Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a ƙurya da wajen zuciyata. please ki so ni ko da kwatankwacin yanda nake sonki ne, domin idan babu ke tare da ni Allah babu makawa sai na zama gawa". tai saurin ɗago ido ta kalli raunanun idanunsa. "ina sonka ai kaima kasan da wannan, kuma ba zamu rabe ba insha'Allahu, matarka ce ni har a aljannah insha'Allahu". haka ta faɗa, kuma hakan ke maimaituwa a cikin ransa, maimaituwar kuma ke haifar da jin daɗi tare da shi. da taga kamar yau bai da niyyar suyi karatun muryarta a sanyaye tace,"yau ina da aiki a cikin gida". take annurin fuskarsa ya ɗauke, ya haɗe rai ɓacin rai na ziyartarsa. ya miƙe kawai ba tare da yace mata komai ba ya nufi inda suke zama suyi karatun, baya son wannan aikin nata ya tsane shi. ko wannan karatun da ya tsira yi mata, yayi hakanne dan ya daƙile mata zuwa aikin shi yasa ya saka da safe zasu ke yi, amma ashe na banzar yayi, kamar mayu sun liƙe ita zata ke musu aikin, yanda baya so tai aikin haka baya so Kaka tayi, to amma baida yanda zaiyi, shi ba me ƙarfi ba ne, idan ita ya nemi hanyar hanata bai isa ya hana Kaka tayi ba, to amma me yasa ba zasu nemi wata yarinyar da ta dinga yi musu ba?, su bar masa Fillonsa ta huta kamar a baya. Fillo ta ƙaraso jiki a sanyaye ta shimfiɗa masa dardumar, sannan ta shimfiɗa ɗankwalinta ita kuma ta zauna akai, har sanda ta zauna shi yana tsaye kamar ba zai zauna ba, ita dai bata ɗago ta iya kallonsa ba, saboda hawayen cikin idonta zasu sami nasarar zubowa, ko kaɗan bata son ganin ɓacin ransa, musamman ace itace sila. sai da ya zauna sannan tace da shi,"kayi haƙuri, dole ce tasa ba dan muna so ba mu kanmu. aikin nan shine rufin asirinmu, kana gani Kaka daɗa tsufa takeyi jikinta na ƙara saki, ba zata iya ɗawainiyar da tayi a baya ba, ni kuma da ta riƙe ni bayan banda kowa dole na taimaka mata a yanzu dana kawo ƙarfi, tana buƙatar taimakona. kuma yanzu idan banyi aikin nan mun sami kuɗin ba da me kake so Kaka ta kaini gidanka Amir?". ya tsayar da ƙwayar idonsa akanta yace,"ni ke nake so ba abinda za'a kai ki da shi ba". ta girgiza kai tace,"a'a Amir, duk da bamu da komai, kuma ni ɗin ba kowan kowa bace, amma ina so na wuce gori a ko ina ne. kuma baya nan ina so ko bayan ran Kaka na kalli wani abin da zan gani naji daɗi, na san nima an tafi an bar min gado". yace,"shikenan, bismilillah". ya faɗa yana mata alamar ta fara karatun. tasan maganarta bai masa daɗi ba amma dole ta faɗa, kuma gaskiyar kenan. ba'a san gawar fari ba, kuma ba fata take ba, amma idan Kaka ta mutu, shi kuma ta aure shi shima ya faɗi ya mutu rabo bai samu a tsakaninsu ba, wa take da shi kuma me zata kama?, gwara tai duk kalar wahalar aiki tayi su sami kuɗin da Kaka ke fatan su samu ta cika burinta na siya mata fili, da kuma jarin da zata samu sana'ar yi. cikin zazzaƙar muryarta ta fara biyo masa haddar karatun da yake biya mata kullum, acikin ƙira'a me daɗin gaske, kuma tartilan tajwidan, kace wata balarabiya. haka tai ta biyawa har sai da ta kawo inda suka tsaya sannan tai shiru, ta buɗe ƙur'anin yay mata ƙari. yau ko tajweed ɗin bai biya mata ba ya miƙe yana mata sallama, muryarta a raunane tace,"tun yanzu?, kuma ba zamu yi tajweed ɗin ba? kayi haƙuri dan girman Allah". bai juyo ba daga tsayen da yake, hannayensa na aljihu idanuwansa a kulle. abinda ba tai zato ba abinda bata taɓa tsammata ba daga gare shi, magana ce ya faɗa guda ɗaya tal, amma magana ce me zafi, wadda take daidai da tsawon kalmomi fiye da dubu, zafinta ke dai-dai da sukar mashi a ƙahon zuci. bata san lokacin da ta miƙe tsaye ba, ƙafafuwanta na rawa suna neman su gaza ɗaukarta, kallonsa take amma wani Amir ɗin na daban take gani ba Amir ɗinta da ta sani ba. tasan dai ɓacin rai kan iya saka mutum yay komai amma batai zaton ɓacin rai zai iya sa Amir ya huda ƙirjinta da kibiya ba. zata jure komai ba, amma ba zata juri maganar ba, cin fuska baya ɗaya daga cikin abinda zata ɗauka, dole zata mayar masa, dole itama ta saka masa ɗacin da ya saka a tata zuciyar, ya kamata ace shima yasan wacece asalin Fillo, wannan Fillon da bata ɗaukar wulaƙanci daga ko waye, duk kuɗinka, mulkinka, matsayinka, muƙaminka, basu zasu hana ta rama abinda akai mata ba. ta tattaro sauran courage ɗin da take da shi, laɓɓanta suka tale da niyyar yin magana daidai lokacin shi kuma ya juyo ya fuskance ta. taja dogon nunfashi ta sauke, ta haɗiye wani abu da bata san menene shi ba, ta dunƙule hannunta da zuciyarta ke ingizata akan aikata abinda dole zai saka tayi da na sani. Amir kallonta kawai yake yana ganin yanda take haɗa zufa duk da iskar dake kaɗawa a wurin, ɓacin ran dake fuskarta na haɗewa da jin zafin abinda ya faɗa mata acikin zuciyarsa, yana jin tamkar wuta ce ke ruruwa a tare da shi, me zai ce yanzu?, ta ina zai fara?, me zai faɗa mata da zai goge tabon da dasa mata yanzu?. _"akwai abinda bai sani ba, tabbas akwai abinda bai sani ba a tare dake, ki faɗa masa hakan Fillo"._ abinda zuciyarta ke faɗa mata kenan, sai dai at the moment da ta ɗago kai suka haɗa ido sai komai nata ya ruguje, dukkan plan ɗinta na cin zarafinsa ya rushe, ta sauke idonta ƙasa tana jin ba zata iya komai ba, ba zata iya yiwa wannan mutumin komai ba, wannan mutumin dake gabanta ba ɗaya yake da kowa ba a duniyarta. ta duƙa ta ɗauƙi qur'anin da dardumar ta juya zata tafi, sai taji muryarsa a sanyaye ɗauke da sautin nadama da danasi yana cewa,"dan darajan Allah kiyi haƙuri ki yafe min, ba laifina ba ne, na kasa controlling zuciyata ne". Fillo taji wani dunƙulen abu ya tsaya a maƙoshinta ya hana yawu wucewa, halaccin da Amir yay mata ba zata manta da shi ba, amma bata jin ko me Amir zai faɗa mata ayanzu zata iya ci gaba da tsayuwa a wurin nan, bata jin akwai wani mahaluƙi a wannan duniyar da ya isa ya hana ƙafafuwanta takawa ta bar wajen nan, ba zata saurare shi ba, ba zata taɓa sauraronsa ba, kuma ba zata ƙara zuwa wurin nan ta tsaya ba wai saboda Amir, ko da ace kuwa gawar Amir ce. tana ɗaga ƙafarta taji yace,"ki tsaya ki fahimceni dan Allah". a ranta ta maimaita ta tsaya?, yana nufin ta tsaya su fuskanci juna ya bata haƙuri ta haƙura?, ai ba zata taɓa tsayawa ba balle ƙwayar idonsa ta karya alwashin data ɗauka. cikin ƙunar rai ta bar wajen, tana ji yana ƙwala kiran sunanta yana roƙonta, kuma wannan kiran sunan nata da roƙon da yake mata na dawo mata da rayuwar ta a baya, yana tuna mata wani lokacin a can baya, lokacin da ta haura katangar gidansu ta dire, cikin duhun dare ba da rana ba. har ta isa ga ƙofar shiga ɓangaren nasu Amir bai daina kiran sunanta ba, kuma duk da irin tazarar dake tsakaninsu bata bar jin kiran sunan nata ba a bakinsa, kiran sunan da take jinsa ba daga muryar Amir ba, daga wata murya ta daban, muryar Yayanta abin ƙaunarta Hamid, Hammah Hamid. ayanzu Kaka kawai take lissafawa wadda ta rage mata a cikin rayuwarta, amma duk ranar da Kaka ta faɗi ta mutu to tasan tana da Hamid, shi kaɗai take da shi ko da ace kuwa har lokacin Hayyo na raye. tun da Kaka taga ta shigo ɗakin a fusace tai shiru bata tanka mata ba, tana kallo ta wurgar da dardumar da ɗankwalin tai cikin ɗaki da qur'ani a hannunta, ko sallama ba tai ba. Kaka ko ta girgiza kai a fili tana faɗin,"Allah ya shiryaki, banda me ƙaunarki wane zai miki wannan gatan na ɗaukar ɗawainiyar yi miki karatu kullum, karatun ma na qur'ani, kuma ba biyansa kike ba, ya kashe uzurinsa da lafiya ko babu yazo ya koyar dake, shi ɗin ma dai da zai iya kenan, idan wani ne tuni bai rabu dake da wannan halin naki ba...kina asibiti yaron nan sai daya zama kamar marayan da bai da gata". Maijidda ta shigo bakinta ɗauke da sallama, Kaka ta amsa mata. a tunaninta ko Fillo bata dawo daga karatun da take ɗauka a wurin Amir ba ne shiyasa ma batai maganarta ba. ta zauna nan kusa da Kaka suna hira, Kaka tace,"ke ni fa tunda muka baro asibiti lissafin karɓar aikinmu ya kubce min, Yami bata ce miki komai ba?". Maijidda tace,"ku zaku karɓi na rana yau, amma naji kamar Yami na cewa ma yau ba za'ai girkin sadaqa anan ba, daga can masarauta za'a kawo". Kaka tace,"ohh ke haka ne fa, jiya Hajiya ta aiko a faɗa mana kinga na manta". suna hirar Maijidda na duba agogo tana kallon ƙofa da jiran shigowar Fillo, amma ganin har tara da rabi ta wuce bata shigo ba yasa tace da Kaka,"Fillo daga wurin karatun zata wuce aiki?". Kaka tace,"ai zatona faɗan ma dake akai da naga baki yi zancenta ba". Maijidda tace,"a'a ba muyi faɗa ba, me kika gani Kaka?". Kaka tace,"tun ɗazu fa ta dawo daga wurin karatun, tana shigowa ta shige ɗaka bata fito ba, Allah masanin fushin nata". Maijidda ta miƙe da azama tayi cikin ɗakin, tana shiga taga Fillo tsaye ta kifa kanta da bango, jikinta sai karkarwa yake yi. haka take ita, indai ranta ya ɓaci duk haƙuri da lallashin da za'a mata ba zasu yi tasiri ba sai tayi kuka ko kuma tayi masifa, idan ba haka ba ba zata huce ba, haka ba zata kwana a tsaye ne tana ta fizgar numfashi da karkarwar jiki, babu me iya controlling ɗinta. Maijidda ta kalli wayar hannunta dake ringing, tunaninta ko Dr Yusuf ne ya ƙara kira dan sau biyu yana yana kira a safiyar nan yana cewa ta haɗasa da Fillo tace masa bata dawo daga wurin karatu ba, to sai taga ma ba shi bane Amir ne. ta kalli Fillo ta kalli wayar, ya zatayi dole masifar dai akanta za'a juyeta ta sani, ai ba yau farau ba, tasan halin ƴar'uwarta, idan tana cikin irin wannan yanayin ko magana bata so ayi mata, ita kuma ba zata iya barinta haka ba tunda Kaka ba sauraronta za tai ba, in akai haka kuma Fillo da wartsakewa sai dai gobe. "Fillo wai menene?, wa ya ɓata miki rai?". Maijidda ta faɗa. Fillo tai shiru ba motsi balle amsa. ta ƙara cewa,"to kiyi haƙuri kinji, fushi fa na abokan sheɗan ne, ki zauna muyi kukan tare to, ni bana son ganinki a haka Allah". Maijiddan ta faɗa in breaking voice. nan ma dai babu amsa babu motsi. hakan yasa Maijidda ta dafata,"ni ce fa nake baki haƙuri Fillo, Hassanarki, Hussaina Hassanarki ce fa, ko kina so na mutu ma barki ke ɗaya?". Maijidda dai kamar me magana da gawa ko kuma gunki, ta yarfar da hannu kamar zatai kuka, ta ƙara kallon kiran Amir dake shigowa a karo na uku, ta dafa kafaɗar Fillo zata juyo da ita tana cewa,"kinga fa Amir ne ke ta kiranki, kar...". ai bata ƙarasa ba Fillo ta ɗago a harzuƙe cikin fusata tai wurgi da hannun Maijidda dake kan shoulders ɗinta, wayar Yami ta faɗi a ƙasa ta wargaje, ƙashin hannun Maijidda yay wata ƙara kamar an karya shi. a zafafe kuma cikin amon muryar da ya cika ɗakin Fillo ta ce mata,"dilla Malama ki rabu da ni, ki ƙyaleni, babu ruwanki da ni, ki matsa daga kusa da ni in ba haka ba duk abinda na miki ke kika jawa kanki". tana faɗin hakan kuma sai ta fashe da kuka, Maijidda cikin jin zafin hannunta ta matso ta rungume Fillo, sai suka durƙushe a ƙasan wajen, sosai Fillo ke kuka Maijidda kuma na tayata, Kaka dai na daga falo tana jinsu bata bi ta kansu ba. sai da aka ɗan ɗau lokaci sannan Fillo ta fara samun sauƙi cikin ranta, har daga ƙarshe ma ya zama ita ke lallashin Maijiddan. itama kuma a sannan sai taƙi yin shiru, taci gaba da zubar da hawayenta a kafaɗar Fillo. Fillo na shafa bayanta tace,"ke Hassana wai mene haka, ki daina mana". Maijidda tace,"to ai kece, na faɗa miki bana so kike bari Shaiɗan yana tasiri akanki akan fushi". Fillo tace,"to ba na daina ba, idan kuma ba zaki shirun ba sai mu ci gaba dan kin san dai ba zan zuba ido kina kuka ina zaune ina kallonki, zuciyata ba zata ɗauka ba". Maijidda tace,"nima ai baki saurareni ba a farko har ma kika ji min ciwo". ta faɗa muryarta na daɗa bayyana kukan da take yi. muryar Fillo ta karye tace,"to kiyi haƙuri, idan kuma ba zaki daina ba shikenan sai mu fasa auren miji ɗayan". sai a lokacin Maijidda ta ɗago suna gogewa junansu hawaye, Kaka na daga falo tace da su,"ke Maijidda kin san dake za'aje gidan sarki ko, ke kuma idan kinga dama ki fito kije kiyi musu aikinsu, in ba za ki ba kuma ki faɗa min sai na miƙe". Fillo tace,"to Hajiya Kaka gamu nan". sai da zasu fita sannan suka lura da aika-aikar da suka yiwa Yami, Maijidda tai salati tana rufe baki da faɗin na shiga uku. Fillo tace kin shiga uku ko mun shiga uku, yau akan akwalar wayar nan Yami ba sai ta cinyemu a ɗanyanmu ba. Kaka da ta jisu tace,"zan kuwa faɗa mata". hannu na rawa Fillo ta ɗau wayar tana haɗeta suka fito falo. "yanzu Yami sai tace mun cuceta mun datse hanyar da zasu ke gaisawa da bazawarinta". Maijidda ce ta faɗa, Kaka tai dariya, Fillo dai duk ta tsure sai ɗaure kyauraye takeyi, fatan ta ɗaya tana ɗora batirin wayar ta tashi. bakinta faɗi yake,"kece me Jidda ki kai magana da ƙarfi, da Kaka bata ji ba ai sai mu ajiye a kusa da ita bata sani ba muyi ficewarmu, Yami ba zata ce komai ba ƙarƙari tace da Kaka Ƙawata to ya za'ai babu komai ai, da saninki ai ba zaki fasa ba". ta faɗi maganar tana kwaikwayon muryar Yami. su duka sukai dariya, kuma cikin sa'a tana saka batirin ta kunna sai ga wayar ta kama. a tare suka sauke ajiyar zuciya. lokacin kira ya shigo da sabuwar lamba, ta miƙawa Maijidda tana miƙewa. ita kuma tace da ita,"ki ɗaga Dr Yusuf ne, tun safe yake kira wai na haɗaku, yama dai ce na masa kwatancen gidan nan nayi masa, ƙila ko zuwa zai yi". Fillo ta harareta tace,"yazo yayi me?". tace,"haka nace miki zai zo?, ce fa nayi ƙila zuwa zai yi, ki ɗaga kiji koma menene daga bakinsa". ta aje wayar a cinyar Maijidda ta tashi sai Kaka tace,"babu kyau dai wulaƙata mutum, musamman wanda ya taimaka maka a rayuwa, ba masu gidan nan ne kaɗai suka taimaka miki ba, harda shi likitan, dan shima ya bada jininsa an zuba miki". Fillo na ɓata fuska tace,"to Kaka yanzu sai kiji yace ai wani magani ko wata allura ya kawo". Kaka tace,"to ki ɗaga mana kiji dai me zai ce tunda ya neme ki, in allurar ce tunda ba shi ne zai yi miki ba ai sai kin so za'ai, abu da kece Halimanki, tun kan ki shigo nan zaki jefar da ita, sai kace kwanciyar asibiti tasa kin manta wacece ke". ba dai haka Fillo taso ba, sai dai bata son jayayya da Kaka, ta karɓi wayar ta ɗaga, tana yin sallama Yusuf ya ɗauki muryarta. daga cikin motar da yake ya kwantar da kansa jikin kujera sannan ya amsa sallamar. Fillo tace,"ina kwana, ya kake?". maimakon ya amsa mata sai taji yace,"ai na shanyu har na bushe, daka ni kawai ya rage ayi". taso yin dariya amma sai ta maze tace,"kaman ya?". yace,"kamar yanda Sister ɗinki bata faɗa miki ba, na kirata nace zanzo na duba jikinki before na bar gari tace min to, ta ban address kuma nazo inata kiranta taƙi ɗagawa, at the end ma sai ta kashe wayar, nayi zuciya zan tafi kuma sai na tuna da saƙonki nace to lallai ko zan kwana anan ba zan tafi ba". bakin Fillo a gaba tace,"saƙon me?, kuma ai ba daidai tayi maka kwatancen gidanmu ba". yay murmushi yace,"tambaya har guda biyu a jere, duk ranar da kika zama lauya ai sai ki ɗaure mutum. to da fari dai address daidai aka ban, domin kuwa gani a ƙofar gate ɗin gidan Alƙali Dikko, kuma gate na ɓangaren ma'aikatan gidan, gani ina kallon me gadi baƙi ɗan lukuti kamarki. saƙo kuma sai kin fito kya gani". da ƙosawa tace,"na san saƙon allura ne kuma bana so kuma ma bama gidan mun tafi ƙauyenmu, sai ka tafi". cikin kwaikwayon muryarta Yusuf yace,"kuma ma ba allura kaɗai bace harda magani, kuma ma da wuƙar farke ciki, kuma ma me gadi yace min kuna nan ba kwa fita, kuma ma ba zan tafi ba har sai kin fito". a wannan karon dai sai da sautin ƙaramar dariyar Fillo ya fito, Yusuf ya gyara zamansa yana sosa kansa wanda yasha sabon aski yace,"kinga Malama ki fito kawai nai miki tiyatar nan a wuce wurin, ni ban haƙura ba har yanzu nafi gane ai miki bakinki acikinki sai a ɗinke wannan bakin tsiwar da Maijidda tace yana isarsu". tasa hannu ta rufe fuskarta cike da kunya, sai kuma tace da shi,"to ka shigo kawai me gadin ba zai hanaka ba, sai kace masa wajen Kaka kazo". Yusuf ya kalli gate ɗin sai kuma yace,"a'a dai ki fito ɗin kawai, ba jimawa zanyi ba akan hanya nake". tace,"tom". ita da Maijidda suka fita, hannayensu saƙale dana juna, hijab ɗin jikinsu iri ɗaya komai da komai. yana cikin motarsa fara BMW, sai da suka isa wurin sannan ya fito. jikinsa shadda ce ƴar ubanta dark blue, ta amshi farar fatarsa, tunda ya fito yake ƙarewa girman gidan kallo tare da jinjina kai, yasan wannan gidan ko filoti goma sha albarka, har ƙasa suka tsuguna suka gaishe shi. hannayensa harɗe a ƙirjinsa yace,"Hassana da Hussaina". su kai murmushi kawai basu ce komai ba. Fillo ta lura yana da magana, hakan yasa tace,"Kaka tana gaisheka, kuma muna da aiki a cikin gida". yace,"ina amsawa, nima yanzu zan tafi ai ba sai kin kore ni ba, saboda nan da minti 20 jirginmu zai tashi. kawai ji nayi ina so nazo naga mara lafiya ne". Fillo tace,"ai naji sauƙi". yace,"ehh naga alama ai, Allah ya daɗa lafiya". ta amsa da amin, sai kuma duk suka yi shiru. Yusuf yace,"ranar da zaku bar asibiti baki bari na baki amsar tambayarki ba kika gudu". ta ɗago ta kalle shi tace,"amsar me? aini ban tambayeka komai ba". yace,"ehh bakinki bai faɗa ba amma ƙwayar idonki ta faɗa...kina jin kamar kin taɓa sanin me wannan fuskar ƴan gayun ko". ya faɗa dan raha yana shafa fuskar tasa. bata ce komai yace,"ko ba haka bane?". tace,"nayi mamaki daka fahimta". sai yay murmushi yace,"zaki iya tuna watarana?, lokacin baki kai haka girma ba, time ɗin gidaje uku ne kawai a estate ɗin nan, kin fito yawo kika ji ciwo kika zauna kan yashi kina kuka, wani bawan Allah me tausayi yazo ya sameki yasa ki kai shiru da ƙyar, yace ki nuna masa gidanku ya kai ki kika ƙi kika ce Kakar ki zata dukeki saboda bata san kin fito ba, yace to ki tsaya ya ɗauƙo first aid a mota ya wanke miki ciwon kamin ya dawo kika ɓuya a bayan bulo, kuma ya durƙusa yana haɗa hydrogen kika felle da siraran ƙafafunki kika bar wajen, kina gudu kina waige saboda kar ya kamoki". Maijidda ta ƙyalƙyale da dariya, Fillo kuma kunya ta kamata tasa hannu ta rufe fuska tana murmushi, Yusuf ma murmushin yake. tace,"kuma baka manta kamannina ba har wannan lokacin?". yace,"to yaushe akai abin?, shekara ɗaya da rabi ne fa kawai. kuma ai ba wani girma kika ƙara ba da za'a kasa ganeki, kin dai ɗan ƙara wayo ne kawai, sai abinda ba'a rasa ba, amma ai nasan ko yanzu kika ji ciwo zaki tirje a tsakiyar layin nan ki ta kuka abinki ke ɗaya har sai kinga me allura zaki gudu". murmushi bai bar fuskar Fillo ba har lokacin, taji hirar na tafiya da ɓacin ran da Amir ya haifar mata. Maijidda tace,"gaskiya baka da mantuwa". yace,"ai duk randa zan wuce ta wurin nan ai sai na tuna, kin ga fa haka ta riƙe ƙafa tana kallon ciwon tana ta tsala kuka kyace yanke ƙafar akai, kuma abin takaici ciwon fa ɗan ƙaɗanne ba me yawa ba". ya faɗa yana kwaikwayon yanda takeyi a lokacin. ya basu dariya sosai, yana da fara'a da barkwanci, Maijidda tace,"wallahi na tuna lokacin, ai in faɗa maka ciwon nan anfi wata guda ana jinyarsa, haka take ko ya taga jini a jikinta sai ta hargitse". yace,"kice da idonta biyu aka kaita asibiti ran na da mun shiga uku, ƙila duk patients namu sai sunce a sallamesu dan babu me iyawa da kukanta". Fillo ta harari Maijidda tace,"sharrin Hassana ne fa". Yusuf yace,"zan yarda ai, kece fa". ya kalli agogo yace,"kun ce zaku yi aiki nima kuma zan tafi, bara na ƙyaleku kar na cika ku da surutu, ina da yawan hira da ƙannena, ina son sisters mata musamman kamarku, amma ku ɗin sai naji kuna burgeni sosai". suka ce,"mun gode". yace,"nima na gode, amma ya kamata dai aje ayiwa Kakata godiya na dubiyar dana zo nayi". Maijidda tace,"tom shikenan kayi mana kwatance, sai mu zo wataran". yace,"yaushe kenan". tace,"ehh tou sai mun sami damar fita idan kamar Yami ta aikemu gidan sarki". yace,"to ai kuma ƙila lokacin bana nan". Fillo ta sami kanta da tambayarsa,"ina zaka je?". yace,"ai a kano nake da zama, nan nake zaune ni da matata, nan garin kuma gidanmu ne da Inna Wuro ta samu tayi bake-bake acikinsa ta hanamu sakat, ta mayar da gidan kamar nata...saboda haka idan zaku zo ku tabbatar kun fesa turare kamar zai yi magana, kun kuma kai mata ƙunshin leda ko da babu komai aciki in ba haka ba kun shigesu da sababi". Maijidda tace,"Kakarku ce Inna Wuron?". yace,"ita ta haifi Dad namu amma ta zamar mana ciwon kai, kowa ya gaji da ita...nima dan dai ita ta raine ni banda haka tuni na ɗinke bakin maganarta". sukai dariya su duka, Fillo ta katse hirar da cewa,"tom bari mu tafi, mun gode sosai Allah ya kai ka gida lafiya". suka faɗa a tare suna niyyar wucewa. sai ya tsayar da su. "tsaya ki karɓi alluranki Malama, ki kaiwa ɗaya Kakar taku da kuke cewa Yami wadda kike ɗan tsoro ta dinga tsira miki". Fillo ta ɓata fuska tana kama hannun Maijidda dan su tafi. sai gani sukai ya fito da fararen ledoji guda biyu manya, Fillo na ganinsu ta gane irin ledar kantin da Zaytuna ke yin siyayya ce. ya miƙawa Maijidda yace,"ga shi duka na na mara lafiya ne amma kema idan kina so ana iya tsira miki ko guda ɗaya ce, tunda naga da amana a tsakaninku". Maijidda ta karɓi ledojin tana masa godiya, shi kuma ya zagaya ɓangaren driver seat ya buɗe motar, idonsa na kan fuskar Fillo da ta cukule, sai haɗe gira takeyi kamar zata yi kuka, tana ta harar Maijidda. ya shiga motar yana ta smiling, ya zuge glass na ɗayan kujeran me zaman banza ya leƙa da salon tsokana yace,"Auta ya dai? a saki ran please kar Kaka tace na taɓa mata Hussaina, kuma dan Allah banda kukan allura kinji, kinga kin girma". Fillo da ta gama kumbura tai tafiyarta ta bar Maijidda a baya, yana kallon Fillo har ta shige cikin gida, haka kawai yake jin yarinyar ta tsaya masa a rai. ya kuma kasa gane dalilin hakan, tun randa suka bar asibitin yaji kamar zuciyarsa ta shaƙu da yarinyar, kamar yana ya dinga ganinta kullum, kamar dai yana so ya fahimci wani abun amma ya gagara. sai daya tabbatar da shigarsu gidan sannan ya bar layin yana ji a ransa yana so ya ƙara kasancewa da yarinyar. *Please Vote, Comment, and Share.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *21* Maijidda ce ta wuce da ledar kayan, Fillo na faɗa mata

Chapter 17 of 73