Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
matar Hakimi ta shigo ɗakin, itama tai mamakin ganin Ihlam tace,"yaushe kika dawo?". tace,"jiya da yamma, tun jiyan ma naso nazo naga Boɗejo Mami tace na bari dai zuwa yau". Hajiya Atika na murmushi tace,"lallai ne to sannun da zuwa, fatan an kammala karatu lafiya?". tace,"lafiya lau Hajiya, ai banma taho ba sai dana jira result ya fita. jiya ina dawowa Me Martaba yay min kyautar wannan gidajen guda biyu na estate ɗinsa". Hajiya Atika tace,"masha'Allahu, Allah yasa a amfana da karatun da akai, ita kuma ƙawar taki fa?". Ilham ta kalli Aisha sannan tace,"ai ba tare mukai karatun ba, tazo min sannu da zuwa ne, itama ta kusa kammalawa tana karantar AEE ne a Germany". Aisha ta gaida Hajiya da Boɗejo, suka amsa suna sanya musu albarka. Ilham tace,"Hajiya ita ɗin fa ƴar sarkin kano ce". Boɗejo tace,"ni fa ince, shiyasa da ta shigo taƙi gaisheni ta hakimce mana akan kujera, ashe izzar masu sarautan ce, to ni nan da kike gani na haka kamar ba kowa ba to sarauniya ce ada, kuma ni na haifi Baban wannan yarinyar, kinga na zama matar sarki uwar sarki, nan gaba kaɗan ma zan zama Kakar Sarki, dan sai an sami wani jikan nawa ya hau kujerar sarautar nan, dan haka ki sadda kanki ƙasa ki min biyayya ki kwashi albarka, ko me gidan nan Hakimi da kike ganinsa ɗana ne shine na fari, kinga kuwa indai girman izzar sarauta ne aini ke da ita bake ba yarinya". dukansu suka yi dariya. sai yanzu Hajiya Atika ta samu damar isar da saƙon Hakimi. "dama Hakimi ne yace na faɗa miki ko kema zaki je wajen taron nan na buɗe company ɗin su Turaki". Boɗejo tace,"shi Turakin ne zai buɗe kamfani ko kuma ɗana Dikko ya buɗe masa?". Hajiya Atika tace,"ehhh Alƙalin ne ya gina ya kuma mallaka masa shi da Khalil, kamfanin haɗa lemuka ne". Boɗejo tace,"ni dai ince, amma ina Turaki yaga kuɗin buɗe wani kamfani ai sai dai ɗan nawa. kuma tunda dai ya riga ya mallaka masa ba zani ba, babu wani taro da zanje ni kam, gwara naja mutuncina". Aisha da Ilham na kallonta, Hajiya tace,"to akwai wata matsala ne Boɗejo?". tace,"matsaltsalu ma kuwa, wa ya aikeni zuwa gurin da yake mallakin Turaki!, tun fa ranar da akai wannan zaman akan batun aurensa nace ko aikin asiri ke cinsa shikenan fa ya daina kulani, idan ya ganni ma ɗauke kai ya ke, jiya ma da suka zo gidan nan shi da ubansa kallon arziƙi bai min ba, yana ji Dikko na gaishe ni amma balagaggen yaron nan sai yasha mur ya kauda fuska gefe, to yanda ya ƙullace ni ɗin nan na sake naje kamfanin nasa ai sakawa zai yi a kore ni, kaɗan daga aikinsa, dama ya taɓa korata daga ɗakinsa daga zuwa in dubasa, kinga kuwa me zai kaini kamfani kuma, a'a ku ɗin dai kuje sai kun dawo, wannan ɗan ai halin wan Kakansa yayo, Sarki Adam ba, basu da kyau sam". Hajiya tace,"to Allah ya kyauta, bari na sanar ma Hakimin". Boɗejo tai shiru bata ce komai ba tana ta shafa kan Ilham, har Hajiya ta fita sai ta dawo tace,"Ilham ku ba zaku je ba?, su Hanifa tun ɗazu suka tafi. shi ma Me Martaban yanzu naji sunyi waya yana batun zasu tafi". kafin Ilham tace komai Boɗejo tace,"kinga Atika du Allah tafiyarki, yaushe yarinyar ta dawo ko hutawa bata yi ba ace ta wani kama shiga cikin hayaniya, ƙila ma taje taron buɗewar kuma a fara haɗa lemon aƙi sammata, tunda me kamfanin ba mutumci garesa ba, gwara taja mutumcinta da ajinta". Ilham tace,"Boɗejo ina son zuwa fa, dama haka nace ma Mami zan bi ku mu tafi, kuma fa idan banje ba Hammah Turaki ba zai ji daɗi ba tunda yasan na dawo, yaga duk ƴan'uwa sunje ni banje ba, sai yay zaton wani abu". tana rufe baki Boɗejo tace,"Allah ba zaki ba, babu wani taron buɗe kamfanin lemu da zaki je, ki zauna ki huta abinki. mene wani wani Hammah Turaki balle rashin jin daɗinsa, ya daɗe bai ji rashin jin daɗin ba, Turako ba Turaki ba". tunda Ilham taji ta rantse kawai sai ta haƙura, ita da Aisha suka durfafi dubulan da alkaki da aka kawo musu. suna ci Boɗejo na basu labarin sarautarsu ta da. *Comment, Vote and Share Please.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *22* After 4months, cikin ƙaton office ɗin da sanyin Ac ke ta busawa yana haɗewa da daddaɗan ƙamshin turaren dake jikinsa yana bada wani irin sanyayyan ƙamshi me motsa zuciya. Turaki ne zaune akan kujera dake ɗan juyawa da shi gefe zuwa gefe, one of his fingers on his lips, cikin yanayi na nazari akan wani lissafi nasa. numfashi ya sauke sannan ya shiga operating laptop ɗin dake kan table a gabansa, ya ɗau lokaci kafin ya ɗauƙi wayarsa a gefe yay calling numbern Khalil. in the next 3minutes sai ga Khalil ya shigo office ɗin, tun shigowansa Turaki ke kallonsa har sanda ya ƙaraso ya zauna kan kujera. "Director". Turaki ya faɗi sunan da yake kiran Khalil da shi a yanzu tun bayan mallakar wannan company ɗin da sukai. Khalil ɗin shima yana kallonsa ya amsa da nasa sunan da yake kiransa da shi na yanzu. "yes Manager". anan ne kuma Turaki ya ɓullo da wata magana wadda ta shafi aikin company ɗin nasu, sun ɗau tsawon lokaci suna tattaunawa akan issue ɗin, Khalil nata ƙara kawo dabaru da zasu daɗa ɗaga company ɗin nasu zuwa sama, dan sam basa saka kamfanin nasu a matsayin ƙarami saboda yana sabon buɗewa, so suke cikin ƙaramin lokaci ya kai wani babban mataki da ba kowanne company ke samu ba at once. a lokacin Turaki ya haɗa urgent meeting da staffs nasu, aka shiga aka ƙara tattaunawa kowa na bada POV nasa akan ganin kamfanin ya haɓɓaka. sai da suka ɗauki tsawon awa guda sannan suka gama. suna kammalawa kuma Turaki ya bar office ɗin, ya tafi airport ɗauko Bello Ƙaraye wanda ya dawo daga sudan yaje wani course. akan tinin barin Gombe international airport, cikin motar ƙirar Bugatti, motar da Mai Martaba ya bawa Turaki ita a ranar buɗe company ɗinsu, Bello ya kai hannu yay reducing volume na karatun qur'anin da suke saurare tun barowansu airport, can kuma sai ya kashe gaba ɗaya. yace,"Kana ciwon baki ne?". Turaki yayi masa shiru bai tanka masa ba, idonsa na manne akan titi. Bello yay tsaki,"duk inda ɗan rainin hankali yake daga kanka an rufe ƙofa. banda iskanci tun tahowarmu nake magana but you refuse to answer me, kuma tsabar miskilancinka ya kai intaha ina kallon bakinka yana motsi amma ba zaka faɗi abinda ke cikinka ba...i don't know what is exactly wrong with you, i saw some changes in you tun before na tafi, to ni ba ɗan iska bane da zan ta tambayarka kana min banza". Turaki yace,"ka bani damar magana ne balle na faɗa maka abinda ke cikin nawa?, tun fa da na ɗaukoka ka isheni da Bima Restaurant, sai kace baka taɓa cin abinci ba a duniyarka. tun saukar ka you din't ask about my health, abinci abinci kawai shi ka sani, kai idan kana jin yunwa you see nothing balle ma ka lura da ramewar da mutum yay". yanda yay maganar a ƙufule Bello Ƙaraye ya bushe da dariyar ƙeta, shi dai tunda ya fito a jirgi ya kalla kamar idanun Turaki sun faɗa loko, to amma bai lura da muguwar ramewar da yay ba sai yanzu, yanwa yake ji sosai shi yasa idonsa ya rufe da ganin komai. yace,"to ka bani damar ganin ramar da kayi ne balle nace Muhammad Turaki baka da lafiya ne?, tunda fa da ka ɗaukoni fuskarka take a ɗaure, sannu wannan bata haɗani da kai ba, to ta ina zanga wata rama?, motsin bakinka kawai na lura da shi...anyway what is wrong with you?, did you go to the hospital?". Turaki yay masa wani kallo yace,"ciwon uban me nace maka ina yi da zanje asibiti?, ni lafiyata ƙalau". Bello yace,"ikon Allah, to naji lafiyarka lau. what is the problem?". Turaki yay masa shiru yana kallon titin gabansa, cikin ransa yana tunanin ta inda zai fara yi masa maganar, sarai ya san rainin hankalin Bello, yanzu sai ya faɗa masa kuma ya ɗauki maganar a gantale. ba zai nutsu ya fahimci naganar ba balle ya basa damar fayyace masa komai. Bello dai na gefe yana kallonsa, ganin baida niyyar cewa komai ya ɗaga kafaɗa ya maida hankalinsa kan wayarsa, ko mene idan tayi tsami zaiji, ba zai iya da wannan miskilancin ba, yunwar dake rarakar cikinsa ma ta ishe shi. shirunsu ya ratsa cikin motar, sai can Turaki yace,"just give me your full attention let's talk". yay maganar a hankali. Bello ya kallesa yaga Seriousness ɗin dake kan fuskarsa, sai ya kifa wayarsa a kan cinyarsa yace,"na baka duka attention ɗina, idan ma so kake na cirosa na miƙo maka gaba ɗaya sai nayi hakan". Turaki ya waigo yay masa kallo ɗaya ya ɗauke kai, ya dinga motsa bakinsa kamar bebe, shi yasan hali na rainin hankalin Bello shi yasa yake ta shakkar faɗa masa, he never take things seriously a lokacin da ya kamata. Bello ya katse tunaninsa,"mu tafi Restaurant ɗin kawai, ba zan iya isa gida banci komai ba". sai a sannan Turaki ya buɗe baki yayi maganar da tasa Bello ya zabura, har yana ƙoƙarin miƙewa akan kujera. da wani mugun shock Bello ke kallonsa yana ganin kamar ba Turakin da ya sani ba ne, wannan wani Turaki ne na daban da zai iya aikata abunda yake faɗa, amma nasa Turakin ko da ace giyar wake yasha ba zai iya aikata abinda wannan ya faɗa ba. "what! kace mene?, na kasa fahimtar me kake son cewa". Bello ya tambaya har sannan idanuwansa a waje. Turaki yace,"abunda kaji na faɗa". Bello Ƙaraye ya cire hular kansa yana goge wani uban gumi da ya fara keto masa, ya koma kamar wanda yaywa sarki ƙarya. "wait Turaki! wait!, abar zancen wasa dan wannan maganan naka ba magana bane da za'a ɗauka matsayin wasa...". bai ƙarasa abinda zai ce ba Turaki ya katse shi,"ni dama na taɓa faɗi maka abu a wasa ne? balle ka ɗau maganar nawa a shashance". Bello yace,"to idan ba wasa kake ba Hauka ka yi?, dan maganar da kayi bata masu hankali bace kuma ba magana bace da hankalina zai ɗauka...kasan kuwa me ka faɗa?, Turaki are you in your sense? yaushe lissafinka ya fara kwancewa?". danger ta tsayar da motarsu, fuskar Turaki a ɗaure ya juyo ya kalli Bello yace,"kaga Malam, ban faɗa maka personal issue na ba dan ka dinga min ihu aka ba, idan ka gane fine, idan ba gane ba just keep quite". Bello yace,"ba zanyi shirun ba". yay ɗan jim yana maimaita furucin Turankin acikin kansa, anya kuwa bai sha wani abu ba kafin ya ɗauko sa?. ya ɗaga kai ya ƙara kallon Turakin da tsananin mamakin da yaƙi barinsa, da ƙyar ya iya buɗe baki yace masa,"da sanin wa kuma da izinin wa akai hakan Muhammad?". Turaki yace,"da sanin kaina da izinin kaina ni ɗaya, sai kuma me?, sai akayi ya ya?". da wani mugun jin haushinsa Bello yace,"sai ka yi ba dai-dai ba, kuma tun wuri kaje ka warware kwaɓar da ka aikata kai ɗaya, karma akai gaba naji kana ambatar sunana". murya a sanyaye Turaki yace,"abinda nake ganin ya dace nayi shi nayi Bello, sakayyar da ya kamata nayi kenan Bello, kai kanka ka sani komai da lissafi nake yinsa, bana abunda bai dace ba ka sani. and na san babu wanda zaiyi suppprting nawa shi yasa nayi komai ni ɗaya, even if its you na tabbata hakan zaka aikata...ba zaka gane komai ba sai na maka cikakken bayani Bello, wannan hargagin naka duk ba shi bane, ka fara ɗaukar maganar da nai maka da mutunci sannan sai nai maka bayani dalla-dalla". "bayanin banza Turaki, wane bayani zaka min dalla-dalla da zan fahimce ka?, wait! tunaninka ma kaina zai ɗauki maganar daka zo min da ita ne?, to ba ni kaɗai ba, babu me ɗaukar wannan zancen banzan naka, so tun wuri ma kwaɓar da kaje ka aikata kai ɗaya kaje ka warwareta kawai Malam". a fusace yayi maganar, shima kuma Turaki cikin fusata yace,"Bello Tukur Ƙaraye karka ƙara min ihu acikin mota, karka ƙara ɗaga min murya". shima Bello ya ƙara fusata yace,"Muhammad Turaki Habib ba zanyi ƙasa da muryata ba, kayi duk abinda kake ganin za kayi, ya za'ai ka aikata ba dai-dai ba kuma kace ba zanyi magana ba. tunda dama kasan ba zan goyi bayanka ba ai dole kaƙi yin shawara da ni kaje ka aikata abinda kake ganin ba zai zame maka matsala ba...ni har yanzu na kasa gane menene acikin kanka balle na fahimci kan zancen naka, anya baka sha wani abun ba?". Turaki yay masa banza, Bello ya dinga kallonsa da bala'in mamaki, ko a mafarki bai taɓa zaton Turaki zai iya aikata abinda ya faɗa ba balle kuma a zahiri. shi ya san waye Turaki, tun suna yara suke tare, ya san sarai abinda zai aikata da wanda ba zai aikata ba, and ya san ba zai taɓa aikata abu ba tare da ya nemi shawararsa ba ko kuma ya faɗa masa ba. Turaki baya gaban gansa sai da sanin mutum huɗu, dole Maama ce mutum ta farko da Turaki zai sanarwa abunda zai aikata, sannan shi ya biyo bayanta, sannan Baffa, sannan Zaytuna, dole mutum huɗun nan sai san abu kafin ya aiwatar da yinsa. amma this time around baya zaton cikin su huɗun akwai wanda yasan da wannan batun, sai a yanzu da shi ɗin ya sani, ya san abinda ba zai iya ƙaryatawa ba tunda yaga gaskiyar lamarin akan Fuskarsa da kuma furucinsa. wai har yana faɗa masa abunda ya dace shi nayi Bello?, tukunna ma! Bello ya sauke numfashi yace,"Maama ta sani?, ni ne daka mayar da ni banza yanzu kaje kai gaban kanka baka faɗa min ba?". har yanzu murayar Turaki da sanyi yace,"itama bata sani ba". Bello ya zaro ido,"what!". yace masa,"yes, bata san komai ba akai. kai ɗin ma na faɗa maka ne saboda na kasa riƙe abin ni kaɗai, ban san wane kalar asiri kayi min ba da bana iya riƙe sirrina sai na sanar maka". fuskarsa a tamke yayi maganar kamar yanda muryarsa ma take a tamke. Bello yay ƴar dariya yace,"Allah ka hauka ce ko kuma ka fara shaye-shaye, faɗa min waye ya baka gurguwan shawarar nan na fara shaye-shaye?". Turaki ya kallesa ta gefen ido yace,"Bello ni nake shaye-shaye?, ni kake cewa ina hauka? just saboda na fita hakkinka tunda na san bama ɓoyewa juna komai". Bello yace,"ai mahaukaci ma ba zai yi abinda kayi ba, sai me shaye-shayen dai, dan abinda ka aikata na ƴan ƙwaya ne, wanda yake cikin hankalinsa ba zai taɓa aikata haka ba wallahi...and imagine, ko kunya baka ji ba kake faɗa min wai Maama bata sani ba. so ko me zaka yi a haukace kake sai dai kaƙi yarda, kana buƙatar ganin likitan ƙwaƙwalwa dole". Turaki yay parking motarsa, without looking at Bello yace,"fitar min a mota". yace,"inje ina?". Turaki yace,"kaje inda masu hankali suke". Bello yay dariya sosai, dariyar dake ƙara ƙular da Turaki, ya dinƙa jin wani tuƙwiƙwi a zuciyarsa. Bello yace,"dan Allah dan Annabi ka juyo ka fuskance ni muyi maganar gaskiya, ka faɗa min cewa ƙarya kake yi, becouse the only Turaki i know ba zai yi wannan haukar ba". Turaki ya kallesa yana jin kamar ya bubbuge shi, wani takaicin Bello ya ƙara cunkushe masa a heart. yaja tsaki kawai ya fice daga motar, Bello na kallonsa ya tsayar da me napep ya hau suka bar wajen. ya tafi ya barsa da tunani kala-kala acikin ransa, abunda Turaki yayi sam ba na mutane ba ne. sai kuma yay shiru yana dogon nazari, to ma...sai kuma ya sauke numfashi, da ya sani ya basa damar yi masa bayani dalla-dalla, ƙila ya fahimce shi ɗin, amma duk da haka idan shi ya fahimta ta ya iyaye zasu fahimce shi?, da wanne idon ma zai jewa Hakimi?. fitowa yayi daga motar ya koma driver seat yaja motar, yana ta kiran wayar Turaki amma bai picking ba, kuma yasan yana sane, kuma ko da ace ya bisa gida yanzu ba zai taɓa sauraronsa ba, so gwara ma ya bari sai gobe sa haɗu, saboda haka kawai sai ya wuce gida da motar tasa. **** Fillo na zaune cikin inuwa a filin ƙofar ɗakinsu na ƴan aiki, littafi ne a gabanta da biro a hannunta. bitar karatunsu take yi dan gobe lesson teacher ɗin nasu zai yi musu exams. Ɗausiyya ta ƙaraso wajen itama, ta zauna akan tabarmar kusa da Fillo, ta leƙa abinda take karantawar sannan tace,"yauwa du Allah ki ƙara min bayanin wannan, ni ɗazu duk ban gane ba, ya saka turanci da yawa a maganar tasa". Fillo ta aje littafin, ta falli takarda ta shiga yiwa Ɗausiyya bayani turyan turyan kamar itace teacher ɗin. suna cikin yin karatun ne suka ji wayar ɗakinsu na ringing, Ɗausiyya ta miƙe tana ƙorafin ba za'a barsu su dinƙa hutawa ba, yanzu sai ace suzo suyi aiki yen yen yen. Fillo ta bita da kallo tana faɗin,"ke kuma da samun wuri, dama me kika zo yi idan ba aikin ba". Ɗausiyya ta ɗaga wayar, daga ɓangaren Zaytuna tace da ita,"ina Fillo?". tace,"tana waje tana karatu". tace mata,"kice tazo ta sameni". "tom Anty". ta faɗa tana ajiye wayar ta fito daga ɗakin. inda suke ta koma ta zauna ta ɗauki nata littafin tana sanarwa da Fillo saƙon. Fillo tace,"wacce Antyn?". tace mata,"Anty Zaytuna mana". Fillo ta miƙe tana faɗin,"au nai zaton Anty me dogon baki ce, wallah har gabana ya faɗi". Ɗausiyya tayi dariya tace,"idan itace ai ba zaki ga na dawo yanzu ba, da tuni tana nan tana surfa min zagi ni da iyayena kafin tace min kiranki take". Fillo ma tai dariya tace,"ba kya nan ai ɗazu aka ce mana shegu masu warin baki". Ɗausiyya tace,"sai kika mata shiru baki yi mata rashin kunya ba?". Fillo ta harareta tace,"ai tunda na faɗa miki sai kije ki mata tunda you are the boss". su kai dariya gaba ɗayansu Ɗausiyya na faɗin,"Anty Samha ta mu ta bala'i". kafin nan Fillo ta wuce kiran da ake mata. a ɗaki ta sami Zaytuna tana waya, ta tsaya daga bakin ƙofa tana jiran ta kammala, Zaytuna tayi mata alama da hannu cewar ta shigo ciki ta zauna. ta bar ƙofar a buɗe ta shigo daga ciki ta zauna akan carpet. Turaki yazo shiga ɗakin ganin Fillo sai ya fasa, ya tsaya yana kallon duk su biyun, babu wanda ya gansa kamar yanda basu ji alamar zuwansa wurin ba. yasa hannu ya janyo ƙofar a hankali yanda ba za tayi ƙara ba sannan ya wuce, duk dan kar suga giftawarsa. sanda Zaytuna ta kammala wayar ta dubi Fillo tace,"me kike yi yanzu?". Fillo tace,"babu komai, mun gama aiki, ina karatu ne dama kamin na tafi". Zaytuna tace,"to kinga dama kayan wadrobe ɗin nan zaki gyara min, Hammah na min yankan farce ya yanke ni, na kasa taɓa komai". Fillo tace,"sannu Addah". tace,"yauwa, na gode...idan kika gama ki ɗauki wancan ƙaraman trolly ɗin ki tafi da ita". Fillo ta kalli trolly ɗin da take nuna mata, small size ce kamar waccan da ta bata, tace,"tom Adda, na gode Allah ya saka da alkhairi, Allah ya ƙarawa Baffa da Maama lafiya". Zaytuna tace,"amin...na dai faɗa miki tun ranar nan, duk wasu tsaffin kaya da kika san kina da su ki bayar". Fillo tace,"na bayar Adda, wanda muke iri ɗaya da Maijidda kawai na bari". Zaytuna tai shiru for few seconds kamin tace,"tom shikenan, goben kuzo ke da Maijiddan, ina son ganinta". ta amsa,"insha'Allah Addah". Zaytuna ta shiga toilet, ita kuma Fillo ta fara gyaran da ta sakata. lokacin da Zaytuna ta kammala shiryawa zata fita wayarta tayi ringing, ganin sunan Happiness a jiki tayi saurin picking tana faɗin,"Hammah nah". daga inda yake ya amsa da,"na'am Zaytun". sai kuma tai shiru tana jin cewarsa. ta waigo ta kalli inda Fillo take kafin ta amsa masa da cewa,"to Hammah". ta ƙara yin shiru na few seconds sannan ta ƙara cewa,"to Hammah, nima zan fita ne yanzu sai na dawo". da haka wayar tasu ta katse. tana sa wayar a jaka tace da Fillo,"idan kin gama kar ki tafi kinji, ki kunna system sai ki ƙarasa kallon da kike yi ran nan". wani daɗi ya mamaye Fillo, tana masifar son film ɗin, tun wancan ranar da ta kawowa Zaytuna assignmnt ta tarar bata nan sai Turaki ne a ɗakin, ta juya da sauri zata koma taji ya kirata yace ta dawo, ta shigo ɗakin ta zauna tayi tsilli-tsilli kamar ɓeran da aka girgiza acikin ruwan buta. tun zaman da tai a wurin gaba ɗaya sai ya manta da ita, kallonsa kawai yake acikin system. time to time sai yayi dariya ko kuma yay tsaki, Fillo dai na durƙushe a wurin kamar me neman gafara, kuma tun tana jin tsoro har tsoron ya barta, sai dai taita kallonsa ta wutsiyar ido, tana ƙara jin sabon haushinsa, idan taji yay dariya sai ta tambayi kanta dama yana dariya?. tafi ƙarfin minti goma sha biyar duƙe a wajen, tun tana a takure har ta saki jiki itama ta shiga kallon da yake yi a system ɗin, sai da aka kirasa a waya sannan ya tashi ya fita, ya fita ya barta da ci gaba da kallon, daɗin kallo ya mantar da ita yammar da tai, ta miƙe ƙafafu har sai da cajin laptop ɗin ya ƙare, lokacin ana sallar magriba. kuma sanda ta miƙe zata fita daga ɗakin sai ga shi ya dawo, ya kalleta ya kalla room ɗin, ta dabarbarce tana sarƙe yatsunta, ƙirjinta yana ta bugawa. daga sama taji muryarsa yana tambayarta,"ina Zaytun?". kanta a ƙasa tace,"bata dawo ba". sai yay mata kallon tsab yace,"ke kuma me kike yi anan?". ta ɗago kai tai masa duban mamaki tana saurin ɗauke ido daga cikin nasa da ya kafeta da su, bata bar jan yatsunta ba tace,"kaine ai ka tsayar da ni, kace nazo kuma aka kiraka ka tafi". yay shiru bai ce komai ba, ya juya zai tafi muryata na ɗan rawa cike da tsoro tace,"na tafi?". yace,"a'a kiyi ta zama". daga haka ya wuce ya barta a wurin. ta bar ɗakin da kewar film ɗin da bata ƙarasa gani ba, kuma da ta koma ranar raba dare suka yi tana bawa Maijidda labarin film ɗin, bata ma san ya akai Zaytuna tasan ta kalli film ɗin ba. kanta a ƙasa tana wasa da yatsunta tace da Zaytuna,"Adda ban iya kunna laptop ɗin ba". Zaytuna tace,"kina buɗewa zata kama, Turaki is the password". tace,"tom". sai ta ƙara ce mata,"zaki iya ɗin ko na kunna miki?". tace,"zan iya Adda, Adda Nihal ta taɓa gwada min". Zaytuna tayi murmushi tace,"ranar da kika sa ta dinƙa mana mitar ƙauyancin da kika mata?". kunya tasa Fillo rufe fuska. bayan fitar Zaytuna babu jimawa ta kammala gyaran wadrobe ɗin, ta ɗauki ƙaramar trolly ɗin ta buɗe taga sabbin kaya ne kamar wancan time ɗin da ta bata. abaya guda huɗu sai riga da skirt na material guda biyu da na atamfa guda ɗaya. duka kayan kamar sai da akayi measurement ɗinta, dan babu alamar ma kayan ragesu akayi. cike da farin ciki ta mayar ta zuge zip ɗin, wannan ma rabawa zasu yi ita da Maijidda kamar yanda suka raba wancan. maimakon taja trolly ɗin sai ta ɗauka ta ɗora akanta, ta fito ta rufe ɗakin farin ciki duk yaƙi barinta. zata sauka a stairs sai taji kamar mutum na sauke wahaltaccen numfashi a cikin ɗakin da yake gaba dana Zaytuna. sai taji ta kasa tafiya, ta tsinci kanta da komawa da baya har ta iso ƙofar ɗakin, ta tsaya tana ƙara tabbatar da abunda kunnuwanta ke jiyowa. bata manta da wani lokaci ba da suka zo gyara ita da Ɗausiyya, Nihal ta ke ce musu su gyara kowanne room dake upstairs banda wannan da yake da coffee door, shi ba'a buɗe shi totally. for sure daga room ɗin take jiyo sautin, to anya kuwa daidai ta ke ji acikin kunnuwanta?, ai ranar har suka gama zaryarsu anan basu ji wani abu makamancin haka ba, ta tsaya tana Contemplating ta buɗe ko ta tafi, abunda kunnenta ke jiyowa dai ba na wasa ba ne, ba irin abunda mutum zaiji bane ya ƙyale ya tafi. sai kawai zuciyarta

Chapter 19 of 73