ta zabga uban tagumi sai taji kamar hayaniya a compound, ta miƙe da azama ta leƙa ta window sai taga su Adda Asma'u ne, ai kuwa babu shiri ta wancakalar da hijab ɗin jikinta ta fice da sassarfa me kama da gudu, saura kaɗan ta zame a steps, ta sauko parlon a san da ta ga ana ta shigo da manyan kuloli na abinci ana wucewa da su kitchen, taji Inna Hajar na cewa da masu shigar da kayan,"kar ku saka su da ga in da babu iska kayan gara ne". ta yi tsallen murna da farin ciki ta faɗa jikin Raudha, duk su ma sauran sai suka maƙalƙaleta anata Allah sarki ƴar marainiya, sai kuma aka ɓige da yi ma ta tsiya ana tsokanarta amaryar ƙamshi, har ta fara kumatu, ta harari Maijidda da ke ta kallonta tana murmushi. ta zame da ga wajensu san da Adda Asma da Dadda ke shigowa, ta tafi da sauri ta faɗa jikin Dadda, sai ga hawaye kamar da ma jiran ganinta su ke. Adda Asma ta ce,"yau naga tsiya, to in dai kuka za ki yi kam sai mu juya". ta yi saurin goge hawayen tana faɗin,"ku yi haƙuri Adda Asma na daina". ƙememe Adda Asma ta hana su Raudha zuwa bedroom ɗin Fillo, kamar ta san gulma ce zata kaisu, ta ce wallah duk wanda ya kuskura yaje ma ta ɗaki sai ta ɓata masa. ita dai Fillo ba ta ce komai ba, daɗi duk ya isheta saboda ganin ƴan uwanta, ji take kamar kar lokacin tafiyarsu ya yi, Dadda tasa su Raudha suka shiga kitchen ɗinta su ka ƙara gyara ma ta shi da cikin store, su kuma suka haura sama zuwa bedroom ɗinta, wasu kayan da aka zazzo ma ta da shi aka ƙara kimtsa ma ta su, da aiken Dada da ta bayar a ƙawo ma ta, sannan su ukun duk suka zauna suka ƙara yi ma ta ƴan nasihohi da ba'a taɓa daina yiwa ƴa mace in har an aurar da ita. a parlo suka zauna akai ta hira har akai sallar magriba tukunna suka yi haramar tafiya, Fillo ta riƙe Maijidda akan lallai ba zata tafi ba, ta rakosu compound tana ta kuka irin na jiya. bata ƙara jin kewarsu ba sai da magriba ta yi, lokacin ne kuma ta fara jin yunwa ta shiga kitchen, ta buɗe freezer taga babban botiki na miya da su ka zo ma ta da shi ɗazu, ta ɗauko flask ɗin da Inna Hajar ta faɗa ma ta akwai ferfesun kifi a ciki, ta zuba kaɗan ba da yawa ba, ta buɗe oven ta ɗauko gasassan biredi, sai dai ko da ta zauna sai taji kasa ci, dole haka tasa hijab ta fita ta kaiwa Baba me gadi. tana zaune a parlo har akayi sallar isha'i, a lokacin tsoro ya fara kamata, tayi azamar barin parlon ta koma upstairs ta kulle ɗaki, ta dunƙule akan gado tare da toshe kunnuwa dan sam ko ƙarar AC bata son ji, kamar dai yanda ta kwana jiya ita ɗaya haka yauma ta kwana ita ɗaya, cike da tsoro fal kamar zuciyarta zata bar ƙirjinta. *Masarauta Kaltungo.* wani mugun ɗoyi ne ke tashi a cikin turakar ta Fulani Azima, tana can da ga kusurwar ɗakin an kwantar da ita akan gado, ba ma lallai ka lura mutum ba ne idan ka shigo, halittarta tayi mugun muni kamar ba wannan macen ƴar gayu da ƙwalisa ba, me ji da mulkinta da kuma girman izzarta. idanuwan da suka firfito waje kamar na ƙwarangwal sai kallon Ilham take yi wacce ke durƙushe da ga can bakin ƙofa, tayi tagumi tayi nisa acikin tunani, taji bala'in tausayin yar tata ya kamata, ta sa ni alhakin mutane da dama da ta ɗauka ba lallai ya bar ɗiyarta taji daɗin zaman gidan aure ba, ko me ya faru da ita ta san ita ta janyo ma ta, ga shi ba ta da bakin maganar da zata nemi yafiyar mutanen da ta cuta su yafe ma ta ko ta samu sauƙin wahalar da take ciki, ƴarta ma ta samu hutu. ta san babban alhakin wanda ke bibiyarta ita ce Hajiya Ramla, domin ita ta yiwa cutarwa mafi munin zalunci, kuma yanzu a cikin tsoro take matuƙa ma kuwa, domin hausawa sun ce ka guji shirun wanda ka zalunta, shirun da Hajiya Ramla tayi har yanzu yana matuƙar ɗaga hankalinta, yana tsoratata, gani take kamar shirun nata shi ke ƙara shigarta wannan matsanancin halin da take ciki, kuma kamar tana shirya ma ta wani abu ne da zai ƙara jefata halin da yafi wannan da take ciki, domin ta san babu wanda zai san kayi masa cutarwa irin wannan ya ƙyaleka, ko da ace ya yafe maka to dole zai tona maka asiri, amma ita babu ɗaya cikin biyun. a kullum babu abin da take kira face mutuwa, ta gaji da wannan wahalar da take sha, jikinta ya fara addababben ƙaiƙayin da shi kaɗai taƙi jin ya tasar mata, ta ɗago hannunta guda ɗaya da ya shanye ya koma tamkar ba'a taɓa halittar tsoka ba ajikinsa, karkarwa kawai yake yi yama ƙi kaiwa inda take so ta sosa ɗin. ta fara rera kuka a hankali, kukan babu daɗin ji, shi ba na mutane ba kuma shi bana dabbobi ba. Ilham ta ɗago ido tana kallonta, ta miƙe tana jin duk duniyar ta isheta, ta sani mahaifiya ta wuce duk inda ake zato, babu me so ya rabu da mahaifiyarsa a kowanne irin hali kuwa, amma ita dai a yanzu zata ce gwara mahaifiyarta ta mutu, ba wai zata ce ta gaji da zaman jinyarta ba ne, but cutuwar da take yi a zamanta tare da ita shi tagaji da shi, a kullum ba tayi amai ba tayi sama da sau biyar. ta ɗauki facemask ta saka sannan ta ɗauki sandar share yana, ta isa gaban gadon tasa sandar tana sosa mata jikinta da ita, saboda ba'a saka hannu wajen sosa ma ta gudun kamuwa da cutar da likitoci suka faɗa, sun tabbatar da cewa duk ranar ruwan ƙurjin ya taɓa jikin wani to shi ma yana iya kamuwa da wanannan cuta ta ƙuraje wadda har yanzu suke bincike akan su. wahaltaccen amai ya tahowa Ilham babu shiri ta jefar da sanda ta fita a ɗakin da gudu ta shiga toilet, amai sosai tayi kamar wacca zata amayar da kayan cikinta, ban da haki babu abin da take yi idanuwanta duk sun yo waje saboda galabaita. ta wanko bakinta ta fito ta tsaya a ƙofar wajen tana sauke numfashi, wucewar daƙiƙa ta fita ta zagayo ta window inda me martaba yake tsayawa duk sanda zai ga Fulani Azima, a yanzu ban da shi da ƴarta babu wanda yake iya zuwa wurinta hatta kuwa da mahaifiyarta, suma ɗin da suke zuwo roƙar ma ta mutuwa suke yi a wajen ubangiji kamar yanda take roƙawa kanta itama. cikin muryar me rauni Ilham ta ce,"Mami don Allah kiyi haƙuri, zan je inci abinci sai in dawo, banda ƙarfi a jikina yanzu duk abin da naci ya dawo". ta faɗa tana kuka. Fulani Azima ta bi ta da kallo hawaye na biyo gefen fuskarta, kullum roƙon Allah take yi ya bata aron dama ko da na lokaci ɗaya ne tayi magana da bakinta ta sawa Ilham albarka ta kuma yi ma ta godiya. su kai ta kallon junansu duk su na tausayin kowannensu, Ilham ta share hawayenta ta bar wajen ta tafi ɓangaren Boɗejo, in da ta dawo da zama gaba ɗaya tun ranar da aka yi sakin Ilham, ta ɗau fushi da Baffa da Hakimi ta ce duk Me martaba shi ya fi son ta da ƙaunarta, kwanciyar Turaki a asibiti ma sai da ta taushi zuciyarta ta iya zuwa, shi ma dan taji ance ya na can rai a hannun Allah. ta shiga parlon da sallama, kana ganin yanda take tafiya kasan damuwa tayi ma ta ƙatutu, ta zauna kusa da Boɗejo wacca ke shan kayan marmari da aka ajiye ma ta a faranti, ta cire hand gloves ɗin da ke hannunta ta wanke acikin ruwan da wata baiwa ta kawo yanzu. sannan ta shiga cin fruites ɗin da Boɗejo ta dawo da shi gabanta. "Sannu Ilham Allah ya yi miki albarka ya ba ki ladan ɗawainiya da mahaifiyarki, ita kuma ya kawo ma ta hanyar hutu, wannan ciwo na ta gwara mutuwa da jinyarsa, shiyasa akace kullum ka roƙo Allah ya rabaka da doguwar jinya". cewar Boɗejo. hawaye na bin kumatun Ilham ta ce,"amin". sannan ta karɓi plate ɗin alkubus da miyar taushe da Boɗejon ta miƙo ma ta. tana ci tana zubar hawaye na tsananin tausayin mahaifiyarta. **** bayan sati ɗaya Fillo ce zaune a parlo tana kallo, tv ɗin da tun da ta tare sai jiya da Bello ya shigo ya sa aka haɗa ma ta ita. kuma sai yanzu ta fara jin daɗin zaman tun da tana ɗebe ma ta kewa, jiya ma tana kallon tayi bacci ba ta sa ni ba sai wajen 12 ta farka ta kashe tv ɗin ta haye sama, tsoron ma da take ji ya fara raguwa, da zarar ta kunna karatun qur'ani shikenan sai tayi baccinta lafiya lau. cikin sati ɗayan nan banda zaman kaɗaici babu abin da ta ke yi, kewar Umminta da Kaka kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu, kullum sai taji kamar ta fita ta roƙi me gadi ya ara ma ta wayarsa, sai kuma ta tuna idan ta karɓo babu lambar wanda ta riƙe akanta, lambar Yami ma ta mance balle ta ce zata kira Maijidda ta kawo ma ta lambar Kaka, ita kanta Maijiddar kewarta take yi. babu wani wanda yake leƙo ma ta, ko da ga gidansu Turaki kuwa, tayi tsammanin ganin su Maama ma amma shiru ba su babu su Zaytun, hatta shi Turaki rabonta da ganin inuwarsa ma tun washegari, sau tari tana jin dawowarsa da daddare in an zuge gate ba ta ko leƙan windon balle ta kalli takaici, dan Allah ɗaya ya san adadin haushinsa da take ji a yanzu, kwatakwata bata ƙaunar ma wani abu da zai haɗata da shi, lokaci kawai take jira ta bar masa gidansa. kullum iyakarta da ga sallah sai bacci sai cin abinci haka take fama, fatar nan tata kam ta ƙara yin fresh saboda hutu, kuma duk ta gaji da hakan, sai uwar rama da take yi saboda damuwa da ta sakawa ranta da kuma rashin cin wadataccen abinci. ta ɗau remote ta sauya tasha zuwa africa tv, daidai lokacin da aka hasko marigayi Shaik Albani Zariya yana amsa tambayar wata mata da ta aiko akan bambancin iddah da kuma Takaba, hakan yasa ta dire remote ta tattara hankalinta gaba ɗaya tana sauraron bayaninsa. _"Takaba shi ne zaman da mace za tayi na tsawon wata 4 da kwana 10 bayan mutuwar mijinta. Ita kuma Iddah ita ce zaman da mace za ta yi idan mijinta ya saketa har sai ta yi jinin al'ada sau 3. Iddah mace za ta iya yin kwalliya da sauransu, amma ba zata iya yin maganar aure da wani ba har ta fita daga iddar. Ita kuma takaba mace ba zata iya yin kwalliya ba amma za ta iya yin tsafta, banda sanya duk kayan da suke ɗauke da ado na kwalliya. Amma dukkanninsu idan mace ta na da ciki to dole ne idan aka haife cikin nan to iddar ko takabar ta yanke, Idan ma aka saketa yau kuma ta haihu Yau to iddar ta ƙare. Idan ma mijinta ya mutu a yau kuma ta haihu anjima to ta gama takaba. sai dai kuma idan akayi aure miji bai tare da mace ba, ko ya tare da ita amma bai taɓa kusantarta ba, to ba zata yi masa iddah ba duk tsayin lokacin kuwa da suka ɗauka tare, da zarar ya bayyana sakin tana iya yin aurenta ko da ace a daidai wannan gaɓar wani ya zo ya bayyana cewar zai aureta to ana iya ɗaura aurensu anan take insha'Allahu...wannan shi ne taƙaitaccen ba yani a game da tambayar da kika yi, wallahu ta'Ala a'alam"._ gama bayanin nasa yay haɗe da taruwar ruwan hawaye a idon Fillo, a hankali kuma sai taji hawayen su na sakkowa saman kuncinta, ta rumtse ido tare da cije leɓenta na ƙasa ta kifa kanta akan cinyarta, haka ɗaya ba tare da sanin dalili ba taji tana so tayi kuka, irin kukan da zata yi ya isheta, taji zuciyarta na matsewa da wani irin zafi tamkar ana hura wuta, ciwon kan da ta kwana biyu ba ta yi ba ta ziyarce ta, ta kasa danne kukan da ke neman ƴancin fita a bakinta kawai sai ta sake shi, ta miƙe da sauri ta haye upstairs tana jin wani irin wahaltaccen yanayi a tare da ita, tana shiga ɗaki ta faɗa kan gado ruff da ciki, kuka sosai take yi ta rasa ta ɓangaren da zata lallashi kanta. sai da ta kusa rabin awa tana kukan sannan ta daina, ai kuwa kanta yayi ma ta wani uban nauyi kamar zai faɗo, ta miƙe ta shiga toilet ta yi wanka a daddafe ta fito, ta buɗe wadrobe ta ɗauko doguwar riga ta atamfa ta saka, ta taka stool ta ɗaga ƙasan trolly ta ɗauko takardar sakin, ta zura hijab ɗinta tare da buɗe drower ta ɗebi kuɗi ta saka a jaka, abu biyun nan su kawai take buƙatar tafiya da su, takardar sakinta da zata zama shaida da kuma kuɗin da za su kaita Taraba. ta zauna bakin gado zuciyarta na karanto ma ta kuskurenta, ita ai duk ɗan guntun ilimin da take da shi ce take sai tayi masa iddah shiyasa har ta yarda ta zo gidansa, ashe yanzu ita kwata-kwata ma ba ta da wata alaƙa da shi, zaman haukarta na rashin iliminta kawai take yi. abun da ta kasa ganewa shi ne; me yasa ta damu da sakin nan?, me ya sa take jin kamar rabuwa da cikin gidan nan tamkar rabuwa da wani ɓangare ne na jikinta?, abu ɗaya kawai ta san yana rubuce a tafin hannunta, babu wani abu da zai hanata barin gidan nan ayau tun da har ba ta da wata alaƙa da shi, za ta tafi tabarsa nisan tafiya kuwa ta har mutuwa. sabbin hawaye suka shiga sauko ma ta, taji kamar hayaniya da ga downstairs, bata ta shi ba taci gaba da zamanta tana tunanin ta yanda za'ai ta tafi, ita ba sanin hanya tayi ba, ita ba lambar wayar kowa ba, ba ta taɓa sanin ina ne tasha ba balle ta kai kanta, anya ba zata nemi taimakon Baba me gadi ba?, dan ba zata iya zuwa gidan su Turaki ba. zuciyarta ta yarje ma ta hakan, dan haka ta miƙe tana ƙara goge hawayen fuskarta ta fita da ga ɗakin tana jin wani baƙin ɗaci a zuciyarta, tana fara sakkowa da ga steps ta hangi Nihal da wasu yara da za su yi sa'anni da ita, kuma kallo ɗaya ta yi musu ta tuna maganar Bello da yayi mata jiya cewar za'a kawo ma ta ƴan aiki, tai saurin komawa yanda ba za su jita ba, ta cire hijab ɗin jikinta ta ajiye tai saurin shiga toilet ta wanke fuskarta da sabulu, tana fitowa taga Nihal a tsaye tana ƙarewa ɗakin kallo. tayi ƙarfin halin ƙaƙalo murmushi kamar yanda Nihal ɗin ke yi ma ta. cike da zolaya Nihal ta ce da ita,"kai Antynmu ai sai muyi zaton ko honey moon ku ka wuce babu sallama, 1week ba ku leƙa mu ba". Fillo tai murmushin

Chapter 53 of 73