Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
rufe ido tare da haɗiye wani busashshen yawu na takaici, for few minutes ta kalla fadawan dake yin kamar zasu yi mata sujjada ta basu umarnin tafiya. Fillo na kwance kan gado drip na shiga jikinta, drip na kusan huɗu kenan da aka saka mata a yau, daga safiya zuwa yamma. saman room ɗin kawai take kallo, dan su Kaka duk sun tayar da sallah, Maijidda kuma ta tafi raka Amir. hankalinta yana cikin ɗakin amma tunaninta yana waccan ranar da komai ya faru, komai ɗin da har yay sanadin kwanciyarta a asibiti. tunda akayi admiting nata sai jiya ta farka a kwana na uku, mutumin da idanuwanta suka fara gani a lokacin da ta farka likitan da yake dubata. kallo ɗaya tayi masa ta mayar da murfin idonta ta rufe. ƙoƙarinta a lokacin shine ta motsa amma sai taji ta kasa motsa ko da yatsa. Wani irin ciwo jikinta yake yi masa tamkar wadda aka kwan ana duka. da ƙyar ta ƙara iya buɗe idon, jin eyelids nata takeyi kamar an danne su da dutse. ta ƙara sauke idonta akan likitan da har lokacin yake kanta yana gudanar da aikinsa, bata gani da kyau amma gani takeyi kamar ta san fuskar, tana kallo ya ɗauko allura ya zuba acikin drip ɗin dake saƙale. da sauri ta daɗa rufe ido ta juya fuskarta gefe tana sauke numfashi sama-sama acikin tsoro, giftawar second ɗaya ta daɗa buɗewa ta tsaida ganinta a saman rufin ɗakin. ba rufin ɗakinsu bane, aina take?, a hankali ta zagaye room ɗin da idanunta tana so ta fahimci ina ne nan inda take, kuma waye shi wannan mutumin da ta fahimci daga ita sai shine acikin ɗakin. Sai a lokacin tunanin abinda ya faru da ita ya dawo mata. abinda ta fara fahimta shine nan asibiti ne kenan. but taya akayi tazo wajen?, lokaci ɗaya sai hoton fitowarta daga ɗakin Kaka ya haska mata acikin kanta da cikin idonta, a hankali ta mayar da idon ta rufe, nan take komai ya shiga haska mata daki-daki. tasan ta fito daga ɗakinsu, kuma kai tsaye gate ta nufa da ta fito daga ɓangaren nasu, ta miƙi wata doguwar hanya tana ta tafiya ba tare da sanin ina zata je ba, ita dai kawai acikin kanta tana jin ana ce mata ci gaba da tafiya. kuma sai da tazo bakin wani ruwa ta waiga taga ba gini gaba babu gini baya sannan ta fahimci ta baro cikin gida ta kuma baro kusa da gida. fargaba da tsoro suka nannaɗeta, me ya kawota nan ɗin kuma me tazo yi?, ta tsaya tana ta kallon ƙaton kogin, bata san me zata yi ba?, bata san me take kallo acikinsa ba?, a jikinta kawai take jin bata so ta koma gida, kuma zuciyarta na raya mata cewar bata yi sallar la'asar, magriba da isha'i ba, sai dai ba zata yi su ba, dan tun lokacin da ta ɗauke wannan abin daga ɗakin Turaki taji sallah ta fice a ranta. saboda haka sai ta nemi waje ta zauna a gefen kogin, ta zura ƙafafunta cikin ruwan, kamar mahaukaciya kuma sai ta kunce ɗankwalinta ta ajiye a gefe, gashin kanta dake tuje waje guda ya barbaje. har lokacin hankalinta da tunaninta na jikinta amma kamar bata san tana yin komai ba. a gefen wajen ta kwanta inda tayi matashi da ɗankwalinta, bacci take so tayi amma ba zata iya ba, kamar shikenan idanuwanta sun daina rufewa da sunan bacci, tana ji kamar shikenan ta gama rayuwa a Halimanta, kamar zata koma wata sabuwar rayuwar ne. tsawon lokaci taji kamar an mintsineta, hakan yasa ta miƙe zaune a zabure tana karkaɗa ƙafarta acikin ruwan kogin. cikin rawar hannu ta kwance gefen zaninta ta fiddo da wannan abin, ta tsaya tana kallon abun zuciyarta na cika da mamaki, lokacin data ɗaukosa yana da duhu amma yanzu taga yay haske. me kenan?, kafin ƙwaƙwalarta tayi lissafin komai iska ta kaɗa ta kore abin daga kan tafin hannunta ya faɗi ƙasa yana gangarawa gefe ɗaya, da farko tsayawa tayi tana kallon yanda iska ke daɗa kora shi zuwa gaba, daga bisani kuma sai ta tashi zata je ta ɗakkosa, sai dai tana zuwa dai-dai ciyayin da abin ya shige taga wuta ta kama a wajen, kuma ba'a ƙara ko sakan biyu ba hankalinta ya dawo jikinta baki ɗaya. dan haka take a lokacin wani tsananin tsoro ya kamata, ta dinga waige-waige a wajen, ina zata yi yanzu?, babu kowa a wurin nan daga ita sai bishiyoyi sai wannan ruwan. bata san sanda ta fashe da kuka ba, wutar dake ƙara ruruwa ta kusa kamo rigarta tai saurin matsawa daga wurin, kuka takeyi sosai, "Kaka". sunan da take ta ambata kenan, ita bata san ta inda zata bi ta koma gida ba, saboda haka ta zube a wajen tana daɗa fashewa da matsanancin kuka, tsoro na ƙara cikata. tana cikin hakan taji zuciyarta na biyo mata wasu ayoyi acikin alqur'ani da kuma wasu adu'oi dake cikin hisnul muslim, bakinta na karkarwa ta fara biyosu a fili. sai taji komai dake cikin kanta na washewa, haske na zuwar mata, mafita na zuwa cikin kanta. sai tayi zumbur ta miƙe, zuciyarta na faɗa mata ta bar wajen da sauri. tasa hannu ta toshe hancinta saboda warin hayaƙin, wani irin ɗoyi ne yake tashi aciki, tai azamar barin wajen da gudu amma sai taji ƙafarta guda ɗaya ta riƙe, sai sannan ta tuna da ciwon dake ƙafar. amma a hakan ta dinga jan ƙafar tana ɗaga waccan har ta bar wurin, kuma tana zuwa bakin wata ƙatuwar bishiya taji tushh abu ya fashe, bata tsaya ba taci gaba da tafiya, tsoro kuma na ƙara kamata, haka har ta shigo cikin wasu gonaki, ananne tsoro ya tsananta gareta saboda kukan karnuka dake tashi, bata san lokacin da ta kwasa a guje ba ta manta da ciwon dake ƙafarta duk da tana jin zafin ciwon na ratsata. ta fito kan hanya kawai taga fitilar mota na haskawa, da fari kamar ba zata tsaya ba sai ta tsaya tana miƙa hannu don tsayar da motar, dole zata tsaya ta nemi taimako in ba haka bata san ina zatai ba, haka kuma bata san meke cikin wannan dajin ba, komai zai iya faruwa da ita. tana ta ɗagawa motar hannu, so take tai magana amma ta kasa, ga motar ita take tunkarowa, a wannan lokacin kuwa kan Turaki na ƙasa yana ƙaro volume na karatun qur'anin daya kunna, lokacin har ya ƙaraso inda take ba tare daya san da mutum a gabansa ba, a time ɗinne ta fahimci ko waye na cikin motar baya ganin gabansa, saboda haka cikin hanzari ta ɗaga ƙafarta da tayi mugun nauyi zata janye daga wurin, sai dai inaaa, kafin tai wani yunƙuri Motar Turaki ta daki gwiwoyinta ta kifo kan motar tasa. ta san sanda kanta ya ƙwalu a jikin motar, ta san lokacin da ta silalo ta faɗo ƙasa, taga kuma lokacin da tayoyin motar ke ƙoƙarin bi ta kanta. take ta sallama da rayuwar, yau dai tasan babu abinda zai hanata bin Umminta, zata je su rayu tare harda Addarta, zata bisu shikenan sun bar Kaka ita ɗaya. tana kallon tayoyin motar na ƙara motsi suna tahowa zasu talitse kanta, sai dai daga nan, ji da gani da numfashinta duka suka ɗauke. bata san me ya faru ba bayan nan, sai yanzu data farka, ta farka ta ganta acikin ɗakin asibiti, kan gadon asibiti, that means wanda ya bugeta mutumin kirki ne kenan?, shi ya kawota asibitin ko ya?, idan ba shi bane to wa ya tsintota daga cikin wannan dajin ya kawota nan?, ina Kaka?, ina Maijidda?, ina Yami?, ina Amir?, shin wanne hali suke ciki?. shin sun samu labarin inda take?, ko kuma suna can suna nemanta?, wacce amsa zata basu a lokacin da kowannensu yay mata tambaya?. duk ba wannan bama, idan ta miƙe yanzu zata koma gida, ta san kuma amsar tarin tambayoyinsu, ba zata ɓoyewa Maijidda komai ba domin ita zata kawo solution. abun ɗaya ne kawai ke cikin kanta a yanzu itace sallah, sallolin da bata yi ba a wancan ranar na la'asar da magriba da isha. to kwana nawa kenan yanzu?, sallar kwanaki nawa ne akanta?, wa zai bata amsa?, don tasan ba lallai akan lokaci aka sameta ba balle ta iya ƙiyasta wasu kwanakin, kuma dole zata rama sallolin dake kanta. ta kulle ido ta motsa ƙafafuwanta zata yunƙura ta tashi zaune sai taji tamkar zasu karye saboda sandarewa da kuma azabar ciwon da suke yi mata. kawai sai ta fashe da kuka, kuka sosai, likitan daya gama aikinsa ya tsaya akanta, tana jin yanda kallonsa ke shiga jikinta. baice komai ba har sai da ta tsaya da kukan dan kanta ta buɗe idon tana kallonsa, murmushi taga ya sakar mata tare da ce mata. "sorry". muryarta na fitowa da sautin kuka tace,"dan Allah zanyi sallah". murmushi taga ya ƙarayi sannan yace,"za kiyi sallah amma ba yanzu ba, ki bari ko zuwa safiya ne". sai ta koma tana bin ko'ina na ɗakin da kallo, agogo take nema taga lokaci. tace da shi,"me yasa to ba zanyi ba yanzu?". yana kallonta yace,"saboda ba za ki iya ba...". tun bai ƙarasa maganar ba ta kalle shi da idanunta da suka kawo ruwa ta katsesa da faɗin,"zan iya, Allah zan iya". tai maganar tana son fashewa da kuka. Dr Yusuf yace mata,"to shikenan tashi ga banɗaki nan ki shiga, can kuma jakar kayanku ce sai ki ɗau hijab aciki ga abin sallah can". ta kalli inda yayi mata nuni, ta maimaita kalmar jakar kayanku acikin ranta, ta juyo ta kalle shi yana niyyar fita tace,"dan Allah wa ya kawoni nan?". yace,"police da kuma wanda ya buge ki". ta maimaita kalmar a ranta kan tace,"dama ya tsaya?". yace mata,"ehh yana da imani shisa". hawaye na ƙara sauko mata a sanyaye tace,"Kakata fa?". ya juyo ya kalleta sannan yace,"kin fasa yin sallar ne?". ta girgiza masa kai tare da cewa,"a'a zanyi". ta faɗa tana so ta tashi amma tana jin ba zata iya ba, komai yayi mata nauyi kamar an danneta, kawai sai ta saka kuka. Dr Yusuf ya dawo yana bata haƙuri da faɗin,"na faɗa miki ba za ki iya tashi ba, akan aikina fa nake, zuwa wayewar gari insha'Allah da kanki za ki tashi bama sai an taimaka miki ba". bata bar kukan ba tace,"to idan ban kai goben ba fa naje nace da Allah me?, ni dai dan Allah ka taimaka min na tashi na sauke nauyin da yake kaina". Yusuf dai da yaga zasu yi daru da ita kuma ba jin duk wani bayani da zaiyi zata yi ba kawai sai ya sakar mata allurar bacci. baccin da bata farka a shi ba kenan ba har sai washegari da wajen ƙarfe goma, lokacin su Kaka sunzo, tana buɗe ido akan Kaka ta sauke wacca ke zaune kan kujera ta rafka uban tagumi. Maijidda kuma na tsaye jikin bango kana kallon fuskarta zaka san tasha kuka ta gode Allah, itama duk ta faɗa saboda tashin hankalin da suka shiga. Yami ce kawai me ɗan ƙarfin hali da take ta tausar Kaka akan ta daure ta saka abu acikinta tunda likitan yace zata farka. kuma kwana biyu Kakan banda ruwa babu abinda take sha, shima idan tasha ɗacinsa take ji. "Yami ba zan iya sa komai acikina ba sai yarinyar nan ta farka, yau fa kwana huɗu kenan, faɗa mana suke tana raye, ni dai ina tantamar hakan, gwara kawai a faɗa min gaskiya a bar ɓoye-ɓoye aini musulma ce na yarda da mutuwa". Yami dai tayi shiru bata ce komai ba, sai kallonta da ta maida kan Fillon, itama dai ta fara tantama akan maganar likitocin nan, ace kwana huɗu mutum bai farka ba kuma sannan ace yana raye?, to mene amfanin ɓoyewar?. sai kawai ta gyaɗa kai cikin ranta tana faɗin wataƙila kuma ba'a so a ɗora alhakin mutuwar tata ne akan Turaki shiyasa, tasan zasu iya komai tunda suna da uwar kuɗinsu. Fillo da take jinsu a lokacin ta kira sunan Kaka, wani farin ciki ya baibayesu suka yo kanta. Maijidda tayi mata wata runguma har sai da ƙashin bayan Fillo ya amsa. kuma a sannane Amir yazo, tunda ya shigo ya kafeta da ido, kallonsa take shima kallonta yake, zuciyoyinsu na saƙa abubuwa iri ɗaya dangane da junansu. kalmar da Amir ya fara faɗa mata shine,"za ki iya yin sallah?". kai kawai ta ɗaga masa, Yami ta kamata ta sakko a gadon ta kaita banɗaki. lokacin data fito Amir kawai ta gani har sannan yana tsaye idanuwansa duk sun faɗa ciki, kana kallonsa zai baka matuƙar tausayi. shi ya shimfiɗa mata sallaya, ya tayata saka hijabin, yace mata idan zata iya ramawa duk ta rama, idan ba zata iya ba tayi wasu ta bar wasu sai jimawa. tambayar da tayi masa shine,"kwana nawa yau?". "huɗu". amsar daya bata kenan. kuma tunda ta tayar da sallar bata tsaya ba sai data rama duka sallolin dake kanta, har lokacin Amir bai zauna ba yana tsaye. tana idarwa kuma sannu kawai yay mata, zai fice a ɗakin tabi bayansa da kallo tace,"ina zaka?". "tafiya zanyi". amsar daya bata kenan ya fice daga ɗakin bai jira cewarta ba, jikinta yayi matuƙar sanyi, su Kaka suka dawo ciki ta tambayi Maijidda suka ce ta tafi raka Amir. Yami ta zuba mata abinci ta ajiye a gabanta, har lokacin tana kan sallaryar ta miƙe ƙafafunta, da ƙyar tayi sallar, ƙarfin dauriya irin nata kawai. "na ƙoshi Yami". kalmar da ta faɗa kenan, kuma kafin Yami tace wani abu an turo ƙofar ɗakin an shigo, Dr Yusuf ne, suka amsa sallamarsa sannan ya umarci Fillo da ta koma kan gadon za'a ƙara saka mata drip. gadon ta koma ta kwanta, yay mata wasu tambayoyi dangane da yanda take ji tana basa amsa, acikin drip ɗin ya zuba duk alluran da za'ai mata. yana gama saka mata kuma yace da Kaka,"idan ya ƙare a bata abinci taci". da haka ya fita. sai yanzu su Kaka suka sami natsuwa, Yami ta zuba musu abinci suka shiga ciki, lokaci zuwa lokaci Maijidda na lura da ruwan daya kusa ƙarewa. bayan wani lokaci hankalinsu ya karkata ga turo ƙofar ɗakin da akayi, ganin wanda ya shigo da sauri Kaka ta miƙe tana yi masa sannu da zuwa tare da amsar ledojin dake hannunsa. Khalil ya shigo yana ta kallon Fillo, mamakin da kowa yake akanta shine taya akai ta fita acikin wannan daren?, kuma me taje yi a wannan dajin?. shi dai abinda zuciyarsa ke raya masa shine Turaki ne ya ɗauketa zai je ya cutar da ita, Turaki ne yay komai, har yau haka zuciyarsa ke faɗa masa. *Plss Comment, Vote, and Share.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _🤔zato dai zunubi ko da ya kasance gaskiya, ku daina ɗaukar hakki babu kyau ni gaskiya nake faɗa muku, ahh tou🤣, yo kowa ya tashi sai ya wani kama cewa Hajiya Madina kaza-kaza, banda ma dai neman magana yaushe kuka taɓa ganin ta cutar da wani daban balle Turaki da ya gama nannaɗe zuciyarta😒...to a daina gaskiya ban so, duk wanda naji ya ƙara taɓata zan hau bori😭😭..._ *18* After long minutes sai ga Zaytuna itama ta shigo room ɗin, har lokacin Khalil yana nan bai tafi ba, yana zaune akan kujerar da Kaka ta ajiye masa. yana kallon Zaytuna da mamaki yace,"from where?". bayan duk ta gaida su Kaka tare da tambayarsu ya me jiki tace da shi,"bamu jima da shigowa garin ba, so muna sauka a airpot mukai waya da Hamma yake ce min yana nan". Khalil ya ƙara tambayarta,"ya Granny ɗin?". tace,"tana lafiya, duk tana gaishe ku...da ta saka rigimarma sai munzo tare tana so taga Hammah". yace,"Allah sarki Granny, insha'Allahu zan matsa masa akan muje, sai mu dawo a ranar tunda dai am sure ba zai kwana ba". Zaytuna ta cirewa Fillo drip nata daya ƙare yanzu, itama tana tambayarta yanda take jin jikin tana faɗa mata komai da sauƙi ƙafarce dai har yanzu. after five minutes Zaytuna ta yiwa su Kaka sallama saboda kiran da Baffa yake yi mata, tare suka fita da Khalil wanda yake ta mamakin yacca akai har yanzu Turaki bai shigo ba. bayan fitarsu Maijidda ta dafa shoulders ɗin Fillo tace,"mene damuwar?". tace,"me kika gani?". Maijidda tace,"na san dai ba ki da lafiya amma yanayin fuskarki ya nuna akwai damuwa a ƙasan ranki". Fillo ta haɗiye yawu tukunna ta ɗago ta kalla Maijidda sannan tace,"me yake damun Amir?". Maijidda ta tashi daga kujerar da take zaune ta dawo gefen gadon kusa da ita ta zauna, ta kamo hannunta ta riƙe acikin nata tace,"me kika gani?". Fillo ta dake ta hana kukan dake ƙoƙarin fitowa tace,"sannu fa kawai yace min, ina amsawa yasa kai ya fice". "kinyi masa wani laifi ne?". ta girgiza kanta,"a'a ni banyi masa komai ba. kuma ko da ace ma nayi masa ba zai min haka ba tunma daya ganni banda lafiya". Maijidda tace,"to kwantar da hankali ba abinda kika masa, kawai yana cikin damuwa ne akan lamarinki. yace ya kasa fahimtar me ke faruwa, yana ganin kamar mutanen ɓoye naso su shafeki ne tun a wancan ciwon da kika yi, amma wannan karon sai yaga kamar ma sun riga sun shigeki...baki gani ba wallahi yanda yake ta sadaƙa yana sauke miki alƙur'ani, anan fa yake kwana kullum baya tafiya, abinci sai Innarsa tayi da gaske". Fillo tai ɗan jim kafin tace,"to ai ni banda wasu aljanu, hasashensa ne dai kawai". Maijidda tace,"to aikuwa abinda kowa ke faɗa kenan". Fillo ta kalli su Kaka da suke can gefe suna maganarsu, hankalinsu baya kansu gaba ɗaya. murya can ƙasa tace,"Maijidda ina asirin da nace miki zan ɗauke a ɗakin Turaki?". idanun Maijidda a waje take kallon Fillo da al'ajabi, ai dama tunda hakan ta faru ta fara tunanin da wuya idan ba karambaninta ne ya bata damar ɗauke asirin data gaya mata zata ɗauke ba. ita kam ta fara tsorata da lamarin ƙawarta, ta bakin Amir aljanu sun shigeta domin mutum dai ba zai yi abinda takeyi ba. Fillo taja hannun Maijidda da taji tayi shiru,"kina da matsala wallahi, shi yasa wani lokacin da faɗa miki abu gwara shiru". bata bawa Maijidda damar magana ba taci gaba,"na ɗauke asirin harma ya ƙone". "shima ke kika ƙona shi?". ta girgiza kanta,"aa wallahi ikon Allah kawai, ba ki gani ba kamar tashin bom haka yayi tushhh, kinji yanda yake ɗoyi kuwa Allah kika shaƙa kayan cikinki sai sun kusa zubowa...kuma kin san me?". ta faɗa tana muskutawa ta gyara zamanta akan gadon inda ta juyo ta fuskanci Maijiddan. "ina ga wannan asirin ne yake hana Turaki Sallah, ai dama na faɗa miki naji Maama na kokawa da hakan. kinga nima fa tun sanda na ɗauko shi naji bana sha'awar yin sallah kwata-kwata...bari dai mu bar asibiti zan baki labarin komai". ita dai Maijidda tsuru tayi tana zubawa sarautar Allah ido, ta ɗanja baya kamar tana tsoron Fillo ne. muryarta itama a can ƙasa tace,"wani lokacin idan muna magana sai naga kamar bake ba, shi yasa bakina baya rabo da ayatulkursiyu...to Allah dai ya baki lafiya ya rabaki da su lafiya. insha'Allah sai anyi galaba akansu...". bata ƙarasa ba Fillo ta kai mata duka a kafaɗa ita kuma tayi saurin kaucewa tana dariya. "Allah ki bar wannan zancen Maijidda bana so, ba wasa bane wannan, wani yaji ai sai ya ɗauka gaske. ƴar wulƙanci kawai". Maijidda har sannan fuskarta da dariya tace,"yo daga miki abin arziƙi, adu'a fa Haliman Amir?, ina ga ma wannan dalilin Allah ya duba ya aiko Malam Amir gareki, kinga ai sa dinga cin ƙwal uwarsu a hannunsa, dan ba raga musu zai yi ba...waya sa ni ma yanzun ko ba ke bace". wannan maganar tasa Fillo zuro ƙafafunta zata sauko a gadon ta damƙeta, ita kuma tayi wajen su Yami tana ta dariya. Fillo tayi ƙwafa,"Allah kika ci gaba sai na bugo miki wannan ƙarfen". ta faɗa tana nuna ƙarfen da ake saƙale drip a jikinsa. Kaka dai idonta na kansu tun ɗazun, tana jin zuciyarta na washewa daga damuwar dake tare da ita, sai yanzu hankalinta ya dawo jikinta. ko babu komai tasan Fillo ta sami lafiya, abu ɗaya yayi saura, matsalar jinnu da suke tunani sun shafeta. Fillo ta rafka tagumi tana tunani Kaka ta miƙo mata abincin da bata ci ba ɗazu, ta ɗago tana ɗan yamutsa fuska, murya a narke da shagwaɓa tace,"Kaka na ƙoshi fa". Kaka tai mata wani kallo tace,"amsa kafin ranki ya ɓaci, kin farka za ki ɗora daga inda kika tsaya ko. wadda bata tausayin kanta kawai". Fillo na turo baki ta karɓi plate ɗin. "wallahi ki cinye shi kafin na dawo". Kaka ta faɗa tana kaiwa ƙofa. Yami ta miƙe tabi bayanta suka fita tare. a bakin ƙofar suka tarar da Turaki wanda jin zasu fito yay saurin matsawa daga jikin windon da yake tsaye a wajen tun ɗazu. suna ƙoƙarin durƙusawa ƙasa su gaida shi ya dakatar da su. "dan Allah Kaka bana son kuke tsuguna min irin haka, ni fa jikanku ne, ku daina kallon wani matsayi da nake da shi, mutum nake kamar kowa". Yami tace,"ranka ya daɗe kallon matsayi ai ya zama dole kam. kai ɗin ne dai ka fita daban da sauran da suke da irin matsayinka. kuma muna godiya a gareka bisa kyautata da mutumtawa, Allah ya haɗaka da mace ta gari". Kaka ta matsa daga bakin ƙofar tana basa hanya. "ka shiga ciki yallaɓai bismilillah, ai tama farka tun ɗazu, jiki da sauƙi kam". idonsa na kan handle yace,"to masha'Allahu, Allah ya ƙara lafiya...ina dai daɗa bada haƙuri Kaka". Kaka dai bata kallonsa tace,"kai haba ranka ya daɗe wane mutum, aimu wannan tsautsayin abun farin ciki ne garemu. in banda haka ina ma za'a ganta?, da yanzu muna cikin tashin hankali". bai ce komai ba ya kama handle ɗin ya buɗe ƙofar, su Kaka kuma suka wuce bayan sunce masa zasu je ɗaya ward ɗin ne zasu yo dubiyar wata Ƴar Ƙawarsu da aka yiwa aiki ta haihu ɗan yazo babu rai, yayi musu a dawo lafiya sannan suka wuce shi kuma ya shiga room ɗin. Maijidda nata fama da Fillo kan taci abinci amma taƙi, bai maida ƙofar ya rufe ba, kawai ya tsaya yana kallon Fillo kamar ɗazu daya tsaya. yana kallonta ta window sanda suke abinsu ita da Maijidda. shi mamaki ta basa sosai bai yi tsammanin ma yarinyar na magana ba, da sakewa irin haka, zatonsa a tsorace take ko da yaushe irin yanda ya saba ganinta. idanunsa suka nuna masa irin ramewar da ta ƙarayi, ƙasusuwan jikinta tsab zasu lissafu, idonta ya faɗa yayi loko kamar yanda yaga nasa yayi daya na duba madubi ɗazu. basu san ya shigo ba sai da Maijidda ta miƙe tana faɗin,"kiran Amir zanyi na faɗa masa kinƙi cin abincin, shi kya ji maganarsa tunda kina sonsa". ta harareta tace,"ku kuma da banji maganarku ba bana sonku kenan?". Maijidda ta ɗaga kafaɗarta,"alama ta nuna hakan". Fillo tai shiru ta maida ƙafafunta kan gadon ta jingina da pillow, sai lokacin Turaki ya tura ƙofar ya rufe ya ƙarasa shigowa. dukansu suka kai idonsu bakin ƙofar, gaban Fillo ya faɗi, taji wani tsoro ya kamata. ta wutsiyar ido yake kallonta, kuma yaga wannan tsoron a idonta wanda bai gani ba a ɗazu da take tare da ƴar'uwarta. da sauri Maijidda ta aje abincin dake hannunta ta durƙusa tana gaishe shi, ya amsa muryarsa bata fitowa sosai. ta miƙe ta ɗauki kujera daga gefen gadon Fillo ta kai masa, amma sai bai zauna ba. Fillo dai da bata san ma shi ya kaɗeta ba, dan ba'a faɗa mata ba. tana dai cike da mamakin waɗanne irin mutanene su, ita ba kowan komai ba garesu amma sai zuwa suke suna dubata, taji su Kaka sunce jiya da yau ne kawai Hajiya Madina da Baffa da Boɗejo basu zo ba, amma hatta Hakimi kansa sai daya zo, kuma shima Mai Martaba sai daya aiko iyalinsa suka zo. ƙwarai kirkinsu ya wuce tunanin mutum, kuma la shakka ba zasu taɓa faɗuwa a rayuwa ba sai da cigaba. ba tayi zaton ma Turaki zai iya zuwa dubata ba tunda wanda bai sonka baya sonka, no matter what happen to you ba zai nuna tausayinsa akanka ba. zuro da ƙafafuwanta tayi daga kan gadon zata sauko ta gaishe shi, sai taji muryarsa kamar a saman kanta yace,"ki sauko kiyi me?". bata ɗago ta kalle shi ba tace,"zan gaishe ka ne". idonsa har lokacin na

Chapter 14 of 73