zafin nama ya damƙota ya sunkuceta bai direta ba sai da suka bakin ƙofa, bai ma san ashe a buɗe ya bar motar ba, yana zuwa ya buɗe front seat ya tankaɗata ciki yasa key ya rufe, dan yasan tsab zata iya guduwa before ya zagaya side ɗinsa.
Fillo ta saki wata razananniyar ƙara tana ƙwala kiran Umminaaaa, ƙarar da ta fito tun daga cikin motar har waje, hakan ya ƙara ƙular da shi, yaji kamar ya buɗe ya fito da ita ya rufeta da duka, yay saurin zagayawa side ɗinsa ya buɗe ya shiga gudun karta cire lock ɗin, ya doka mata tsawa sosai da cewa.
"za ki rufe min baki ko saina farfasa miki shi?".
ta ɗago kanta daga jikin glass ɗin da ta kifa, ta waigo tana kallonsa da ƙwayar idonta da tayi jajir, numfarfashi kawai take saukewa kamar wacce tai tseren gudu, magana take so tayi masa but ta rasa ta yanda zata furta saboda neman shiɗewa da take yi, ta kasa cewa komai sai yarfar da ɗayan hannunta da take yi.
ya ɗauke idonsa daga kanta yana kallon wurin da suka tsaya kwanaki ita da Amir, sannan ya mayar inda suka tsaya yanzu ita da Dr Yusuf, tukunna muryasa ta fito da wani irin amon sauti dake shaida bala'in kishin da ke cinsa da kuma ɗacin dake ƙasan zuciyarsa yace,"ke akuyar ina ce da kowanne jaki zai dinƙa zuwa wurinki?, mutuncinki kika siyar ko me da ba za ki iya kame shi ba?, abinda ya faru dake last bai isa kiyi hankali ba shine har kike ƙara sauraron wani namijin saboda baki da hankali, ke kinfi gane kiyita tallan kanki a titi ko?, ko ce miki akayi ƙofar gidan Alƙali matattarar ƴan iska ne da za ki dinƙa tara mana banzaye?".
Fillo ta kasa jurewa azabar da take ji yana shigarta, ta miƙa hannu ta damƙo kafaɗarsa, wannan yasa maganarsa ta katse ya juyo yana kallonta, sai yaga tana ta kallonsa tana hawaye kamar an kunna famfo, yaga jikinta ya saki gaba ɗaya hannunta na barin jikinsa ya faɗi, yaga ta kwantar da kanta a jikin kujerar idanuwanta sun lumshe numfashinta na fita da ƙyar.
sai yaji kamar tsoro ya kamasa, yay sauri kai hannunsa saman fuskarta, jin kamar bata motsi sai ya ruɗe ya shiga kiran sunanta yana girgiza fuskarta. shiru bata amsa ba kuma kamar bata numfashi balle ta motsa, lokaci ɗaya hankalinsa ya tashi ya tattaro ƙafafunsa ya haye kan kujerar gaba ɗaya yana ƙoƙarin janyota jikinsa, can ƙasa yaji muryarta ta fita a wahalce da cewa,"hannuna". ta faɗa tana kama gaban rigarsa ta riƙe.
yace,"what?". ta ƙara cewa,"hannuna". ta faɗa tana fizgar numfashi.
a burkice yace,"hannunki?, me ya sami hannun naki?". bata iya ce masa komai ba sai rufe ido da tayi ta ɓingilar da kai a jikinsa.
sai ya kamo hannunta dake jikinsa ya duba yaga babu komai, ya kai hannu zai kamo ɗaya kawai sai ƙwayar idonsa ta sauka akan yatsunta dake jikin ƙofa ya ɓame da su, bai san lokacin da ya furta,"innalillahi wa'inna ilaihi waji'un". a matuƙar gigice ba ya saketa daga jikinsa.
da sauri ya buɗe murfin motar, daidai lokacin ta sauke wata wawiyar ajiyar zuciya ta wahala, gumi ya keto masa kamar yanda itama ta haɗa uwar zufa duk da ac ɗin dake cikin motar, ya kamo hannun yana duban yatsun, sunyi jazur jini ya tare a waje ɗaya, fatar da farcen sun haɗe sun laguɓe, siririn ƙashin wajen kamar ya karye, sai kawai ya rufe idanunsa yana kai yatsun ya saka su cikin bakinsa, ya cika bakin da iska ya hura musu iska, ɗumin iskar ya ratsa yatsun har ɓargon jikin Fillo.
tayi wani zullo a jikinsa saboda tsananin azaba, ta saki sabon kuka tana cewa,"da zafiii". ta faɗa da ƙyar cikin mawuyacin hali.
ya rugumeta sosai yana ɗora haɓarsa kan fuskarta yace,"am sorry Fulaniii, i didn't do it to you on purpose, please am very sorry".
yaji yacca tai wata iriyar shaƙuwa, irin shaƙuwar dake fitowa ba saboda ƙishirwa ba sai dan tsananin azabar da mutum ke ji, ya rumtse idonsa sosai yana cije leɓensa na ƙasa, yana jin kamar duk duniya ya rasa jin daɗinsa har mutuwa.
wucewar sakanni 30 ya miƙa hannu ya ɗauko wayarsa ya kira Zaytuna, tana ɗagawa bai ko amsa sallamarta ba yace,"fito da sauri".
Tsantsar damuwar data tsinta a muryarsa ita ta shaida mata babu lafiya, kuma ita tasa ta fitowa da gudu bada sauri ba, tana zuwa bakin motar ta leƙo tana cewa,"Hammah lafiya?". ta tambaya da fargaba ganin tashin hankali shimfiɗe a fuskarsa.
bai amsa mata ba ya fito daga motar ya zaga ya ɗauki Fillo ya shiga baya da ita, sannan ya iya cewa da Zaytuna,"mu wuce asibiti". ya faɗa muryarsa a sama kamar ita ke da laifin.
akan hanya tana tambayarsa me ya faru amma bai iya ko amsa mata ba, sai jijjiga Fillo yake a hankali kamar yanda ake lallashin jaririn da ake son yay bacci, kuma har suka isa asibitin yatsun Fillo na cikin bakinsa kamar yanda take rungume tsam ajikinsa tamkar zai sakata cikin ƙirjinsa.
ba asibitin su Dr Yusuf suka je ba, dan gani yake idonsa idon Dr Yusuf ba za'a kwashe ta daɗi ba, wani abokinsa ya kira Allah ya taimaka yana asibitin, allurar lidocane aka yi mata don kashe zafin wajen, aka haɗa mata da drugs na pain reliver, duk tsoronta da allura amma ko kusa bata yi kuka ba saboda wahala ba zata barta yinsa ba, tanalafe jikin Turaki sai kallo da ido kawai, haka ma maganin da Zaytuna ta bata tasha sam bata iya musawa ba, ta zama kamar hoto sai kallon Turaki da duk ya hargitse take yi.
ya sauketa daga jikinsa ya zauna da ita kan kujera ya fita cikin sauri, in few minutes sai gashi ya dawo da malt da madara peak kamar wanda likita yace masa tana da buƙatar jini.
Zaytuna dai sai kallonsa take yi tana murmushi tana kuma tausayinsa, ganin yacca duk yake ta abu kamar ba Hammansu da ta sani ba, ko su suka ji ciwo ko rashin lafiya baya wannan rawar jikin akansu, akwai shi dai kulawa kamar me ba irin wacca take gani a yanzu ba.
ta bisa da kallo har ya isa dispenser ya ciro cup ya haɗa malt ɗin da madara, ya durƙusa gaban Fillo ya kama hannunta ɗaya yana murzawa tare da kai cup ɗin bakinta, idonta ƙyam akansa da rashin makamar ma wanne irin tunani zata yi, ya kwantar da murya cikin sigar roƙo da lallashi yace,"please kisha kaɗan". ta girgiza masa kai idonta na tara ruwa, yay saurin saka handky ya matse hawayen yana cewa,"kukan ya tsaya haka please bana so, ciwon zai warke yanzu, aima ya kusa daina zafin ko?". sai kuma ya ƙara kai cup ɗin bakinta yana cewa,"please drink a little".
yacca face ɗinsa tayi turning zuwa na ban tausayi da kuma magiyar da yake yi mata yasa ta buɗe bakin ta sha kaɗan. yana ganin ta kau da kai ya miƙawa Zaytuna cup ɗin ya ɗora hannayensa saman ƙafarta yace,"am sorry pleaae forgive me, ba da niyya nai ba ban san hakan zai faru ba".
ya miƙe ya fita ya dawo, lokacin Dr Anwar ya gama shafa mata wani magani a wajen, Turaki ya kasa tsayuwa waje ɗaya sai durƙusawa da ya ƙarayi agabanta yana riƙe hannun a hankali yace,"zafin yana raguwa?".
tana kallonsa kawai wasu sabbin hawayen suka sauko mata, wannan ya ƙara rikita shi ya miƙe yana ɗagata ya rungumeta a gaban mutane dake ta wucewa.
"Fulanii bana sane, am sorry dan Allah".
yanda taga duk ya gigice ɗin nan ya ruɗe ta tabbatar da baya sane ɗin, dan haka kawai sai tai masa knodding kanta dake ƙirjinsa, tausayin kanta take matuƙa amma ji take kamar tafi tausayinsa saboda ganin kamar ma kuka yake so yayi koma yayi bata sa ni ba, so take ta zame daga jikinsa amma ya hana hakan, har sai da Zaytuna ta dawo daga pharmacy tukunna ya saketa ya duƙa ya sunkuceta kamar wata ƴar baby, tana ta kai masa duka kan ita ya sauketa amma yaƙi har suka zo mota. sai da suka shiga mota ta kallesa suka haɗa ido ta hararesa tana murguɗa masa baki tace,"ni nace maka bana son irin haka ba kyau".
tun ɗazu sai yanzu ya ɗan sami relief jin muryarta da yay, murmushi ya sauka a leɓensa ya kai hannu zai shafo fuskarta ta ture hannun tana cewa,"nace ma ba kyau". a wannan karon kawai sai ya saki murmushi me gaba ɗaya yace,"to naji".
cikin allurar da akayi mata dama har da ta bacci, so ko doguwan tafiya basu yi ba bacci ya ɗauketa, ya kwantar da ita sanda yake nunawa Zaytuna wani suya spot yana cewa ta tsaya a wajen.
haka ya dinƙa tsayar da Zaytuna yana siyan kalolin nama a duk suya spot ɗin da ya gani, Fillo dai nata bacci bata san me ake ba, fruites ɗin ma da ya siya kamar me kafa tebur, a ƙarshe ya shiga wani store ya kwaso uban choculates kamar zai buɗe sabon kanti da su, gaban motar nan dai sai da ya cika maƙil da uban kaya kace mara lafiyan da ya shekara a asibiti za'a kaima.
akan cinyarsa taita baccinta har suka iso gida, yace da Zaytuna ta zagaya ta can bayan part ɗinsu tayi parking acan, lokacin yamma tayi ana gab da magriba garin yayi duhu, ya fito ɗauke da Fillo ya shiga ta ƙofar da babu me ganinsa ya shiga part ɗinsu, Bello ya tarar zaune a parlonsu ya ɗauke kansa kamar bai gansa ba yay bedroom ɗinsa, akan gadon ya kwantar da ita yaja blanket ya rufeta da shi yana yi mata peck a kumatu.
Zaytuna kuma ta dinƙa shigo da uban kayan da ya siya tana ajiyewa, ta tsaya tana kallonsa yanda ya zube a gaban gadon gwiwoyinsa duk a ƙasa ya riƙo hannunta yana kallon fuskarta kamar zai haɗiyeta, ko me neman gafara ko wanda akace in ya tashi za'a saceta, ta sauke numfashi tana tunanin ta yanda za'a faɗi wannan aure dai, da kuma yacca za'a karɓe shi, sannan ta ankarar da shi cewa an fara kiran sallah a masallaci.
kansa kawai ya gyaɗa mata alamar yaji, ita kuma tasa kai ta fita daga ɗakin haka kawai tana jin faɗuwar gaba da kuma tausayinsa.
da ƙyar ya iya miƙewa yaje yayi alwala ya fito shap shap, ya ƙara zubewa a gaban gadon yana shafa fuskarta, ji yake kamar ya bari kawai yay sallarsa a gida ba sai yaje masallaci ba. ya kamo hannunta me ciwon wanda hakan yasa ta ɗan motsa amma bata tashi ba, sai ya dakata da motsin da yake yi, ya dinƙa kallon yatsun yanda suka koma, ta ƙara basa tausayi sosai yana jin kamar ya ciro zafin ya dawo da shi jikinsa, yana jiyo sautin ƙarar da ta ƙwala tana kiran sunan Ummi.
jin ƙarar buɗe ƙofa yasa shi waigawa, ganin Bello yasa ya miƙe da sauri yana haɗe rai tare da ɗaukan keys ɗin room ɗin yace da shi,"lafiya?".
Bello ya kalli Fillo sannan ya kallesa yace,"uban me ka yiwa ƴar mutane?". Turaki yace da shi,"ina ruwan munafuki da abinda ya shafeni ni da matata".
Bello yay dariya yace,"you find the solution right?".
yace,"you don't have any access to worry about that, its my personal issue, so get out".
ya faɗa yana nuna masa ƙofa.
Bello na kallonsa ido waje yace,"in fita daga ina?".
Turaki ya kuma ɗaure fuska yace,"i don't want to waste my time masallaci zanje, dan Allah fita". ya faɗa yana tura Bello.
a ƙufule Bello yace,"dilla Malami alwala zanyi ko baka ji ana kiran sallah ba ne".
yace,"ba anan kaɗai ne akwai famfo ba, in ba zaka iya shiga other toilets ba sai ka bari kayi a masallacin, ko in kaje gidanku kayi".
Bello na ƙunshe dariyarsa yace,"ban key ɗin zan rufe idan na gama".
Turaki yay masa wani kallo yace,"ka rufe ina in ka gama?".
yace,"to ai naga kamar saurin da kake yi ne yasa ba zaka iya barina nai alwalar ba".
Turaki ya juya ya kalla Fillo dake baccinta peacefully, yay ƙasa da muryarsa yana cewa da Bello,"kayi a hankali mana karta tashi, dan Allah dan Annabi kayi haƙuri kaje toilet ɗin Khaleel ko na Sameer kayi".
da rainin hankali Bello yace,"to ni anan naga damar yi dan haka ba inda zanje, mene za'a ɓoyen da za'a hanani alwala, shigowarka ai bai isa har ka aikata wani abu ba".
Turaki ya rumtse ido yana jin kamar ya saka masa ƙafa yace,"kaiwa Allah ka bar ɗakin nan Bello, baka san zafin da nake ji a zuciyata ba kana kalle min matata kwance akan gadona, kai baka san haramun bane hakan?, Allah banda bana so ta tashi tuni nasa maka ƙarfi ka fita".
Sai da Bello yaga ransa ya ɓaci sosai sannan ya juya ya fita, yana faɗin,"sannu me mata". Turaki ma yabi bayansa da sauri yasa key ya rufe ƙofar.
yana kallon Bello dake tsaye ta ƙasan ido yace,"maye kawai". Bello yay ƙwafa yace,"ka buɗe ɗakin sai in nuna maka ƙarshen maita a gaban idonka". Turaki yaja tsaki yay gaba bayan yace masa,"mahaukaci, kuma ka bar min ƙofar ɗaki in ba haka ba na dawo na sameka Allah sai na ji maka ciwo".
ana idar da sallah ko cikakken azkar bai yi ba ya baro masallacin, kuma tun bai shigo gida ba ya kira Zaytuna yace ta kira Ummi ta faɗa mata Fillo zata kwana a wurinta.
Zaytuna da ɗan tsoro tace,"but Hammah kasan at any time Mum zata zo ɗakinka ko".
yace,"zance mata zan kwana office saboda wani aiki".
yana faɗar hakan ya kashe wayarsa yaci gaba da tafiya a gaggauce, a parking lot ya sami Bello ya fito zai tafi, bai ko tsaya ba ya wuce shi fuskar nan babu ko annuri kamar bai taɓa sanin Bello ba, Bello ya bisa da kallo yana dariya sosai.
sai da yay me isarsa sannan ya ɗaga wayarsa ya kira Turaki, yana picking yace masa,"in tafi?". yace,"ehh tafiyarka". daga yanda yake maganar a daƙile yasan haushinsa yake ji. yace,"baka buƙatar shawarar tawa kenan?". yace,"ehh bana buƙata". ya faɗi hakan yana kashe wayar.
tun a masallaci hankalinsa ke kan Fullo, yana tafiya yana haɗa hanya saboda rashin ganin hanyar da kyau, hoton fuskarta kawai ke haska masa, a yanzu ma da zai buɗe ɗakin hannunsa duk rawa yake yi. yana buɗewa ya ganta tsaye a bakin ƙofar kamar dama jira take yi a buɗe, ganin tana neman saka kai ta fice yay saurin tura ƙofar ya saka key ya kama hannunta ya kaita bakin toilet yace,"shiga ki alwala".
ya faɗa yana tamke fuskarsa dan yaga kamar sai yayi hakan tukunna zasu dai-dai da ita.
kuma bata musa ba ta shiga toilet ɗin jikinta sai kyarma yake, ba jimawa ta fito tana kyaɓe fuska kamar zata yi kuka tana yarfe hannun me ciwo, ya kamo hannun ya dinga hura mata iskar bakinsa me ɗumi har sai da ruwan wajen ya tsane tukunna ya ƙyaleta. ya riƙe hannunta yaje ya shimfiɗa mata darduma ya buɗe closet ɗinsa ya ciro sabon hijab da Granny taje saudiyya ta taho dasu ta raba musu tace suyi kyautarsa, shi kuma baida wanda zai bawa hakan yasa ta ajiyarsu suna nan kusan guda biyar.
Fillo taƙi karɓar hijab ɗin har hannunsa ya ƙage, ya ƙara ɗago da hannun ya miƙa mata taƙi karɓa, shi dai ya san mayafinta na mota balle tace da shi zata yi.
ita ko ta bisa da kallo da mamakin zuwan hijab cikin kayansa, zuciyarta taji tana neman dasa mata wani banzan tunani tayi saurin kawarwa, itama ta haɗe rai daidai da yanda ya haɗe nasa ta turo baki ta bar kusa da shi ta tafi kan dardumar tana kunce ɗankwalin kanta ta yafa.
kawai sai ya tsaya yana kallonta da mamaki baki a buɗe yace,"a hakan za ki sallar?". ta ɗaga masa kai kawai, abinma sai ya kusa basa dariya, ya tafi yaje ya tsaya ta gabanta yana ƙare mata kallon mamaki da kyau, bilhaqqi da wannan guntun mayafin zata yi sallar tunda gashi har kabbara tayi, mamakinsa bai ƙare ba kawai yaji ta fashe da kuka tana cewa,"to ni ba zanyi da wannan hijab ɗin ba".
ya kalli hijab ɗin ya kalleta sannan yace,"ba'a sallah da irinsa ne?". ya tambaya da gaskiyarsa saboda irin me kwalliyar nan ne na saudiya.
taja majinar hancinta tace,"ni kawai ba zanyi da shi ba". ya ƙara gyara zaman hannunsa a ƙirji yace,"saboda?". tace,"to ai ban san na waye ba". yace,"aina kika ga na ɗauko?". ta ɗan kallesa tace,"to me zai kawo kayan mata cikin kayanka?". yace,"sawa nake idan zan fita".
bata kulasa ba kawai ta tsuguna ta ɗauki dardumar ta bar wajen ta sauya wuri, zata tayar kawai taji ya saka mata hijab ɗin yana gargaɗinta akan,"Allah kika yi gigin cirewa sai na ji miki ciwon da yafi na ɗazu". ta kallesa tace,"da ma kana sane?". ya bar wajen yana faɗin,"ehh ina sane sai ki rama".
tai masa shiru ta tayar da sallar, saboda bata son lokaci ya ƙure mata shisa ma bata sa masa darun sai ya buɗe mata ƙofar ta fita ba. tana idarwa ta yasar da hijab ɗin a wajen ko adu'a bata tsaya yi ba ta nufi ƙofa, ta dinga murɗa handle taji ta kasa buɗewa, sai tayi ƙasa da murya ta shiga roƙonsa tana cewa,"dan darajan Allah kazo ka buɗe min, Maama ce fa ta kirani kuma ko wurinta banje ba, kaje ka ɓallo min yatsuna, kuma ni Allah bana so kake min irin haka, na faɗa maka bana so babu kyau kana kawo ni ɗakinka ka kulle, babu kyau kana taɓani, kuma ai yanzu kai ba yaro bane tunda ka yi aure ka daina irin haka".
ya ɗaga ido yana kallon yanda ta rufe ido tana ta maganar kamar me shirin sa masa duka, yaci gaba da buɗe ledar kazar da ya ɗauko yace,"zan buɗe miki amma sai in kiyi duk abinda nace".
tace,"ai nasan halinka". yace,"wane hali gare ni?". tace,"ai ko nayi ba zaka buɗe ba". yace,"ki ci gaba da saka ni magana kici gaba da zama anan, tunda nace miki zan buɗe ai zan buɗe, but in kinyi abinda nace".
tana hararsa tace,"to rantse da Allah". kamar ƙaramin yaro yace,"Allah da gaske". tace,"to me zan maka?". ta faɗa still tana tsaye bakin ƙofan, ya kalleta yana ɗan ƙunshe dariyarsa yace,"to anan zan saki aikin?". ta turo baki gaba ta taho kamar mara laka, har ta ƙaraso inda yake bai ɗauke idonsa akanta ba. ta tsaya ƙeƙam akansa yace,"hau saman kan nawa sai ki tsaya da kyau".
ta shiga dukan ƙafa a ƙasa tace,"wai mene hakan?". ya jawo ledan fruite ɗin yana yanka abarba yace,"abinda yay hakan shi yay hakan, sai an tambayeki tare aka haife ku da Kuka kice ba haka ba".
yaci gaba da yankan lemonsa yana kallonta ta gefen ido, ganin zata bar wajen yace,"dawo". ta tsaya ya ɗago yana mata nuni da gefen gadon yace,"zauna". kamar zatai masa musu sai kuma ta zauna tana aikin kumbure-kumbure.
zai kama hannunta ta janye tana neman fashewa da kuka tace,"nace maka babu kyau, Allah zan faɗawa Mum". ya ɗaga gira ɗaya yace,"i will escourt you". ta langaɓar da kai cikin wata iriyar shagaɓar da bata san sanda tai ba tace,"Allah to sai in faɗawa Baffa".
da sauri ya zaro ido waje yace,"kice masa me?". tace,"ince masa Turaki yana taɓani kuma har kulleni yake a ɗakinsa". ganin da gaske take maganar yay saurin cewa,"Allah ya baki haƙuri".
ya faɗa yana dawowa gabanta ya gutsuro kaza ya kai bakinta,"wannan za ki cinye sai in barki ki tafi". ta kallesa ta kalli gudar kazar sannan tace,"duka?". ya girgiza kansa,"a'a iyaka yanda likita yace kici". ya faɗa yana kama hannun ciwon da ƙara cewa,"wai sai kinci iyakar yanda fatar nan da ta loma zata ciko".
ta kalli yatsunta da fatarsu ta shafe sannan ta kai hannun hagunta zata karɓa ya janye yace,"kafirai ke cin abinci da hannun hagu, kawai ki yarda in taimaka in baki tunda dai baki da hannun musulmai".
ba yanda ta iya haka ta dinga amsar naman da ya gutsuro yana bata, tun tana kawar da kai tana ƙin karɓa har ta gaji ta dinƙa karɓa a dole tana ci, bai ƙyaleta ba sai da yaga taci da yawa sannan ya ɗauko madarar kwali ya bata itama sai da tasha rabi sannan ya yarda ya barta, ya bata ayaba da kankana suma tasha tana jin kamar zata yi amai saboda ƙoshi, ita dai kallonsa kawai take yi tana jin wani irin abu tare da ita.
ya tattare komai ya kaisu gefe sannan ya ɗauko jakar uban choculates ɗin ya ɗauko ɗaya ya buɗe ya kai bakinta, ta kauda fuska tana yamutsa fuska tace,"na ƙoshi fa, zanyi amai". ya ɗauke yana faɗin,"ashe ba ki shirya fita a ɗakin nan ba".
da sauri ta janyo hannunsa ta kai choculate ɗin bakinta ta gutsura sai ɓata fuska take yi, a haka sai da ta shanye guda ɗaya tass tukunna ya kafeta da ido yana kallonta da wani sihirtaccen murmushi.
bata hanasa kamo hannunta me ciwon ba, ya tmbayeta,"yana zafin ko ya daina?". tace,"yana zafi sosai dauriya kawai nake yi, kaine ina ta maka alama ka datse min hannu amma baka gani ba kaci gaba da masifarka, dan Allah ka mayar dani wajen likitan ya yanke min su na huta, kuma dan Allah ka rage masifa in ba haka ba wataran zaka iya ɓallani gaba ɗaya".
ya shafo wuyansa yana wani irin murmushi da yake jin yana motsa ilahirin jikinsa da wani feelings na daban.
sai taga ya sauke daga kan stool da yake zaune ya zauna gaban ƙafafunta, sannan ya ɗora kansa da hannunsa ɗaya kan ƙafafunta yace,"idan aka yanke kuma da wanne za kike wa mijinki ƙunshi yana kallo yana jin daɗi?, a barsu dai insha'Allahu zuwa safiya zasu daina zafin".
ta ture kansa da ɗayan hannun tace,"ka ɗagani ba kyau". ya riƙe hannun ya mayar da kansa yana cewa,"naji, Allah kuma kika ƙara ce min ba kyau sai kin kwana a dakin nan yau".
tai shiru tana sakin kukanta mara sauti, ya ɗago kansa haɓarsa kan gwiwarta yana kallonta sosai yace,"ai dama ranar nan kince min ni ke saki kuka, dan haka yi me isarki tunda yau Allah ya haɗa mu".
da mamakinsa sai yaga ta saki kukan sosai, sai turesa daga jikinta take yi, tana so ta tashi, shi kuma har ga Allah yau karo na farko kenan da yaji kukan nata na masa daɗi saɓanin da sai ya dinga kukan na haifar masa da jin zafi a zuciyarsa.
har tsawon minti uku bai daina kallon yanda take da bakin kukan ba kamar yarinyar ƴar 3years, yasa wayarsa yana ta mata vedio, dan kansa dai yaji kukan ya fara taɓasa tukunna ya tashi ya kamota ya miƙar da ita.
jikinsa ya janyota ya rungumeta yana lallashinta yana bata haƙuri, ita dai bata daina kukan ba kuma ba tai ƙoƙarin fita daga jikinsa ba.
a ranta kuwa rayawa take yau babu abinda zai hanata faɗawa Maama irin wannan abinda yake mata.
ya kai bakinsa saitin kunnenta ya kira sunanta, tana shagwaɓe murya tace,"ni Fillo sunana ba Fulani ba". yace,"ba haka naga damar faɗa ba". ya faɗa yana kai hannunsa saman sumar kanta. tasa ƙarfi tana ture shi tana faɗin,"dan darajan Allah ka ƙyaleni in fita, wallahi hakan da kake yi babu kyau, ni fa ba muharramarka bace, kuma idan wani ya shigo ɗakin fa?".
yace,"zan barki ki wuce yanzu i promise, but you answer me first me yasa kika dinƙa taimakona?".
ya faɗa yana janyeta daga jikinsa yana kallon cikin ƙwayar idonta, ta ƙanƙance ido tace,"taimako kuma?, wane irin taimako na maka ni kam?, ni ban taɓa maka taimakon komai ba, kaine ma ka taimaka min aka kulle Amir".
ya matse tsintsiyar hannunta yana cewa,"kar na ƙara jin kin ambaci sunansa ko ba'a gabana ba". ya faɗa da sautin ɓacin rai da kuma kashedi me kyau.
tace,"to ka sakeni in tafi". yace,"fara ban amsata tukunna, asirikan da kika dinga ɗaukewa akaina me yasa kika ɗauke su?, me yasa baki bari sun same ni ba?, kuma me yasa baki taɓa faɗawa kowa ba?".
tai ƙasa da idonta tana so ta ƙaryata zancen nasa sai taji hannunsa a haɓarta ya ɗago fuskarta yana ɗagamata kai,"ehen am hearing you, ba kuma na son ƙarya dan nasan komai".
tayi narai-narai da idanu tace,"ni fa duk ban san me
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 43 Chapter of 73