yaran nasa yace,"Jibril, ka siyo kaza ka bashi yaci, domin ina sha'awan wannan yaro, ina so na huta da shi. a siyo masa kayan gina jiki a bashi yaci kafin nazo na biya buƙatana akansa, tun a ranar farko naji ina sha'awan budurci nasa, i know by that time uban Alkalai ya kawo mana 200Million namu, sai muna sakinsa yana tafiya".
Kalmar Virginity yay wani duka a ƙwaƙalwar Fillo da yasa taji ta girgiza gaba ɗayanta, her virgin?, kamar dai bata fahimci maganar tasa ba da kyau, sai kuma taji wanda aka barta da shi na faɗin,"kash Oga banji daɗi ba kana riga ni shiga daɗin wannan kyakykyawan yarinyar, nima ina ta kwaɗayinta tuntuni, amma da zarar ka sha naka rabon daɗin nima zan sha nawa kafin a sallameta". yaja igiyar ƙafarta ya ƙara ɗaurewa da kyau yana cewa,"kai Budurci yana da daɗi, gaki da ganinki za ki daɗi ƴan mata".
ƙwayar idon Fillo tun ɗazu ƙafe take a wuri ɗaya, tun bayan fitar wancan mutumin take so ta fahimci abinda ya faɗa kafin ya fita, kuma bata gane komai ba sai a yanzu, sai yanzu ta fahimci abinda yake nufi daga shi har wannan, suna maganar zasu amshi budurcinta ne kafin ta fita daga hannunsu.
da sauri ta shiga jujjuya kanta da ke barazanar tarwatsewa, hawaye masu zafin gaske na daɗa biyo kuncinta, ta jinginar da kanta jikin bango tana jin ƙirjinta yay mata wani irin nauyi tamkar an ɗora dala da goron dutse akai, a hankali ta shiga ambaton sunan Allah tana fashewa da wani kuka me ƙarfin sauti cikin fitar hayyaci.
ta jima tana kukan tana kiran sunan Allah, bata ma san time ɗin da mutumin da aka barta da ahi ba ya fita ba. zuwa yanzu ta san ruwan hawayenta sun ƙare, ƙazaman maganganun mutanen ke tayi mata yawo acikin kanta.
ta sa ni shikenan tata kuma ta ƙare, dan haka ta sallama da rayuwar gaba ɗaya, kanta ta buga ajikin bango tana addu'ar,"Allah ka ɗauki raina kafin waɗannan azzaluman su cimma burinsu akaina, Allah ka ɗau raina ayanzu ko na huta da wannan bala'in".
tsananin tausayin kanta ya lulluɓeta, babu ta yanda ta-ke tsammanin zata iya guduwa daga wajen nan, dan tayi attempting sau ɗaya suka kamata, shine tun daga ranar suka ɗaureta basu ƙara ƙunceta ba har zuwa yau, jini har ya gaji da daskarewa waje ɗaya a jikinta.
idanuwanta a rufe taji kamar mutum na taɓata, a mutuƙar firgice ta buɗe ido tana sakin ihu cikin ƙaraji da bala'in tsoro, da sauri farin mutumin dake gabanta yasa hannunsa ya toshe bakinta.
ta ƙwalolo ido waje tana kallonsa, ta san shi sosai kullum shine yake kawo mata abinci. a hankali taji yace,"ki shiru zan taimaka miki ne ki fita daga wajen nan, ki yarda da ni wallahi ba zan cuceki ba saboda haka karki yi ihu"
ya sauke hannunsa a bakinta, cike da tsoro dan bata tunanin za ta yarda da shi. ya miƙa mata plate na abinci gabanta yace,"ki fara cin abincin tukunna".
tace,"dan Allah karka yi min komai".
yace,"wallahi tallahi banda niyyar cutar fa ce taimakonki, amma kici abincin ko kaɗanne kinji".
tana ta kallonsa tace,"ba zan iya ci ba. dan Allah ka taimaka min".
yace,"zan taimaka miki amma in har ba kiyi wani yunƙuri na tona min asiri ba".
da sauri ta jijjaga kanta tana cewa,"zan bi duk ubarninka in har ba wanda zaka cuceni ba".
yasa hannu ya kunce ɗaurin igiyar ƙafarta, sannan ya kunce ɗaurin na hannu, amma sai dai bai warware ba.
yace,"kowa ya fita daga gidan nan, ni kaɗai ne amma zuwa nan da minti goma zuwa sha biyar Babban Oga zai iya zuwa saboda haka ba zan ce miki ki fita nan da wuri ba. kawai dai kiyi hankalin da ba zasu gane cewar wannan igiyar a kwance ta-ke ba, idan kika ta shi akwai ƙofa ta nan baya kusa da parlo da aka cire ki jiya, kibi ta nan ki fita. kina fita za ki hango wata ƙofa a wurin sai kiyi saurin buɗewa ki fita, za ki ganki cikin daji karki tsaya a kusa-kusa sai kin tabbatar kinyi nisa sosai da babu me iya riskar ki".
yasa hannu a aljihu ya ɗauko ƙaramar waya yace,"ga wannan kina iya kira gida ki faɗi inda kike ko da za ki kasa gane hanya".
tabi ƙaramar wayar hannun nasa da kallo kafin ta ɗago ido ta kallesa tana nazarinsa.
yay mata murmushi yace,"ni dai har ga Allah iyakar abin zan miki kenan, ya rage naki kuma ki kuɓutar da kanki ko kuma ki zauna su cuceki tun kina ƙaramarki. dan wallahi ina mai tabbatar miki sai sun mayar dake yarinyarsu after sun gama talauta danginki, ƙarƙari ki kasa juriyar ɗaukarsu ki mutu su jefar da ke, dan Babban Oga bai da imani wallahi".
yana gama faɗar hakan ya miƙe ya fitar ya barta, tabi bayansa da kallo kafin ta dawo da idonta kan wayar da ya bar mata. jin kamar motsi tayi saurin ɗaukar wayar ta tura acikin rigarta, Allah ya taimaketa kuwa tana sawa ana turo ƙofa a shigo.
jere ta gansu duk kusan kansu ɗaya, zata iya cewa bata taɓa ganinsu ba duk da cewar fuskokinsu a rufe yake da mask irin wanda take gani a film, suka wuceta suka shiga ciki, in ta lura da kyau kamar harda mace, na ƙarshen ya duƙa gabanta ya mammari fuskarta yana wani makirin murmushi yace,"zamu huta sosai da kai".
da faɗin hakan ya miƙe yabi bayan sauran.
taji sabon hawaye ya taho mata, ta rumtse ido sosai tana rasa ma me take ji a ranta.
dai-dai nan taji mutumin ɗazu ya dawo can ƙasa da muryarsa yana cewa,"you got the chance, zasu yi zaman meeting yanzu and atleast they will take up to 30minutes kamin su gama, babu wanda zai ji motsinki har ki fice, karki yi wasa da wannan chance ina daɗa jadadda maki if not wallahi a yau ko ba'a ɗau gawarki ba sai kin mugun raina kanki, dan kaf wannan mutane da kike gani sai sunyi amfani da ke".
yay saurin ficewa gudun kar wani ya fito ya gansa tare da ita.
*A dai-dai wannan lokacin.*
wayar Hajiya Madina da ke riƙe a hannun Nihal tayi ringing, tai saurin miƙa mata sanda ta ke tambayarta,"waye?". tace,"ba suna a jiki".
Hajiya Madina da jikinta yake a sanyaye ta karɓi wayar, dai-dai kuma da katsewar kiran, ta sauke numfashi jikinta duk a mace saboda halin da Kaka ke ciki, tun ɗazu suka zo asibiti amma har yanzu bata dawo hayyacinta ba, a sannan likita ya shigo ɗakin yana cewa,"Hajiya meet me in my office".
da hanzari Hajiya Madina tabi bayansa, nan kiran lambar ɗazu ya ƙara shigowa, ta ɗaga tana yin sallama tana ci gaba da bin bayan likitan. daga can ɓangaren taji wata gwandareriyar murya na faɗin,"Hajiya mune kidnapper na ƴarku".
tsabagen rikicewa sai wayar ta suɓuce daga hannunta tana tsaya daga bakin ƙofar tana haki kamar wadda tayi tsare, saura ƙiris wayar ta kai ƙasa Allah ya shigo da Turaki yay saurin riƙo wayar yana dubanta.
"lafiya Maama?". da shi da kowa na ɗakin suka tambayeta a tare suna yowa kanta. tsabar gigita tama kasa cewa komai sai nunawa Turaki wayar ta ke da hannu. ya kalla screen ɗin wayar yana kallon yacca call ke tafiya, ya kara wayar a kunnensa yana cewa,"Salamu Alaikum".
cikin ɗaga murya aka ce masa,"karku ƙara yi mana sallama ba ita muke buƙata ba".
mamaki ya bayyana akan fuskar Turaki yace,"wake magana?".
aka ce,"wanda suka yi garkuwa da yaro naku ne, kuna san yaron naku a raye ko kuma mu kashe shi mu aiko muku da namansa?".
Turaki bai san lokacin da yaywa hannu Maama wata muguwar damƙa ba da yasata yin ƴar ƙara tana faɗin,"Me Babban suna zaka karya min hannu".
bai ma san tana yi ba becouse he is totally getting out of control, ƙwaƙwalwarsa ta shiga faɗa masa anger ɗinka ba zai yi amfani yanzu ba, just relax and control your self.
ya buɗe idonsa da ya rufe in just 10seconds, yaja leɓensa ciki ya cije da ƙarfi sannan a hankali ya sauke dogon numfashi, ƙwayar idonsa da ta sauya kala ta dawo yanda ta ke.
ya ɗauko wayarsa a aljihu yay ɗauki lambar tasu, sannan ya bi bayan kiran nasu da suka katse. bugun farko suka ɗaga, cikin kwantar da murya Turaki yace,"muna jinku, me ku ke da buƙata?".
mutumin yay dariya sosai yace,"kun tabbata za ku bayar da komai muka ce?, idan kun san baku shirya karɓan ƴarku ba karku sa mu ɓata bakinmu wajen yi muku bayani".
Turaki ya ƙara rumtse ido yace,"duk abinda kuke so na tabbatar da zaku sa me shi".
mutumin ya kuma dariya yace,"good. ga yaronku nan yana ta kuka kullum yana so yazo ya ganku, amma munce ba zamu sake shi ba sai an bayar da miliyan ɗari biyu tukunna mu barsa ya dawo gida da ƙafafunsa".
zuciyar Turaki na bugawa fat-fat yace,"you got additional of 300million, zan baku miliyan ɗari biyar muddin baku taɓa lafiyarta ba wannan alƙawari ne, ta ya zaku karɓi kuɗin?, or throught bank za'a tura maku".
mutumin yay dariya sosai yace,"zaka kawo mana kuɗin da hannunka". nan ya shiga korawa Turaki bayanin inda zai je ya kai kuɗin ya ajiye. Turaki ya tabbatar masa da cewar zai zo ɗin in the next few minutes amma su tabbatar ba su yiwa Fillo komai ba.
mutumin na bushewa da wani dariyar yace,"ga yaronku kuyi magana dan ka tabbatar yana lafiya, idan kunji jishi yana kuka ba komai bane akayi masa, soro ne kawai da yake ciki".
daga can inda mutumin ke zaune kan kujera ya ɗorawa Fillo wayar a kunnenta a tsawa ce yace,"yi magana da father naki".
cikin matsanancin kuka tace,"Kaka".
Turaki ya ƙara matse hannun Maama da har yanzu ke hannunsa, muryarsa a hankali yace,"Fulaniii". sai kuma ya fesar da iskar bakinsa me zafi yace,"kina jina?".
a wahalce tace,"Turakii, dan Allah kazo ka cece ni, kashe ni zasu yi sun ce, wai zasu yi amfani da ni, ka faɗa musu Kaka bata da kuɗin da suke nema". ta faɗa cikin kukan da duk wanda yaji sai ya zubar mata da hawaye.
Turaki ya tattaro jarumtarsa da yake jin tana neman barinsa yace,"kiyi shiru ki daina kukan kinji, zan zo in ɗauke ki yanzun nan. babu abinda suka isa suyi miki in har bakinki bai gushe da ambaton Allah ba, amma na faɗa miki ki daina kukan kinji Fulani".
wannan jarumtar tasa ta maza yaji ta ƙwace, bai san sanda ya zube a gefen gadon Kaka ba, idonsa na cika da tarin hawaye, ya buɗe baki yana jin kamar ba zai iya magana ba, acikin zubar hawayen da babu wanda ya lura da shi a fuskarsa yace,"karki bari suyi miki komai kinji Fulani, i know who you are, i know you can protect your dignity, dan Allah karki bari suyi miki komai, dan Allah".
yanda take sauke numfashi a wahalce kawai yake jiyowa, ya matse idonsa sosai yana jin zuciyarsa na wani mugun matsewa, yaci ta sassauta kukan tace,"to zaka zo yanzu".
yace,"yes, i will come right now, just some minutes kinji". ƙit yaji wayar ta katse, ba tare da yabi ta kan kowa dake jiran cewarsa ba ya ratsa ta tsakiyar Maama da Yami ya fice daga room ɗin cikin sauri.
yana shiga mota yay dialling number D.P.O yace masa,"ranka ya daɗe kun fara tracing numbern?". yace masa,"yes, before wayan naku ya katse har mun gano a inda suke, yanzu haka yara sun ɗau hanya. ka tsaya ka ɗauke ni a hanya".
Turaki nasa hannu ya sha re zufar goshinsa yace,"please ka faɗa musu suyi a hankali kar suja su cutar min da ita". da haka ya katse wayar sannan ya kira wayar Khalil yace,"Bro i need five hundred million naira in cash right away, kaje Zenith Bank wurin Faisal, on my way to meet you there in the next 10minutes".
acikin motar Turaki da yake sharara mahaukacin gudu akan hanyar zuwa ƙauyen pindiga, lokacin ƙarfe bakwai da rabi na dare har tayi, waya ce maƙale a kunnensa yana tabbatarwa da kidnappers ɗin cewa shi ɗaya ne ba tare da kowa ba kamar yanda babu wanda ya shaidawa maganar..
sai dai a dai-dai wannan lokacin da yake wayar da su, a dai-dai wannan lokacin Fillo ta samu damar zare igiyoyin jikinta ta miƙe tana bin hanya saɗaf saɗaf ta yanda babu me jin motsinta, kuma ta tabbata har ta fice babu wanda zai ganta kamar yanda mutumin nan ya faɗa mata.
sai dai kuma me?, sanda ta ke zuwa gab da ƙofar zata fita, dai-dai jikin windown wani ɗaki, bala'in tsoron dake tare da ita sai ya koma zuwa tsantsar mamakin abinda kunnuwanta ke jiyo mata, muryar wanda ta ke ji da kuma sautin dariyarsa da abinda yake faɗa na saka jijiyoyin jikinta tsinkewa.
ta ja ƙafarta a hankali ta isa jikin window tana leƙawa ta yanda ba za'a ganta ba, tana tsaye a wurin kunnuwanta na ci gaba da jiye mata abubuwan da yake faɗa, maganganun nasa da take jinsu tamkar ɗigar dalma ajikinta, in one time sai taji jikinta gaba ɗaya ya zama kamar na statue, ko hannunta ta kasa motsawa, ko idonta ta kasa ƙiftawa, zata iya rantsewa cewa zuciyarta kanta ta tsaya da aikin buga jini zuwa sassan jikinta.
a sanda ƙyar idonta tayi tozali da shi ta siririyar ɓular, zaune tsakiyar mutanen wanda ya tabbatar mata shine Babban Oga da taji suna ta ambata, kuma yana ɗaya daga cikin mutanen da suka shigo ɗazu har tabi su da kallo.
sai ta koma da baya ta lumshe idonta tana jin zuciyarta kamar ta zama ƙanƙara tana narkewa ruwan yana taruwa acikin idanunta, taji duk wani tsoro nata yana bin iskar wajen dake kaɗawa, taji kamar duk wani abu da yake cikin kanta yana farfashewa a ƙasan wajen da ta ke, taji duniya gaba ɗaya tayi mata zafi. sai ta ƙara matsawa da baya tana saka hannu ta goge hawayen da ya taru cikin idonta amma sai taji ƙamas babu komai, idonta a bushe yake kamar famfon da ya shekara guda babu ruwa, haka ma fuskarta.
"Amir!". taji zuciyarta ta furta da wani irin amo kamar ba nata ba. "Amir ta ke gani anan, Amir ta ke ji yana faɗar shi zai fara keta haddinta kamin kowa, shi ta ke ji yana faɗar ya cika burinsa na shekara da shekaru ya gama handame musu komai, har yana faɗin bai zama lallai ma su barta da rai ba".
gaba ɗaya sai taji jikinta ya ɗauki rawa kamar an jona mata electric shock, haka ma zuciyarta na harbawa fat fat kamar zata faso ƙirjinta ta fito, numfashinta na fita da ƙyar tana jin kamar ana zare ranta.
ta jingina kanta da bango tana kasa rufe idonta, komai da ta ke ji ta ke gani kamar mafarki ba gaske ba. ta ƙara dafe bangon wurin tana rumtse idonta tana girgiza kanta da ɗan saurin kuzarin da take jin tana da shi, cikin ranta tana addu'ar Allah yasa ta buɗe ido taga ba Amir ta gani ba, Allah yasa idan ta buɗe idon taga mafarki ne ta ke yi ba muryarsa ta ke ji ba acikin azzaluman mutanen da tasan babu makawa sai wutar Allah ta ci su. Ta shiga buɗe idonta a hankali tana mai tsoron buɗewa bugun zuciyarta na ƙara tsananta.
a lokacin ta ƙara jinsa yace,"ba zata san ni na tsara komai ba kuma na shirya ba har sai bayan na gama da rayuwarta. zanje yanzu dan ana kan hanyar kawo kuɗin fansarta...in ance ma nasan mutanen nan a shirye suka da yin komai akanta da tun farko ba'a ɗauki tsayin wannan lokacin ba, da ban tsaya na jira na gama haifar da tashin hankalin da bai da misaltuwa ba a wurin Kakarta, da a yanzu kuma bamu ambaci miliyan ɗari biyu ba, da 2billion naira zan ambata musu".
Fillo ta buɗe baki tana ƙoƙarin furta kalmar innalillahi a fili amma sai taji ta kasa sarrafa harshenta, sai bakinta da ke rawa kawai, cikin fitar hayyaci ta juya da gudu ta buɗe ƙofar ta fice tana jin kamar numfashinta zai ɗauke.
gudu take sosai acikin duhun daren, cikin jejin da take gani kamar ba'a duniya ba, ko gabanta bata iya gani sosai, sai da ta tabbatar tayi nisa sosai sannan ta duƙa tana haki a wajen da ta ke, wucewar daƙiƙa biyu ta ɗago ta ɗora daga inda ta tsaya, tun ƙafafunta na ɗaukarta har taji suna dab da dainawa, kuma a lokacin da ƙarfinta ya ƙare lokacin taji tayi karo da abu, karo da abu kamar mutum.
tsoron da ya barta tun a ɗazu sai ya dawo sabo a sanda ta ɗago ido tana kallon halittar dake gabanta, da sauri taja da baya tana dafe kanta cikin ranta tana jin anya kuwa yau itace?, anya bata yi gamo ba?, anya zamanta a wajen can bai sa aljanu sun shiga jikinta sun rikita mata tunani ba?.
sai ta juya tana kallon bayanta kan ta juyo ta ƙara kallon matar da ke gabanta wadda ta ke duk a firgice, firgicin da zata ce ya ninka nata, kuma mafaka take nema, inda zata tsira da ranta ta ke nema.
sai taga matar ta ɗaga hannunta biyu tana haɗe tafun hannunta alamar roƙo, ruwan hawaye na bin idanunta, jini ya taru a ƙwayar idonta, a cikin rawar murya irin wadda ta sa ni taji tace mata,"dan Allah ki taimaka min zasu kashe ni, amma dan Allah kema karki cuce ni".
ta faɗa acikin yaren fulatanci muryarta na shaida tsananin tsoro da kuma tashin hankali.
hasken farin watan da ya hasko su ya haskawa Fillo sarƙar da aka ɗaure hannun matar da ita, ya kuma haska mata abayar dake jikinta wadda taci ubanta da mugun dauɗa sai wani kalar wari ke fita a jikinta, yalwataccen gashin kanta a barbaje ɗauke da tsirarrun furfura duk ya tuttuje.
Fillo ta tsayar da ƙwayar idonta akan dogwayen yatsun matar tana jin wani kalar hawaye me zafi da bata taɓa zubar da irinsa ba na bin kumatunta, kallon yatsun nata ta ke amma a yatsun wani hannun na daban, furucin da matar tayi na maimaituwa acikin kanta da irin sautin muryar da ta sani, ta rumtse idonta sosai tana jin ruwan hawayen dake ciki na ƙarasa sauka.
bata san lokacin da ta faɗa jikin matar ba ta rungumeta tana fashewa da kuwa, kuma ƙarar harbin bindigar da suka jiyo ya cika dokar dajin yasa ta fizgi hannun matar sukai gefen wata bishi suka ɓuya, ba nata ƙirjin kaɗai ba, har na matar tana jin yanda yake bugawa kamar zai faso.
a bakin bishiyar wajen suka duƙe Fillo na kamo kan matar ta kwantar akan ƙirjinta tace,"Alhamdulillah, welcome back to the family".
*please vote, comment and share.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_Avoid any mistake._
*35*
Fillo na rungume da matar har bayan wucewar wasu daƙiƙu sannan ta zare jikinta anata, ta ƙara saka idonta akan fuskar matar don tabbatar da abinda ta gani ɗin kar taje ko idonta ke mata gizo.
ai ko da ace bata taɓa ganin hotonta ba, tsananin kamannin da take da yaranta kaɗai ya shaida mata wannan itace matar da suka ɗauki shekaru ashirin da biyar basu ganta ba.
ita ayanzu ma sai ta iya rantsewa hoton fuskar Turaki kawai ta-ke gani a fuskarta, ta kamo hannayenta tana daɗa kallo da suke sak da na Zaytuna tun daga kan tsayin yatsun har farcen, haka ma a sautin muryarta sai ka rantse kace Zaytuna ce tai magana, daga nan sai kuma ta sauke idonta akan sarƙar dake ɗaure da hannuwan nata.
taji hawaye ya kusa sakko mata tsaboda tsananin tausayi, tayi attempting kunce sarƙar sai taga ba zata iya ba.
ji tayi matar ta ƙara ce mata,"dan Allah karki cutar da ni kema".
Fillo tai murmushin ƙarfin hali, taji tausayin kanta na bin iska yana tafiya, yayinda na matar ke biyo iska na lulluɓeta.
tace,"ba zan cutar da ke ba Mum, adu'a nake so kiyi mu fita daga wurin nan lafiya".
Hajiya Ramla ta dinƙa kallon Fillo tana jin kamar wani ya taɓa kiranta da wannan sunan Mum.
Fillo tasa hannu a rigarta ta ɗauko wayar ɗazu, ta kunna sannan ta kalli Hajiya Ramla tace,"Mum za ki iya faɗin lambar Baffa ko ta Maama? sai mu kira su azo a tafi damu".
Mum tace,"su waye hakan?".
Fillo ta ɗago ido ta kalleta sannan tace,"lambar mijinki Alƙali Dikko ko ta abokiyar zamanki Hajiya Madina".
Mum ta girgiza kanta tace,"ni ban san su ba ai, ban taɓa jin sunansu ba". sai kuma ta haɗe hannayenta tace,"idan kin san sune mutanen da suka saka ni a ɗakin duhu don Allah karki kira su, sunce zasu yi tsafi da ni ne, kuma babu abinda nayi musu".
Fillo tasa hannu ta goge hawayenta, babu makawa ƙwaƙwalwarta tayi formating abubuwa da yawa, kuma ba lallai ta tuna komai ba ayanzu ƙila sai ta gani da idonta.
a lokacin suka ƙara jin harbin bindiga, cikin azama Fillo ta miƙe ta kamo hannunta a rikice tana cewa,"Mum zo mu gudu kar su kama mu".
Hajiya Ramla ta miƙe da ƙyar suka nausa inda basu san ina zasu ɓulle ba suna ta zabga gudu, da sun gaji sai su tsaya su huta, sannan suci gaba da gudun, gaba ɗayansu a galabaice suke.
*A dai-dai wannan lokacin.*
Fulani Azima zaune a gaban boka dunƙus, idanuwanta na manne acikin ruwan ƙwaryar dake gabansa yana mata bayani, tana jin zuciyarta na tafarfasa saboda baƙin ciki.
"to ban san dai abinda hakan ke nufi ba, amma kwata-kwata ko aljani ɗaya ya kasa nuna mana fuskar yarinyar, amma tabbas dai aljanu sun shaida ita ke lalata miki aiki".
maganar ta ƙara ƙona ran Fulani Azima, ta ɗaga murya tana saka hannu ta toshe kunnenta tace,"wacece wannan?, wacece ita da har aljanu suka kasa gano min fuskarta?".
sai kuma tayi ƙasa da murya tana kallon Boka tace,"ni dai na roƙe ka da Aljani Jambus ka nuna min fuskar yarinyar nan ko kuma sunanta, nayi maka alƙawarin ko menene zan bayar ko da kuwa kaina ne".
Boka yay dariya yace,"haba Azima, yanda muke da ke ai kin fi ƙarfin haka a wajena. abinda nake so ki fahimta shine yarinyar nan tafi ƙarfinmu saboda tana tare da tsari a jikinta".
sai yasa wani mifici ya rufe ƙwaryar sannan ya buɗe yace,"leƙo ki gani". ta leƙa kanta ta hango wata mace a tsaye doguwa siririya, amma baka ganin komai nata sai ɗan banzan duhu.
yace,"to kinga ni babu ta yanda zamu ga fuskarta haka kuma sunanta ɓacewa yake akan aljanunmu".
fuskar Fulani Azima na shaida mamaki matuƙa tace,"to saboda me boka?".
sai yasa hannunsa acikin ruwan ya zuƙo hoton, daidai inda hannun Fillo yake yace,"ba lallai ke ki gani ba amma ni ina iya gani, wannan azurfar ta yatsanta azurfa ce ta tsari wadda ba zata taɓa barin wani aljani ya ganta ba balle har ya sami damar shigarta, bayan haka kuma ɗan autan aljanu ya faɗa min cewa yarinyar na kasancewa kullum cikin yin adu'oin tsari, bata minti ɗaya bata ambaci sunan Allah ba haka kuma bata min ɗaya bata ambaci adu'ar neman tsari ba. saboda haka babu yanda zamu yi da ita gaskiya, kuma shugaban Aljanu ya shaida mana muddin yarinyar na tare da Turaki babu abinda asirinmu ya isa yayi masa, domin ita ɗin kamar sila ce ta kariya a tare da shi".
kan Fulani Azima yay matuƙar ɗaurewa, ta dinƙa hasaso tsayin yarinyar tana so ta kwatanta shi da na Ilham amma sam babu haɗi, tsayin Ilham bai ko kusan nata ba. to wacece wannan ɗin?, tabbas ya zamar mata dole taje gidan Alƙali Dikko da ƙafafunta, idan aljanu sun kasa ita ba zata gaza ba domin ba ta taɓa barin wani ya shiga gaban al'amarinta, dole sai taga bayansa ko waye.
ta numfasa tace,"shikenan me girma boka, yanzu ya batun mu na janyo hankalin Alƙali Dikko kaina?".
Bokan ya bushe da dariya yace,"kin haƙura kenan, ai nayi zaton har yanzu kina kan bakanki na cewar son gaskiya kike so Dikko yayi miki ba sai anyi amfani da asiri ba gudun lalacewa wataran".
tayi shiru kamar ba zata ce komai ba sai tace,"mu bar tuna baya. yanzu dai a san abinyi akan Mai martaba, a kashe shi kawai na huta da aurensa da ke kaina. shi kuma Alƙali ayi aikin da za'a gama da rayuwarsa kawai, ina nufin ya saki kowa ya kamani ni ɗaya hatta kuwa da mahaifiyarsa. tashin farko abinda nake so shine Alƙali ya fita daga hayyacinsa yaywa Madina saki uku sannan duk ya kori ƴaƴansa, daga baya kuma sai ya dawo kaina ya mallaken ta yanda zamu yi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 36 Chapter of 73