yaƙe ta tsuguna tana gaida ita.
Nihal ta ce,"kar ki ban kunya don Allah tashi mana, ni ya kamata na tsuguna miki yanzu ai ba ke ba, matar babbar Yaya".
Fillo taja yatsun hannunta ta ce,"Adda Nihal ina Maama da Mum?".
ta ce,"su na kan hanyar zuwa ai, ashe ba ki da lafiya shi Hammah kwata-kwata bai faɗa ba sai yau. ya sauƙin jikin naki?".
Fillo ta ɗago tana kallonta sai kuma ta ce,"naji sauƙi ai".
Nihal ta ce,"kin ga ma yanda ki ka rame kuwa".
buɗar bakin Fillo zata yi magana suka ji shigowar mutum, Nihal ta gaida Turaki tana yi masa sannu da zuwa, bai ko amsa ma ta ba yayi ma ta nuni da hanyar fita ta zo ta wuce tana ɓata fuska, tun da Baffa yay masa gate da gida shikenan ya sauya musu ko magana ba yay musu up to now, sai kace su ne suka hana shi zuwa gidan.
sai da Nihal ta fita tukunna Fillo ta ɗago ta yi masa kallo ɗaya ta ɗauke kanta, yana tsaye jikin ƙofa ya harɗe hannayensa a ƙirji ya zuba ma ta ido, kamar me son karanto wani abu a tare da ita, jin idonsa a kanta yasa ta haɗe gira sama da ƙasa ta juya masa baya.
wucewar daƙiƙa biyu wayarsa da ke aljihu ta shiga ringing, ya sa hannu ya ɗauko yana picking tare da cewa Hajiya Madina,"Maama ba ta fito ba ne idan ta fito zan kira ki".
muryar Hajiya Madina na bayyana damuwar rashin lafiyar da yace musu Fillo na yi ta ce,"to da ta fito ka kirani kaji ko?, nima gamu nan muna kan hanyar dawowa na tsaya her excellency ne za ta shiga office ta fito, ka dai ce kunje hospital ko?".
ya shafo wuyansa ya ce,"ehh Maama ta ji ma fa sauƙi, na faɗa miki ma zatona ko Baffa ya dawo ne shiyasa bamu zo ba".
ba ta ce da shi komai ba ta kashe wayar tana shaida Mum batun rashin lafiyar.
"da me babban suna mu ka gama waya, ashe rashin zuwan na su ba ta da lafiya ne, ni dama dai ince cin amarci ai ba zai hana su zuwa su gaisar da mu ba muna kusa da su. yanzu kawai mu tafi gidan na su ko? duk da naji yace ai jikin da sauƙi".
Mum ta ce,"ni kam ba zan iya zuwa gidan su ba, tun da taji sauƙi shikenan, ki kwantar da hankalinki please".
Maama ta ce,"ni kam gaskiya sai naje na dubo su hankalina zai kwanta, sati guda ban saka me babban suna a idona ba".
Fillo na murguɗe murguɗe da harare harare ta nufi hanyar toilet za ta shiga, yay amfani da sautin muryarsa wajen buga ma ta tsawa akan ta tsaya, duk ta yanda taso ta dake ta nuna rashin firgitarta sai da ta tsorata ta ƙame a wuri ɗaya jikinta na kyarma.
ya ƙarasa shigowa ciki ya ja stool ya zauna akai, ya saita kira akan lambar Maama, sannan ya ɗago yana kallonta yaga har yanzu rawar jiki kawai take kamar me jin sanyi tama ƙi buɗe idanuwanta, hawaye na sauka a kuncinta. yay tsaki na ban haushi da takaici, ya miƙa hannunsa ya fizgota sai ga ta ta wancakalo bakin gado kamar sandar da aka janyo, abunka da mara ƙiba sam sam.
"buɗe idonki". yanda ya yi amfani da sautin muryarsa abin ya bata tsoro, kuma da ta buɗe ido ta kalle shi tsoron sai ya ƙaru fiye da misali, dan rikiɗewa ya ke yana komawa kamar ba mutum ba.
muryarta na breaking ta ce,"tafiya zan yi".
ya danna kiran Maama ya jefa ma ta wayar a jiki, niyyarta ta miƙe wayar ta tarwatse a ƙasa, amma sai taji Maama na magana, sannan ne ta ɗauka tana magana ta yanda Maama ba zata fahimci kukan da take yi ba a muryarta.
*comment, share and vote.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*48*
"Daughter nah". Hajiya Madina ta kirata da sabon sunan da ta raɗa ma ta tun a ranar da aka kawo musu ita.
"na'am Maama".
with much care Maama ta ce ma ta,"ya jikin naki?, da sauƙi ko kuwa?, kina shan magani?, yanzu ya kike ji?, mene yake ya damunki?".
waɗannann tarin tambayoyin yasa ta kallon Turaki ta gefen ido, idonsa na kan ɗaya wayar da ke hannunsa, fuskarsa kamar baƙin hadarin da ya haɗo, ta rufe ido ta ce,"Maama lafiyata lau, shi ne kawai ya ce miki ban da lafiya". ta faɗa kamar zata sa ki kuka.
furucin na ta yasa Hajiya Madina murmushi, ko ba komai ta san da gaske jikin na ta da sauƙi kamar yan da ya ce, ta furta alhamdullahi sannan ta ƙara cewa,"kina cin abinci sosai ko?".
ta ce,"ina ci".
"to Allah ya ba ki lafiya Daughter, Allah ya sa kaffara, ki daure ki dinƙa shan magani kinji, becx bana so na ji wani abu yana taɓa min ke, zan zo anjima na duba ku, Allah ya yi muku albarka".
a hankali Fillo ta ce,"Maama Ummina fa?". ta faɗa muryarta na ɓallewa da kuka.
zaton Hajiya Madina ko tana so ta ganta hakan yasa ta ce ma ta,"za ki je kiga Ummin ki very soon, ni da kaina ma zan kai ki".
kamar ta faɗawa Maama komai sai kuma tayi shiru, ita tambayar da tayi saboda Maama ta ce zata haɗa su a waya ne, in yaso sai ta ce da Ummi azo a ɗauketa dan ba ta fatan ta ƙara kwana acikin gidan da ba zaman aure take yi ba.
ta sauke wayar da ga kunnenta bayan Hajiya Madina ta kashe, ta waiga tana kallon Turaki ta ce,"ka ba ni lambar Kaka ko Ummi please".
maganar tata sai ya zama tamkar da dutse tayi, yay banza da ita ban da ma waya da ya kara a kunnensa yana amsa sallama, ba ta ɗauke idonta akansa ba taci gaba da kallonsa, hotunan kasadar da ta dinƙa yi wurin ceto rayuwarsa yana haska ma ta a ido, sai a yanzu ne ta yarda da cewa ɗan adam butulu ne, ita ba wai don ya saketa ba, a'a irin wulaƙanci ma da yake ma ta na nuna da ita da banza da wofi ɗaya, kuma ƙila duk yana ma ta haka ne saboda sanin mahaifinta da yay, da ma sai da ta faɗawa Ummi cewa wallahi bai aureta ba saboda abubuwan da ya faɗa sai don ya wulaƙantata, a lokacin Ummin ba ta yarda da ita ba hasalima faɗa suka haɗu suka dinƙa yi ma ta ita da Kaka, but yanzu ta san dole za su yarda da abin da ta ce, kuma ko ba komai ta san Turaki zai ga ishara akan aurenta da yay ba don komai ba sai domin ya tozartata.
maganar da yake yi a cikin wayar ta shiga kunnenta.
"no ba haka ba ne Faruq, bana fatan na ƙara maimaita kuskure, this time around ba zan yi gaban kaina ba, ba zan ƙara yiwa kaina aure ba sai da sanin iyayena, kai ba ma aure ba kawai, dukka wani abu na rayuwata, gaban kaina da nayi banji da daɗi ba, ni ɗaya na san halin da na shiga, but da na rabu da kowacce yanzu komai ya zamar min normal, ina cikin farin ciki da kwanciyar hankali".
_na rabu da kowacce._ kalmar ta maimaitu a cikin kan Fillo, kenan har Ilham ma ya rabu da ita?, ita kuma me ta yi masa?, wai wanne irin mutum ne shi ɗin?, kenan shi ma yana sahun mazan da basa mutunta aure, burinsu su aura su saka?.
ta yiwa kanta tambayar da zuciyarta ke ba ta amsa, tunaninta ya tsaya cak san da taji yana cewa,"sunanta Aisha ƴar sarkin kano ce, insha'Allahu gobe nake so naje na gana da iyayenta, zan fara neman izininsu before na kai maganar gaban su Baffa, ita ba ni da matsala da ita becx ita ta fara cewa tana so na, so pray for me kar na sami matsala da Baffa, dan nima ina son yarinyar sosai...".
cak maganarsa ta katse dalilin ƙarar fashewar abu da yaji, yay saurin ɗago ido yana kallon wurin da Fillo ke tsaye tana ƙoƙarin saka hijab, sai kuma idonsa ya kai kan wayarsa da ta tawarwatse a ƙasa, ta yi ragaga tamkar tayar mota ce ta bi ta kanta.
bai san lokacin da ya miƙe ba yana bin ƙasan tiles ɗin da kallo, yana kallon kowanne pieces na glass ɗin wayar da ya barbaje.
Muhimman abubuwansa da suke kan wayar!, hakan ya gimla a zuciyarsa, lokaci ɗaya ransa ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, ya dunƙule hannu ya ɗago kansa a fusace yana kallonta wacce ke shirin ficewa, da zafin nama ya janyo hijab ɗin nata ya dawo da ita gabansa yana cewa,"are you mad?". ya ɗaga hannu sama a zafafe zai sauke ma ta kyawawan mari tayi saurin yin ƙasa da fuskarta, take jinkinta ya ɗauki rawa saboda yacce take jin hucinsa na cika ɗakin.
babu shiri taja da ba ya tana rarraba ido, sai da ta kai jikin bango tukunna ta sami damar ɗago da kai tana kallonsa, tayi mugun tsorata da yanda ƙwayar idonsa ta sauya kala, da yanda taga kamar yana huruwa yana sacewa, tsananin tsoron abun da zai iya aikata ma ta yasa ta ɓallewa da kuka tana faɗin,"to ai bana sa ne".
ta faɗi hakan dan ba ta tunanin kalmar haƙuri za ta iya fitowa da ga bakinta zuwa gare shi.
Turaki ya rumtse idonsa gam for few minutes yana so ya taushi zuciyarsa, ya buɗe ido yana furzar da iska daga bakinsa, ya watsa ma ta wani mugun kallon da ya ƙara hargitsata, cikin ɗagowar murya ya ce,"zo ki ɗauko ki ban".
hakan bai sa ta ko motsa da ga in da take ba, illa ma haɗe rai da tayi tana juyar da kanta gefe guda, Turaki ya daɗa fusata yay taku ɗaya ya isa gabanta, ya shaƙi wuyanta ya manna kanta da bango.
ya zaro mata idanuwansa waje ya ce,"ke wacce kalar halitta ce ne da babu ƙwalƙwalwa a jikinki?". ya faɗa da wani amon sauti da ba nasa ba, zai iya rantsewa tun da yake ba'a taɓa ɓata masa rai ba irin yau, fashewar wayar ba shi ne damuwarsa ba, crucial documents na office da yay saving a phone storage, jiya ya gama ɓata lokaci wajen saving wani document na contract ɗin da suka karɓa, Bello kawai yake jira ya zo ya tura masa, yanzu shikenan ta jiƙa masa aiki, kwana yayi yana typing bai ko runtsa ba, haka ya dinƙa aikin babu daɗi saboda ya baro laptop ɗinsa a office.
ya cije leɓensa na ƙasa yasa ƙafa zai fyaɗeta ta kife a ƙasa sai kuma ya fasa, ya buga mata tsawa da cewa,"wu ce ki ɗauko ki ban".
tuntuni ta daina tsoronsa, sai dai ta rasa dalilin da yasa ta kasa daina jin tsoron tsawarsa ba, tana tafe yana bin ta a baya.
ta durƙusa sai kyarmar jiki takeyi ta ɗauko wayar ta ba shi, yasa handky ya karɓa gudun kar glass ya soke shi, ta yi tsaye tana zumɓura baki, ta ƙara jin saukar tsawar muryarsa da cewa,"tattaro glass ɗin".
zata wuce ɗauko tsintsiya ya fincikota. "hannu za ki saka". ta kallesa ta ga babu alamar imani tare da shi hakan ya sa ba shiri ta durƙusa ta shiga tattara kwalban, idonsa ƙyam akan hannunta da ke zubar da jini dan tun a ɗauko wayar kwalabar ta soketa.
sai da ta gama tattarawa ya wurga ma ta ɗayan handky ɗin, ta ɗauka ta zuba glass ɗin a ciki ta miƙo masa, ya karɓa yana nuna ta da yatsa cikin kakkausar muryar da ke shaida kashedi me girma ya ce,"kar ki kuskura, kar kiyi saken da zan dawo cikin gidana na sameki, in har kuwa na dawo na tadda ke ki tabbatar da cewa alƙiyamarki ta tsaya, dan sai kin ƙwammace ba ki taɓa sanin zuri'ar Alƙali ba balle kuma ni, and ki san da cewa sai kin biya ni wayata".
yana faɗar haka ya fice fuuu ya bar ɗakin, ta bi bayansa da kallo kafin ta kifa kai da gwiwa ta fashe da kuka sosai, babu abin da take ji a zuciyarta sama da danasanin saninsa, sai da ta daɗe a haka sannan ta miƙe tunawa da kashedin da yayi ma ta, ta ɗauki jakarta ta fita da ga ɗakin tana jin zuciyarta kamar za ta buga, jiri ne ma yake neman zubar da ita dan da ƙyar idanuwanta suke kallon gabanta, tana sakkowa da ga benen ta faɗi kanta ya ƙumu da ƙarfen benen, cikin ƙarfin hali ta tashi tana daddafa bango ta iso har ƙofa ta buɗe.
daidai da zuge glass ɗin ƙofar da Hajiya Madina tayi, karaf idonta ya fara sauka akan hannun Fillo da ke zubar da jini, ta zaro ido waje tana ambaton,"subhanallahi". sai kuma ta kalli Fillon ta ga tana hawaye ga shi kamar ba ta cikin hayyacinta, tai saurin kamota ganin tana neman faɗuwa.
"Daughter lafiya?, wannan jinin fa da ga ina?".
Fillo ba ta iya ba ta amsa ba, haka ba ta iya kallonta ba, Hajiya Madina ta riƙeta suka yo waje tana cewa da Nihal,"ko ma ki tayar da mota". sannan ta ƙara ce wa da Fillo,"ina me babban sunan?". sai a sannan ta iya buɗe baki ta ce,"ya fita".
san da motar Maama ta fita da ga gidan Baba me gadi ya girgiza kansa cike da tausayin Fillo, yarinya ƙarama ana neman a ɗora ma ta hawan jini, tun ranar da aka kawota ya fuskanci ba auren soyayya akayi ba, dan shi dai bai taɓa ganin Turakin ya shiga part ɗin ba sai ɗazu da ya fito a fusace kamar macijin da aka dannewa kai.
direct asibiti mafi kusa suka wuce, tun tahowarsu Maama da Nihal ke jera ma ta sannu, su na zuwa cikin gaggawa Dr yay ma ta treatment ɗin wajen, ya cicciro pieces na glass yafi biyar a tafin hannunta, aikuwa tasha azaba dan jini kamar ana tatsarsa hannun duk ya caɓe, akai ma ta allurai, Nihal taje pharmacy ta karɓo maganunguna, lokacin da ta dawo an naɗe hannun Fillon da uban bandage.
da ga fitowarsu zuwa yanzu kuwa Maama ta kira wayar Turaki yafi sau bakwai duk ba ta shiga, kuma duka lines ɗin nasa, hankalinta duk a tashe yake da ciwon Fillon, ta kira wayar Mum ta tambaya ko Turaki ya zo gida ta ce ma ta a'a, Bello ma yace ba sa tare.
kan hanyarsu ta dawowa Maama ta matsa ma ta da tambaya akan yacca akayi taji ciwon, ta kasa haɗa ƙaryar da zata faɗawa Maama ɗin, tai shiru ita dai sai rera kuka takeyi a hankali, har sai da taji ɓacin rai a muryar Maama tukunna ta ce,"wayarsa na fasa masa ban sa ni ba".
Maama na kallonta ido buɗe ta ce,"fasa waya kuma sai kiji ciwo haka?".
tayi shiru tana daɗa yin ƙasa da kanta, Maama ta dinƙa kallonta tana so ta nazarci yanayinta, uwar ramar kaɗai da yarinyar tayi ya isa ya shaida maka hankalinta ba'a kwance yake ba sam, dole akwai wata matsalar a ƙasa, dole da akwai abin da yake faruwa wanda basu san da shi ba, tun da me gadi yace ma ta Turaki ya fita babu jimawa ta san akwai matsalar da ke faruwa musamman da taga Fillo a wannan yanayin, babu tantama saɓani suka samu duba da yanda duk Fillon take a tsorace.
_me ce matsalar?._ tambayar da ta yiwa kanta kenan, sai dai babu amsarta. hakan ya sa ta kamo hannun Fillo tana kallonta ta ce,"ɗago ki kalle ni a matsayin Umminki wacce ba za ki taɓa iya ɓoyewa damuwarki ba".
idanuwanta suka kawo sabon ruwa sanda ƙwayar idonta ke shiga cikin ta Maaman, tausayin Maaman shi ya fara kamata ganin duk ta damu, kafin girma da kwarjinin Maaman su mamayeta gaba ɗaya, ba zata iya yi ma ta ƙarya ba sam saboda ta kare kanta ko kuma ta kare shi, ta sauke kanta ƙasa muryarya a hankali ta ce,"da wayar ta fashe ne shi ne ransa ya ɓaci ya ce sai na kwashe glass ɗin da hannuna".
da tsananin mamaki Maama ta ce,"me babban sunan da kansa?, ya ce ki kwashe glass da hannunki?, cikin hankalinsa yake kuwa?".
wannan furucin kaɗai ya shaidawa Fillo ran Maama ya ɓaci sosai. Maaman tai shiru ba ta ƙara magana ba sai faman jijjiga kai da takeyi, idanunta na kan waya tana ƙara trying lamar Turaki, cikin sa'a kuwa yanzu ta shiga sai dai har ta gama ringing bai ɗaga ba, ta ƙara kira nan ma bai ɗaga ba, sai da ta kira har sau uku sannan ta haƙura ta jefa wayar a jaka, cikin zuciyarta sai jinjina abin da Turaki ya aikata takeyi, ko da yake da ma ba'a sanin wani mugun halin namijin sai bayan ya yi aure.
Fillo dai idonta na kan hanya, tunaninta ɗaya ta yanda zata faɗawa Hajiya Madina a sauketa a hanya, ta ga motar ta tsaya bakin wani islamic chemist, Maama ta buɗe ta fita ba tare da tace da su komai ba, ta bi ta da kallo ta glass har ta shiga kantin.
a lokacin ta buɗi baki ta cewa da Nihal,"Adda don Allah ina ne hanyar tashar barin gari?".
Nihal ta waigo tana kallonta ta ce,"me za ki yi acan?".
tai shiru ba ta ce komai ba, lokacin Maama ta buɗe motar ta shigo, sanda ta rufo ƙofa Nihal ta ce ma ta,"Maama wai tambayar tashar da za'a bar gari take yi".
Maama ta waiga taita kallon Fillo, wacce idonta ke kan hannun ciwon nata, tana nufin gidan su zata tafi kenan?, ta san ba komai bane ke damunta fa ce yarinta, bata ce komai ba tayi ƙwafa me ƙarfin gaske tana ɓallo maganin da ta siyo a islamic chemist ta bawa Fillo.
Nihal ta kashe sautin waƙar da ke tashi, saboda ta san idan ran Maama ya ɓaci ba ta son jin komai na shiga cikin kunnenta.
bayan doguwar tafiya Fillo taji motar ta tsaya, ta ɗago kanta tana kallon gate ɗin gidan, gabanta taji ya faɗi hakan yasa babu shiri ta juya tana kallon gefen da Maama take tace,"Maama ya ce na bar masa gida".
"ki bar masa gida?".
ta ɗaga kanta tabbacin hakan.
"saboda kawai kin fasa masa shegiya waya ya buɗi baki ya ce ki bar masa gida?".
sai kuma ta bar kallon Fillo ta koma kan Nihal ta ce,"shiga ciki ki gano min ko ya dawo".
a tsure Fillo ta ce,"Maama ai...".
kuka ya kubce ma ta ta kasa cewa komai.
Maama na kallonta ta ce,"ai me?".
ta buɗe baki tana jin kamar yawun bakinta yayi kaɗan su yi maganar da zata yi, tace,"he divorce me".
da wani mugun shock Maama ta ce,"what?, divorce!, ƙalu innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ya sake ki fa kika ce?".
tayi maganar tana jin kanta na mugun sara ma ta, tai saurin dafe shi tana rumtse ido ta jinginar da kanta jikin kujera.
Fillo ta fashe da kuka, Nihal ta shigo motar tana cewa,"bai dawo ba Maam...".
maganartata ta tsinke jiyo numfashin Maama na fita da ƙyar, a ruɗe ta ce,"innalillahi, Maama".
ta faɗa tana fitowa ta zagayo ta buɗe side ɗin da take, "Maama". ta faɗa tana kamota.
Hajiya Madina na dafe da ƙirjinta da ƙyar ta iya cewa,"mu je gida da sauri".
tun kamin su ƙarasa gidan Nihal ta kira Mum a waya ta sanar ma ta cewa BP ɗin Maama ya tashi, kafin su ƙaraso tana tsaye a compoud hankalinta a tashe sai safa da marwa takeyi.
ko parking Nihal ba ta ƙarasa ba Mum ta buɗe, ita ta kama Hajiya Madina suka wuce, ko lura da Fillo ma bata yi ba, sai bayan ta kai Hajiya Madina bedroom ne ma taji tana ce mata,"ina amanar da mu ka karɓa?"
Mum ta ce,"wacce amana?".
Maama na magana da ƙyar ta ce,"Fillo". sai kuma muryarta ta karye tana cewa,"your excellency me babban suna ya cuce mu, sati ɗaya da aure ya saki yarinyar mutane".
Mum ta zabga wani salati tana waro ido waje ta kalli Nihal da Fillo da ke shigowa ɗakin. sannan kuma ta juya tana ƙara kallon Maama wacca taga kamar ba'a hayyacinta tayi maganar ba, ta ce,"wai saki kamar ya ya dai Madam?, saki na aure? ko wanne kalar saki ban gane ba?".
cikin ƙarfin hali na irin zafin da Maama ke ji a ƙirjinta ta ce,"divorce dai da kika sa ni, kawai saboda ta fasa masa waya ba ta sani ba, ki duba hannunta ma ki gani ciwon da yaji ma ta".
farat ɗaya ran Mum ya kai ƙololuwar ɓacin da bai taɓa yi ba, ta ce,"ba shi da hankali ko kuwa shaye-shaye ya fara bamu sani ba?".
ta kalli Nihal ta ce,"kirawo min shi dan ubansa".
sannan ta kalli Fillo tace,"laifin me kika yi masa da har zai sake ki?".
ta zube gwiwoyinta a ƙasa tace,"ai dama tuntuni na ya sake ni".
Maama ba ta san lokacin da ta miƙe zaune ba tayi warkewar lokaci ɗaya, Mum ta nemi wuri ta zauna, a tare suka jefa mata tambayar,"wacce tuntunin Fillo?".
"tun before na tare, na kasa faɗawa kowa ne...". kuka yaci ƙarfinta tayi shiru tana rumtse ido.
Maama ta saki baki kamar yanda Mum tayi duk suka kasa cewa komai, wucewar daƙiƙu muryar Nihal ta kutsa cikin shirun na su da cewa,"Mum bai ɗaga ba".
ba tare da tace ma ta komai ba ta miƙa ma ta hannu Nihal ta ɗora ma ta wayar, ta lalubo lambar Bello ta kira, bugu uku ya ɗaga, a fusace tace da shi,"da kai da shi kunci kutumar ubanku, kuna ina?". tayi tambayar a tsawace.
zagin da tsawar suka daki kan Bello yayi zillo akan kujerar da yake, ya haɗiye yawu da ƙyar ya ce,"Mum". tai saurin katse shi,"zanci ubanka idan ka ƙara kiran sunana, na ce kuna ina?".
cikin ƙinƙina Bello yace,"ni ina office shi kuma ban san inda yake ba".
"ƙarya kake yi munafiki".
yace,"wallahi Mum rabona da shi tun last week, ko haɗuwa bama yi a office".
tai shiru kafin tace,"to ka kira kirasa ka faɗa masa minti ashirin na ba shi yazo ya sameni".
ta katse wayar, Nihal tayi saurin karɓa ganin tana ƙoƙarin jefar da ita a ƙasa.
bayan minti biyu kiran Bello ya shigo, ganin Mum bata da niyyar ɗagawa Nihal ta ɗaga yace ma ta,"ki faɗawa Mum wallahi ina ta kiransa bai yi picking ba for morethan 4times, kuma ni ban san inda yake ba".
Nihal ta faɗawa Mum, sai tace ta kira ma ta Khalil, yana ɗagawa Mum ta ce da shi,"ka kira min ɗan banzan Hamma'nku ka faɗa masa tun banyi masa baki ba ya sameni a gida cikin gaggawa".
ba tare da jiran cewarsa ba ta kashe wayar.
ɗaki dai yay shiru tamkar babu wata halitta acikinsa, ran kowa a cunkushe, zuciyoyin kowa da abunda take saƙawa.
minti goma minti ashirin suka wuce, rabin awa ma haka, aka cika awa guda ma, duk su na zazzaune jungum jugum, Hajiya Madina ma ta kasa shan magungunan da aka ajiye ma ta.
can suka ji buɗewar ƙofa an shigo, Zaytuna ta shigo tana ajiye jakarta, ta cire labcourt ɗin jikinta tana zazzare idanu wajen kallon kowa kafin ta buɗi baki tace,"Mum, Maama lafiya?".
babu wanda ya kalleta balle ya amsa ma ta, sai tayi tsuru-tsuru ta kalli Nihal suka yi magana da ido ta nuna ma ta Fillo dake durƙushe a ƙasa.
sai taja bakinta tayi shiru ta fasa sanar da saƙon Turaki da ya faɗa ma ta cewa tace da Mum yaje kano ne after magrib zai dawo, wayar da take kira ba ta ɗaguwa.
shirun da yay yawa yasa Mum miƙewa ta fita, aka bar Maama da Fillo har sai da akayi sallar la'asar tukunna tace da ita ta tashi tayi sallah.
gida dai sai yay ɗiff kamar gidan mutuwa, ran iyaye babu daɗi yara kuma duk sun shiga damuwa saboda yanayin da iyayensu suke ciki, bayan sallar magriba Hajiya Madina tana lazimi Turaki ya tura ƙofar ɗakinta, haka kawai yaji gabansa ya faɗi duk da bai san abun da ke faruwa ba, Hajiya Madina ta waigo dan ganin mai shigowa, tana ganinsa ta miƙe ba tare da ta shirya ba ta fuskance shi.
murya a sama ta nuna masa hanyar fita ta ce,"fita, fitar min da ga ɗaki kafin na sa ƙafa na take in take banza". muryarta ta fita da tsananin ɓacin rai.
yay tsuru tsuru ya buɗe baki zai yi magana ta ɗaga hannu ta wanka masa wari, ta shiga nuna shi da yatsa tana faman huci tace masa,"da ga ranar yau zuwa ranar da za'a busa ƙaho babu ni babu kai, in har ka ƙara shiga sabgata tabbas hukuma ce zata rabani da kai, ma za juya ka bar min ɗaki".
ganin ba zai fita ba ta rarumo ƙaramar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 54 Chapter of 73